Author : Jamila Janafty Category : Romantic Hausa Novels
Ta Toshe kunni Cikin karaji Tace"Ya isa haka..Ya Isheki Zakiya.."Hajiya Batula kuwa Bata yi ji wani mamaki ba Domin Barewa batayi gudu Danta ya Rarrafa ba Ba Tun yau Tana Zargin Lalacewar Dina Ba Banza ba Hajiya maimuna Kuwa kai kawai ta Sunkuyar kunya Duk ya kamata su Umma sai Kallon kallon.
Zakiya Ta Murmusa Tana Kallon Kowa Dai dai kafin tace"Nasan Zaki ji Durum Da jin wannan mganar ai na Dade ina Miki Shaguben haka baki gane ba Kuma Wlh ki Godema Allah ban manta da alherinki gareni ba Da yanzu Wani Labarin ake ba wannan ba Domin sai na Tabbatar da Uban naki ya Kusamin Ciki nima na Haife..Sai kash Ni bana wannan Cin Amanar kuma ina ganin Girman Tsohon Wasu Ko da ba Na Kirki bane.."
Dina Ta Fashe da kuka Tanayi Harda Shessheka Zakiya Tayi Dariya Tana Fadin"Bama Kiyi Kuka ba Yanzu Zaki koka...Domin Na Tabbata Burinki bazai Taba Cika ba Kinga in hakan ta Faru sai ki gane ina da amfani.."
Dina ta Dago Jajayen Idanuwanta Tana kallon zakiya kafin Ta Nuna mata Kofa Tana Fadin"Fice kibar nan Zakiya..Kije Duk Abunda kikayi zai koma kanki..Nidai nayi Nadama kuma Allah ya karbi Tubana Kije Allah zai min mganinki.."Zakiya tace'Umh daman ai ko baki ce ba Zan Fita Dina..Ga key din Motarki Kije Chan ki karata kada ki kara Nemana Nima haka bani bake Dina.."Tana gama Fadin haka ta Wurgamata Key din Motar ta Zo Zata Fita ta leka Arman dake hannun Hajiya maimuna ta saka Dariya Tana Fadin"Wlcom to d Word Dan Gaba da Fatiha.."
Daga haka ta Fice tana wani Taku Tana Fita Dina ta Duke Tana kuka Su Umma kuwa Jiki sanyaye suka Koma Falo suna Jajanta Abun Daga Dinar har Hajiya Batula Ba wanda ya kara mgana Dina na kuka Hajiya Batula na Sauke ajiyan Zuciya.
*Alhamdulillah Anyi Biki lafiya Lau an gama Lafiya Nagode Bisa Yadda kuka Karbi Uzurina Allah ya bar Zumunci Insha Allahu yanzu komai zai zama Daidai Da yardan Allah..*
*Janafty..."*
8/3/21, 5:10 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ....B21️⃣8️⃣*
*IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*
"Dina tayi kuka kamar Ranta Zai Fita ba wanda ya bata Hakuri ko yace karta yi kuka Daga Hajiya maimuna har ita Hajiya Batulan wacce itama Abun ya Daketa sosai Sai dai ajiyar Zuciya Bata bari tayi kuka ba ammh Tana kallon Dina Tana Tunanin Dole ta koka Domin Zakiya ba karamin cin Zarafinta Tayi ba.
Achan Falo kuwa Su Umma sai Janjanta abun suke Daman masu aikin Naman hayansu akayi suka Gyara Naman suka Soya,Zakiya kuwa Tana Fita ko Ja"afar bata Kira ba Ta hau Abun Hawa ta koma Gida Ranta Fes Daman Ta Dade Tana so Ta Fayyacema Dina Komai bata samu Dama ba yau ta Cika mata Ciki Gwara Ta Fahimci Ita Iskancinta mai Lasisi ne gado Tayi.
Yammah Nayi su Inna Rukayyah suka Tafi Gidan Alhaji Tsoho Chan sukeje suna Bama Hajiya Mama da Alhaji Tsoho Labarin Abunda ya Faru Hajiya Mama ta kama Salati Tana Salallami,Zain Lokacin ya Shigo Dakin Shida Haddir sun ji Komai Alhaji Tsoho bai yi mgana ba sai da Yaga Inna Hannatu Nata Zage Zage Tana Fadin kaddara ta sa Zasu Hada Zuru"a da bara Gurbi Lokacin ne ya Tsawarta mata Dole ta kama bakinta.
Zain kuwa bai yi wani mamaki ba Sanin abaya yasha Zuwa Gidansu Dina yayi kwanaki Koda Kwamishina Bayanan ai Hajiya Batula na gidan ammh Bata Damu Data Bincika me suke aikatawa da sunan Abokin karatun Dina..? Ammh Ina sai dai kawai ta saka musu Ido Daman ai an ce Barewa bazata Taba Gudu Danta ya Rarrafa ba.
Abunda yasa ma har ya tsaya yaji Mganar yana Cikin Farinciki Jiya yayi mafarkin Yaga Zain da yaro ahannunta Bayan ya Farka da Safe sai ya Danganta haka da Tabbas Firstlove ta Haife Abunda ke Cikinta Kenan Hashashensa ya Zama gaskiya Shiyasa ya Tashi Cikin Farinciki da Fara"a yaje asibiti ya Duba Maraasa Lafiya Daganan ya karisa masallacin Cikin asibiti ya bada Sadaka mai Yawa anan ne suka Hadu da Haddir Shine suka Nufi Gidan Alhaji Tsoho suka iske su Inna Rukayyah na maida Zencen Haddir kuwa aransa Allah ya kara yayi Daman ai Duk Taran da ba Alheri ake kullawa ba Allah sai ya Watse gayyar Gabadaya.
Bangaran Dina kuwa kwana Tayi batayi Barci ba..Tana Tunanin ashe daman Duk Shaguben da Zakiya take kan yan Siyasa Da ita take..? Ammh Daddy bai kyauta ma kansa ba..? Wata Zuciyar ta Tambayeta da Cewa ke kin kyauta ma kanki ne..? Ai kema baki kyautama kanki da Rayuwarki ba Gabadaya Dina Tayi kuka Tana Tunanin Dole nema Rayuwarta Ta Lalace Tunda Daddy na Lalata ya"yan wasu Dole itama Wannan Munannan Tabon ya Faru da ita Abun Takaichi ma Gaban Mutane Zakiya ta Kira Daddy da kwarto..! Kalmar ne in Ta tuna Take mata Muni ko yayane Daddy Uba yake gareta wanda ya bada komai nashi Saboda Cigabanta Bazata so ko Taji Dadin wani na aibatashi ba.
Hajiya maimuna ne Dataji kukan Arman yayi yawa Dina Taki Daukansa ta Bashi Nono Ta Tashi Tana mata mgana Cikin kuka Dina Tace"Ummi In na Tuna kalaman Zakiya sai naji kunyar kaina ya kamani..? Daddy fa Tace ma kwarto agaban kowa da kowa..?
Hajiya maimuna Tayi Mirmishin Takaichi kafin tace"Daman ai irin wannan Ranar ne bawa baya so..Shiyasa gwara mu Shuka alheri kodomin Wata Rana Tunda Kowa ya sani Sheri Dan aikeni Inda ka aikashi nan zai Dawo..Ki Dauki Aliyu ki bashi Nono Ki kuma Daina wannan kukan Baki da yadda Zaki yi ki Kankare wannan kaddaran.."Da wadandan kalaman Dina ta Daina kuka ta Dauki Arman ta Rumgume wani Sonsa na kara Shigarta Tana ganin Shine nata aduka Duniyanan.
Washegari Tun Safe Hajiya Batula Tayi Shirin Komawa Daman Direban Daya kawota yanan nan bai komai ba Su Umma suka Diban mata naman sunan da yawa da Farko ma Taki karba sai da Suka matsa mata Sama sama sukayi sallama da Dina Hajiya maimuna kuma Daman sai Dina Tayi arba"in an Daura auranta Da Zain ta Mikata Dakin Mijinta Zata Koma Sudan.
Hajiya Batula Da su Waled da Wuri suka Dauki Hanyar kano ta Guduri niyyar in ta Koma sai ta gayama Kwamishina Komai ko zai Dawo Cikin Hayyacinsa koda ta Koma Baya nan yana Abuja Washegarin Ranar ya Dawo ta kuma Kwashe komai Ta gayamai Hajiya Batula na kuka Tana Fadin"Dame na Rageka..? Ban Rage ka da komai ba Sai dai ina so ka sani Wlh in Yayana yasan kana Neman mata bazai Baka Ni ba ammh nagodema Allah ko ahaka ka Tsaya kaga Karshenka Yarka Tayi Cikin Shege kuma Kawar yarka ta Tona maka asiri gaban Bainar,mutane Sirrikan Yarka me yafi wannan kunya..? In ma baka Daina ba ka Daina Tun kafin Itama Waleda wani ya Lalatata. "
Kwamishina sai kuka yana ma Hajiya Batula rantsuwa Wlh ya Daina Tun Lokacin Da ya Fahinci Zakiya ce wacce abokinsa ya Hadasu tun alokacin ya Tuba ya Daina Neman mata Hajiya batula tana kuka ta barshi nan ta Shige Ciki kwamishina kwana yayi bai barci ba yana jin kunyar kansa Data su Umma da Labarin yaje Musu harda kunya ma Dina Data Kasance yarsa kaicho...Bariki Batayi ba Kuma bata da Riba Domin ita din Tana Rage ma Mutum Daraja Kimarsa awajen Mutane Yayi Nadama abaya ammh ayanzu ya kara Ninka Nadamarsa yana kuma Rokon Allah ya yafe masa Duka Laifinkunsa.
******
*Zaria..*
Bayan Sati Daya..!
Kwana Bakwai Zaina ta Shafe a asibiti Tana karban kulawan Likitoci Saboda C.S din da akayi mata Kafin Satinan Zulaihat da Farida ke ta Fadi akanta Bata ma da bakin Gode musu bayan Kacharalle sai Uwar mata ba wanda yasan Labarin Haihuwan Zaina Suby Tagaji da neman Diddiginsu ta Hakura uwa uba kuma Tana Tsoron Uwar Mata Da Kashedin Datayi mata Uwa uba kuma Harda ita da kanta Sholly din Shiyasa ko Bata ma Allah ta Daina Bin Diddingin Rayuwarsu.
Uwar Mata tazo Ranar kwanan Zaina uku asibiti Tazo Ko Daukan yaran batayi ba Daga Cikin Dan gadonsu suka Lekasu Ita Da Hajiya Zabba"u suna wani Tabe baki,kamar sun ga Kashi Farida bata Damu ma Dasu ba sai kallon Zaina suke suna kare mata kallo Ita kuwa Uwar mata da Kawarta ma Wlh Tsoro suke bata bata iya Kallonsu Sun fi Kama da Tantirin karuwai sun Girma basu san sun Girma ba.
Basu Dade ba suka Fita Bayan Farida Taje rakasu Uwar Mata Ta kalleta Tana Fadin"Kekam meke Damunki ne Sholly..? Yarinyar nan Zuly Uban me take yi zaune tana Miki..? Ita ba karuwa da ita zakiyi ba komai ba gwara ki Koreta takama gabanta kawai Tunda ita Karuwancin ma bai karbeta ba."Farida tace"Saboda me Zan Koreta..? sa"adiya na son Zama da ita kuma Nima Ina Jin Dadin Zama da ita bata da wata Mtsala ban ga aibunta Ba mganar karuwanci kuma Taga ba Riba ta bari Daman kuma ai bai Dace da ita ba..!
Uwar Mata tace"Ah Lalle Dole ta bari Tunda Tana kwance kina Ci da ta.."Hajiya Zabba"u tace"Shiyasa Duk ta sauya ta kara Kiba ta Zama wata Mai kyau da ita.."Uwar Mata tace"Uhm ai ni Zuwan Wannan yarinyar ba alheri bane awajena Duk ta sauyaki Sholly Sai dai ina Fatan Tunda ta Haihu Zata koma Inda Ta Fito..!
Farida Tayi Dariya kawai kafin Tace"Insha Allahu.."Uwar mata ta Dafa kafadanta Tana Fadin"Yauwa Kokefa..Nifa Daman Fargabata Daya kada Watarana Kice Zaki bar wannan Sana"an da tayi Miki Riga Har da Wandon sakawa Sholly..?
Farida tace'Wannan kada ya Dameki ai Ni na Zabi Karuwanci Dakaina ba Talla kikamin ba kin ga kuwa ai ina Jin Dadin Rayuwar nan yasa Kika ganni Cikinta Har yanzu.."Uwar mata Tana Dariya Tace"Hakane Shalelena..Nace ba Baida ke zaki biya Duka Bill din asibitun ba..?
Farida Data gaji da Mgana da Uwar mata tace"Ni zan Biya wani abu ne..? Uwar mata ta ce'Bakomai Tana Kada kai Daganan Farida Tayi musu Sallama ta koma Ciki ta Iske Zaina Suna mganarsu da ZulaihatSuna ganinta sukayi Shuru basu Cigaba ba ita kuwa aranta Mirmishi Tayi Tana Tunanin waye zai gayanmata Uwar mata..?Tafi kowa sanin Wacece ita Tasan Sirrinka Da Duka Sharrinta.
Ranar da suka kwana Bakwai aka basu sallama Tunda Zaina Taji Sauki,Har Tana Takawa da kanta Tayi ma kanta wanka ta Shirya, kuma Ruwan Nono ya samu yaran suma Sunyi Bul Bul Dasu,Dayake Zaina tana samun Cima mai kyau Ferfesun kayan Ciki da Nama take ci Tunda ta Haihuwa daTea mai kauri Cikin Lokaci Nonuwa suka Cika yaran suka Fara samu ammh da haka Likitan yace akwai Bukatan A kara da madara Zuwa gaba Saboda in sun kara wayau bazai Isheshi su sha su Koshi ba.
Mota guda Farida ta sami suka kwashe kayansu Bayan Ta Biya Duka Bill din asibitin bata Damu da yawan kudin ba,An basu Sati Biyu su Dawo bayan an Rubuta ma Zaina wasu mgungunar karin Jinin Da yammah aka Sallamesu wajen 6:30pm suna Gida suna Komawa Zulaihat ta saka Ruwan Zafi Farida tayi ma Zaina wanka Sosai Tun a asibiti baaa saka Ruwan yayi Zafi Soaai bayan Tagama gasa mata Jiki Ta Koma ta wanke yaran Tas Zulaihat nata mamakin ganin Farida ta iya komai
Da Daddaran ta Kira Kacharalle a waya ta Bashi Kudi tace ya Siyio mata Raguna Guda Biyu,Washegari kuwa sai gashi Dasu Shi ta saka ya kira mata Wani Mahauci ya yanka ya Gyara mata ita da Zulaihat suka Soya Zaina Ta rasa me me Zatace Da Daddare kuma sai ga Limamin masallacin Anguwan Daman Kacharalle tayi ma mgana wanda zai ma yaran Huduba yace karta Damu zai kawo mata sai ko gashi Sun zo Tare Bayan gaishe Gaishe Farida ta Dauki yaran takai mai ita da Zulaihat Daman sun gama mgana da SA"ADIYA kan sunan da yaran zasu ci.
Tace Maryama da Fatima Domin Ta Tuna Firstlove ya gayamata in ya Haifi ya mace ta Farko Sunan Mahaifiyarta zai saka In ya kara samun wata kuma ZAI saka Sunan Nene Aisha sai dai ita tana son yima Umma Takwara Domin ance so So ne Umma uwace agareta Data gayama Farida taceTayi Daidai Ta gayama Limanin Sunayen ya Dagasu yayi musu Hudubu Bayan ya Tauna Dabino ya basu ya kuma Tofe da addu"an Neman Tsari da ZAI ,tafi Farida ta bashi 5k da Naman sunan yakai ma Iyalai yana ta Godiya bayan Tafiyarsa ne Farida da Zulaihat suka Zauna suna Zabo inkiyan sunayen da zasu Dinga kiran yatan dasu sai Zaba suke su Sauya Zaina na gefe Tana Musu Dariya.
Dakyar suka Tsaida mga kan za"a Dinga Kiransu Maryama itace Babba ANAN ita kuma Fatima ANUN bayan sun gama suka waigo suna Tambayan Zaina Tana Dariya ta Daga Musu Yatsunta alamun Sunan yayi Zulaihat ta Daka Tsalle Daman ita ta samo sunan a wani Musliman Name wanda Kacharalle ne ya Bata Littafin..
Naman sunan su kuwa isu isu sukaci kayansu sai kuwa Kacharalle da Farida ta Dibanmawa Zaina kuwa da yawa Farida Ta Diban Mata tace taci ta More Abunta Ta Zubar da Jinin Haihuwa.
Kwanci Tashi ba wuya awajen Allah Farida da Zulaihat suna Cigaba da kula da Zaina dasu Anan kafin Sati Biyun Da Zasu Koma asibiti Daga ita har yaran sun sauya sunyu Bulbul Dasu kida sukaje aka Duba wajen Dinkin akace ya Riga ya Hade Sai dai bata zata Dinga aiki mai Wahala ba yaran kuma sun ce Tana da Ruwan Nono kyau nan da wata Biyu Zuwa uku sun kara Wayau sai asiya madara adinga Basu Daganan suka Dawo Gida Suna Cigaba da kula da ita Su Anan kuwa Har gajiya suke da Goyo wajen Farida da Zulaihat Allah ya Dora musu kaunar yaran acikin Ransu Ita Zaina Tana Gefe ta zama yar kallo,Sai dai Farida na kula da Jegonta Sosai Tunda ita Ta Haihu Ta kuma san Komai bata ma Sa"adiyan Wasa.
********
*Bayan Kwana arba"in..*
Yau Dina Take Cika kwana arba"in da Haihuwa Ita da Arman sun Chanza sun zama wasu Lukata ye dasu,saboda suna Samun kulawa Sosai Daga su Umma ga kuma Hajiya maimuna Data Dage wajen gyara Dinar Tunda aure Zatayi
Bangaran Arman kuwa yaron ya Shiga ran Mutane Sosai Wuni yake hannun Zainab in Tana makaranta Hannun Nene ko Umma in Abba ya Dawo ma adauka kai mai Arman ya Fara wayau yayi Bulbul yana samun kulawa Nene Har Goyashi Tana yi in ya Fara Rigima Ranar Har Wajen Alhaji Tsoho Haddir da Zain suka kaimai ya kara ganinsa ya Sakamai albarka Domin Daga Zain har Haddir Arman ya Shiga ransuTunda kaf afamily din ba wani karamin yaro sai Shi Musamman in suka Dawo Daga wajen aiki suke yada Zango su Daukesa suyi ta mai wasa Zain kuwa yadda yaron ya Shiga Ransa har bama su Umma mamaki yake in ka ganshi Wajen Dina sai dai in Nono zai sha Dina Har acikin Ranta Tana Murna da Arman bazai Tashi Cikin wani maraici ba Tunda kowa ya maida komai ba komai ba.
Ranar Datayi arba"in din Alhaji Tsoho ya Kira Abba sukayi mgana kan mganar Daura auran Zain da Dina,Sai yace a Tuntubu su Abban kaduna kana kuma akira shi Kwamishan aji nashi Tsarin kamar yadda suka Rabu Shi Abba Shi ya Kira Abban Kaduna da Daddy Abuja ya gayamsu Yadda Alhaji Tsoho yace yana so Ranar Jumma"a Daura auran Sai suka ce Akira Uban yarinya atambayeshi dashi Zain din mgana na Hannunsu haka kuwa akayi Shi Alhaji Tsohon shi ya Kira Kwamishina ya Tuntubeshi kan mganar Kwamishina Dayake jin kunyarsu su Alhaji Tsoho Tun Abunda ya Faru yace ai mgana na Hannunsu yadda ya yanke haka Za"ayi yace Shikenan In yayi mgana da Zain zai Kirashi ya gayamai Rana da komai da komai.
Da Daddare bayan sun Dawo daga aiki Daman Tunda yayi Yaji bai koma Gidan Abba ba,Da Alhaji Tsoho yatuntubesa kan wannan mganar bai iya cewa komai ba yace yadda suka yanke nan take yace Jumma"a mai Zuwa sai Hajiya mama tace A Daga Zuwa na sama saboda ba"a sanar da ita Dinar ba Da wannan Shawaran ta Hajiya Mama aka Tsaida nan da kwana Goma sha Hudu Za"a Daura Auran Dina da Zain.
Alhaji Tsoho Da kanshi ya Kira Kwamishina ya gayamai Shi kuma yace Allah ya Nuna mana,Da kansa ya gayama Hajiya Batula yace ta Kira Dinar Ta Tambayeta in da wani Abu Datake Bukata tace Shikenan Hajiya Maimuna kuwa Abba da kansa ya Sanar da ita tace bakomai Allah ya nuna mana Daman Tana son ta koma Suhaima ba Lafiya,Duk Abba ya Kira su Baban kaduna ya gayamasu su Inna Rukayyah kuma Hajiya Mama Harta Chan Gada Umma ta Kira Goggo Halima ta sanar da ita tace Zatayi Kokari tazo Taga Arman Daman Tun sanda akayi Haihuwan Umma ta Kirata ta gayamata suka Rabu Cikin kuka Bayan Goggo Halima tace"Umman Zareena har yanzu dai Ba Labarin Halima..?Umma Na Sharan kwallah Tace"Har yanzu Goggo Halima muna nan dai muna gayama Allah..!
Goggo Haliman itama kwallar Take Tana Fadin"Allah ya Dawo da ita lafiya in tana Raye..In kuma karshen Saduwan kenan Allah ya Hada Fuskokinmu da alheri. "wannan kalaman shi ya saka Umma kuka da ita kanta Goggo Haliman Allah Sarki Rashin Zaina ba karamin Babban Gibi bane da Iyalan Saulawa in suka Tuna sai sun koka.
Da Dina Taji Labari Bata iya Cewa komai ba Gashi Dai Burinta ne zai Cika ammh bata wani Farinciki ballatana Murna,Zuciyarta bata Farinciki da wannan auran Fargabanta Daya bata san wata Rayuwa Zata Gudanar ba In Gida ya Zama Na Daga ita sai Zain ba Bata dai nuna ma kowa ba ta bar Fargaban acikin Ranta Hajiya Batulane ta Kira Hajiya maimu sukayi mgana kan Abubuwan da za"a Bukata tace sai tayi ma su Nene mgana Data Tambayesu suka ce sai Abunda Alhaji Tsoho yace in Gidan Zain na Lowsot ne ba Mtsalan komai akwai komai na Rayuwa aciki in kuma wani ne basu sani ba Gaskiya Sai Abba ya Dawo sun Sanar mai.
Da Abba ya Dawo Nene ta gayamai Shi kuma ya Kira Alhaji Tsoho ya gayamai Abunda ke Faruwa sai yace A"a koda Halima bata nan bai kamata Dina ta Zauna agidan ta ba Domin Tun jiya sunyi mgana da Zain kuma yace bai yarda Dina Ta Zauna agidan ba Gida Gidan Zaina ne ba macen Data isa ta Shiga Abba ya Jinjina kai Shima yayi Tunanin haka Sai dai suka Rabu kan zai yi Tunanin a ina Za"a ijiye Dinar.
Sai da sukayi waya da Baban kaduna Yana