Author : Jamila Janafty Category : Romantic Hausa Novels
Tafi ba Ta Dauki waya ta Kira Haddir Tana mai Shagwaban gasunan zasu Tafi sai yace ta bama Zaina wayar ta karba ya Roketa su zauna gayinan zuwa in yazo sai su tafi kada su bar Zafeera ita kadai Zareena naji ta Faramai Tsiya yana Jinta ya Datse sai Wajen Biyar ya Dawo Zareena ta Tasashi da Tsiyarta Bai biyemata ya kyaleta Yaji Dadi Dayaga Zafeera Harda Girki Tayi yana ta ma Zaina Godiya yana Shaida mata Zain ya kusa Dawowa Domin jiya sun yi waya ya gayamai kadan ya Rage ya kamallah Cikin Karshen watan nan ko Sabuwar wata yana Tafe Zaina acikin Ranta Tana Fata Da kuma kaguwa tasaka Firstlove acikin Idanuwanta Ta Rokeshi Gafara ko Allah yasa zai yafeta sai da yaci abinci yayi wanka ya sauya kaya yazo ya Dauki su Anun yana Musu wssa har sun saba dashi.
Sai Wajen 6pm na yammah suka bar Gidan Har wajen Mota Haddir da Zafeera suka Rakosu suna Daga Musu Farida Tana ganin Girman wannan Ahalin kowa nasu ne tunda suka zo ba wanda ya nuna musu wata kyama da sukaje gidan Alhaji Tsoho haka suka Dinga Hira da Hajiya Mama da Alhaji Tsoho kamar sun san juna afakaice kuma suna ta mata Nasiha sai bayan Isha"i suka Tafi bayan Alhaji Tsoho yabama Farida Jarka guda na Ruwan addu"a yace ta Dinga Sha tana Shafawa ajiki Ta karba Tana ta Godiya Koda suka koma Gida Umma nata Fadan sun kai Dare awaje ko Tsoron Su Anun su kamu da Mira basa yi Zainab nata Dariyan Umma ta jikokinta take ji.
Farida Ta yi ma zaina mganar Tafiyarsu ita kuma tagayama su Umma Abba Dayaji da kansa ya Kira Alhaji Tsoho ya gayamai Shi kuma yace Su bari sai Zainullhi ya Dawo bai sako mgabar komawar gida ba yace kafin nan Insha Allahu da kanta Zata nemi ta koma da yarda Allag Jin Abunda Alhaji Tsoho yace batayi gaddama ba Domin Tsohin yana da kima acikin Idanuwanta Bangaran Zulaihat kuwa ko ajikinta Domin Tabbas Nan ma Gida ne awajenta.
Bangaran Uwar mata kuwa Tafiyar Farida tagama Daga mata Hankali Hatta da Alhaji Badamasu bai san Farida ta Tatafi Bauchi saiDa suka zo ta Fadamai ya Tada hankalinsa kan zai Biyota ta Dakatar dashi Shidai ya Fadamata yana Sonta in ta amince zai aureta ita kuma tace Bazata auresa ba su Cigaba da Harkan Bariki kawai Uwar Mata Hajja Zabba"u ta Kira ta gayamata Abunda ke Faruwa ita ta Zugata su koma Wajen malamin Da yayimata aiki kan Farida aikuwa suka koma ya yi Dube Dubensa cikin kasa yace Tabbas Zaina ba alheri bace Zata Hanata Dawowa kuma zata Rabata da Harkan Gabaki Daya Ammh kada ta Damu zai mata aiki Farida Zata Dawo da kafarta Cikin Farinciki suka Zube mai kudi suka Tafi ya kwashe kudinsa ya Soke yana Musu Dariyan wawaye Domin ba aikin da zai Dakatar da Farida komawa ga ahalinta Domin suma Chan basu zauna bA suna ta addu"an Allah ya bayyana Musu ita araye ko amace.
Zaina sai da Tayi sati da Dawowa garin Bauchi Zainab Ta rakasu Gidan Laila,Ta wayarta Tayi musu kwatancen Gidan Zainab ta Kirata zata zo bata gayamata Zaina ta Dawo ba ashe ma itama Lowcost Take zaune Tare suka Tafi da Zulaihat dasu Anun Farida ce kadai Tana Gida Tare da Zareena da suka Zama kawaye Sosai.
Karamin Falt ne gidan Laila Ita Tazo ta Bude musu karamin Get din gidan ba karamar Girgiza Tayi ba da ganin Zaina Kafin su Rumgume juna suna Murna sai kuma kuka Laila Tayi murna Tayi murna kanar mene ta Dauki su Anun ta Rumgume Cikin Farimciki Bayan sun shiga Cikin Gidan ne ta Daga waya ta Kira Mamanta ta gayamata ga Halima har ta bata sukayi mgana Tana yi mata barka da arziki Tace zata zo har Gidan bayan nan ta Kira mijinta ma"aikaci a Hukunar Ruwa nan da nan sai gashi Tace mai ga Halima nan ya zauna yana Ta murna yana gayama Zaina Tunda ya Hadu da Laila Damuwarta Dayace na Rashinta Shiyasa yaasan Labarinta Zaina Sai hawaye Domin Ta Tabbatar da laila mai kaunarta ne nan ya Dauki Su Anun yana yi musu Wasa nan Suka barsu suka Shige Ciki Zaina na bata Labarin Rayuawar Datayi bayan Barinta Gida Laila Tayi kuka kuma Ta jinjinama Farida ta kara Gayamana Zaina kada ta bari ta koma Zaria Daganan sai Gida Zaina tace Insha Allahu nan Laila ke bata labarin Haduwarta da Mijinta Ahmed bayan Barinta Gida,Da irin yadda ya nace sai da ayi Auran ammh ita duk ta gama Sakewa da Namiji Zaina tace Wlh ta Daina Daukan haka Kaddara ce abunda ya Faru da ita da kanta Take Fada Mata Zain ya auri Dina Har tana da wani Cikin Laila Tayi matukar mamakin ganin Zaina wannan karon ta iya Daukam komai da kanta Sabanin Baya Lalle Rayuwa kenan ko Zaina bata goge kan karatu ba ta goge kan Harkan Rayuwa.
Zaina Tana ta Tambayan yan Course dinsu Laila na gayamata Zaina Taji Hawaye Lokaci da Laila tace zasu Shiga aji Hidu ne yanzu sauransu shekara Daya da wani abu su kamallah Zaina ta Murmusa tace bakomai indai da Rabon Karatu Zatayi Domin bata Cire rai ba nan suka Wuni sai gabda mangariba suka Tafi Bayan Laila ta cika su Anun da kayansu Choculate Daman aikin su kenan Shan Zaki Abba ya Siyo musu Faruq ya Siyo Musu zainab Tsaraban kenan bayan ta Dawo Daga makaranta.
******
Bayan Sati Biyu..!
Bayan Sati da Biyu da Bayyanar ZAINA abubuwa sun Daidaita Farinciki ya wanzu a Duka ahalin Alhaji Tsoho Zafeera da Haddir kuma Satin suka Fara Cin Amarcinsu Domin Ta bada kai Bori ya hau Rayuwarsu suke gudanarwa Cikin Farinciki da kaunar Junan da basu san yauahe suka Fara ba.
Zaina kuwa ta kwantar da Hankalinta kamar ba ita ba sai kara kiba take Farida kuma bata kara mganar komawa Zaria ba kuma tana amfani da mganin Alhaji Tsoho kuma Alhamdulillah da alamun Nasara,Su Anun an zama yan Bauchi sune Dakin Umma Dakin Nene Shashen Abba su Shiga nan su Fita su da Arman Har Shashen Dina suna zuwa watarana Har wanka take musu Tana so yaran Sosai haka kawai Allah ya Doramata Sonsu Zaina bata Taba Shiga Shashen ba Duk da nan ne Shashen da iyayanta suka Zauna ammh bata Taba Shiga ba sai in Dinar taShigo Gaida su Umma su Hadu su gaisa Abun na bata mamakin ganin Zaina Ta zama wata babar Mace ko mganarta ma ta Manya mata ta koma sai dai in Tayi Laakari da inda ta zauna da kuma Tunanin Ta Haihuwa Idanuwanta sun kara Budewa.
Zulaihat kuwa bata da bakunta ba wanda bata saba dashi agidan ba Hatta Abba ma kuwa Haka zasu zauna dasu Faruq afalo suyi ta Hira suna Dariya Sadiq ne bai Cika Hayaniya ba ammh Shima yana Sakin Jiki Haka Ahalin suke basu nuna kyama ga wanda Yake Bako Duka Daya suke Daukan kowa.
Zain kuwa yana waya dasu Umma ba kuma Wanda ya Taba gayamai Zaina ta Dawo,an barshi yarda Alhaji Tsohon yace sai dai kila yaji ajikinsa Domin ya gayama Umma Hankalinsa ya Dawo Gida baisan Dalili ba ya kira Alhaji Tsoho ya gayamai ya kamallah Abunda yakaisa nan da Sati Biyu zai gama Komai yana Tafe Alhaji Tsoho najin haka ya kira Abba sukayi mgana yace Su Umma su je Chan gidan Zaina Su gyara a Share ko"ina Domin da Zain ya Dawo Aranar ya wuce da Matarsa da ya"yansa Gidansu yakwashe Tsawon Lokaci Cikin Wata kewa wanda zaina ce kadai Zata Gusar mai da wannan kewar Hajiya Mama tace Shawarace mai kyau.
Abba na komawa Gida ya gayama su Umma sukace ai ba Damuwa Nene tace Zataji da gyaran Gidan Umma Taji da gyara yarta Umma tace Taji bakomai Tun adaran Abba ya Kira Zaina ya gayamata Halin da akeci na dawowar Zaina Cikin Sati Biyu Da kuma Shawaran Alhaji Tsoho Duk Dokinta sai Taji ya koma Ciki CikinLadabi ta amsa ma Abba Umma kuma su Zareena da Farida Taje ta Fadamawa sukace Hakan yayi wannan Tunani mai kyau ne.
Washegari kuma Tun Safe Nene da Farida da Zulaihat da Zareena suka Tafi Gidan Zaina Suka Fara gyara sun iske Cikin kayan abinci akwai wadanda suka Lalace irinsu Dankalin Turawa,da Kwai da Sauran haka acikin Fridge kayan Miya Duk Sun Rube har sun Fa Wari suka kwashe komai suka Zubar suka wanke Wajen suka Fara gyaran Gidan Daya yi kura Domin an Dade ba"a Shigo ba Tanimu Megadi kuwa baki yaki Rufuwa Da Nene ta gayamai Gimbiyan Dakta Zata Dawo sai yammah suka koma Gida suka gayama Abba Abubuwan da za"a kara Tunda Daman yace su duba in akwai abubuwan da babu suyi mgana Kayan abinci wasu basu Lalace ba ammh Wasu kam sai Bola Abba yace Shikenan za"a Cika Store Din Insha Allahu.
Umma kuwa Goggo Halima ta Kira ta Shaidamata Halin da ake Ciki Tace Shikenan zata aiko da Isuhunta da kayan gyaran da Zata Hadama Zaina din Umma Tayi ta Godiya kana suka yanke Kiran Umma dai Daga bangaranta Ta Fara sakata Tana Shiga Cikin Ruwan bagaruwa Data Dafa mata da Sakata Shan kayan Marmari da madara da Zuma,Zainar ta Fadamata Data Haihu Farida ta mata amfani da Ruwan bagaruwa Umma ta Jinjina ma Farida duk da Karancin Shekarunta Ta yi ma Zaina Jego mai kyau.
Abba ya bada kudi an Cika ma su ZainaStore da kayan Abinci da komai na Bukata kuma an Sauya mata Sabbin Labulai da Zannuwan gado sai wasu kayan Kitchen kayan Daki ma Abba yaso ya Sauya kayan Gidan Gabadaya sai Umma tace Ya bari Zuwa gaba Tunda basu Lalace ba,kwana Biyu da mgana da Goggo Halima Isuhu yazo da Sako Dagachan bai kwana ba ya Juya leda Cike da Tsumin mata sai Turaran Jiki dana Daki,sai Gumbar nasha da Madara da kuma Hadin Zuma kaya dai da yawa,nan da nan Umma ta kimkima takai Dakinsu su Zaina tace nan da kwana Goma Zata Shanyesu Duka ita dai Zaina ba Mgana Domin Tagama Sarewa Da samun kamar Umma sai antona.
Dina Duk bata san meke Faruwa ba Taga dai ana ta Shige da Fice sai da Ta Tambayi Zainab Ta gayamata Ranar tayi kuka kamar me ta kara Tabbatar ma kanta Zain bai Dauketa a mata ba Tana Dauke da Cikinsa ammh Ko Sau Daya bai Taba Damuwa da ita ba sai dai Bata Damu ba ta Riga ta sani Allah ne ya kamata Tunda wajen Cikar Burinta ta saba mai Shiyaasa ya barta da Daburanta Tana Tunanin gashi Zaina ta Dawo bata Bakinciki Sai ma Taya zain Murna Datake Tana Tunanin Kila in Zaina Ta kasance Tare Dashi Kila zai iya yimata wani kallo Na arziki ko ba na Soyayyah ba.
Shiryan Shiryan Dawowar Zain kadai ake tayi Umma Har mai Dilka ta kira Tayi ma Zaina Domin tace kamar Amarya Haka take so amaida mata ita,Zaina ta Kara kyau Fatar ta da Murje Sai Sheke take Ita kanta Tana Jin Sauyin yanayi atare da ita saboda magungunar datake Sha Ba wanda take so da Muradin gani irin Firstlove Zafeeraa Tazo Gida Sau Daya Haddir ya kawota Taga Zaina ta koma Amarya ai sai ta karkace kai Tana Sakin Guda Zaina na Hararanta su Farida na Dariya Abba ya Dinkama Zaina sabbin Dinkuna Har da su Farida da Zulaihat su Anun kuwa Haddir yace shine Uba Shi yaje dasu Shida Zafeera sukayi musu Shoppig din kayan sawa dana ci Zafeera kuma taki Tafiya tace sai Zain ya Dawo Zasu koma Duk da Daman Sun samu Hutu ne.
Har Satin Biyun Ta kare ammh Ba"aji Daga Zain ba sai ranar jumma"a Da Daddare Zain ya Kira Wayar Haddir yace Zai sauka Nageria gobe da Karfe 5pm na yammah zai Sauka Ta Lagos In ya sauka zai Hau Jirgi zuwa Abuja in ya sauka yazo ya Daukesa Jibi kenan Haddir yayi murna Sosai yayi mai Fatan Sauka Lafiya nan Zain din fadamai Abunda ma ya Tsaidashi Wata Takardan ya Tsaya karba ammh yanzu komai ya Zama Ready.
Suna mgana ya gayama Zafeera ita kuma ta kira su Umma ta gaya musu Umma na jin haka ta Saka aka Kira mai Kunshi akayi ma Zaina Washegari kuma taje akayi mata gyaran kai Zaina ta Fito kamar Amarya su Umma basu Damu da sanar da Dina ba Tunda suna Tunanin suna mgana ta waya Sai da ta Shigo ne Taga Nene ta Soya Nama take cema ya Shirin Taran yaronta gobe,Sai Dina ta Fara kame kame ammh sai tayi Fuska kawai ta basar Nene ta Fahimci wani abu sai dai Bata Nuna mata ba Koda Dina ta koma Shashenta Tayi kuka Kafin ta Share Hawayenta Ta tashi ta Dan gyara Gidan ta Raasa wa zata Kira sai ta Kira Hajiya Batula ta gayamata ita kuma ta bata Shawara tayi Girki ta kuma ci gayun Taran Megidanta kada ta Damu da komai.
Jin Haka yasa ta Fara Shiri Direba ta aika kasuwa yayi mata Siyayyah ta waya ta Duba Girkin Tayi Farar shinkafa da Miyar ganye mai nama sai Kunun Aya ta kuma soya kaza Tayi pepe,Kuma Alhamdulillah Tayi ba Laifi Kunun Ayan ne Zainab ta Taimakamata sukayi Tare,Bayan sun gama ta koma Tana gayanma su Umma Ba wanda bai ji yaji Tsausayin Dina ba Shiyasa da Umma ta kawo Shawaran ko su maida zaina Gidan Gobe da safe ne kawai in Zain din ya Diro ya sameta Chan da Abba yaji sai ya gayama Alhaji Tsoho Shi ya Hana yace su Duba fa su gani yana da wata Mata kuma in sukayi haka basu yi ma Dina adalci ba Domin in Zaina ya ga Halima ya Tabbata Dina Zata Dade bata ganshi ba Tunda Tana da Hakkin akansa abari Zuwa ya kwana Biyu sai su maida Zainar Dakinta Hakan Shine adalci Jin haka yasa kowa yayi Na"am da mganar ammh Banda Zafeera Datace ya kamata Abar Masoyan gaskiya su Sake bai kamata ayi musu haka ba.
Koda Jirgin su Zain ya sauka afilin Jirgi na Nmadi Azikiwe International Airport,Abuja su Mama Safiya da Daddyn Abuja suna Zaman Jiransa zain yayi Kiba ya kara Fari Sai kuma kasumba Daya bari Yakara Girma alamun ya samu Hutu da jin Dadi,Dagashi sai jakar kayansa Sai kuma Wata jaka Da yayi ma Firstlove Tsaraba Sai su Umma dasu Abba sai Arman Da kuma Abunda Firstlove ta Haifa yana ji ajikinsa Firstlve ta kusa Bayyana Soon.
Mama Safiya ta Rumgume Zain Hakama Daddyn Abuja Cikin Farinciki Ganinsa ya sauya kamar bashi ba,nan suka Dumguma Zuwa Gida Dakin Haddir Dake gidan ya Sauka su Lauratu nata Hidima Dashi sai da yayi wanka ya yi Sallolinsa yaci Abunci Suka zauna ana Hira Yabama Daddyn Abuja Labarin Chan,yana Sanar dashi yana so ya koma Yayi karatunsa na zama Consultant.
Barinsa sukayi Yaje ya Huta Saboda Gajiyan Tafiya bayan Shigarsa ne Dadyn Abuja sukayi waya dasu Abba inda suka gayamai Zain ya sauka Lafiya sai Gobe zai kariso Haddir ma Zain din ya kirashi Ya gayamai Shiyasa Washegari Tun Safe Suka Dau Hanyar Abuja Shi da Zafeera data matsa sai taje 10am suna Abuja Zain mamakin ganin Haddir yayi kiba ga Zafeera agefe Abun sai ya bashi mamaki yace Lalle Hadiru an samu Wajen Hutawa.
Basu Tsaya ba kamar Zain din yasan akwai abun mai mihummaci Dake jiransa suka Dauki Hanyar Abuja Suna Mota yana ji Zafeera na waya dasu Umma bai kawo komai ba Sai Wajen 3pm na Rana suka iso Bauchi Direct gidan Abba suka Wuce Suna yin Hon Gabadaya su Umma suka yo Haraban Gidan,Zaina Dake Dakin Umma anyi mata Makeup wacce Kawar Zainab tazo tayi mata,Tana sanye da Doguwar Shadda Gezner Taji Stone Work sosai Anyi mata Dauri ta Dauki Kyau Sosai kamar ba ita ba su Anun ma sunci gayunsu Abba ma yana gida bai je aiki ba Sadiq,Faruq,kowa dai yana Gida ita kanta Dinar ta Shirya Cikin Doguwar Rigar material Saboda Cikin Jikinta,Arman ma yaci gayunsa Tunda Da Safe kafin su Haddir su wuce Abuja sun Biyo Ta gidan shiyasa ta san an Tafi Daukosa.
Tunda Zaina Taji Hon Taji ta Rasa Natsuwarta Sosai Jinin Jikinta sai ya Dauke na wani Lokaci kadan nan suka barta suka Fice Zuwa Haraban gidan su Saudart nata Ihun murnan ga Yaya Dakta.
Tunda suka Shigo Haraban Gidan Zain ke Cikin Farinciki ganim Duka Kannensa da iyayansa suna Jiran Saukarsa Saboda su Tareshi,Nene da kanta ta Bude mai Mota Tana mai oyoyo Rumgumeta yayi yana Fadin Neneta,kafin ya isa ga Umma itama ya Rumgumeta Daya bayan Daya yabi ya Rumgumesu Abba ya Dafa kansa yana mai Addu"a su Jalal Duk sun Nanikemai ya Daga Arman sama yana mamakin Girmasa Dina na gefe tamai Sannu da zuwa ya amsa yana kallonta Daga sama Har kasa ya kauda kai Su Zulaihat da Farida na Baya rike da Anun da Anan sai Lokacin Zain ya kula dasu Da Farko mamakin Bakin Fuska Daya gani yafarayi sai dai kuma su Anun sun sa ya kasa mgana ya Daskare Tsaye Sanye da Riga da wando Blakt and White Sai Doguwar Bakar Rigar Data kaimai Gwiwa da kuma Hula Fecing Cap Dinsa Farida sai da Taga Zain ta Tabbatar da Su Anun shi suka Debo kyau na Dukan kyau kenan.
Zain ya Daskere yana kallon su Anun kawai yama kasa mgana Kowa ya kalli Inda yake Kallo Nene Taje ta karbo su da kafarsu tace su Taka su Tafi Wajen zain suna zuwa gabansa yaji kafafunsa sunyi Rauni yaji ya Durkushe gabansu Yana Binsu da kallo Nene ta Kallesu su Anun Tana Fadin"Anun da Anan ku Je wajensa ABBANKU NE..!
Mamaki ya kara kama Zain Dayaji kalaman Nene ya Dago Daga kallonsu Anun Cikin mamaki bai samu Zarafin mgana ba Umma tace"Dauke su mu Shiga Ciki Zainullahi zaka ga Komai da idanuwanka..."
Jikinsa sai ya Fara rawa Sai da Nene ta Turamai su Anun yaji ya Rumgumesu Tuni yaji wani Natsuwa ya kamasshi Bai kawo cewa Ya"yan zaina bane ammh Yaji Soyayyarsu ya shiga ransa Sosai ya Rumgumesu ya Mike Tsaye Dauke dasu Abba yace su Shiga Cikin Gida sai komai ya Biyo Baya yana Dauke dasu Anun ya Riko Hannun Arman suka Nufi Cikin Gidan Dina Dataji Hawaye ya taho mata Tayi Saurin Sharewa Ta Bi bayansu Umma.
*Janafty...*
8/10/21, 6:44