Chapter 4 Reading Zainazain Book 2 Complete By Janafty Arewa Novels

Zainazain Book 2 Complete By Janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   4 / 37

9K to 12K   out of 108.5K words

Hotel Service ko Ta samo mana wani Abu na Tsani harka da yan Tayi nan da kuke yi Suby..

Suby Zatayi mgana Uwar Mata Ta Daga mata Hannu Tana Fadin"Kowacce Ta kama gabanta Baku da amfani..Ita wanchan Banda Shaye Shaye ba bu abunda Ta iya ko..? Da Sauri Kacharalle ya kalli Rufy Dake Busa Sigari Tana Layi kafin yace"Hm bari Hajajju ai Rufy Ta Fara Haukacewa Da wannan Shaye Shayen.."

Cikin Muryan Maye Ta Mike Tana layi Take Fadin'Kacharaleee...Uwarka ce Ta Haukace ammh bani ba Don mai Cin Uwarka.."Ta antayamai Zagi Uwar mata Ta saki Baki Ita da Hajiya Zabba"u Kacharalle yace"Uwarki dai Data ce Jeki kya gani badai Tawa Uwar Da Har ta Mutu Tana sakamin albarka ba irinki Da Uwa da Uba suka Sallama ba suka ce Jeki kya gani ba.."

Rufy Tataso mai Uwar mata Ta Daga Mata Hannu Tana Fadin"Dillah ku Saurara min..Kai Kacha kama gabanka Don Allah baka da aiki sai karewa Gindin mata ina aikin Gogen Gogen Da na baka agidan Abincina...?ka wuce ka Tafi Chan yanzu zan Shigo..!? Baki ya Washe yana Fadin"Angama Hajjaju...Toh in ban Rabi Mata Ba Maza kikeson na Raba..? Mata Sune Mu mune su Uwar mata.."Tana Hararansa Tace"Fita Waje ka Jirani Nace.."Da Sauri yace"Angama Uwar mata mganin kukana.."Da Sauri ya Fice yana waka yana Fadin"Mata akama Sa"ana Mata..Macen da bata Sana"a Sauna ce Lale Lale maraba Da Mowar mata..!

Yana Fita Uwar mata Ta Daga Baki Tana Fadin"Sholly Fito..Nasan kina jina Hajiyar mata Fitowa ne bazaki yi ba..Maza ki Fito keda Bakuwar Da Kika Dauko batare da Sanina ba.."Tafada Cikin Kakkausan Murya Zaina Dake Tsuma Daman Tun Zuwan Uwar mata Tayi Saurin Mikewa,Tana Wani Kifkifata Ido Tana kallon Sholly Dake shan Complex abunta Hankalinta Kwance Cikin Rudewa Tace"Anty Farida...Wa...'

"karki Damu saka Mayafinki muje....."Farida Ta katseta Tana Mikewa Lokaci Daya Kofin Hannunta Ta ijiye nan saman Center Table din,Bata Saka mayafi kan Kayan Jikinta ba Ta kallo Zaina Data yane kanta da Mayafinta Datazo Dashi Idanuwanta Duk sun kumbura Saboda Kuka,Farida ta kalleta tace"Karki Damu Sa"adiya..Uwar mata bata da tacewa akan zamanki awajena..Ki kwantar da Hankalinki.."Sai ga Hawaye Sharr sun Zubomata Tana Fadin"Ina Fargaba..In na var Wajen ki ina zani..?

Farida Ta Riko Hannunta Tana Fadin"Bazama ki bari Ba..Muna Tare Har sai kin ga Yuyuwar Komawar Ki Gida na maidaki da Hannuna Insha Allahu..Taho muje.."Tafada Tana Janta suka Fito Daga Dakin Tun da suka Fito Uwar mata ke kallon Zaina Haka Hajja Zabba"u Su Suby ma Daga Dakunansu sai Leke suke suna son kara ganin Zaina Sholly Ta Tsaya gaban Uwar mata Tana Fadin"Dama ai nasan Sai Magulmata sun Kiraki sun gayamiki ina ganin Kiranki na kyaleki Saboda Ni bana son Harkan Munafukai in zanyi Abu Kai Tsaye nake bana Kumbiya kumbiya kema kin sani.."

Uwar Mata Ta Murmusa Tana kallon Sholly Kafin Tace"Nasani Shiyasa ban yi Fushi Dake ba Shalelena...Abunda ma yasa nayi Mgana Saboda kinsan dai Abunda ya Faru na Hana karban baki Batare da izinina ba ko..? Wacece ita wannan Din Da kika kawo Duk da naganta Yar Shila ce Sosai in Ta Kide Zata Zama kamarki Watarana ko zabba"u..?.."Tafada cikin jin Dadi.

Hajiya Zabba"u Tace"Sosai ma..Hajar zatayi Daraja Uwar mata akashe mata Dala zaki Fanshe.."Dariya Uwar mata Ta kwashe Dashi Har suna Tafawa Cikin Wani Sakaran kallo Farida ke kallonsu

Kara kallon Zainar Uwar mata Take Daga sama Har kasa Tana Ayyana Abubuwa Dadama acikin Ranta,Taji Zaina tace"ina wuni.."Tafada Tana Boyewa bayan Farida kamar ace kyat ta Gudu,Uwar mata ta Washe baki Tana Fadin"Lafiya lau yanmata ya kk..?

Da Sauri Sholly Tace"Uwar mata wannan fa ba irin Wacce kike Tunani bace..Sa"adiya Sunanta kuma kanwatace ba Haja bace.."Wani Sakaran kallo Uwar mata Ta Bita Dashi kafin tace"Kanwarki..? Sholly yaushe kika Fara karya..?
Sholly Tace"Ban fara ba..Gaskiya na gaya miki Kanwata ce ba Haja bace..'

Uwar mata Ta kallesu Dukkansu kafin Tatabe baki kawai Ta kada kai Ta Juya Tana Fadin"Wannan mganar Bata nan bane..Ki Sameni Gidan abincina Zabba"u muje Zaman gidanan ya Isheni Shegu kazamai na Tara Sun kazancemin Gida ko Shara basu yi.."

Hajiya Zabba"u tabi bayanta Suka Fice Sholly Ta Rakasu da kallon Kafin Ta Juyo Wajen Zaina Wacce ta Bude baki Zatayi mgana Ta Dakatar da ita da Fadin"Karkice komai...Muje mu sameta Kada ki damu ina tare Dake.."Daga Haka Ta jata suka Fice Suna Fita suka Fada Gidan Abincin Uwar mata Wanda zaina Tana ta mamakin Girman wajen Da kuma Turuwan Maza awajen sai Taga mata masu Kula da Wajen suma Din Duk kama suke da karuwan Kowacce Shigarta ba kyan gani Sanye da karamin Mini Sakat baki da Jan riga kamar Shine Uniform dinsu Tunda suka Shiga Wajen Mazan wajen suka Yi musu caa da Ido Sholly na Rike da Hannun Zaina ta Hade rai Shiyasa ba"a samu Fuska ba Cikin Office dinta suka Sameta Zaune ita da Uwar mata an kawo musu lemu da Snacks.

Suna Shiga Uwar mata Ta Kalli Sholly Cikin Kakkausan Murya Tana Fadin"Ki gayamin gaskiya ita din Wacece..? Me kuma manufar kawota Gidana..?,sholly Ta kauda kai Tana Fadin"Sunanta Halimatus Sa"adiya kamar yadda na Fada miki Yar garin Bauchi kuma kanwa take awajena.."

Uwar Mata Tace"Karya kike Sholly wannan ba kanwarki Bace ke Bafullatan Gomben ce..Ita kuma yar Bauchi ne Ta ina kika Hada Dangi da ita..? Malama ki gayamin Zaman me Zatayi agidana matukar ba Haja bace..!?
Tafada Tana kara kallon Zaina wacce kanta ke kasa Ammh in ka Lura Jikinta ne ke Rawa kamar Mazari Ganin Haka yasa Farida Ta kalleta Tana Fadin"Sa"adiya koma Daki Ki jirani kinji ko..? Kada ki Tsaya ko"ina..'

Zaina Ta gyada kai kafin ta Fice Cikin Fargaban Makomarta In Uwar Mata Ta Koreta ina Zata..? Sai dai ta koma Gida Domin Bata Fatan Daganan Taci Gaba Domin Bata san kuma Wajen wa zata Fada ba tana Fita Farida Ta Waigo Tana kallon Uwar mata Tana Fadin"Na gaya miki Ba Haja bace..Zata zauna awajena nadan Lokaci in Lokacin Tafiyarta Yayi zan maida ita Gidan Iyayenta Da kaina.."

Uwar mata Tace"Akarkashinki Zata zauna kenan..? Bazai sabu ba sai dai ki bani ita na Tafi da ita Kaduna Na Gyarata achan Donin Har na Hango yadda Zata koma da irin Riban da zan samu Yarinya Itama kamar ki Take gata yarinya Karama ga Dirin Mata sai dai Rama ce ammh Zatayi ta cin Abincin Gina Jiki Tana Cikowa.."Farida Ta saki Baki Tana kallon Uwar Mata kafin Tace'Wlh Bazan iya baki ita ba Uwar mata kiyi Hakuri kawai..'

Uwar Mata Tace"Lalle Sholly ina mgana kina cewa A"a..? Farida Batayi mgana ba Ta kauda kanta kawai Hajiya Zabba"u ce tace"To Ai naga itama Sholly Karkarshin Ikon ki Take Balle Wata Da ta kawo..?

Uwar Mata Tace"Shi nagani..bar ganin Ina Sangartaki kina Abunda kikaga Dama Wannan Dalilin bazai saka na Dauki Raini ba Zaki bani yarinyar nan Sholly nagama Mganata.."Sholly Tace"Uwar mata Kiyi Hakuri..Ban ta Miki gadda ma ba ammh wannan karon Zan yi miki bazan iya baki Sa"adiya ba Haba Don Allah me kike nema Wanda bana baki shi..? In kudi ne Damuwarki Zan Dinga Ninka Miki Abunda nake baki Harda na Sa"adiya ammh Ki cire Idanuwamki akanta Don Allah..'

Tafada Tana Hade Hannayenta alaman Roko Uwar mata Ta kalli Hajja Zabba"u itama Ta kalleta sai ta gyada mata kai kana Ta maida Kallonta kan Sholly na dan Lokaci kafin Tace"Kin Tabbata zaki Dinga Biya mata Haraji..??mganar Daukan Dawainiyar kanta wannan ya Rage naki Tunda ke kika ji kuma kikagani kuma In Wata Matsala Tataso Allah ba Ruwana.."Sholly Tace"Na yarda..Matsala kuma da yardan Allah bazamu ganta ba.."

Jinjina kai Uwar Mata Tayi kafin Tace"Shikenan kya iya Tafiya.."Farida Tace"Ba shikenan ba Ina so Ki Fadama Sauran Kananun yan iskan Dake Gidanki Koda bana Gidan nan Kada wata ko wani ya sake yayi ma Sa"adiya kallon Banza..Ki Gargadesu akanta In baHaka ba kuma Zanyi Rashin Mutumci Wlh.."Uwar Mata Tace"Jeki..Zan gaya musu Balle ma sun san Duk Abunda yake naki ne ba irin nasu bane.."Farida Bata kara mgana ba Ta Fice Tana gyara Daurin Dake kanta Bayan ta Fito Maza na Tayi mata mgana suna Kiranta Sholly ammh Tayi musu Burus Domin Farida bata Harkan kananan kwarin dasu Suby suke yi dasu Ita Harkanta da Manya Kuraye takeyi

Tana Fita Waje Taga Zaina Kacharalle da Suby sun Tare ta suna Ta Zuba mata Zence har Suby na Dafa kafadarta Ranta ya Baci Tana Zuwa Ta Daka musu Tsawa Dole suka Dare Kacharalle zai yi mgana Farida Bata Bi Ta kansa ba ta Figi Hanun Zaina Tana Fadin"Me na gayamiki ne..?nace ki Jirani adaki ko..? Nan fa ba irin Rayuwar da kika sani ba ne Ina Kiyaye Rayuwarki ne ke baki sani ba ko..?

Haka Take ta Fada Har suka Shiga Daki kana ta Saketa Zaina Kamar Tayi kuka Tana Fadin"Ya zanyi Anty Farida..! ? Na Fito zan Tafi suka Tare ne suna ta cemin wai kina so ki Cuceni ne na Hada kai dasu Wlh zan yi kudi sai na fiki kudi.."Farida Ta kwashe Da Dariya Tana Fadib"Bariki Kenan Gidan kazo nazo..kinga yadda sukamin kema Watarana Haka zasu Miki Ba Amana da Yardan a Wadanda Watsewa da Duniya ta Hadaku Sa"adiya ki Rike wannan Koda Watan Wata Rana.."

Zaina Tace"Ai ban ma Nuna na Jisu ba ko mgana ban musu ba sai Gaki.."Farida Ta wuce Tiolet Tana Fadin"Bari nayi wanka Zamu Fita nayi Miki Shooping Muci Abinci Har asibiti ma nake so nakai ki aduba ki Cikin ki Har ya Fara Fitowa bana so a samu Matsala.."Cikin Mamaki Zaina na Kallon Cikinta sai Lokacinta Taga ya Turo kadan bada yawa ba Mirmishi Ta saki Tana Shafa Cikin Kafij Tace"Nagode ma Allah Daya Hadani dake Anty Farida..Zaki Tayani Cika alkwarin Da nayi ma Firstlove kan Kula mai da kaina da Abunda Ke Cikina.."

Take Fada Tana Mirmishi kafin kuma ya Rikide ya koma kuka,ammh Sai Tayi Saurin Share Hawayenta Bayan Farida Ta Fito Itama ta Shiga Tayi wanka Ta bata Wata Doguwar Riga baka ta Saudiya ta saka da Gyalenta ita kuma Riga da Wando Ta saka sun kamata ta Saka Siririn mayafi Dakin Suka Kulle kana Suka Fita ba wanda yace musu komai Suna Fita Waje suka ga Uwar mata da kawarta Zasu koma kaduna Kebewa sukayi da Farida sukayi mgana kana suka Shiga Mota suka Tafi Su kuma suka Gangara Titi suka samu adaidaita suka Hau.

Cikin Sabon Gari Farida ta kai Zaina Wani Shago Datake Siyan kaya Ta sata ta zabi Dogayen Riguna da irin Kayan pakistan Haka,sai Riga da Sikat,bra,sikat da kuma kayan kwalliya,Takalma da Sauransu,Sai da suka gama Siyan komai Farida ta Biya kudi Kana Suka Dauka Daman Drop din mai adaidata Farida Tayi Daganan Restaurant suka je Farida Tayi musu Oda suka ci Abinci Daganan Ta Dauketa suka je Apple White ta Siya ma Zaina Gashashen Kifi da Ice Cream Kuma ta Lura Tana so Sosai Take Shan Ice cream,Daganan Wani Private Hospital Takaita Almadina Dama Tasan Wani Likita Suna zuwa Ta Fadi Abunda ke Tafe dasu ba Dadewa aka Bude ma Zaina Fayel Likita ya Dubata yace komai Normal Zasu Dawo nan da 2 week ayi mata Scan agani Ya bata mgangunar karin Lafiya kuma yace ta samu Hutu sosai Daganan asibitin suka koma Gida Koda suka je Gidan ya Cika wai Adamalle na Birthday Karuwai maza da mata gasunan kawayensu Sun Cika Gidan anata Rawa da Kida Haka suka Raba suka Wuce Zaina mamaki kawai Take ganin Maza da mata sai Shaye Shaye suke wasu kuma suna Ta Rawa wwsu kuma na Gefe suna Shanshancinsu.

*******

Achan Bauchi kuwa Abubuwa duk sun Taru sun Rikice Bangaran Zain dai ba wani Cigaba Domin indai yana Farke Bashi da wani aiki sai sambatu Yana kuka yana Kiran sunan Firstlove mganguna da alluran Barci ake mai suke Taimakamai yana Samun Barci.

Daga Baban Kaduna har Daddy Abuja ba wanda ya koma Duka su da matayensu suna nan ba kwanciyar Hankali,Umma dai an samu Taji Sauki Ta Daina koken sai dai Damuwa Ta Daina yawan mgana Kullun sai Ta Tagumi Chan Gidan Alhaji Tsoho ma sai a Hankali Hajiya Mama da goggo Halima Sune ma masu karfin Halin Matar Isuhunta Tuni ta koma Goggon Haliman ne sai an kwana Biyu Zata koma.

Bangaran Dina Kuwa Ta Kara Shiga Taitayinta ganin Nene ma Ta Daina Bi Ta kanta gashi Tanaso Tasan Halin da Zain yake Ciki ba Dama bamai Bata Fuska sai dai Tayi ta zaman Daki Tana kuka Dole ta kira Hajiya Maimuna Tana kuka Ta gayamata komai ita ta Kira Kwamishina Ta gayamai abunda ke Faruwa yace shi bai sani ba Da yaso nan Weekend yaje Bauchin ammh zai yi Kokari Yaje Zuwa Gobe yaga Abunda yake Faruwa.

Haka kuwa akayi Washegari Shida Direbansa suka Tafi Bauchi Sai da Alhaji Tsoho Yaga Kwamishina kamar Daga sama Bayan gaishe gaishe da Jaje aka Fara maida Yadda akayi,kwamishina ya Janjanta Lamarin Sosai Tare da Alhaji Tsoho suka Tafi cikin asibitin Tunda Duk su Abba na chan sai dai suka gansu kawai Lokacin da Alhaji Tsoho Yaga yadda Zain ya koma sai da ya Share musa kwallah Duka ya"yansa Nashi Sun Rame Atsaye ga Haddir Dashi Duk ya Zabge Saboda Fargaba Suna Dakin Zain ya Farfado yana ganin Alhaji Tsoho ya Fara Fadin"Yauwa gwara da kazo..Ka saka baki Alhaji Tsoho Su Abba Su bar na tafi naje na nemi Matata..Tunda su sunki Nemo Min ita Taya zan kwanta anan Wajen Ina Barci Bansan Wani Hali Matata ke Ciki ba..?ciki fa gareta ko Kun manta ne..?

Yake Fada yana Tsiyayan Hawaye Su Abba dukar Da kai kawai sukayi Cikin wani Hali Alhaji Tsoho ne ya Dinga Lallashinsa yana Fadamai Insha Allahu Halimar Zata Dawo Da yardan Allah kana ya daina Sambatun sai kuka sai ajiyar Zuciya,,Alluran Barcin bata Sakeshi ba sai ya koma Sai da suka bar Dakin kana Alhaji Tsoho yace Su Dawo da Zaunullahi Gida adaina dura mai Abunda zai sakashi Barci Hakanan kada kwalkwawarsa Ta samu matsala Adawo Dashi Gaban Iyayensa zai Dinga mai Rubutu yana Sha zai samu Natsuwa Da yardan Allah.

Da Shawaran Alhaji Tsoho akayi amfani Cikin Lokaci kalilan suka Dauko Zain din Zuwa Gidan Abba sai dai su Abba suka gansu kwatsam Dashi,Alhaji Tsoho da kwamishina Suma Dasu akazo Dakin Sadiq Babba aka Saukeshi Umma da Nene dasu Zainab da Zafeera suna Ta kai da kawo Kuma Alhamdulillah Ganinsa agida yasa Sai ya samu Natsuwa Zain din ba Sambatu ammh yana ta Bin Kowa da ido kawai Barinsa sukayi a Dakin Shida Haddir Dukkansu suka Fito Falo sai Lokacin Alhaji Tsoho yace Nene Tayi ma Kwamishina Jagora Zuwa Dakin Dina ya ganta Haka kuwa akayi Tana kaishi Ta Fito Dina na ganinsa Ta Mike ta Rumgumeshi ta Fashe da kuka nan ya zauna yana aikin Lallashinta Shi ya gayamata an Dawo da Zain Gida anjuma Ta Shiga Ta Dubashi Sai Lokacin taji Hankalinta ya kwanta bai Jima wajenta ba suka Fito Tana Rike da Hannunshi Ganin Daddy yasa Ta Duka Ta gaida su Abba suka amsa ba Yabo ba Fallasa Fatan Allah kara Lafiya yayi musu da kuma Sallama Har Waje Alhaji Tsoho yace Su Abba su Taka mai ya kawo ma Dina Katan katan dib Hollandian Dama yasan Taso ne Megadi ya kwasa Zuwa Ciki Tana Dagamai Hannu Har Motarsa Tabar Haraban Gidan Kana ta Dawo Cikin Gidan ganin ba Fuska yasa Bata Tambayi ina aka kai Zain ba sai Ta koma Dakinta nan Taga Duka Abunda Daddy ya kawo mata an Shigo mata dashi Sai kuma Taji bata ji Dadi ba ko bakomai ai su suke ci da Ita bai kamata a kawo matasu Duka ba sai tace bari Ta bari in su Abba sun Fita Ta Fita Tayi ma Nene mgana.

Sai Bayan Isha"i su Alhaji Tsoho suka bar Gidan Bayan Zain ya Farfado Har Nene ta bashi Tea yasha Ya Tafi kan gobe da Safe Haddir yazo ya karbi Ruwan Zamzan din da zaiyi addu"o'in aciki arika bama Zain din yana Sha,Sun Tafi Da Jin Dadi ganin Zain din ya Daina Sambatun Alhamdulillah anga Cigaba Ranar Dai Haddir ya kwana Wajen Zain din Saboda Baza"a barsa Shi kadai ba Washegari kuma Yaje ya karbo Ruwan addu"an ya kawo aka Fara Bama Zain,Ranar su Mama Safiya da Sauran yan"uwanta da basu Tafi ba su Mom Iklima ne su Goggo Halima ne Harda Hajiya Mama inna Rukayyah Inna Hannatu,,Su Waleeda da su Lauratu hajiya karama dasu Muhammed Amin duk nan Gidan Abba suka Wuni Hamdiya ma Amarya Daga kaduna sai Kira Take Tana Jin Ya ake ciki.

Washegari kuma Kowa ya Dauki Iyalansa suka koma Baban Kaduna da Daddyn Abuja Yan"uwan Mama Safiya ma Tun Safe suka Tafi,Goggo Halima ce kadai Ta Rage sai Zareena itama Jawaad Yace Ta zama Cikin Shirin Sati mai Zuwa Visar su zata Fito zasu koma,Inna Hannatu kuma sai yammah Jirginta ya tashi Zuwa Lagos Inna Rukayyah kuma sai da ta kara kwana suka Wuce ita da Shema da Zafeera,Zafeeran ma Saboda makaranta da Bazata koma ba,Aka bar su Umma suna Kula da Zain Wanda Sauki ya Fara samuwa Dina Ta Shigo Ta gaisheshi Sau Daya ya kalleta bai kara kallonta ba, Ya kauda kai Sai dai Kaga yayi Shuru kawai kamar me Wani Zurfin Tunani Daga Umma Har Abba yanzu Tsauyama Zain suke Sun kuma furtamai sun yafemai Tuni Suna kuma addu"an duk inda Halima Take Allah ya Bayyanata Shi kanshi Haddir sai da Sadiq ya Dawo ne ya samu Sukuni har ya koma Asibiti Saboda bashi ba Zain abun yayi yawa Zuwan Sadiq ne yasa yake barinsa Wajen Zain din yana Tafiya asibiti sai ya Dawo da yammah yake zuwa ya kara Dubashi Ba laifi Tunda ya Daina Sambatu kuma yakan ci Abinci yana kuma Mgana Daya zuwa Biyu.



*Ki biya ki karanta Cikin Salama..Rashin Daraja ne ki Saka kudi ki siya abu kuma ki Fitar dashi..Mace mai aji Bata kiran Abun sata komai nata mallaka take..*






*Janafty...*
7/10/21, 8:40 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B20️⃣4️⃣


*IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*

*Bayan sati Daya*

"Bayan Sati Daya Da Dawowar Zain Gidan Abba Abubuwa Duk sunyi Sauki Sosai yake samun Sauki anata kuma ganin Cigaba Tunda yanzu yana iya yin Wasu Abubuwa da kansa kamar Wanka cin Abinci Da Sauransu Sai dai ya koma wani so Silemt Shuru Shuru ba mgana ya Rame Kamar bashi ba Ya Daina Yawan Kukan da Kiran Sunan Firstlove sai dai kuma Zaka ganshi Cikin Tunani mai Zurfi Wanda

4 / 37