Author : Jamila Janafty Category : Romantic Hausa Novels
ta bar wannan Harkan.."Salati su Hajiya Mama suka Dauka Zulaihat da Zaina suka kalli Juna suka Hada baki Wajen Fadin"Uwar Mata ce..!
Alhaji Tsoho yayi Mirmishi kafin yace"Bazata so Ta bar wannan Harkan ba kamar yadda kuka bada Labari Tunda Tana samun Kudi ta Bangaranta kada ku damu Zata Dawo Daidai da kanta zata ce Zata koma ga ahalinta da ya"yanta Tunda kun Riga kunzo bazan Taba bari ta koma Chan ba Insha Allahu Zata koma Cikin ahalinta wanda duk inda suke sun Dade da yin Nadama yanke Hukunci Cikin Fushi da Rashin Bincike.."Kowa ya gyada alamun gamsuwa Kafin Alhaji Tsoho ya kalli Baban kaduna yana Fadin"An kira Sallar La"asar ko Bashir..?
Baban Kaduna na Duba agogon Hannunsa yana Fadin"Yanzu dai za'a kira Alhaji Tsoho.."Gyada kai yayi yana Fadin"Sai mu tashi muyi sallah..Halima tafi da baki Dakin Hajiya Mama abasu abinci kuci kuyi wanka da Sallah ku huta ita Faridan ku kyaleta Tayi kukanta kada kuce mata komai..Hannatu da Rukayyah da Ke Umman Zareena ku Shirya ku mika Zafeeraa Dakinta Alhamdulillah yau Komai ya zama sai Godiya ga Allah kai Takwara na Babba Rufemana Taron da addu"a.."
Sadiq babba Shi ya Rufe Taron da addu"a kafin Taron ya watse Zainab da Shema suka kama akwatunan Su Zaina zuwa Dakin Hajiya Mama Umma da Nene suka karbi su Anun su Inna Hannatu da Inna Rukayyah Dake zaune gefe duk al"ajabi ya kamasu suma suka mike Zaina da Zafeera suna Rike da Hannun Juna Ta Riko Hannun Zulaihat Suka Nufi Dakin Hajiya Mama Sauran kawayen Zafeera suna Wani Daki Ganin mganar ba nasu bsne basu Fito ba su Hamdiya suka Biyo Bayansu Harda Dina su Abba kuma dasu Haddir suka Fice da Alhaji Tsoho Domin su Daura alwala su Tada sallah
Suna Shiga Dakin Hajiya Mama suka Iske har Farida ta Shiga Tiolet tayi alwala Sai Zainab ta bata Darduma da Wani Dogon hijabi Zaina na Rike daHannun Zafeera kamar wani Zai Rabasu Dina ta Shigo Dakin Kai tsaye wajen Zaina ta Nufa tana Zuwa sai ta Rumgumeta Gabadaya sai kowa ya saki baki ana kallon Ikon Allah kafin ta Dago Tana Mirmishi tace"Almdulillah..Ina Murna da Dawowarki Gida zaina."
Cikin karaya da Hawaye acikin Idanuwanta zaina tayi yake Tana Fadin"Nagode Dina.."Kawai ta iya Fada kai Dina ta gyadaa mata kafin ta Kada kai Zata Fita sai ga Arman ya Shigo da dan Gudunsa na yara Jalal ya Biyosa yana Fadin yazo suyi alwala Ganin Dina yasa ya makaleta yana Fadin Momy Cikin mganarsu na yara ita kuma sai ta Rikeshi Tana Tambayan Jalal me yafaru nan yake Fadin Uncle Faruq ne yace suyi alwala suzo suyi sallah Shine ya gudo Cikin Gida.
Dina Tayi Mirmishi Tana Fadin"Kai baka son Sallar ne..? Jalal kamasa kuje ka nuna mai yayi ko Arman din Nene da Umma.."Kai ya Dagamata yana Dariya kafin Jalal ya Rike hanmunsa suka Fita Dina bata waigo ba itama Tabi bayansu Zaina Data Daskare saboda mamakin ganin Arman ta Dago Tana kallon Zafeera kafin tayi mgana ta Rigata da Cewa"Aliyu zainullahi Usman Saulawa Arman keman Shine Cikin da kika Tafi kikar bar Dina Dashi.."Zaina tayi Jagale gabanta na Fadi tace"Toh...na..naga taana da wani Cikin kuma.?
Zafeera ta Kauda kai Batayi mgana ba Hajiya mama da Goggo Halima Dake Kofar Dakin suka kariso Goggo Halima Tace"Wani Cikin ta samu..Bayan ta Haifi Arman tayi arba"in an Daura musu aure da zain.."Kowa sai ya kura ma Zaina ido Farida Dake sallah Bata idar ba ta sallame haka zulaihat suka Nuna mamakinsu.
Cikin Lallami Hajiya Mama ta Dafa Kafadar Zaina ganin tayi ma Goggo Halim kuri da ido wani abu na sukan Ranta wanda bata iya gane komai ba tace"Kiyi Hakuri Zaina..Komai ya wuce an zama Daya kaddaran Zuwan Arman ne ya Haifar da komai kinji kada ki Damu kanki kowa ya Tabbata kina nan a Sanyin Idanuwan zainullahi.."kowa Abunda Zaina Tayi sai da ya basu mamaki Mirmishi ta saki kafin tace"Laa..Hajiya Mama bakomai Wlh..Hakan yayi daidai ma..Allah sarki Arman na Tabbata ba zai tashi Cikin Gori da maraicin wani bangare ba."Daga haka bata kara cewa komai ba ta Sabule Jikinta Ta Shige Tiolet ta barsu nan bata yarda Tayi kuka ba ko kadan Domin ai yanzu Ita ta Riga ta san Rayuwa ta kuma san Juriya ammh in tace bata jin Kishi Tayi karya sai dai kawai ta Shanye wajen nuna Gogewarta arayuwa yanzu.
Wanka Tayi ta Dauro alwala ta Fito kamar ba ita ba kana tace ma Zulaihat ta Shiga ta Watsa ruwa Mikewa Tayi Tana Tambayansu Anun Hajiya Mama tace suna Chan Dakin tare dasu Umma Tanayi ma su Anun din wanka,Kowa sai mamakin Zaina yake yadda bata nuna komai ba da kuma mamakin ganin Takara Cika da Girma Har Farida sai da tayi wanka suka Sauya kaya suka zo sukaci Abinci suka Koshi Zafeera sai kallon Zaina take duk inda tabi Hardai Ta gaji da Daka mata Duka Tana Fadin"Wai wannan kallon fa..? Bafa ya Haddir bane Jira Lokaci kadan ne yanzu zaMu mika ki kije Chan kiyi ta kallonsa ki More.."
Mikewa Zafeeran Tayi zata Rama Dukanta Zaina ta Boye Bayan Farida Tana Fadin"Anty Farida kin ga Ukti Ko..?dukana Zatayi Daga na gayamata gaskiya."Farida na Dariya tace"Yi hakuri Zafeera..Ko Mutuwa tana Jin kunyar Uwa da Anty saboda haka Raga mata..'Zafeera tace"Badai son kai ba Ko Anty Farida..?
Farida tace'Wlh ba son kai..Waya isa ya Shiga Tsakanin ku..Jata ki Rama.."Zaina na Jin haka ta kwabe Fuska mai Su Zainab zasuyi in ba Dariya ba Zulaihat ma Dariyan Take Tana Fadin"Kullim kafin mu kwanta sai Sa"adiya Ta bani labarin Rayuwarta ita da Ukti Zafeera...Sai da na ganin ma Idona na Tabbatar da abun ya wuce yadda take fada..'Nan su Zainab suka zauna suna bama su Farida labarin Tashin su Zafeera su kuma Rigima Har Falo sai da Goggo Halima da Hajiya suka Raba Fadan Kowa kagani Fuska Cikin Farinciki Sai da suka Matsa gefe ne Zafeera ke Fadin Zaina ta Cika ta zama wata Big Mama ita kuma Tana Dariyan Farincikin yau gata Cikin Damginta tace mata Haihuwa ne ya Budani kema kwana nawa ne..? Yadda naga Idanuwan Ya Haddir bazai yi wasa ba.."
Duka Zafeera ta kaimata Tana Hararanta kafin su koma Hiran Rayuwa nan take Fadamata Laila Tayi aure Zaina tace Dole taje gidan Laila Allah Sarki kawar Amana kana ta koma bata Labarin Abubuwan da suka Faru bayan Tafiyarta da Tashin Hankalin da suka Shiga da Ciwom zain da Barin gidansu da komai da auransu da Dina Zaina Sai hawaye suna ma Cikin mgana basu gama ba,Su Inna Rukayyah suka Tada Hiran suka Tafi da Zafeera suka Shiryata Koda 5pm Tayi an gama Shirya Amarya sai kuka Take Tana kuma makale da Zaina kamar wani zai kwace Mata ita su Anun kuma sun zama yan Gida Suna Kwakwame da kakaninsu Nene da Umma su Farida ma suna Cikin su Zareena ana ta Hira yadda kasan an Shekara Tare.
Daddyn Abuja Shi ya Dauki Amarya amotarsa ita da Zaina da Goggo Halima sai yayar Mama Safiya sai Faruq Daya Shige Gidan gaba,su Farida Motar Sadiq babba suka Shiga,ita da Zulaihat da Zainab da Shema su Anun na Tare dasu Umma Direban Abba ya Daukesu Dina ma Motar Kwamishina suka Shiga Tunda Gobe zata koma,Hajiya Batula sai bata Wasu Shawarwari take kan kada Tace Zatayi Kishi Da Zaina aran Dina tace me zai kaita Ai Zaina tayi mata Nisa Sosai Arman kuma yana Tare da su Zareena da Jalal Motar Haddir suka Shiga wanda Sadiq karami ke janta Sauran kawayen Amarya kuwa Abokan Haddir suka Daukesu sai Gidan Zafeera.
Har kan gadonta dayaji Shimfidun alfarma zaina takai Zafeera sauran kuma suna ta yawata Gidan suna ta Dubawa suna Santi Zaina dai na Tare da Zafeera Tana ta bata baki Ba"a Dade ba Bayan an gama gyare gyare Akace azo atafi Duka aka Tarkatasu Domin Umarnin Alhaji Tsoho ne ba wanda zai kwana Tunda kusa ne kuma an gama komai..!Zafeera taso ta Rike Zaina Tana kuka Umma ta Hana tace ta wuce su koma Gida Zafeera naji Tana gani Kowa ya Fice ya barta ita kadai Tana kuka Zaina na ta yi mata alamun Sorry din nan shi ke kara sakata kuka.
*Janafty...*
8/9/21, 3:25 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ....B22️⃣7️⃣*
*IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*
"Gidan Alhaji Tsoho suka koma ana ta maida Zence Goggo Halima Tuni ta kira yan Chan Gada ta sanar dasu dawowar Zaina wasu basu yarda ba sai da ta Hadasu sukayi mgana da ita ta waya kana suka yarda nan da nan sukace gobe suna kan Hanya Dole ne suzo su Taya Iyalan Alhaji Tsoho Murnan Dawowar Halima.
Su Anun kuwa sun zama yan gata Suna Wajen Abba ya Dauki jikokinsa yana jin wani Farinciki mara Misaltuwa Farida kuma Tana Tare da Zareena sai Hira suke kamar Sun Dade da Haduwa Zaina Taji Dadi ganin babu wanda ya nuna kyama ga Farida Zulaihat kuma duk suna Tare dasu Zainab.
Dina ma duk suna nan Tare sai Dare Zaina taga Arman ta Daukeshi Tana kallonsa sai Tsausayinsa ya kamata ta Rumgumeshi Tana Fatan Allah ya Rayashi Kowa yaga Jarumtar Zaina Umma acikin Ranta tace Zainata ta karo Ilimin wani abu Boye da Damuwarta da kuma Rashin Nuna gazawa uwa uba kima Taga Juriya acikin Idanuwanta Lalle wata Tafiya Mabudin ilimi ne kamar yadda ta kasance Wajen zaina.
Basu koma Gidan Abba ba sai Dare bayan sun ci Abinci nan Gidan Alhaji Tsoho Direban Abba da Sadiq ya kwashesu Zuwa Gida nan sukabar su Mama Safiya da Danginta Su Kuma suka Dawo Gida suna Dawowa Zareena Taja Farida Zuwa Dakinta Datake sauka su Kuma su Zaina suka yada zango Dakinsu na baya ita da Zulaihat sai Shema Data Biyosu ita kuma Zainab ta koma Dakinta Suna Gajiye ne kowacce sallah kawai sukayi suka kwanta su Anun kuma Suna Tare da Abba sai Wajen 10pm na Dare ya Dawo Tare dasu Anun dasu Faruq, Lokacin Tuni Zaina Tayi Barci Nene ta karbesu Tayi musu wanka Ta basu Tea suka sha sun Fara Rigima Daga Baya sukayi Shuru barci ya Daukesu Dina ma Tare suka Dawo Sai Su Umma sukace Tatafi Shashenta da Hajiya Batula dasu Waleed Taji Dadi kuwa ta kwashe Suka Tafi zam sufi samun kyakyawan Sakewa.
Haddir Ango kuwa ba wanda ya Rakashi Zuwa Gidansa Shi kadai ya Tafi bayan ya Tsaya kan Hanya ya siya kazar amarci Da madaran Holladian ya Shiga Dashi Ciki Duk da ba auran Soyayyah sukayi ba,Ammh bai Taba Jin ya Tsani Zafeera ba Tunda dai Iyayansu sunga Dacewarsu Tare yakamata su zauna Suyi ma Juna adalci.
Sai da ya Shiga Dayan Bedroom din da kayansa da yazo Dashi yayi wanka ya saka Jallabiya kana ya Shiga Bedroom din da Zafeera ke Ciki ya sameta Idanuwanta Biyu Tana ta kuka Zama yayi gefenta Har Tana Saurun Matsawa sai abun ya bashi Dariya Ledan Kazan ya ijiye mata kafin ya Fara mgana Cikin Sanyin murya Farawa yayi da Godiya ga Allah Sannan ya gangaro kan Hakkin iyayansu akansu Da kuma Muhummancn Biyayyaj garesu Daga karshe ya gayamata zasu yi Zama na Fahintar juna amatsayinsu na yan"uwa yayi alkawarin bazai Taba Takura mata,Itama ta saki Jikinta nan Gidan Mijinta ne in Tana Bukatar wani abu ta gayamai Shi zai iya Bakin Kokarinsa Wajen Sauke Nauyin Dake kansa Mganar makarantanta kuwa Hutunta na Karewa yayi mata alkawarin zai maidata kano da Hannunsa Shidai Fatansa ta saki Jikinta su Zauna Lafiya.
Tunda ya Fara mgana Zafeera Taji Jikinta yayi Sanyi ashe ba ka yanke ba ba kyau yanke Mutum Hukumci baka Zauna dashi ba da Farko Kallon mai girman kai take ma Haddir ammh kalamansa yasa ta Fahimci yana da Hankali da Natsuwa sai ta samu kanta Dace mai Insha Allahu bai Takura mata ba yace Taji kazan ta kwanta Daganan yayi mata sai da Safe ya fita Tabishi da kallo Tana Sauke Numfashi Tana Jin yunwa Shiyasa Taji kazan Kadan Ta Kora da madaran ta kwanta Tashi Tayi ta Sauya kaya Zuwa na barci Daman bayan Fitansu Umma tayi wanka Tayi sallarta Fargaba yahanata sauya kayan Tana Tunanin wani abu zai Faru sai gashi ya bata mamaki Ko Hannunta bai Taba ba,addu"a barci Tayi ta koma ta kwanta sai kuma Taji kewar Shema ta Kamata Tare suke kwana sun Komawarta kano Gidan Inna Rukayyah sai ta koma Farincikin da suka Shiga Sakamakon Dawowar Zaina ayau Lalle Allah ne Abun Godiya Tana wadanan Tunane Tunanen bata san sadda Barci ya kwasheta ba sai da Taji Haddir na Tashinta Lokacin ma yayi Shiri Zai Fita masallaci sai Da ya Tabbatar tatashi kana ya Fice Zuwa masallaci.
Bai Dawo Gidan ba sai 6am na Safe koda ya Dawo ta Koma Barci Shima Da Gajiya ajikinsa ya Koma Ciki ya kwanta Wajen Goma yaji Knooking ya Taso ya Bude sai ga Direban Abba da kayan Karyawansu ya karba yamai Godiya ya Tafi kan Dinning ya ijiye komai ya koma Ciki yayi Wanka ya Sauya kaya yana Fitiwa Falo suka Hadu da zafeera itama ta Fito Tayi wanka Gaisheshi Tayi ya amsa Cikinn Kulawa Yace mata suje su karya Tare suka zauna suka karya Duk da ba mgana suke ba ammh Kusancinsu ma wani abu.
Bayan sun gama karyawan ne ya samu Kiran Mom Ilklima Kan kada ya Fito yau ya zauna agida ya kula da Amaryansa yana Dariyan jin kunya yace zai Fita yaje suyi sallama da abokansa Tace Shikenan bai tsaya ba ya gayama Zafeera zai Fita sai ta Fara nuna Zatayi kuka yace Yanzu zai Dawo.
Saboda kada ya barta ita kadai Yana Zuwa sukayi sallama ya Dawo Gidan Zafeera tagama cika Ta Kira Umma Kan Zaina dasu Zainab suzo Umma tace ba wanda zai zo ta zauna agidanta Zaina kuma Tana barcin gajiya Kada ta Dameta Har sai da Tayi kwallah Har Shema ta Kira ammh Tace bazata zo ba sai Gobe in Zasu koma kano Zata zo Suyu sallama Dole Zafeera ta Hakura ganin Haddir din ya Dawo Gidan Tare suka wuni Duk da ba wani mgana ke Shiga Tsakaninsu ba Tabbas sun Debema Juna kewa Abincin Rana da Dinner Dare Duka Direban Abba ya kawo musu Basu da mtsalan komai Sallah kadai ke Tadasu kallo ma daya kunna Bai dameta ba Wayarta take ta latsawa.
Washegari Tun Wajen 10am Sai ga su Inna Rukayyah da Su Inna Hannatu da Shema sun zo mata Sallama zasu Tafi Zafeera Taga ba Zaina Ta Tambayeta Shema tace Taso Zuwa kuma Sai ga yan Gada sunyo waya suna Hanya ammh Zata zo ko Zuwa gobe ne ita da Zainab basu wani Jima ba suka Tafi Haddir ya Dauki Inna Hannatu da iyalanta Zuwa Filin Jirgi suka Hau suka Tafi Inna Rukayyah kuma Direben Babansu Shema yazo ya Kwashesu Zuwa Kano cike da kewar Zafeera.
Su Babban Kaduna da Daddyn Abuja Duk Ranar suka koma Saboda Aiki,Dangin Mama Safiya sai tun Safe suka kama Hanya,Mama Safiya kafin sun Wuce sun Biya sun kara yima Amarya da ango Nasiha,Hakama Daddyn Abuja Duk Sun Biya sun kara yi musu Fadan Nasiha da zama Lafiya kafin su wuce sai Zuwa Dare Umma Ta kirata Ta bata Zaina sukayi mgana kan Gobe Ta na nan Zuwa ita dasu Farida da Anty Zareena yau baki sukayi yan Gada suna na ma nan sai Gobe zasu koma Zafeera tace Tana Jiranta Domin akwai mgana.
Dina kuwa baiwar Allah da ita ake ta Hidima Hajiya Batula kuma Tun Ranar Lahadi ta koma Kano bayan tayi ma su Umma Sallama Da yan Gada suka Shigo Har nan ta Shigo Suka gaisa kana ta Shiga wajensu Zaina suka gaisa Har taDauki su Anun Arman ma yana wajensu Zainab suna ta wasa da su Anun din Abun mamaki yara kamar sun san su Jini Daya ne sai suka saki Jiki Dashi
Zaina bata nuna ma Dina komai ba ko afuskarta Ta nuna Dakewarta da Jajircewarta wanda Bata yarda ta nuna mata wani abu ba,alhalin Allah kadai yasan ya Take ji in Taga Dina kuma ta Tuna amtsayin Zaman wa take.
Yan Gada sunyi murna Da Dawowar zaina aka nuna musu Farida Da Zulaihat amtsayin Wadanda suka Taimaka ma Zaina suna tayi musu Godiya Daganan Gidan Alhaji Tsoho suka yada Zango Chan ma suka kwana sai da Safe da zasu Tafi Suka biyo sukayi ma su Umma Sallama Tare da goggo Halima suka wuce bayan su Umma sun Cikata da kayan arziki tatafi Tana Fadin sai taga Zaina agada ita dasu Farida,Zaina tace insha Allahu suna Tafe aran Farida kuwa itama Tana saka ran Tafiyarsu Gobe ko Jibi.
Zaina basu samu Zuwa Gidan Zafeera ba sai a washegarin Ranar da yan Gada suka Tafi suka samu Zuwa Shima sai da Abba ya basu Izini Zainab ta Rakasu Chan suka wuni Har da su Anun Da Arman da Anty Zareena dasu Jalal da Saudart,Zafeera murna kamar zai kasheta Saboda ganin yan"uwanta Ranar ta Fara Girki Zainab da Zaina da Zulaihat suka Taimaka mata ta Dafa Jallop din Shinkafa aranar Daman Haddir ya Koma asibiti Duk kewa ya Damu zafeera ammh Zuwansu yasa Taji sanyi yana Office ya kirata yaji ya take Daman ya karbi Lambar wayarta Da gaske yake zai kula da Amanar da ya hau kansa kuma zai Sauke Nauyin Dake kansa ta Dauka bayan sun gaisa tace su Zaina sun zo ma sai yaji Dadi yace mata patient sunyi yawa kila sai Dare zai dawo Tacr ba Mtsala sai ya Dawo.
Sai da suka gama cin Abinci kana Zafeera Taja zaina Zuwa Cikin Bedroom Dinta Harda turo Kofa Zareena tana Tsokanarsu da Gulmamu Farida na Fadin ta kyalesu Hira ce ta barke sosai a Tsakaninsu Zafeera na kara bata Labarin Abubuwan da suka Faru Zaina Tayi kukan Tsausayin Halin da Firtlove ya Shiga akanta ta kuma Gayama Zafeera Shi take son gani Zafeera tace kada ta damu Soon Zai Dawo sun karkato kan mganar Haddir sai ga Zafeera yau na yabonsa zaina ta Fara Dariyan Shakiyanci har Zafeera Taji Hauahi sai Daga baya Ta Saurereta har ta bata Shawaran ta saki Jikinta ta Rike Mijinta Domin Wlh Haddir samun kamarsa sai an Tona su zauna su Fahimci Juna sosai Zafeera ta yarda da Shawaranta Sosai kuma Tace zatayi aiki Dashi.
Bayan La"asar suka Fara Shirin Tafiya Domin zasu Biya ta Gidan Alhaji Tsoho Tun Ranar Biki rabonsu dashi Zafeera tace basu isa su