Author : Jamila Janafty Category : Romantic Hausa Novels
kuma Sanayar wasu manyan kasa yasa a kashe mganar wannan Shine ma karin Dalilim Dayasa Uwar mata ta bar Garin Zaria sai dai tazo Lokaci Bayan Lokaci Ta kuma kafa Dokar kada Akarbi Wata bakuwa batare da izininta ba.
Aranar da kika ganni naje Service ne ni da wani Alhaji Badamasi Dan Chaji a kano yake ammh Iyalansa na Abuja,Yana da Tarin Dukiya sosai kuma Shi so yake ya aureni yana so na bar wannan Harkan ya Aureni ni kuma naki yana kashemin kudi kuma yana Kashema Uwar mata Wacce har kamin kafa yayi wajenta Ya aureni Taki bashi Fuska saboda bata san nayi aure,Saboda Tana samun Dukiya Daga wajena Munje Na Rakashi wani Taro sai kuma aka kiraahi Wata Daga Cikin Iyalansa ba Lafiya Dole ya Wuce Abuja bayan ya Bani Kudade kan na koma Gida sai yazo Shine Dalilin Haduwarmu ammh ba Domin haka ba,ba zamu Taba Haduwa ba.
Farida Ta karishe Fada Tana Runtse Idanuwanta Cikin kunnan Zuciya dana Ruhi,Zaina Dake kallonta Cikin Tsausayinta Ta Dago Habarta Lokaci Daya Tana Share Mata Hawaye,itama Farida Hannu ta saka Tana Share ma Zainar Hawaye Lokaci Daya Tana Fadin"Ina alkwarin da kikamin na bazaki yi kuka ba..?
Zaina Ta Ja Majina Tana Fadin"Ya zanyi Anty Farida..?hakika Labarinki ya Chanchanta ayi mai kuka sosai..Gaskiya Kin Hadu da mummunar kaddara da kuma Sharrin Kishiya,abunda ya bani mamaki Tayaya bayan Kinsha Lemo kika Tsinci kanki Cikin wannan Halin..? Kuma waya Kira su Abba dasu Baffa awaya ya gaya musu..?
Farida Ta Sunkuyar dakai Tana Kokarin Danne Abunda ke Taso mata Daga kasan Zuciyarta,Ta Bude Dara Daran Idanuwanta ta Saukesu kan Zaina Tana Fadin"Tunda nasha Wannan Lemon da Zubaida ta sakamin mganin Barci ban kara sanin Inda kaina yake ba nadai san na Sulale nan saman Cafet din Dakina na kwanta Daganan Sai Zubaidan Ta Tattabarda nasha Lemon Daman Tana Labe ne sai Tazo Tajani Zuwa Cikin Bedroom din Tamin Tsirara Sai Ta Fita Bayan awa Biyu sai ta Kira Yaron da ta bama aikin Wanda ake Hada Hotunansa da nawa Ana Turama Ya Musbahu yana Zuwa tamai Jagora Har Shashina Ta kuma gayamai yadda komai zai kamkama Sai ta Dauki areef Dake Barci Ta tasheshi Ya Fara kuka sai ta kawoshi Falo ta ijiye,lokacin yar aikina Bata nan tatafi garinsu Sai ta koma Shashenta sai da ta bar mganin ya Kusa rage karfi ajikina kana ta Daga waya ta Kira Ya Musbahu Tace yazo Gida Shashena wani Abu na Faruwa Yana zuwa ta Fashemai da kuka Tana Fadin daman Ta Dade Tana so Ta gayamai kullum in ya Fita sai wani yazo Gidan ya Shiga Shashena ya Dade kana yake Fitowa yau ma yazo Tunda ya Shige bai Fito ba kuma Tun Dazu Take jin kukan Areef Fadin Haka yasa Ya Musbahu ya Shiga Shashena da Hanzarina yana zuwa ya ganni Tsirara shima Saurayin Tsirara yana kwance ya Rumgume ni kam kam alamar bayan mun gama Shashancin mune mukayi barci Ya Musbahu ya Rude sosai yayi kuka kamar me yaso ya Kiramin Hukuma ne sai Zubaida ta Hana Ta bashi Shawaran ya Kira Gidanmu ita kuma bari ta Kira Baffa Haruna Wannan Dalilin yasa Ya Musbahu ya Kira su Abba wanda daman suna Garin na Jemeta sunzo Family House din mu da Niyar Har nan zasu so su Dubani kuma su Dawo dasu Hassana Suna Gidan Goggo Zaliha suna Jin Kiran ya Musbahu suka Dungumo suna Zuwa sai gasu Baffa Haruna ba Bata Lokaci Ya Musbahu yayi musu Jagora Zuwa Shashena suka Iskeni Cikin wannan Halin Wanda Dalilin sa ne nake Cikin Wannan Rayuwar sa"adiya.."
Ta Karishe Fada Cikin kuka Zaina Dake Sharan kwallah Tace"Zubaida da Mommy bazasu Taba gamawa da Duniya Lafiya ba Anty Farida sun Zalunceki Kuma suma sai Sunga Sakayyah,Toh kuma duk ya akayi kika san duk wannan Abubuwan..?
Farida Tace"Zahra Take maida yadda Zubaida ta Dinga Fada Tana kuka ni kuma sai a Hashashena na Hasaso yadda Ta Tsara komai Tunda Dagani sai ita agidan.."Zaina Tace"Ba Shakka Hasashenki Daidai ne Anty Farida..ammh meyasa bazaki koma Gida ba..?kila Zuwa yanzu gaskiya Tayi Halinta...?
Farida Ta Girgiza kai Tana Fadin"A"a Bazan koma Gida ba..Koda na koma sai dai naje na kara Tabbatar musu da bakinsu akaina na Zama karuwa..Sa"adiya har yau har Gobe ina Tuna kalaman Abba da Mami akaina Sunyi Tur dani sun Kirani karuwa gaban ya"yana da a Dangina Mijina yayimin Allah ya isa ya sakeni gaban Iyayena da ya"yana yana Kirana karuwa Ki gayamin Sa"adiya akwai wata Sauran Kima Data Rage min..?bata Babu sam Bani da wata Sauran Kima Sa"adiya Shiyasa gwara ki barni na karasa Rayuwata ahaka Duk da ina karban mgani ammh ina ji araina Kila wannan Ciwon Zuciyan Watarana Shine ajalina..Ammu kafin nan sai na Cika miki alkawarinki zan maida ke gidanku Bauchi da kaina na Damkaki Hannun marikanki Ni kuma na Dawo nan na Cigaba da Harkokina ammh Ki sani ba anan Gidan zaki Haihu ba saboda Bariki ba kamar kowani Gida bane ba wanda yasan da Labarin Cikin ki Saboda haka ki Boyesa kada ya bayyana a cutar Dake nasan In kowa ya gansa ya Fito Zan Fuskanci Barazana Har Daga wajen uwar mata Saboda haka na yanke Shawaran Siyan wani Gidan Dabam batare da sanin Kowa ba mu koma Chan Har ki Haihu Lafiya..."
Zaina Ta gyada kai Tana Sharan kwallah Tace"Har Zuly kada na Bari ta sani.."Farida tace"Eh..Itama kada ki bata yarda..Domin a bariiki babu yarda Babu Amana Ko bata ci Amanarki ba Watarana Za"aiya amfani da ita acutar dake..Ki kula da wannan.."Zaina ta jinjina kai alaman Gamsuwa kafin Ta koma Tayi Tagumi Tana Fadin"Kema Zaki koma Gida Da uzinin Allah Anty Farida..Na kuma Tabbata duk inda su Abba suke so sun gane gaskiya...Ko domin komai ba Domin su Hassana Anty Farida da kuma karaminsu areef.."
Farida Ta Sauko Daga kan Gadon Tana Fadin"Kina Tunanin Su Hassana suna mim kallo uwa mai nagarta..? A"a suma a amatsayin karuwa suke kallona Sa"adiya."Daga haka ta Tura Kofar Tiolet Tana Kokarin Danne Abunda ke taso mata Daga kasan Ranta da kallo Zaina ta Bita aranta kuma Tana ganin Zuciyar Farida ta Riga Ta Kekashe Da Abunda ya Faru da ita ammh Ta Tabbata a yanzu Tuni Allah ya Tona ma Zubaida asiri,Bazata bari Anty Farida ta Dawo ma wannan Rayuwar ba Zata yi iya bakin Kokarin Taga Itama ta saka mata da Abunda Itama Tayi mata.
******
*Monday..*
Yau ta kama Monday ne Tushen aiki Kowani ma"aikaci yana Shirin Tafiya wajen aikinsa ne Kamar yadda Take wajen ZAIN domin ya Riga ya guduri Niyyar Bazai kara kwanciya ba ganin in ya cigaba da kwanciya Watakila Har Abada bazai kara ganin Firstlove da abunda ke Cikinta ba ya yanke Hukuncun Tashi Tsaye ya Nemi Zainarsa a ko"ina afalin Duniyar nan batare da ya nemi Taimakon Kowa ba.
Tun Jiya Lahadi da Haddir yazo ya Rakashi suka Tafi Gidansu Sun samu Tanimu megadi Cikin Damuwa Domin Gidan ya zama wanu iri ba Gimbiyar Dacta ba Dactan kansa yana ganinsu sai yaji Dadi bayan ya gaishesu ne ya Kalli Zain ganin yayi wani iri Dashi kamar bashi ba yace"Dakta Lafiya kuwa..? Ka daina kwana agidanan nan Gimbiya kuma Tun watan Daya wuce Bata gidanan Dom Allah kada ka gayamin kun Rabu da Gumbiya Halima ne Ranka ya Dade..?
Ya Fada kamar yayi kuka Zain Da Kansa ke gefe yana Sauraran Tanimu megadi Har Haddir zai mai mgana Zain yayi Saurin waigowa yana Fadin"A"a Tanimu har Abada babu saki Tsakanina da Zaina..Ni dai da wadanan Hannuwan nawa bazan iya sakinta ba...Tanimu ka Tayamu addu"a Firstlove ta bar Gida bamu san inda take ba.."Yafada yana kallon Tanimu Cikin wani yanayi,wanda sai da Haddir ya kara jin Tsausayin Zain din daya koma kamar bashi ba.
Kasa Tanimu megadi yakai Hannunsa Daya Dafe da Kirji Daya kuma Bisa Cikin Zaro Ido yace"Mun Shiga uku Dacta badai Halimatus Sa"adiya ba..?haddir ya bashi amsa da ita fa Kawai sai Tanimu ya Fara matsan kwallah yana Fadin"Innalillahi wa"inna Illaihirra"jun Kai Duniya ina zaki Damu..? da izinin Lahi Ya Allah ya Allah Duk inda Gimbiyar Dacta Take tana Tare da Tsarewar Allah..Allah ya bayyanata Allah ya bayyanata Dakta bakai kadai kayi wannan Rashin ba Wlh muma munyi Allah ya bayyanata.."Yake Fada yana kuka Zain na kallon Tanimu Lokaci Daya yana Fadin"Insha Allahu..Ameen Ameen ya Allah..Nagode Tanimu.."Haka suka Shige Cikin Gidan suka bar Tanimu nata kuka yana addu"an Allah ya bayyana Zaina.
Kayansa Duka Zain ya Hado da duka Abubuwan da zai Bukata Ya Dade Cikin Bedroom dinsu yana Hawaye ya Bude Bangaran kayan sawan zaina yaga komai yana Cikin Muhallinsa ne,in ya Waiga sai ya Dinga ganin kamar zai ganta Dakin da Gidan Gabadaya suna Dawowa mai da Wata Rayuwar da sukayi acikin Gidan Zain ya karajin Zama bai Gansa ba Dole zai Tashi ya Nemo Zainarsa Ko zai samu Sukuni,Haddir ya Tashi suka Fita da akwatunan daya saka kayansa kama Daga Kayan sawa Zuwa Takalma da abubuwan da zai Bukata Domin bazai iya zama agidan indai ba Firstlove ba kuma su Abba sun yarda ya dawo Gida ya zauna Zasu fi samun Kwanciyar Hankali.
Tun karfe 7:30am ya Fito Daga Dakin Sadiq da ya ke zaune aciki Yanzu Cikin Shirin Fita Yana sanye Suit masu Ruwan Toka na kamfanin armani ya Tsuke Wuyansa da Nektie,Kafarsa Sanye Cikin Takalmi Rufaffe na Fatar Damisa,hannunsa Rike da makullin Motarsa Da wayarsa kana mai kallon Farko zaka Hangi Damuwa Firgici da kuma Rama a tare dashi ba,Gashi ya zama wani so Cool kamar ba Dr Zain ba.
Yaso ya Tafi Tun Lokacin ammh Nene Ta hanashi Ta matsamai sai da ya karya ita ta Dinga Fifitamai Tea din har ya Wuce yasha sai ga Umma da Abba sun Fito sun ji Dadinsa ganninsa haka Zain ya Duka Ya gaida Abba da Umma Abba ya Dagosa yana kallon kwayan Idanuwansa Tuni wani Tsausayi da kuma Soyayyar Uba da Dansa kawai sai ya Rumgumeshi kamar yayi kuka yana Fadin"Allah yayi maka albarka..Allah ya kareka Allah kuma ya baka ikon Cin wannam Jarabtan Rayuwar da Allah ya Dora maka kana da kananan Shekarunka Allah ya baka karfin Gwiwa da kuma Jarumtar Daukan wannan al"amarin Zain.."Yake Fada Lokaci Daya yana Bubbuga bayansa Nene da Umma suka kalli juna kafin su Rike hannun Juna Suna Fadin Ameen Ameen da karfi Zain ma Dagowa yayi yana kallon Abba Lokaci Daya yana Fadin"Ameen Abba..Nagode kwarai...Nima ku yafemin Halin Damuwar da na sakaku..."
Abba ya Girgiza mai kai yana Dafashi Lokaci Daya yana Fadin"Shiii..Karka damu..Mun yafe maka Duniya da lahira..Allah yayi maka albarka.."Su Umma suka kara amsawa da Ameen Sallama yayi musu ya Fice da cewa zai Fara Zuwa Gidan Alhaji Tsoho kafin ya wuce asibiti Suka Bishi da Allah ya Kiyaye Hanya da kuma Kallon Tsausayi har ya Fice
Daman Motarsa tana Haraban Gidan Haddir ya kawo mai ya Bude ya Shiga Bayan ya zauna ya saka Set belt yayi addu"a Hawan abun Hawa Domin abaya baya yi Duk kuwa da Fadan Da Firstlove take mai ammh yau gashi bata,Tazo taga ya koma yadda Take so Tashin Motar yayi bayan yayi Hon megadi ya Budemai get ya Fice sai gidan Alhaji Tsoho.
Koda yaje Haddir bai Riga ya Fita ba,Suna Dakin Hajiya mama suna karyawa,Suna ganinsa Dukkansu suka zubamai ido Cikin wani yanayi Takalman kafarsa ya Cire bayan Ya Shigo da sallama Gaban Alhaji Tsoho ya Duka yana Gaishesa ya amsa mai Cikin Farincikin ganinsa ahaka Zain ya Juya a sanyaye yana gaida Hajiya mama kawai sai ta tashi Ta isa garesa ta Rumgumeshi Tana Fadin"Allah ya kara maka Juriya Jikana...Allah ya bayyana halima Lafiya Allah ya Tsareta duk inda take.."Gabadayansu suka amsa da Ameen.
Alhaji Tsoho ya kalli Zain yana Fadin"Zainullahi har an Fito..? Kai ya gyadamai batare da yayi mgana ba Haddir ne dake Shan Tea yace"Ka karya..?Zain ya Dago yana kallonsa Cikin Sanyin Da ya koma yace"Eh...! Kawai ya iya Fadi ya maida kansa ya Sunkuyar Alhaji Tsoho yace"Masha Allah..Allah yayi albarka naji dadin ganinka ahaka Zainullahi..Abu na gaba shine ka ga dai duka abubuwan da suka Faru ko..? Akwai sakaci da addu"a sai ka Dage kaji ko..?mganar Halima kuma muyu ta Rokon Allah Insha Allah Allah zai bayyanata..Amina mikomin Ruwan zamzam din chan.."Ya fada yana kallonta Tashi Tayi ta Mikomai Ruwan Zamzam din Dake Cikin wani Dan Gora shi kuma ya karba ya mika ma Zain yana Fadin"Karbi kasha...Ku daina sakaci da addu"a da kuma azkar Domin neman Tsarin Kanku Daga Shedanun Mutane Dana al"janu Hadiru yafi ka Kokari kan wannan Fanni kaima sai ka Dage.."Zain ya Gyada kai bayan ya karbi Ruwan yana Fadin"Insha Allahu Alhaji Tsohio nagode Allah kara Nisan kwana.."
Alhaji Tsoho ya amsa da Ameen yana Fadin"Ku tashi kuje..Allah ya bada Sa"a.."Zain ne ya Fara Mikewa Ya Fice Kana Haddir Kusan Tare suka Jera zuwa Haraban Gidan kana Kowa ya Shiga Motarsa suka Fice Zain ne ke gaba Haddir na Binshi abaya Har Zuwa Cikin Haraban asibitin..
Likotoci da Nurses din Dake asibitin sunyi Murna da ganin Zain ya Dawo bakin aikinsa Batan kuma Zaina ashe ya Zaga ko"ina sai Allah ya kyauta ake mai da addu'an Allah ya bayyanata Ya Shiga Office dinsa yaga Tarin Folder nan da nan ya Fara Duba maarasa Lafiya Cikin wani Kuzari yana Tunanin kafin nan da 1pm na Rana zai bar Cikin asibitin ya Fita Domin Fara Neman inda Zainarsa ta Shiga Daga garin Bauchi.
*Ki Biya ki karanta Cikin Salama Hajiya*
*Janafty..*
7/15/21, 11:41 AM - Aisha Srtr Mt: *ZZ....B20️⃣9️⃣*
*IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*
"Karfe 1:30pm ya Fito Daga Cikin office dinsa Zuwa Haraban asibitin Lokaci Daya yana Duba agogon Fatan Dake Hannunsa.
Ba haka yaso ba yaso ne Tun 1pm ya baro asibitin ammh Patient sunyi yawa kuma ya Dade bai Shigo Cikin asibitin ba Shiyasa ya zauna Har sai da yagama Dubasu Kai Tsaye masallacin Dake Cikin asibitin ya Shiga ya Daura alwala ya Shiga Masallacin Bangaran Maza ya Tada sallah bayan ya idar ya Rusuna gaban Ubangiji sai da ya Fara da Rokon Gafaran Allah Bisa Zunuban Daya aikata Kana ya Gangara kan addu"a awannan Fita neman Firstlove da zai yi Allah ya bayyanata Allah yasa tana Cikin Koshin Lafiya da kwanciyar Hankali Allah ya bayyanamai ita ya Dade yana addu"o"insa Kafin ya Shafa Cikinsa najin yunwa ammh Yanayin Dayake ciki yasa bai Damu daya Nemi abinci ba yana Fitowa Daga masallacin ya Fada Motarsa ya Bata Wuta ya Fice Daga Cikin asibitin.
Abun Tsausayi Abun kuka Zain Duk inda yaga wasu Gungun Mutanesuna zaune haka zai Faka Motarsa yaje wajensu bayan sun gaisa sai ya Fito da wayarsa Hoton Zaina ya Bayyana da kayan Data bar Gidan Domin Zafeera ya Kira ya Tambaya Ta Turamai,In ya nuna musu sai yayi musu bayanin Ta bar Gida Sati Uku Daya gabata sai su ce basu ganta ba wasu Har suna bashi Shawaran yakai Cigiya gidajen Radio yace an kai ammh Har yanzu Shuru Tun wasu suna ganin Shirme har suka zo Suna Tsausayama Zain din ganin yadda yake wahala Sallah kadai ke Tsayawa ya Tsaidashi Bisa Hanya Tun bayan Faruwar almarin Da Alhaji Tsoho ya ankarar dashi Sakaci da Ibada bai kara bari sallah ta Wucesa ba.
Ranar sai Bayan Mangariba ya Koma Gida ya Zagaya anguwanni ba adadi yana Neman Zaina ammh ba Nasara bai Karaya ba washegarima Daidai wannan Lokacin ya kara Barin Cikin asibiti ya Fita Neman Zaina Ranar ma sai Dare ya Dawo ba Nasara Allah Sarki sai da Zain ya Jera sati yana Zagaya Tashshon Garin na Bauchi Ba Wanda yace mai yaga Ko mai kama da Zaina Ammh Duk da haka bai karaya ba Babu Inda bai je ba agarin Bauchi Ba Wani Labari sai ya Fara Tunanin Lokaci yayi da zai Fara Duba Zaina a Makotan garin na Bauchi Tunda dai Bata Cikin garin na Bauchi.
Ranar Daya Cika kwana Bakwai yana Fita Ranar Haddir yabi Bayansa Domin Tun kwana Uku Da Fara Fitan Zain ya ankare da Haka Tunda yana Zuwa Office dinsa sai ace ya Fita abun sai ya Fara bashi mamaki yana Zaton Gida yake zuwa,ashe ba nan yake zuwa ba Domin yaje gidan yagani,Sai Yagayama Alhaji Tsoho shi kuma yace ya sakama Zain din Ido ya gano ina yake Zuwa,Dalilin Haka ne yasa yau din yabi bayansa abun Tsausayi sai da Haddir yamai kuka Dandalin masu adaidaita yaje Daya bayan Dayan yake nuna musu Hoton Zaina Koda wanda ya Ganta ammh Ba"a dace ba Domin Anyi Rashin Sa"a Mai adaidaitan Daya Dauki Zaina Zuwa Tasha Dan kano ne aiki ne ya Shigo Dashi Bauchi kuma Tuni ya koma.
Zain Jikin Motarsa kawai ya koma Ya Dafe kanshi Zuciyarsa na wani Irin Suya sai kawai yaji an Dafa bayansa yana waigawa yaga Haddir Tsaye yana kallonsa Cikin mamaki ya Kara Waigowa yana Fadim"Haddir..Kai ne anan..?me kazo yi..?
Haddir yace"Kai na Biyo..!
Zain yace"Ni kuma..? Haddir yace"Eh mana na lura Dakai Tunda ka koma aiki Kullum iwar wannan Lokacin kake Fita Sai Nagayama Alhaji Tsoho Shi kuma yace nabi bayanka naga Ina Kake zuwa."Zain yayi Shiru kawai yana kallon Haddir kafin yayi wani Mirmishin takaichi Yana Fadin"Uhm...Ina kuwa Zani Daya wuce Neman inda Matata Uwar ya"yana Ta Shiga..? Kuna Tunanin zan zauna ne kawai ina ji inagani Firstlove Ta bar Rayuwata Gabadaya..? Ko kuwa kuna Zargin Wajen wata Karuwar na koma ko..?uhm..Wlh nayi Tuban Gaskiya Yanzu awannan Halin Da nike Ciki Duka Sauran mata ma Maza nake kallonsu babu Abunda ke Burgeni Balle ya bani Sha"awa Wlh Haddir Zaina Itace Gishinkin Rayuwata Rasata Tamkar Rasa Duka Walwalatace.."Ya karishe Fada kamar zai saka kuka.
Haddir ya kara Damke Kafadarsa yana Fadin"Am Sorry...Na sani ba kuma wai Muna Zarginka Da sake aikatawa Wani Laifin bane Kaga baka da lafiya bai kamata kana wannan yawon ba Kazo mu koma Gida Zaina kuma addu"a zamu Dake dayi mata Insha Allahu Tana Cikin Koshin Lafiya,kuma Allah zai Bayyanata.."Zain ya Ture Hannun Haddir yana Fadin"No...Ba zan iya komawa Gida na Zauna Bansan Inda Firstlove take ba..Ba zan iya ba Haddir Bana samun Wani Kwanciyar Hankali.."
Haddir yace"Is ok...Zo mu koma Gida kayi wanka ka Huta..Sai muyi mganar yadda zamu bullo da wata Hanyar kaji.."Zain yayi Shuru bai yi mgana ba Haddir ya Kara Dukan Kafadansa yana Fadin"Be a man..Kaji ko shiga Mota muje Plz..."Jin haka yasa Zain ya Kada kai Ya Bude Motarsa ya Shiga Shima Haddir ya Shiga Shine agaba Zain