Author : Jamila Janafty Category : Romantic Hausa Novels
gefen Gadon Ta Jingina Tana ajiyar Zuciya Tana Tuna sanda Taje bayi Tayi Kakin jini kenan ciwon Zuciyanta yana neman Tashi kenan..? Ta samu wani Salama Saboda kukan da tayi.
******
Kamar yadda Zaina ta kwana tana Kuka haka Zain shima ya kwana yana kallon Duka Hotunan Zaina yana kuka kuka mai Cin rai da wani Muradi mai Girma,Wasikarta Tana Hannunsa awajen Haddir ya karba Da ita yake kwana da ita yake tashi ya gama Haddace Duka kalaman Zaina na Ciki In ya Tuna Zaina nada Ciki sai yaji Rauninsa ya kara Karuwa,Yana kuka kukan Tsausayin kansa da kuma Kukan Tsausayin Halin Da Zaina Take ciki Da kuma kukan Nadaman Abunda ya aikata ya Tabbata Da Bai Zama mai aikata Zina ba da Duk Haka bata faru ba Gashi yanzu Auransa da Dina Dole ana kuma Nufin da ita zai zauna..? Wlh Tun Da yake da Dina bai Taba Sonta ba Sai Sha"awarta To yanzu Faruwan haka ma yasa yaji kamar komai ya Fita kansa Baya son ganinta in ta Shigo gaishesa yaga wannan Cikin sai yaji kamar shima gobe a nemeshi arasa sai dai bazai yi Sanadiyar saka wani Raunin azuciyar iyayan nashi ba Ammh yayi alkawarin Da kafarsa da kudinsa Sai ya Nemo Firstlove Duk inda ya kamata acikin Duniyan nan sai ya Nemeta yaji ya Dauki Dukkan Kaddaransa Zai Tashi Tsaye Da kafarsa Ranar Monday zai Koma aiki Insha Allahu Tun Daga Ranar zai Fara yawon Neman Firstlove zai Fara da Cikin garin Bauchi Da kewayanta kafin ya Fita Zuwa garuruwan Dake Makota dasu Batare da kowa ya sani ba shi Zai je ya Dawo da Matarsa da Cikinsa Kodomin ya samu Natsuwa ammh ya Tabbata Matukar Firstlove bata Cikin Rayuwarsa kamar kawai gangar Jikinsa ne ammh Ruhinsa da komai suna Tare da ita ne.
Shima Daga Karshe alwalan ya Dauro yazo yana ta Sallah yana Rokon Allah ya Bayyana mai Firstlove aduk inda Take Ya kuma kareta ya Tsareta Har Zuwa Lokacin da Zai sameta,Haka ya Dinga addu"a yana kuka yana gayama Allah Shima nan kan Sallayar Barci ya kwasheshi.
****
Washegari da Safe Farida Tatashi kamar ba ita ba,Ammh Daga ganinta bata da Walwala Tea ta Hada musu suka Sha,Kana Zaina taci Sauran kazanta Ta Jiya Ta Dora da Maltina Tana ta Jin muryansu Suby a tsakar gidan ammh bata ji Motsin Zuly ba Ganin Tayi Zuru ne yasa Farida Tace Mata"Zuly bata kwana agida ba...Kacharalle yayi kawalinta karki Damu Zata samu Abunda Zataji achan kici ki Koshi Saboda bake kadai bace.."Jin haka yasa ZAINA taci Ta Koshi Ta Kora da Maltina.
Dukkansu sai da sukayi wanka yau Shigar Atamfa Dukkansu sukayi Cikin kayan Farida ne Zaina ta saka Tunda bata Siyamata Atamfofi ba sai dai kayan Kanti,Farida ita ta Share Dakin Tas ta kai Bolar Waje Zaina na jinsu Adamalle na Mata Gudan Da Kirari Sholloy ke mai kyau ce komai kika saka sai ya karbeki So suke ta sakar musu sai dai kuma basu samu dama ba Ta koma Daki ta barsu nan suna Gulamta da kuma Gulman Zaina Suna mamakin yadda Farida ke Ji da Zaina Da taki barinta Har yanzu Kowa yana ganinta da kuma mamakin yadda Uwar mata ta kyaleta basu san Farida Ta koma ta Tura ma Uwar mata Kashi Biyu Cikin ukun Abunda Take samu Wajen Maza Saboda Idanuwan Uwar mata yafi ta kan Zaina ya kuma Fita Domin Tuni bakinta ya Mutu Daman Burinta kudi ne kuma Sholly Ta Gama da wannan Bangaran.
Sai bayan Sun gama Komai kana Farida Ta ja zaina suka zauna kan gado Suka Tankwashe kafa wayarta ma kasheta Tayi Kana ta kalli Zaina Tana Fadin"Zan baki Labarina..Ammh keman alkawarin bazaki kuka Sosai ba..!
Da sauri Zaina Tace"Nayi..I promise Anty Farida.."jinjina kai Anty Farida Tayi kafin Ta Lumshe ido Ta Bude Cikin Sanyin Murya Ta Fara Fadin...
"Sunana Aisha Farida kamar yadda kika sani....
*Ki biya ki karanta Cikin Salama..Rashin Daraja ne ki saka kudi ki Siya Abu kuma ki Yadashi a waje..Mace mai aji komai nata mallaka ta ke bata Taba Jiran Abun Sata...!*
*Janafty...*
7/12/21, 9:14 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B20️⃣6️⃣*
*IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*
"Kuma ni Haifaffiyar garin Jahar Gombe ce,Mahaifiyata Ummu Salma wacce muke Kira da Mami Yar Gombe Ta uwa ta Uba Mahaifina Alhaji Abubakar Shehu Dan asalin Jahar Jemeta ne Dake Yola,Kinga kenan Mahaifiyata Bafullatan Gombe ce Mahaifina kuma Bafullatanin Jemeta ne Ta Gaba da Baya ni din na gaji Fullanci Ta ko"ina.
Mahaifina Alhaji Abubakar Shehu Wanda muke Kira Abba Su Biyar ne wajen Babansu,Mata Biyu Maza Uku,Baffa Haruna ne babba sai Abbanmu sai Baffa Umaru sai Goggo Fatu,sai Goggo Zaliha su Uku Dakinsu Daya Wato Goggo Zaliha da Baffa Haruna da Baffa Umaru Tsohuwa Gita ita ta Haifesu mu kuma Abbanmu da Goggo Fatu Tsohowa Kaltume itace Mahaifiyarsu.
Tun kafin Rasuwar Mahaifinsu ya kafasu Tunda asalin Babban Gidansu Gidan yan Boko ne Ko alokacin Alhaji Shehun ya Rike mikamin Manaja a ma"ikatar Nepa Ta Jemeta Shiyasa su Abba suma suka Kasance masu Ilimi ammh su Goggo Fatu Suna Gama Sakandiri ake aurar dasu.
Dukkansu suna Jemeta da Zama ne Illah kawu Umaru Dake Zaune da iyalansa a Yola yana aiki da gidan Ruwa na Jahar sai Abba Dake aiki a hukumar Inec ta Garin Gombe,kuma ma agarin Gomben yayi karatunsa anan ma ya Hadu da Mamin mu har suka Daidaita sukayi aure.
Mun Taso mun ganmu muna Rayuwa acikin Katon Gidanmu na Zamani da Wadata Dake anguwan New gra Gombe,Dani Da kanwata Zahra mu kadai Iyayanmu suka Haifa kuma suka Dauki Dukkan Wani Soyayyah suka Dora mana Alokacin gaskiya matsaloli sun Taso kan Rashin Kara Haihuwar Mami har su Baffa Haruna suka matsa sai da Abbanmu ya kara Auran Anty Yahanatu muna Kiran ta Anty Toh itama Tazo ammh kuma Bata Taba Haihuwa ba sai Dangin Abbanmu suka Fahimci Abun badaga Maminmu bane Daga Abbanmu ne,sai sukayi Shuru da bakinsu shi kuma Abba ko ajikinsa Yana ganin Tunda Allah ya bashi mu ya gama mai Komai.
Tsakanina da Zahra ba wani Tazaran Nisa sosai Domin Mami Sai da ta Shekara bakwai da Abba kana ta samu Cikina wanda Tun ina Ciki nake ganin gata iri iri Daga Bangarori Da Dama,Lokacin da nazo Duniya kowa ya Shaida da Kanwar Abba nake kama Wato Goggo Fatu Wacce ke aure nan cikin Garin Jemeta Mganar gaskiya Kamana da ita ya baci yadda kikasan itace ta Haifeni Hatta Tsawona Idanuwana irin Nata ne komai da komai wannan Dalilin yasa Allah ya Dasa ma Goggo Fatu kaunata Sosai acikin Zuciyarta Musamman Saboda ni Take Dauko Kafa Daga Jemeta Zuwa Yola saboda Ta ganni Saboda itama Allah bai bata Haihuwa da yawa ba Da"nta kwara Daya ne Dal aduniya Musbahu Har Mijinta ya koma ga Allah sai Mutane ke Tunanin ko sun yi Gado ne Wajen Tsohuwa kultum Tunda itama su Biyu kadai ta Haifa Har ta koma ga Allah.
Ban kai Shekara Daya da Haihuwa ba mami ta samu Cikin Zahra,sai da suka je asibiti Likita yace bakomai acigaba da Shayar dani in nakai Shekara Daya da wata uku sai ta yayeni haka kuwa akayi Ban ma kai ga Cika Da wata ukun ba aka Cireni A Nono Ranar Goggo Fatu Tazo Ta ganni Ina ta kuka nakin Cin komai da aka Damamin sai Taji Tsausayi na tace In har Abba ya yarjemata Zata Tafi Chan Jemeta ta yayeni Abba kuwa da Mami suka Hado mata kaya suka Bata Tatafi Dani Jemeta Tafiyar da Ban Dawo ba kenar chan nayi Rayuwata Har na Girma a Hannun Goggo Fatu kuma Ita ta aurar dani Takaini Har Dakin Mijina Allah Sarki Allah ya Jikanki da Rahma Goggo Fatu..!
Farida Ta Fada Tana Share wasu Siraran kwallah Dake Zubomata kafin ta Cigaba da Fadin
"Na zauna agidan Goggo Fatu Cikin gata da jin Dadin Rayuwa Tun ina rigima har nazo na Saba da ita,Goggo Fatu taci kashina Taci Fitsari na Komai nawa itace Mami kawai Wahalan Cikina Tayi da Naguda na Dana cika Shekara Biyu sai Abba ya nemi da na Dawo Gida ammh sai Shakuwar da mukayi Da Goggo Fatu yasa Mami tace a kyaleni na Kara Girma lokacin ma har an Haifi Zahra wannan Dalilin ne yasa sai bayan na Fara Girma ne ma na Fahimci ba Goggo Fatu ta Haifeni ba.
Na Taso Gidan Goggo Fatu Ni da Da"nta kwara Daya mai Suna Musbaha Lokacin Mijinta nada Rai Domin kamar ina primary 4 ne Allah mai yamai Rasuwa sakamakon Hadarin Mota Lokacin Ya Musbaha yana Bording School a yola yana kamar Shekarar Fita Daga Sakandiri School bayan Rasuwar ma Abba yaso na koma Gida Goggo Fatu ta Fara Kuka kan in ya Rabata dani Bazata ji Dadi ba Musbahu ne kuma yana makaranta Ni kadai ce nake zaune da ita Wannan kukan na Goggo Fatu yasa Abbana yace ya bar mata Ni Duniya da Lahira sai dai Mami Taji Labari Daga Baya kuma Bata Nuna komai Domin Tana da kawaici da kunyar Fulani.
Haka Rayuwa Ta Cigaba da Tafiya Da Dadi ba Dadi,Duk da Mahaifin Ya Musbahu ya Rasu ya bar Tarin Dukiya su Abba basu bar Goggo Fatu haka ba Duk wata suna Cika mata Store da kayan Abinci Shi kuma Baffa Haruna ya Dauki Nauyin Cigaba da karatun ya Musbahu Bayan ya gama Secondary School Lokacin ni kuma na gama primary Section.
Duk a lokacin Gida Daya muka yi Rayuwa bana wani Sakin Jiki da Ya Musbahu Tunda bai Cika zama agida ba sai dai in ya Dawo Hutu koda kuma ya Dawon Kullum yana Cikin Dakinsa yana karatu,ni kuma Allah bai yoni Rayuwa mai Kirniya ba Tun ina karamata Nake da Hankali Koda yaushe indai ina Gida ina Tare da Goggo Fatu a Kitchen ina Koyon wasu Abubuwa awajenta Tsakani Dashi Gaisuwa ne da Girman Tsakanin Yaya da kanwa.
Lokacin Daya gama Sakandiri School dinsa sai yace shi baya son Zuwa kasar Waje kamar yadda Baba Haruna yaso ya Tafi ammh Yana Sha"awar karatu a BUK dake kano Wannan Dalilin yasa Zamansa agida bai Dade ba aka gama mai komai ya Tattara ya koma kano da Zama Gabadaya yana karantar Engnearing..!
In kika ga naje Gombe nayi kwanaki Har Wajen sati Daya sai dai in Goggo Fatu ce ta matsamin Muka Tafi Tare sai Ta koma ta barni na kwana Biyu wajen Iyayena Tunda suna mata kawaicin ammh Suma suna son Zama Dani Musamman kanwata Zahra,Mukan je Jemeta Family House din su Abba Dani da Goggo Fatu Ko kuma in wani Sha"ani ya Tashi Mukan je kuma Gidan Baffa Haruna Duk da shi Daman Hatta su Goggo Zaliha basu Damu da Zuwa ba Saboda Matarsa mai Suna Salamatu Suna Kiranta Mommy.
Matan Baffa Haruna Uku ne kuma Mommy ce ta Biyu ammh kamar ita ke Fada aji acikin Gidan Baffa Haruna yanada Kudi Tunda Dan kasuwa ne Dake Shigowa da kaya da kasashen Ketare,Duka ya"yan Baffa Haruna Maza ne macensa Daya ne Zubaida kuma itace ta Uku kuma Diyar Mommy ce ita kadai Gareta Zubaida ba Sa"ata bace Sa"ar Zahra ne ta Girmi Zahra dai da kadan sai dai Tana da Girman Jiki Shiyasa Har ta Kamoni a tsawo,itama Din Fara ce Doguwa mai kama da Mommy sak tunda itama Bafullatan Adamawa ce chan ya Aurota Cikin Fulanin Daji Shiyasa ake Zargin Baffa Haruna ma Ba Banza ta barshi ba Shiyasa baya ji baya gani sai Mommy da Zubaida Domin gatan Dayake yi mata Ko ya"yansa Maza bai nuna ma wannan Gatan Sauran Matansa Kuwa Hakuri kawai suke ammh kamar Hoto suke agidan Mommy ce Matar so kuma Matar Gida.
Tun Tasowar Zubaida ta kwaso Duka Halin Mahaifiyarta Mommy ga rawan kai ga Fi"ili da kuma Isa da Takama Tun Tana karama Take ji da kanta da Nuna ita din Watace Babanta nada kudi kuma Tana makaranta mai Tsada Tana saka kaya mai Tsada Ko cikin Dangi Ta Shiga ta Rika ma Kowa kallon Kashi kashi kenan ko Su Goggo Zalihan Batabari ba Gata bata da kunya Ganin Yarinta Tare da ita Shiyasa ba wanda yabi Ta kanta Da kuma ganin yadda Baffa Harunan bayason Laifin Zubaida komai kankantarsa.
Tun asali Daman Jinina Dana Zubaidaa bai Taba Haduwa ba Ta Tsaneni Nima na tsaneta Ko Haduwa mukayi Family House din su Abba a jemeta Tsakanina Da Ita kallon kallo ne Domin Tana Jin Haushi yadda Kowa ke yabona wajen Natsuwata da Hankali Da kuma Rashin kwaramiyaniya,In tazo Haka ya"yan yan"uwa suyi ta Shige mata ammh Ni kuwa kallo Bata Isheni ba Ina Tare da Goggo Fatu ko In su Mami sun zo Ina Tare da Zahra ko kuma Tare da Saratu Diyar Goggo Zaliha wacce Sa"atace.
Ashe Abun na Matukar Bakantama Zabaida rai Ganin Ina nuna nafi karfin na Dinga mata mgana ni kuma ganin ita Din ba Sa"ata bace shiyasa bana Shiga Harkanta uwa uba kuma Rashin Kunyata ganin har ManyaBata bari ba Bazan Taba manta Dalilin Daya sa Goggo Fatu Har ta Koma ga Allah bata Kaunar Zubaida ba Shine akwai Wani Lokacin da Bikin Diyar goggo Zaliha ya Tashi Duka Dangi an Hadu agida ana ta Sha"ani Ni da Goggo Fatu mun zo ita ma Zubaida sun zo Ranar Bikin Fada ya Hada Zubaida da Zahra Har ita Zubaida ta Dibi kasa ta watsa ma zahra afuska Mu muna Cikin Gida Ni da Saratu Tunda Lokacin muna yara bamu Zama yanmata ba Tunda muna Jss1 ne alokacin.
Ni da Saratu muka Fita mukaje muka Tarar da Zubaida da Zugan kawayenta sun Tarun ma Zahra sai na Shiga na Raba ina Tambayan Zubaidan me ya Hadasu Bude bakin yarinyar sai ta kalleni Tayi Tsaki Tana Fadin Ni kuma awa..? Wai ni a yayar Zahra..? Dama basu san komai bane Ance ba Goggo Fatu ta Haifeni ba ammh kuma da ita nake kama ba Mami ba,waya sani Ko Goggon Fatun ce Mamata ta Gaskiya alokacin Data Fadi mganar karaf akunnan Goggo Fatu Taga Fitarmu Tabi yi sawu,ShineTana Zuwa Taji Abunda Zubaida Take Fadi gabadayanmu kuma muka Zura ma Zubaida ido Cikin Mamakin kalaman Zubaida.
Goggo Fatu da Ranta ya baci da kalaman Zubaida Tana Zuwa batayi wata wata ba ta Tsinka mata mari Ta Dungure mata kai Tana Fadin karta kara Jin wannan mganar abakinta in ba Haka ba sai tayi mata Dukan Tsiya,Yin haka keda wuya Zubaida ta Saka kuka Har Da Birgima Tana Kiran sunan Mommy nan da nan Jama"ar Cikin Gidan sai gasu a Haraban Gidan Goggo Zaliha Mommy na Zuwa Hankalinta Tashe Ta Kama Zubaida Ta Tada ita Tana Faman Tambayanta wa ya Daketa Bude bakin Zubaida sai ta Nuna Goggo Fatu Tana Fadin Ita ta Daketa bata mata komai ba Daga Suna Fada da Zahra sai gani nazo na Shigar mata ina ta Dukanta Shine goggo Fatu na Zuwa itama ta mareta.
Goggo Fatu ta saka Salati Tana kallon karamar yarinya da makirci Jin Haka yasa Mommy ta Fara Bala"i har tana Zagin goggo Fatu wai kan wani Dalili Zata Dakar mata ya" ai ya bata fi ya,ba sai gayan mganganu Take har Matar Baffa Umaru da Anty Yaha suka Shigar ma Goggo Fatu Wacce ta Fara kuka da cin Mutumci da Mommy ke mata Fadan ya koma kanta Nima Jikin Goggo Fatu na Koma ina kuka ganin Tana kuka,Mami ita ta Kira su Abba awaya ta gaya musu Abunda ke Faruwa Shi kuma yagaya ma su Baffa Haruna nan da nan sai gasu Lokacin Har Goggo Zaliha Ta ce Mommy Ta Tarkata yarta su bar mata gida ba"a auri Wata macen Daga wata Zuru"a tazo Tace Zata Taba mata yar"uwa ba Bata isa ba.
Kalaman Goggo Zaliha sukayi Zafi Mommy na gayan mganganu Ta zari mayafinta Rike da Hannun Zubaida Zasu Tafi sai gasu Abba nan fa aka Fara Maida Zencen Abun mamaki Mommy na ganin Baffa Haruna Ta fara kuka Zubaida nayi Hankalinsa ya tashi ya Nufeta yana Tambayan Ba"asi Goggo Zaliha namai mgana bai iya Saurareta ba Mommy yake Saurara Tana kuka Tana Fadin Goggo Fatu ce Ta Daki Zubaida bata Mata komai ba Saboda Ni,Shine Saboda Tazo Tayi mgana Cikin lumana Matar Baffa Umaru da Anty Yaha suna ta Zaginta Har goggo Zaliha Tana ce mata ta bar mata gidanta ita da yarta Tana Fada Tana kuka,Abun mamaki maimakon Baffa Haruna ya Tsaya yayi Bincike a"a sai kawai ya Fara Fada yana Zagin Goggo Fatu yana Ce mata Meyasa Zata Daki Zubaida a kaina..? Mganganu dai na Cin Fuska da Cin Zarafi kamar ba yar"uwansa ba ya tsaya ma ya Saurari su Goggo Zaliha yaki itama Daga baya Fata fata yayi mata ya kuma ce Duka iyalansa su Tattaro su Tafi Tunda Haka Goggo Zalihan ta Bukata nan fa Gidan Biki ya koma wani iri Baffa Haruna bai Saurari Kowa ba sai Mommy ita kuma ta kulla Abunda zata kulla ba wanda ya Hanashi Tafiya Suna Tafiya Goggo Fatu na kuka ta kwasheni muka TafiGida Duk da Rokon da su Abba sukayi ta mata ta Tsaya Bakincikin Abun yasa ta kasa Tsayawa
Har muka koma Gida Tana Sharan Hawaye Tana Jinjina Abun Wai yau ace Dan"uwanta ne zai ci Zarafinta saboda Matarsa da yarsa Lalle Duniya ce Tundaga Lokacin Goggo Fatu ta Fita Sha"amin Gidan Baffa Haruna Shi kanshi sun Dade basa wani gaisuwan Zumunci sai Da su Abba suka Hadu suka Sulhuntansu Ammh Goggo Fatu Ta Rike Abun acikin Ranta ta kuma Daina Zuwa Gidan Baffa Haruna Ballatana wani Hulda ya Hadata da Mommy da yarta suma ba ZUWA suke ba sai Kowa ya Zauna a matsayinsa.
Kwanshi Tashi ba Wuya awajen Allah Ina SS1 Ya Musbahu ya gama Digree dinsa ya Dawo Gida Daman In ya samu Hutu bai cika Zuwa ba kano yake Zamansa Tunda shi ba Mutum bane mai Hayaniya Lokacin Da aka Turashi Service dinsa jemeta aka Turasa A hukamar Lantarki ta Jahar Dalilin haka yasa Baffa Haruna yace ya Koma Gidansa ya zauna tunda ma"aikatar Tana kusa da Gidan ne, hakanFiyemai ya kama Haya ba yadda zai yi Domin Shi Musbahu asalinsa Bamai son Hayaniya bane ko Gidan Goggo Fatu bai cika zama ba Ballatana wani Gida,Dalilin yana Jin kunyar Baffa Haruna yasa ya Koma Gidansa da Zama aka Ware mai Daki Guda Da ababen More Rayuwa.
Tun Dawowar Ya Musbahu Gidansu Zubaida Shikenan Tunda ta kyalla Ido Ta ganshi ya Shiga Ranta Dama ganinta