Chapter 23 Reading Zainazain Book 2 Complete By Janafty Arewa Novels

Zainazain Book 2 Complete By Janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   23 / 37

66K to 69K   out of 108.5K words

mai mgana ba Yayi kamar bai gane ba.

Yau da suka Cika Sati Daya da Aure Haddir ya Ritsashi Da Daddare acikin Office dinsa yace ko yana so ko bayaso sai Ya kaishi Gidansa yau ya gaji da yin wannan Wasan yar Boyen dayake yi ma Mutane Zain dai bai samu ta cewa komai ba yayi Kokarin yayi Zille ya Gudu Haddir ya Kasa ya Tsare suna Tashi Daga Cikin asibitin Gidan Alhaji Tsoho ya wuce dasu ya Sakashi Daki yayi wanka ya bashi Wata Farar shadda yace ya saka yace Wlh bazai saka ba Shi ba Farinciki yake ba Haka ya Lallabasa ya saka wata Shadda mai Ruwan kasa Daganan ya kaisa Wajen Alhaji ya Xayyanamai komai Alhaji Tsoho yaji Ransa ya baci ya Dinga yima Zain Fada da Nasiha wanda bawai bai ji bane yaji ammh Duka sun Shiga sun Fita ne yayi Riga yayi alkawarin yadda Dina Tayi sanadiyar Rasa Farincikinsa Wlh itama tabar samunsa har Abada.

Sadda kai yayi ya nuna bakomai Hajiya Mama tayi mai Fada soaai ta kuma gayamai Hakkin Dina yanzu yana kansa ne,Sai ya Kitaye ya nuna musu yaji Fadansu har da yi musu Godiya nan kuwa bai Dauki Ko Daya ba Suka Fita Alhaji Tsoho da Hajiya mama suna saka musu albarka


Da Haddir ya Daukesa bai Zame da shi ko"ina ba sai Tukubun Tsire shi ya Fita ya Siyo Tsire da Kaza da Lemukam Sanyi bayan ya Dawo ya bama Zain wai na Tarbam Amarya Zain ya Turbune Fuska yana ma Haddir wani kallo Kafin ya Kece da Dariya yana Fadin"Wacece Amarya din..! Dina..?
Yafada yana Dariya Haddir ya ijiye ledan nan gaban Motan yana Fadin"Ohon maka Dan iska kawai koma Wacece ai kafimi saninta ni Daga Taimako kada Allah yasa ka kaimata din
."

Ganin Haddir din yaji Haushi yasa ya Daki Kafadarsa yana Fadin"Sorry My Best Friend..!Haddir yayi banza Dashi kamar bai ji sa ba Ya Tada Motar suka bar wajen har suka kai Gidan Abba Ba wanda ya kara mgana.

Haddir yana gama parking ya Kashe Motar ya Fito Dole zain ya Fito yana wani Bata rai Haddir ya kallesa yana Fadin"Ina Ledan kazan..?

Zain yace"Baka Daukota ba Tana Cikin Mota.."Haddir yayi Tsaki yayi gaba yana Fadin"Au Daman ni kake jira na Dauko maka Kazan amarcin naka..? Lokacin da Zan rakaka Wajen Halima inace ba ledan na hannunka ba..?


Zain yace"Ita kace.Ita din Annurin Zuciyata...Dina fa.
! Itace wacce na Tsana aduk Duniya.."Haddir yace"Kai dai ka sani..zaka Dauko ledan ne ko na kama gabana..?jin kalaman Zain yasa ya koma Motar ya Bude ya Dauko Ledan yana wani Tura baki Suka wuce Haddir na kallonsa ta Gefen ido Yana mamakinsa aransa yana Fadin Daga baya kenan.


Kai Tsaye Shashen Da aka Saka Dina Suka Nufa Tunda Falon suke jin Kukan Arman Da Sauri Dukkansu suka karisa Falon Zain ya ijiye ledan na saman Center Table ya Shiga Cikin Bedroom din inda yake jin kukan Arman yana Shiga ya gansa akan gado yana kuka ya kusa ma Fadowa yayi saurin Daukanaa ya Rumgumesa yana Lalashi sai ga Dina ta Fito Daga Tiolet suka ci karo da Zain Dukkansu suka kalli juna Cikin wanu yanayi ita Dina na Faeincikin ganinsa ne shi kuma na Tsana ne Cikin Fada ya kalleta yana Fadin"Wani irin Iskanci ne Zaki bar yaro karami Shi kadai a kan gado yana neman Fadowa..?

Cikin Sunkuyar dakai Dina tace"Kayi hakuri..Barci yayi na kwantar Dashi Na shiga na Yi alwala Shine ya tsshi ya Fara kuka.."Zain dai Dogon Tsaki yaja ya Fice Dauke da Arman yana Fadin"Ki Fito Falo ga Haddir yazo.."


Da kallo Ta Bishi sai kuma ta saki Mirmishin Farinciki har Abada bazata Daina Son Zain ba Sallar ta Tada Sai da ta idar kana ta Fito Falo Cikin katon mayafinta su Dina an Zama musulmai,.
Ta iske su Dauke da Arman Haddir yako lafe jikinsa yayi Shuru sai wasa irin ta jarirai yake yi Kan Daya Daga Cikin Kujerun Falon ta zauna ta gaishe da Haddir ya amsa yana kallonta yana kuma Tambayanta Allah sa batayi Fushi ba..?

Kanta na kasa Dina ta Girgiza kai Zain na kallon Gefe yana jin kamar ya Daki Haddie ganin ya Dake sai bata Hakuri yake na Rashin kawo ango kan Lokaci Daga Karshe yayi musu Nasiha Kafin ya Mike ya mikama Zain Arman Dina Tana ganin haka ta Mike Tana Fadin bari ta Kawo musu abinci,Bata fara Girki ba Sai gobe Daga Shashen su Umma aka aiko mata dashi.

Haddir yace Alhamdulillah ya Gode Sallama yayi mata Ya Fice Zain yabi bayansa Dauke da Arman sun Dade suna mgana aharaban Gidan Haddir nata kara bama Zain baki kan yaji Tsoron Allah Zain kawai karkace kai kawai yayi yana Jinsa yana kuma kallonsa Adage ammh afili sai ya nuna ya Gode kuma zai Gyara,nan suka yi sallama Haddir ya Shiga Motarsa Domin Dare yayi wajen 9pm na Dare ko Shashin su Abba bai Shiga ba kuma sun ga Motar Abba alamun yana Gida

Sai da Motar Haddir tabar Haraban Gidan kana ya koma Cikin Gidan ya Iske Dina na Tsaye afalon tana Jiransa Batare da yayi mata mgana ba ya Mika mata Arman ta saka Hannu ta karba Daidai Lokacin da Hannayensu suka Hadu da Sauri ya Jaye hannunsa yana Jifanta da wani kallo na Komai Mayanta sai kin barni.

Ya juya yana Shirin Shiga Dayan Bedroom din yace"Ga Leda nan..Haddir ne ya mtsa sai an Siya.."Daganan yaja key din Motarsa ya Shige Dayan Bedroom din ya Banko kofa yana Tunanin Zai yi Lambo ne ya nuna komai Normal kafin Shirinsa ya kamallah bai da ko Jallabiya anan kuma Gashi Dare yayi Allah kaimu da Safe zai yi parking din kayansa Daga Shashen Abba ya kawo su nan zai Dinga zuwa yana kwana kada irin su Haddir su kara lura da bai kwanan Shashen ammh kuma Da kwanansa agidan da Rashinsa zai zama Duk Daya ne.










*Shakira...*
8/4/21, 3:29 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B22️⃣0️⃣*

*IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*

"Tunda ya Shige Dakin Dina bata kara jin Duriyar Zain ba Haka taja sanyin Jikinta ta Wuce Dakinta ta kwantar da Arman kana tazo Taja ledan Ta Bude taga abunda ke Ciki Bata da wani kwadayi abakinta sai ta Rufe komai ta saka Cikin Fridge din Dake Kitchen Wani yanayi na Shiga ranta Lalle Tsanar da Zain yayi mata ba kadan bane.

Komawa Daki Tayi wanka tayi tazo Kusa da Arman bayan ta saka kayan Barci,Tunanin Duniya duk ya isheta Ammh ta wanni Fanmi sai taji Dadi ko banza Tana jin kamshin Zain din acikin Gidan yafi Abaya da Baya kwanan Gidan Ta Dade batayi barci Ba Tana Tunanin mganar Dataji Hajiya maimuna sunayi da Nene inda Ana gobe za"a Daura musu aure da Zain take gayamata Shashen Da take Zaune yau aciki Aciki Iyayan Zaina suka Zauna ta Tabbata da abaya ne ko sama da kasa zassu Hade bazata zauna ba sai dai ina ayanzu bata da wani Zabi ko ahaka aka Tsaya ta Tabbata Zaina Taci gari.



Washegari kamar yadda ya Gudiri Niyya Tunda ya Fita Sallar asuba Tare da Abba da Sadiq da Faruq suka Dawo Abba nata sakamai albarka ko bai Fada ba yaji Dadin ganinsa Gidan kai Tsaye Cikin Gidan ya Shiga yabi Umma Da Nene Daki Dukkansu ya gaishesu Su Zafeera ne akitchen suna abun karyawa nan yake ji yau Zasu koma kano.

Dakin Sadiq ya shiga ya Tattara Duka kayan sa Duka Dayake Dakin Dama basu dawani yawa wasu Suna gidan Alhaji Tsoho wasu ma kawai zai sake siya,Kayansa Dake lowsoct kuma bai ma bi ta kansu ba Rabonsa da Gidan har ya manta Ko albashin Tanimu megadi Haddir ke Zuwa yana Bashi Shi Tunda Firstlove ta bar Rayuwarsa ya ji gidan ya Fita Ransa...

Kowa yaga Zain yayi parking din kayansa sai yaji Dadi ammh banda Zafeera da Zainab da suke Taya Zaina Kishi Nene kuwa Har waje ta rakashi Umma dai na Ciki ba fito ba Bayan sun Fito Haraban gidan ne yake Tambayanta waya kawo Motar Dina nan kuma Saboda yana ganinta ya gane Motar nan Nene ke gayamin Zakiya ta kawo mata Ranar da suka Rabu Baram baram kada kai kawai yayi Daganan Nene ta koma Shi kuma ya wuce Shashen Daya zama  Nashi yanzu.

Koda ya shiga Dina Tana Kitchen Tana Dafa Ruwan Zafi Domin Tama rasa me zatayi Tunda bata iya komai ba Shi kanshi Ruwan zafin don yana Ruwa ne,Taji Shigowar Zain da Sauri ta Fito tana gaisheshi ko kallonta bai yi ba sai da yakai kayan Dakin ya Fito yana kallonta yana Fadin"Ina Arman..?

Dina Tace Cikin Sanyin Murya"Yana Daki yana Barci..Ina kwana.."Zain bai amsa mata ya kada kai ya wuce Dakin Dina ta Bisa da Kallo wani Sanyi ya Shiga ranta na ganinsa da kayansa Ta Tabbata Kodai mgana mai Dadi bazai Shiga Tsakanibsu ba zai zauna agidan kuma zai kula da Dansa.

Da Sauri ta koma Kitchen Tana Kokarin ta Soya kwai kada Zain ya Fita sai dai bataci Sa"a Ba Tana Kici kicin Soya kwan wanda sai da ta kira Hajiya batula ta gayamata yadda Zata Soya nan ne ma Take shaida mata Gobe Hajiya maimuna Zata koma Sudan bata Cikin Hayyacinta yasa kawai tace zata kirata Hajiya batula bata Ji wani mamakin kiran Dina na ya ake Soya kwai sanin Ko Dafa Ruwan Tea ma Dina bata iya ba Gata yayi mata yawa.

Tana Kokarin Soya kwan Kawai Taji Fitarsa koda ta Fito ta leke ta window Ta Hango Fitar Motarsa daga gidan har yayi wanka ya Shiga kai kawai ta Kada wata Zuciya na Fadin Ki yi Komai saboda kanki kawai Dina Domin ko kanki Zaki Dafa awannan karon Zain bazai Dawo yana Miki kallon Mace ba.

Dole ta koma Kitchen din ta Cigaba da Soya kwan Wanda duk ya Kone bata iya ba karshenta kasa Ciyuwa yayi mata Sai watsa mai Ruwa Tayi Lokacin Taji kukan Arman ta Ruga Zuwa daki Duk ta Fige ta Rame saboda ta Fara Wahala ga Arman ga kuma na Gida,wanka Tayi mai ta bashi Nono yasha yayi barci itama Taje tayi wanka Ta fita Falo Tasha Tea kadai Tazo ta Dauki Arman ta Saka mayafinta ta Nufi Shashensu Umma kamar yadda Hajiya maimuna tace kullum da safe ta Rika Shiga Tana gaishesu kuma taji Nasihan kullim Tana Shiga da Safe su gaisa ko bakomai hakan yana ma su Umma Dadi Tunda Dinar ta Darajasu.

Lokacin Data Shiga ne ta iske su Zafeera na Shirin Tafiya Abba ya Fita Tun dazu nan falo ta zauna suka gaisa da Nene Umma Ma na wajen ita tama karbi Arman Dake ta Lumshe ido alamun barcin bai Ishesa ba,Yaron yayi Girma sai wayau yake abinsa Shema Ta karbesa Zainab Tana ta yi musu Hotuna Domin Arman yaro ne mai Shiga Rai Dina na Shashen Har su Zafeera suka Tafi Motar Haya suka Shiga Direba na Tare da Abba a office.

Sai da suka Tafi Tana Shirin baro Shashen Tunda Arman yana Wajen Nene ta goyashi ya koma Barci Sai ga Goggo Halima ta iso Daga gada su Umma suna ta ina suka sakata,Kwallah ya Cika idanuwanta sanda Nene ta kwanto Arman ta mikamata Tana kallonsa Tana Kara Jinjina Gudurin Allah Tana kuma ma Halima Fatan Allah yasa itama ta Haife Cikin Jikinta Lafiya

Goggo Halima Tayi tayi ma Arman addu"a da ita kanta Dinar Wacce taji duk kunya ya kamata Ta sani itace sanadin Tafiyar zaina ammh ko kadan Goggo Halima bata nuna mata ba, Ganin Arman din na hannunta yasa Tatashi Tatafi Shashenta Tana Tunanin me zataci yunwa take ji kamar Nene ta Shiga Ranta Ba Dadewa Zainab ta Biyota da abinci ta karba kamar an saka ta a aljannah Dama ta gaji ita ba iya Girkin nan tayi ba Batasan kuma Yaya Rayuwarta Zata kare ba Dambun Zogale mai Hanta Taci tasha Ruwa ta Hayr Bisa kujera ta kwanta Arman kuma na Chan Shashensu Umma nan barci ya kwasheta bata sani ba.

Da yamma Daga asibiti Haddir da Zain Gidan Alhaji Tsoho suka je bayan ya gaishesu ya kwashi Wasu Daga Cikin kayanshi Zuwa Gida Har ya shiga ya Fito Dina Bata sani ba Tana  cikin Dakinta ta Shiga Tiolet tadai ji Motsi kuma Tasan shi ne Daganan Shashen Su Umma ya shiga sai yaga Goggo Halima murna ta kamashi itama haka ya zauna kusa da Goggo Halima yana kallonta kamar yayi kuka ganin ta Goya Arman Tsab Tun Safen nan yana nan Shashensu Umma Sai ya fara kuka akaisa yasha Nino.

Zain najin Taruwar kwallah ya kalli Goggo Halima yana Fadin"Insha Allahu goggo sai kin goya ya'yan Firstlove da Wannan bayan naki insha Allah.."Goggo Halima na Sharan kwallah Tana Fadin"Allah ysa.Allah ya yarda Zainullahi Allah yasa zan ga wannan Ranar.."

Ta Fada Tana Sharan kwallah ba Zain ba Hatta su Umma sai da Jikinsu yayi sanyi Zain ya Kada kai yana Fadin"Ina ji ajikina Firstlove Tana nan Lafiya ita da Abunda ta Haifa kuma Zata Dawo gareni da Zarar Lokaci yayi.."Dukkansu Suka Bishi da kallon Mamaki kafin Umma tace"Taya akayi ka sani...?

Kansa na kasa yace"Ina yawan yin Mafarkinta kuma ayadda nake ganinta bata Cikin wani Wahalan Rayuwa kuma na ganta da yaro a hannunta acikin Barcina.."Ajiyar Zuciya suka Sauke Nene tace"Allah yasa haka.."Daganan suka Cigaba da Tattauna mganar Zaina har Abba ya Shigo Nan ya Tsaya suka gaisa da Zain da kuma Gogggo Halima ya Shiga Ciki Zain kuma Sai da ya Tsaya yaci Tuwon Shinkafa Miyar agushi da Nene tayi ya koshi Lokacin Arman yayi barci Goggo Halima Ta mikamai Arman din bayan yayi musu sallama ya Fice Zuwa Shashensu.

Koda ya Shiga Dina bata Falo Sai ya wuce Bedroom dinta Direct ya isketa Zaune gefen Gadonta Tana waya yaji Tana Kiran Daddy shi yasa ya gane da Kwamishna take mgana bai Tsaya ma Jiranta ba ya kwantar da Arman nan kan gado ya Fice Dina Ta Bishi da wani Kallo Wanda ita kadai ta san Ma"anarsa.


*****

*Zaria..*

Bangaran Zaina kuwa itama Tuni Tayi arba"in Daga ita har su Anun sun sauya sunyi Kiba Jajir dasu Zaina Ruwan Zafi ya amsheta Haihuwa ya saka ta Kara Budewa ta zama Babba Daga Faridan Har Zulaihat din tafi su Girma su Anun kuwa basu da mtsalan komai Domin Iyaye uku Garesu in Farida bata nan suna Tare da Zulaihat in kuma Ta na nan suna Hannunsu Sun Fara wayansu na Jarirai Turbarkallah Masha Allah.

Farida ce komai nasu bata kyashi Ta yarda ta Fita taje ta bada Jikinta abata kudi Saboda Hidimar Zaina da yaranta wadanda take gani kamar wasu alhalinta ga kuma Zulaihat da suka Riga suka zama yan'uwa Zaina akoda yaushe addu"anta Daya Allah ya karkata Hankalin Farida taji Tana Sha"awar komawa Gida Domin bata so Takoma Gida ta bar ta acikin Wannan Rayuwar ba Daga ita Har Zulaihat Tayi alkawarin yadda Suka Tsaya Domin Inganta Rayuwarta itama sai ta Tsaya tsayin Daka sai sun Samu Farinciki kamar yadda take samu Daga wajensu.

Sun koma asibiti an Basu madaran da za"a Rika bama su Anun Farida ta siya aka Cigaba da basu ana Hada musu da Nono Cikin Ikon Allah Madaran ta Karbesu sunyi Kiba kamar ba su ba,Daman ko da suka Dawo an guwan basa harka da Kowa su kadai suke Rayuwarsu kuma banda Kacharalle da Uwar mata bamai Zuwa gidan Shiyasa ba wanda ya saka musu Ido Tunda ba"a ga wasu maza na kara kaina Acikin Gidan ba Farida bata kawo Maza ita haka Salomta yake sai dai ta Bika ka Biya Kudin aikinta kawai.

Kuma Tunda suka Baro Gidan Uwar mata koda wasa Daga ita Har Zulaihat ba wacce ta kara Komawa sai dai In kacharalle yazo ya basu Labarin Abubuwan Dake Faruwa Shine ma ya gayamasu Fada ya kaure Tsakanin Suby da Rufy,Rufy ta Dauko Wuka ta yanki Hannun Suby Gida ya Rikice Suby Taje ta Dauko ma Rufy yan sanda Aka Tafi da ita da Uwar mata taji labari ta saka aka tafi Harda Suby din aka kulle bata zo garin ba sai da suka Ci Ubansu Bayan Tazo Tayi Belling dinsu tace su bar mata Gida sai da sukayi ta kuka suna bata hakuri kana ta Hakuri da alkawarin in suka kara Mata Dambe sai sun bar mata Gida.

Daga Faridan Har Zulaihat Allah ya kyauta kadai suka ce Zaina kuwa abun ma mamaki yake bata kai Allah ya Rabamu da Mummunar kaddara ta gode ma Allah da suka bar Wanchan Rayuwar kuma Tana Fatan sunbarta Chan Har Abada kenan.

*******

*Bayan wata uku..*

Bayan Shafewar watanni uku Abubuwa Dadama sun Faru masu Dadi da akasasinsa Ta bangaran Dina dai ba masu Dadi bane Domin har yanzu da suke Cikin Wata uku da Aure da zain bazata Dora komai a zamansu ba Domin ba Zaman aure suke ba kowa yana Zaman kansa ne


Bai Taba cin Abincinta bai taba kwana adakinta ba bai taba Cin Abincinta ba bai taba mata wani kyakyawan kallo da sunan Tana matsayin matarsa ba,Iyakarta Dashi ya Fita Tin Safe Zuwa asibiti Sai Dare yake Dawowa Tsakaninta Dashi gaisuwa Sai ko in ya Shigo Daukan Arman wanda yayi Wayau har ya Fara koyon Zama wani Lokacin ma Chan Shashensu Umma yake Tarar da Arman din.

Wani Lokacin ma baya kwana agidan acikin asibiti yake kwana Saboda ko ya kwana ma agidan ba wani amfani Duk da Bata iya Girki ba Ammh Tana Kokarin ta jagwalgwala hakanan ammh Zain bai taba ma kallonta ba balle har ta saka Ran Watarana zai ci Ballatans Har ta burgeshi.

Harkan Gabansa kawai yake yi bai Hanata walwala da Rayuwarta ba ammh ya kuntata mata Rayuwar nata gata dai Ta Cika Burinta na mallakan Zain sai dai bai mata wani amfani ba,Tun Dina na Hakuri har tazo ta Kasa Itama mace ce Tana Bukatar Namiji balle kuma Tana Ci ta Koshi koda yaushe in Ta ganshi Sha"awarsa kara kamata yake sai dai ta Shige Daki Tayi ta kuka kamar me bamai Lallashinta bata iya gayamawa kowa ba suna Waya da Hajiya maimuna Danginsu na Chan Sudan Sai dai tayi Shuru bata cewa komai,Haka ma ko sunyi mgana da Daddy ko Hajiya Batula sai dai tace komai Lafiya gashi duk ta Rame saboda Raino da kuma Tsotaon Arman inda ma Allah ya Taimaketa su Umma na Rage mata wasu Wahalwalun ai Data gane bata da wayau bata da wanda Zata gayama Damuwarta Zakiya ce kuma Bata ma

23 / 37