Chapter 16 Reading Zainazain Book 2 Complete By Janafty Arewa Novels

Zainazain Book 2 Complete By Janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   16 / 37

45K to 48K   out of 108.5K words

Biyo baya Kwamishina Kamar ya kwantama Alhaji Tsoho Saboda Godiya Shi kuma yace Bakomai Kada ya Damu an Zama Daya basu wani Dade ba Lemo suka sha sai Ruwa Hajiya Mama Tayi musu Rakiya Zuwa Chan Gidansu Abba.

Koda sukaje Nene ta Shirya musu Abinci kala kala Daga Umarnin Abba Shima kansa yana Gida,Koda suka isa sun samu kyakyawan Tarba ba kamar na Baya ba,Umma ce kadai Bata tsaya ba suna gaisawa ta koma Daki yau din Abba ya Fito sun gaisa da Kwamishina da Hajiya Maimuna Da Hajiya Batula Tunda da ita akazo Harda Walid da Walida,Bayan gaisuwa da Kuma ganin Juna,da nuna kayan da suka zo Dashi,Nene da Abba da Hajiya Mama suna ta Saka albarka, Nene tayi musu Jagora Zuwa Cikin Dakin Dina Wacce Farinciki ya Cikata Tun Jiya da Daddy ya gayamata Zuwansu Har Zakiya ta Kira ta Shaidamawa Tadai ce mata Zata Shigo ammh Ba Lalle ba sanin Zakiya yanzu Hankalinta baya kan Dina yana kan Ja"afar ne Wanda ya zama Jini da Tsokarta

Lokacin da sukayi ido Hudu da Dina sai da suka Tsauyamata ganin yadda ta koma kamar ba ita ba Hajiya Batula kuwa Tana kallonta aranta Tana Fadin Uhm yarinya waya gayamiki Barno gabas Take kin kusa Fara Jin maza Tana Jinta Tana ma Kwamishina Shagwaba wai Cikin ya Isheta Shi da Hajiya Maimuna suna Lallashinta ita dai Tana Gefe Tana kallon Ikon Allah Sun Shisshiga da kayan da suka zo mata dashi Shine ma ta Nuna musu wanda Nene ta kawo mata Hajiya Batula na Daga kayan Tana Yabama wannan ahalin Saboda duka kayan Expansive ne Bana Banza Shi kanshi Kwamishina yana Jinjina ma Ahalin Alhaji Tsoho Domin yasani Cikin Dubu wlh sai an Tona za"a samu kamarsu.

Nene da Zainab suka yi ta Shigowa da abincin da suka Shirya musu Hajiya Maimuna nayi musu sannu da aiki nan suka ci suka Sha suna Ta Hira Dina Bakinta yaki Rufuwa Saboda Farinciki Nan sukayi Sallar Azahar da La"asar Hajiya Mama Tuni ta koma Gida Sai da sukayi Sallar La"asar sukayi Shirin Tafiya bayan kwamishina ya Dawo Daga Cikin gari Daman Tun bayan Sallar azahar ya Shiga Cikin gari ya dawo Shida Excort dinsa.

Da Zasu Tafi Abba da Nene har Haraban Gidan suka Rakasu Dina ma da Hajiya Maimuna Sun Fito Dina Ciki yayi Nauyi sai Dingisawa Take tana wani Cije baki Dina Harda kuka ta Rumgume Kwamishina Tana kuka Shi kuma ya Biye mata yana Lallashinta Dakyar ta Sakeshi ya Shiga Mota Hajiya Batula Takaichi ya Cikata Gamsamemiya Dake ga Ciki ammh Kina Abunda Walida ma bazai yi ba ita Har yau har Gobe Bata ganin Laifin Kowa sai na Dina Ta Tattaba ba Shege sai Da akayi Shegiya.

Bayan Tafiyarsu Kwamishina,Hajiya Maimuna Ta kama Dina suka Koma Ciki,Ta Fara gyaran kayan da suka zo dashi,Tana Ijiyesu Cikin muhallinsu,Sai Chan bayan Mangariba Nene ta Shigar musu Da Dinner Har ta Dan Tsaya suna Hira da Hajiya maimuna kafin Tayi musu sallama ta Fito Ta koma Dakinta Tayi wanka Umma dai na Ciki Bata ma Fito ba Ballatana aganta.

Bayan Nene ta Fito wanka ta Shirya ne Ta kaima Abba Abincinsa Ta Fito kenan suka ci karo da Zain ya Dawo Daga Asibiti bayan sun gaisa Nene ta Kalleshi Tana Fadin"Yauwa Nace ba..'

Ya waiwayo yana kallonta Nene ta Cigaba da Fadin"Kanwar Mahaifiyar Dina Tazo fa..Yau suka zo Tare da mahaifinta da Matar Babanta da kannenta ammh su sun koma ita dai Ta na nan sai Dinar ta Haihu zata koma.."Zain yayi wani Jagale yana kallon Nene kafin yace"Nan zata zauna kuma Nene..?

Nene tace"Eh Zata zauna nace Maka har Allah ya sauki Dinar Lafiya.."

Zain ya kada kai kawai yace"Allah ya kyauta To.."Yana Shirin Shiga Dakinsa Nene tace"In ka natsa ka Shiga ka gaisheta.."Da Sauri ya waigo Yana Fadin"A"a Nene ni ba inda Zan Shiga ina ma Ruwana dasu.."Nene tace"akwai Ruwanka mana..Kuma Umarnin Abbanka Yace na gayamaka ka Shiga ku gaisa.."Daga Haka ta Wuce ta barsa nan Ya Bita da kallon Takaichi Da Bakincikin Dake Cikin Ransa Karamin Tsaki ya Saki ya Tura Kofar Dakin ya Shiga.

Sai Da yayi wanka ya Sauya kaya Zuwa Farar Jallabiya Zainab Ta Shigomai da abinci Da Hannu yabata Umarnin Ta koma Dashi kana yace mata Tea Zata Hadomai Iya Bonvita kawai banda Madara,Ta Fice Zuwa Kitchen ta Hadomai ta kawomai yana Zaune Gefen gado Yana Duba wayarsa Sanda Zata Mikamai Mug din ta Hangi Hoton Zaina Daya Cika Sreendin Wayar Shi Zain ya Kura ma Ido yana kallon Cikin wani kewa da Muradi mai Girma Har ta Fice Tana Jin Tsausayin Ya Dakta acikin Ranta Duk ya koma wani Iri Dashi Saboda Chanjin Rayuwar Daya samu Allah Sarki Halima Ki Dawo ko Saboda kada Watarana Mu Rasa ya Dakta Gabadaya.

Tuna Nene tacemai Umarnin Abba ne yasa Bayan yagama Shan Tea din Ya ijiye wayarsa nan Gefem gadon ya Zura wani Takalmin Dake gefen gadon ya Fice Zuwa Dakin Da Dina ke Ciki ya Dade a Kofar Dakin yana Tufka yana warwara kafin yayi Knooking din Kofar Daga Ciki yaji ana Bashi Izinin Shigowa ahankali ya Tura Kofar ya Shiga Da Karamar Sallamarsa Yana Tuna Tun bayan Dawowar Dina Gidsnsu yau ne karo na Biyu Daya Taka Kafarsa Cikin Dakin.

Koda ya Shiga ya samu Dina Zaune Rashe Rashe a kasa Ta Jingina Bayanta da Gado Hajiya maimu Ta saka mata Filo Daga Bayanta Saboda Taji Dadin Zama Gefe Daya kuma Tana Matsa mata kafafunta da suka Kumbura suna Hira sama sama Yana Shigowa Dukkansu suka Dago Suna kallonsa Dina Kuwa sai da ta waro Idanuwanta Tana so Ta Tabbatar Zain din ne ko Mafarki ne,Dadai Ta Tabbatar dashi ne sai wani sanyi ya Cika Zuciyarta Tuni Ta Rika Godema Zakiya acikin Ranta Tana Tunanin Duk Cikin aikin Mallam ne.

Hajiya Maimuna kuwa Tana ganin Zain ko ba"a Gayamata ba Ta gane shine Uban Cikin Dina ammh Daga kallonsa Kamili ne ga Natsuwa Bazaka Taba Zatom zai iya aikata wani aikin Assha ba Sai dai Ita kaddara ba Ruwanta Daya Nagartan Mutum yake Fadamai kawai Zatayi.

Dakatawa Tayi da Abunda Take Tana gyara zamanta Dina kuwa Ido ta Kafeshi Dashi kamar wata mayya Shi kuwa Tunda ya Shigo kallo Daya yayi mata ya kauda kansa Kamar bai ganta ba Daga Nesa ya Durkusa yana Gaida Hajiya Maimuna ta amsa Cikin Fara"anta Ta kasan Ido yake kallonta aransa yana Fadin Ashe ga Inda Dina ta Dauko Kyau nan Domin Duk da Hajiya Maimuna ta kwana Biyu a Duniya kyawunta na nan bai Dishashe ba.

Cikin Sanyin Muryansa yace"An zo Lafiya..? Tace"Lafiya Alhamdulillah ya muka same ku..? kansa na kasa yace"Alhamdulillah.."Daganan kuma sai yayi Shuru Idanuwansa na kallon Cafet din Dakin Ita kuma Hajiya Maimuna Tana Nazartan yanayinsa yayinda Dina Take Ta kallonsa Ganin Duk ya Rame ya kara Fita Hayyacinsa Kishi ya Cika Ranta Tana Tunanin Saboda wannan Shegiyar Zainar ne ya koma Haka Har Abada bata Batan zaina ta Dawo Gida ko aganta.

Yana Shirin Tashi Hajiya Maimu Tace"Ya mukaji da wannan Abun da yafaru..? Allah ya bayyanata Allah ya kyauta na gaba an ce itama Matar naka da Ciki ta bar Gida? Ya za"ayi sai Hakuri Allah ya bayyanata.."Zain Sai Lokacin ya Dago kansa Karaf kuwa suka Hada Ido da Dina wacce Take jin kamar Taje ta Rumgumosa Cikin Tattausan Murya yace"Ameen Ameen Nagode.."Sai Lokacin Dina Tataba Jin Zain yayi mgana mai Tsawo Tun bayan Barin Zaina Gida Tunda bama ganinsa Take ba Cikin Kallon Tsana da wani Bakinciki ganin Yadda Cikin Dina yayi Girma Cikin yake kallo kawai yana Hasasho ajikin Zaina wani Tiriri na Fita Daga Ransa Cikin Sauri ya Tashi kamar zai Fadi Jin yadda Zuciyarsa ta Fara Zafi yace ma Hajiya maimu sai da Safe ya Fice ta Bishi da kallon Tsausayi kana ta juyo Tana Cema Dina"Allah sarki yaro karami ya Hadu da Jarabawan Rayuwa..Na Lura Batan Matarsa Ta tabasa sosai.."

Dina Ta Tura baki Tana Fadin"Insha Allahu Tatafi kenan Har Abada.."Gum Hajiya maimuna ta Make bakinta Tana Fadin"Kul..Wawiya kawai kina ma wannan Halin na Siradin Rayuwa har Wata zaki ma Fatan Tatafi har Abada..? Dina Ki Kya kanki Wlh kada na karajin wannan mganar Daga Bakin ki Kina Ji ko..?

Cikin Bata Rai da Tura Baki Dina Tace"Naji.."Daga Haka ta Tsuke bakinta ammh Har Cikin Ranta Bata Fatan Zaina ta Dawo Rayuwar Zaina Tana addu"an Allah ya Dau ranta a inda Taje kada Tataba Dawowa Har Abada Tana Jin Hajiya maimuna Nata yabon Dangin su Zaina ammh kala batace mata Domin Ranta Duk abace yake Saboda Tunawa da Yadda Zaina Tatafi da Duka Ruhin Abun kaunarta Zain.

Shikowa Zain Dakyar yakai kansa Daki Jiri na Dibansa ya hau gado ya kwanta yana Sauke Numfashi Dole gobe yaje yaga Likita Dagashi sai Haddir ne suka san ya samu Hawan Jini Bayan Tafiyar Zaina Shi ya Hana Haddir ya gama iyayansu Bayan Dr.Imran ya gaya musu Saboda baya so Hankalin su Abba ya tashi Da Taimakon mgungunan Hawan Jini yake Tsaye da kafarsa har yau ammh ya sani Watarana sai ya Gaza Tunda Baya Kiyaye Dokar Likitoci na Rage Shiga Damuwa da Tunani mai Tsawo Wanda shi kuma kullum Cikin yake kwana Cikin yake Wuni.

Daran Ranar Dakyar ya iya yin Barci Ciwon kai mai Tsanani ya Rufeshi ammh haka ya Dage ya Shirya Tun Safe ya Shiga asibiti Office din Dr.Imran ya Fara Zuwa Shi ya Gwada B.p dinsa ya kuma gayamai Jininsa yayi Mugun Hawa sosai sai ya Rage Tunanin Ganin Halin Dayake Ciki ne yamai allura ya kwanta nan Patient bed na Cikin Office din ya samu Barci Shi da Dr.Imran din ya Kira Haddir ya gayamai Daman ya Shigo Cikin asibitin sai yazo ya Duba Zain din shi ya zauna Tare Dashi Har ya Farka ciwon kan ya Sauka Har yaji Dama Ba yadda Haddir bai yi Dashi yazo ya maidasa Gida ya kara Hutawa yaki yace yana komawa Umma da Nene zasu Zargi wani abu Shi kuma ahalin yanzu bayason Damuwarsu Dole ya kyaleshi ammh bai barsa ya Duba Kowa ba Yajasa Office dinsa yace ya kwanta ya Huta Shi kuma yana Gefe yana Attempting din Marasa Lafiya.

Har suka Tashi aiki Haddir ya Rakoshi Gida,kowa Motarsa ya Shiga,Har Ciki ya Shiga nan Falo suka ga Hajiya maimuna ta Fito suna Hira da Nene Umma na Gefe bata saka musu baki sai dau Tayi Mirmishin yake,Dayake ita Wayayyiyace bata Zaman Daki Tare Haddir da Zain suka gaisheta ta amsa Tana Yi musu sannu da Zuwa Daganan suka Shige Ciki Damann Shi Haddir din yaji labarin Zuwansu Abakin Hajiya Mama Tun Jiya bayason yana Tadama Zain Hankali Shiyasa basa ma wannan mganar da juna.

Sai da sukayi Dinner tare kana Haddir ya wuce Gidan Alhaji Tsoho,Washegari kuma Haddir Abuja ya Tafi sai yace Zain ya zauna agida ya Huta Toh kawai yace mai ammh yana Tafiya ko Abuja bai kai ba Ya Shirya ya Tafi asibiti saboda baya son Zaman Gidan Da azarar ya zauna Shi kadai sai Tunane Tunane suyi mai Cha Ammh in yana asibiti yana Duba Marasa Lafiya hakan na Debemai kewa.

*******

Azuwa wannan Lokacin Tuni Zakiya Tagama Saki da yardan ma kanta ta samu Miji Daidai da Ra"ayinta wanda kuma take so,Ta Riga ta gama Shakuwa da Ja"afar ta sakarmai komai nata Sirrinta kuma kalilan ne bai sani ba sai dai bata yarda yasan ita yar Bariki bace tayi kokarin Duk ta yakice Abokan Shashancin nata Tunda Tana so Tayi aure.

Hatta Motarta Tana wajen Ja"afar Shi yake kaita Wajen aiki kuma yazo ya Dauketa Ko"ina Zasu Tare suke Zuwa wadanda suka san Ja"afar abaya in suka gansa yanzu bazasu gane shi ba ya zama wani Gaye mai Tashe Tunda Zakiya ta sakarmai kudi yana Yadda yaga Dama Hatta Bankin kansa ta Bude ta sakamai kudi Saboda Laluransa da baisai yagayamata,Tana so ta Tsarkake kanta ne da auransu kuma Bataso Ja"afar din ya Fahinci wani abu Shiyasa Bata Taba Nunamai Tana Sha"awarasa ba ammh yadda Take Mutuwar Sonsa da kaunarsa kamar Tayi mai Fyade haka take ji.

Bata Fito mai da Niyyarta na Son Auransa ba sai da Tagama maidashi Dan gata ta sakarmai komai ta Fiti mai da maitatarta na son auransa,Da Farko ya nuna mata Shi fa bai da komai Ai Tafi karfinsa ammh sai ta Nuna mai kada ya Damu Tana Sonshi ahaka sai yace mata Shi bai da kowa agarin Bauchi sai ogansa,tace karya Damu Zatayi mgana Dashi Ranar Dayace ya amince zasu aure Rumgumesa Zakiya Tayi Saboda Farinciki Washegaro kuma bayan Taje gareji wajen ogansa Tagayamai komai yace Shi baida matsala Tunda Ja"afar din ya yarda suka Rabu kan Zata kai shi kano Wajen Babanta in ta Dawo Zata zo Suyi mgana kan Kudin Sadaki da Sauran Shiryan Shiryan aure Tunda kamar Shi Zai zama Waliyin Ja"afar din.

Ranar Saboda Farinciki Tana Dawowa aiki ta Dauki Ja"afar suka Tafi wajem saida Motoci Tace ya zabi Duk wanda yake so shine ya Zabi wata 4Matic Fara mai kyau Nan take Zakiya Tabi ya Kudin kawai Facaka take da kudu Batare data Damu ba.

Basu Samu Tafiya kano ba sai Weekend Saboda aikinta Duk Iskancin Zakiya Tana Daraja aikinta Amotar Ja"afar din sukayi Tafiya suna Hanyar Zuwa kano ne Dina ta Kirata Tana mata korafin Ta Daina Nemanta yanzu Har Hajiya maimu Tayi sati agarin Bauchi batazo sun gaisa ba sai Take bata Hakuri Tana gayamata yadda komai ya Faru nan take sanar da ita gasu ahanya zasu kano Zata kaima Babanta Ja"afar amatsayin Mijin Da Zata aura Take gayama Dina Kilama ta Rigata aure ayadda zakiya ke mganar Tana Dariya kamar wacce akayi ma gafara Dina Jikinta yayi sanyi ta Fara Tunanin anya wannan Rayuwar da Zakiya ta Tsinci kanta mai Bullowa ne..? Haka kurum take jin kamar Tayi gaggawa sakarma Yaron komai Duk da Bata Taba ganinsa ba koma menene Tana yi mata Fatan Ta samu Dacewa kan Abunda take Buri da so.


*Sai kun sake min Hakuri..muna da Hidima ne ammh Insha Allahu in na samu Lokaci zaku rika jina Nagode..*






*Janafty...*
7/25/21, 9:05 AM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B21️⃣4️⃣*

*IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*


*Kano..*


Tsuru kawai Mallam Nuhu mahaifin Zakiya yayi yana Bin Ja"afar da kallo Mamaki da al"ajabi sun Cikashi na ganinsa wai amatsayin Mijin da Zakiya Zata aura.


Duk da bai san Shekarun yaron ba Ammh ido ba mudu ba yasan Kima ya Tabbata Zakiya bazata Girmemai ba,Kuma ayadda yake gani wannan yaron yayi ma Zakiya yaro a matsayin wanda Zata aura sai dai bashi da tacewa ganin Yana Fama Kan Zakiya Tayi aure sai yau Allah ya amsa mai wannan addu"an ta kawo mai Mijin da Zata aura.


Daman Lokacin da suka Zo yana Tsakar Gida kan Tabarma ne yana Shan iska nan suka Yada Zango,Ya Dade yana Jan Jasbahabsa bayan yagama jin Zakiya Tagama Kore bayananta bai yi mgana ba kana ya jinjina kai kawai kafin ya kalli Zakiya yana Fadin"Naji Duka bayananki Zakiya..Tashi Ki Shiga Cikin Daki zan yi mgana Dashi.."


Batayi Gaddama ba Ta Mike ta Shige Dakin Amaryan Mallam Nuhu Daman ita ta Tarbesu Da suka iso,Sai da ta Shige ne Kana Mallam Nuhu ya kalleshi Sosai yana kara Nazarinsa Dakyau haka kurun acikin Zuciyarsa Yake jin bai yarda da yaron ba.

Gyara Zama yayi yana Fadin"Ja"afar ya sunan Mahaifinka achan Yola din..? Ja"afar kansa na kasa yace"Sunansa Mallam Isma"il baffijo..."Mallam Nuhu yace"Sunansa kenan..? Dashi yake amfani kenan..?


Ja"afar ya gyada kansa alamun Eh Shuru Mallam Nuhu yayi yana kara Nazarinsa kafin yace"Achan Yola wata Anguwa kuke zaune..,? Ja"afar yace"Muna lowcost Lokacin Iyayena Nada rai Daga baya kuma Dana koma Hannun kakana mun bar nan da Zama.."mallam Nuhu yace"Itama Kakar Taka ta rasu kenan..?

Ja"afar yace"Eh Allah yayi mata Rasuwa Shekaru Biyar da suka wuce..."Mallam Nuhu yace"Allah ya Jikanta da Rahma..'Ja"afar yace"Ameen Ameen ya Allah


Mallam Nuhu ya kara gyara Zama yana Fadin"Sauran yan"uwanka fa ina Nufin Koda anje chan Bincikawa za"a iya samun wani..? Ja"afar yace"Gaskiya a"a saboda Dangin Mahaifiyata ba yan nan bane yar Gudun Hijirace Daga Niger Mahaifina ya aureta Duka ta rasa Danginta Mahaifi na ma bashi da wasu Dangi Tunda na taso Bayan Iyayena Kakata wacce ta Haifi Mahaifina kadai na sani..."

Mallam Nuhu ya Dade yana kallonsa kafin ya kada kai yana Fadin"Bakomai zamu Bincika kasan shi aure sai da Bincike Ba"ayinshi kai Tsaye.."Ja"afar yace"Hakane.."


Shuru yabiyo baya Shi Ja"afar yana Zaune Kansa na kasa Mallam Nuhu kuma nata Jan Casbahan sa yana kara Nazarin Yaron da Zakiya ta kawomai a matsayin wanda Zata aura,basu wani jima ba Sallar azahar kadai sukayi anan ko abinci ma basu ci ba Lemo kadai suka sha sukayi Haraman Tafiya Har Zakiya Tashiga Mota Mallam Nuhu ya aika aka Kiramai ita Bayan Tazo ta zauna gabansa ya kalleta yana Fadin"Anya Zakiya kina ganin auran wannan yaron Da zaki yi Daidai ne..?

Zakiya ta Muskuta Tana Fadin"Eh Baba Ina Sonshi kuma Shima yana Sona.."Mallam Nuhu yace"duk ba wannan ba..Yadda kika gayamin fa yaron nan bai da wata Sana"a Dame zai Rike ki..! Kuma ni aganina ba yaro ya Dace Dake ba Zakiya ashekarunki gwara ki samu Mai Hankali Wanda Rayuwarku zai Daidaita.."


Zakiya Tace"Baba yana da Sa"ana fa Bakanikr ne..Kuma ni ina aiki na Tabbata zan iya Rikemu...Auran nan fa kake so nayi Baba gashi kuma Zan yi Meye kuma abun Damuwa Baba..?

Mallam Nuhu yace"Uhm..Shikenan Allah ya sa albarka..."Zakiya tace"Ko Kaifa Baba..Ameen Ya Allah Haka Daman nake so ka Fada kawai.."Mallam Nuhu yayi Shuru kawai ganin Idanuwan Zakiya ya Rufe Bataji bata gani.

Tana Shirin Tashi Ya Dakatar da ita da Fadin"Kin san cewa aure bazai Hallasta ba sai kin Tsarkaka..? Yafada yana kallonta Cikin Sunkuyar Dakai Zakiya Tace"Na sani Baba..Ina Cikin Isbira"in din ne ma.."Mallam Nuhu ya Girgiza kai Cikin Takaichi Yana Fadin"Kin san ya zaki Tsarkaka kanki kuwa Zakiya..! Da son samu ne Da kin Dawo Kin samu Tsarki sai adaura muku auran kamar yadda kika Bukata..

Zakiya Tace"Na sani Baba Ba jini uku bane..? Ka tsarkake kanka ga Duk wani Datti ko..? Mganar kuma na dawo nan Baba aikina In na Dawo nan akwai Damuwa Gwara na zauna chan nayi maka alkwarin Nayi Niyyar aure zan Tsarkake kaina Insha Allahu.."Mallam Nuhu ya gyada kai yana Fadin"Shikenan Allah ya Rufamana asiri.."


Sallama Tayi mai ya Bita da addu"a Tabashi kudi yaki karba sai da ta Rantsemai cewa Cikim kudin albashinta ne Kana ya karba ya Bita da addu"an Allah

16 / 37