Chapter 33 Reading Zainazain Book 2 Complete By Janafty Arewa Novels

Zainazain Book 2 Complete By Janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   33 / 37

96K to 99K   out of 108.5K words

Duka Damuwarsa ta kare yana Gidan Haddir yazo suka Tafi Gidansa Dashi bai Dade ba ya Tafi bayan yayi ma Zafeeran Nasiha a matsayinshi na yayanta Sai yammah ya koma Gida yau din ma sai da Abba yayi da Gaske ya bar Shashensu Umma ya koma Shshensu yana Manne da zaina kamar wani xai kwaceta ita dasu Anun Dina kuwa sai dai Hakuri Domin ta zama yar kallo.

Washegari kuwa Tun Safe Zain ya kwashi Zaina suka koma Gidansu yace basai an Rakata ba baya Bukata Umma taso ta hana Abba yace ya Dauketa suje ai matarsa ne Dina Kuwa tana Shashenta Tana kuka Kukan Nadama da Rabuwa da Masoyi Domin tasani ita da Zain sai kallo Daga nesa Ganin yadda yake wani Rawan kafa ne Nene ta karbi su Zaina tace gobe za"a kawosu.

Fadin irin Soyayyah mai Hade da kaunar da Zaina da zain suka Nuna ma juna bata Baki ne kuma sai na Cika wannan littafin ban gamashi ba mai karatu kadai zai iya Hasashen Abun Tanimu megadi Daya ga Zaina Har sai da yayi kwallar Farinciki addu"a kuwa tashashi kamar ya goyata Ranar Akan gadon Auransu Da suka Dade basu Haushi ba sun Hau shi kuma Sun Raya sunnar Ma"aiki sosai Gyaran da akayi ma zaina sun kara Taimakawa wajen Fitar da Zain Daga Hayyacinsa ya Dinga Sambatu Da kukan Don Allah kada ta kara Barinsa Ssi da Tagaji ta Rufemai baki kana yayi Shuru.

Sallah kadai ke Fitar da Zain Daga Gidan Tunda ya Dawo bai Taka yaje ko"ina ba basu kara Fita ba sai da sukayi Sati Daya Cur kana suka zo gidan Abba Shima Dalilin Rasuwar Kakar Dina achan Sudan Wanda kwamishina ya kira Zain ya Rokeshi ya bar Dina su Tafi saboda Taga Danginta na chan Shine Dalilin Zuwan nasu kowa ya gansu sai ya kara kallonsu Saboda kyan da sukayi Zain Tuni Zaina ta saka ya aske wannan gashin bakin da Sajen yayi kiba ya Fara maida Jikinsa Su Anun Kuwa Daman yaye su kawai Nene da Umma sukayi suka Hada da Arman ganin yaran basu da Rigima Iyayansu na chan na cin Amarci Koda Zain yazo ya gayama su Abba Rokon kwamishina Abba yace Shima ya kirashi ya gayamai Alhaji Tsoho ma yace Ya barta Tatafi Taga Danginta Zain bai Damu ba yace Allah ya kiyaye Hanya.

Zaina Da kanta ta Shiga Har Shashen Dina suka gaisa Tayi mata gaisuwa ta amsa Tana Sharan kwallah ga Cikinta ya girma Domin ya Shiga watansa na Bakwai sai Ta bama Zaina Tsausayi Domin har Fada sukayi da Zain akanta Kan tamai mgana ku Dubata ya Rika Zuwa yanayi ammh yace Kada ta karamai mgana babu Ruwanta,Dole ta Kyaleshi tunda Haka ya zama Sai yau Zain ya Taba Yin mgana Datafi Daya da Dina Bayan yayi mata gaisuwa kuma yace ta Shirya Gobe Babanta zai aiko da Direba ya Dauketa ta Chan kano Zasu tashi Zuwa Chan Sudan din ya kuma bata kudi 100k yace ta Rike a Hannunta Dina taji mamaki Sosai sai ta Danganta hakan da Dawowar Zaina Bata san Cewa kawai yayi Ra"ayi bane ganin Zataje ganin Danginta ya kamata ya Fita Hakkinta.

Washegari Kwamishina ya aiko da Direba aka Tafi da Dina bayan Tayi ma su Umma sallama Arman wajen Nene ta barsu suka Rabu kan in ta isa Zata kirasu ta Hadasu da Hajiya Maimuna suyi mata gaisuwa Har Motarsu Ta bar Haraban Gidan suna mata Fatan Allah ya kiyaye Hanya Ta Dauki kaya da dan yawa Tunda zata kwana Biyu achan Taga Dangi Domin ta Dade bata je ba,Koda Tatafi Zain bama zo ba sai da yammah Suka zo shi da Zaina Saboda Tafiyar Zareena Gobe da Zuwan Jawaad wanda nan zai kwana Gobe zasu hau Jirgi Zuwa Lagos ta chan zasi tashi Zafeera ma agoben Haddir zai maidata makaranta Shiyasa suka zo Gidan Abba sukayi sallama da Zarrena nan suka iske ma Zafeera Tazo sallama dasu Umma tare suka Fita Zuwa Gidan Alhaji Tsoho sai Dare kowanne ya Dauki Matarsa Zuwa Gida Su Anun dai suna Wajensu Umma Zain Dayaji An yayesu Sai da yayi Fada wai sun yi yara dayawa Umma tace Kaniyarsa ai da ya Dauki Matarsa bai Tuna da yaran ba sai Lokacin yaji kunya.

Zareena sun Tafi hakama Zafeera Haddir ya maidata har kano Gidan Inna Rukayyah Sallaman kauna yasa nan ya kwana sai Washegari ya dawo Gidan Abba ya Rage Daga Zainab sai Zulaihat da Farida Duk kuma sai sukaji kewa Domin Sadiq ma ya samu aiki a kamfaninsu Abba Faruq kuma sati mai zuwa zasu koma makaranta Shida Sadiq karami,Zain kuma da Zaina suna Gidansu suna Cin Soyayyarsu sai da Zain yayi Da gaske ya koma Bakin aiki Kamar dai Baya kafin ya Duba Patient Goma sunyi mgana yafi sau Biya Suna Tambayan Lafiyan Juna Dina kuma Bayan sun isa sudan ta Kira Umma sun yi mgana da Hajiya maimuna sun mata gaisuwa har Abba ma ya gaisa dasu Ta kuma Kira Hajiya Mama ita da Alhaji Tsoho suksyi musu Ta"aziya.
Shine zaina ta matsamai sai da ya Karbi Lambar Dina ya kira Yayi mata gaisuwa kuma Ya bama Zaina ita tayi mata Bayan sun yima Hajiya maimuna Tana Ta godiya da saka albarka Tana kuma yima Zain barka da arziki Da dawoewar Zaina ya amsa baki har Kunni Dina Ta Fara Tunanin Lalle Zaina itace komai na Zaim Tunda Dalilimta yau har yana Kira yayi mata gaisuwa Ita Da Hajiya Batula dasu Waleeda da Kwamishina suka Taho Sudan dim ammh Su zasu Dawo su barta sai Tayi wata Daya Dayake daman Duka Dangi An gaya musi Dina tayi aure har wasu na Fadan ba"a gaya musu ba banda Kakar Dinan Data rasu ba Wamda yasan Abunda ya Faru Shiyasa koda suka ganta da Ciki basu Damu ba.


Bayan Sati Biyu da Tafiyar Dina Farida ta Fara Tunanin Gida da Cin Dacin Rayuwar Data gudanar Ta Farajin Zata iya komawa Gida Domin Taga ya"yanta da Iyayenta Alhaji Badamasi yanzu tama Daina Daga Kiransa Uwar Mata kuma bata kara nemanta ba Tana Jiran Ta Dawo da kanta kamar yarda Boka yayi mata karya Farida Sai ta Wuni kuka Cikin Damuwa duk su Umma Na lura da ita ana Jira ta Furta Damuwar da kanta sai gashi ta samu Umma tana kuka Tana gayamata Tana son ta koma Gida Cikin jin Dadi Umma tagayama Abba Shi kuma ya gayama Alhaji Tsoho wanda ya bada Umarnin ashirya Tafiya Gombe cikin Lokaci kuma Hardashi zai Tafi Duk da ya Dade bai yi Tafiyar Mota ba.

Da zaina taji Labari tafi Kowa Murna Zain shi ya Tsara Tafiyan Ranar asabar Saboda aikinsu,Duka Gidan zasu Tafi Yara ne kadai za"a barsu wajen Hajiya Mama da Tabawa Ranar Jumma'a Su Faruq jirginsu ya Tsshi a Lagos Ranar asabar da Safe kuma Tun Misalin karfe 8:39am na safe suka Dauki Hanyar gombe,Motar Abba da Direban ke Tukasu Abba ne agaba sai Alhaji Tsoho saboda kafarsa kada ya matsu.

Motar Zain kuma Zaina da Farida Da Zulaihat sai Nene da su Anun Da Arman Motar Haddir kuma Umma da Zainab da Sadiq sai Anan Dake barci ajikinta Suka Dauki Hanyar Gombe su Baban Kaduna duk sun san da Tafiyar sun bisu da Allah ya kiyye Hanya sun yi Gudu Bisa Hanya Wajen 12pm na Rana suka Shigo garin Gombe Lokacin Tuni Farida ta Fara kuka ganinta a garin Data Fidda rai da Dawowa garinn Lokaci Daya Abubuwa Dadama suna Dawomata kamar yanzu Abun ke Faruwa.




*Kuyi hakuri Ban cika alkawari ba..Wlh Bamu da wuta bana da Chaji wannan Ma dana samu bashi da yawa ammh da Zarar na samu Chaji Zaku kara jina da yardan Allah..*




*Shakira...*
8/12/21, 8:31 AM - Buhainat😝: *ZZ...B22️⃣9️⃣*

*IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*


"Farida ita ta Dinga yin kwantace har kofar gidansu wanda Motarsu ce agaba sai tasu Alhaji Tsoho na Biye dasu abaya.

Farida Tayi matukar mamakin ganin yadda gidansu ya koma Duk da abaya tasan suna da Rufin asirin Allah ammh Yadda Gidan nasu ya koma ya bata mamaki an kara Fadadashi an karamai Girma an Sauya tsarin get din Gidan Daga karami Zuwa Babba Da farko ta Fara Tunanin,kilama ba gidan bane sai da ta kwankwansa get din Sabon megadin ya leko suka gaisa Data gansa sai Jikinta ya karayin Sanyin Tambayarsa Tayi Sunan Mahaifinta ko nan ne gidan yace mata Eh bai yi gaddaman bude mata get ba Ganin yadda take diban kama Sosai da Alhaji Duk da bai Taba ganinta ba ya Tabbata tana da alaqa da ahalin Gidan

Get ya Bude musu suka Sulala Da Motocinsu Zuwa Haraban Gidan Farida bin Ko"ina na Gidan da Kallo Tana ganin yadda aka gyara komai na Gidan ba yadda Tatafi ta barsa ba,Firftowa sukayi Daga Mota Har da Alhaji Tsoho yana Dogara Sandar sa Farida na Tsaye ta kasa shiga Hawaye kawai take Sharewa Umma ce ke Lallashinta da bata kwarin Gwiwa Har ta samu Damar Fara Tafiya Tana tunkaran Kofar da Sadasu da Cikin Gidan Duk da itama an sauyata wannan Chanjin da Farida Ta gani haka kawai yake sata Faduwar gaba.

Tura Kofar Falon Farida Tayi Bakinta Dauke da sallama Cikin Rawan Murya su Umma na Binta abaya su Mazan sun Tsaya Daga waje Tukunnah,Suna Shiga Babban Falon babu kowa Tsit kamar ba Motsin Mutane Sai dai Falon ya kawatu da Kayan More Rayuwa Farida sai Bin Ko"ina da kallo Take Tana jin kodai Tayi kuskure su Mami sun Tashi Daga wannan Gidan ne bata sani ba..? Bata samu amsarta ba Wata yarinya da bazata wuce Shekara Biyu da Rabi ba Ta Fito Daga wani Daki Dauke da Teddy a Hannunta Tundaga Nesa Farida ta sakarmata Ido Tana kallonta Cikin wani yanayi kamar yadda Itama yarinya ta Lura dasu ta tsaya Tana kallonsu Farida hawayenta sun kara gudana wanne dai ba Hassana bace kuma ba Usaina bace Domin yanzu sun fi haka girma To wacece..? Duk yadda akayi Ahalinsu ne domin Taga Tsananin kamarsu da Zahra sai dai Tafi Zahra Haske da Kuma Dogon Hanci.

Yarinyar ganin Bakin Fuskokin da bata sani ba sannan kuma Taga Farida Wacce Maminta ke yawan nuna mata ita a Hoto Sai Taji Tsoro ta Ruga Zata koma Daki Tana Kiran Mama mama Anty..! Haka take Fadi karaf suka ci karo da Anty Yaha ta Fito Daga Dauke da Karamin Kofi a Hannunta Tana Fadin'"Aisha Farida taho ki karishe shan T..."mganarta ta makalene da karon da sukayi da yarinyar Har da ta kusa barar da Tea din Dake hannunta Cikin Fada tace"Kinga gani ko..? Kirika Tafiya ahankali mai Sunanki Tana da Natsuwa da Hankali"

Tafada tana Dan Mirmishi bata ma Lura da su Umma Dake tsaye ba Farida kuwa Tana kallon Anty Yaha tana Jin wani kuka na Tsso mata sai ta saka Mayafinta Tana Toshe bakinta Yarinyar ta Dago Daga Jikin Anty Yaha Tana Nuna mata Farida Tana Fadin"Mama..Anty ce.."Tafada Tana nuna Mata saitin su Farida Anty yaha ta Dago da kanta karaf suka Hada Four Eyes da Farida ai sai ta zabura Taja baya Lokaci Daya Tana Sakin Kofin Dake hannunta Tea din ya Bare sai da Yarinyar ta Tsorata taja baya Cikin Tafiyar Mamaki da wani Rashin Kuzari Anty Yaha ke Tafiya Tana Nuna Hannunta kan Farida baki na rawa tana Fadin.

"Ais...Aisha...Fa...Farida....!

Take Fada da son Tabbatarwa Aisha Farida Da Kewar Gida da komai na Rayuwarta ya Dabaibaye Rayuwarta yasa bata san sadda ta kwashi Gudu ta Fada Jikin Anty Yaha Tana Fadin"Anty...Anty..Nice.."Take Fada Tana wani irin kuka da wani Wawan Rumguma Ta Rumgumeta Tana Fashewa da kuka Kamar Wasu kananan yara Anty Yaha Fadi take"Ina kika Shiga Farida..? Wata Duniya kika Shiga muna ta nemanki kika barmu Cikin kewa?

Haka Take Fadi Tana wani irin kuka Itama Faridan kukan take Zaina Dake gefe sai Sharan kwallah take,Daga bayansu Suka ji ance Cikin wata irin Murya mai Cike da Rauni"Da gaske ne Aishata ce ta dawo Gida..? Kokuwa dai mafarkin dana Sabayi ne..?

Ko a mafarki Farida Taji wannan muryan zata shaidata Muryan Mami ce Cikin Sagewar murya Ta Dago kanta sai Cikin na Mami Dake Tsaye Daga Kofar Daki Kallon Farko zakayi mata kasan cewa ta Rame ta lalace Tayi baki kamar ma bata da Lafiya Farida Taji gwiwanta ya Sage kamar An Jona mata wani Abu Kukanta yana kara karuwa Cikin wani Fitan Hayyaci ta Furta.."Mami na...! Kafin ta Zura da gudu Zuwa gareta ta Fada Jikinta Ta saki wani marayan kuka Mami ta Rike Farida Tana Sharan kwallah take Fadin"Ashe da Rabon zam sake ganinki na nemi gafaranki kafin Allah ya Dauki Raina.? Ki yafemin Farida a matsayina na uwa Ki yafemin Ban Dube ki nayi miki kallon yarinya mai natsuwa ba na jefeki da kalmar da bata dace dake ba da kalmar da wasu sukayi amfani wajen bata Miki suna Ki yafemin Farida wlh Tallahi Tunda kika bar Gidan nan banta Barci Cikin kwanciyr Hankali ba Aisha ki yafemin..'

Mami Take Fada tana wani kuka Farida Ta kukan Mami ya Dauketa nata Ta Dago Tana Share ma Mami Hawayenta Tana Fadin"Mami ki daina kuka..Nice yakamata na Roki gafaranku baku ba.."Take Fada Tana kuka Anty yaha nata Sharan kwallah sai Lokacin Ta Lura da su Umma baki ta Rike Tana Fadin"Kai.Aisha Farida Tare kike da baki baki mgana ba..?

Tafada Tana goge Hawayenta Sai Lokacin Farida Ta Tuna dasu Umma ta waigo Tana Fadin"Don Allah Umma kuyi hakuri ku kariso..Anty Harda Maza suna Waje Fa ina Abba yake..?

Anty Yaha ta kalli Mami itama ta kalleta Sai Anty Yaha tayi Saurin Kauda Zencen da Fadin"Kuma kika barsu a waje..? Maza ki Shigo Dasu.."Tafada Tana Komawa Daki ta Dauko mayafi ta Dauki ma Mami ta kamata zuwa kan kujera su Umma ma duk sun zauna suka Fara gaisawa dasu Mami Sai ga Farida ta Shigo dasu Zain Alhaji ne Agaba Da dan Sandansa yana Dogarawa sai Abba da Haddir da Zain sai Sadiq Dake rike da Arman Zain kuma yana Dauke da Anan Haddir ya Dauki Anun.

Alhaji Tsoho da Abba suka zauna kan kujera su Zain kuma suka samu kasa suka Zauna Aka Fara gaisuwa Anty yaha ta mike Zuwa Kitchen ta Dauko musu Lemo da Ruwa Kana ta koma Daki Ta daga waya ta Kira Goggo Zaliha ta gayamata Dawowar Farida Bayan ita Baffa Umaru ta kira ta gayamai Sai ta Kira Musbahu ta Fadamai ga Farida ta Dawo Gida da wasu Mutane yana jin Haka sai da yayi Sujidun Shkuran na Godiya ga Allah yace Jirgi zasu Taso Daga Abuja Zuwa Gombe da yardan Allah.

Farida na Kusa da Mami sai kuka Take Yarinyar Dazu Dake Makale Gefe Farida ta kallah Tana Fadin"Mami wannan yarinyar fa..! Banga Abba ba ina Zahra kuma..?

Anty Yaha Dake Fitowa Daga Daki Tace"Zahra Tayi aure a kano..Wannan Diyar ta ta Farko kenan Sunanki taci Aisha Farida sai kaninta Mai sunan Abbanku....'Farida taji hawaye ya Tarun mata haka suma su Mami ke ta Sharan Kwallah ta Kira Takwaranta tazo ta Rumgumeta Tana ta kuka Kamar ta santa ta ko Nane ajikinta Tana kallon Bakin Fuskoki.

Girki AntyYaha tatafi Kitchen Ta Dora kafin isowar su Goggo Zaliha Zahra ta kirata bata sameta ba sai dai ta kira Mijinta ta Sanar dashi Komai Zahra Take ta bari tazo Gida Aisha Farida ta Dawo Taliya da Kifi Sharp Sharp Anty Yaha ta Dafa musu ta Zubo akololi tazo ta Kawo Ta ijiye su Umma nata mata Sannu Alhaji Tsoho ne ya gyara zama yana Fadin"Ina shi Mahaifin Faridan..? Ina son ganinsa kafin Duka bayanan su Biyo baya..'

Mami Sunkuyar Dakai Tayi Tana Kuka,Sai Anty Yaha ce Dake Sharan kwallah da Haban gyalenta Tace"Allah yayi masa Rasuwa yau wata bakwai kenan.."Gabadaya aka saka Salati Farida kuwa mikewa Tayi Jiki na rawa Hannu Dafe Kirji Tana Fadin"Abba ya Rasu..? Na shiga uku ni Farida Abba ya Rasu yana Fushi dani bai yafemin ba..?

Take Fada tana wani Gunjin kuka Mami ta kamata ta Rumgumeta suna Cigaba da kukan Tare Abba ya Girgiza kai yana Fadin"Allah ya Jikansa da Gafara.."Su Umma suka amsa da Ameen Alhaji Tsoho kuma Shuru yayi kafin yace"Allah ya jikansa Allah yamai Rahma.."Anty Yaha ta amsa da Ameen Ameen tana kuka ta Cigaba da Fadin"Ya rasu da sunan Ki Farida abakinsa..Ya Rasu yana ambaton ki yafemai yayi kuskuran yanke hukunci ba Bincike ya Rasu da kewarki da son ganinki.."Ba Farida kadai ba Hatta su Umma sai da sukaji Taruwar kwallah Tuni Mutuwat ta Dawo sabuwa su Mami sai Kuka suke Su Umma na basu Hakuri ammh kamar suna kara Zugasu ne sai da Alhaji Tsoho yayi ta musu Nasiha kana suka Tsaigata Cikin Muryan Data Dakushe Mami ta kalli Anty Yaha Tana Fadin"Kin kira Goggonsu Zaliha kuwa Antynsu..?

Anty Yaha tace"Eh na kirata na kira Baffa Umaru ma na gayamai Ban samu Zahra ba ammh na kira Mijinta na gayamai nace Farida ta Dawo Gida.."Mami na Sharan kwallah tace"Musbahu fa..? Farida ta Dago Daga kukan Datake tana kallonsu Mami Anty Yaha tace"Shima na Kirasa yace yanzu Zasu biyo Jirgi Zuwa nan din.."Mami ta kada kai Tana Fadin"Allah ya kawo su Lafiya Don Allah ku dan jinkirta Iyayan nata su zo..Naga kamar Daga waje mai Nisa kuke..!

Zain ne yace"Bakomai sai mu jira...Daga Bauchi muke..! Anty Yaha tace"Allah Sarki ashe duk tsawon wannan Lokacin kina Bauchi Aishafarida..? Farida na Kuka Tayi Mirmishi tace"Bana Bauchi Ina Zaria duk Tsawon wannan Shekarun..!

Mami ta kalleta Cikin Raunin murya tace"Zaria kuma Farida..? Farida na wani irin kuka tace"Eh Mami Labari ne mai Tsawo sai mun zauna Zan gaya muku irin Rayuwar Dana Tsinci kaina Bayan barina Gida.."Kawai sai ta kara sakin kuka Zaina ma Sharan kwallah take Ita da zulaihat Zain ne ya Miko mata Anan Da tafara kuka Yace ta bata Nono sai ta Dauke ta Ta Dago Tana kallon Farida Tana Fadin"Anty Farida ina so nayi sallah.."

Tafada Bata so ta ba Ma Anan Nono gabansu su Abba kunya Take ji Haddir ya Duba agogon Fatan Dake hannunsa yana Fadin"12:40pm kai Lokacin Sallah ai yayi muma ya kamata mu yita kan Lokaci.."Alhaji Tsoho yace"Tabbas hakane Zamu yi sallah.."Anty Yaha ta Mike Tana Fadin"Bari na Bude muku Shashin Baki sai kuje chan kuyi sallah kafin Lokacin nasan sun Kariso.."Abba yace"Ba laifi.

Daki Taje ta Dauko key din Shashen Bakin ta Bude musu Alhaji Tsoho yace Jam"i zasu ja Bayan kowa yayi alwalansa

33 / 37