Chapter 27 Reading Zainazain Book 2 Complete By Janafty Arewa Novels

Zainazain Book 2 Complete By Janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   27 / 37

78K to 81K   out of 108.5K words

Allah ya kaddara.

Zafeera Dataji Labari a bakin Zainab baki ta Rike kawai Tana Jinjina Munafuncin Namiji Zareena kuwa Kiran Zain Tayi tana mai Tsiya Shidai ya kasa Mgana Ta kira Haddir Shima Tana mai Shakiyancin ango yasha kamshi Sai Lokacin ma mganar Bikin Ta taso mai Shidai Tunda akayi mganar bai kara Tada mganar ba kuma ba wanda ya kara mai magana abunda bai sani iyayansu suna nan suna ta Shirinsu batare da sun Saureresu ba Haka ma Zafeera itama bata damu kanta ba Sanin Datayi Auran nan Dole ne sai ta maida hankalinta kan Jarabawan da zasu yi na Shiga aji Hudu nan da wata Biyu da wani Abu,Tunda shi Uban gayyar bai Taba Nemanta ba itama Baya gabanta Daman ko Lambarsa bata dashi Sai dai in Ta Tuna yau gata Zatayi aure ba Ukti a kusa da ita sai Taji kwallah ya kamata Tana addu"an Allah ya bayyanata Suna mgana da Laila ta Chart kullum mgarta kenan An ji Labarin Zaina Tace mata Wlh Shuru ne haka zasu yi ta Tattaunawa Cikin Jimami Suna addu"an Allah ya bayyanata Lailan Ta gayamata an saka Ranar Auranta anan Bauchi In Lokaci yayi Zata zo har Gida ta kawo ma Umma kayan Biki Koda Zafeera Taji haka bata iya gayamata itama Zatayi aure ba Tunda Mijin ma bazata Dora komai akansa ba Shi yana mata kallon mai Girman kai itama tana mai kallon Haka sun Ki bama Junansu Dama ballatana Su Zauna su Fahimci juna.

Samuwar Cikin Dina yasa Duka Su Umma suka koma suna Kula da ita Har wata yarinya mai aiki suka samar mata Domin ta Rika Taimakamata,Kwamishina da Hajiya Batula sun zo sun Duba Dina suka Koma Ganin Taji Sauki Sosai Cikin yayi mata kyau kamar na Arman,wanda akeTunanin nan da wata Biyu Dina Zata yayeshi Tunda yayi wayau Sosai Sai ya Wuni Shashensu Umma bai Damu da Nono ba Sai abubuwa sukayi ma Dina Sauki,Sai dai Tunanin Zain da kaunarsa suna nan acikin Ranta Zakiya kuwa bata san isalinta ba sai da taje kano Sun Shiga Shopprite ita da Hajiya Batula da su Waled Da Arman suka Hadu da wata Ashanty da sukayi karatun Prine Collage Tare Nan take ce mata bata ganta wajem Bikin Zakiya ba Dayake ita Ashanty taje suna Mgana da Zakiya ta waya Dina Taji mamaki ammh Sai ta Boye mamakinta kawai tace Lokacin bata nan ne Sai Ashanty tace haka Zakiyan ma tace nan take mata Tsegumin Zakiya tayi kuskuran auran wannan yaron ta sakar mai komai nata awannan zamanin ba"ayi ma Maza Haka Dina dai bata Tofa ba tace Allah ya kyauta Bayan Sun Dawo gida ne Hajiya batula ke Tambayanta Daman Zakiya tayi aure ne..? Dina tace bata sani ba Domin Rabonta da zakiya Tun Ranar sunan Arman Hajiya Batula tace yafi ne gwara Kowa ya kama kansa Tunda zaman ba Mutumci.

Dina Tana ma Zakiya addu'an Allah yasa kada Ja"afar ya zama Jarbta Gareta kamar yadda Zain ya Zame mata Komai ya Faru Tsakaninsu bazata so wani Abu ya Faru da Zakiya ba ammh Tasan tama kanta karya Dole ne Daga ita har Zakiyan sai sun Girbi Abunda suka shuka sai dai Tana Fatan Koma menene Allah yasa ya Tsaya mata haka Tunda Ta Tuban ma Allah Ko Rashin Samun yadda take so ga Zain Allah ya barta Ta gane bata da wayau.

******

Achan Zaria kuwa Jikin Farida Gabadaya yaki Dadi Cikin Wata Hudun nan ta kwanta asibiti ba iyaka Ciwo Biyu ne ya Hade mata Lokaci Daya ga Hawan Jini ga Ciwon Zuciya.

Gabadaya Ta Rame ta Fige kamar ba ita ba Tayi baki,In kaganta sai ka Tsausayamata Saboda yadda ta koma,Ga su Anun Sun yi wayau suma Sun Fara Tatata Zaina da Zulaihat su kansu basa Cikin kwanciyar hankali Domin Farida ce komai na su yau in Ta Fadi ta Mutu Sun Shiga uku sun gama Lalacewa.

Yanzu Bata Cika Zuwa Ko"ina ba Saboda Jiki yaki Dadi kuma Taki Cire Damuwan Dake Damunta In Abun ya tashi Ta Dinga Aman Jini kenan Sai Lokacin Ciwon Farida Suka San Alhaji Badamasi da Idanuwansu sun kuma Shaida Bayan Abokin Shashanci Shi din mai Son Farida ne yayi Hidima da ita Suma kuma yayi dasu babu Abunda suka nema suka Rasa na Bangaran Rayuwa sai dai Zullumi na Zuciya da ganin Halin Da Farida ke Ciki.

Ita Kanta Uwar mata bata da Natsuwa Domin Inta Ra sa Sholly Tayi Rashin Gibi Sosai acikin Harkallanta Dole ta Dage wajen Ganin Faridan Ta yarda Alhaji Badamasi ya Fita da ita Kasar Waje anyi mata aikin Zuciya sai dai Duk Hikimarta Farida taki yarda Ta gwammace Ta Zauna ahaka ammh Tace kafarta Bazai Taba Taka ko wata kasa ba Batare da Zaina ba dasu Anun ba Jin haka yasa Alhaji Badamasi yace sai yayi Visa har da Zaina sai su Tafi Dukkansu nan ma Tace A"a ita bata Bukatar ta Warke Tafi Bukatar Mutuwar ta Da komai ita da Rayuwarta Bata da wani Sauran amfani Ba Ahali ba ya"ya ba wani Jigo Daga Sa"adiya Da su Anun sai Zulaihat ne kadai Zasu kukan Rashinta da kewarta Sai dai Tana Fatan Kafin Karfinta ya kare Ciwon nan ya Zama ajalinta Zata Cikama Sa"adiya Alkawarinta na maidata Hannun Ahalinta kuma ayadda take jin kanta yanzu Lokaci ya kusa yi da Hakan Zai Faru.

Uwar mata Ganin Farida ta Nuna Taurin kai sai ta Hadata da zaina Tace tayi ma Faridan mgana Ta bari afita da ita ayi mata aikin Zuciya ko ta samu Lafiya Tunda Saboda ita Farida tace ba inda Zataje Zaina Saboda Samun Lafiyar Farida yasa Ta amince Faridan Taje ko"ina Neman Lafiyanta kada ta Damu da ita ammh Fafur Farida taki yarda Dole Dukkansu suka Zura mata ido Allah yasa ma Tana Da mgunguna Tunda Tana Zuwa ganin Likita abun sai yake Zuwa da Sauki.

Akwai Ranar da suka kwana Cikin Tashin Hankali Farida kwana Tayi Datayi kaki sai Amai Kamar bazata kwana da Rai ba da asuba Zulaihat ta kira Uwar mata Ta gayamata Hankali Tashe Ta Kira Alhaji Badamasi ta gayamai shi kuma yace Uwar mata Tayi Shatan Mota Suzo Abuja Uwar mata Karachalle ta Kira tace yaje ya Samo Mota yaje ya Dauko Farida ya kawota Kaduna jin haka yasa ba Bata Lokaci ya samu Shatar Mota yaje Gidansu Farida ya iske Zaina da Zulaihat nata kuka Yana gaya musu sakon Uwar mata Zaina tace Zata je Farida na Cikin Ciwo ta Hana tace su Zauna agida Insha Allahu Indai taji Sauki Zata Dawo Ta zama Cikin Shiri Zata maidata Gida Tana kuka suna kuka Aka Tafi da Farida Anun da Anan Harda Birgima Domin Sunan Anty Farida shine abu na Farko da bakinsu ya iya Fada Cikin Yaren su na yara suna ganin Mamarsu na kuka da Zulaihat farida kuma Za"a Tafi da ita suma suka Fara kuka Allah Sarki ko yaro yasan mai kyautatamai.

Tunda aka Tafi da Farida su Zaina basu samu kwanciyar Hankali ba sai bayan kwana Biyu da Farida ta Kirasu ta gayamusu Gata acikin wani asibitin kudi dake Abuja an Dorata kan mgani Taji Sauki su kwantar da Hankalinta ta na nan Dawowa jin haka yasa sukaji Hankalinsu ya kwanta Har suka iya cin Abinci Ammh Fa Zukata sun Raunana.

Dama Da karachalle ya kaita Kaduna Uwar mata da Hajiya Zabba"u suka Tafi da ita Abuja Koda sukaje Direct Wani Babban asibiti,suka Nufa da ita Inda Alhaji Badamasi ya basu address din Suna Zuwa aka karbeta Daman already yayi ma Wani Babban likita bayani wanda kuma karatunsa ya shafi masu mtsalan Zuciya shi yayi attempting dinta har ta Dawo Hayyacinta Uwar Mata da Hajiya Zabba"u suna Tare da ita Abuja Alhaji Badamasi kuma nata Wahala dasu.

Chan Gidan Uwarmata kuwa Labarin Rashin Lafiyan Farida Tuni yakai musu Suby kamar ta Zuba ruwa akasa Tasha aranta kuma Tana addu'an Allah yasa Faridan ta Mutu taga karyan Tsiya su Deezee ne da Adamalli suka Tsauyamata Kalaman Suby kuma ba wanda yaji mamaki Sanin Daman Bata Taba kaunar Farida ba Kowa sai Tambayan Sa"adiya yake Domin Tunbarinsu gidan basu da labarinta yanzu hakan ma ba wani Labari akanta Tunda Farida Ta Toshe Duka Hanyar Samun Labarin Karachallre ne Daman ya Fada musu Farida ba Lafiya Tana Abuja Shima Domin yaga Ciwo ne bai Zata wasu Zasu ji Dadin haka ba Daganan ya kama bakinsa yayi shuri yana Tunanin Irinsu Suby ba imani acikin Zuciyarsu.



******

Bangaran Zakiya Amarya Kuwa Anga Ribar amarci da Aure Domin Tana Dauke da karamin Ciki Dan kimanin Wata Uku,Tuni Fi"ili da iyayi ya karu Wajen Zakiya sai dai kuma Cikin ya zo mata da Bala"in Laulayi da amai Har da kwanciya asibiti tayi,aka Kara mata Ruwa Ja"afar ke kula da ita Duk da Shima ya Fara karatunsa a ATBU Bauchi yana karantar Political Sciences,Zakiya tayi Shige da Fice ta sama mai Takardan Sakadiri Har ya samu Gurbin karatu a jami"ar kuma ita tayi Duka Kashe kashen da komai Domin Uban ya"yanta ya Samu Tsayuwa da Kafafunsa Watarana.

Ganin Halin Data ke Ciki Komai sai dai ayi mata Wahalan Laulayi sai Wajen aikinta suka bata Hutu ta Dawo Gida da Safe kafin Ja"afar ya tafi makaranta shi zai Mata komai in ya Tafi kuma Wuni Zatayi kwance Tana Zubar da Miyau Sai dai in Taji Kishi ko tana Bukatar wani abu Tatashi taje ta Dauka Ja'afar Baya Dawowa sai Dare,Tun Abun baya bata mamaki har ya Fara Bata ba Ranar da Ja"far baya Cewa suna da karatu har Asabar da Lahadi sai yace mata suna da Assigment ko suna da Group Dicussiom Ga kuma yawan Cewa ance akawo kaza kudi ba Kanana ba Zakiya In Tana so Taji wani Shakku game da Ja"afar sai ya Shafe mata wannan Sakkun Abunda ya Fara bata mamaki Duk Wata Tana Raba albashinta Biyu ne Tana Turamai Rabi Sauran kuma Tayi hidimar kanta Data Gida Tunda ta Daukan ma kanta ammh Ko Rabin Wata baya kai masa sai yace sun kare ta karamai kudi karatu ya Cinye kudin da Mota,Tun bata Dora abun a Mizani har ta Fara Ga kaiwa Dare awaje sai ya Dawo yace yana Gareji yaje su gaisa da abokansa Haka zai barta ita kadai tayi ta Wahala Abunda ke kara sakawa tana kara yarda dashi Shine in ya Dawo haka Zai ta Wahala da ita yayi Girki ysyi mata wanka in Tayi amai ys Share Da wannan kyautatawar nashi Da Yadda yake Nuna mata Soyayya yasa Koma Wani abu ya Shiga Ranta Take Saurin Fiddashi.

Taso ta koma Dataji Sauki Sai ya Nuna mata A"a ya kamata ta samu karin Hutu,Dole ta Biye mai Ta kara Sati Uku Cikin Hutun da suka bata kana ta Koma Bakin aikinta abokan aikinta sai Tayata Murna suke ita kuma Tana jin Dadi acikin Ranta Tana ta Tunanin Daman Haka Allah yake lamarinsa Tagama Cin Duniyarta da Tsinke Gashi yau tayi Auranta Da wanda take so kuma Take Muradi har da Rabon Ciki ita aganinta wata mai wayau ce da Dubara bata Taba Tunanin Talala Allah yayi mata ba.

Labarin Samuwar Cikinta Har kano Mallam Nuhu Dayaji ya kirata awaya yayi mata Fatan Alheri Duk da yaji Hankalinsa ya kwanta ammh Haka kurum acikin Zuciyarsa yake jin bai yarda da Ja"afar ba Tunda Daga Binciken dayasa akayi masa in yayi mgana Lubabatu ta kwabeshi Da Fadin yayi Shiru kawai yayi mata Fatan Alheri Dole ya kama bakinsa yayi Shuru acikin Zuciyarsa kuma Yana Taya Zakiya addu"an Allah yasa Alheri ne da Sanadin Shiryuwanta yasa ya Kulla wannan Auran..


******

Farida ta Dauki Tsawon Wata Daya agarin Abuja kafin Taji Sauki Kamar ba ita ba ta Fara maida Jikinta Uwar mata Sati Daya Tayi a Abuja ta Dawo a asibitin akwai Nos masu kula da Mara Lafiya Kudi Alhaji Badamasi ya saki suka Dinga kula da Farida har tasami Sauki an Dora ta again kan mgunguna ammh Likitan yaja mata kunni Zuciyarta Tana ta kumbura Kada ta kai karshen da sai an yi mata aiki Da kuma yawan Saka Damuwa Dake kawo mata Hawan Jininta Duk tace Zata Kiyaye kana da gargadin Cin Abinci mai Gina Jiki da samun Hutu Sosai.

Alhaji Badamasi da kansa ya Dawo da ita kayan Dubiya irin na masu Ciwonta iri iri katan katan din Madara maltina da kayan karin Jini su Zaina sunyi murna su Anun da suka Fara dan Takawa sai Murna suke Anty Farida ta Dawo Bakin Zaina da Farida yaki Rufuwa ganin Farida Ta Dawo Cikin Koshin Lafiya Duk da ko da take chan suna mgana ta Waya Alhaji badamasi bai Dade ba ya Tafi Bayan yaJadda musu Farida ta Rika samun Barci da Hutu.

Jin Haka yasa Bayan Tayi wanka Taci Abinci tasha magungunarta Su Zulaihat suka Janye su Anun ganin Zasu Dameta suka barta Tayi barci Sosai sai bayan Mangariba Tatashi Daman Tun bayan Rashin Lafiyan Farida suka Daina Zuwa makaranta suka koma sunayi agida.

Zaina ce ke karama Zaina karatu Dukkansu suna Sanye da Hijabai ne bayan sun idar da Sallah,Su Anun kuma suna Gefe Anan Tana Hawa kan kekensu na Koyon Zama ne Anun kuma tana Wasa da Wani Abun wasa mai kara Zaina sai Dakamata tsawa take tana Kiran Anun ne Datadaina Kada abun ya Tashi Farida Daga Barci.

Suna Cikin Hakane sai ga Faridan ta Fito Daga Bedroom din Tana Mirmishi tace"Barta ta Tasheni..Daman ya kamata na Tashi nayi sallah.."suna Jin Muryanta Daga Anun din har Anan dukkansu suka yarda Abun Wasansu suka Nufeta suka Rumgume ta kamasu Tana Dariya Dayake Tafiyarsu Ta Nuna Sosai Zulaihat ce ta Dago Tana Fadin"Anun Anam kada ku kada Anty baku ganin Bata da lafiya ne.."

Farida Ta Daukesu Dukkansu Tunda Daya bazata yarda ta Dauki Daya ta barta ba,Dole ta Hada Ta Daukesu Tana Nishi ta is kan Kujera Ta zauna Zaina Tace"Allah ki daina Biye musu kina Daukansu Kada su kada ke Baki da lafiya.."


Farida na Dariya Tace"Ku kyalesu mana Sa"adiya da Zulaihat zan saka kafar wando Daku kuna Takurama ya"yana nan da Wata Biyu fa ba ganina Zasu yi ba sai dai suga su Umma Dasu Nene.."


Gabadaya Daga Zaina har Zulaihat ido suka sakamata Cikin Mamaki Zaina tace"Umma da Nene kuma..?

Farida tace"kwarai kuwa..Domin Insha Allahu Zamu Fara Shirin Tafiya Bauchi nan da wata Biyu da yardan Allah Zan je na maidake ga Marikanki kamar yadda nayi Miki Alkawari Sa"adiya Tukafin Wannan Ciwon yayi ajalina in barki Cikin Rayuwar kila wakala.."Zaina kai ta Sunkuyar sai Hawaye Zulaihat ma Jikinta Duk sai yayi Sanyi ita kanta Farida Dauriya take Mirmishin karfin Hali Tayi Tana Fadin"Me ye kuma na kuka..? Keda Zaki Farinciki..Zaki koma ma Firstlove dasu Umma Da kyautarsu Anun..Kinga Zulaihat Daukan munsu na samu nayi Sallah.."

Zulaihat ta Mike ta Daukesu ita kuma Farida ta Mike Zuwa Ciki Domin Tayi Sallah Tana Jin Gwara ta Sauke wannan Nauyin ta maida Sa"adiya Bauchi In ta Mutu bayan Haka bata bar Baya da Kura ba.

Ita kuma Zaina kitchen ta Shige Tana kuka haka kurum Take jin Wani kewa da wani abu Data batasan Ko miyeshi ba na kewar Farida da Tunanin me Zataje Bauchi Da Tarar..? Firstlove ya auri Dina..? Ta Haihu..? Me ya Faru bayan Tatafi..? Duka wadanan Amasoshin Suna sakata Fargaba da Faduwar gaba.









*Janafty...*
8/7/21, 10:28 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B22️⃣5️⃣*

*IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*


*BAUCHI..*

"Achan Bauchi kuwa an Tashi Da Hatsaniyar Biki aranar Asabar din Duka Gidajen Biyu suna Cike da jama"a yan"uwa da abokan arzuka Gidan Abba nan Amarya da Tawagarta suke Taronsu a Shashen Dina su Umma kuma suna Shashensu suna nasu Taron tare dasu Mama Safiya da wasu Daga cikin Danginta da Su Mom Iklima.

Su Inna Rukayyah kuwa da Inna Hannatu Harda Goggo Halima su manya ne Suna Gidan Alhaji Tsoho suna nasu Sha"anin Tare da yan katsina Sauran Danginsu Hajiya mama kowa ka gani Fuska Cike da Annuri da Farinciki wanda Rabonsu da irin Wannan Farinciki sun Ma Manta sai gsshi da suka Fauwala ma Allah komai suka Dauki Kaddaransu komai yazo ya wuce kamar bai Faru ba.

Haddir Ango baya Tare da kowani Aboki sai Sadiq Babba Duk da yana kaninsa Shi ya Rufamai Baya a Hotel din da Sauran Abokan karatunsa suka kwana Shida Sadiq achan kuma sukayi wankansu suka Shirya kana Suka zo nan Gidan Alhaji Tsoho da Safe Suka bar Sauran abokan achan sai sun gama Shiryawa, Haddir ya Sanya Farar Shadda Dinkin Zamani Harda Babban Riga sai yayi amfani da Hular Dara baka da Bakin agogo da Takalmi Rufaffe baki Shima Sadiq sai yayi mai kara shima yayi irin Shigarsa yau ya Chanji Matsayin Zain wanda Da yana nan Tare zasu Zuba wannan Angon Suna Tafe suna kwalisa haka Su Hajiya Mama suka Dinga Fadi bayan su Haddir din sun Fito su Abba kuma Tun Safe suka Fita haraban Gidan ana gyara Inda Za"a Baza Dardumai Saboda Mutane masu Zuwa Daurin Aure Tunda bakin Nesa sun Taso.

Bangaran Amarya Zafeera kuwa sai wanda ya gani anyi mata Dilkan Amare Tayi kyau kamar ba ita ba Tun Safe Tayi wanka Ta Sanya Wani Leshi Cikin na akwatinta ne Wanda Mama ta bata Shi Ita ko kayan ma bata gani ba Suna Gidan Alhaji Tsoho Daman bayan an gama Daura auran Bikin Zai koma Chan Tunda chan Zasu Tafi Duka Hardasu Umma Dagachan ne Za"a Dauketa Zuwa Gidan Auranta.

Tun Safe Mai makeup din da Zainab ta Dauko Tazo ta Fara ma Amarya kwalliya su kadai ne ashashen na Dina ita ta Fita Shashensu Umma Arman Daman Wajen Nene ya kwana Zareena Tayi musu wanka Ta Shiryasu Sunci Fararan Shadda Suma Harda Arman wanda sadiq Babba ya Dinka musu in kaga Arman sai kaji kamar ka Saceshi ka Gudu Saboda kyansa Umma da Nene sukace Wlh kamar Zain yana karami ne Sadiq karami da Faruq suka Daukesu Zuwa Gidan Alhaji Tsoho Wajen Daurin Aure Dashi Arman din da Junior sai Jalal din Abinci Daman Duka aikatau suka bada Tun Safe an kawo komai Cikin Manyan Kololi Drinks kuma Tun Shekaran Jiya aka Sauke Tare da Ruwan Gora.

Lokacin da aka Gama ma Amarya Makeup sai waje ya Dau Sowa da ihun ganin yadda Tasha kyau sai kiga kaga Flash na Tashi Zafeera Duk Sonta Data Daure sai da Hawayenta Data ke Rikewa suka zobamata In Ta kalli Hagu da Damanta bata ga Ukti

27 / 37