Chapter 2 Reading Zainazain Book 2 Complete By Janafty Arewa Novels

Zainazain Book 2 Complete By Janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   2 / 37

3K to 6K   out of 108.5K words

yi mgana ba.

Komawa Zaina Tayi ta kwanta kawai Tana Jin gajiya na Tambayanta Sai Lokacin Farida ta Kunna wayarta Tana Jinta tana waya Dawani sai Shagwaba take mai kamar yana Tambayan Ya ta iso Gida ne,Ita dai Sama sama Daganan Taji Idanuwanta na Rufewa Bata kuma Farka ba sai Wajen 12 na Dare Ta ganta saman Gado Farida Ta maida ita kuma Tana kwance Gefenta Sanye da kayan Barci Tana Barci Tuna batayi Sallar Isha"i ba yasa ta Ta mike Sadaf Sadaf sai ji Tayi Farida Ta Bude Idanuwanta Tana Tambayanta ina zata Tace Bayi alwala zatayi Tayi sallah kana ta Gyada mata kai.

Bayan Tayi sallar sai ta kasa komawa nan kan Darduman  ta zauna Tana ta Tsiyayan Hawaye acikin Ranta Tana jin wani iri na yau itace zata kwana agidan karuwai Farida ce Tatashi Tace Ta Koma saman katifa ta kwanta Tana da juna Biyu kuma ana so Ta Rika samun Barci Sosai Batayi musu ba ta Mike ta koma kan katifan ta Dunkule Farida Ta Rufamata Bargo Tunda akwai Wuta Fanka na Gudu Gudu da dan iska iska..!

****

*Washegari*
*Bauchi..*

Su Abba dukkansu sun Dawo Gida Haddir ne yakwana asibiti Wajen Zain wanda Har yanzu bai Farfado ba,Dukkansu har su Umma nan gidan Alhaji tsoho Suka kwana Wanda kuma sai da Aka kira mata Likita ya Dubata ya Bata manganuna Harda na Barci aka samu tayi ta Barci sai koken koken ya Ragu,Da Safe kuma Wajen 11am na safe sai ga su Inna Hannatu sun Dawo Domin suma Chan tunda suka Tafi ba wani kwanciyar hankali sai Zullimi Tun suna chan suke ta Kiran su Abba kan Yaya ake Ciki Suna gaya musu ba wani Labari sai dai addu"a Abba yayi kuka kamar mene duka yana Dora laifin akansa.

Umma kuma an samu sauki Tunda tayi Barci ammh Data Tashi Sai Hawaye dai ba mgana Goggo Halima kuwa sai kiran Chan Gada take ko da wani Labari Ammh Shuru sun ce Zaina bata je Chan ba,Shi Kanshi Alhaji Tsoho yana Cikin Damuwa sosai Hajiya mama Fadi Take gata yarinya ga juna Biyu Oh Allah ka Tsare wannan yarinyar Nene kuwa dasu Zareena da Zainab suna Tare da Umma ne Domin Tana Bukatar wani Kusa Daita Baban kaduna kuwa yana ta Kiran Abokinsa Dan Jaridanan yana gayamai Shima ba wani Labarin Abun dai sai addu"a.

Sai Zuwa yammah Haddir ya Kira Waya yace Zain ya Farfado Suka Dumguma Dukkansu Harda Umma Zuwa asibitin in ka ganshi sai ka Fashemai da kuka Cikin Kwana Daya zain ya Fita Daga Hayyacinsa sai sambatu yake yana kiran sunan Zaina yana kuka yana Kokarin tashi kan sai yaje ya Nemota Sai da aka kara mai alluran Barci Su Nene da kuka suka bar asibitin Zuwa Gida Daga Umarnin Abba  Dukkansu suka Tafi Gida Umma da Nene sai Zareena da Zafeera da Zainab dasu Saudart su Inna Hannatu kuma dasu Mama Safiya suka koma Gidan Alhaji Tsoho su Abba suka bari a asibitin Wajen Zain bawan Allah.

Koda su Umma suka Dawo Gida Dina bata Gidan ba kuma wanda yabi ta kanta Zafeera Da kuka ya Kodar da ita Ta Taimakama Umma Tayi wanka Tasha Tea ta bata mganugunanta tasha sai barci Ranar ko Salollinsu gamasu Sukayi Waje Daya abinci kuwa sai dai Ruwan Tea suka iya Sha Duk Dauriyan Nene haka ta Zauna afalo Tana kuka Labari kuma yakai Ko"ina Sadiq babba ya Kira Waya yace Shima Sadiq karami ya kirashi ya gayamai Shima kuma Faruq ne ya gayamai Cikin kuka Zareena Daya kira Take gayamai Abunda ya Faru Cikin Rudewa yace Gobe yana Tafe.

Dukkansu suna Zaune afalo Bayan Umma Dake dakinta Tana Barci,Kowa kagani Fuska ta Kode,da kuka kaya kuma Duk ya yamutse Domin Tun kayan Bikin Jiya ne ajikim kowa bama Natsuwar wanka ballatana na Sauya kaya Sai ga Dina ta Shigo Daga Rakiyan Kawarta Zakiya Sun Shigo Falon gabadaya su Nene suka Dago suna kallonsu da mamaki Suma kallonsu suke kafin Dina ta Daga Jajayen Idanuwanta da suka sha kuka Ta kallo Zakiya itama ta kalleta kafin Ta maida kallonta kan su Nenee Wacce Ta Mike Cikin Fushi Lokaci Daya Tana Share kwallar Idanuwanta ta Nufi Su Dina.





*Ki Biya ki karanta Cikin Salama..Duk mace mai aji bata Jiran abun sata In Ta isa Takai Mace Mallakan Komai nata Take...*


*Shakira...*
7/8/21, 11:30 AM - Aisha Srtr Mt: *ZZ....B20️⃣2️⃣*

*IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*

"Cikin Fushi Nene ta isa gabansu Dina Tana Fadin"Daga ina kike..? Kafin nan ma Uban wa ya baki izinin saka kafa ki bar Gidan nan..?

Tafada Cikin Fushi da wani bacin rai,Dina da Zakiya suka kalli Juna Dina ta kasa mgana Saboda bakinta ya fara Rawa ne Zakiya ce ta Bude baki zatayi mgana Nene Ta Daga mata Hannu Tana Fadin"Karki Sake ki sakamin baki badake nayi mgana ba..!

Yadda Nene ke mgana Cikin Fushi yasa su kansu Su Zareena suka Fahimci Tana Cikin Bacin Rai Wanda bako da yaushe ake ganin Fushin Nene ba ammh kuma Bayyanan Bacin Ranta wani Abu ne da kada Mutum yayi Fatan gani.

Zakiya Dolenta Ta Hadiye mganar Bakinta ganin yadda Nene ke binsu da wani kallo kamar takai Musu Duka,Hannu Nene Ta Nuna ma Dina Cikin Wani Tsantsan Bacin rai Tace"Kin san meyasa nayi miki mgana..? Saboda kaddara Ta Hadamu Zama Dake ne kuma kafin Uwarki da Matar mahaifinki su bar nan sun Damkamana Amanarki kuma mun Karba bai Dace mu saka Miki Ido ba Da kuma Cikin Yarona Zaina Dake ajikinki Domin Duk Abunda ya Shafi Zain ba abun Wulakantawan mu bane Ba Domin haka ba ke Har Kin isa..? Kee din Banza Da Wofi Wlh ba Domin wannan Bakar Kaddaran ba, irin ku marasa Tarbiya basu Isa su Tunkari wannan Gidan da ahalinmu gabadaya ba,Tunda kika Shigo Rayuwarmu muke Cikin wani Hali Kin sakamu Cikin Wani Hali Yanzu kuma Gashi Halima ta bar Gida Umma Zareena na kwance Zain na asibiti yana Sambatu Mu kuma muna Cikin Tashin Hankali bamu da natsuwa ammh ke ko ajikin ki ko..? Wlh kada na kara ganin kin Saka Kafa kin bar Gidan nan Indai Batare da Izininmu ba Wuce kibama Mutane Waje mara Tunani kawai..'

Tafada Cikin Sauke Hannuta Dina da Maganganun Nene suka Shigeta musamman ma Datace Zain na asibiti Cikin Wani Hali sai Ta kara Raunana Dama gidan Zakiya ta kwana Ta na Cikin Damuwa Tun ajiyan taso Ma ta Dawo ammh Ta Hanata ganin Tana Cikin Damuwa Ga Ciwon kai ga Zazzabi sai da Tasha mgani,Shine Da safe bayan Ta samu Sauki Dinar ta Damu sai sun Taho Taga Halin da Zain yake ciki Suna Zuwa Gidan Alhaji Tsoho Da Hajiya Mama suka Fara Cin karo Bayan sun gaisa ita take gaya musu Zain yana asibiti chan ya kwana su Umma kuma suna Gida itama sai ahankali Shine suka Nufo Gidan

Da gudu Dina Ta Shige Dakin da aka Sauketa,Zakiya Ta Daga kafa Zata Bita Nene ta Dakatar da Ita Tana Nuna mata Hanyar Barin Falon Lokaci Daya Tana Fadin"Juya ki koma Inda kika Fito..Ba sai kin Shiga ba..Kuma kada na kara ganin kafarki acikin Gidan nan Don Allah ki bari Ranar da Aka Daura auran Aka kai Dinar Chan Gidan Zain din sai ki Share Kafa ki Dinga Zuwa chan ammh nan ki barmu mu Huta hakanan Don Allah.."Ta karishe Fada Idanuwanta suna kara Kadawa

Dole Zakiya Ta Juya ta koma Baya Jikinta Duk yayi Sanyi,Dama Abunda Take gudu kenan Shiyasa Take kwabar Dina awannan Gabar Suna ganin Itace Silan komai Shiyasa Ta gayamata kada Tayi murnan Bacewar Zaina Domin itama Hakan sai ya Ta bata ta

Haka Ta Fice Daga Falon Nene ta Rakata da Tsaki kafin ta koma ta Zauna Kawai ta saka kuka,Zainab ma sai kuka Take Zafeera kuwa sai Sharan kwallah Zareena kuwa Tana bama mai Sunan Umma Nono Jalal Na Gefenta Shima ya Rakube haka su Saudart Dina kuma Tana Ciki Tana ta kuka,Hankalinta Duk ya Tashi Na Jin Zain dinta na cikin wani Hali acikin Ranta kuma Tana ta yi ma Zaina Allah ya isa bata Tafi ba sai da Tatafi da kurwan Zain dinta.

Kiran Daddy yasa Dole ta Tsagaita Da kukan ta Dauka suka gaisa yana Tambayanta Abunda Take bukata tace bakomai yace zai zo Sati mai Zuwa kuma sun yi mgana da Hajiya Maimu tace yakamata Taga Likita,Ko Daga nan Gidan akwai Likitan Dake Dubata ne tace A'a Sai yace mata zai zo Sati mai Zuwa ya ganta,Tace Shikenan sai yazo Daga haka sukayi sallama Ta Zurfafa wani Tunani Tana Tunanin Cikinta ya Shiga Wata na Hudu har ma ya wuce Ta kosa Ta Haifeshi Auranta Da zain ya Tabbbata Shine kadai Burinta.

Su Nene kuwa sallar mangariba ya Tadasu kowa yaje gabatar da Sallah Umma kuma Har Lokacin Tana Barci sai bayan sun idar da sallan ne Zainab Ta Shiga Kicthen Ta Dafa musu Taliya sai Bayan Isha"i Abba ya Shigo Gidan Shima in ka gansa kasan Yana Cikin wani Hali,Duk ya Kode Saboda Tashin Hankali Suna ganinsa suka mimmike suna mai Sannu da zuwa suna kuma Tambayansa Jikin Zain din yace ya barosa har yanzu bai Farka ba Haddir ke wajensa su Baban kaduna ma sun Dawo Suna Gidan Alhaji Tsoho.

Sai da ya Duba Umma kana ya Shige Shashensa yayi wanka yayi Sallah koda Nene ta Gabatar da abinci kasa ci yayi Ruwan zafi kadai yasha Nene ta kalleshi Cikin wani yanayi Tana Fadin"Shuru ba wani labarin Sa"adiyan..?

Abba ya Sauke Numfashi Yana Fadin"Babu Neene..Ba wani Labari..Wlh nayi Nadaman Fushi da na rika nunawa kan Zain Dana saka baki Fatima ta bashi matarsa da Duk Haka bata Faru ba gashi yanzu mun bata Goma ko Daya bata gyaru ba Ga Fatima kwance ga Zainullahi can Yana Sambatu kamar ya Zare ya zanyi Nene..? Wannan Shekaran sai Godiyar Allah kawai.!

Ya Karishe Fada kamar yayi kuka Cikin Wani Tsausayawa Nene ta karisa kusa Dashi Ta Dafashi Tana Fadin"Kayi hakuri...Kaddara ce Bamu da yadda muka iya Allah ya bamu ikon Cinta Insha Allahu Zain zai samu lafiya UmmanZareena ma haka Halima kuma Insha Allahu Zata Fada Hannu nagari kuma Zata Dawo Cikin Koshin Lafiya da ita da Abunda ke Cikinta kawai mu cigaba da gayama Allah.."Cikin gamsuwa da mganarta yace"Ameen Ameen Allah yasa..!

Daga Haka ya koma ya kwanta ita kuma ta Rufa mai Blanket kana ta Dauki Tiran Abincin Data kawo mai Ta Fita Dashi Gabadaya itama Tafe kawai take ammh Rauninta abayanna Ranar Ko ita Datake Bi takan Dina Wannan karon ta Fita Batunta Domin Ta Bala"in Bata mata Rai Abunda Tayi Gidan Alhaji Tsoho Ita Ta lura kowa na Gudun Abun kunya banda Dina Ita Sonshi Take yi ma Zata gane bata da wayau ne in Sakaryace ita.

****

*Kaduna*
Malali Gra..!

Daga Bakin Symbol din Shagon Tundaga Bakin Titi Zaka ga An Rubuta HAJIYA HAUWA UWAR MATA BAGS AND SHOES..!

Daga kallon Farko in kayi ma Shagon zaka Fahimci ma mallakiyar Wajen Ta Kashe Dukiya Domin Duka Wajen Gilas ne,Sai wanda ya gani Waje je mai ban Sha"awa da Tsari Wanda kuma zai Dauki Hankalin mai Wucewa yaji Ko baya Sha"awar Siyan komai sai ya Shiga yaga yanayin Tsaruwan wajen...

Daga Cikin Shagon Kuwa Jakunkuna ne da Taklma Masu kyau da Tsada yan Waje Cikin Kowani Kwaba,Babban Shago ne,Domin yana Fadi kuma yana da Girma kuma Cike da Kaya akwai yaran Shago Guda Biyu Namiji Daya mace Daya masu Taya Uwar mata kula da Shagon Amintattunta Duk da Itama Duka Harkokinta suna Garin Kaduna ne Domin Wajen Shekaru Uku da suka wuce ta baro Zaria Gidanta na nan a Acikin Malali Gra din Sai dai Taje Zaria Ta Dawo Saboda Akwai Harkokinta achan kama Daga Gidan Abincinta Zuwa Matattaran Karuwan data Tara Tana basu matsuggguni Suna karuwanci Suna Bata kudi Duk da Itama Din Tsohuwar karuwa ce mai Zaman kanta sai dai yanzu ajinta ya Girmi haka Ta zama Uwar mata Sai dai Ta samu yarinya Danya Sharaf ta Ji da ita ta kashe mata Kudi yadda Itama Zata jawo mata kudi Ta baza Hajarta Data samu Shiga Shikenan kuma Uwar mata Likafanta ya Daga Da haka Tayi Gida Da Motar hawa ta kuma Mallakin wannan Shagon Gidanta Na Zaria kuma wannan Tsohon mganace Tun Tana gwalewa da kanta Ta mallakeshi ba yanzu Data ke ganin Ta Girma da hakan ba.

Dagachan Karshen Shagon Uwar Mata ce Zaune kan Kujera kawarta Hajiya Zabba"u na Gefenta Tana kallon yadda ake ta Jera kaya Dayake jiya Da Daddare sabbin Oders suka Sauka,Shiyasa tazo Taga yanayin yadda Za"a Tsara kayan Ita kuma Uwar mata Hankalinta na Bisa Wayarta sai Sakin Tsaki Take kafin Ta Dago Tana Fadin"Zabba"u Kina ganin Wulakancin da Sholly keman ko..? Tun Shekaran jiya da Suby Ta Kirani Tagayamin gata Ta Dawo da wata Bakuwa nake kiranta taki Daga Kirana Saboda Iskanci..!

Tafada Tana kallon Hajiya Zabba"u sai Lokacin na kare ma Uwar mata kallo Wata katuwar mata ce mai Kiba,Komai na Jikinta mai Kiba ne Fara ce irin Farin Alluran kanti Gajren Hanci Gareta da wani katon Baki Sai Fuskarta mai Fadi,Hancinta da Hujin Zinare,Haka ma bakinta ma Dauke da Hakoran makka Ja da Fari Hakama Wuyanta da Hannayenta Duka Zinare Tana sanye da Doguwar rigar Shadda gezner,Taji paint work,sai kyalli Take Hannayenta Duka Tayi karin kumba kuma ta Cikasu da kalan Pick har kafafuwanta Wadanda ke Cikin wani Takalmi mai Tsini akallan Farko in kayi ma Uwar mata sai ka Kara kallonta Gata Babbace Domin zata bama Shekara 55 baya ammu Bata yarda Takai wannan Shekarun ba.

Ita kanta Hajja Zabba"u Haka Take Domin wata Narkekiyace anci Bilicin har an gaji cikin Kulawa Tace"Ai Hajja kefa Uwar matace kuma Uwar Sholly kike Kin Fi kowa sanin Halinta.."Uwar mata Tace"Umh...Nasani Zabba"u ammh akallah Ta Daga Kirana Taji kiran me nake mata ko..?

Hajiya Zabba"u Tace"Bazata Daga ba..Kila tasan Dalilin Kiran naki ne.."Uwar Mata ta Bude baki zatayi mgana kenan Taji Wayarta Tayi kara Tana Dubawa Taga Sholly ce ta Tura mata Naira Dubu Dari da Hamsin Cikin Washe baki Tace"Yar Halas muna mganarta..Sai ga alert dinta Ta Turo min 150k yanzu nan.."

Hajiya Zabba"u Tace"Kai Uwar Mata kin yi Sa"an Haduwa Da yarinyar nan Wajen Shekara Hudu kina ta cin Moriyanta..'Uwar mata na wani irin Mirmishi Take Fadin"Bari kawai Zabba"u naci albarkacin Jikin Sholly kuma Har yanzu ina kan ci Inaga Alhaji Badamasi ya Sauke mata Kudi ne kinsan Tafiyar Datayi Kano Ta Rakasa Kai Wannan Alhaji akwai kudi Hajiya Ita kanta Sholly bata sani ba Kowani Lokaci yana Turamin Kudade fa.."Hajiya Zabba"u Tace"Ta sani Uwar mata..Kawai Samun masu Zuciyar Farida Cikin karuwai sai an Tona ne yarinyar Tana Burgeni Iyayanta Sunyi Sa"an Haihuwa sun Haifa kuma sun Bar miki Uwar mata kina Ta Moran Abunki.."Dariya suka kwashe Dashi Suka Tafa kafin Uwar mata Tace"Bari kawai Shiyasa nakeDaga mata kafa...Sholly Bata karya komai Dacinta Sai ta gaya miki Gaskiya Bata kuma munafunci Da Tsegumi Ita fa Dabam Take Na Hadu da Farida Cikin Halin Bakinciki Abunda ya Faru da ita na Dauketa na Taimaketa na Inganta Rayuwarta Kinsam Allah Zabba"u Bani nayi ma Sholly Tayin wannan Harkan ba Ita da kanta Tacemin Tana son Ta zama karuwa mai zamanta kanta Lokacin Danaji Haka naji Dadi Domim komai zai zo Min Da Sauki Tunda na Fahimci Yarinyar ta Mori Abubuwan da Zata Samo mana Kudade,Lokacin Tana Cikin Raunin Abunda ya baro ta da Gida,Tunda Naga na Fara samun Abun Duniya Ta Dalilinta naji bana Sha"awar Watarana Sholly Ta Tuba tace Zata koma garinsu Shiyasa na kai Sunanta wajen Mallam Gobe da Nisa nace ya kara Nesanta ta da Garinsu yakuma kara Wutar Bacin Rai Da Rauni kan Abunda ya Faru da ita wanda zai sa Taji Gwara Tayi zamanta anan Tana Cigaba da zaman kanta ni kuma ina Morarta.."Baki Hajiya Zabba"u Ta saki kafin tace"Ke Uwar mata..Kinfini Bala"i..."

Uwar Mata Tace"Ah ki zauna Zabba"u..Dole yau ma zaki Rakani Zaria zan je naji kan wani Dalili Ta kawo min Wata Bakuwa batare da sanina ba Ko Ta manta abun ya Faru dani ne Abaya..? Nan fa Samira ta kusa akai ni Gidan yari,Ashe Yarinyar Data Daukomana Yar Sandan Ciki ne tazo Leken asirina ne,Karshenta da aka kamani Nan fa kaduna aka kawo ni awulakance State Cid Kamar Wata mara Gata Lokacin ba Domim nasan wasu Yan Siyasa da Ita Sholly Tana Harkan Da masu Garin gabadaya ba ai da yanzu bani a nan Zaune kina Sane dai Yadda akayi Ta Fadi Tashi kafin Case din nan ya Mutu Shiyasa nake Kiyayewa Duk da yanzu nawuce Hakan Domin Dan Zaki ya Riga ya Girma ba kuma yarda Za"ayi Dashi.."

Hajiya Zabba"u Tace"Kwarai kuwa..Ai kin koma Ciwon ido yanzu sai Hakuri.."Dariya suka Sheke Dashi Suka Tafa Lokaci Daya suka Cigaba da Hiransu basu bar Shagon ba sai da aka gama Jera kayan Da komai da komai Wajen Azahar Direban Uwar mata ya Daukesu Zuwa Zaria awata katuwar Bakar Jeep Dinta.

*****

*Zaria..*

Yau kimanin Kwananan Zaina Biyu Cikin Wata Rayuwa Wanda Ko amafarki Bata Taba Fatan Shigowarta ba,Akwana Biyun Datayi Wajen Farida Tayi Nadamar Fitowar Daga Gida yafi Sau Dari Domin Rayuwar Data Shigo ba Rayuwar Da ta saba gani bane Wata Rayuwa ce da kazo nazo,Inda Allah ya Taimaketa Haduwar Ta da Farida Hakika Farida Macece mai Kirki da karamcin Tunda Ta Daukota Bata barta Ta Shiga Wata Damuwa ba komai ita ke mata Wanka kadai Zaina keyi Sai dai taci ta kwanta kawai Farida Bata Barinta Fita Ko kofar Daki.

Washegarin Ranar da Tazo Gidan Haka suka wayi Gari da Fada acikin Gidan Tsakanin Deezee Da Suby Fada mummuna Harda Wukake Duk Dukk su yanke Junansu kamar Wasu mahaukata kuma Abun mamaki Babu wanda ya Damu Dasu balle ya Rabasu,kowa Harkan Gabansa kawai yake Zaina Taji Tsoro Ta Rabe Jikin Bango Tana ta kuka Farida na Gefe Tana danna wayarta Bata ma Lura da ita ba sai da Ta gama ne Ta ganta Tana ta kuka Shine ta Fara Lallashinta Cikin kuka Tana Fadin"Anty Farida..Ina jin Tsoro...Tsoro nake ji..!

Sholly Tace"Kima Daina Jin Tsoro..Domin indai Wannan Abun ne yanzu kika fara ji kuma kika Fara gani..Bariki ba kamar Rayuwar da kika sani bane Rayuwar kazo nazo ne Sa"adiya ki kwantar da Hankalinki Nayi miki alkawarin Ni Aisha Farida Zan zameki Garkuwa Babu Abunda zai sameki kuma ba Wanda ya isa ya Tabaki acikin Gidan nan Ko ina nan ko ba na nan.."Da wannan kalaman yasa

2 / 37