Author : Jamila Janafty Category : Romantic Hausa Novels
ya Dauko allura ya Fasa Wata karamar Kwalba ya Zuka yayi ma Dina a Hannu kafin Ya Zare safan Hannunsa Ko Takan Haddir Dake Nuna mai Jinjirin bai yi ba ya Dauki Karamin akwatinsa ya Bude Kofa ya Fita Su Hajiya Maimuna suka Taso mai Cikin wani yanayi yace su Shiga su gyara ta ita da Bby Hajiya Mama Fadi take badai Wata mtsala ko Zainullahi..?
Zain Yana Bin Hanyar Dakinsa yace"Babu...Insha Allahu.."Daga Haka ya Shige dakinsa Ko su Abba Dake Falon bai bi Takai ba.ya Shige Dakinsa ya Bango Kofa kyankyamin kansa yake ji Tiolet kawai ya Shige wani abu na Shiga ransa yana Tunanin da ace Firstlove ce Da yanzu Da ita da Abunda ta Haifa da Jinin da komai zai Hada ya Rumgume ya kamkame ya nuna mata Tsatsan Godiyarsa Yana Chuda Jikinsa yana Jin Taruwan wasu Hawaye acikin kwarmin Idanuwansa.
Umma da Hajiya Mama Dasu Nene da Hajiya Batula da Hajiya Maimun suka Yi Rige Rigen Shiga Dakin,Suna Shiga Haddir ya Mikama Hajiya Mama Jinjirin yana Fadin"Hajiya mama kalli kiga anya wannan Baby ba Photocopy Zain bane yana karami.."
Da Sauri Hajiya mama ta karbeshi Tana kallonsa na wani Lokaci,Wasu Shekaru achan Baya suna Dawowa mata Ranar da Fatima da Aisha suka Haihu a asibitin Saulawa Wannan yaron Tamkar Zain ne Lokacin Dayazo Duniya Duk da yana Cikin Kazantan Haihuwa kamininsu bai bace ba.
Tuni Hawaye sun Cika Idanuwan Hajiya mama Jikinta kuma ya karayin Sanyi Cikin Wani irin Tsausayama yaron da yazo Duniya yau tace"Allahu akbar..Allah kadirun Allahu akbar..Nene da Umma Zareena ku Taho kuga wani Ikon Allah.."Da Sauri suka Taho Wajenta Dama suna Wajen Su Hajiya Batula ne Inda Hajiya Maimu Ta kama Dina Zuwa Cikin Tiolet Don tayi mata wanka Hajiya Batula kuma Tana Kokarin Tsaftace Inda Kazanta Haihuwan ya bata sai Nene tace Cafet din Tsakar Wajen ya Tashi Aiki Ta Nananndeshi Afita Dashi kawai Sukaji Kiran Hajiya Mama.
Su kansu Tsaye kawai suke sun kurama Sabon Haihuwan Ido Umma Taji Idanuwanta sun kawo Kwallah ba Domin Tasan komai da tace wannan Zainullahi ne yana karami Nene kuwa Sai da ta karbeshi Ta Rike a Hannunta Itama Jikinta yayi Sanyi Take Fadin"Allah Sarki..Tabbas wannan Jinin Zain ne..yadda kusan Zain Yana Jariri Ranar Daya Fito Duniya.Allah Sarki wannan yaron ga Shigo Duniya mai Cike da Rudani Iyayanka sun samar dakai bata Hanyar daya Dace ba Ina Rokon Allah ya Tsareka Daga aikata Zina Insha Allahu Bazaka Taso kaji wannan Bakin Fentin ba Tunda iyayanka Zasu zauna Waje Daya mu kuma Zamu Kokarin Boye Wannan Sirrin Kodomin ganin Cigabanka.."Take Fada Tana Sharan Kwallah haka ma su Umma Hajiya Mama na amsawa da Ameen.
Nan da Nan Nene Ta taimakama Hajiya Batula suka yaye Cafet din suka Fita Dashi Haraban Gidan In mai Shara yazo zai Fitar Dashi Waje Haddir kuwa Dakin Zain ya Shiga Shima yayi wanka ya Iskesa har yafito yana Shiri zai Koma cikin asibiti Abba Shi ya Kira Alhaji Tsoho ya gayamai Dina ta Sauka da Taimakon Zain da Haddir yayi Hamdalan da Fatan Allah ya Raya Daya Tambayi mai aka samu Abba yace Tukunah dai su Umma na Ciki sai sun Fito tukunnah.
Yana Gama wayar sai ga Umma ta Fito ita ke gayamusu an samu Da Namiji Kwamishina sai da yayi kwallah acikin Ransa kuma yana Ta Neman ma yaron Tsari Daga aikata Abunda iyayansa suka aikata Suka Sameshi zainab Ta taimakama Umma suka Saka Ruwan Zafi Bayan ya Tafasa Hajiya Mama ta Diba Cikin Sabon Bahon wankan Bby Ta Faramai wanka Sauran kuma Umma Ta Diba abotiki Ta Mikama Hajiya Batula ta mikama Hajiya maimu Dake Tiolet Tanayima Dina Wanka.
Dukkansu Suna Dakin Suna ganin Yadda Hajiya mama kema Jaririn wanka Cikin Lokaci ta Wankesa Tas Nene ta Miko Man Zaitun aka Shafemai Jiki Dashi Aka Sakamai kayan Sanyi masu Kyau Cikin wanda Nene ta Siyo ne,Sai Lokacin su Hajiya Maimuna suka Fito Daya Bayi Tagama Yima Dina wanka Duk tayi Laushi kamar ba ita ba Idanuwanta sai Lunshe wa suke Umma Ta kalli Hajiya Batula Dake gyaran Gadon Tana Fadin"da kin Fito mata da kayan da Zata saka Daga gani sun mata alluran Hutu.."
Hajiya Mama Dake Kokarin Fita da Yaron Tace"Kada ku bari ta kwanta sai ta Cika Cikinta..Ke Nene Hado mata Shayi mai kauri kafin anjuma na koma Gida na Damo mata Kunun kanwanmu na Jegon mu na da.."Nene ta amsa da Toh kusan Tare suka Fita da Hajiya Mama da Nene Umma kuma Ta Tsaya Tana Taya Hajiya Batula gyaran Gadon Ganin su Dinan suna Tsaye ita kuma ta Dauko mata Kaya Hade da Pant da pad Ta Mikama Hajiya maimuna Tana Fadin"Kinga alamun akwai Ruwan Nono kuwa..?
Hajiya Maimuna Tace"Eh Zai samu ko Zuwa gobe ne da yardan Allah.."Umma da Hajiya Batula suka ce Allah yasa Umma Fita Tayi Zuwa Falo Ita kuma Hajiya Maimuna ta Taimakama Dina ta saka Doguwar Hajiya batula ta Sakamata Pad dinta Cikin pant Ta bata ta saka kana suka Zaunar da ita Kokarin Kwanciya Take Hajiya maimuna Ta Riketa Tana Fadin"A"a kada ki kwanta sai kin sha Tea.."
Cikin karaya da wani Sanyi Jiki da wani yanayin da Tunda Dina Take arayuwarta Bata Taba Tsintar kanta ba Tace"Zan kwanta ne Ummi..Ina jin wani iri.."Hajiya Batula tace"Ai wannan wani irin Dole ce haka kowacce mace Take ji in ta zama Uwa.."Jin haka yasa Dina Taji Toh in har hakane meyasa ta Zabi Ta Haihuwa bata Hanyar aure ba..?meyasa mataa Suke karuwanci su Haihu sukuma Yar da abunda suka Haifa Indai wannam Bakar azabar ake sha..? Lalle sun zama Jakuna Indai Kuwa suka Sha Wannan Wahalar suka kuma Banzatar da Abunda suka Haifa.
Umma ce ta Shigo Dauke da Burner Ta saka Turaran Wuta Dakin ya Dauki Kamshi sai ga Nene da Wani katon Jug Dauke da Tea da Buradi awani Faranti Harda kwai ta bama Hajiya maimuna ita kuma ta mikama Dina ta karba Daman Cikinta ya Rarake Tana ji kamar Batataba Cin Abinci ba nan fa ta Fara Shan Tea din Tana Hadawa da kwai da Buredin kafin kace kwabo Ta gama dashi sai Zufa kawai yake Ketomata A Saman Goshinta Nene na kallonta tace"Masha Allah ta Fara samuwa.."Sukayi Mirmishi Dukkansu bayan Tagama tace Zata Sha Ruwa Umma ta Fita Taje Kitchen ta Dauko wani katon Fulas Cike da Ruwan zafi ta kawo shi aka Tsiyayamata da akabama Dina sai taki sha ta bata Rai Nene tace"karbi ki sha..Wacce Ta haihu bata Mu"amala da Ruwan sanyi Saboda Jego.."Dole Dina ta karba Tasha kana ta koma ta kwanta Tana Sauke Numfashi Hajiya Batula tagyaramata kwanciya So take Ta Tambayesu Ina Jaririnta sai kuma Idanuwan Umma yasa Tayi Shuru da bakinta Umma da Nene suka Fita Zuwa Falo Inda Abba da kwamishina ke Zaune Yaron na Hannun Kwamishina ya kamkamesa Shi kuwa Abba yana Gefe yana waya da Baban kaduna yana gaya mishi Haihuwar Su Zain kuwa Tuni sun Fice Daga Gidan Asibiti Suka Koma Dukkansu Tunda sun bar Tarin patient achan.
Bayan Komai ya kamallah Har Dina ta samu Barci Hajiya Mama ta koma Gida Taje ta Damo Kunun Da zai kawo Ruwan Nono,nan gidan Abba kuwa Zainab Ta Dafa kayattacen Abinci kowa yaci yasha Ruwa Natsuwa ta Dawo Jikinsa sai Lokacin Kwamishina yace Hajiya Batula ta Shirya su koma su Nene suka ce yammah Tayi yace kada su Damu Jirgi zasu bi Misalin Karfe 6:30pm na yammah Sai ga Haddir ya Shigo Bayansa Hajiya mama ne da Tabawa Dauke da katon Jug sai Kuma Alhaji Tsoho wanda ya Shigo yana Dafa sandansa nan fa su Umma baki yaki Rufuwa suna ta mai maraba da Zuwa Hakama Abba da kwamishina nan Falon ya Fara zama suka Gaisa Alhaji Tsoho yayi musu barka da arzkii Su Hajiya mama na Dakin da Dina take Lokacin Har Tatashi Tana Dauke da Jaririn Tana Kallonsa Wani Sonsa da kaunarsa na Ratsata Babban Abun Farincikinta yayi Kama da Zain ko ahaka ta samu ta Godema Allah gefe Daya kuma Tana Jin kunya Domin Kowa yanzu ya Fahimci Ita ce Shedaniyar ba Zain ba.
Katon Jug aka cika mata da kunu aka mikamata kana Hajiya Mama ta karbi Jinjirin ta Fice Zuwa Falo ta Mikama Alhaji Tsoho ya karbeshi yana Hamdala Shima ya Dade yana kallon Sabon Haihuwar kafin yace"Masha Allahu...Abunda ya Hada Iyayenka Rabonka ne..Gashi yau kazo Duniya Allah ya Rayaka kan addinin Musulinci.."Gabadaya suka amsa da Ameen Dagasa yayi sama ya Fara mai Huduba acikin kunnuwansa Har ya gama kana yace Haddir ya bashi Dabinon Daya bashi yana Mikamai ya Karba ya saka abaki ya Tauna Kana ya sakama yaron abaki sai gashi ya Fara ma"mula Cikin Mirmishi Hajiya Mama tace"Allah ya Rayaka Bisa Sunna..Allah ya Tsare Farjinka Daga aikata Zina ALIYU ZAINULLAHI USMAN SAULAWA.."
Gabadaya Kowa ya amsa da Ameen kenan Da Sunan Daddyn Abuja Alhaji Tsoho yayi mai Huduba bai wani Jima agidan ba Bayan Tafiyar Kwamishina da Hajiya Batula bayan Haddir ya Dawo Daga kaisu Filin Jirgi yazo ya maidasu Gida,aka bar su Umma da nene suna Taya Hajiya Maimun Hidima Zuwa Dare Tuni Haihuwan Dina ya Karade Duka Dangi Daddyn Abuja ya Kira yana yima Abba barka Tare da Jin Dadin Sunansa da Alhaji Tsoho ya saka Zafeera kuwa Dataji Labari Cewa Tayi an Cuci Daddyn Abuja da aka sakama Shege sunansa sai da Inna Rukayyah ta Tsawatarmata Zain kuwa ko kara ganinsa ma ba"ayiba Gidan Alhaji Tsoho ya kwana da Safe Umma ta Kira Hajiya Mama awaya Ta gayamata an samu Ruwan Nono har Dina ta Shayar da Aliyu wanda zasu Dinga Kira Daddy kowa yaron ya Shiga Ransa kuma yasa ya saki komai Hatta da Umma yanzu da ita ake komai Hakama Zainab Bata Taba Zaton Zata so yaron ba Haka tazo ta Daukeshi bayan Hajiya Mama tazo tamai wanka Ta Shigamai Hotuna Duk Ta Turama yan"uwa su Sadiq karami da Babba Faruq da Zareena da Zafeera wacce Data ga Hoton Sai da tace"Allah Sarki Fine Boy."ita kanta Taji Zuciyarta Tayi wani Rauni kadan.
Kwana Hudu da Haihuwan Dina tana samun kulawa takowani Bangare Haihuwa ya Budeta takara zama wata katuwa sai dai Tayi baki Umma da Nene suna iya bakin Kokarinsu da Hajiya Mama Dake Jigila Kullum sai Tazo,Tuni Ruwan Nono ya samu Daddy sai sha Abunshi yake shima ya Fara zama Bulbul har kuma yau din Da ake kwana Hudu da Haihuwa Zain bai kara Takowa Gidan ba Har sai da Abba yayi mgana yace zai Kirashi awaya yamai Fada Dina Kuwa Bata Damu ba Domin Tagama yin Sanyi da Rayuwa Da Duniya kuma Har yau bata Kira Zakiya awaya ba yadda bata Nemeta ba itama Bata Nemeta ba Domin yanzu Gabadaya Taji Zakiya ta Fita acikin Ranta Tana da Tabbacin Ko yayane Zakiya ta bada Gudummuwa wajen Kara Lalacewar rayuwarta.
Kowa ya Kira waya yayi Barka Hatta da Zareena dake U.S Ranar da Dina ta Cika kwana Biyar da Haihuwa sai ga Inna Hannatu ta iso da Kaya Niki Niki nan gidan Abba ta sauka Tunda sunyi mgana da Inna Rukayyah itama Tana Tafe Zaso su Suyi Taronsu isu isu Tundai Kaddaran Allah ya Riga ya Faru ba yadda bawa zai yi ita kanta Inna Hannatu Data Dauki yaron sai Taji ta saka ijiyesa Tana Kallonsa Tana Ayyyana Rabonsa ne Duk ya kawo Abunda ya Faru babu yadda Bawa ya iya.
Aranar da Daddare Zain Yazo Gidan Domin Abba ya Kirashi yamai Fada Tare da Haddir suka zo Ya Shiga har Dakin Dakyar ya iyama Dina Sannu ta amsa Tana kallonsa kana Haddir ya Dauko Jinirin ya mikamai Ya karba da Farko ya kauda kai ne sai Daga baya ya Dawo da kallonsa kan yaron Sai da yaji gabansa ya Fadi Jikinsa yayi sanyi Kafafunwansa sunkasa Daukansa ya Dade yana kallon Yaron Shima yayi mai kur da ido yana Motsi da bakinsa da Hannunsa irin na Jarirai sai Zain yaji ya Fashe da kuka Wata Zuciya tace In ka Tsani Dina bai kamata ka Tsani Abunda ya Fito Daga Tsatson ka ba,kada ka manta babu Abunda wannan yaron yayi maka baisan komai ba Kai da Dina ne masu laifin bai kamata ka Dora ma yaron da yazo Duniya Jiya jiya ba karan Tsana.."Tunanin Dayake Tayi acikin Ransa kenan Baisan sadda yaji ya kamkame yaron ba yana Jin wani kaunarsa na Ratsata Daga Dina Har Haddir sai suka saki Baki suna kallonsa ya Dade Rumgume dashi kafin ya Saussautamai Rikon ya Dago Jajayen Idanuwan Dina yana kallonta kafin ya mikamata shi yana Fadin"Allah ya Rayashi..Allah ya saka ya Biyo Halin mai sunan ina Rokon mai Allah yamai Tsari da Daukan mugayen Hallayarki.."Yana gama Fadin haka ya sakarmata Shi ya juya yafice Haddir ya Kada kai ya mara mai baya Dina da Idanuwanta suka kawo Ruwa Tana kallon yaron tace"Ameen..Bana Fata Nima ya Biyoni..Ammh kuma ina Rokon Allah kada yasa yadda Nayi Rashin Uwa da kulawar Uba Wacce Tayi sanadin Zamowata haka kada Aliyu yayi Irinshi..Allah ya sa ka Tallfeshi Ka bashi Dukkan Tarbiyan Daya kamata.."
Daga Gefenta Taji an ce Ameen Tana Juyawa Taga Hajiya Maimuna ne itama Cikin Sanyi da karaya yaron kawai Dina ta mikamata ta koma ta kwanta Tana Kokarin Hana kukanta Zuwa Ta Tuna wayar da sukayi da Daddynta kamar ma kuka yake yana Rokonta Gafara Domin yace shine Silan komai ita kuma tace Ta yafemai Domin bata ganin Laifinsa ya kasance Uba ne nagari mai Son abunda ya Haifa Kawai Gata da Rashin Kulawa ya sa ta Fada wata Rayuwa Dabam
Wata Zuciyar tace"Dina Harda So..!
*****
*Zaria..*
Ranar da Dina ta Cika kwana Biyar da Haihuwa itama Zaina Tatashi Da Naguda Bata Cika EDD dinta da kwana Goma ba, Da Safe ne Nagudan ya Tashi Allah yasa Farida na Gida Hankali Tashe ta Fita Zuwa Bakin Titi ta samo Mota Koda ta Dawo ta Iske Duka kayan Haihuwan Zulaihat ta Hadasu Waje Daya ta kuma sanya Zaina Hijabi wacce ke Zaune Tana Cijewa sai dai su kansu sun jinjinamata kan wannan Dauriyan nata suka kamota Zuwa waje bayan sun sakata amota Zulaihat ta Koma ta Dauko akwatin da Key ta Kulle Gidan suka Shiga Mota sai asibitin.
Asibitin Data ke awo suka ce Wato Almadina suna Zuwa aka karbeta sai Labour Room Suka kuma suka zauna zaman Jiran Tsammani Hankalinsu tashe Tun suna Jiran Labarin Haihuwa Zaina Shuru kawai kake ji Likiti yace su kara Jira Haihuwa bata kariso ba ammh Zaina na Ciki sai Shan bakar Wahala take ahaka fa har Dare ba wani Labari Nan asibitin suka Wuni ita da Zulaihat ko Ruwa basu iya kaiwa baki ba Sallah kadai ke Tadasu addu"a kawai suke Allah ya Sauki Sa"adiya Lafiya.
Farida ta Fara Tsorata ne ganin Har gari ya waye Zaina bata Haihuwa da asuba sun shiga wajenta da kuka suka Fito sau Biyu ana sakamata Ruwan Naguda ammh Shuru ba Haihuwa Zaina Duk Dauriyan Ta Riga Tagama galabaita Tana kuka Tana Fadin Anty Farida ta yafemata In ta Mutu Taje Bauchi Gidan Dr.Abubakar Saulawa ta basu labarin Rasuwarta su Cire Tsammani irin mganganun Datayi ta gayamusu kenan suka Fito da Gudu suna kuka Zulaihat Da bata san Zafin Haihuwa ba Taji Tayi Tir da Rayuwar yan Barikin Da zasu yi Ciki a bariki kuma su Haihu Cikin wannan Bakar azaban Tun Likitoci na basu Hakuri Har Farida ta Sare ta Fara Bala"i Tana Fadin wani irin Haihuwa ce zasu bar yarinyar Karfinta ya kare sai Taso da Naguda suke suna bama Yarinya Wahala ammh suna Fadin su kara Hakuri Zata Haihu Ganin haka yasa Dr Dake On Duty yace sai dai ayi mata Operaton Farida tace Ta yarda gwara ayi mata acire Abunda ke Cikinta da wannan Bakar azabar Data ke sha.
Nan da nan Farida Ta Biya Kudin aiki wajen 100+,Faridan Ita ta saka Hannu atakardan aiki aka Fara Shirin Shiga da Zaina Dakin Tiyata Lokacin da za"a Tafi da ita haka ta kamkame Hannayensu Farida tana kuka Tana Fadin su yafemata suma kukan suke suna Fadin Insha Allahu Za"ayi aiki Lafiya Suna Ji suna gani aka Shiga da Ita Dakin Tiyata Nan Farida ta bar Zulaihat Tatafi Masallacin Cikin asibitin Tana da addu'an Allah yasa ayi aikin nan Cikin Nasara In Sa"adiya Ta Rasu Bata da karfin Gwiwan Tunkaran Danginta da wannan labarin ba Uwa uba Firstlove mijinta Da duk inda Take ya Tabbata yana ji ajikinsa Sa"adiya Tana Raye.
Tabbas Zain yaji ajikinsa Wani Abu na Faruwa yana asibiti acikin Office dinsa yana Duba Patient yaji gabansa ya Fadi Jikinsa yayi sanyi yaji wani Sanyi na Shiga Jikinsa Daman Tun bayan barin Zaina Gida yana Jin wannan yanayin Lokaci Bayan Lokaci Dayaji haka sai ya Danganta Haka Da Zainarsa ce koma Miye wani abu mara Dadi na Faruwa da ita.
Kansa ya Dafe bayan ya sallami mara Lafiya Yana Jin Jikinsa kamar ba nashi ba afili ya Furta.."Kodai yau Firstlove zata Haihu ne..? Tuni yaji gabansa ya kara Fadi da Sauri ya Mike yana Jin Wani Zufa na Ketomai Ficewa Yayi Daga Office din Lokacin misalin 12pm na rana Masallacin asibitin ya Shiga bayan yayi alwala ya Dauki Qur"ani yana ta karantawa Domin yaji Faduwar gaban nashi yayi yawa ne bayan ya gama karatun ya Daga Hannu yana Addu"an Duk inda Firstlove Take Allah ya kareta Allah ya Sauketa Lafiya yana nan Cikin masallacin har aka Kira sallah bayan an Tada sallar an Idar ya karisa ga liman yace a sakashi a addu"a matarsa na kan Gwiwa nan da nan Liman ya sanar yana ta addu"a Jama"a na amsawa da Ameen Haddir na msallacin mamaki ya Cikashi bayan an gama Addu"o'in Jama"a sun watse Kana Haddir ya Karisa kusa da Zain yana kallonsa yace"Wata matar Taka ce Zata Haihu.?
Bai Tankamai ba sai da suka Fito Daga Cikin Masallacin kana ya kalli Haddir yana Fadin"Wata mata gareni Bayan Firstlove?itace Zata Haihu yau naji ajikina.."Yana gama Fadamai haka ya wuce ya Nufi Cikin asibitin Haddir ya Bishi da kallon Tsausayi kawai kafin ya Kada kai yana Fadin"Toh..Allah ya Rabasu Lafiya.."
Adaidai kuma Lokacin ne Daya Daga Cikin Nurse din da suka Shiga Tiyata da Zaina ta Fito Fuskarta Cikin Fara"a Zulaihat Dake kai da kawo a kofar Wajen Tataso Tana Fadin"likita yaya..? Ta Sauka..?
Nurse din Tace"Alhamdulillah anyi aiki Cikin Nasara mun samu Nasara Ciro mata Ya"ya Biyu Duka mata.."Saboda Farinciki da Murna Jikinta Zulaihat ta Fada Tana Fadin"Alhamdulillah...Allah mun Gode maka ina