Chapter 22 Reading Zainazain Book 2 Complete By Janafty Arewa Novels

Zainazain Book 2 Complete By Janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   22 / 37

63K to 66K   out of 108.5K words

gayamai Abunda ke Faruwa shi ya kawo Shawaran agayaran Tsohon Flat din da Iyayan Zaina suka Zauna aciki Duk da ba abunda Falt din yayi Tunda ana KulaDaahi kuma baki na sauka aciki sai dai kayan Ciki ne kawai suka Tsufa sai an sauya Wannan Shawaran Tayi ma Kowa Barin ma zain Dayaji Gwara hakan ma Alhaji Tsoho yace komai yayi Dai Shi Abba ya saka aka afitar da Duka kayan Shashin agyara a Sake sabon Fenti ya kuma Sauya wasu kayan amfanin Gidan.

Hajiya mama sai da Tayimgana kan me zai ce Abba ya Saka komai ga iyayan Dina Alhaji Tsoho yace Bakomai an Riga an Zama Daya Arman ya Hada su Har Abada ba yadda Abba zai iya Dole yabi Umarnin Alhaji Tsoho Bayan ya gaya ma su Nene suma basu da ta cewa aka Fitar da komai aka Fara gyara Cikin kwana Uku komai ya kamallah an saka Saitin kujeru Gadaje a guda Bedroom din da wasu kayan Kitchen din kana Su Umma sukayi Hajiya maimuma Jagora Taje ta gani ta Dudduba abunda babu sai saka albarka Take bayan sun Dawo ta Kira Hajiya Batula ta gayamata Komai Abba yayi komai Abunda babu kadan ne, ta gayamata ita kuma tace Zata Siya komai Tunda kwamishina ya bar kudi a Hannunta Zata Taho Ranar alhamis Tunda shi kwamishina sai Ranar jumma Zai Taho da Safe.


Dina Duk Budirin da ake yi Bata Cewa komai Ballatana Uban gayyar Allah Sarki Laila kawar Zaina Tana kiran Umma Lokaci Bayan Lokaci Taji ko an samu Wani Labari Umma tace A"a Sai addu"a Taji labarin Haihuwan Dina abakin Zainab Tana Taya Zaina Kishi yasa bata Shigo Gidan ba Bikin ba wanda aka Gayyata Tunda daura aure ne kawai sai a Mika amarya Inna Hannatu tace Bazata samu Zuwa ba wannan karon sai Inna Rukayyah wanda Zata Taho Tare da Zafeera da Shema wannan karon dai ta Hakura Zata zo ganin Gida.

Dina Kuwa Ba wanda Ta gayamawa Daman Zakiya ce konai nata kuma ga yadda suka Rabu Tama Goge lambarta basu kara Neman juna ba bata san Ina Isalinta ba Bata Labarin Halin Data Ke Ciki Ta kanta kawai take.

Ranar Laraba Inna Rukayyah suka iso...da Safe da yammah sai ga Sadiq babba ya Sauka Ya gama Defence dinsa ya Dawo Gida Gabadaya Washegari da Safe sai ga Umar Faruq ya sauka Shima yazo Hutu gida ya kara Cika sosai da Farimciki wanda basu Taba yin irin shi ba Tun bayan Faruwan lamarim Kowa yazo Arman yake Fara Tambaya Domin Suna ganin Hotunan kyakyawan yaron Hatta Kuwa da Zafeera da Shema sai da suka Dauki Arman din yaron yana da Shiga rai sosai.

Wajen La"asar sai ga jeep din kwamishina Dauke da Hajiya Batula Booth cike da kaya Bayan ita kuma bayanta Mota ne Cike da kaya ba ita kadai tazo ba ita da Kanwarta Mariya suka zo Kayan ma ba"a Shiga dasu Cikin Gidan Abba ba Shashen Da Dina Zata zauna aka Nuna musu suka sauke komai anan Hajiya maimuna tabisu Cham dasu Umma aka gaigaisa Bayan an kawo musu abinci da kayan Sha Daganan suka barsu suna kara gyara Dakunan sun saka Labulayan da kayan Kitchen din da babu sai zannuwan gado da abubuwam da ba"a rasa ba sai yaba Wajen suke Domin in ba an gayamaka ba sai kace Sabon Gini ne su Umma kuwa na Cikin Gida Cikin ya"yansu Dina na Daki ita Kadai kamar mayyah Arman na Tare dasu Faruq suna ta tuna Zaina suna kwallah da addu"an Allah ya bayyanata.









*Janafty...*
8/3/21, 5:26 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B21️⃣9️⃣*

*IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*


"Ranar da Daddare Nene ta samu Abba da mganar Kayan aure na akwati Zain bai ce komai ba Abba yace bari ya Kirashi bayan ya Daga waya ya Kirashi yace yazo Yana son ganinsa ba Jimawa sai gashi ya iso Abba ya sakashi adaki yamai Mganar Kayan Lefe Domin Nene tace bai kyautu Dina Taje gidansa ba kayan Da Zatayi Fitar Biki ba.


Zain ya karkace Baki yace ma Abba Shi bashi da kudi a hannunsa Da Zai iya Yima Dina wani Hidima Da Abba ya Tambayeshi Ina yakai kudinsa sai yaki Fada yadai ce Yana wani Shirye Shirye ne zai yi wani Abu Dasu Daganan Abba bai matsa mai sai yaji komai ba ya Dai ce ko 50k ya Bama Nene asiya mata Ko kadan ne ya fi Babu ba yadda ya iya haka ya Cire ya bama Nene ita kuma ta Kira Telansu Daman bayan Dinki Har kaya yana Saidawa Dinkakku kawai Gayamai Tayi Tana Bukatar Shadda,Da Leshi da Material,Sai atamfa guda Daya Takalmi da jaka kuma da yammah ta Fita ta Siyi harda dan kunnaye Koda ta Dawo ya aiko da kayan ta Hada ta bama Hajiya maimuna Ta Raka da ban Hakuri Cewa bayan komai ya kamallah Zain din zai yi ma Dina Lefenta Nene harda Arman ta Siya ma Riga tace Shima yaci Biki dashi.

Dina Data ga kayan Tasan Ba Zain bane ya siya koma Shine ba Domin Ransa na so ba Shiyasa bata Damu ba kamar ta sani Domin yayi alkawarin yadda Tayi Sanadiyar Farincikinsa Shima sai yayi Sanadiyar nata Bazai iya gaddama da iyayansa ba kuma ba zai iya Sakin Dina ba kamar Cin Fuska ne garesu ammh Yanan yana Wani Tsari Wlh sai Dina ta gwammace bata Aureshi ba.

Washegari karfe 11am na Safe aka Daura auran Dina da Zain kan Sadaki Dubu100 wanda Baban Kaduna ya Biya,Kwamishina yayi ma Alhaji Tsoho kara yace yazama Waliyin Amarya Daurin aure bai yi wani Taro ba a haraban Gudan aka Daura auran Daga Zain sai Haddir sai Baban kaduna da Daddyn Abuja sai kwamishina da wani abokinsa sai Alhaji Tsoho sai Sadiq da Faruq su kadai suka Shaida wannan Daurin Auran.

Tunda aka Daura Auran Zain ya Sukuyar dakai yana Jin wani Abu namai suya acikin Ransa Daman bai yi Niyyar Xuwa ba asibiti ya gudu Alhaji Tsoho ya saka Haddir yaje ya Taho Dashi Ji yayi kamar bai ma Firstlove adalci ba ace yau ta Dawo ta Iskeshi ya zama Mijin Dina Bakin Ciki haka yasa ya Tashi da Sauri Motarsa ya Fada yabar Haraban Gidan Cikin asibiti ya koma ya Shiga Office dinsa ya Zabga Tagumi yana ji kamar ya kurma Ihu Kewar Zaina da Komai nata ya Dawo mai Sabo ya Tabbatar ma kansa ya Zama Dole Dina ta Dandani Gudarta.


Achan Gidan Abba kuwa Taron ba wani karKashi ballatana wani armashi Bangaran su Umma ne Zafeera da Shema Da Zainab ma sukayi wanka sukayi kwalliya Suna Hotuna su Faruq tunda suka Tafi Gidan Alhaji Tsoho basu dawo ba,Sai su Umma Abinci ma kadan suka Dafa bada yawa ba Tunda iyakarsu kenan Bangaran Amarya Dina kam ba"a mgana Domin Tun bayan da aka Daura auranta da Zain Ta rasa Duka Natsuwarta Daman Tun da Akayi ma Arman wanka yasha Nono yana Wajen Nene itama Tayi wanka ta Sanya wani Leshi Cikin wanda Hajiya Batula tazo mata dashi.

Gashi dai yau Burinta ya Cika na mallakan Zain ammh meyasa bata Farinciki..?Meyasa Burinta ya cika acikin wannan yanayin..?Ta Tabbata Wani irin Zama ne zasu yi Tsakaninta da Zain wanda bazata Dora komai acikinsa ba har yau har Gobe Tana Son Zain kuma babu abunda ya Sauya acikin Zuciyarta In da zai karbi Tubanta da ban Hakuri da Zasu yi Zaman lafiya da kaunar juna Gefe Daya su na Renon Dansu Armaan sai dai ta san hakan bazai Taba Faruwa ba.

Tana Zaune Hajiya Batula da kanwarta Mariya suna ta Hiransu su Waled daman In suka zo suna Tare dasu Saudart ne,Hajiya maimuna kuma Tana Falo Wajen su Umma Acikin mganarsu Take jin yau za"a kaita Gidanta kuma Gobe Tare da Hajiya maimuna Zasu wuce kano Tuni Dina Taji hankalinta ya Tashi kamar ta Fashe da kuka Sai ma tashi Datayi ta Bude Kofar Tailet ta Shiga Domin bata so Hajiya Batula ta Fahimci Tana kuka.

Wajen uku saura na Rana sai ga su Faruq sun Dawo nan suka ci abinci suka zauna ana Hira Misalin 4:30pm bayan Sallar La"asar,Su Hajiya maimuna da Hajiya Batula su ka saka Dina ta sake wanka ta Shirya ta saka Mayafi ta yane kanta Inna Rukayyah ta musu Rakiya Zuwa Gidan Alhaji Tsoho Dakin Hajiya mama aka Fara kaita bayan yan Nasihu Dai dai Sauransu aka kaita wajen Alhaji Tsoho dasu Abba Fatan alheri yayi musu da saka albarka.

Sai aka bama Kwamishina Dama ya Kebe da yarsa bai ce mata komai ba illah Allah ya Zaunar da ita lafiya Daga karshe yace ta yafemai Dina ta Rumgume Kwamishina Tana kuka Shi kuma yana Lallashinta Sai gabda Mangariba suka baro Gidan Hajiya mama Tayi musu Rakiya da kara suka koma Gidan Abba wajen su Umma Hajiya maimuna ta Sake Damka Amanarta Wajen su Umma a karo na Biyu suka karba da Hannu Bibbiyu Tare da Fatan Allah ya basu ikon Rikewa.

Daganan Harda su Umma aka Dunguma Zuwa Shashen Da Dina Zata zauna Banda Zafeera Datace bazata je ba Shema ce Taje Daman Tun Dazu Hajiya Batula Ta gama Tattara Duka kayan Dina Dana Arman dakomai nata Zuwa Shashen da Zata zauna Suka gyara mata komai,Saman makeken gadonta suka Sauketa suna Mata Fatan alheri Umma Dataji Hawaye ya Taho mata Tayi Saurin Sharewa Tana Tunanin Wannan Shi ake Kira Kaddara wanda ya bar Halima Daga Gida yau ga Dina Mtsayin Matar Zain ba wanda ya Isa yaja da Ikon Allah


Basu Jima ba su Umma su kabar su Hajiya Batula nan suka koma Shashensu Nene ta Tafi da Arman Tace wajenta zai Kwana Su kuwa su Hajiya maimuna yan Nasihu ne da Shawarwari wanda Dina ta Tabbata ko Tayi amfani Dasu ba aiki zasu yi mata Tunda wanda Zatayi Domin sa yaTsaneta fiye da komai a Rayuwarsa.

Bayan Dogon Nasihan sukayi mata Sallama suka Tafi suka barta Daga ita sai Halinta sai Lokacin Dina Taji kuka yazo mata ta kwanta kan gadon Tana kuka kamar ranta zai Fita sai kuma kewar Arman Dakyar Ta iya Tashi Ta Shiga Tiolet din Dake Bedroom din Taje ta Dauro alwala tazo tayi sallar mangriba Ta nan Zaune kan Darduma Tana Tunanin makomar Rayuwarta.

A bangaran Ango Zain kuwa ba wanda ya kara ganinsa Kwamishina Gidan Alhaji Tsoho Xasu kwana sai Gobe zasu koma ,Haddir ne Daya Ga Dare yayi ya Nemi Zain din ya Lallabashi ya Rakashi Wajen Dina sai bai samu wayarsa ba Tana kashe Dole ya Hakura,Ammh Haddir bai ji Dadin hakan ba Tunda yayi ma Alhaji Tsoho alkawarin Zai kai Zain din harGida.

Dina Kuwa Nan Tayi sallar Isha"i Ta koma Ta Zauna Tana Jiran Tsammani Tun Tana saka Ran ganin Zain har ta Fidda Rai da kayan jikinta ta kwanta Tana kuka,kukan da bamai lallashinta yau dai gata amatsayin Matar Zain ammh kuma ba amfani Ta Tabbata yanzu Zain yafi kowa Tsanarta kuma yana ganin Duk Abunda ya Faru itace sila Tana wannan kukan bata san sadda Barci ya kwasheta ba Batare data Leka ko"ina ba Ballata ta Rufe wani Kofa Tana Tunanin Duk Gida ne Babu Abunda zai Faru.

Zain kuwa acikin Office dinsa yayi kwanciyarsa bayan ya kashe wayarsa Domin yasan Tabbas Kokowa bai Nemeshi ba Haddir sai ya Takuramai Shiyasa ya kashe wayarsa yayi kwanciyarsa Cikin Office dinsa yana Tunanin hakan ne kadai mafita koda garin Allah ya waye bai Damu ba Bayan ya Dawo masallacin Cikin asibiti ya Gyagice kawai ya Fara Duba Patient bai damu Daya koma Gida ba Ballatana yayi wanka yagama Tabbatar ma kansa Tunda Aka Daura mai aure da Dina Kila Sai ya kulla Zumunta da Kazanta Tunda office dinsa zai zama wajen kwanansa ne Tabbas.

Haddir sai da ya Shigo Cikin asibiti yaga Motar Zain kana Tunanin yana asibiti ma ya kawomai Daganan Office dinsa yaje Direct ganinsa da kayan Jiya ya saka ne ya Tabbatar mai da Zarginsa ganin Zain din ya Hade rai ne yasa Haddir bai mai mgana illah Allah ya Shiryeka kawai Dayace ya Kada kai Zuwa Nashi Office din Zain yabi sa da Harara Ta Gefen ido Yana Tunanin Shirin Dayake in Haddir Yaji Daga baya bazai ji Dadi ba zai ce ba Shawarcesa ba.


Chan agidan Abba kuwa Dina Datashi Da Safe ta Fahimci Zain bai Shigo Barayinta ba batayi wani mamaki ba Tatashi Bayan Tayi sallar asuba Tayi wanka Sai Lokacin Ta Zagaya Flat din yayi daidai na Misali ammh yadda ta Tsara rayuwarta Da Zain bata Tsammaci Zata kareta awannan karamin Shashen ba,sai dai bata da yadda Zatayi Tunda ita kam Cikar Burin nata ga yadda yazo mata bata iya Tsinana ma kanta komai ba,Damuwarta Arman Nononsa nata Zuba alamun yana Chan yana Rigima Duk ta damu Falo ta Fito Ta zauna Tana ji kamar ta Tafi Shashensu Umma sai ga Zafeera da Shema suna Dauke Da kayan Breakfast sai kuma Arman Dayake kuka.

Tana ganinsu Dauke dashi Ta Mike Cikin Rawan Jiki ta karbeshi,Ta Rumgumeshi Tana Sauke Numfashi Shima yasan Dumin Jikin Mamarsa,Zafeera da Shema suka kalli Juna ganin Dina ta Zauna tana Fito da Nono Arman ya karba har yana Sauke ajuyar Zuciya sai kuma,ya basu Tsausayi Domin jiya Cikin Dare ya Tashi yana ta kuka Nene bata samu Barci ba Shine yanzu akace su kawosa.

Sudan Zauna kadan Zafeera sai kallon Kofar Bedroom din Take wai Taji koda alamun mutun sai dai Daga Dukkan alamu ba kowa kana suka yi mata sallama suka Tafi Bayan Dina ta gama Bama Arman Nono sai yayi Barci taje ta kwantar Dashi Tazo ta karya Tea kadai tasha sai Kwai Dataci da Buredi,Daganan ta kwashe komai Zuwa saman Dining ta koma Ta Zauna Tana Cigaba da Saka da warwara Tana Tuna Irkn Amintar Dake Tsakaninta da Zakiya kamar ta Kirata sai wata Zuciyar ta Hanata Tuna irin Rashin Mutumcun da Zakiya ta aikata mata.


Wajen karfe 10am na Safe sai gasu Hajiya Batula dukkansu Sunyi wankansu Dasu Waled sai Shirin Tafiya Hajiya maimuna na Shashen su Umma,jin yanzu Zasu Tafi ya saka Jikin Dina ya karayin Sanyi ta Dauko mayafinta Da Arman Zuwa Shaahensu Umma Domin suyi sallama Tunda Sai sun Biya Gidan Alhaji Tsoho Ta Chan zasu Wuce.

Hajiya maimuna Saboda Sabon Zama dasu Umma Harda Hawayenta Su kansu su Umma sun ji Dabam Sun hadamata Turaman atamfa Abba ya bata kudi 5k da Farko taki karba sai da Su Umma suka matsa mata Anyi sallama Cikin Sabo da Mutumtawa Dina itama Tayi kukan Tafiyar Hajiya maimuna ammh Bata da yarda Zatayi Tana ji Tana gani Suka Shisshiga Mota suka Fita Daga Haraban Gidan Ita kanta Hajiya maimuna Tayi kuka ta Dauki Arman Tana ta sakamai albarka tace Zuwa Sati mai Zuwa Zata Tafi Sudan.


Dina Shashenta ta koma Tana ta kuka Shi kanshi Arman kuka yake Dina Tana kukan wani abu Guda Daya na Rashin Sanin Tabbas kan wannan Rayuwar Data Sako kanta aciki Sai taji kamar Tabi Hajiya maimuna su koma Sudan Tare ammh Soyayyar Zain fa..? Taya zata iya Rayuwa batare dashi ba..? Ammh ai Shi bai Shirya Rayuwa da ita ba asali ms ya Tsaneta kuka kawai take bamai Lallashinta Daga Karshe ta Rumgume Arman Tana kuka Domin ahalin yanzu Shi kadai ne nata.

Achan Gidan Alhaji Tsoho bayan Sallama da Fatan alheri Da Godiya daya Biyo baya Sai Alhaji Tsoho yace Baban Kaduna ya Kira Zain awaya yace yazo yayi sallama da Surukansa Daya Kirasa bai Daga ba sai ya Kira Haddir shima bai Dauka ba sai da ya kara Kira ya Daga ya gayamai Sakon Alhaji Tsoho koda Haddir yaje Office din Zain Ya gayamai Sakon Murje ido yayi yace ba inda Zashi yana kan aiki ne Haddir fa ya Fara Tsinkewa da Lamarin Zain Dole ya Kira Baban kaduna ya Zabga mai Karya Cewa Aiki yayi ma Zain din yawa ammh In yayi Sauki Zai zo.

Da Alhaji Tsoho yaji haka bai Damu ba Kwamishina ma bai Damu ba yace bakomai,Hajiya maimuna ne taso Ta gansa Kafin Tatafi sai dai ta Fahimci baya son Haduwar Tasu Har Bakin Mota Hajiya Mama da Inna Rukayyah suka Rakasu dasu Abba bayan sunyi hannu da kwamishina yana yi musu Godiya Kamar ya kwanta musu Kafin ya Shiga Mota Jifa Jifan Guda 2 suka bar Haraban Gidan kana su Abba suka koma Cikin Gidan suna kara Tattaunawa Abubuwan da suka Faru Alhaji Tsoho na kara Nusar dasu yarda da Hakuri Komai sai ya Wuce batare da an sani ba.

Alhaji Tsoho yayi amfani da wannan Damar yace Gobe kafin su koma bakin aikinsu yana son yayi Wata mgana dasu sukace Shikenan Allah yakai musu Rai.

Kamar yadda ya Faru yau din ma Wasan buya akayi Tsakanin Zain da Haddir bai yadda sun kara Haduwa ba sai Washegari da Safe Dayazo Gidan Abba Shima yaje gaida su Umma ya bar su Abba agidan Alhaji Tsoho suna Kara sallama dasu Baban kaduna Hatta dasu Umma sun san Zain baya kwana agidan sai dai wannan karon basu da Hurumin cewa komai wanka yazo yayi ya Sauya kaya Da Suka Hadu da Haddir Fuska ya Hade bai ma bashi Damar wata mgana ba Sauri Sauri ya kara Ficewa Daga Gidam Ko Barayin Shashen Dina bai kallah ba Duk da yayi kewar Arman yaso ya aiki Zareena taje ta Daukomai sai yaga suna aikin Share Sharen Dakin da Dina Ta Zauna Shiyasa kawai ya Wuce abunsa.

Aranar Inna Rukayyah Ta koma kano tabar Shema da Zafeera Zuwa Sati mai Zuwa Zasu Dawo Daddyn Abuja da Baban kaduna suma sun koma Cike da Farincikin Gudurun Alhaji Tsoho kan ya"yansu hakika yayi Tunani mai kyau kuma Dukkansu suna Maraba da Wannan Hadin Tunda sun Lura Duka ya"yan nasu so suke sai Sun Zama Tazurai ba aure Batare da sun gayama Kowa ba su kayi Shuru da bakinsu sai Lokaci yayi Ko Hajiya Mama Alhaji Tsoho bai sanar mawa ba Ya bari sai Lokaci yayi Tukunnah.


Allah Sarki Rayuwa Dina Tana ganin Rayuwa Domin har yau Datake Sati Daya da Aure bata saka Zain acikin idanuwanta ba Tayi kuka har ta gaji,Tadai san Kwana Hudu da auransu Zainab Tazo ta Dauki Arman tace ya Dakta ya aikota Daganan Ranar kullum da Safe in yazo Gida yin wanka ya Sauya kaya kafin ya koma Cikin asibiti sai ya aika a Daukomai Arman ya gansa Hatta Abba ya Fahimci Zain baya kwana a Shashen Dina ammh bai

22 / 37