Chapter 13 Reading Zainazain Book 2 Complete By Janafty Arewa Novels

Zainazain Book 2 Complete By Janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   13 / 37

36K to 39K   out of 108.5K words

Saboda tana ganin Zatayi sanadiyar Rabata da Sholly Saboda Haushi Ko Tsayawa Batayi ba ta bar Garin.

Farida Ta gayama Kacharalle Tana son Gida shi kuma yace ta Bashi kwana 2 sai gashi kuwa an samu wani a gyallesu Tudun Wata Flat house mai 2bedroom da falo sai Kitchen da Tsakar Gidan da Farida akayi Ciniki da Dilallai Miliyan 4 ta Siya Cikin Lokacin Ta Biya kudin Gida aka bata Takardu suka zama nata Washegari kuma suka Tashi da kwasan kaya Mota Guda Farida ta saka Kacharalle ya samo ta kwashe Duka Kayan Dakin Harda kayan sawansu Da duka Abunda zasu Bukata Komai Farida Bata bari ba Zuly kuwa Daman Tun Washegarin Ranar da Abun ya Faru bayan ta Farka Daga Barcin Dolen da Suby ta sakata Deezee ta gayamata Abunda ya Faru Tana kuka Taje Dakin Farida Tana bata Hakuri Tana yi mata Rantsuwan Bata san Komai ba Farida dai bata wani yarda ba Zaina ce Uwar yarda da Tsausayi,Toh Bayan ma an kwashe kayan da yammah Farida ta saka Kacharalle ya samo Musu Golf da zasu Wuce acikinta Koda Zasu Tafi Babu wanda Farida Tayi ma sallama Kacharalle ne ya Daga Murya yace Shalele Hajiya Zatayi Hijira Ita Da Sady Shi ya Fito dasu Rufy Daman Adamalle bata nan Tabi wani Saurayin nata Hotel Service.

Ganin Zasu Tafi ne yasa Zuly Ta Fara kuka Farida ta Tatafi da ita Har da Dukawa Tana Rokonta,Tana Fadin mata bata da kowa sai ita sai Allah Shafson ne Tunda aka sakosa ya haye Mota sai kudu Daman chan yake Zuwa Neman kudi Farida Bataso Tafiya da Zuly ba ammh Zaina ta Fara kukan Tsausayinta Tana Rokon Faridan su Tafi da ita Shiyasa tace ta Hado kayanta su Tafi Tare Zuly sai Murna kamar Zata Suma Irin su Deezee sun manta Murna Kuma suna Kewar Tafiyar Farida ammh banda irinsu Rufy da Suby Da kamar su Xuba Ruwa akasa su sha Har Kofar Gida suka Fito suna ganin Tafiyarsu Wasu na Jimami wasu na kuka sai da Farida Zata Shiga Mota ne ta Juya ta kallesu Ta Daga musu Hannu Tana Fadin Allah kaddara saduwa su Deezee ne da zeezee kadai suka amsa banda su Suby Ita kanta Zaina Tana ma Gidan kallo Karshe har kuma acikin Ranta Tana Fatan Daga Ita Har Farida sun bar kara Dawowa Rayuwar Gidan nan Harda ma Zulaihat din.

Wasu na Daga musu hannu wasu ana agayas suka Wuce Kacharalle ne agaba Domin zai Rakasu Har gayallesu suna Zuwa Daman already Farida ta saka Kacharalle ya samo mata ma"aikata Maza sun Share Ko"ina sun koma Jera komai inda ya Dace sai Abunda ba"a Raasa ba,Kacharalle bai Dade ba ya Koma bayan Farida ta Cikashi da kudi da gargadin ko Uwar mata bata yarda yabama wannan adireshin sabon Gidanan ba yace Alqur"an ba wanda zai gayamawa kana ya tafi Bayan Tafiyar sa ne Zuly da Farida suka Zage suka kara gyara Wasu Abubuwan Dayan Bedroom din Daman Farida ta Siya wata katuwar Katifa 6by 7 tace nan Dakin Zuly Zata Rika kwana Dayan Bedroom din Data kwafa gadonta da wardrope da Sauran kayansu kuma tace ita da Zaina wacce ke zaune Tana Kallonsu Idanuwanta na Cike da kwallar Tsausayin kanta da Tsausayin Yan"uwanta Mata masu baro Gidajen iyayansu saboda wani kaddara.



*Ki Biya ka karanta Cikin Salama...Amanata na baku..Kuma Amanata tana Wajen Allah..*





*Janafty..*
7/17/21, 2:25 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B21️⃣1️⃣*

*IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*


"Rayuwar Zaina a sabon Gidansu Dake gyallesu Rayuwa ce Datake kwatanta ta da Garinsu na Gada,Domin Rayuwa ce Cikin Sauki da Sakewa ba Fargaba babu wani Dar Dar babu Hayaniya Ballatana wani abun da zai Damesu Suna Rayuwarsu ne kai Tsaye kuma su kadai Kullum Gidan yana kulle ne ko Harka da Makota Farida bata yarda su yi shi ba.
Uwar mata Taji labarin Tashin Farida ta Kirata awaya Tana nacin Jin ina ta koma Farida bata Boye mata ba ta gayamata Suna Tudun Wada gyallesu,Jin Dadi da kwanciyar Hankalin Uwar mata Shine da Ta Tabbatar da Farida Bata bar Harkan Bariki ba Domin bata kaunar Farida yau tace ta Tuba ta bar wannan Harkan Domin Babban asara ce agareta Gabadaya.

Zaman Zuly agidan kamar wani Garkuwa ne ga Farida duk da Dai bata cika sakarma Zuly Fuska ba sai dai akwai Shakuwa da Fahintar juna tsakanin Zuly da Zaina,Yes kuma Faridan Tana Jin Dadin Hakan Tunda Tana Fita koda yaushe ta barsu su kadai agidan Tana Tunanin Inda ace ba Zuly batasan kuma wa zata Dauko Ta kular mata da Sa"adiya ba,Ammh Duk da haka Bata Saki Jiki da Zuly ba har yau Tana Tunanin wata Rana Zuly zata iya cin Amanarta Duk da Ta Rantse mata Bazata Taba Fadama kowa ba.

Tun Dawowarsu Gidan yau da suke da Sati Daya da Dawowa Suna zaune afalo bayan sun gama karyawa da Safe Zaina na zaune kam Cafet sanye da Doguwar Rigar Cikinta agaba ta Mike kafa Zuly ta saka mata Filon Kujera Ta bayanta yadda zataji Dadin zama,Tunda kafafuwamta sun Kumbura Alamun Cikin ya Riga ya Tsufa.

Farida na Cikin Bederoom Tana Shiryawa Zata Fita Kaduna zata je Alhaji Badamasi zai aiko da Direba ya Dauketa Tana ta Sauri Tana Daga Cikin Dakin Taji Zaina na Tambayan Zuly" Zulaihat yanzu Watarana zaki iya Komawa Gida..?

Zuly Ta kalli Zaina Tana fadin"Me zai hana Sa"adiya..? Wlh zan koma sai dai Tunani ban san ina zan je ba Na Tabbata Inna Larai da Baffa bazasu karbeni ba,...."Zaina ta ggyara zama Tana Fadin"Me zai hana..? Zasu karbeki mana kuma ma ina kyautata Zaton Cewa zuwa yanzu sunyi Nadama kuma Allah ya nuna musu Kuskuransu na watsi da Rayuwar maraya ni yanzu Bukata gareki Ki Cire komai aranki Ki kuma yi Tuba ga Allah kan wannan Rayuwarki Kiyi istigifari ki kuma yi Niyyar Tsarkaka kanki Daga wannan Rayuwar kiyi Istibura"i Ki Tabbatar Tsarkin Na Dattin wannan Rayuwar da kikayi.."

Zuly Ta Dukar Dakai Kafim ta Dago Idanuwanta sun cika da kwallah Tace"Nagode Sa"adiya..Daman ina ta Fargabane Shin In na Tuban ma Allah Zai karbi Tubana..? Zama na Dake yasa na karu da abubuwa Sosai,naji Dadi da kika gayamin Allah zai iya yafemin Duka laifukana,Daman Tun Tuni naji wannan Rayuwar Ta fita Raina sam Nayi Miki alkawarin na bar Rayuwar bariki har Abada.."Zaina ta Dafa kafadanta Tana Fadin"Karki Damu Zulaihat Ina Tare dake..Duk Abunda kuma baki gane ba Ki Tambayeni zan Koya Miki..'

Da sauri Zuly tace"Yauwa Ina son na Koya Hausa..Karatun Islamiya Harda Turanci ma Don Allah Sa"adiya zaki koyamin.."?Zaina Ta gyada kai Cikin Tsausayin Zuly Tana Fadin"karki Damu Zulaihat zan koya miki iya Abunda na iya Insha Allahu.."Zuly Taji Dadi Sosai Sai Murna take tana ma Zaina Godiya,Farida na Ciki Tana Jinsu Sai dai Ta Murmusa wata kwalla na Zubo mata Tayi Saurin Sharewa Ta Tuna mganar Zaina na Jiya da Daddare bayan ta Dawo Ta Cire kayan Jikinta Zata Shiga Tiolet tayi wanka Zaina ta kalleta Tace"Anty Farida meyassa bazaki bar wannan Rayuwar ba..? Sam bata dace dake ba..?

Sai da ta kalleta Sosai kana ta kada kai Tana Fadin"In na Bar wannan Rayuwar wazai ci Damu..? Wazai kula Dake da Abunda ke Cikin ki..? Karki Damu dani Daman ni Tuni Wannan Rayuwar ta Dace dani Sa"adiya Kedai nayi ma alkawarin Zan kula dake da iya karfina Kuma alkawarin danayi Miki na maidaki gabansu Umma sai na Cikashi ammu barin wannan Rayuwar bata Taso ba Sa"adiya Ko saboda ke da Abunda zaki Haifa bazan zauna ba Dole zam Rika Fita ina Bada Jikina Domin samun Abunda zan Rike kaina dake da kuma Zuly Datake Karkashina.."Tana gama Fadamata Haka ta Shige Tiolet Tana Jin wani kuka yana Taso mata da Nauyin Kirji ba Domin Tana zuwa ganin Likita da yanzu Ciwon nan ya kwantar da ita ko ayanzu ba sai ahankali karfi hali kawai Take in Tana Tuna wani Abubuwan sai Taji bama Rayuwar data dace da ita sai Wannan Rayuwar Tunda Ta rasa Goggo Fatu Tayi Babban Rashi arayuwarta.

Sai da Tagama Shiryawa Tsaf Ta Fito Dauke da karamar Jakarta da wayarta Tana Fitowa Falon ana Kiranta Ta Daga Tana mgana Zaina da Zuly suka Bita da kallo sai da ta gama wayar Zuly ta gaidata ta amsa Tana Fadin"Zulaihat ki kula da Gida da Sa"adiya ku dafa Abunda kuke so kuci Kafin na Dawo...na Tafi Kaduna sai anjima zan dawo.."

Zuly Tace"Allah Dawo Dake lafiya..Ammh bazaki karya ba zaki Fita..? Farida ta yamutsa Fuska Tana Fadin"In naje chan zan karya..Sai na Dawo Sa"adiya.."Zaina ta Daga kai Tana kallonta Fuskarta ba Fara"a tace"Don Allah Anty Farida kada ki kwana achan ki Dawo da wuri.."Farida na Mirmishi sanin Fushin Zaina ta wuce Tana Fadin"Zan dawo...Ko saboda ke Sa"adiyata.."Ba Zaina kadai ba Hatta Zuly sai da ta Murmusa ta Fice Zuly ta Bita Ta Kulle gida Ta bar Zaina ta Lumshe ido Tana Tunanin Hanyar da zata bi Ta Raba Farida da wannan Rayuwar ammh bari ta Haihu Tayi ma kanta alkawarin yadda Farida Za zama garkuwanta itama sai Tayi Sanadiyar Rabata da wannan Rayuwar Data ke Ciki.

******

*Bauchi..*

Zakiya ne Tana Tafe Bayan Tatashi Daga Office dinta Zataje Wajen Dina Domin Tun Jiya Da Daddare Ta Kirata Tana mata kukan ita tagaji da Cikin Jikinta kuma Tana Cikin Damuwar Saboda Kwatakwata Zain Bata gabansa Ko son ganinta baya son yi Tana Tunanin kada Wahalarsu Tatashi a Abanza Jin Irin mganganun Da Dina ke Fada ne yasa ta yanke Shawaran Zataje Ta kwantar mata da Hankali Duk da mutanen Gidan basu Bukatar Zuwanta Zataje ko saboda Dina.

Sai da ta Biya gida Tayi wanka ta Sauya kayanta Kana ta nufi Gidan Abba Dake Gra Tana Cikin Tafiya Motarta Ta lalace,dole ta Daga waya ta Kira Garejin Datake kai gyara Direct da ogan Tayi mgana kan tana so a aiko mata da Yaro Nan Wajen Gra zai Duba mata Motarta nan take ogan yace yanzu zai Turo mata da wani yaro zai Duba mata Motarta ta Insha Allahu.

Jin Haka yasa ta koma Jikin Motar Tajingina Tana Jiransa Tagama yanke Shawaran in yazo Zata barmai key Din Motar ne Ta hau Abun hawa ta wuce Tunda yammh Tayi Misalin 5:30pm na yammah ne alokacin,Tana ta Jiran wajen Shida Saura ta kara Kiran ogan yace Mata kada ta Damu yaron ya Taho yana Hanya Ranta bace ta kashe wayar ta Juya baya Tana Waige waigen ganin Ta Ina Wanda aka Turo zai Bullo.

"Assalamu Alaikum Hajiya Barka da yammah.."

Taji wata Sanyayyar Murya mai cike da Zaki da wani Gardi mai Harbawa da Shiga Zuciyar mai Sauraronta Cikin Sauri Zakiya ta waiwayo Tana kallon wanda yayi mata sallama ido Cikin Ido Suke kallon Juna Tuni Zakiya Taji gabadaya Jikinta yana saki kamar wacce Taga wani Abun mamaki Kallonsa Take Cikin Buguwar Zuciya Dana Gangar Jiki.

Shi kuwa Kallonta yake yana Jifanta da irin Kallonsa da Kuma Mirmishin Dayasan yana Rudar da ya"yam mata komai ajin mace kuwa Ja"afar yasan Kallon da zai yi mata taji Abun yana Shiga Cikin Zuciyarta Har Tsakiyan kanta.

Sanye yake da Riga da wando blue Na kayan Kanikanci Wadanda sukayi baki Duk bakin mai alamun kayan aiki ne Kafarsa Sanye da Takalmi Shaku Shaku Shima Duk yasha Baki da Wahalan aiki ammh Duk ba wannan ya Damu Zakiya ba Illah kyan yaron da kuma Tsabar Haiba da kuma Wani irin kwarjini Dayake  Dashi wanda yasa Ta kasa Dauke Idanuwanta akansa Bata san Dalilin Daya sa Zuciyarta Take Bugawa Tana Tsalle Waje Daya in Tana kallon kwanyan Idanuwansa ba.

Farin Namiji ne Dogo gint Karkkarfa Mai Dauke da Dogon Karam Hanci mai Dauke da Sexy eyes,sai Bakinsa karami mai Dauke da Pick lips,Doguwar Fuskar garesa kana mai kallon Farko Zaka Fahimci Duk inda ya Fito ya Hada Iri da Fulanin asali Ko kuma Shi din Ruwa Biyu ne kyakyawa ne ajin Farko Ya Dace komai Daman an ce Mutum Tara yake bai Cika goma ba ammh acikin Zuciyar Zakiya Tana ayyana wannan Zankadeden Saurayin ya gama Samun Goman Cif Cif a bangaran kyau da Zati.

Ta Shagala da kallonsa Yana ta mgana Bata Jisa ba sai da ya saka Hannu ya Kada mata a saman Fuskarta kana ta Dawo Cikin Hayyacinta Firgigit Tayi Tana kallonsa sai kuma taji kunya Tayi saurin kauda kai Mirmishi yayi kafin yace"Hajiya nine wanda oga Usman ya Turo..Ina ne mtsalan bari na Duba Miki.."

Yafada Cikin Sanyayyar Murya Daburcewa Zakiya Tayi ammh Tunda tasan kan Duniya sai ta wani Rausayar dakai Tana Bashi Key din Motar Tana Fadin"I don"t know..Kawai Ina Cikin Tafiya sai ta tsaya kum nayi nayi tatashi Sai kuma Taki Tashi.."Tafada Tana kallonsa Shima kallonta yake kafin ya karbi Key din Yana Fadin"Ok...Bari naDuba.."
Daga Haka ya Bude Murfin Motan yaShiga ya Tada ita yana Dubawa Zakiya na GefeDuk wani Motsinsa Tana gani Gabadaya jikinta ya saki Idanuwanta sun kasa Dauke Ido daga kan Wannan Saurayin wanda Ta Tabbata ta Girmeshi Domin in yayi Shekaru bai Wuce Shekarun Sahura Kanwarta.

Daga Cikin Fiton ya motan Ya Daga gaban Motan yana gani Duka Tana Tsaye Tana kallonsa Kayan aikinsa ya Fito Dashi ya Fara gyara kenan ya gano Mtsalan Saboda Shagala da kallonsa sam Zakiya ta manta Shawaran na Tafiya tabar mai Motar Cikin 30min Sai gashi ya kamallah gyara ya Rufe mata gaban Motan ya Shiga Motan ya Tasheta sai gashi Tatashi Tana Tsaye Taga yayi gaba kadan kana ya Dawo Baya ya Kashe Motar ya Fito Zuwa gareta Key din ya Mikamata yana Fadin"Hajiya ga key...An gama gyaran da yardan Allah.."

Zakiya Ta kalleshi kafin Ta saka Hannu Ta Karbi key din Tana Fadin"Yauwa Nagode..Nawa zan baka kudin gyaran naka..?

Kai ya sunkuyar kafin yace"Ah Bakomai Hajiya wannan gyaran ai bamai yawa bane ki barshi kawai.."Galala Zakiya ke kallonsa kafin tace"Haba dai Taya zan saka aturo ka kuma sai kaki karban Kudinka.? Ai Hakkin kane ya kamata ka karba Don Allah.."Tafada Tana Zaro mai yan Dubu Dubu Guda Biyar Daga Cikin Jakarta Kin Karba yayi sai ta matsamai kana ya Karba yana ta mata Godiya yana Shirin Hawa Mashin Haya,Tace kada ya hau ya bari ta maidashi Garejin Ba yadda ya iya Haka taDaukeshi agaban Motarta Zuwa Chan Garejin nasu Bata Shiga ba Daga Bakin Garejin ta saukesa Bayan yayi mata Godiya zai sauka kenan ta kalleshi Wanda Daman Tunda ta Daukoshi Take kallonsa Shima Daya Lura da haka sai ya Dinga satan kallonta da wadandan Idanuwan nasa.

"Me sunanka..?kai dan nan garin ne..?kai yagirgiza mata kafin yace"Sunana Ja"afar Ni Dan asalin Garin Yola ne.."Zakiya ta Jinjina kai kafin tace"Ja"afar Nice Name...Kana da waya ahannunka..?bai mata mgana ba ya saka Hannu a aljihun wandonsa yaFito da Wata karamar Nokia Duk taci Ubanta yana Fadin"Eh Ina da ita gata ma.."Zakiya Ta kalleshi Cikin Tsausayawa ganin ga Namiji Har Namiji ammah Babu abokam Rayuwa,Wayarta Ta Ciro Dake cikin Jakarta Ta mikamai Tana Fadin"Sakamin Lambarka.."Cikin Sanyinsa ya karbi Wayar ya saka mata Lambarsa Yana Mika mata wayar ta Karba Tayi Saving din Lambar ta Kirashi sai ga Kiran ya Shigo Sai ta katse ya kalleta yana Fadin"Wani suna zan saka Hajiya..?

Zakiya na wani Mirmishi Tace"Zakiya zaka saka.."Cikin Sanyin Muryansa yace"A"a Hajiya Zakiya dai.."yafada yana wani karya wuya kai ta Girgizamai Tana Fadin"No..Zakiya dai zaka saka ni ba Hajiya bace..Ko Hajiya nake awajen Ja"afar ai ba Hajiya nake ba Zakiya ta nake ko..? Ta Fada Tana kashe mai Ido Daya sai ya wani Daburce kamar bai saba gani ba ya Bude Murfin Motan ya Fice yana Fadin"Nidai Hajiya Zakiya zan saka..Waye Ja"afar Dake bazaki zama Hajiyarsa ba..?

Kai kawai Ta kada kafin tace"In na kiraka zaka Daga Kirana.? Kansa ya Leko Dashi Ta Glass din yana Fadin"Me zai Hana Hajiya..? A shirye nake dana amsa Dukkan Kiranki Insha Allahu.."Mirmishi Ta sakarmai Tanakallonsa kafin tace"Nagode.."Hannu ya Daga mata itama Tadagamai kafin Taja Motar ta Tayi Riverse ta koma Kan Hanyarta na Zuwa Wajen Dina Ja"afar Dake Tsaye ya Bita da kallo Lokaci Daya yana Shafa Siraran Gemun da suka Fito Allah kadai yasam Abunda yake sakawa acikin Ransa game da Zakiya.

Zakiya Tana Shiga Falon su Umma ana Kiran Sallar mangariba Kusan tare suka Shiga da Zainab Cikin Sabuwar Motarta Itama 306 wacce Abba ya Siyamata ta Dawo Daga makaranta sai ta Biya Islamiyan su Sauda ta Daukosu Kallon Kallon sukayi ma Juna Tsakaninta da Zakiya ba wanda yayi ma wani mgana kuma kusan Atare suka Shiga Falon Gidan Nene ce kadai Zaune afalo Tana kallon Tashar africa Tv,Umma ta Shiga Dakimta Zatayi Sallah da Gudu su Saudart suka Nufe Nene Dake musu oyoyo,Zainab kuma ta Zauna Kusa da ita sai Lokacin Nene Taga Zakiya gaisheta Zakiyan Tayi ta amsa Fuska ba Fara"a Kafin Tayi Shuru Tana Tsaye ganin haka yasa Nenen Tace ta Shiga Ciki Dinar Tana Cikin Jin Haka sai ya bata kwarin Gwiwan Tashi Ta Nufi Dakin Dinar Nene da Zainab suka Bita da wani Sakaran kallo.

Tana Shigewa Dakin Zainab TaRakata da Tsaki Tana Fadin"Wlh Nene na Tsani ganin Dinar nan agidan nan wai bazatayi ta Haihu bane ta kama gabanta ba Kowa ma ya Huta..?

Nene tace"Ko ta Haihu ba gabanta Zata koma ba Gidan Yayanku zata koma Zainab..Ya muka iya Wannan Abubuwan da suka Faru sune kam namu kaddaran sai Fatan Allah ya Tsaremu kawai Allah kuma ya Sauketa Lafiya,sai a daura musu auran Tatare gidan yarona Ina ce ba komai ya kare ba..?Zainab Ta kada kai Tana Fadin"Umh...Yanzu Nene shikenan Har yau ba Labarin Anty Halima ko..?ko yau sai da mukayi mganar da kawarta Anty Laila bayan mun Hadu a masallacin Cikin makaranta baki gani ba Nene Wlh sai Sharan kwallah take muna mgana Yau.."

Nene ta Sauke ajiyar Zuciya Tana Fadin"Uhm..bari kawai Zainab...Muna yau mukayi waya da Goggo Halima Daga Chan Gada suma sunaTsumayin jin wani Mgana Daga garemu muma Shuru ne Zainab Mukam bama Cikin kwanciyar Hankali Ballatana yarona da kullum yake karewa a tsaye kamar kudin Guzuri saboda Batan Halima,sai dai kamar yadda Alhaji Tsoho yace addu"a ne kadai mganin Komai Insha Allahu mu Cigaba da gayama Allah Halima zata Dawo Cikin Koshin Lafiya.."

Zainab Tace"Allah yaso ya kuma yarda Nene..Zafeera ma yau munyi mgana Ita kanta ga karatu ga Damuwa Nene.."Nene tace"Ai ba ita kadai ba Duka Ahalin gidan ne Sai dai mu Tayata da addu"an Allah yasa ta Fada Hannu nagari yasa koma Tsakanimmu akwai Rabon ganawa.."Zainab ta amsa ta Ameen kafin ta tashi Ta Shiga Ciki su

13 / 37