Chapter 6 Reading Zainazain Book 2 Complete By Janafty Arewa Novels

Zainazain Book 2 Complete By Janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   6 / 37

15K to 18K   out of 108.5K words

kika ganni nan Marainiya ce Ta uwa ta Uba Tun ina da Shekara Goma aduniya Iyayena suka Rasu sakamakon Ginin Daki Daya Fado musu Su da karamin kanina Yusha"u Maraici da Rashin Gata ya Kawoni wannan Rayuwar.."Ta Karishe Fada Cikin Kuka Kamar Zata Shide..

Zaina Har Taji Taruwar kwallah Saboda Tsausayin Zuly Cikin Lallashi Tace"Allah sarki Kamar Ni kenan ni ma Tun Ina Da Shekara Daya da wani abu aduniya iyayena suka Rasu..Allah ya jikansa da Rahma.."Zuly Ta amsa da amin kafin tace"Kema Maraicin ne ya kawo ki nan Sa"adiya..?

Zaina Ta Girgiza kai kafin tace"Ban Taba Kukan Maraici ba Zulaihat..ban Tashi na Sanshi ba Ko masu Iyaye basu kai ni samun gata ba..Abunda ya Baroni Da gida Dabam..Kedai nake so ki gayamin Labarinki.."

Zuly Tace"Labarina ba wani mai yawa bane Sa"adiya ba kuma mai Dadin ji bane..Da Farko Dai ni sunana Zulaihat Shehu Yashe ni Haifaffiyar garin Yashe ne ta Jahar katsina Uwana da Uba Duka yan chan ne na taso Naganmu bamu da wani Cikakkun Dangi kuma Mu Takalawa ne masu Neman na kansu,Babana Manomi ne Mamata kuma Masurfiya ce Dashi na tashi Naga suna Rufama kansu asiri Ni da kanina Yusha"u kadai suka Haifa Shima kuma Tare suka bar Duniya,Alokacin Iyayena Nada Rai bana Tallah sun Ingantamin Rayuwa sosai ina Zuwa Makarantar da Allo Data Islamya Ammh Bayan Rasuwarsu sai komai ya Tsayamin Cak na Fahinci maraici da Rashin Gata Baffa Idi Shi ya Daukeni Wanda suke Uba Daya da Mahaifina Shima Dalili Saboda Dan Gidan Da iyayena suka Mutu Suka barmun ne Yasa Ya Daukeni Ya Damkani Hannun Matarsa Larai.



*Ki Biya ki karanta Cikin Salama..Rashin Daraja ne ki Siya abu kuma ki Fitar dashi Waje..Mace mai aji bata Jiran Abun Sata komai nata mallaka take..*




*Shakira...*
7/11/21, 4:56 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B20️⃣5️⃣*

   *IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*

               

"Larai irin Muguwayen Matan kauyan nan ne wadanda basu san komai ba sai kansu da ya"yansu Tunda na koma Gidan Baba Idi nake Cikin ukubar Rayuwa Duka ayyukan Gida ni nake yi ga Tallan Shinkafa Safe da Rana da Yammah kuma Tallah Duka ya"yanta Mata ne ammh bata Dora musu Tallah sai ni,Gashi Baba Idi Shima Dan Duniyan ne Son Abun Duniya kuma Larai Ta Riga Tagama Mallakesa Da Shawaranta yake amfani Gadona kuwa Tuni Ya Saida Gidan Da Shawaran Larai suka Cinye kudin da sunan Suna Taramin kayan Aure.

Makaranta Daga Ta Islamiya Harta Boko Duka na Daina Zuwa Larai Ta hanani Tun ina Son karatun araina Har na Cire Raina ganin Burina bazai Taba Cika ba,ahaka na kwashe Shekaru hudu acikin wannan Rayuwat Duk na Jeme na Lalace Wahalan Rayuwa ta maidani Wata Tsohuwa Rana Tsaka Yakubu Gala ya Fito Neman Aurena.

Yakubu gala Dan wani Babban Manomi ne agarinmu,kowa yasan Yakubu gala ba yaron Kirki bane Shi kadai iyayansa suka Haifa sai suka Sangartasa Tun yana Yaronsa Takadiri ne Dan Shaye shaye ne ba Kwayar Da baya Korawa,Da kuma ya kyalla Ido yaga yarinya In yace yana Sonta zai aureta Shikenan an gama mgana tun Da Dadewa Ake Zargin Yakubu Dala yana Neman Maza Har dai Abun ya Tabbata Saboda in ya auri mace Ta Bayanta yake Nemanta Sai ya gama Morarki ya Dankara Miki Saki ya Kada ki Gida kije Kiyi ta Jinya Daga Karshe kuma Cutar Tsitsontsin Daya Saka Miki a Cikin Ciki suyi Sanadiyar Mutuwarki.

Lokacin Daya Fito Neman Aurena na Tsorata Sanin Halin yakubu Gala Ko shi Lokacin Baba Idi yaso yayi gaddama ammh Da larai ta saka baki Dole ya amince kuma Mahaifin yakubu Galan ya Sakar musu Kudi Alokacib Bani da wata Mafita,Tun alokacin naso na Gudu sai kuma nayi Tunanin Bani da Wajen da zani Ina ji ina gani aka Dauramin Aure da yakubu gala akai ni Gidan iyayansa Ba wani Abun arziki Daga Tabarma sai K'walla da Tukwanen Girki Ranar nayi kuka na kuma Shaida Rashin Gata da Maraici Illah ne.

Adaran Ranar ban Tsira ba Yakubu Dala ya Turmusheni Ya Sadu Dani Ta Baya ina kuka ina Komai yace saboda haka ya Biya Sadakina ammh ai ni kaina na san Cewa bam kai matsayin da zai So ni ba,Nayi kwanan Bakinciki Washegari Tun Safe na Gudu Gida na samu Larai Ina gayamata ina kuka ammh Larai Ta karyatani Ta kuma ta sani Ta maida Ni Tana fada Da mganganu Tana Fadin In na Kashe Auren nan sai dai na Shiga Duniya badai Gidannsu ba.

Wannan Furucin na Larai yasa Bani da wani Zabi sai na Zama da Yakubu Gala yana yadda yaga Dama Dani a kullum sai ya Sadu Dani Ta bayana,Kamar Wata Dabba Safe da Rana da yammah Tun ina kuka har na hakura na Daina Tun Bana Fahimtar yakubu namin Illah har na Fara Fahimta ya Rarakemin Duburata da Rami Sosai sai na Fara Tsorata in yazo sai nayi gaddama haka zai Min Duka kuma ya kwanta Dani yayi yarda yaga Dama,Ganin in na Zauna Ni zan Cuta Ranar yazo zai yi ni kuma naki na bari ya kwanta Dani Ta bayana Ya Fara Dukana Ni kuma sai na Rarumi karfen Da nake kare kofata dashi na Bugamai saman kai ya Fadi a sume jini na Zuba ganinsa ahaka yasa naji Tsoro na Gudu Gida ina Zuwa gida Nayi Ta kuka naki gayama Larai Abunda ya Faru sai Zuwa Dare sai ga Uwar Yakubu gala Tazo Tana Fadin In Danta ya Mutu Nima sai an kasheni nan take gayama Larai naso na kashe mata d'a yanzu haka yana kwance a asibiti baisan inda kansa yake ba.

Da Larai Taji haka sai ta Tsoratar da Baba idi kan cewa In Ya barni nacigaba da zama agidansa Zan jazamai Bala"i Gwara ya Koreni na kara gaba Shi kuma ya yarda Dashi suka Taru sukamin Koran kare ina kuka ina Komai ina Rokonsu ammh basu Tsausayamin ba,Na bar garin Yashe nayi Ta garagaram na Hadu da Wani Dan Daudu shi ya Taimakeni ya kaini Tafa Chan na Hadu da Hajiya Zabba"u Kawar Uwar mata Ita ta kawo ni Zaria wajen Uwar mata Ta karbeni ganin Halin Danake Ciki yasa Ta kaini asibiti Akamin aiki kan Dubura na da yakubu ya Rarakemin Bayan naji Sauki Uwar mata Ta Saka Jarinta akaina Har nayi makari Ta Tallatani kuma aka Siya Da Farko kamar na Shigo Barikin a Sa"a ammh Daga karshe sai komai ya Tsaya na Farko ba kyan Fuska ba na Jiki Har Uwar mata tazo Tana ganin Laifin Hajja Zabba"u Data kawo mata Ni Ta kashe kudi akaina Bata samu Riba ba Daman Batayi Niyar karbana ba ita ta Matsa mata Da taso ma ta sallamani ba,sai Kuma ta Fasa Tunda ganin ina ta kuka bani da Wajen Zuwa Daman kuma Tun Farko Hajiya Zabba"u ta gayamata Labarina da nata bata.

Tun ana Zuwa Daukana Ina House Service har kuma nazo Sai dai kallo Daga nesa,Tun ina sanun Nacin Abinci har yazo yana Gagarana naso Uwar mata Ta Daukeni aiki agidan Abincinta Taki tace bani da kyan Fuska ballatana na Jiki Zan Korar mata Costumer,Dole na Hakura Dama Suby ce kawata Tunda nazo Gidan Itama Bata da Mutumci sai Taga Dama Take samin wani Abu Kacharalle ne ke Taimakona Shima sai yayi kawali ya samu Wani Abu sai Sholly wacce duk Gidan ba kamarta Bata da yarda ammh kuma Abun hannunta bai Rufe mata ido ba Shafsson Da kike gani shi kadai ke Tare Dani Ni kaina Bani da yarda zan yi ne Ina samun na abinci in na Koresa zan Zauna da yunwa bame bani Shiyasa Nake Hakuri Domin Nasani Rashin Gata da Maraici ya kawoni wannan Rayuwar na Gwammace zamana anan sau Dubu kan na Koma Gaban Larai na Tabbata bazasu karbeni ba..!

Zuly Ta karishe Labarinta Cikin Wani Irin kuka mai Dafa Zuciyar mai Sauraro,Zaina da Tun da Zuly Ta Fara bata Labarinta Take kuka Kashirban mai Neman kuka ne aka Jefeshu da kashin awaki,Zuly Ta Dago Tana kallon Zaina kafin tace"kinji Takaitattacen Labarina Sa"adiya..Da ace yau Uwa da Ubana suna Raye da ban Fado wannan Rayuwar da bata da kima ba.."

Take Fada Tana wani Kuka Hawaye Zaina Ta Share kafin Ta Dafa Zuly Tana Fadin"Hakika Labarinki akwai Taba Zuciya..Larai da Baba Idi sun yi Zalunci kuma Allah bazai barsu ba Yansu ina Yakubu galan ya Rasu ko yana Raye..?

Zuly Tace"Ban sani ba..Ban kara Komawa garin ba..Bani da Masaniyar yana Raye ko Baya Raye.."Zaina tace"Allah Sarki..Kiyi Hakuri ki Daina kuka Inshs Allahu Watarana zaki Bar Wannan Rayuwar kuma Zan yi ma Anty Farida mgana Zata Taimaka Miki.."Zuly Ta Share Hawayenta Tana Fadin"Nagode...Nagode Sa"adiya Tunda nazo Gidan nan ban Taba Haduwa da wanda ya tsaya ya Saurareni kuma ya Fahimceni kamar ke ba..Nan Gidan Kowa kansa ya sani kuma babu yarda Saboda Cin Amana Tayi yawa abariki.."

Tafada Lokaci Daya Tana Mikewa Zaina Ta kada kai Tana Fadin"Lalle Rayuwa Darasi ne..In kaji Rayuwar wani sai kayi Tunanin kai kana aljannah ne Allah na Tuba ka yafemim.."Take Fada Tana Sharan kwallah,Zuly Ta kalleta kawai ta kauda kai Ruwan wanka ta Juye mata ta Surka ta kaimata Bayi kana ta Fice Tashi Zaina Tayi tayi wanka bayan ta Dauro alwala Tazo tayi sallah ta Sauya kaya tayi sallah kana takoma Ta Zauna Tana Tunanin Labarin da Zuly Ta bata Allah sarki Allah kadai yasan adadin Matan da suke Shiga Gararin Rayuwa Saboda Maraici Da Rashin gata.

Wajen 2pm na Rana Zuly Ta Dawo Dakin Ta girka ma Zaina Taliya mai Kifi sukaci Tare suna Hira kamar sun Shekara Tare Hakama Da Daddare Zuly Ta Dafa Musu Cuscus suka ci Har Wajen 10pm Farida bata Dawo ba sai Zaina Hankalinta ya Fara Tashi Zuly ke kwantar mata da Hankali sai 11pm sai ga Farida Ta Dawo da Niki nikim kaya Da Ledoji Ta Shigo Sai da Zaina Taga Dawowarta kana ta Sauke Numfashi Zuly ke Fadamata Damuwar da Zaina ta Shiga Dariya kawai Tayi,Ganin Zuly Ta Kula da Zaina yasa ta Bata leda Daya Cikin Ledojin Data zo Dasu Ta karba Tana ta Godiya Ita kuma Zaina Ta bata Ledarta ta Kaza da kuma Ice.Cream mai Sanyi ita kuma ta tube ta Shiga Wanka Bayan Ta Fito ne Tazo ta Fara Rama Sallolinta Tundaga azahar har Isha'i Duk Zaina na kallonta Sai da ta idar kana Zaina Ta kalleta Tana Fadin"Anty Farida ina kika je ne Haka Da bama ki samu yin Salollinki kan Lokaci ba sai yanzu..?

Farida Ta Mike Tana Yaye Hijabin Jikinta Wardrope dinta Ta Turasa Ciki Dama Zani ne ajikinta ta Cireshi Ta saka wata Doguwar Rigar barci mai Taushi Tana Fadin"Naje nema mana Abunda zan Rike ki kuma na Rike kaina Sa"adiya..Kuma Zama ai bai kamani ba Ciki gareki kuma nayi alkawarin Zama Garkuwa gareki Zan kula Dake kamar yayar da zata kula da kanwarta Saboda ki cika ma Firtslove Burinsa da alkawarinsa Ki koma mai Ke da Abunda zaki Haifa Cikin Koshin Lafiya.."

Zaina Da Hawaye suka Cika Idanuwanta Ta dukar dakai kawai Tana kallon Cikinta Farida na kallonta Tana Daga Tsaye tace"Sati mai Zuwa zamu kuma Asibiti ayi miki Scan..Sa"adiya ina Farincikin Haduwa Dake ta sanadinki Zan kara Zama uwa akaro na Biyu aduniya.."Tafada Cikin Wani Rauni Cikin Muryanta Cikin Natsuwa Zaina Tace'Anty Farida a nan Gidan Zan Haihu..?

Farida Ta gyada kanta Tana Fadin"Eh Sa"adiya bamu da wani Gidan Dayafi wannan..Duk da zan iya kaiki wani Waje..Ammh dai bari mu gani In Hakan bai Samu ba zan Daukeki mu koma Wani Waje Daga ke sai ni sai ki Haihu achan mu cigaba da kula da Bbynmu Har Zuwa Lokacin da zan maida ke gida.."Zaina Tace"Tare da Zuly zamu koma ko..?

Farida Tace"Zuly kuma..? Saboda mene Sa"adiya nan zamu barta Saboda Daman nan muka ganta.."Zaina Tace"Don Allah in zamu Tafi mu Tafi da ita Anty Farida..Yau ta bani Duka Labarinta Akwai Ban Tsausayi Cikin Labarin Maraici Da Rashin Gata ya kawo ta wannan Rayuwar nayi Matukar Tsausayamata kuma na kara Jin Darajan Iyalan Alhaji Tsoho acikin Raina da Tun Da nake Dasu Basu Taba barina na Dandani Maraici Ko Rashin Gata ba.."Take Fada Tana Sharan Kwallah Mirmishi Farida Ta saki kafin tace"Yaro Yaro ne..Yaro man kaza...Ban ce kar kuyi Hira da Zuly ba Saboda na Fi yarda da ita kan kowa na Gidan nan ammh ko Ita ban ce ki Saki da ita ba ina Fata baki Fadamata kina da Ciki ba..?

Da Sauri Zaina Tace"A"a Allah ban Fada mata ba."Farida Ta gyada kai Tana Fadin"Yauwa..Kinsan Bariki ba Amana duk yadda kika yarda da Mutum sai yaci Dunduniyarki..Karki Damu in Abun Taimako yazo zan Taimaka mata ammh Ban yarda Ki sakar mata ba,Basu da Amana Kin ji na gaya miki Ina Tsoron ahada baki da ita Watarana acutar Dake."

Zaina Ta gyada kai Tana fadin"Shikenan Anty Farida..Ammh ke yau zaki bani naki Labarin..? Farida na Dannar Wayarta Tace"Ki bari Insha Allahu gobe zan Fada Miki Komai tunda ba inda Zani.."Kada kai Zaina Tayi Tana kallonta ta Dauko wani mgani Ta balla Tasha da Ruwa Sai bayan Ta sha ne ta koma kan Gado Ta kwanta Daman Tun Fitan Zuly Ta sakama Kofar sakata Cikin Lumshe ido Tana Dafe kanta tace"Ib kin gama Chan Ice.Cream din Kizo ki kwanta Sadiya na dawo da Ciwon kai.."

Zaina Tace"Allah ya sauwake..Ammh ya kamata kije asibiti Anty Farida.."Tace"Zan je..Ammh nasha mganin Hawan Jini ina jin Bp ne ne ya Daga.."Cikin Wani Tsausayawa Zaina ke binta da kallo ashekarun Farida bai Dace ace Tana Da Hawan Jini da Ciwon Zuciya ba ammh Wahalan Rayuwa da kuma yanayi ya Jefata Cikin wani Hali.

Zaina Ta Dade batayi barci ba Bayan Tagama Shan Ice Cream Dinta Daga kan Kujeran Datake Zaune Data Runtse ido sai Dai Taga Rayuwarta da Firstlove Tana Gilma mata Allah sarki Haka Take Fadi Tana Shafa Cikinta Hawayenta na Zuba Cikin Muryan kuka Take Fadin"Ka yafemin Firstlove..Nasan aduk Inda kake yanzu kana Cikin Damuwa da alhinin Barinka da nayi alhalin nayi maka alkawarin bazan Taba Barinka ba..ba saboda komai na barka ba sai saboda Kauce ma ganinka a matsayin Mijin Dina na Biyu kuma nayi Nesa Dakai ko Zuciyata Zata Farfado Daga Raunin Datayi na uku kuma na Kula da Abunda Ke Cikina Duk da Umma Soyayyah da kauna ta Nunamin Ina Sonka Firstlove ina so na Tsira da auranka akaina Koda Hakan bazai amfaneni ba."Take Fada Tana kuka Farida na kwance Tana Jinta sai Ji tayi Tace"Bazaki Taba barin ma Wata Mijinki ba Sa"adiya Tun da dai yana Sonki kuma bai Juya Miki baya ba..Yaci amanarki ammh kada ki girmama Cin Amanar nashi na Tabbata ya Hadu da Shedancin Mata Gobe da Safe acikin Labarina Zaki Fahimci Gwara Namiji yaci Amanarka ta Bangaran Rayuwa Da yaci Amanarka Ta bangaran yarda da Amanar da ka bashi Ammh Rana Tsska ya manta Dasu yayi Fatali Dakai ya kuma Kiraka da Munanan kalmomi Saboda Abunda yagani ba Zahiri ba.."Kawai sai Ta jita Tana Shawaran kwallah sai Zaina Taji ai ita kukan Dadi Take yi Da Sauri Ta Share Hawayenta Ta Mike Kazan Cikin ledan Ko Ta bata batayi ba ta Bude Fridge ta sakata Ta Zo Gefen Farida ta kwanta Tana Fadin"Kiyi Hakuri Anty Farida ki Daina kuka..Nima kamar yadda kikayi alkawarin kula dani Har ki maidani gida Nima zan Kula Dake kamar yadda kanwa Zata kula da yayarta Bayan kin maidani Gida bazan bari ki kara Dawo ma Wannan Rayuwar ba Kema zan Kokarta na Rakaki har Gaban Danginki.."

Cikin Daga Murya Farida Tace"Bazan Taba Komawa ba..Koma zan koma garesu sai dai naje musu Ziyaran gani da Ido A matsayin Cikakkiyar KARUWA mai Lasisi,"Tafada Tana Jin wani Bakinciki acikin Ranta Tana ganin Ranar da Abba ya nunata da yatsa yace Karuwa bazata Zauna na mai agida ba Tunda ta kashe Auranta Shima ya sallamata Ta Tuna sanda Anty Take ta kuka Tana Rokon Abba ya Tsaya yayi Bincike yaki Sauraranta Ta Tuna Sanda Mami ta kalleta Tana Zubar da kwallah Tace Kin Cuceni Farida Ashe Dankon Karuwa nayi na Tsawon Wata Tara aciki kuma nayi Nagudarta..? Tir dake da Auranki kike Karuwanci..? Allah ya sakama Musbahu.."

Tuna Haka Yasa Farida ta Saki Bakinta kawai ta Fashe da wani kuka mai Cinrai Zaina ta Tsorata Ta Mike Zaune ta Rikota Tana Fadin"Anty Farida Don Allah ki Daina kuka.."Jin Muryan Sa"adiya yasa kawai ta Fada Jikinta Ta Rumgumeta Tana Fadin"Nasani Rashin Gogggo Ce aduniya na Tsinci kaina awannan Rayuwa yau da ace Goggo Fatu nda Rai na Tabbata Da yanzu Rayuwata bata Koma haka ba..Allah ya jikanki da Rahma Goggota Allah yakai Haske kabarinki Da Kina Raye ke kadai ce Zaki Fito ki gayama su Abba Aisha Farida ta ba Karuwa bace Wannan Sharri ne kuma Kazafi ne."Tuni Zaina Ta Fara kuka Itama jin Abunda Farida ke Fadi Faridan ma kukanta Take kamarzata Shide Zaina Tana kuka Tana Fadin"Anty Farida kece fa ke Hanami kuka indan inayi kece mai Sharemin Hawayena..Don Allah nima Ki bani Dama na Hana Hawayenki Zuba.."Da Sauri Farida Ta Dago kanta Bayan Ta Mike Zaune kan Gadon Idanuwanta sun kala Sun Jajir Tana fadin"A"a Sa"adiya Kiyi hakuri ba zan iya Miki wannwn al'farman ba Ki barni nayi kuka in ina Cikin Wannan Halin wlh Kukan ne Kadai Jin Dadina Wayyo kaina..Wayyo Kirjina Wayyo Zuciyata Ina kewar ya"yana ina Kewar Hassana da Usainata Ina Kewar Al"ameen arif dina Ina Tunanin Wani Hali Suke Ciki..? Kila ma Zubaida ta Kasheminsu Tunda bata kaunata ta Tabbata Bazata kaunaci Abunda na Haifa ba.."Take Fada Tana Sulalewa kasa Ta wani Dunkule Tana kuka kawai Gefe Zaina Ta koma Itama Tana kuka wannam karon ba kukan Tsausayin kanta Take ba Kukan Tsausayin Uwa Wacce aka Rabata da Ya"yanta Allah Sarki Anty Farida Lalle Kinga Jarabawa.

Ranar haka sukayi kwanan kuka ba mai iya Lallashin Wani Daga Baya Farida Tatashi Taje Tayi alwala Tazo Ta Fara sallah Tanayi tana kuka Bayan Ta Idar ta Daga Hannu sama Tana Fadin Allah na Tuba Allah ya femin Itama Zaina alwalar taje ta Dauro Itama tazo Tabi Faridan Sallah itama Tanayi tana kuka tana kuma kallon Farida Da Hannunta ke sama Tana Ta Fadin Allah ta Tuba,Tun Zaina na Zaune kan Sallayar tana kallonta Har Barci yaci Idanuwanta ta koma ta Kwanta nan kasa Sai da Farida ta gama Duka addu"anta kana ta Tada ita ta koma Bisa gado ta kwanta Ita kuma

6 / 37