Chapter 29 Reading Zainazain Book 2 Complete By Janafty Arewa Novels

Zainazain Book 2 Complete By Janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   29 / 37

84K to 87K   out of 108.5K words

Direba ya Sauke bayan ya Sauke Duka kayansu akwatinsu ne Daman ta Rika Jansu Tana Shiga dasu Haraban Gidan ganin bazata iya Dauka ba yasa ta barsu nan Cikin Faduwar gaba da wani Fargaba ta Nufi Falon Hajiya mama Lokaci Daya kuma Tana Tuna Ranar da Ta bar Gidan a irin wannan Lokacin


Da Siririyar sallamarta ta Shigo Sanye da nikabinta Turus Tayi ganin yadda Falon ya Cika Abba Umma,Nene Alhaji Tsoho,Goggo Halima,Hajiya Mama,Mama Safiya,mom iklima,Baban kaduna,Dadyn Abuja zainab,Shema,Zafeera,Zareena Da kowa Dake Falon ya Sakarmata ido Sai taji kafafuwanta sun Fara rawa ta kasa ma Daga kwayar idanuwanta Saboda Rauni da wani kunyar da suka kamata.

Umma Ta Mike Dauke da Anan bakinta na Rawa tace"Ina ji ajikina yata ce..Halima ce....Don Allah ki Bude Fuskarki Ko hankula Zasu kwanta.."Zaina da kuka yaci karfinta Kafafunta na rawa sai da ta Duke kana ta Saka Hannu ta Cire Nikabin Fuskarta ta Bayyana Gabadaya sai Falon ya Kaure da Kabbara.

"Allahu Akbar..Itace Wlh..Zaina...Halima..Sa"adiyace.."Hayaniya ta Cika Falon Atare Umma,Nene,zainab da Zafeera da Zareena suka isa ga Zaina sai Tajii Duka sun Duka Sun Rumgumeta Cikin kuka Ita dasu Anun din gabadaya suna Fadin"Alhamdulillah..Allah ya karbi addu"an mu ya Dawo mana da Halima Lafiya.."


Suke Fada suna kuka Suna Dariya Zaina ma kukan Take ta Rumgumesu Tana Fadin"Ku yafe..Min...Ku yafemin.."Kaawai take iya Fada tana wani kuka Dina Dake gefe ta Share kwallah Tana Hamdala Batayi Bakinciki da bayyanar Zaina ba Hakama Falon kowa ke Hamdala Goggo Halima da Hajiya mama sai da suka kai goshinsu kasa Saboda Godiya ga Allah Shema kuwa na Gefe Tuni har ta Kira Haddir awaya ta gayamai ai yadai jita ne bai yarda ba shima ya Kamo Hanya yana Fatan Allah yasa haka ne Tare yake dasu Sadiq dasu Faruq.

Zulaihat da Farida ma an manta Dasu suna Gefe suna kara Jinjina ma Tsantsan kauna da kuma Soyayyar da wannan ahali kema Sa"adiya ya wuce yadda ta basu labari.





*Ina Bukatar addu"anku kan Allah yayi min Zabin Alheri acikin Rayuwata In Abunda nake so acikin Zuciyata Alherina ne Allah ya Rikemin shi Ya Tabbatarmin da alheri ya Kauda Sharrin Dake ciki in kuma babu Alheri Allah ya Musanyamun da Abunda Zai zamemin alheri Duniya da Lahira Ameen Nagode..*






*Janafty..*
8/8/21, 1:27 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B22️⃣6️⃣*

*IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*



"Daga Umma Har Zafeera Haka suka Rirrike Zaina suka Taso da ita Zuwa Tsakiyar Falon kamar in suka Saketa Zata sake Guduwa ne Anun kuma da Anan Sun koma Hannun Nene da Zareeba sai kallon Kowa suke ganin sun zo Bakon wajen da kuma Mutanen da basu Taba sani ba.

Gaban Hajiya Mama da Goggo Halima su Umma suka Dire Zaina kowanne Fuskarsa Tayi Jage Jage da kukan Farinciki mara Misaltuwa Zaina ta Dago Tana kallon su Goggo Halima Tana Zubar Hawaye ta Rike Hannayensu Duka atare ganin Suna kuka Tace Cikin Taushin Murya.."Zaku iya yafemin..? Me nayi kenan..? na saka ku kuka fa.? Take Fada Tana jin wani irin Tahowar kwallah da kuka alokaci daya atare suka Rumgumeta Cikin Kwallar Farinciki Hajiya Mama ke fadin"Baki mana Laifin Komai ba Halima wannan kukan da kika ga munayi na Farincikin ganinki ne kin Dawo Cikin Koshin Lafiya Tare da Rabon da kika Fita Dashi acikin ki kin Dawo mana Dasu Suna kallonmu muna kallonsu wannan kadai ya Ishemu kukan Farinciki Halima.."


Zaina sai ta kara Volume din kukanta Goggo Halima ta Dago Tana Share mata Hawaye Tana Fadin"Bar kuka Halima..Allah ya Karbi addu"an mu..Allah mungode maka.."Take Fada Tana Share mata kwallah Zaina ta Kwantar da kanta kan Hannun Goggo Halima Tana Fadin"Goggo Ina su ya isuhu da Sauran Mutanan Gada..?!Nasan suma na sakasu kuka ko..?

Goggo Halima tace"Kada ki Damu yanzu zaki wanke musu Zuciya da Farincikin ganinki kin Daawo Cikin Koshin Lafiya sai dai ina Miki Fatan Allah yasa Kada Hakkin wannan ahalin ya kamaki Halima Sun Shiga Tashin Hankali Saboda Rashinki Ni kaina Wlh Halima kara nake musu ammh Sun kai makura.."Take Fada Tana Sharan kwallah Zaina Taji Rauninta ya kara Bayyana ta Kara Fashewa da kuka Tana Fadin"Ku yafemin..Wlh Nima Tunda na Tafi nake Cikin kewarku...Nayi kuka Har bansan iyaka ba,ba Domin na Hadu da masu kaunata ba da yanzu ban Dawo agabanku Cikin wannan yanayin ba.."


Abba ne ya karisa Gaban Zaina ya Dafa kanta yana Fadin"Ki daina kuka Sa"adiya mu babban Farincikin mu Daya kin Dawo Gida lafiya so sai mu gode ma Allah mu daina Tuna Baya.."Jin haka yasa Zaina ta gyada kai Tana Fadin"Abba ka yafemin..Nayi Butulci gareka...n.."Kai Abba ya girgizamata bayan ya Rufe mata baki ya Dafa kanta yana Fadin"Allah yayi miki albarka Sa"adiya.."Gabadaya kowa ya amsa da Ameen Haka Zaina ta Dinga su Baban kaduna tana Kuka Tana Fadin su yafemata Ana cikin Haka ne sai ga Haddir ya Shigo kamar an jehosa Sai da yaga zaina kana ya gasgata mganar Shema Alhamdulillah yake Ta Fada acikin Ransa Su Faruq kuma suna Shigowa sukaci karo da akwatin su Zaina su suka Daukosu suka Shigo Dasu Cikin Falo ba karamin mamaki da Murna sukayi ba da ganin Zaina ba Faruq ya kirata Cikin Zumudi"Ukti..'

Ta Juyo Tana kallonsa ta Mike Tatafi gareshi Tana Fadin"Ahki.."Rumgume juna sukayi Cikin Farinciki Faruq ya Dagota Hawaye sun Cikamai ido Yana Fadin"Ina kika Tafi kika barmu muna ta kuka,Ina kika je kikabar Umma Cikin Damuwar Rashinki..? Ina kika Tafi kika bar Ya Dakta Cikin Halin Rayuwa mara Dadi Ukti..?

Zaina Tana Hawayen Farinciki Take Fadin"Labari ne mai Tsawo Ahki..Ka yafemin kukan dana sakaka..Ya Sadiq sannunku Ya Haddir Ina murna fa.."Take Fada Tana kallonsu suna kallonta suke Cikin yanayin Farinciki Haddir kusa da ita ya karisa yana Fadin"Alhamdulillah..Allah na gode maka Daka Dawomin da Farincikin Aminina gida Lafiya Allah ne abun Godiya Allah ya sa karshen Wahalan kenan Zaina ta Zain.."Gabadaya Falon sai da kowa ya Murmusa Zaina ta Sunkuyar Dakai Tana son Tambayan Zain Domin bata ganshi ba Anun ta Fara kuka Tana Hannun Umma Hankalin sai ya koma kansu,Anun na Fara kuka Anan ta Fara ganin yar"uwata na kuka Farida Dake gefe ta kalli Zaina Tana Fadin"Daukesu ki shayar dasu Sa"adiya kinsan Rabonsu da Nono tun Safe fa..."Su Haddir ne wannan karon ke mamakin ganinsu Anun basu gama mamaki ba sai da su Umma suka kawo ma Zaina su ta Zauna ta Shige Cikin Hijabi ta Fara Shayar da Anun kana Sai da ta Koshi ta mikama Umma Ita Tana Fadin"Umma riketa Takwarki ce.."Umma da Farinciki yacika Ranta tace"Haka wacce kuka zo Tare tace..Nagode Diyata Allah yayi albarka.."aka amsa da Ameen kana Zafeera ta miko mata Anan Tana Dariya Hararanta Tayi tana yar Dariya Ta kara Shigewa Hijabi Tana bata Nono Gabadaya ita aka Sakarma Ido Haddir kuwa wani Farinciki ne ya kamashi yana Tunanin in Zain ya samu Labarin zaina ta Dawo har da Ya"ya Biyu Dayake Fadin yana Mafarkin Zainarsa ta Haifi Abunda ke Cikinta Tabbas So ba karya bane ya yarda ayau din nan.

Bayan Tagama Bama Anan Nono Ta Mikama Zafeera Tana Fadin"Rike Diyarki...Anan Maminki ce Zafeera..'Anan tabi Zafeera da kallon Rashin Sanin Kowa sai kallon yaran yake da Sha"awa Alhaji Tsoho ne yayi gyaran Murya yana Fadin"Bangane wannan wariyar ba Amaryata Halimatus Sa"adiya..?ni baki bani Ya"yana na Dauka ba..! Domin bana ce Tatattaba kunnina ba."

Gabadaya Falon kowa yayi Dariya Zaina Kunyar Alhaji Tsoho Take ji ta mike Tana Raba ido Umma da Zafeera suka kai mai su Anun suka Doramai kan Jikinsa Zaina ma ta Matso kusa Dashi Ta Zauna Tana Sharan kwallah Alhaji Tsoho ya kurama su Anan ido kamar yadda suke kallonsa yana Mirmishi wani Sanyi na Ratsashi Cikin Farinciki yake Motsi da bakinshi kafin ya Dafa kawunsu Daya Bayan Daya yayi musu addu"a kafin yace"Allah yayi muku albarka..Allah ya raya fatima Ib kika gado mai sunanki Kin yi sa"a Domin Fatima gatachan ita ce marikiyar Mahaifiyarki Halima Ke kuma Maryama Ki gado Hakurin Maryama Kinci Sunan Maryama mahaifiyar Halima ce Allah ya Jikanta Allah yasa Hallayarta na gari ya Bita Ita da Abdullahi da Mallam Umar da Marigayiya Atine Allah ya Hadamu dasu acikin Aljannar Allah.."Yake Fada Cikin Wani yanayi gabadaya Falon sai da kowa ya Share kwallah barin ma Zaina Data Ke ta kuka su Abba nata amsawa da Ameen


Alhaji Tsoho ya Kalleta yana Fadin"Bifa na bar auran nan Dake Halima..Na samu Sabbin Amare masu Jini ajika.."Dariya aka saka gabadaya suma kamar sun san Abunda yace sai suka Fara Dariya Farida da Zulaihat na Gefe Suna kallon Tsabar kauna da Soyayyar Tuni kewar Gida Dana ya"yanta ya Shige Farida Har tana Share kwallah Dina ma Tana gefe sai kuka Take Kuma ta rasa kukan Farinciiki take ko kuma kukan Dawowar Zaina sai dai Tana Murna ga ahalin nan da yau Allah ya Bayyana wacce Rashinta ke sakasu kuka Musamman Zain.

Alhaji Tsoho ne ya Lura ZainaTaki barin kuka ya muskuta Yana kara Rike su Anun yana Fadin"Halima ki daina wannan kukan hakanan Don Allah..Dukkanmu nan mun Riga mun yarda da kaddara mun kuma bar komai a Hannunsa Shi muka Dinga Roko Har ya amsa mana ya Dawo mana Dake lafiya.."Zaina ta kara Saka kuka Tana Fadin"Ina jin kunyarka Alhaji Tsoho..Tunda kafin nazo Duniya ka zama mai Alheri ga Kakanina da iyayena Har nazo Duniya kuka Daukeni kai da Duka ahalinku Kuka maidani yar Gata Kuka Sharemin Hawaye baku Taba sakani kuka ba,baku barni nayi kukan Rashin Gata ba ammh yau gashi ni na sakaku fa..Abba ya Fifita ni qsn Duka ya'yansa ya ki Firstlove saboda ni Alhaji Tsoho Umma Taki Abunda ta Haifa acikinta Saboda Ni Alhaji Tsoho Daga karshe na Nuna Butulci gareku na Tafiya na barku Wlh ina Jin kunyarku Inaji kamar Duk Duniya Tana kallona a matsayin Bulutu wacce bata san karaminci ba.."


Alhaji Tsoho ya girgiza yana Mirmishi yace"Ko Daya Halima..Tafiyarki wani Rubutattace ne Daga Allah..Allah ya Rubuta wadanan yaran ba anan garin Zaki Haifesu ba Cibiyarsu na garin Da kikaje kuma Kila Tafiyarki Allah yasan zai iya Warware wasu abubuwa Da Dama Duk da mun Shiga Damuwa Saboda rashin sanin Takamammen Ina zaki..? Wani Hali Kika Fada ammh ayau komai ya wuce Tunda gaki kin Dawo da kafarki kuma keda Abunda kika Haifa Cikin Koshin Lafiya Sai dai kawai muyi ma Allah Godiya.."

Kowa sai gyada kai yake yi alamun gamsuwa da kalaman Alhaji Tsoho Baban Kaduna ne yace"Ki Daina kuka Hakanan Sa"adiya yau din Ranar Farinciki ne garemu..Suma Da kika ga suna kuka na Murnan ganinki ne ki Dakata kukanan hakan kafin suma yaran nan su kama Domin gasunan sunyi Shuru suna kallonki kina kuka.."Sai Lokacin aka Lura dasu Anun Dake ta kallon Zaina suna Bata rai alamun suma suna Gabda Fara kukan Kowa Sai Kallonsu yake da Sha"awa Zafeera ce ta Duka tana Share ma Zaina Hawaye Lokaci Daya Tana Fadin"Ukti.Daina wannan kukan..Ki bari sai mun Shiga Ciki Sai na Dargagji Bakin ki Da kika sakani kuka.."

Zaina na Dariya ta Tsunguleta Cikin Farinciki Tana Fadin"Mara kunyar Amarya.."Hararanta Zafeera Tayi Tana zama kusa da ita Tana Fadin"Su Amare manya.."Wani kallo Zaina Tayi mata irin zamu gamo Dinan Hajiya Mama ce tace"Ke Halima nifa na Kosa naji Da kika bar gida ina Kika Je..?


Zaina Ta Dago Tana kallon Barayin da su Farida suke Tana Nemansu Sai ta gansu Chan Gefe da Hannu ta yafitosu suka Taso suka Taho Matsa musu Tayi saman Cafet din Tana Fadin"Ku zauna na Nuna ma Ahalina Wadanda suka Zama garkuwata su kuma bada Komai nasu saboda ni.."Tafada Idanuwanta na Cika da kwallah

Farida da Zulaihat suka samu nan kasa gefen Zaina suka Zauna sai kowa ya koma ya zauna irinsu Nene Dake Tsaye suna Kallon su Farida Tunkafin Zaina ta bada labarin har wasu sun Fara saka musu albarka acikin Ransu Zaina ce Ta muskuta Tana kara kallon Kowa Dake Falon har Idanuwanta suka Sauka kan Dina wacce ke gefen Hajiya Batula sun Dade suna kallon Juna Cikin Wani irin Fargaba Domin Zaina bata so Taji wani labari kan Dina Cikin Jikinta take kallo tana Wani Tunani Kardai ace Cikin Data bar Dina Dashi har yanzu bata Haihu ba..?

Farida ce ta Katse mata Tunani Da Fadin"Wai Sa"adiya Ina Firstlove ne..?Kamar ban gansa acikin wannan Taron ba kuma banji Kin Tambayesa ba..?

Zaina ta Dukar da kai Domin Tun Zuwanta Idanuwanta ke son ganin Firsrlove tana kewarsa Sosai Duk da Tana jin kunyarsa Alhaji Tsoho yayi gyaran Murya yana Fadin"Zainullahi Baya kasar nan Tun Wata bakwai da suka wuce ya Tafi india hallatar wani Course akan Harkan Fida,ammh Insha Allahu ya kusa kamallawa nan da wata Daya zai Dawo Da wannan nake Rokonmu Dukkanmu anan wajen munsan Halin da yaron nan ya Shiga Bayan Barin Halima Gida abubuwa sun Faru marasa Dadi ammh Alhamdulillah komai ya zama Daidai yanzu Kuma mun san Cewa Rashinta ne yasa yayi Nesa da Gida Toh In har ya samu Labarin Dawowarta na Tabbata kun Tabbata bazai bari ya Cimma abunda yakaisa ba zai Tattara ya Dawo kuma in hakan Ta Faru dukkamu bazamu ji Dadi ba da wannan nake Rokon kada wanda ya Fadamai Dawowar Halima mu jira Har yagama abunda yakaisa ya Dawo lafiya koma Menene sai yazo Daga baya.."

Kowa afalon yayi Na"am da Mganar Alhaji Tsoho Harta kuwa da Haddir Daya Tabbatar ma kansa Zain bazai yarda ya kara kwana agarin Delhi ba yau zai Taso Zuwa Gida Baban Kaduna yace"Tabbas Mganar Alhaji Tsoho mganace mai kyau..Saboda haka kada wanda koda waasa ya sanar da Zain Labarin Dawowar Sa"adiya.."Kowa yace Insha Allahu Bazai Fada ba Zaina kanta na kasa Jikinta Duk yayi Sanyi Jin irin Halin da Firstlove ya Shiga saboda Rashinta ga kuma Dina Wanda Ita kanta Tafi Tsayama arai Shin wai anyi Auranta da Zain ne ko yaya ne..? Itafa ta kasa gane komai.

Ganin Duk kowa ya Zuba mata ido ne ana Sauraranta yasa ta Fara Bada Labarin Ranar data bar Gidan Har Zuwa Haduwarta da Farida da duka Rayuwar Da Tayi agidan Uwar Mata Zuwa Tashinsu da komawarsu gyallesu da Haihuwanta Da Duka Rayiwar da tayi achan da Labarin Farida da Labarin Zulaihat Ta kareshe da Fadin"Anty Farida ta zama garkuwa gareni..Ta yarda ta Fita Ta bada Jikinta abiyata kudi Saboda Takula dani da Abunda ke Cikinta Tun su Anun na Ciki take wahala dasu har sukaxo Duniya Wlh Tallahi Ko da Da Rana Daya basu Taba wani maraici ba Komai na Rayuwarmu Ta kare mana shi..Tana da Ciwon Datake Bukatar Tsallaka wata kasa Domin nemab Lafiya ammh Saboda ni da Su Anun taki yarda taje Ko"ina Saboda ta Cika alkawarin Mikani ga Ahalina ga Zulaihat nan ita ta kasance wata Uwa ce ga su Anun Taci kashinsu da Fitsarinsu komai na Rayiwarsu ita take yi musu ni kawai sunan ni na Haifesu ne ammh Duka Wahalarsu Zulaihat ce da Anty Farida suka Dauki wannan Nauyin Tunda na Tafi basu Taba barina nayi kukan wani abu ba sai dai kukan Rashin ku da kewar Duka ahalina ammh ba kukan yau na Nemi wani abu na Rsaa ba ni kam dame zan saka musu..? Ku tayani nuna kauna da Godiya garesu don Allah.."Tafada Tana Hada Hannayenta Waje Daya kowa afalon kuka yake Zafeera kuka Share Share haka su Umma sun koka da Wannan irin Rayuwar da Zaina ta Fada ammh sun Godema Allah da Haduwarta da Farida Labarin Farida ya Tsuma Kowa Rashin gatan Zulaihat ya Taba Duka Zukatan su Umma Rauni Hardasu Abba.

Ita kanta Farida kai ta Sunkuyar Tana kuka Hakama Zulaihat Dina kuma,Kukan Nadama kawai take Tana Tunanin su da suka Zabi Bariki da kansu ashe akwai wadanda Rayuwar Barikin ma Ba"a son Ransu suke yinta ba wani Sanadi ne ya kawosu Cikinsu kafin kace me kalmar Godiya yabo Tare da Jinjina da addu"o'i ne ke karade Falon ga Farida da Zulaihat Hajiya Mama ta Rike Hannuwan Farida Tana Fadin'"Wannan Rayuwar ba ita ta Dace kamilar nace irin ba..Wannan Rayuwar bata dace da kamilar Uwa irin ki ba...Tun kafin naji irin Taimakon da kikayi ma Jikata Halima naji Kin Shiga Raina kidaina kuka da yardan Allah zamu sadaki da duka ahalimki kuma Insha Allahi Zubaida da uwarta sai sunyi mutuwar Wulakanci.."Nene tayi Saurin Cewa"Fade ma Bata baki Hajiya Mama na Tabbata yanzu sun ga Sakayyah.."


Hajiya Mama Ta kalli Zulaihat Tana Fadin"Ke kuma Kidaina kuka...Daga yau baki ba kukan Rashin Gata Daga yau kin Zama mai gata Kamar kowacce ya"Zaki koma ga Danginki Insha Allahu na Tabbata Larai Nemanki Ido Rufe take Domin Fadin Allah ne baka Taba Cin Hakkin Maraya ka zauna Lafiya..'


Mama Safiya Tace"Ina..Ai Tuni Allah ya Dade da Nuna musu Kuskuransu ammh Dai Zumunci ya Lalace awannan Zamanin.."Kowa sai Tofa albarkacin Bakinsa yake Alhaji Tsoho yayi Shuru bai ce komai ba sai da Surutun yayi sauki kana ya Fara mgana"Hakika Allah ne abun godiya kuma Shine Sarkin Duniya..Daman Tafiya akace mabudim Ilimi Daman kuma Kaddaran Haduwa dasu ne ya Fitar Dake Daga gida yau Dalilin haka mun san Labarin Wasu Mutane guda Biyu wadanda Labaransu suka Bamu Tsausayi kuma muka Dauki Wasu Darussa babu abunda Zance Face Allah yayi Muku Sakayyah da Gidan Aljannah Firdausi ke Farida da Zulaihat Allah Ya Jikanku kamar yadda kuka ji kan Halima Allah ya Tallafa muku kamar yadda kuka Tallafa mata sannan Daga Karshe ke Farida Zamu maidaki Gidan Wajen Danginki Da kafata zani Domin na an karar dasu kuskuran da iyayanki sukayi wajen aibataki wanda Tabbas Shiyasa Kika Fada Harkan karuwanci Domin Kaifi ne da bakin iyaye wanda yafi ma Kaifin Takobi.."Su Abba sai gyada kai suke alamun gamsuwa Hajiya Mama tace"Tabbas furucin Iyayanta akanta Shi yake Binta har yanzu..Kuma Shi ne Dalilin Fadawarta wannan Harkan.."Farida Dake kuka Ta Mike kamar Wata mahaukaciya Tana Fadin"Kuyi hakuri..Ban kawo Sadiya gabanku da Rokon ku maida ni ga Dangina ba..Duk da ina Jin kewarsu araina ammh Bazan koma ba Koda zan komai sai dai naje na Nuna musu Shedar Karuwancin da suka Kiramin ba inda zan koma Zan koma Zaria na Cigaba da Abunda suka kirani Dashi Har Abada bana Fatan su ji Labarina.."Daga haka kawai ta Kwashi Gudu Zuwa Dakin Hajiya Mama Kowa ya Bita da kallo.

Zaina da Zulaihat hankalinsu ya Tashi sun Tashi Zasu Bita Alhaji Tsoho ya Dakatarsu yana Fadin"Ku koma ku Zauna..Na Fahimci wani abu..Sihiri na Dawainiya da ita wanda ke kara mata Wutar abun aranta kuma yana Nesantata da Kusantan ahalinta koma yayane akwai wanda baya so

29 / 37