Chapter 18 Reading Zainazain Book 2 Complete By Janafty Arewa Novels

Zainazain Book 2 Complete By Janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   18 / 37

51K to 54K   out of 108.5K words

ya shiga ya gani Tare da Hajiya Mama suka Kutsa Dakin suka iske Dina Ta fita Daga kamaninta Ta Cire duka kayaanta Daga ita sai karamin Sikat duk ta Fixge kanta kamar Wacce ake yankawa Yana kallonta ya Fahinci Juyin Ciki ne ba Haihuwa bace Haka kuma yagama su Nene yace zai Tafi Cikin asibiti ya Dauko allura zai zo yayi mata Zata samu Sauki Daga Nene har Hajiya Maimuna sun Fara gajiya da Ihun Dina da kururuwa harda Hajiya maimuna Bayan Fitan Haddir ta Dauki Zanin Dina Tana Rufemata Fararan Cinyoyinta Dake Waje Tana Fadin"Don Allah dago kanki Dina..Dakike wannan Ihun banza naki bana Haihuwan bane Juyin Ciki ne Toh.."

Duk da Dina na Jin azaba sai da Tadago Fuska Duk Majina da Hawaye Tana Fadin"Ummi Juyin Ciki..?kina Nufin wannan bama Nagudan bane..? Hajiya mama ta Murmusa Tana Kallon Dina Tace"Haihuwa..? Daman kuna Jinta ne kawai abaki baku santa ba ko nace kuna karban Haihuwan ne batare da kusan Wahalarta ba Naguda Dabam Take sai Kinzo yinta Zaki Tantance ya take ammh Wata mace Bata isa ta Fayyace miki ya Zafin Naguda yake ba Shiyasa Akace Mace mai Naguda kafarta Daya aduniya ne Daya Lahira in kuma Ta Rasu alokacin Haihuwa tayi Shahada Saboda Girma da kuma Wahalar Dake Cikin Ita kanta Nagudan da Haihuwan.."

Dina Sai Taji kukanta ya kara Yawa,Tana Tunanin ahaka ma Ba Nagudan take yi ba kenan Innalillahi,Bata Taba Zaton Haka Zafin Masu Ciki yake ba Tasha karban Haihuwa Ta Dinga ma Mata Masifan sun damesu da kuka ashe ashe Haka suke ji sai ta kara Sakin kuka Tana jin Nadamar Biyema Shaearan zakiya yanzu duk wannan Wahalan Tanayinshi wajen Haihuwan Dan Shege ne kai Abun yazo mata Cikin wani yanayi ai sai ta koma Tana kukan Kasa kasa ba Dadewa Haddir yazo da Abun awom Naguda ya sake Dubata ya Tabbatar da ba ita bace ammh any Moment Tana iya Zuwa allurai yayi mata Harda na Barci nan kasa ta Bingire Tana Barci kamar wata mahaukaciya Hajiya maimuna da Nene suka Kamata suka maida saman Gado.

Haddir shi ya Fita Falo yana ma Abba Bayanin ba Haihuwa bace Juyin Ciki ne,Umma na Gefe Sai da Ta Dara aranta tace Iskancin yarinyarnan dayawa yake Tunda tasan ta Gwale kafa Tabi Namiji ai sai ta Shiryama Haihuwa Sai alokacin Hankula suka kwanta Tunda ta samu Barci sai Gabda Asuba Haddir ya Dauki Hajiya mama suka Koma suka Iske Alhaji Tsoho ya kasa Komawa Barci Daman yace in Takai Safe bata Haihuwa Dole akaita wani asibitin Kudin ta Haihuwa achan kar abarta agida wani Abu ya Faru Sai yaji aiba Haihuwa bace Hajiya mama sai Fada take Tana Fadin sai Rakin Tsiya ammh da sai Iskanci Haddir na Jinta bai Tankata ba.

Washegari da Safe yaje Office Din Zain bayan sun gaisa ya kallesa yana Fadin"Ya mai juyin Ciki. ? Hop bayan Tatashi ba Wata mtsala..?

Zain na Cigaba da Duba Folder din Patient din dake gabansa yace"Wata mai Juyin Cikin kenan..? Haddir yace"Dina mana ko kana Nufin duk wannam Ihun Data Dinga yi baka Ji bane..?

Karamin Tsaki Zain yaja kafin yace"Mtseww..Naji sai me..? Zan fito na Tayata ne ko kuwa.? Ai ita Ta Neman ma kanta Ta zata Haihuwan wasa ne..? Ai Mace Daya ce Zaka ga Tana Cikin Wannan Halin na Dimauce Firstlove dina itama Ina kyautata Zaton Duk inda Take ta Kusa Haihuwa kuma zanji ajikina Koda bama Tare ammh Wannan Tsinanniyar yarinya Dana Tsana wlh Ina addu"an Allah yasa ta Mutu Daga ita Har Abunda ke Cikinta.."

Da Sauri Haddir yace"A'uzubillahi Haba Zain wannan kalmar bai Dace ba ko bakomai ai Cikin Jikinta nakane kuma babu kyau yima Bawa Fatan Mutuwa kaima ka sani.."Tsakin ya kara ja yana Fadin"Gwara ta mutu yanzu.ammh in ta Bari ta Rayuwa Ta kuma yarda Aka Dauramama aure Wlh sai na Kasheta da Bakincikina yadda Sanadinta na Rasa nawa Farincikina Nima sai Nayi sanadiyar Rasanata Farinciki.."Daga Haka kawai ya Mike yana gyaran Zaman Tektie din Wuyansa ya Bude Kofar Office din ya Fice ya bar Haddir baki Hamgame yana Binsa da kallo kai ya Girgiza yana Tunanin wani abu Tabbas yaga Tsanar Dina mai tsanani akwayan Idanun Zain Tabbas Zamansu bazai yi Dadi ba.

Ranar Daya Dawo da yammah Nene ta matsamai sai ya Shiga ya Duba Dina Batare data Sani ba ya Gudu Gidan Alhaji Tsoho ko gidan ma bai kwana ba Washegari ma Haka Daga asibiti Chan ya wuce Daga Alhaji Tsoho har Hajiya mama ba wanda ya Tambayeshi Ba"asi Haddir ne ya san Abunda ya Faru Dayaje gidan Duba Dina Nene ke Fadamai har Abba na Fadan meyasa Take Takuramai ne ta Kyaleshi Tafasan Halin Dayake Ciki Dina kuwa Tagama Fita kamininta Tun kafin ma Ta Haifi Abunda ke Cikinta.

*****

Kwana uku da Faruwar Haka Nagudar Gaske ta kama Dina Wannan karon da asuban Ranar Alhamis ne Tatashi da Abun Daga Shiga Tiolet Tayi Fitsari Sai bayanta ya Kage Daganan kuma sai Taji wani azaban Ciwo ya Biyo baya mai Wuyar Misali Ta Fara kuka Tana Kiran Sunan Hajiya maimu Wacce ke Tahiyan Karshe na Sallar asuba da Sauri Ta Sallame ta Runtuma cikin Bayin..
Halin Data samu Dina ya Tabbatar mata da Cewa Haihuwa ce Tazo mata Dakyar ta kamata suka Dawo Falo bayan Wayyo Allah da zan Mutu Ummi bayana Kafafuna kuguna Zan mutu Babu Abunda Dina Ke Fadi.

Nan kan Cafet Ta kwantar da Dina Wacce ta Saki Jikinta Gabadaya Tana wani Mirginawa Cikin azaban Ciwo Bude Kofa Hajiya Maimun Tayi Ta Fita Zuwa Dakin Nene ta kwankwasa mata Daman itama Ta Idar da salla Lazimi Take Taji Buga Kofa arude Tatashi Ta Bude sai Taci karo da Hajiya maimuna Tun ma kafin tace wani Abu ta Fahimci yau Dina ana kan Gwiwa.

Cikin Sauri Suka Nufi Dakin Umma Hayaniyarsu Nene ya Fito Da ita Daga Daki ita da Zainab Ganin Kofar Dakin Dinan abude yasa suka Fahinci komai Tare da Zainab suka Shiga Dakin sai dai Halin da Zainab Taga Dina yasa Dole ta Fice bata da komai ajikinta sai Wata karamar Rigar Barci Ko pant bata Dashi sai Faman Bude kafa Take Tana kiran Wayyo Allah Hajiya maimuna na Buge kafa Tana Fitowa suka ci karo da Abba ya dawo Masallaci Daman Zain bai kwama agidan ba Tun Ranar dayayi musu Yaji yana Gidan Alhaji Tsoho.

Zainab Tagayama Abba Ga Halin da Dina ke Ciki,Ba bata Lokaci ya Kira Alhaji Tsoho ya gayamai shi kuma yayi mata addu"am sauka Lafiya Nan take ya Shaida ma Hajiya mama ya kuma Umarceta da Su Tafi ita da Haddir da Zain ammh Koda Suka Dawo masallaci Hajiya mama Ta taresu da Halin da ake Ciki Tsaki kawai Zain yayi ko mgana bai yi ba ya Shige Dakin Haddir ganin haka yasa Hajiya Mama tace Haddir din ya Taho suje ya Dubata bai yi gaddama ba ya Sauya kaya suka Tafi Gidan Abba.

Koda sukaje Dina Ta Fara galabaita Da Fita Daga Cikin Hayyacinta Haddir yana ganinta yace Haihuwa ce,Shi kuma bai da wasu kayan aiki anan Sai dai atafi asibiti Hajiya mama Ta Kira Alhaji Tsoho ta gayamai yace Bayason mganar nan Ta Fasu a garin Bauchi ne Acigaba da mata addu"an Allah ya Sauketa Lafiya yanzu zai yi Mata addu"a aruwan Zamzam Zain zai zo Dashi yanzu..Da Mganar Alhaji Tsoho kowa yayi Cirko Cirko ana Jiran ikon Allah kawai ammh Duk mai Imani yaga Dina sai ya Tsausayamata Sosai Hatta ko da Umma yau da ita acikin Dakin tama manta Abunda Ke Cikin Dina Dan Shege ne.

Misalin Karfe 7:30am na Safe Zain Da ko ajikinsa ya Shirya zai Tafi asibti Alhaji Tsoho ya Ritsashi ya kuma bashi Ruwan addu"a yace yakai Gida yanzu abama Dina tasha Ba yadda ya iya Haka ya karba ya Tafi yakai iyakarsa Falon Gidan inda Zainab da Haddir da Abba ke Zaune Abba kadai ya gaida ya Mikama Zainab Ruwan addu"an awani Jug ya Fice Daga Haddir har Abba kanzil ba wanda yace mai.

Zainab Bata iya Shiga ba Umma ta kwalama Kira ta Leko Ta karba,Ta Shiga Dashi Nene da Hajiya Maimuna suka Tada Dina suka Bata Ruwan addu"a Kadan tasha ta koma ta kwanta Tana Sauke Numfashi ai wasa Farin Girki sai Dina ta Rikice Naguda ta Dawo Sabuwa,Nene ta lekata Taga bama alamun kan yaro na Tahowa da alamun Dina Zatayi Tsawon Naguda kenan kuma mace mai Tsawon Naguda Wahala take Ci sosai.

Tun abun ana Daukansa wasa Har yaWuce wasa Tunda Har Goma na Safe Dina na Fama bata Haihu ba,Daman tun Safen Hajiya Maimuna ta Kira Hajiya Batula tagayamata ta kuma ce ta gayama Kwamishina Cikin Dubara Allah yasa yana Gida yana jin Labarin Dina na Naguda Hankalinsa ya Tashi ya Hada musu Tafiya saboda Sauri ma Flight sukabi Zuwa Bauchi Saboda su isa kan Lokaci aikuwa Misalin 11am na safe sai gasu sun iso sai dai aka gansu kwatsam.

Kwamishina Dai bai Shiga Dakin ba nan Falo ya Tsaya Wajensu Abba da Haddir wanda ke Shiga yana Dubata Lokaci Bayan Lokaci ammh Daganan suna iya jiyo muryan Dina Cikin Raini da galabaita Tana Kiran Zata Mutu Ko Hajiya Batula Data ga Halin da Dina ke Ciki sai da Taji Ta bata Tsausayi Tana Tunanin yau inda Dan Sunna ne ai baza"a ki kaita asibiti ba ammh Gudun Fasuwan mganar angwammace Tayi ta Shan wuya agida.

Sun bata Ruwan addu"an Duka ta Shanye Haihuwa Shuru Alhaji Tsoho nata Kira Haddir na Gayamai bata Sauka ba yafara Tunanin akaita asibiti kada Yar Mutane ta Mutu Sai ya Kira Abba awaya yace mai Su Hajiya Mama su Dauki Daina Haddir ya kaisu wani asibitin Kudi Dake Cikin gari Ta Samu kulawa Achan kila ta sauka Lafiya Abba yake shaidama Haddir shi kuma Sai yace A"a Yace Abba ya Jirashi yana zuwa ya Fita da Sauri ya Shiga Mota sai Cikin asibiti Yana Zuwa kai Tsaye Office din Zain ya Nufa yana Shiga ya Iskesa yana Duba wata mara Lafiya yanayin yadda yaga Haddir din ya Shigo aransa yaji Dadi Domin ya zata Zai ce mai Dinar ta Mutu da ita da Abunda ke Cikinta ne sai kuma yaji sabanin Haka Haddir sai yayi ma karyan Cewa Alhaji Tsoho yace ya dauki kayan aiki Yaje gida ya Duba Dina Tunda Bangaransa ne kada Ta Mutu agida.

Da Farko yaso yaki Zuwa ammh Jin Alhaji Tsoho ne ya Umarcesa sai yakasa yin gaddama hakanan ba Domin yaso ba ya Kwashi kayan aiki suka Tafi Kowanne ya Shiga Motarsa Koda suka je suka iske Abun mamaki Hatta su Abba suna Dakin,Suna Shiga suka iske Dina Rike da Hannun kwamishina Tana kuka Tana Cije baki Sai dai An Rufe mata Jiki da wani Zani Fadi take su kira mata Zain ta Nemi Yafiyarsa kafin ta Rasu sai gasu sun shigo..


Tana ganinsa Sai ta saki Hannun kwamishina Tana kallonsa Cikin Wani azaban Ciwon Da Dina Take Tunanin Bazata Rayu ba Burinta na auran zain bazai Cika ba Ta Kiran Sunansa"Zainnn..."

Kallonta yayi Ido Cikin Ido ya Tsaya Cak da Karamin akwatin kayan aikin Dake Hannunsa Haddir ne ya Turasa yana Fadin"Kaje mana Zain.."Taku Zain ya Farayi Kowa na Binsa da kallo Har Zuwa gaban Dina Tun kafin ma ya Durkusa ta yafito Hannayensa Cikin Fitan Hayyaci Take Fadin"Ka yafemin Zain..Don Allah ka yafemin ko Zan mutu naje gaban Allah Cikin Salama Hakika na Cutar dakai Nice Silan komai nice Silan Barin Zaina Gida Nice Sillan Zubar da Kimarka Data iyayanka kuma Nice sillan Fushi da iyayenka keyi akanka Duka nice Sila ba Saboda komai ba sai saboda son da Nika maka da kuma Idona ya Rufe wajen Mallaka ka ammh Wlh ba Laifina bane Zakiya ce ta Dorani kan wannan Shawaran Don Allah ka yafemin.."

Take Fada Tana kuka Ga Zafin Naguda Sai Umma sai suka zama wasu Shuru suna kallon Ikon Allah Kwamishina ya kalli Dina yana Fadin"Meya Faru Dota..?Dina na kuka tana Fadin"Kaima Daddy kamin afuwa nayi sanadiyar bata maka Suna...Domin neman wani Cikar Burina Ban Taba Duba Hakan dana aikata wani Illah ne gareka ba amtsayin ka na Mahifina Daya bani Kowani Jin Dadin Rayuwa.."Kanta ya Shafa Cikin Tsausayinta yana Fadin"Bakomai na yafe miki Duniya da Lahira Dina Allah ya saukeki Lafiya .!

Zain kuwa Daya kusa yaji Wani irin Laifi Dina ke Rokonsa da ya yafemata Cikin Karfin Murya yace"Ina Jinki wani Laifi kikamin Da kike Rokona gafara..? Kuma ya akayi yau kika yarda duk kice sanadin komai.?."Dina Dataji wani azaban Ciwo ya Dawo mata ta Dafe bayanta Tana Fadin"Na Cutar dakai wajen Baka kaina kana Lalata dani Mganar gaskiya ni nakai kaina gareka bakai ka kawo kanka ba kuma na Zalunceka wajen kai sunanka Wajen Boka ya sakamaka Wata Muguwar Sha"awata wanda in baka Kusanceni bazaka iya Rayuwa ba.."Gabadaya Dakin sai aka Dauki Salati Hajiya Mama na Tafa Hannu Tana Fadin"Nifa Koda naji wannan Batu..".

Ita kuwa Zainab Daman Tunda Dina Ta Fara mgana ta Kira Zafeera Bayan ta Dauka tace ta Saurari abunda ke Faruwa Umma kuwa acikin Ranta Sai Taji Wani iri ashe daman Zain ya Hadu da Shedaniyar Macece Dina kuwa Cikin azaban Ciwo ta Shiga Bada Labarin komai da yadda Zakiya Ta Hada Duka plan dinsu da komai da komai da hotunan Data Turama Zaina Har zuwa yau din nan sai da Ta Fadamusu ta karishe da kuka Tana Fadin"Don Allah Umma Nene Da Abba ku gafartamin Wlh ko hanyar Gidan Boka bansani ba Zakiya tajani takaini Ina Son Zain na Tsakani ga Allah banta Tunanin zan iya Cutar dashi ba..Gashi yau Ina Dauke da Cikinsa bata Hanyar aure ba,ina ji ajikina Mutuwa zan yi Me zan je na gayama Ubangijina kaichona Na Tabbata na zama asararriya na Taso Tun ina karama na Cikin Sakewa wanda Daddyna yabani Damar ganin Komai na Rayuwar nan zai iya Nema kuma in samu ashe ba haka bane Ina ji ajikina Zan Mutu..Mutuwa zan yi Don Allah Zain ka yafemin.."

Zain da mamaki suka gaba Sandaranshi Dashi Idanuwansa sun kala sunyi Jajir yama kasa Wani Motsi Haddir kuwa daman aransa yasan za"a arina Zakiya tafi Dina zama Shedaniya Abba kuwa sai yaji wani Sanyi acikin Ransa Da Zain ba Cikin Hayyacinsa yake aikata Zina ba Hakama Umma da Nene Hajiya mama kuwa baki kawai ta Rike yayinda Hajiya Batula tace"Uhmm..Za"a rina Daman ammh ai Dukkanku Shedanu ne in ita Ta zama Wacce Shedan yama Fitsari akai kefa..?

Hajiya Maimuna kuwa Ajiyar rai ta Sauke Tana Fadin"biri yayi kama da Mutum..Daman ni Tuni nasan wannan kawar Taki Dina ita ce ke Doraki kan wani Shedanci Tur Allah ya Wadaranku Wlh Daga ke har ita.."Daddy kuwa zaune kawai yake ya kasa mgana to yace me..? Shima yasan Shedaniya ce Sai ace kuma ka barsu tare da yarka..? Dole yaja Bakinsa yayi Shuru ransa na kuna wani Shashi na Zuciyarsa kuma yafi ganin Laifinsa akan kowa.

Hajiya Maimuna Ta Kalleshi Cikin matse kwallah Tana Fadin"Duk Lalacewar Dina ba Laifin Kowa bane ssi naka Gaddafi..Da ace sanda Sarah ta Rasu ta kabamu Rikon Dina da Duk Haka bata Faru ba da kuma ace ka zauna ka kula da ita baka Sakrmata ba da Haka bata Faru ba Tun Sarah nada rai Siyasar ka kadai ka sakama gaba ba Ruwanka da Mtsalan iyalanka Koda ka auro Batula bata Saka kanta Wajen Bama Dina Tarbiya ba Tunda taga ga yadda ka Tsara Taka Rayuwr kai da yar Taka yau wa gari ya waya..?da kunyar Duniya Wlh gwara kunyar Lahira..!

Kai ya Sunkuyar kawai bashi da tacewa Hajiya Mama ta gyada kai Tana Fadin"Duk da Haka Itama Batulan da nata Laifin ai Ko bakomai Dinar ya Take gareta Tunda Tana auran Ubanta Kuma ai Da na Kowa ne Mugu sai mai shi.."Su Umma suka ce Hakane Hajiya Batula bata ce komai Domin tasan gaskiya suka Fada Dina kuwa Mukurkusu kawai take Zain ya Dade yana kallonta kafin ya Murmusa Cikin Bakincikin ma sanin Dina yace"Ai shi Sharri dan aike ne..In da ka Turashi Zai je ammh kuma zai Dawo maka.."


Yafada yana Tauna Lips dinsa na kasa Dina kuwa wani Zabura Tayi Tana Kiran Wayyo Allah Zata Mutu Mikewa Zain yayi yace Dukkansu suje waje banda Haddir zai Dubata Cike da al"ajabi suka Fice bama su kadai ba Hatta Zainab Da Shema da Inna Rukkaya da suka gama Sauraran Komai wannan al"ajabin ya Rufe musu.
Suna Fita ya maida Kofar ya Kulle Yace Haddir ya Matso ya Taimakamai Dina nata Ihu ko Takanta Zain bai bi ya kware Zanin da aka Rufe Jikinta sai da Haddir ya kauda kai Shi kuwa aranshi yace ai babu wani Sauran Kima awajen Dina kuwa.

Abun awon Naguda ya saka ya aunata sai yaga Haihuwan ta matso Kusa Tunda Yaron ya Fara Mutsu mutsun Fitowa Kanta ya Rike yana Fadin Tayi Nishi mai karfi Duk ta galabaita bata iyama Numfashi Sosai ammh Jin wani abu ya Tokare mata gaba yana Shirin yagata yasa ta kwamsama ihu mai karfi wamda yayi daidai da wani Kashi mai karfi yabiyo baya Cikin Ikon Allah kuma Tare da kan Bby,Haddir Da ya sanya Handglof ya Tari kan yaron Lokaci Daya ya Jawosa sai Dina ta Sauke wani Gwaran Numfashi ta koma ta Fadi Saman Cafet ta sauke Numfashi kamar wacce ta Mutu ta Dawo Tuni katon Jaririn da Haddir ya Daga kansa kasa Kafafunsa sama ya Daki Duwawunsa sai Kikaji ya Canyara kuka.


"inya..Inya..!inya...inya....!




*Ku Sake min min Uzuri don Allah...Yar"uwata ce Zatayi aure Wacce muka taso tare..Hidima da Surgullah sun min yawa ammh Zaku Dinga Jina Da Zarar na samu Lokaci..*






*Janafty...*
7/29/21, 3:26 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B21️⃣6️⃣*


*IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*


"Su Umma Dake Falo suka Hada Bakin Wajen Fadin Alhamdulillah Abba kuwa sai da sukayi Hannu da Kwamishina Suna ma Juna Barka Haka Hajiya maimuna da Hajiya Mama.

Achan Dakin Kuwa Haddir bayan ya yanke ma yaron Cibi ya saka Zanin Dina Dake kan gado ya Nade Jaririn acikin Zani alokaci Daya yana kallon Jinjiri yana kara yima Allah Kirari Domin Gabadaya Yaron ba inda ya bar Zain Komai na yaron Kamar Shine yana karami Ko kadan Bai Dauko Dina ba yana Chan yana kallon Jaririn Har Uwa Ta Biyo Baya Dina na Kwance Tana maida Numfashi kasan Cafe din Duk ya baci da Jinin Haihuwa da kashin Dina,Zain Ya Dubata yaga bata Karu ba Ya Bude Dan akwatin Dayazo Dashi

18 / 37