Chapter 28 Reading Zainazain Book 2 Complete By Janafty Arewa Novels

Zainazain Book 2 Complete By Janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   28 / 37

81K to 84K   out of 108.5K words

ba sai taji wani Rauni ya kamata Allah Sarki yau Ranace mai matukar Farinciki gareta Wanda Ta Tabbata da Ukti na nan Bata da Wata Damuwa sai gashi yau bata agefenta Fada su Shema suka Fara mata ganin Zata Bata Sauran kwalliyata Dole ta Tsaida kukanta Daganan su Shema suka Fara Wanka Da Shiryawa Tunda 2pm Mama Safiya Tace Zasu Tafi Chan Gidan Alhaji Tsoho Din.

Dina na Shashensu Umma sai ga Hajiya Batula dasu Waleeda Farinciki ya Cikata tatashi ta Tarbota Tana Tambayan Daddy Hajiya Batula tace Sun Saukesa shi da Waleed Gidan Alhaji Tsoho Su Umma suka karbi Hajiya Batula Hannu Biyu Tunda yanzu an zama Daya Tuni aka Cika Gabanta da abinci da abubuwan sha sai Kallon Dina Take yadda ta saki jiki ana ta Hidima da ita Umma ta Kirata Nene ta Kirata abun sai yayi ma Hajiya Batula Dadi kamar tayi kwallah Tana kara Godiya ga Allah Daya Hadasu da mutanen kwarau irin Iyalan Dr.Saulawa da Wasu ahalin ne Tabbas Dina da yanzu Tana Cikin Wata Rayuwa ammh kalli yadda Tayi Kiba Harda Rabon wani Cikin

Bayan Dina ta gama Jera ma Hajiya Batula abinci da kayan Ruwa ta koma ta Zauna suna kara gaisuwa Hajiya Batula Tana Tambayan Arman Dina tace Su Faruq sun Tafi Dashi Wajen Daurin Aure Hajiya Batula tace Zasu hadu da kwamishina achan Daman Koda yaushe Cikin Zencen Arman din yake Sun dan Taba Hira da Dina kan mganar chan Suda ne domin Hajiya Maimuna Ta Kirasu Ta gayamasu kakar Dina bata da lafiya Hajiya Samina Har an kwantar da ita asibiti Shine Hajiya Batulan ke gayamata Taji kwamishina na Zencen zasu je Dina ta marairace wai Zataje Hajiya Batula tace Mijinta Baya nan Ta Bari in ya Dawo ya barta sai Tatafi Dole Dina tayi Shuru Bata Jima ba Tace bari taje Tayi wanka ganin har su Umma sunyi wanka Sun Shirya.

Tana Komawa Shashenta Taga Amarya da kawayenta sun Cakare basu yi anko ba aammh Kowacce ta saka kayan Nuna Sa"a Ana ta yi musu makeup Ganinta yasa Shema tace Matar ya Dakta kije kiyi wanka Kizo ayi miki kwalliya Dariya ta kwace mata Domin sunan Da Shema ta Kirata ya sanyayamata Zuciya sosai Ta kada kai tace bari taje ta Shirya Kada ta watsa mata a kasa a ido Ta Wuce Ciki Tana Koda kyan da Zafeera Tayi Duk Da taga Fuskarta ba Walwala.

Wanka Tayi ta Shirya Cikin Wani Tsadadden Material Wanda yaji stone work anyi mata Dinki Buba Tayi kyau ta Gyara Gashinta ta Fito Falo ta Iske har Hamdiya Dake da Ciki Tayi kwalliya itama suka Tarota ta Zauna akayi Mata Duk da bamai yawa bane ammh Tayi kyau Saboda Daman ita mai kyau ne bayan anyi mata Dauri Ta koma Daki Tana kallon kanta a madubi ita kanta ta Shaida Tayi kyau Tun Bayan Samuwar Cikin Arman Bata kara Kwalliyan Datayi kyau kamar ta yau ba wani Dan kunne Zinarenta ta saka Hannu da Wuya Wanda Daddy ne ya Siyamatashi ta Dauko Sabon Mayafi da wani Takalminta mai Tudu Tana Fitowa su Zainab suka Sakamata Ihu suna Daukanta Hoto ga Dan Cikinta Daya Bayyana Shema na Fadin kyanshi Yaya Dakta yaga wannan wanka Ita dai sai Mirmishi Take acikin Ranta kuma Tasan ko yana garin bazai Damu ba da ita ba ballatana Har ya yaba mata Ko bakomai Taji Dadin Rayuwarta yanzu Tunda Ta samu kwanciyaar Hankali Zain kuwa Daman Ta Gama sanin ya Riga yayi mata Nisa Har Abada...

Amarya Zafeera Dake gefe Ta cika Kamar Zata Fashe gabadaya Haushin yadda suka Rufu kan Dina suna Ta yabon kyanta ne ya kamata Tana Tunanin Wlh ko ba Ukti a wajen ne akallah a Nuna Kishinta karamin Tsaki Taja tatashi Fuu Ta Fice sai kowa ya Bita da kallo Dina kuwa ta san Dalilin haka suma su Shema sun Fahimta Basu ce komai ba itama Dinan Bata Nuna ma ta saki Mirmishin Dole tabi bayan Zafeera Zuwa Shashensu Umma.

Tana Shiga ta iske Zafeera na Rumgume da Umma tana kuka Umman ma kukan Take Su Mama Safiya na basu baki Daga yanayin mganar ta Fahimci kan Zaina suke wannan kukan Sai Taji Jikinta ya karayin Sanyi kawai sai ta Juya ta Koma Mom iklima Ta ganta sanda ta Shigo kuma ta koma sai ita kanta Dinar Taji ta bata Tsausayi ba Laifinta bane haka Allah ya kaddara.

Shashenta ta koma ta Shige Daki Itama Tana kukan makomar Rayuwarta Wlh yanzu addu"a take Allah ya bayyana Zaina Kila Ko Darajanta ta samu wani Kyakyawan kallo Daga zain Yanzu tafi Bukatar yaga Zainarsa Domin ta kara yarda da itace Rayuwarsa,Kukanta ya Tsaya ne da Zainab ta Shigo Tana RokontaTazo Ta Tayasu Bama kaawayensu abinci nan da nan ta saka Tissue ta Share Hawayenta ta Fito kamar ba ita ba ta iske Zareena tazo anyi mata kwalliya Tana ta Duba agogo wai an kusa Daura aure Jawad zai zo su Asma"u natayi mata Tsiya suna Dariya.

Nan suka Hadu da Dina da Shema da Zainab sukayi ta Bana Mutane abinci har kowa ya samu kana suka zauna suma suka ci suna Cikin cin Abincin ne Faruq ya kira Wayar Zafeera Dake hannun Shema tana Dauka sukaji ana Daura auranta da Haddir Abba Shine Waliyin Ango Haddir sai Daddyn Abuja Yazama Uban Amarya suka Nema suku ma suka basu Nan da nan Shedu suka Shaida Daurin Auran Dr.Haddir Aliyu Abubakar Saulawa Tare da Amaryansa Zafeera Usman Abubakar Saulawa kan Sadaki Mafi Daraja 200k sai sukaji waje ya Dau Hayaniya da Hamdala suma Daganan sai suka Dauki Ihu Shema ta Mike tana ,Juyi Tana Guda ta kwasa Zuwa Shashensu Umma Zafeera na Dakin Umma tana Zuwa ta Fada Jikinta Ta Rumgumeta Tana Fadin"Finally Mrs Haddir Aliyu Abubakar Saulawa...Aure ya Dauru Allah ya baku Zaman Lafiya.."

Kawai sai Zafeera ta saka kuka Su Mom Iklima me zasu yi in ba Dariya Ba Mama Safiya ne ke kare mata Tana Share mata Hawaye Tana Fadin Amarya bata kuka Ranar Bikinta.

Achan Farfajiyan Gidan Alhaji Tsoho Kuwa ya Cika da baki na Nesa Dana kusa Hatta da Mijin Inna Hannatu da na Inna Rukayyah Duk sunzo Tare da manyan Ya'yanasu Abokam aikin Haddir ma su Dr.Imran Dr.Petter,Dr Aliyu da Sauransu Da Sauran Abokan karatunsa Suna ta bashi Hannu Tare da Tayashi Murna Bakinsa a Washe Bazaka Taba gane wani yanayi yake Ciki ba su Faruq ne suka Mike suka Fara Raban Abinci Zasu yi Repction Su Arman na kan Darduman da Alhaji Tsoho ke kai da ya"yansa Tare da irinsu kwamishina Haddir na Gaisawa da baki yaji karar wayarsa yana Dubawa yaga zain ne yaTuromai Sako da Sauri ya Duba sai yaga.

*Alhamdulillah..Mrs Zafeera Usman Abubakar Saulawa..Ina nan ina Kintatan Lokaci by Now nasan ka tashi Daga gwauro..Allahu ya baku Zaman Lafiya ina gaida kowa da kowa ka Fada musu I Miss my Home.*

Kayattacen Mirmishi Haddir ya saki kafin ya maida wayarsa aljihu Hakika yafi kowa kewar Zain musamman wannan Rana Da Ya kasance bashi a kusa Dashi,Ya cigaba da karban gaisuwan baki Cikin Fara"a wasu Tafiya sukayi basu Tsaya ba wasu kuma sun Tsaya har akayi Reception kana suka Watse Sannu Sannu baki suks Fara Tafiya Haraban Gidan ya Rage Mutane sai irin su Abba da su Kwamishina suna kan Katuwar Darduman da Alhaji Tsoho ke Zaune shi da ya"yansa da Jikokinsa da Tattaba kunnuwansa su Arman dasu Jalal.


Chan Gidan Abba kuwa sai Shagali akeyi su Zainab suka kunna Mp a Shashen Dina suna ta Chasewa abunsu Ransu Fes,Zafeera kuwa na Shashensu Umma kwata kwata Ranta babu Dadi Ga Rashin zaina ga Damuwar an kakaba mata auran Wanda Bata so kuma babu Wani Jituwa Tsakaninsu.

Anayin Sallar azahar Aka Fara Shirin Tafiya gidan Alhaji Tsoho,Mama Safiya ta Kira Haddir tace suna Bukatar Motoci Sai shi kuma yayi ma Sadiq mgana da Sauran abokansa Motarsa kuma Faruq ya bama key din Sadiq yana da Tashi Motar Abba ya Siyamai bayan Dawowarsa su suka je Gidan Abba kwaso amare dasu Umma sai da suka Jirasu suka Gama Hada kaya Tawagan Amarya Da Zafeera Na kawayenta Dasu Zainab suka Fara yin gaba sai da suka kaisu Kana suka Dawo suka kwashi su Umma da Amarya Gidan Babu Kowa Sai Megadi hatta da Dina Motar da Nene ke Ciki Ta Shiga Ita Da Hajiya Batula da Mom iklima,Sadiq babba ke Tukasu sai gidan Alhaji Tsoho Inda suka samu Tarban su Inna Rukayyah Tunda Abun Duka Gida ne Tuwona maina Sai Tarban Dangin Mama Safiya.

Zafeera Dakin Hajiya Mama aka kaita,Ta Rumgumeta Tana mata Guda Alhaji Tsoho suna Haraban Gidan ammh yace zasu shigo Ciki Saboda yima Amarya Nasihu Tunda da Wuri yace za'a mikata Gidan Mijinta Haddir kuma ya Tafi Masaukin Bakin da Sauran abokan sa suka Sauka.


****

Koda suka Shigo Garin Bauchi Anun da Anan sun Dade da yin Barci Don ma sun Tsaya Bisa Hanya sunyi Sallar azahar sukaci Abinci Saboda yaran kana Suka Dauki Hanya Tunda suka Shigo Cikin garin Bauchi Zaina Taji gabadaya Ta rasa natsuwarta Tana Tunanin kamar Jiya ne ta bar Gida gashi yau Zata koma me zatace ma su Umma..? Da wani ido Zata kalli Firstlove bayan ta bashi kunya..?Me zata Tarar...? Yaya Labarin Dina..? In ta tuna Hakan sai taji Bata da wani karfin Gwiwa ta Cikin nikabinta Take Share Hawaye Bataji Ba ashe Farida nata mgana sai da Zulaihat ta Tabata kana ta Waigo Tana kallonta.

Farida Dake kujeran gaba tace"Gamu agarin Bauchi Sa"adiya Wata anguwa ne Gidan Abba yake.?."Cikin Sanyi Jiki Dana Zuciya tace"GRA..! Direba najin haka ya kada kai Daman Daga ganinsa ya saba Kila Shigowa garin Cikin Lokaci kadan sai gasu Cikin Gra Zaina sai Bin Ko"ina da kallo take lalle ko yau kabar waje gobe ka Dawo sai kaga ya Sauya maka Taga abubuwa sosai wadanda suka Chanzamata acikin Idanuwanta ji Tayi Direban na Fadin gasu Cikin GRA ina ne gidan..?


Da kwatace da komai Sai gasu Kofar Tamgameman Get din gidan Datayi Rayuwa aciki Cikin Sanyin Murya Farida ta Kalleta Tana Fadin"Nan ne gidan Sa"adiya..? Zaina na kura ma Gidan Ido Tana Tuna wasu abubuwa ta gyada kai Tana Fadin"Eh nan ne Anty Farida.."Farida bata ce komai ba Sai da ta Bude Murfin Mota ta Fita kana ta leko Tana Fadin"Ku Zauna amota bari na yi mgana da Megadi..Mai mota don Allah bari nazo..'Da Sauri yace bakomai Zaina kuma kai ta kada Zulaihat kuma banda Kallon Gidan babu abubda take aranta Tana Tunanin Daman wannan Daulan Zaina ta baro ta Fada Wata Rayuwa..?

Suna kallo Farida ta Buga Get din Audu megadi ya leko Zaina na kallonsa Shine dai Audi Megadi Cikin kallon Rashin Sani yake Bin Farida dashi sai ta gaisheshi ya amsa Yana kallon Motar dasu Zaina ke Cikin Cikin Alamun kamar bai yarda da ita ba yace"Baiwar Allah Lafiya..? Ko bikin gidan kika zo ne..?
Cikin mamaki Farida tace"Lafiya lau Baba...Eh gida nan nazo Daman yau ana Biki ne..?

Da Sauri yace"Eh Diyar Megidan ke Aure Zafeera basu ma Dade da Tafiya Chan Babban Gidan nasu ba Gidan Alhaji Tsoho ba Daga Chan za"a kai amarya Dayake Duk na Gida ta Aura Hadiru ne ta aura.."Farida ta Gyada kai Cikin mamaki kafin tace"Shikenan nagode..Bari mu karisa Chan gidan.."Da Sauri yace"Kinsan gidan ne..?.Farida tace"Eh Baba nagode.."Da haka ta Dawo ta Bude Mota ta Shiga Tana Fadin"Ba kowa agidan wai suna Gidan Alhaji Tsoho..".


Zaina ta Zaro Ido Cikin Faduwar gaba Tana Fadin"Na Shiga uku ni halima meya Faru haka..? farida tace"yace Biki akeyi yau..Zafeera ce ke aure wai ko habiru take aure na Manta.."Wani irin Zabura Zaina Tayi Tana Fadin"Yau Ukti take aure..? Wa kikace Ta aura..?

Cikin Mamaki Farida tace"Wani suna Ya Fada Habiru ko wa..? Na manta Wlh yace dai suna Chan Dukkansu mu karisa Chan Tunda kinsan Gidan.."Zaina da Bakinta yaki Rufuwa sai kuka Cikin kukan take Fadin"Allah na gode maka Da na Dawo akan gaba..Ukti yau tana aure...Kuma Tana auran ya Haddir ayau,lalle na Cika mai Sa"a Ko bakomai zan wanke Laifina na yau kadai Mu kasance Tare da Ukti.."Daga Farida Har Zulaihat ba wanda yayi mata mgana Farida tace Direba yaja su Tafi Zaina ta Dinga Nuna Hanya Tafiya kadan sai gasu abakin get din gidan Alhaji Tsoho koda yanayin Wajen zaka Fahimcia acikin Gidan ana wani Taro.

Farida ta Waiga Tana kallon Zaina Tana Fadin"ki Zauna amota Zamu shiga Tare da Zulaihat da su Anun,In Lokacin Shigarki Tayi zan Kira wayarki..Direba ga kudin Motarka In Na kirata sai ka Sauke mana kayanmu.."Tafada tana Mikamai yan Dubu Dubu 20k ya karba yana ta Godiya da Toh Zaina ta ce Daman gabanta sai fadi yake Tana kallo zulaihat ta Dauki Anun ita kuma Farida ta Dauki Anan Duk da suna Barci ammh jin an Daukesu suka Farka suna kallon Sabon Waje Zaina na gani suka shiga Gidan Tunda yau get yana Bude ne saboda Sha"ani.



Tun da suka Shiga gidan Zulaihat ta saki baki Tana kallon Tsaruwan Gidan ita kanta Faridan Sai da ta Jinjina Ganin basu gane Kofar da Sadasu da ainihin Babban Gidan bane yasa suka Tambayi su Jalal Dake Wasa aharaban Gidan Tunda Lokacin su Abba sun Shiga Ciki Saudart Dake da wayau ita ta Tsaya Ta kurama Anun Dake Hannun Zulaihat da kallo ganin Kamar Arman karami Su kansu sunga yanayin kallo sai dai Tun kafin suyi mgana sai ga Arman ya Rugo da gudu suna wasa da Waleed Daga Zulaihat har Farida baki suka saki suna kallon Arman suna kuma kara kallon su Anun Wlh in ba Domin yanzu suka Shigo garin ba sai suce su Anun yan Uku ne wani ne ya sace Arman.

Boye mamakinsu sukayi da Saudart ta Nuna musu Kofar da Zata sadasu da Falon Hajiya Mama Farida da Zulaihat suka wuce suna waigan Arman suma ma Haka su Saudart ma Haka Balle su Anun din da sukayi wani iri suna Bin Kowa da kallo.

Falon ya Cike da yan"uwa da abokan Arzuka Amarya Zafeera Tana Dakin Alhaji Tsoho dasu Abba sun Taru suna yi mata Nasiha su Umma ne ke Falo ana Hira Dina na gefe suna Hira sama sama da Hajiya Batula kwamishina bai Dade da Tafiya ba su Farida sukayi sallama acikin Falon Gabadaya su Umma suka waiga suna amsawa Farida ce kan gaba Zulaihat na bayanta.

Umma,Da Nene da su Mama Safiya Hankalinsu ya koma kan su Farida Hajiya Mama Dake kokarin Fitowa Daga Dakin Alhaji Tsoho itama ta amsa Sallamar sai dai me tunda suka Shigo Kowa ke kallonsu da Tsabar mamaki da al"ajabi ba kuma komai yasa Kowa ya saki baki yana kallonsu Farida ba sai Anun da Anan Dake Hannunsu wadanda ganin Idanuwan Mutane duk suka Rikesu suna kauda kai.

Kowa afalon yarasa bakin mgana sai mamaki da al"ajabi Umma ta Mike Tsaye tana kara Kurama Anun ido wacce Harta Bakinta irin na Zain ne hakama Nene ke kallomsu Hajiya Mama da Bata iya gani ta kyale ta Shiga Tafa Hannu Tana Fadin"Wa nake gani yaran suna kama dashi..? Ku Dubamin Jama'a yara kamar Yaron nan Arman Zainullahi Tsab Fuskarsu fa.."Kalaman Hajiya Mama ya Dawo da Duka Hankalin Mutane Falo harda kuwa Na Dina da Hajiya Batula suma sai suka Fara Ankarewa da Abunda ke Faruwa.

Kowa ba bakin Mgana Mama Safiya ce ta isa kusa da Farida ta Na kara kallon Anan kafin ta kalli Farida Tana Fadin"Ikon Allah..Wlh Hajiya Mama yaranan Duk yadda akayi Jininmu ne bayin Allah Daga ina kuke dauke da yara masu kama da ahalin mu.."Zuwa Lokacin Har su Zainab Dake Dakin sun Fito Falo ganin Falon yayi Shuru anata mgana.

Farida ta Murmusa Tana Fadin"Wacece Umma..!? Ina Nene..? Ina Goggo Halima..? Ina Alhaji Tsoho..? Ina Abba..? Ina Firstlove..? Duka Sunanayen Data Lissafo bai Razasu ba sai Sunan karshe Wato Firstlove gabadaya sai suka Zuba Mata ido kafin kace me an Zagaye su Farida Bakin Umma na Rawa ta Rike ma Farida Hannu Tana Fadin'"A..i..na kika san wannan sunan..? Ko kin Taba Haduwa da Halimana ne..?

Tafada Hawaye na kawo mata sai Yanzu ta kara kallonsu Anun Taga Kamanin Halima Atare da yaran Farida tayi Mirmishi Tana kallon Umma kafin tace"Ko ban sani ba kece Umma ko..? Da Sauri Umma ta Daga mata kai Anan ta Mikamata Tana Fadin"Karbi Jikarki...Takwaranki ce sunanta Fatima Zainullahi Usman Saulawa muna Kiranta Anan..."

Gabadaya sai Falon ya Dau Salati da Sallami ana maimaita sunan da Farida ta Kira jiki na Rawa Umma ta karbi Anan wacce ta Bare baki Zatayi kuka Farida ta kalleta Tana Fadin"Shii..Kada kiyi kuka...Nan gidanku ne Anan yan"uwan Ummanku ne.."Tafada Tana kara kallon Kowa Dake Falon Zuwa Lokacin har su Abba sun Bayyana Domin Hajiya Mama ta Ruga ta sanar dasu Abunda ke Faruwa Zafeera har tana Tuntube Dataji Labarin Wata Tazo da yara masu kama da Arman kamar kuma Tana san Wani abu game da Zaina,Goggo Halima ma Tuni ta Fito Tama kasa mgana sai kuka acikin Ranta kuma Tana Fatan Allah yasa Halima ta bayyana ko labarinta

Kawai sai ganinta akayi gaban Farida Cikin Hawaye Zafeera ke Fadin"Ina Uktita..? Don Allah Tana ina..? Kada ki sanar dani Ukti ta bata Raye don Allah..?

Zulaihat ce wannan karan ta Mikama Zafeera Anun Tana Fadin"Ga yar"uwar Haihuwar Anan..Sunanta Maryam muna Kiranta Anun.."Da wani Sauri Zafeera ta karbi Anun Tana kallinta Cikin kuka Take Fadin"Wlh wadanan ya"yan Ukti ne da Yaya Dakta ne..Ko Rantsuwa nayi ba zanyi kaffara ba Cikin Data Fita Dashi ne.."Take Fada Tana kuka Tana Rumgume Anun

Zuwa Lokacin Umma ma Ta Fara kuka su Abba kuwa mamaki ya hanasu mgana Alhaji Tsoho na gefe yana Hamdala acikin Ransa Umma ta Durkusa agaban Farida Tana rike da Anan take Fadin"Don Allah bayin Allah kuyi gaggawan gayamana ina Halima take..? Kada kucemin ta Rasu wajen Haihuwan yaran nan Wlh Zukata Dadama zasu Raunana Ba kuma mu da karfin Gwiwan gayama Zain cewa Zainarsa Bata da Rai.."


Take Fada Tana kuka kowa kuma sai Jikinsa yayi sanyi Dina Dake gefe sai Zufa take tana Zare ido Farida Batace komai ba illah Waya Data Daga ta kira Layin Zulaihat Dake hannun Zaina Cikin Rawan baki Zaina ta Daga wayar Farida tace"Ki shigo Ciki Sa"adiya.."


Kowa sai ya koma kuma kallon Farida da kuma Jin sunan Data ambata,Sai kuka ya Tsaya Cak kowa ya Zubama Kofa Ido Cikin Fargaba da Damuwa Zulaihat kuwa Tana Gefe kawai tana Hawayen Taya Sa"adiya Murna ita yar gatace gaba da baya.

Zaina Da

28 / 37