Chapter 1 Reading Zainazain Book 2 Complete By Janafty Arewa Novels

Zainazain Book 2 Complete By Janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   1 / 37

1 to 3K   out of 108.5K words

 *B2ZZ...0️⃣1️⃣*

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

*IS NOT FOR FREE...Via Card ₦300via Bank ₦250, 0552179550...Jamila Umar Gtb or 09069067488..*


*ZARIA*
_Area:Sabongari_
*Anguwan gwado*

"Tunda suka Shigo anguwar Halima ke ta waige waige Tana kallon Wurare Abun ya bata mamaki ganin inda suka Shigo anguwa ce Gatanan dai Sai Cikowar Jama"a ko"ina da kuma Rashin Tsarin Gina ginan Gidaje ko"ina dai gashinan Rakwachan kawai Haka Take gani acikin Idanuwanta In sun Hada ido da Farida sai dai kawai ta sakar mata Mirmishi Itama ta maida mata Martanin Mirmishinta ammh Azahirin gaskiya Jikin Halima ya gama yin Sanyi Tana Tunanin Ta shigo wani Fannin Rayuwa kuma na Dabam.

Hankalinta ya Tsaya ne Cak Dataji Farida na Fadin Mai Adaidaitan ya Dakata anan Da Sauri ta Dago kanta Tana Kare ma Inda suka Tsaya kallo,tunda Suna Cikin adaidaitan Ta Hangi Dandanzon Mutane maza da mata Suna ta Shige suna Fita,Tana chan Tana kalle kalle Taga Farida Ta Fita Daga Cikin adaidaitan Ta Bude jakarta Ta zaro Naira Dubu Ta mikamai ya karba yana Ta Godiya,Lokaci Daya Ta Juya Tana kallon Halima Data kasa Fitowa Daga adaidaitan Tana Fadin''Sa"adiya Fito mana mun iso.."

Jin Haka yasa Halima ta Gyara zaman mayafin kanta kana ta Sako Kafarta ta Fito Tana kara Jan Sikat dinta Daya kaimata Har kasa yana neman kadata Lokaci Daya kuma tana kara Damke Dankwalin Dake Hannunta,Tunda mai adaidaitan ya Saukesu Ido ya Dawo kansu Kamar Dama su ake Jira Riko Hannunta Farida Tayi Ta nufi wani Mulmulallan Gidan Siminti Ginin zamani Wanda yake Shafe da wani Fenti mai kurzukurzu kalan Ruwan kuka Daga Kofar Gidan akwai manyan Dakali Dama da Hauni Daga Gefensa kuma akwai wani katon Smybol da akayi Rubutu da Manyan Baki *GIDAN ABINCI NA UWAR MATA* Taga an Rubuta kana ta kai Duba da wajen Data ga Zirga Zirgan mutane maza da mata yafi yawa sai taga Daga bakin Wajen Tana Hanga ciki Waje ne Falo Babba,Wanda aka kawatashi da Kujeru da Teburan cin Abinci Rukuni Rukuni,Mutane Dai dai ku suna kai suna cin abinci Duk da bata Shiga wajen ba ta Fahinci Irin Gidan Abinci ne namu na Gargajiya ammh an zamanantashi.

Kofar Da zata sadashi su da Shiga Cikin Gidan Dake Hade da Gidan Abincin Farida Ta Nufa Tana Rike da Hannun Halima Namiji Daya ne ke zaune kan Dakalin Sai wasu mata Biyu sun sakashi a Tsakiya kowacce kanta ba Dankwali sai Uban gashin Doki kuma Dukkansu Suna Sanye da Shigace ta Banza Wanda ya bama Halima mamaki na yadda mace Zata iya Fita Har Waje ta zauna cikin wannan yanayin.

Namijin ne ya mike da Sauri ya sha Gaban Farida Yana Washe mata baki Gefe Daya yana Kura ma Halima ido Wacce ta koma Bayan Farida Ta Rabe Tun bada ga Irin kallon Banzan da Matan Dake zaune suke Jifanta dashi ba Ga kuma wannan Bakin Namiji Wanda Shaye Shaye ya maida shi Wani kamar mahaukaci.

Cikin Mamaki da Hade Fuska Farida tace"Kacharalle Lafiyanka kuwa..? Bani Hanya na wuce..?

Tafada Cikin Hade Duka Fuskarta Cikin Washe mata Jajayen Manyan Hakoransa yace"Allah taimaki Sholly dinmu..Allah ya Taimaki manyan Mata naku ba irin namu bane.Allah ya Taimaki Shalelen Uwar mata..Allah Huci Zuciyar Hajiya Sholly Dama Sannu da zuwa zan yi miki kawai..'Yafada Lokaci Daya yana kara Kure Halima da wani kallo Har yana wani karkace kai Tabe baki kawai Tayi taZuge Jakarta Ta Zaro 1k ta mikamai Tana Fadin"'Karbi..aje asha Ayi Tatil..Dama Ita kazo nema ba Sannu da zuwa kazomin ba.."

Tafada Tana kokarin Jam Hannun Halima ammh sai yaki bata Hanya Karban kudin yayi Yana wani Sosa gemunsa Dashi Ganin irin kallon Dayake ma Halima ne yasa Jikinta ya Fara Rawa ta kara Rabewa jikin Farida Idanuwanta sun Cika da kwallah Cikin Fusata Farida Tace'Bamu Hanya Kacha..."

Dariya ya saki yana Fadin"Miye na Fusata..? Abun bana Fada bane daman wannan Haja nake Tambaya Sholly itama yar Eh ya nen ne..? Da sauri Tace"Kul...Karka kuskura Wannan ba irin wacce ka sani ba..Wutsiyar Rakumi Tayi nesa da kasa Kar in kara ganin kana kallonta.."Da Sauri ya Daga Hannu alaman Saranda yana Fadin"Na Tuba nabi Allah na Biki...Shalelen Uwar mata ai in nakara sai ki saka Ta Korani na Shiga Duniya na lalace ko ba Haka ba Suby..?

Wacce aka Kira da Suby Tawani Juya ido Tana Fadin"Uhm...mutum dai yasan Uwar mata Ta hana kawo Wata bakuwa gidanan sai da izininta.."Tafada Tana Wani Taunan Cimgam Tana kuma kallon wani Barayin Farida Ta Ja Hannun Halima suka Shige Tana Fadin"Ki kirata ki Fadamata Ni Sholly na kawo Wata Bakuwa bada saninta ba Kinji Suby..? Karamar yar iska kawai."Daga haka suka Shige Suka bar Suby na tura baki Tana Kunkuni Kachallare ya Kwashe Da Dariya Shida Adamalli Wacce Ta kalli Suby Tana Fadin"Ashe dai kina Tsoron..?

Suby Tace"Bana Tsoronta...Ita din Banza..Karuwanci Take shi nake yi bata isa naji Tsoronta ba.."Kachallare ya karkace kai yana Fadin"Yo daman Uban wayace ba karuwanci kike ba Suby..? Ammh kema kin sani Duk Lalacewar Daji bai kai in Giwa ta Mutu Kiyashi Yajata ba Kinsan kaf karuwan Gidanan ba wacce Ta kama kafar Sholly Daga Sabbin Har Tsoffin su ku Wlh Baku kama Kafarta ba Yarinya ga kyau da Dirin mata ga Farinjini Sholly Tana Iskanci ammh nata mai aji ne Suby kema kinsani Gata dai Cikin Batattu irinmu ammh Zuciyarta mai kyau ne Shiyasa ta zama ta gaban Goshin Uwar mata bata da kamarta ko ya kika ce Adamalli..?

Hannu Ta bashi Suka Tafa Kafin Ta Saki Guda Tana Fadin"Wlh Kam Fadi ka kara Kacha..mai Hassada da Sholly sai da fa ya yagaji ya Bari..Ta samu Duniya Allah ya Daga Tauraruwarta Inda Taso Bazata zauna acikin Gidan ba Domin Tana da kudi Tana Harka da masu kudin Shiyasa komai tace Uwar mata bata Musu da ita saboda Tana Ijiye mata yan Bugun Abuja.."Kacharalle yace"Sosai..Zainabu abu zakice mai mganin Tsofaffin zamani.."Suby Data Cika da Batse ta mike Fuu Ta Shige Cikin Gidan su Adamalli suka Rakata da Dariya.

Kimanin Dakunan Dake wannan Gidan goma sha Biyu ne12 kenan Shida ajere Shida ajere kuma kowanne da Room Lambarsa ajiki Tunda Ga Room1 har zuwa Room 12 gida ne dan madaidaici mai karamin Tsakar gida ammh yana Shafe da Siminti,Suna Shiga suka ga wasu mata Biyu Zaune Suna Buga Lido,kofar wani Daki Dake kulle da kwado Lokacin da Halima ke kare ma Sauran Dakunan kallo Babu wanda ke Bude sai Guda Daya Shima kamar an sakayoshi ne Suna Shigowa yan matan Dake Buga Lidon nan suka Juyo suna kallonsu Ba Farida suke kallo ba Sun fi kura ma Halima ido Suna kallonta Cike da mamaki Itama su Take kallo Cikin mamakin Shigar da yanayinsu Daya Tana sanye da Gajeren wando na maza da wata Half vest,Dayan kuma Daurin Kirji ne da karamin zani Duka Cinyoyinta Suna Waje kawunansu ba kallafi Kowace gashin doki ya Zubo mata.

Cikin Mamaki Dukkansu suka Mike Farida kuwa Cikin Daka musu Tsawa Tace"Wani irin iskanci ne kuma wannan Zuly da Deeze..? Kofar Daki na ne ya zama Dandalin Buga Lidonku..? Ku ina naku kofar Haraban..?

Cikin Sanyin Jiki Wacce aka Kira da Zuly Tace"Yi hakuri Sholly ba..."Ku kaucemin Daga gani Don Allah bana son wani Dogom Turanci kada wacce ta karamin wannan iskanci...Kowaccenku ta Tsaya Inda aka ijiyeta bana son Iskanci da Burauba Wlh.."Tafada Cikin Bacin rai Lokaci Daya Tana Hararansu ba Gaddama suka Duka suka kwashe komai nasu suka Wuce simi simi suka koma Kofar Room8 suka Kafa achan Farida Ta Rakasu da Tsaki Tana Fadin"Kananan kwari.."

Daga haka ta karisa Jikin Kofar Ta Bude Jakarta ta Fiddo wani karamin key ta Zura ta Bude katon Kwadon Dake Jikin Kofan kafin ta waigo Tana Fadin"Bismillah Sa"adiya..Shigo ki yi wanka kici Abinci ki Huta ko..? Halima Tayi Mirmishin yake kafin tace"Nagode Anty Farida.."Lokaci Daya Tana kokarin Cire takalminta Farida ta Dakatar da ita da Fadin"A"a shigo Dashi Ciki."

Cikin suka Shiga Tana Bin Bayan Farida suna Shiga Farida ta saki Labulan Dakin Loksci Daya da sakayo Kofar Zully ta kalli Deeze Kafin Cikin Rada Tace"Wai kinga me nake gani..? Kardai Bayan karuwanci Bin mata Sholly ta koma..?

Deezee tace"Hm...Bansani ba..Nidai Zully kyaleni da wannan Gulmar Koma menene ta koma ina Ruwanki Bariki gidan fa kazo ne nazo ne..Ko Uwar mata da muke karkashinta Bata ce maa Dole ga Abunda zamu yi ba Kowa Abunda yaga Dama yake aikatawa ai Yancin kenan.."Zully Tace"Lalle fa..Ammh ai ta Karya Dokar Uwar Mata Tunda Tunda aka samu mtsala kan wannan Yarinyar da Samira ta kawo Uwar mata ta hana kawo wata Bakuwar Fuska batare da saninta ba.."Deezee na Sosa kanta Tana Fadin"Kowa ya iya allonsa ya wanke Zully..In kikace Gulmar Sholly zaki yi Tayi haka zaki kare...Sai ta Biya allonta Tawanke tazo ta Hada da naki  ta karanta kuma ta Biya ta wanke Bariki ai gidan kazo nazo ne...Ammh kisani itama Shigowarta Sa"a ce Wanda yayi Sa"a ya gama Dacewa kamar Sholly.."Jin Deezee bata bata Fuska bane yasa Ta bar mganar suka Cigaba da Buga Lido Dinsu.

Halima mamaki ya Daskaran da Ita ganin irin kayan More Rayuwan Dake Dakin Farida Daki ne Babba mai Ciki Daya sai ta saka wasu Hadaddun Labulaiya Ta Raba Falo da Uwar Daka Daga yammah ga Kofar Tiolet afalon akwai kayan kallo Kujera guda Biyu Daga kasa kuma karamin Cafet da Center Table,Daga chan kuma Gefe wajen kofa kayan Girki ne kama Daga gas Tukunya Filets Da kofuna Da sauransu sai kwalayan su Indomie Macaroni Cuscus,Taliya Madara Da sauran kayan Tea,su Complex da kwai ne Tarkace dai gasunan su Kittle ne Kaya dai gasunan kamar irin Kitchen Tunda ga Duk alamu nan take Girki Halima bata kara Sakin baki ba sai Da Taga ta Dake Labulan Daya Raba Dakin Ta Hangi Wata Dundumemiyar katifa Kwance akasa Dataji Shimfidu alfarma,Sai Gefenta kuma wani katom Wardrope ne mai kofa Hudu samansa kuma Tarin akwatuna ne masu kyau da Tsari Daga gefe kuma ma"ajiyar Takalma ne da jakunkuna Dakin in ka kalleshi zaka Fahimci cewa Dakin ne yayi kankanta da anga kaya acikinsu Kodaga yanayin Faridan zaka Fahimci yar gayu ce ta Karshe kuma Ta Shigo Harkan bariki a sa"a ta Tara Dukiya Domin kayan Kudi ne Duka Suka cika Dakin kuma Duk Gidan Dakinta yafi ko"ina Girma kuma ita kadai keda Tiolet aciki ba saboda komai ba sai saboda ita yar gaban Goshin Uwar Mata ce Tana Matukar ji da ita.

Gyalenta ta Cire da jakarta ta Wurgasu nan saman katifan kana ta Cire takalminta ta watsashi nan gefen mika Tayi alaman ta gaji Sosai barci ne ma a idanuwanta Domin Jiya Alhajinta bai barta ta Runtsa ba, Juyowa Tayi ganin Halima na kallonta yasa Tace"Sa"adiya Taho ki zauna mana kin Tsaya atsaye..'

Halima Ta kasa gaba ta kasa Baya sai da Farida tazo Ta Riko Hannunta Zuwa Gefen Gado Ta zaunar da ita Tana Fadin"Kinga inda nake Rayuwa ko Sa"adiya.? Zaina ta kalleta Tana gyada mata kai bata Damu ba Ta Mike Tana Fadin"Kafin na ce miki komai dai bari na kunna Gas na Saka miki Ruwan Dimi ki Shiga ki Watsa kafin ki Fito na sama mana Abunda zamu ci ko..?

Kai Zaina Ta Daga Tana Jin Taruwar Hawaye kafin tace"Toh.Anty Farida.."Farida ta Saki kayattacen Mirmishi Tana kallonta Kafin tace"Ban taba ganinki ba sai yau..Ammh naji Lokaci Daya Zuciyata ta yarda Dake..Kuma Ta bani Damar kar na bari ki Tafi Tunda na Fahimci Kina cikin wani Hali aklllah Farko Danayi miki sai najiki kamar wata kanwata ta Jini,Da kika kirani da Sunan Anty Farida Sai naji Tamkar kanwata Zahra ce ta Kirani..Wanda Rabon da naji an Kirani Farida Tun ina Aisha Faridata kafin na koma Sholly.."

Tafada Cikin wani yanayi Lokaci Daya Kuma da Taruwar kwallah acikin idanuwanta Zaina Tana kallonta da mamakin kafin tayi mgana Tayi Saurin Juyawa ta Share kwallarta Ta Fara Kokarin kunna Gas nan take ta kunna ta Dora wata Karamar Tukunya ta Bude wani karamin Botikin Ruwa ta Diba ta Cika Tukunyar kana ta saka Murfi Ta Rufe ta koma Kusa da Zaina Dake Zaune Gefen gado Tana Binta da kallo Tace'Sa"adiya me zaki ci.?

Zaina Ta Sunkunyar dakai kafin Ta Dago Tana Fadin"Bakomai Anty Farida..Bana jin Cin komai...Da Farko na Fara Nadaman wani abu ammh Haduwata Dake ya sakamin Natsuwata Nagode Anty Farida.."Tana Fada sai ga Hawaye Sharr Farida Tace"Ashh...Sa"adiya Bar kuka Taho..Ta jata Jikinta Ta Rumgume kawai Sai Zaina ta saka mata wani marayan kuka Tana Fadin"Anty Farida naji nayi Rauni gabadaya na rasa kwarin Gwiwata ban kyauta ma Umma ba ban kyauta ma Abba ban kuma kyauta ma Firstlove ba...Taya taya zan saka Rauni a Ahalin da suka maidani Mutum Anty Farida na zama Butulu Saboda Dalilin Tseratar da Aurena da Cikin Dake Jikina Na baro Mutanen da bani da kamarsu Duk Duniya na gwammace na Shiga Duniya Allah na Tubaa yanzu In da ban Hadu Dake ba wata Rayuwa zan Fada..?

Take Fada tawani Kuka mai Raunana Zuciyar mai Sauraro Ita kanta Faridan Sai da Jikinta yayi sanyi ta Fara Lallashin Zaina kafin ta Dago Tana Share mata kwallah Tana Fadin"Tun kallo Farko Da nayi miki naga alaman Sabon Ciki Tare dake.."

Ido Zaina ta zaro kafin Tace"Dama ana gane inada ciki Anty Farida..? Mirmishi Farida Tayi mata Har Hakoranta suka Bayyana Waje ta Mike Tana Fadin"Eh..Ga duk macen Datake iya gane alamun hakan ba...Aganin Farko Danayi miki da yanayin Tsarinki da Shigarki na Fahimci ke ba Mutuniyar banza bace..Na farko akwai yarinta Tare Dake barin ki Haka zai sa ki Fada Hannun Banza Shiyasa na zabi Tahowa Dake inda nazabi Rayuwata Duk da nasan zaki ta mamakin Me ya kawo ni nan ko..?kinga abubuwa wadanda baki gane ba ko..? Nan ba Gidan kowa ba ne Gidan KARUWAI ne wanda muke karkashin Uwargijiyanmu Wato Hajiya Hauwa Uwar mata.."
Zaina ta kwalalo Ido kafin Ta Dafe Kirji Tana Fadin"Mun Shiga uku gidan karuwai Anty Farida..!?

Tana Mirmishi Tace"Kwarai kuwa Sa"adiya...Nan din Gidan Karuwai ne Duk wacce kika gani agidanam Karuwa ce zaman kanta Take da Zaman yancin kanta.."Cikin Faduwar gaba Zaina Tace"Har...Harda ke Ma Anty Farida..Ke...Karu..."

Ta kasa karisawa Saboda mganar Ta mata Nauyi kana kuma Wani Tsoro ya Shigeta Farida Ta saki Wani Mirmishin Dayafo kuka ciwo kafin Tace"Eh Sa"adiya...Ni nan da kika ganni Karuwa ce mai zaman kanta Da kudin Kariwanci nake komai nake kuma Rike kaina nasan zaki mamakin Meyasa banji kunya Fada miki Haka ba..? Domin wasu Karuwan in sukaje wani waje sai su rika Boye zahirinsu ko..?ni Aisha Farida bana karya bana kuma mu"amala da mai karya Duk inda na Taka ban zan ji kunyar Fadin Ni Karuwa bace Domin Tunda uwa da Uban da suka kawoni Duniya suka Kirani Karuwa Toh me ya Ragemin Sa"adiya..? Mijina wanda na bama Duka Soyayyata da kaunata Ya kirani Karuwa akwai Saura ne..? Ya'yana dana Haifa da Cikina Suma an gaya musu ni karuwa ne ina da Wani Sauran Boye Ko kuwa Wani Sauran Kima acikin Wannan Duniyan ne Sa"adiya..!Babu Wata Sauran Kima Shiyasa a ko"ina bana jin kunyar Fadin Ni KARUWA ce mai zaman kanta.."

Ta Fada Lokaci Daya wasu Zafafan Hawaye masu zafi Suna Biyo Kuncinta Zaina ma kuka Take Cikin Tarin mamaki Take Fadin"Dama..Dama kina da Aure har da ya"yana Anty Farida..? Toh duk suna ina da Kuma iyayenku me kuma kika aikata suka kira karuwa har yasa Rayuwarki ta koma Haka..? Hakika zan so naji labarinki Anty Farida Ada ina kallon Nawa Labarin yafi na kowa sai kuma yanzu na Fara Tunanin naki Labarin ba komai bane akan Nawa.."

Farida Bata Juyo ba Tana So Tayi Control dinta kanta karan Wayarta yasa tayi Saurin Share Hawayenta Ta juya ta Nufi Wayarta Tana ganin sunan Uwar mata na Kira Ta Tabbatar da an kai mata Rahoton Dawowarta Da Sa"adiya Bata Daga Kiran ba sai ta yanke ta saka Wayar Cikin Mode ta Tura ta kasan Filo Kafin ta Waigo Ga Zaina Tana Fadin"ki bari zan Fada Miki komai ammh ba yanzu ba..Yanzu Tashi zakiyi kiyi wanka Kiji Dadin jikinki.."

Tana Gama Fadin Haka ta Juya Zuwa Cikin Tiolet din Ta Dauko Wani Botikin karfe tazo Ta Zuba maZaina Ruwa ta Surka mata Ta Dauka Ta kaimata Bayi Tace Taa Tashi Ta Shiga jikin zaina asanyaye Tatashi Ta Cire mayafin Kanta Farida ta miko mata Babban Towel tana sakarmata Labulan wajen Domin Ta bata Damar Cire kayanta ganin haka yasa Zaina ta Tube kayanta ta Daura Towel din Ta kuma Rufu da gyalenta kana Ta Fito Koda ta Fito ma Farida Bata Dakin ta Fita da Sauri Ta Bude Tiolet din Ta shiga sai Tashin kamshin Dettol yake Tiolet na Na kashin mai Floshing ne,Bayin Tsaf Dashi Komai na Bukata akwai acikin Cikin Natsuwa Zaina Tayi wanka Ta Dauro alwala Ta Fito Ganin Duhu ya Shiga Gashi Batayi Salollin Dake kanta ba.

Tana Fitowa ta Iske Farida na Soya kwai Tana ganin ta Fito Ta ce ta Shiga Ciki ga kayan nan ta Dauko mata ta saka ga Darduma  nan ta Shimfida mata Tayi sallah da Toh ta amsa kafin ya Bude labulan Daya Raba Dakin Ta Shiga Ta iske ta Dauko mata Wata Hadaddiyar Doguwar Rigar yar Dubai Tana da Irinta Wanda Firstlove ya Siya mata Tuna Haka yasa sai da ta Share kwallah Zura Rigar Tayi Tana so Tace Hijabi Taga wani mai kyau kusa da kayanta Farida ta Ijiye mata Ta Dauka ta Zura Ta Tada Sallar Azahar,bayan ta idar tayi La"asar kafin ta zauna Tayi Zugum Tana Tunanin Wani Hali kuma Chan Bauchi yake..! Tasan Zuwa yanzu sun samu sakonta..!

Shigowar Farida ya katse mata Tunani inda Tace bari ta Shiga wanka,Wani Babban Towel ta Dauko Ta wuce Bayi bayan ta Fito ne Itama Tayi Sallolinta Lokacin ana Kiran sallae mangariba suka Mike suka Gabatar suna Idarwa Farida Ta Ja Hannun Zaina suka koma Falom Suka zauna saman Cafet Ta jamata Farantin Data Hada komai Indomie ne ta Dafa sai kwai DataSoya sai kayan Tea Zaina Tea dim kadai Tasha kwan kuma ta Fara ci kenan Sai Tatashi Da Gudu Zuwa Bayi sai Amai Farida Ta Taimakamata ta Wanke Jikinta bayan ta gama Kana Tazo ta matsa mata ta kara Shan Tea din Tunda bata son kwan itama sama sama Taci Indomie tace ta Koshi Ta hada komai Ta kwalama Zully Kira wacce suke Tsakar Gidan suna ta Shewa sai gashi Tazo Daga Kofar Dakin taTsaya Farida ta Leka Ta mika mata Farantin Ta karba Tana ta Godiya mamaki ya kama Zaina Bata dai

1 / 37