Author : Jamila Janafty Category : Romantic Hausa Novels
Motarsa Harta da kayan Cikin Gidan ya Saidamin su kayan sawa ne kuma Duk ya sace ya saida Dagani sai kayan Jikin sai wadanan kayan na Tsira Harta da Ogansa na Gareji yace sai Daga baya ya samu Labarin Ja"afar Dan Damfara ne Dina Bani da komai Tun Faruwar Abun nan na Rasa wa zan Dosa Sati Biyu Wadanda suka Siya Gidana sukabani yau kuma ta Cika Suna BuKatar Gidansu Hatta da wayata Ja"afar bai barmin ba Dina gwalagwalaina Duka ya sace ya Tafi Dasu Bani ko Kudin Motan da zan je kano sai kika Fadomin arai nace bari nazo nan naji nasan Insha Allahu Ba"a rasa wanda zai kaini Gidanki ba ashe kina ma nan.."
Dina Dake kuka itama Ta Dago Fuska Shabe Shabe da Hawaye Tana Fadin"Aikin ki fa Zakiya..?zakiya na Kwallah Nadama da Bakinciki Tace"Tun Wata Biyu da suka wuce Ma"aikatanmu sukayi Sallaman Ma"aikata Hardani aciki Dina.."Gabadayansu kai suka Hada suna kuka Zakiya na Fadin"Tabbas Abunda na aikata ne nake Girbanshi Tun aduniya Dina...Gwara ke Kin yi Auranki Cikin Daraja Harda wani Rabon..Arman bazai Tashi Cikin Wata Rayuwa ba Dina Nifa Kalleni Cikin nan ko yazo Duniya ina zan ga Ubansa..? Wlh Dina Nayi Nadaman Zamowarta yar Bariki Domin Babu Riba acikin Wannan Rayuwar Sam sam.."
Dina Na Sharan Majina Tana Fadin"Babu gwara Zakiya..ni kaina Abunda na Shuka nake Girba wannan Cikin da kika ganmi Dashi Rabon sa ne ya kawosa Tun bayan Auranmu Zain bai taba min Kallon Mace ce ba Tunaninsa da Zuciyarsa suna Wajen Zaina ce Ni na sakamai mganin Da komai ya kamkama Har na samu wannan Cikin Kingani ina zaman karban Duka Hukuncina ne Daga Allah na Ammh ni nasan Dawowar Zaina gareni Tamkar Haske ne.."Zakiya cikin kuka Tace"Zaina ta Dawo..? Dina ta Daga mata kai Kafin ta Fara bata Labarin Dawowar Zaina Ta karishe Da Fadin"ina jin Rayuwata kamar ba Rayuwata ba Zakiya ba.
nayi Nadaman Abubuwan Dana aikata abaya da nasan Cikar Burina na auran Zain ba alheri bane Wlh Tallahi da ban yarda Mun Shiryawannan Plan din ba..Sai dai kash aikin gama ya Riga ya gama kuma Bamu isa mu Dawo Da Hannun agogo Baya ba.."
Hada kai sukayi suna kuka sai da ya ishesu kana suka Tsagaita Zakiya Ta kalli Dina Tana Fadin"Dina nazo ne ki Taimakeni Ki bani Masauki na kwana Zuwa gobe da Safe ki Taimakamin da kudin Mota na Koma kano yanzu bani da inda yafi Chan aduniyan nan.."
Dina Ta Bude Baki Zatayi Mgana Zain Dake Tsaye Kofar Bedroom dinsa Tun Dazu ya daga Murya yana Fadin"Bazaki Taba Samun Masauki anan Gidan ba Zakiya..Sai dai Zan iya baki Kudin Motan da Zaki kara Nisa da garin Bauchi na Har Abada.."Gabadayansu suka juyo Inda Sukaji Muryan Zain Cikin Wani irin yanayi ganin irin Banzan kallon Dayake Binsu Dashi Dukkansu alamun Dukka ya gama jin Mganar da sukayi da komai da komai sai Kunya da Nadama ya kamasu Dukkansu suka Saukar da kai kasa Cikin wani Alhini da Nadama mai Tsanani.
Takowa ya Farayi zuwa agabansu cikin Shigan Shadda Fara da alamu ya Shirya zai Fita ne,Sai da yazo gabdasu kana ya Dakata yana Binsu da wani kallon Kadan kuka gani Kafin ya kada kai ya Tura Hannu Cikin Aljihu ya Zaro Kudi da bai san ko nawa bane ya Zube kan Zakiya yana Fadin"ga kudin Mota nan ba Kano ba ko Lagos ne na Tabbata zasu isheki..Alhamdulillah da Abunda ya Faru dake ko bakomai Kinga kin Fara ganin Karshenki..Nakuma baki wannan kudin ne ba Domin na Tsausayamiki ba sai Domin ki Kara Nesa da garin Bauchi Domin Ina ganin kamar nayi wani Babban jihadi ne na rage Mugun Iri awannan garin..Aje chan Acigaba da Zaman karban Kaddara bama ga Cutar Daya saka Miki ba ko wannan Cikin Da Zaki Haifa baki san ina Zaki ga Ubansa ba Ya Isheki Takaichi Da Nadama.."Yana gama Fadin Haka Ya Nunata da yatsa yana Fadin",Minti Biyar na baki ki Fice mana Daga gida..In ba Haka ba Wlh Zan saka Arakaki har Tasha.."Yana gama Fadin Haka yayi tsaki ya Fice yana Hararan Dina Datake Tsiyayan Hawaye.
Yana Fita Zakiya Ta kara saka kuka Tana Tattara Kudaden Daya Zube mata Tana Fadin"Bari na Tafi Dina kada na Jaxa Miki..Don Allah ki yafemin Abunda ya Faru abaya..Bansani ba Ko Karshen ganawarmu kenan.."Tafada Tana Mikewa Lokaci Daya Tana Daukan Jakarta Dina Dataji Ta kasa Daina kukanta Ta Mike ta Rumgume Zakiya Tana Fadin"Na yafemiki..Nima ki yafemin Zakiya..Ina ji ajikina Kina Kano Zaki ji Labarin Mutuwata..Ina ji kamar ganawar mu Ta karshe kenan.."Zakiya Tana Sharan kwallah Tana Fadin"Ki Daina Fadin haka Dina da Ikon Allah Zaki Haihu Lafiya.."
Haka dai sukayi ta Kokensu har Haraban Gidan Dina Ta Rakota suka Rabu Tana kuka Itama Zakiyan Tana kuka kana ta Koma Cikin Gidan Ta wuce Bedroom dinta Ta Fada kan gado ta Fashe da kuka Haka Zakiya Har takai Tasha Tana kukan Nadama da yima Bauchi kallon Karshe,Ta samu Motar kano ta kusa Cika sai Kawai ta Hau ta kudendena kanta Cikin Hijabi Tana kuka Har Mota Tatashi Bata iya Dagowa ba Saboda Tana gani Kamar Mutane sun san Abunda ya Faru da ita.
Zain kuwa Shi ya gayamasu Umma Daya shiga gaishesu suna ta alhini Nene tace Abunda Zakiya ta aikata ne take gani Tun aduniya ita kuwa Zaina da Zain ya gayamata sai ta Fara kukan Tsausayin Zakiya Zain sai ya saki baki yana kallonta Saboda yasan Halinta Haka take da Tsausayi abu kadan Cikin nan sai ya sakata Rigima da yawan koke koken Daya gane haka sai ya koma yana Lallashi Ranar gidanta ya kwana Cikin Farincikin Dadin da Zaina ta Juyar dashi yama manta da wata Dina wacce ta kwana kuka Da kuma Alhinin Abunda ya Faru da Zakiya Gabadaya sai taji kamar itama akwai Sauran sakamakon da Zata Girba Gabadaya Taji Duniyan ta Juya mata baya.
Har washegari Tana cikin wannan Halin ko Shashensu Umma bata leka ba Tana so ta Kira Zakiya Taji ta isa Lafiya..?ammh bata san Hanyar da Zata sameta ba,Dole ta Hakura Kwana Biyun nan Haka tayishi Cikin Wani Hali Ga Zain bata kara ganinsa ba Tundaga Ranar Daman yana Gidan Zaina ne Arman kuma yana wajen su Umma shi dasu Anun Sunzama yan gatan su Umma da su Zainab Ballatana Zulaihat da indai Ta Dawo makaranta Tana Wahale dasu Ita Haka Allah yayi ta akwai son yara,kuma Yaran sun saba da ita har kuwa shi Arman din Daman yaron Inda ake Lallabasa Chan yake.
Kwana Biyu da Faruwar Haka Dina ta Fito Daga Shashenta Zata Shashensu Umma Ta gaishesu Cikin Ikon Allah kamar an kwasheta an Kifar Akasa haka Ta Fadi kan Cikinta nan da nan Jini ya yanke mata Lokaci Daya ta saki wani karan azaba Wanda ya Tunkudo dasu Umma Daga Shashensu suka iske Dina kwance Cikin jini bata Numfashi Hankali Tashe suka Fasa Ihu Allah yasa Sadiq yana Gida bai je wajen aiki ba Bayajin Dadi Shi ya Daukesu Zuwa asibiti Bayan ya kama ma su Umma sun kamata sun sakata a Mota Zulaihat Bata Gida Tana makaranta Zainab ce kadai agida Ta tsaya wajensu Anun da suke ta kuka Ganin Halin Da Dina take ciki.
Ba tare da Tunanin komai suka kawota asibitin Saulawa Kuma akaci sa"a Dr Imran ne ya karbesu yayi mamakin ganin Dina acikin Halin Mutuwa ko Rayuwa kuma bai yi mamaki ba Daman Dr.Aisha Tataba gayamai Dina Tayi aure ta auri Zain Abun ya bashi mamaki Taya YaDina da Zain zasu yi aure ba wani Labari Lokacin Suna Tare da Zakiya Ya Taba mata mganar Ta tabbatar mai da Tabbas hakane toh Lokacin da aka kawo Dinan ya kara Tabbatarwa ganin su Umma ne suka kawota.
Halin Data ke ciki yasa ya Kira Dr Haddir ya sanar dashi Wanda Saboda Rudewa ma Su Umma sun manta da Haddir da Zain din anan asibitin suke aiki,sai da suka gansa kwatsam Kofar emergency Bai Tsaya yi musu mgana ba ya Shiga Dakin Halin Daya ga Dina ya Razana shi Jini Ya yanke mata sai Zuba yake Cikin Ikon Allah kuma Ta Farfado ammh sai Sambatu take Dr.Imran da Dr.Aisha suna ta Kokarin Tsaida Jinin Kallo Daya yayi mata yasan Cikin Jikinta ya samu mtsala ganin Ya Jirkice kuma Jini ya Yanke mata akwai yuyuwar ayi mata Tiyata Cikin lokaci kafin ayi Biyu Babu.
Cikin Tashin Hankali ya Fito yana Tambayansu su Umma garin yaya haka ta Faru.?Nene ke gayamai Faduwa Tayi suma suna Daga Shashensu Sukaji Ihunta Koda sukaje sun isketa kwance Cikin Jini Bai tsaya Sauearansu ba ya Nufi Office din Zain Cikin Damuwa.
Ya iskeshi yana Tsaka da Duba Patient Cikin Tashin Hankali yake gayamai Abunda ke Faruwa Tashin Hankali Sosai ya bayyana Cikin Idanuwansa ya Mike da Sauri suka Fito Daga Office din Sa Haddir namai bayanin Abunda ya Fahimta game da Hadin da Dina ke Ciki Hankali Tashe yayi ma wata Nurse mgana kan ta kwashi Folder din Dake kan Tuber dinsa Takai ma Dr.Peter shi Zai Tafi Emegercy ne.
Cikin Gaggawa suka karisa Kofar Emergency din inda su Umma Suke Tsaye Hankula tsshe bai ko Tsaya yi musu mgana ba ya Danna Cikin Dakin ya iske Dr.Aisha Da Dr.Imran nata Kokarin Tsaida Jinin Dake Zuba Daga Jikin Dina ammh Abun ya gagara Dr.Aisha na ganin Zain Ta Nufeshi Tana Fadin"Yauwa Dr.gwara Daka zo Matarka Ta Fadi ta Bugu Cikinta Jini ya yanke mata ina Tunanin Yaron Dake Cikinta Shima ya samu mtsala Me zai hana ayi mata Tiyata Domin Ceto ta ita da Abunda ke Cikinta.."Yana Jinta Tana mgana Kokarin Saka Handglop yake cikin Tashin Hankalin Ganin irin Halin Da Dina ke Ciki Zuwa yayi ya Fara Dubata yana gani Domin bai Zata ma Tana Numfashi ba ammh Yana Zuwa Kusa da ita Ta Bude ido Cikin Azaban Ciwo Hawaye na Zubo mata Tace"Zainn....!
Kuri yayi mata da ido Yana kallonta Sai ya samu kansa da Riko Hannunta a karo na Farko Yana Fadin"Gani anan Dina..Kada ki Damu yanzu zan Miki Tiyata insha Allahu Komai zai zama Normal.."Wani Mirmishin Dayafi kuka ciwo Dina Ta saki Kafin Ta kara Damke Hannusa Tana Fadin"Ina Zaina Take..?cikin Mamaki Zain yace"Zaina Tana Gida Dina..Ki.."""
"Don Allah ka Kiramin ita..Ina son mgana da ita ne.."Da Sauri Zain yace"A"a Tiyata zamu shiga Dake yanzu..Ki bari in Komai ya Daidaita zan Kirata Tazo Kuyi mgana.."Da Sauri Dina Tace"A"a Dom Allah Nidai kakiramin ita Ina son na ganta In har baka Kirata ba yanzu bazata zo ta sameni ba Lokacin Dakake mgana ba.."Ba Zain kadai yaji Mganar ta Dakesa ba Har Haddir da Dr.Imran da Dr.Aisha sai da sukaji wani iri
Cikin Sauri Zain ya Kara Damke Hannun Dina Yana Fadin"Ki daina Fadin haka..Bazaki Mutu ba Insha Allahu zaki Tashi...Dr.Imran Ku shirya kai da Dr.Aisha zamu shiga Tiyata.."Yafada yana Kokarin Sakin Hannun Dinan Ta kara Damkewa Cikin Haawaye Hade da Mukurkusu Take Fadin"Don Allah ka Kiramin ita..Ka kuma Kira Daddyna ka Fadamai Yazo mu gana in muna da Rabon ganawa In kuma yazo ya iske gawata Don Allah ya yafemin Nima na yafemai Duniya da Lahira.."
Sai ga Zain najin Gabadaya Kalaman Dina na Neman sakashi Kuka Haddir ma Dake gefe Ma sai da Zuciyarsa ta Tsinke Cikin Dauriya Ya kalli Zain yana Fadin"Plz ka kirasu..Komai zai iya Faruwa fa.."Yafada Cikin kauda kansa Daga kallon da Zain yake Binsa Dashi waigawa yayi yana kallon Dina wacce ta sakarmai Mirmishi Lokaci Daya Hawaye suna kwarara ta Gefen Idanuwanta Cikin Karaya da Sanyi Jiki Zain ya Fita Daga Dakin su Umma namai mgana Hannu kawai ya Daga musu gefe ya koma ya Kira Wayar Zaina Sai da ta kusa Katsewa ta Dauka Bacci ma take ya tasheta Ta Fara mai Shagwaba sai Taji yanayin Muryansa ba Dadi kafin Ta Tambayesa yace Ta shirya Tazo asibiti yanzu ga Halin Da Dina ke ciki ai sai Zaina Ta Fara kuka nan da nan Tace gatanan Zuwa Daga ita sai ya Kira Kwamishina Abunda ke Faruwa Cikin Rudewa yace gasunan zuwa Hankali tashe yake Gayama Hajiya Batula ga Abunda ke Faruwa Daman yana Gida Ranar bai je ko"ina ba.
Zaina Ko Kaya bata Sauya ba Rigar Barci ne Doguwa ajikinta Ta Zura Dogon Hijabinta Ta Fito Bata tsaya Hawa Motarta ba Ta Fito Ta Hau adaidaita Tanimu megadi nayi mata mgana Bata ma kulasa ba Hankalinta yayi gaba Koda ta isa Har an Shirya Dina Za"a Shiga Da ita Tiyata Allah ya Taimaka alokacin Jinin ya Tsaya Ta iske Dinan an Gungurota Sanye da kayan Tiyata Ta Rike Hannayen su Umma Tana ta kuka Tana Rokonsu Gafara Sai ga Zaina Tana ganinta Ta Dinga mikamata Hannu ta kama Da Sauri Tana Fadin"Gani nan Dina ..!
Dina Na Jin kamar Ranta zai Fita ta Damke Hannun Zaina Tana Fadin"Naji Dadi Da kikazo Lokaci bai kure mana ba..Zaina Ki yafemin Abunda nayi Miki Domin inaji ajikina Raina ya kusa Barin gangar Jikina.."Zaina Data Fara kuka ta kamkame Hannun Dina Tana Fadin"Ni bakimin Komai ba Dina Wlh in ma kin min na yafe miki Duniya da Lahira..Kuma Ki daina Fadin Zaki Mutu Insha Allahu ba zaki Mutu ba.."Dina Ta Runtse ido Hawaye suka Kwaranyomata Tayi Mirmishi Cikin Karfin Ciwo Tace"ayyah..Lokaci ya Riga ya kure Zaina..kedai alfarma Daya nake Rokonki Dashi Shine ko Bayan Raina ki Zame ma Arman Uwa Zain ya Zame masa Uba Don Allah kada ki bari yasan Cewa Bake bace Mahaifiyarsa ba, ina Rokon ki ko Bayan ya Girma kada ki Fadamai Ni mahaifiyarsa ne saboda Bazan so yaji Labarina da Ta Hanyar dana Samesa ba Don Allah Zaina Ki Rike Arman Ki Hadasu dasu Anun kada ki Taba Rabasu ki Zamemai uwa ta gari wacce Zai yi alfahari da ita Har Karshen Rayuwarsa.."Ba Zaina ba Hatta su Umma sun Fara kuka Zaina kuwa sai ta Duke Tana kuka Tana Fadin"Ki Daina Fadin haka Dina..Bazaki Mutu ba Insha Allahu Tare zamu Reni Arman.."Dina Ta kara Rike Hannun Zaina Tana Fadin"Ki Min wannan alkawarin Zaina na gayamiki Lokaci ya kure.."Nan da nan Dina ta Fara Shakuwa sai kuma Jinin ya kara yankewa yana Zuba Da Sauri zain Ya isa Wajen yana Riko Hannun Zaina Zai Rabasu Dana Dina ammh suka ki Sakin Juna Dina Cikin Azaban Fitan rai Tace"Zaina kimin alkawari..Kimin Don."Bata karisa ba zaina tace"Nayi miki wannan alkawarin..Nayi alkawarin Zan kula da Arman kamar ni na Haifeshi kuma ba zan Taba bari ya gane niba Mahaifiyarsa bace.."Dina na jin Haka ta saki Mirmishi jin Dadi kafin tace'"Nagode Zaina.."Daga Haka Ta kauda kai Zain ya Rike zaina Dake wani kuka ya mika Hannunta ga Umma shi kuma yabi Bayan Nurses din da suka Tura Gadon Dina zuwa Dakin Tiyata Dr.Imran da Dr Aisha suma Cikin kayan Tiyata suka Rufa musu baya Hakama Zain Haddir ne kadai bai Shi ga ba ya Tsaya Daga waje suna Shiga suka Turo kofa.
Ko Gama Shiga Dakin basu yi ba Dina Ta Fara wani kakari Dukkansu suka Dakata Cikin Tashin Hankali Zain ya Fara Fadan Su shiga da ita yaji Dr.Aisha na maimaita mata kalmar Shahada sai ya tsaya Cak Tunda yaji kalmar Dina Ta karshe Tana Fadin"La"ila ha"illahu..."Daganan bata karisa ba Ba mala"ikun Daukan Rai ya Zare mata rai sai idanuwanta suka Kafe ko"ina na Jikinta ya saki Dr.Aisha Ta saka Hannu ta Rufe mata ido Tana Hawaye tace"Allah ya Jikanki Dina...Allah ya karbi Shahadanki..Kin Rasu kina Dauke da Juna Biyu Allah yayi Miki Rahma.."Dr.Imran da Sauran Nurses da Jikinsu ya gama yin sanyi suka amsa da Ameen Domin duk sun san Dr.Dina Tayi aiki a asibitin Tare dasu barin ma Dr.Imran Dayaji Jikinsa yayi sanyi Sosai.
Zain kuwa wani irin Dum yaji Daya Tabbatar da Dina Ta Rasu sai ya juya kawai ya Fice yana Zarw Safar Hannunsa Cikin wani yanayin Da shi kadai Zai iya Fassarashi ya Fito su Umma suka Taso suna Tambayanshi ya ake Ciki..? bai tsaya wani Tunani ba ya Bude baki yace"Sai Hakuri Umma..Allah yayi ma Dina Rasuwa.."
Ai sai gabadaya suka Dauki Salati Haddir ya Dafe kai yana Salati Shi da Sadiq Umma da Nene sai kuka Zaina kuma Jikin Umma ta Zube Tana Sakin Kuka Da dukkan karfinta Zain Office dinsa ya wuce Ya Dauki wayarsa ya Kira Abba ya gayamai Abunda yake Faruwa Abba yaji Abun kamar Daga sama sai ya Fara Salati Zain da Kansa ya Kira Hajiya Mama ya gayamata itama Sai ta Fara kuka da Salati yace kada ta taho yanzu zasu Taho da gawan nan Gidan Alhaji Tsoho ayi mata Sallah Bayan Sun gama wayar take gayama Alhaji Tsoho Shima yaji mutuwar nan yace Allah ya Jikanta yana ta Jera mata Addu"o"in Dacewa.
Kafin kace kwabo Rasuwar Dina yaje kunnan kowa,Baban Kaduna da Daddyn Abuja Haddir ya Kirasu ya gayamasu sukace dukkansu suna Tafe Insha Allahu,Zafeera Dake kano Taji Rasuwar nan tace Zata Biyo Inna Rukkayah su zo Tare,Inna Hannatu kuma tace sai gobe Goggo Halima kuma Zain ya Kirata ya gayamata Tace gobe Tana Tafe kowa sai Fatan Dacewa yake ma Dina.
Cikin Lokaci kadan Aka saka gaawan Dina a Ambulance zuwa Gidan Alhaji Tsoho Sauran kuma suka Biyo bayansu a Motoci Suna zuwa Gidan kwamishina na isowa sai dai ya iske gawa Allah Sarki yayi Tawakkali addu"a kawai yayi mata su Hajiya Batula ne keta kuka,Kwamishina da kansa ya Kira Hajiya Maimuna Daga Sudan ya gayamata Rasuwar Dina Sai kuka Tana Tambayansa Bata da lafiya ne..? Yace Mata Ajali ne yayi kawai.sai Hakuri Chan Sudan Da Hajiya maimuna Ta sanar da Labarin Rasuwar Dina Hankula sai ya tashi masu kuka nayi masu Sharan Hawaye da Tagumi Duk sunayi nan da nan Hajiya Maimuna ta Fara Neman Visan Da zata Taho.
Zain kuwa Ba wanda zai iya cewa ga yanayin Dayake ciki,Ammh Shi kadai yasan yadda Rasuwar Dina ya Dakeshi Zaina kuka Take har suka iso Gidan Alhaji Tsoho Zainab da Umma ta kira wayarta Ta Fada mata Itama sai kuka Zulaihat kuwa Sadiq Kadai ya Tuna da ita yaje ya Daukota Daga makaranta Daganan ne yake Fadamata Rasuwar Dina Itama sai Hawaye Shiyasa Gidan Alhaji Tsohon ya wuce da ita Zulaihat ita ta kira Farida Ta gayamata Rasuwar Dina Farida Taji Mutuwarta Sosai Ta kuma san Tabbas Zaina Zatayi kukan Rashin Dina.
Ba"a Sallaci gawan Dina ba sai Da akayi idar da sallar Mangariba kana aka yimata Sallah Bayan su Babban Kaduna sun iso Goggo Halima da Hajiya Mama da Tabawa sukayi