Author : Jamila Janafty Category : Romantic Hausa Novels
na Binsa abaya Gidan Alhaji Tsoho suka yada Zango Haddir yagayamai Komai Shi kanshi Alhaji Tsohon kallo ZAIN kawai yake Cikin Halin Tsausayamai Domin yasani Tabbas ya Fada Wata Jarabawa mai yunwar Dauka Da kuma Halin kakani kanin Rayuwa.
Ita Kanta Hajiya Mama sai da Tayi ma Zain din kwallah Tana kallonshi Duk ya zama wani iri Ya koma wani Shuru shuru baya mgana yanzu ma da suke gaban Alhaji Tsoho Kansa na kasa Baya cewa komai Alhaji Tsoho sai Nasiha yake tamai Nasiha yana gayamai ya Dage da addu"a suma iyayansa zasu Tayashi Insha Allahu Halima Zata Dawo Gida Cikin Koshin Lafiya ita da Abun ke Cikinta da wannan Kalaman ya Saussauta zuciyar Zain Yaji Jikinsa ya karayin Sanyi sosai Bai Bar Gidan ba sai da Hajiya Mama ta matsamai yaci abinci Kana ya Tafi bai Isa Gida ba sai da yayi sallar La"asar a massallaci.
Ranar Wuni yayi Cikin Daki Yana Kallon Hoton Zaina yana Kananun kuka,Rayuwa gabadaya ta juya mai baya Umma da Nene suka jisa shuru suka Shiga Dakin Suna ta Lallashinsa Hakama Abba Daya Dawo Domin yanzu Zain Shine Abun Tsausayi,Hatta dasu Baban kaduna dasu Daddyn Abuja Kullum Cikin Kiran waya suke Tambayan ya ake ciki,Hakama su Inna Hannatu Kowa yana ta addu"an Allah ya bayyana Halima Cikin Koshin Lafiya.
Nasihun Iyayansa da kuma Damuwarsa akansa yasa ya saki,Domim ayanzu baya iya yi musu Gaddama yana ganin Bayansu bashi da Kowa,Abaya ya Saba musu ammh ayanzu Bazai iya yi musu gaddama ba Komai suka ce Toh kawai yake Cewa.
Haka Rayuwa Ta Cigaba da Gudana Da Dadi ba dadi,Zain Tundaga Ranar bai kara Fita Neman Zaina ba ya koma yana Wuni Cikin asibiti sai Dare yake Dawowa Saboda zaman asibitin ya fiyemai kwanciyar Hankali akan yazo ya zauna agida sai Tunani kawai da zai Tayi ammh Aikin yana Debemai kewa,ammh kuma Duk da haka bai zauna haka ba yabi masallatai Na garin Bauchi Ya kai Kokensa kan atayashi Addu"a Allah ya bayyana Zaina kullum kuma bayan ya Tashi aiki sai ya Biya bakin kasuwa ko Tasha yayi ma masu Bara Sadaka,Yayi Tsawalli da wannan Sadakan Allah ya bayyana masa Halima yasa Tana Hannu nagari,Alokacin in kaga Zain ya koma wani Gayinan kamar bashi ba,Baya aski Duk yayi Gemu Buzu Buzu ba wani gyara kai sai dai kawai ya saka kaya Fita Zuwa asibiti
Bangaran Dina Kuwa sai dai gani Daga nesa,Domin Aduniyanan Ba wacce ya Tsana irinta Ko kallon arziki bata samu Daga barayinsa in Yana kallonta da wannan Cikin ji yake ksmar ya shaketa ta Mutu,Ita kanta Dinar ta Fahimci Haka Tsskaninta Dashi Daga Nesa ne sai dai in zai Fita Ta Rika lekasa ta Kofa Tana Kukan Soyayyarsa Dake kasan Ranta Gashi Zakiya bata kara Zuwa ba Tun Koran da Nene tayi mata,Sai dai suyi mgana awaya kuma ko Ta gayamata Hakuri Take bata ita kuma ta gaji Gaskiya ta Kosa ta Haihu a Daura musu aure ta Huta,Gashi Cikinta yana Cikin Watansa na Biyar ne ya Girma gashi nan ya Bayyana yanzu Ta Rage iskancinta ganin Bame bin ta kanta Dole ta kama kanta,Nene ne ta Mata dan Abunda Ba"a rasa ba.
Mganar awon Dina kuma Alhaji Tsoho yace Haddir zai Dinga Zuwa Gida yana Duba Lafiyarta Ita da Abunda ke Cikinta Tunda dai Fitar Kamar wani Tonon asiri ne Dina bata so ba Taso Zain za"ace ya Dinga Dubata Abunda bata sani ba Ahalin da Zain yake Ciki inda zaa"a bashi Wuka Da Dina zai Fara yankawa Saboda Tsabar Tsanar da yayi mata yana ganin Duk itace Silam Komai itace Silan da yau aka wayi gari Firstlove bata Tare dashi Shi kuwa har wani kyalli Dina zatayi a wajensa yayi alkawarin bazai karayima iyayansa Gaddama ba Ballatana Har ya saba musu ba,Zai aureta kamar yadda suka Tsara sai dai Dina zata sani zata kuma gane cewa Fadin nan Dayake yi na Baya sonta bai Taba kaunarta ba ba karya bace..Tunda yake da ita bai Taba Sonta bai Taba kaunarta ba baitaba Sha"awar auran mace irin taba..Ammh Tunda Tayi Sanadiyar Lalacewar komai Gata gashi Yadda zai Rayuwa Cikin Bakinciki Da Maraicin Rashin Zaina Haka itama zata zauna Dashi Cikin wannan Bakinciki da Rashin Madafa sai ya Tabbatar da Dina sai Tayi Nadaman Abunda ta aikata.
******
*Bayan wata Biyu..*
Bayan Wata Biyu da suka gabata abubuwan suna nan yadda suke Ta bangaran Zain dai ba wani ci gaba yana nan jiya yau sai ma wami kara Ramewa da yayi ya kara Lalace Duk yayi baki yayi Gemu da kasumba kamar ba Zain dan Gayu ba Baya Fara"a baya Dariya baya zaman Hira Baya wata Walwala Duk Wani Abu na Jin Dadi Zain ya Riga yayi sallama Dasu acikin Rayuwarsa.
Har kuma i yanzu bai Daina Sadaka da Zuwa masallatai yana Bada kudin Sadaka Domin arokamai Allah ya bayyanamai Firstlove bashi kadai ba Duka iyayan nashi basu Zauna ba suma Suna Tsaye kan addu"a barin ma Alhaji Tsoho Tunda sun ga Tabbancin Abunda Zain yake Fada In babu Zaina acikin Rayuwarsa shi ba Cikakken Mutum bane,Gashi kuma yana Faruwa Saukinta ma aikinsa da kuma Haddir Daya kasance aboki na gari Su kadai ke Debema Zain kewa sai kuwa Hotunan Zaina Da Kullum Da Hoton Awayarsa yake iya Samun Barci Har kuma yanzu yana Gida Saboda yace bazai iya zama Gidan da Sukayi Rayuwa Da Firstlove ba kuma yau awayi gari bata Har Abada bazai iya zama ba Dole aka kyaleshi anan Gidan su kansu su Abba Sun Fi Jin Dadin ganinsa kusa dasu Hankalinsu yafi kwamciya.
Zafeera kuwa Bayan sun gama Exms Tazo Gida Dakyar ta iya Sati Daya ta Koma Itama Duk Ta Rame saboda Da Damuwa a yanzu ba iya Tsausayin Zaina Take ji ba har da Tsausayin Halin da Yaya Dakta yake Ciki Lalle ta yarda ta kuma Shaida Soyayyar Dayake ma Ukti bata karya bace Bayyana Dina kuma Wata kaddaran Allah ne Tatafi da addu"an Allah ya bayyana Zaina aduk inda Take hakama Laila Koda yaushe Cikin Kiran Umma Take ko Zataji wani Labari Ammh sai Umma tace mata Zaina dai Shuru har an kwarari Wata Na Hudu da barinta Gida Laila Tayi kuka Ranar da suka gama Exam Ta Tuna yadda zaina ke son karatunta ammah yau wani Dalili yasa ta watsar da Duka Burinta Allah Sarki Ita kanta Duka kamsin Salatin ta addu'anta Daya ne Allah ya bayyana Halima Allah kuma ya Tssreta ya Kareta ita da Abunda ke Cikinta bama Laila kadai ba Kowa Dake ahalin Gidan Dr.Saulawa Yana saka Wannan addu"an Cikin Duka Sallanlolinsa,Haka Zareena itama Tana Chan U.s Koda yaushe sai ta Kira waya its da Jawaaad suna Tambayan ba"aji wani Labari game da Zaina ba..? Duka dai Tambayan Daya ne Hatta Faruq ma Dake Chicago in ya Kira waya haka yake Fadi Balle Hamdiya itama Takan Kira Taji ko ya ake Ciki,Sai dai Fatan Allah ya Takaita abun ammh Zuciyoyi sun Fara sarewa,Umma da Zain kam azumin Alhamis da Jumma"a Baya Wucesu suna Tawasalli da wannan azumin Allah ya kare Halima aduk inda take ya kuma Bayyanata Cikin Koshin Lafiya.
Dina kuwa alokacin Cikinta yana Cikin Watansa na bakwai me yayi girma Sosai Dayake Tana da Girmam Jiki sai kuma Yabi Jikinta ta zama wata katuwa Ganin Cikinta ya Fara Girma ne yasa Nene ta Fara Kula da ita sosai Ganin Amanace Itama agaresu,Dina Gabadaya Tana Cikin Damuwa ganin Ko kallo Bata ishi Zain ba Har Abba da Umma yanzu Tana gaishesu suna amsa mata ammh Shi Ta Lura ko kaunar ganinta ma bayaso Tunda Tazo Gidan Wajen watanta Hudu bai Taba Tako kafarsa Dakin ba sai dai Su Hadu afálo in zai Fita Ta Fito Tana wani Tura Ciki Tana yamutsa Fuska ita adole sai ya kalleta ya kuma Tankata ammh Ko Kallo Bata Isheshi ba batama sani ba Inda zata Daina giftamai acikin Ido Daya Ji Dadi Domin ya Tsani ya ganta ita da Cikinta kuma da sunan Wai Zamansa Take kuma Abunda ke Cikin Nata Shine Ubansa ba Domin bayason ya kara batama iyayansa rai ba Da Wlh da Tuni Tun bayan Tafiyar Firstlove shima ya Bita ya Shiga Duniya Sai Dina Ta Nemi kuma wanda Zatayi ma Burauba ammh Taci Darajan Masu Daraja Shiyasa Bai Taba Bi ta kanta ba Tunaninsa da Burinsa na kan Zainarsa da kuma Abunda ke Cikinta kuma yana lissafe da Cikin Yana kuma Tunanin Itama Cikinta ya Shiga wata na bakwai kenan Yana Fatan Allah ya Bayyanamai matarsa ta Haihu agaban Idanuwansa Shine Fatansa da Burinsa.
Bangaran Zakiya kuwa bata kara Zuwa gidan Abba Wajen Dina ba,Ba Domin taji Haushi ba sai Domin Ta Kiyaye wasu abubuwan bata so Plan dinsu ya Tashi a banza ammh Tana Kiran Dina awaya Tana kuma bata baki kan Cewar datake Ta gaji da Cikin Jikinta da kuma Rashin Ko in kulan da Zain Ke mata ita kuma Zakiya sai ta Tausheta da Fadin Karta Damu Sauran kadan ta zama mallakin Zain alokacin bai isa kuma ya iya Wulakanta taba Tunda ta zama Matarsa kuma uwar ya"yansa,Da iri irin kalaman ne Zakiya ke Tausan Dina Datake Kokarin Fadin Tagaji Tana Chan Tana Cigaba da Iskancinta Itace Tarayyah da wannan Bin Wannan Har kuma aranta Tana Tunanin Namijin daya ya Dace da ita Wato Namiiji kamili wanda Bai yi Rayuwar Bariki ba.
Kwamishina ya sake Zuwa ya Duba Dina Har sau Biyu Hajiya Batula ma Tazo ita dasu Waleed suka Kwana Daya suka koma,game da Lafiyar Dina kuma Da Abunda ke Cikinta Haddir ke zuwa Duk wata yana Cheking dinta Shima Din har ya gama Dubata da yi mata wasu yan Tambayoyi baya sakar mata Fuska Daya gama Abunda ya kawosa zai kwashi kayan aikinsa ya Fice shima kamar ya Tsaneta ammh kuma ba Haka bane Haddir ko Cikin yan"uwansa mata bai da Sakewa mace Daya yakan sake da ita Zareena ce itama Domin Tare suka tashi ne shiyasa.
Bayan Hajiya Batula ta koma Kano ne ta samu Kwamishina Ta bashi Shawaran bai kamata abar Dina ita kadai ba Duk da Su Nene na Kokari akanta kuma Mutanen arziki ne basu Rike komai acikin Ransu ba bai kamata haihuwar Fari ba abarta Ita kadai Ko yaya ne ya kamata akwai wani nata akusa da ita saboda Halin Rayuwa Wannan Mganar Ta Shigi Kwamishina kuma ya aunata yaga gaskiya ne sai ya Kira Hajiya Maimuna sudan ya Tuntubeta kan ko zata zo Ta zauna Wajen Dinar har ta Haihu tace Daman itama Dinar na Ranta Shikenan Zata Shirya Tafiyan Zuwa Watan Gobe suka Rabu kan zai Kira Alhaji Tsoho ya sanar dashi haka kuwa akayi Daya Kira Alhaji Tsoho yamai bayani yace gaskiya ne bakomai sai tazo Ai yanzu anzama Daya Kuma Alhaji Tsoho da kansa ya Kira Abba ya gayamai Hajiya Maimuna zata zo ta zauna da Dina Har Ta Haihu bai yi Gardama ba Domin Shima bazai Taba iya ma Alhaji Tsoho gaddama ba Kowa yaji sai yace sunyi Tunanin Mai kyau Domin fa Mganar gaskiya Ranar naka fa sai Nakan nan.
*******
*Zaria..*
Rayuwar Zaina agidan Uwar mata Wata Rayuwa ce mai Cike da Darussan Rayuwa,Kuma Rayuwa ce Datake gudanarwa kamar Rayuwar yaya da kanwa Domin Babu Wani Bukatan Rayuwar da Farida Bata Dauke mata Shi ba Zaina Bata Da maraici Ko kuma Wani Wahalan Rayuwa Farida Zata Fita Ta bada Jikinta abata Kudi Tazo Tayi ma Zaina da Abunda ke Cikinta Hidima kuma aciki Har Tabama Uwar mata nata kason Dalilin Dayasa Ta kyaleta Ta Zauna wajen Faridan kenan.
Bayan Zuwan Zaina Gidan Zuwanta Uku,ammh bata kara mganar Zaina ba,Tunda Farida Tana Toshe bakinta da kudi,Zaina bata Fita Ko"ina Daga Daki sai daki bata aikin Komai sai dai taci ta kwanta In Tagaji Tayi kallo Komai zai Faru Gidan Farida Ta hanata Fita Koda bata Gidan sai dai In Tana Bukatar gani Ta Leka ta Window Daga Zuwanta Gidan zuwa Lokacin Datake Watanta Hudu acikin Gidan Ta kara Gogewa Da Rayuwa sosai,Banda Zuly Da karacharrale bamai Shigowa Dakin Farida suma Din Ita Ta basu Dama Ammh bata basu yarda ba Tunda Har Tsawon Lokaci babu wanda yasan Zaina nada Cikin Wata bakwai ajikinta Kuma Farida nakaita awo Duk bayan Sati 6 a asibitin Almadina,Kuma Ba wanda yasan Duka Siyayyan kayan Haihuwa Farida Ta gamashi Komai da Za"a Bukata na kayan Jarirai kuma Biyu Duka Ta Siya Komai Tunda anyi mata Scanning Likitan yace yan Biyu ne acikin Zaina Daya mace Daya Namiji Shiyasa ta Tanadi Komai Ko gajiya batayi Zaina Sai dai kawai Watarana Tayi Ta kallonta Tana kuka acikin Ranta Ta kare Lafiyarta ta martaba Auranta da Abunda ke Cikinta Ta gwammace ita ta Rika Fita tana Raba ma Maza Jikinta suna Biyanta Saboda Ita,Tana ji acikin Zuciyarta Farida bata Dace da wannan Rayuwar ba sam Mace Ce saliha mai Nagarta Tana Tsausayama Musbahu Domin yayi Rashin Kamilar mata haka kuma Tana Tsausayama Abba da Mami Domin sunyi asaran Nagartattaciyar Y"a haka kuma Tana Tsausayama Hassana da Usaina da arif Domin sunyi Rashin Uwa Tagari Haka zata zauna Tayi kukan Tsausayin kanta Da Kuma Tsausayin Farida ammh ita bata Damuwa Ko ajikinta.
Tum Zuwanta Gidan Farida Bata Taba kawo wani Kartonta acikin Gidan ba saboda ita,Daman kuma Ita sai dai Ta Bika Chan waje ku gama abunda zakuyi ka Biyata Ita Karuwancinta ba kamar nasu Sady bame da kullum Yan Shaye Shaye Farkan nasu Zuly kuma Har yau bata Rabu da Shafsoon ba Domin In Ta Rabu Dashi bata da Kowa Ba Domin ma Zaina na saka Farida na Taimaka mata ba da ba haka ba Zeezee da Jido Sun Dawo Ranar da suka Dawo Kuwa party akayi agidan kwana sukayi Kida da Rawa Inda Sabo ai Zaina Ta Riga ta saba.
In Kwana ya kama Farida awaje zata Damka Amanar Zaina hannun Zuly Da kacharalle ta sani Ko Za"a Hada Baki da Zuly acutar da Zaina Ta Tabbatta kacharalle bazai bari ba Namiji ne ammh yana da Amana kuma Farida Ta yarda dashi Shima kuma Abunda yasa yake ganin Girmamta Abun Hannunta bai Rufe mata Ido ba, Ko nawa ya Tambayeta zata bashi Ko ma bai Tambayeta ba Tana Bashi,Duk da Tasan Ko Ta Fita ba Ruwan Wata da Zaina ammh Gwara ta saka akular mata da ita Hatta su Zeezee da suka Dawo sun Ji Labarin Zaman Zaina Wajen Sholly,Ranar Har dakin suka Shigo Suna kare mata kallo Sai da Kacharalle yazo yace su Fita ko kuma ya gayama Sholly in ta Dawo Shiyasa suka Fita ammh kuma Zeezee ta Lura da wani Abu Bata dai yi mgana Ba Shigansu Dakin Lokacin Zaina bata saka Hijabi ba,Tana Cikin Manyan Dogayen Rigunan da Farida ke Siyan mata Tana sakawa Saboda Boye Cikinta,Lokacin Datake Zaune Cikin ya Turo Kuma Zeezee Tagani ammh Zuly da Kacharalle babu Ruwansu basu Taba Lura ba kawai dai suna Tunanin Zaina Tana son kayan Labarabawa Domin Koda yaushe Cikin Manyan Riganunsu Take.
Wataranar Asabar Tun Safe Farida ta Shirya tace ma zaina za"a zo adauketa Zata je Abuja sai Tayi kwana3 zata dawo zaina Ta Fara kwalkwal kamar Zatayi kuka Farida Ta lallasheta da Fadin kada ta damu ga Zuly nan zata Dinga Tayata kwana da Kula da ita,ga Kacharalle nan ma kada ta damu ita dai Batayi mgana ba ammh Yau Tafiyar Faridan sai Taji Bataji Dadi ba kamar wani Abu zai Faru ammh Tana Ji Tana gani Tatafi Bayan ta barma Zuly Kudi ko Zata Bukaci wani Abu.
Kwana Daya Ta Tafiyar Farida Suby Taji Labarin abakin Zuly ganin Ta daina kwana adakin ta sai Dakin Sholly Ita kuma zuly da wauta sai tace kwana uku Sholly Zatayi kafin ta Dawo Suby najin Haka Batayi kasa agwiwa ba ta Kira Shafsoon ta Gayamai Ga wata Dama ta samu da zai Mori yarinyar nan da Sholly ta mareshi akanta Daman Tun Faruwar Abun yayi alkawarin sai ya Dau Fansa ta Hanyar Morewa da Zaina Tun Lokacin ya saka Suby aikin yace zai Biyata 50k in dai ta samamai Wata Dama Ta Dade Tana neman Damar bata samu ba Sanin Farida Ta tare ko"ina ga kuma Zuly da kacharalle ammh yau bata da wata Damuwa Kacharalle baya nan ya Tafi kaduna Uwar mata ta aiko adaukesa Zuly kuma Zata san yadda Zatayi da ita Shafsson najin Haka ya saki Ihun Jin Dadi Yace in Komai ya Tabbata zai Cikama Suby kudinta yanzu Rabi zai Bata tace ta yarda suka Rabu kan ta Turomai Acct lambata Ya Turamata kudin Itama Tace mai Xuwa anjuma Dayaji Kira kawai ya Taho Gidan Lokaci Yayi Da Zata so Taga Yaya Sholly zata yi In ta Dawo Daga Hajar Dake ta aikin Boye wani ya Riga ya Wanketa Zata so Taga yaya Sholly Zatayi kuma Daman ba Tun yau ba Ta Tsani Sholly Tana Bukatar ganinta Cikin Kunci Ta tsani Cigaban ta da kuma Finsu da Datayi da komai harda wajen Uwar mata.
*Ki biya ki karanta Cikin Salama..Amanata A hannunku Take kuma Tana Hannun Allah ne..*
*Janafty...*
7/16/21, 2:36 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B21️⃣0️⃣*
*IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*
"Daga Zuly har Zaina basu san Abunda Suby Take kullawa ba Da yammah Rufy ta gayyato kawayenta Suka zo Tsakar Gidan Suka saka Kida suna ta Shaye Shayensu,Da rawa Gidan Duk sai ya Rikice Shiyasa Zaina na Daki Ko Motsi batayi Saboda Gidan ya Cika maza da mata Gashi Farida bata nan Zuly ce kuma Itama Ta Fice ta barta Tun Tana Lekonsu Ta window har ta Gaji Ta Koma ta kwanta Bayan Tayi sallar mangariba Maltina Tasha kawai taji Cikinta ya Cika sai ta koma ta kwanta Saboda Bata son Hayaniya Toshe kunnuwanta da Filo tayi Saboda Kada Taji karan Kidan da agogo Tayi amfani Ta gane Lokacin Sallar Isha"i Daman dashi Take amfani Tunda bata Tunanin akwai masallaci nan kusa.
Har Ta idar da Sallah Zuly bata Shigo ba Shiyasa Ta Shiga Tiolet Tayi wanka Tazo Ta Saka wata Doguwar Rigar Barci mai Igiya,Ta Dade Tsaye Tana kallon Cikinta Daya Girma Sosai ammh Yana Boyewa Cikin Burma Burman Dogayen Rigunan Data ke sakawa ammh ai Duk wanda ya kalletaa yasan ba ita kadai bane Ganin ta kumbura Ko"ina ta Cika Irin dai na masu Ciki Ita Har mamaki Take Zuly Ko Kacharalle basu Taba Fahimtar Tana da Ciki ba ko Kila sun Gane kawai kallonta Sukeyi.
Karamin Hijabinta Datake kwana