Chapter 24 Reading Zainazain Book 2 Complete By Janafty Arewa Novels

Zainazain Book 2 Complete By Janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   24 / 37

69K to 72K   out of 108.5K words

san Isalin Zakiya ba Domin Ranar sunan Arman da suka yi Kacha kacha bata kara Nemanta ba itama bata Nemeta ba.

Haddir taso tayi ma mgana da Farko sai kuma ta Fasa Tunda Shima ba ganinsa take sosai ba Sai Ko ta Shiga Wajensu Umma ko kuma Tabi Nene Ko Zainab Zuwa Gidan Alhaji Tsoho suke Haduwa Shima da sun gaisa Shikenan Ta rasa ya Zatayi da Rayuwarta Bangaransu Umma kuwa basu sanmeke Faruwa ba ganin Zain din ya kwantar da Hankalinsa yasa suka Fara Tunanin ya Fara Yadda da duka kaddaransa suna Tunanin kuma ya karbi Auran Dina Da Hannun Bibbiyu kamar yadda yake Nuna ma Mutane Faruq Tuni ya koma makaranta Sadiq ne kadai agida sai Zainab Zafeera ma tazo tayi sati Biyu ta koma Saboda makaranta Duka ahalin Basu manta ba Koda yaushe suna addu"an Allah ya bayyana Halima ya Dawo da ita Gida Lafiya kamar yadda ta Fita

Zain kuwa kowa mamakin yadda ya koma yake yi ya Fara maida Jikinsa kuma baya nuna wata Damuwa ko kadan,Iyaye sun Fara Murna suna Tunanin Komai ya Daidaita batare da kowa ya sani ba ya Riga ya kamallah Duka Shirinsa jira kawai yake Lokaci yayi ya sanar kuma ya Tabbata azuwa Lokaci ba"a da yadda aka iya Dashi Tunda Bakin alkalami ya Riga da ya Bushe.

Arman kuwa yana Kara wayau Kamaminsa da Zain yana kara Bayyana kuma yana kara Shiga ran Kowa acikin Gidan Hatta da Alhaji Tsoho da Hajiya Mama musamman ake kai musu shi ya wuni chan Tare da Zainab Tunda Ya riga ya saba da Dangi Baya Rigima sosai kuma ya Riga ya saba da kowa Shiyasa baya yawan Rigima ko bai ga Dina ba kuma suna Bashi Madaran yara in yayi kuka Shikenan sai Kaji Shuru.

*****

Achan Zaria ma Tuni su Anun suma sun Fara Koyon iya Zama in ka gansu Turbakallah masha Allah,Yaran suna da ban Sha"awa Sosai in ka gansu Suma kamaminsu da Zain yana ta kara bayyana Kyansu na kara Fitowa.

Kayan Wasa kuwa kusan Rabin Daki Farida ta cika dashi Tunda Anun da Anan din suna son Wasa sosai babu Abunda suka Nema suka Rasa Bangaran kayan saawa Madaransu da Ruwan Shansu Duka kafin Wata ya Kare Farida ta Tanadi komai ,Farida Zuciyar Zinare gareta Zaina Na jinjina ma Irin Zuciya ta Farida Domin Daya ce acikin Dubu.

Da ita Zulaihat sune komai nasu Anun Sun Riga suma sun saba dasu in Farida bata nan data Shigo Zasu fara Zillo suna Rarrafawa Zuwa gareta in kuma Zata Fita sun kama kuka keman sai Zulaihat ta Daukesu Ta lallashe su suke yin Shuru Zaina Tayi ta mamakin Jarirai dasu ammh sai wayan Tsiya.


Ganin Zaman Gidan babu Abunda suke yi yasa Zaina tayi ma Faridan mgana Zasu Shiga wata islamiyan Dake kusa dasu,Batayi gaddama ba ta basu kudu suka siya Form ita da Zulaihat Suka kuma Biya kudin Makaranta,Ammh tayi musu Fadan su kula da kansu bangaran matan aure suka Shiga 2pm zuwa 4pm na yammah In Zasu Tafi kulle gidan suke Zulaihat ta Goya Anun ita kuma Zaina ta goya Anan In Farida na Gida Bata Fita ba kuma sai su bar mata Tuni Su Zaina suka Zama yan makaranta Daman ita abubuwan da ake koya musu Bita ne Tunda duk ta iyasu Sai da Zulaihat wanda Zainar take kara Taimaka mata agida in da bata gane ba basu yarda sun yi kawance da kowa ba,sai dai gaisuwan Sama sama kuma amakaranta Kowa ya san Zaina Mamarsu Anun ce Zulaihat kuma kowa yana Tunanin kanwartace suma ahaka suka barsa basu yarda sun bama Kowa Fuskan da Zata Shiga Jikinsu ba saidai gaisuwan sama sama Tunda Farida ta gargadesu da su kula da kansu.


*****

*Bauchi..*

Yau ta kama Asabar din karshen Mako ne Yau gidan Alhaji Tsoho cike yake da duka ahalinsa Maza da mata Domin Tun Bayan Faruwar Abunda ya Faru na Zain da Dina sai yau kuma aka sake irin wannan Zaman Taron Wanda Alhaji Tsoho ya sake gamgamin Hadawa Saboda wani Kwakwaran Dalili nashi wanda suka Tsaidashi Shi da ya"yansa.

Tun Jiya Bakin nesa suka yi ta isowa irinsu Baban kaduna da Daddyn Abuja da Inna Rukayyah Wacce tazo Tare da Shema da Zafeera Da Farko Zafeeera tace bazata je ba Ammah Alhaji Tsoho yace Inna Rukayyah Tazo da ita Inna Hannatu ma na wajen Kowa da kowa ya Hallara Zareena ce kadai bata awajen Harda Dina Ma Tazo Tana gefe Arman na Hannun Mama Safiya Haddir na Wajen Hakama Zain wanda Daman da Biyu yazo Kamar shi din ma yana Jiran wannan Ranar ne shima ya Fadi Abunda ke Ransa.

Bayan Gaishe gaishe da kuma addu"an Bude Taro Da Sadiq babba yayi Alhaji Tsoho ya Fara Jawabinsa b kamar Kullum nasiha ne kan su hada kawunasu su zama Tsintsiya Daya madaurinta Daya kafin ya Gangaro kan Dalilin Zamansu da Abunda ya Tarasu.

Sunan Haddir ya kira wanda sai da gaban Haddir ya Fadi ya Dago yana kallon Alhaji Tsoho yana amsawa Kai Tsaye kuma ya juya alaqan Kiran nashi kan Zafeera itama sai taji Faduwar gaba Daman Tunda akace Alhaji Tsoho ya matsa azo da ita Ranta ba Dadi Tana ta Fama da Fargaba.

Dukkansu suka amsa Jikinsu yayi sanyi Atare yace su taso su kariso Zuwa gabansa Kowanme Jikinsa bai basa ba suka mike suka isa gabansa suka Durkushe kuma Dukkansu ba wanda ya kalli Dan"uwansa.

Sai da ya Dade yana Nazarinsu kafin yace"Hadiru da Zafeera ku Dago kanku ku kalleni..'

Dukkansu Atare suka Dago Gabansu na Faduwa Alhaji Tsoho ya kallesu yana Fadin"Kusan Dalilin Taruwarmu anan wajen yau..?

Suka Girgiza kai atare Alhaji Tsoho ya Kada kai kafin yaDago yana kallon Babam Kaduna Lokaci Daya yana Fadin"Bashir gaya musu Hukuncin da muka yanke akansu Tunda bazamu Zira musu ido suna Yadda suka ga Dama ba..!


Baban Kaduna ya gyara Zama yana Fadin"Alhamdulillah..Daman ba wani Abu bane yasa muka Taru a nan wajen sai Domin mu Sanar da yaran nan abunda Babanmu ya yanke kuma ya nemi Shawaranmu mukuma muka ga Tabbas Mganarsa Tayi Daidai an hadu ne anan wajen Saboda Kowa yaji kuma yaShaida Mun yake Shawaran Hada Auran Haddir Da Zafeera Insha Allahu Auransu Zai Tabbata nan da Wattani Biyar Zuwa Shida Lokacin Ita Zafeeran Ta Shiga aji hudu amatakin karatunta Domin mun gaji da ganinsu suna Zaune babu Aure duk wanda akayima mgana sai ya Fara yimana yawo da Hankali ba.."

Kowa afalon Baki ya Washe da jin wannan mganar banda Haddir da Zafeera wanda suka Dago suka kalli Juna Lokaci Daya kowa ya kauda kai Cikin Wani yanayi acikin Zuciyansu da basu Nuna ba Hajiya Mamace ta Saki Guda Tana Fadin"Alhamdulililah Alhaji ka Biyani..Lokaci yayi dasu Hadiru Za"a Daina zaman gauranci Ita kuma Wannan mara kunyar me Koran masu sonta Anyi mganinta abu yayi Dadi.."Dariya aka saka su Umma nata Masha Allah Zain dai na Gefe shima yana Dariyan Mugunta Dina kuwa Zaune kawai take tana Bin Kowa da kallo Tana so da za"a bata dama da Ta Fadi itama Damuwarta.

Alhaji Tsoho ne ya kalli su Zafera Dake durkushe kowa yana Saka Abunda ke Ransa yace'Baku ce komai ba..?

Atare suka Dago Bayan sun kalli Juna na wani Lokaci kana Kowa ya Kauda kansa Cikin Sanyin Murya Haddir yace"Bamu da ta cewa Alhaji Tsoho Abunda kuka yanke akanmu Shine Daidai
.Allah ya sa alheri Zaku kullah..'Gabadaya kowa ya amsa da Ameen Cikin Farinciki Zafeera kuma kanta na kasa tace"Banda ta cewa...Duk Abunda kuka yanke akaina Daidai ne sai dai Ina Rokon alfarman abari na gama karatuna sai ayi auran.."


Alhaji Tsoho yace"Karki Damu..Ko Bayan auran Zaki ci gaba da karatunki da yardan Allah.."Ta kara Bude baki Zatayi mgana Alhaji Tsoho ya Dakatar da ita da Fadin"Bikin ku Zai Gudanan nan da wata Bakwai Insha Allahu.."Dole Taja bakinta tayi Shuru Falon kowa sai Fatan Alheri yake da Fatan Allah ya kaisu da rai da lafiya.

Zain na Gefe ya Mike yana Fadin"Ina da mgana Alhaji Tsoho.."Kallo ya Dawo kansa Alhaji Tsoho yace"Muna Sauraranka Zainullahi..."Kansa na kasa yace"Kumin afuwa iyayena na yanke Shawara batare da saninku ba awattanin baya na Nemi wata mkaranta medicine School ne a India Mumbai medicine School inda naje nayi wannan karatun a baya, har na Samu ma kamallah Duka Cike Ciken da Zanyi nan da Kwana Goma Zan Tafi Chan zan je nayi wani Course na Wata Takwas Kan Harkan Fida da abunda ya Shafi Cututtukan mata.."


Gabadaya Falon Kowa sai ya kallesa Dina kuwa Cikin mamaki da al"ajabi take kallon Zain Lokaci Daya taji wani Hawaye sun Cika mata ido.







*Shakira...*
8/5/21, 4:10 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B22️⃣1️⃣*

*IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*

"Gabadaya afalon ba wanda bai goyi bayan Zain ba su Baban kaduna sukace wannan Babban Cigabane gashi Zain din da kuma Cigaban Asibitin Saulawa.

Matan kuwa suna Murna ganin Zainullahi ya fara manta Abubuwan da suka Faru tunda har zai koma karatu azuciyar iyayansa kuwa suna Fatan Allah yasa ba Saboda batan Halima bane zai yi Nisa Da Gida ba.

Alhaji Tsoho ya Kada kai yana Fadin"Tunaninka Tunani ne mai kyau Zainullahi kuma naji Dadin haka..Sai dai Da ita iyalanka Zaka tafi ne..?

Sai da Zain ya juya ya kalli Dina Wacce ke kallonsa Idanuwanta Cike da Hawaye da wani Raunin kar kamin haka kafin ya Dauke kansa Bayan ya Dallah mata Harara Cikin Sanyin murya yace ma Alhaji Tsoho"A"a Ba da ita zani ba Alhaji Tsoho karatu ne zan je nayi na wata Takwas kamar yadda naje nayi ashekarun baya Zuwa da Iyalina Zai iya Taba Abunda naje Dominsa,mun gama mgana da ita Zata zauna tare dasu Umma sai dai in na Samu Dama Kila nazo na ganku ko Sau Daya ne kafin na kamallH Insha Allahu.."Gabadaya kowa yayi Na"am da Tsarin Zain Dina kuwa kanta ta Dukar tana Sharan kwallah Cikin Zuciyarta tana kara Tabbatar ma kanta Zain ya Tsaneta Soaai Tunda har Zai iya Saka kafa ya tafi wata Uwa Duniya ya barta batare Daya Taba Dubanta a Matsayinta na Matarsa ba bai Taba Tunanin ita mace bane Tana da Rauni kuma ita ba Dutse bace Tana da Sha"awa Tare da ita Ta lura Yana Sha"awar yaga ya sakata Cikin Kuncin Zuciya kamar yadda yake Ciki.

Kamar Ta mike ta karyatashi gaban kowa ta sanar Dasu ita bai Tsara haka da ita ba sai kuma Ta Fasa da Tunanin Kila har gwara Zamanta Tare dasu Umma ahakan ma ya ta kare,Balle ya Dauketa ya Tafi da ita Uwa Duniya Batasan kuma Wani hali Zata Shiga ba ta Tabbata Tsanar Datake gani a nan kadan ne da wanda zai nuna mata karshenta yadda ya Tsaneta ma ya barota Chan ya Dawo abunsa Tunda hakam ma bazai Damesa ba Illah ya gayama Iyayanta ta bace ne chan kuma kashashen Turawa Kila har ta gama gararanbanta ta Mutu bamai kara jin Labarinta da wannan Tunanin ta kama bakinta ammh Lokaci Bayan Lokaci Tana Sharan kwallah Zainab Dake gefenta na kallonta acikin Ranta kuma Tana Fadin Daman ya zama Dole ki koka Domin Wannan Ranar tana Zuwa Miki Daman..

Koda aka Tashi Taron Rayukan Kowa na Cikin Farinciki Banda Haddir da Zafeera da Dina Zafeera Dakin Hajiya Mama ta Shige Tana kuka ita an Cuceta arasa dawa za"a Hadata sai da Ya Haddir mai Shigen Girman kai Ko Dariya baya ma Mutane ita Jininsu sam bai Hadu ba Zainab da Shema nata bata baki Suna Nuna mata yanayinsa kenan Shi bamai Hayaniya bane ammh Taki yarda ita Damuwarta Daya makomar karatunta Tunda ta Tabbata Bayan Auran ba Binta Zai yi kanon Suje su zauna ba ammh kuma Bazata yi Shiru ba ana Gama Biki Zata koma kano Abunda Sai ya Nemi matar da Zai Zauna da ita su Umma na Falo bama su san Darun da Zafeera keyi ba su atunaninsu Tunda Suka Fadi wannan mganar Daga ita har Haddir basa Jinsu suna musu kallon Yara ne su masu Biyayya da Gudun Zuciyar iyayansu.

Abangaran Haddir ma Hakan Ta kasance suna Hanya Zasu Tafi asibitin Zain ya Daukeshi a Motarsa Tashi ta Lalace Tana Gareji Gabadaya ya Zurfafa Tunani Bai Taba Zaton Iyayansu Zasu iyamai wannan Dukan Lokaci Daya bai Taba Shiryama kansa Aure nan da wata Takwas ba Yana Tsoron mata da Shedancinsu yana son Samun Mace Tagari wacce Zata soshi Tsakaninta ga Allah kuma ta Girmamashi da Duka ahalinsa bai Taba kin Zafeera ba sai dai Shima yana mata kallon Wata mace mai Girman kai mara Fara"a ga Tsiwa da Rashin Kunya sam Shi kanshi Jininsa da ita bai Hadu ba sai dai bazai Taba watsama Ahalin da suka maidashi Mutum kasa acikin Ido ba Ko bakomai Zafeera ya' take wajen Umma da Abba kuma Mutanen da suka Rikesa Tamkar Dansu komai na Rayuwa Abba yayi mai in ko yace bayason Zafeera bai kyauta uwa uba kuma yaga Duka iyayan nasu sun yi Na"am Da wannan Hadin Baya Fatan ya watsa musu kasa acikin Idanuwansu.

Har suka iso Haraban asibitin bai sani ba sai da Zain ya Dafa Kafadarsa kana ya Dawo Cikin Hayyacinsa Cikin Sauke Rai ya kalli Zain yana Fadin"Yaushe muka iso..? Wlh ban sani ba..?

Zain yana Kokarin Daukan Wayarsa yace"Ina fa Zaka sani kana Chan kana Tunanin Amaryanka Zafeera akun Umma.."Hararansa Haddir yayi Lokaci Daya yana Bude Murfin Mota ya Fito yana Fadin"Zaka sani ne Ina da Fada dakai wlh..Wai ka Shirya Zuwa karo Karatun wani Course ko ka sanar dani kaji ko Nima ina Ra"ayin Zuwa ko..?

Zain Shima ya Fito Daga Motar bayan ya kulleta suka Jera Zuwa Cikin asibitin yana Fadin"Afuwan Abokina..Bana son Ka hanani ne wlh.."Hadddir yace"Ni na isa ne..! Ai bamai iya Hanaka Abunda kayi Niyyah Zain..Alrigh all d Best..Allah ya Bada Sa"a nima inaga Zan je ko Ameriaca ne nayi Kan Harkan Kwakwalwar kai Insha Allahu.."Zain na Dariya yace"Sai dai ka bari bayan Auranka ku Tafi da Zafeera Daganan kusha Honeymoon.."Duka Haddir ya Dagamai abaya yana Fadin"Uwar Honeeymoon ne ba Honeeymoon ba.."Zain sai Dariya yake shi kuma Haddir yasha Kunu Haka suka Karisa Cikin Asibitin kowa ya Wuce Office dinsa Ammh acikin ran Haddir farinciki ya kamashi ganin Zain yau yana Dariyan da tun Bayan Abunda ya Faru bai Taba ganinsa Cikin Farinciki irin na yau ba yana Fatan Allah ya Dauwamar da Farinciki a Rayuwarsa na har Abada.

Washegari Zafeera ko Inna Rukayyah Bata bari sun Jira ba Suka Bi Motar haya Zuwa Kano Ita da Shema tayi ma Abba karyan Assigment gareta Zatayi Submutting aranar Dole aka barta Suka Tafi duk da Shema tasan karyace bata Fada ba,Dina kuwa Ranar kwana kuka Tayi da Neman ma kanta Mafita Zain bai ma san Tanayi ba yana Chan yana ta Shirin Tafiyarsa Ranar da yammah Inna Hannatu tabi Jirgi ta koma su Abba kuma sai da suka kara Kwana kana kowa ya Dauki Iyalansa Zuwa Gida.

Zain nata Shiryan Shiryan Tafiyansa Yagama su Umma Zai Je har Gada yayi sallama da Goggo Halima ya Shirya Tafiyan ana Saura kwana Hudu ya Tafi sai kuma Arman ya Tashi da Zazzabin Da Amai Dole ranar ya Daga Tafiyan bai Tafi ba Asibiti suka Wuni da Arman din a Office din Din Haddir yana kula Dashi sai da aka sakamai Ruwa da allurai Tunda Zafin Zazzabin yasa har suma sai da Arman din yayi Hankalin Zain ya Tashi Sosai bai san yana son Arman ba sai Ranar Dina kuwa kuka Ta wuni yi hakama su Umma Kowa hankalinsa atashe acikin asibiti Kuwa kowa yaga Dina sai mamaki Daman ta na nan..?Abun mamaki gata kuma Dauke da yaro sai dai babu wanda yayi Tunanin yaron yana da wata alaqa da ita Dinar Tunda ma Daidaikun mutane ne suka gansu sanda suka Shigo asibitin Allah yasa Dr.Imram baya Cikin Asibitin da ko da Bala"i sai ya Gano Komai.

Sai Dare suka koma Gida bayan Jikin Arman din yayi sauki har ya Farka Dina ta bashi Nono Shashen su Umma suka yada Zango saboda suma Tun Tafiyarsu suke kiran waya hankalu Tashe sai da suka ga Dawowarasu da kuma Arman Daya samu Sauki kana Hankula suka kwanta Nene ta karbeshi Taje tayi mai wanka da Ruwan zafi mai Zafi sai gashi ya samu Barci nan Suka barsa Wajen Nene suka Nufi Shashensu Har yanzu Dina bata Daina kukan ba Ran Zain ya baci ya waigo a Zafafe yana Fadin"Wai kukan me kike yi haka..?Dallah Kima mutane Shuru Tunda ba Mutuwa Arman din yayi ba.."

Jin Haka yasa ta Damke Bakinta ta karisa Dakinta da Gudu Tana kuka ya Rakata da Tsaki Shima ya Taka Zuwa Dakin Dayake kwana ya tube kaya ya Shiga wanka bayan ya Fito ya Saka Jallabiya ya Shiga Kitchen ya Bude Frigde ya Dauko Ruwa yazo yasha sai ga Zainab da Kololin abinci Daman yunwa yake ji nan ya Zauna yaci ya Koshi ya tashi ya Shiga Ciki yayi alwala ya Rama Sallar mangariba da Isha"in data Subucemai ya koma ya kwanta Saboda gajiya Lokaci Daya barci ya kwasheshi.

Dina Kuwa Dakyar tadaina kuka Taje tayi wanka itama Tazo Tayi sallah Ta koma ta kwanta Tana Kuka ita kadai tasan Halin Datake Ciki na Sha"awar kasancewa da Mijinta in taje ta Tareshi Wulakanci ne Zata gani ganin Idonta kuma in ta bari ya Tafi ya barta Kila Zata Fada wata Halakar a iya Hangenta ta kasa samun mafita,Shigowar Zainab ne ya katseta ta kawo Arman ya Tsshi yana kuka ta Fito Falo ta karbeshi sai Lokacin Taga Kololin abinci Ta kuma Fahimci Har Zain yaci Tunda ga Filet da Cokali nan Zama tayi ta bama Arman Nono Yasha ta Lallabashi yafara barci ta kai Shi Ciki ta kwantar kana ta Dawo ta Zuba abinci kadan ma ta iya ci ta Ture komai ko iya Dauke Kololin batayi ba ta Tashi ta Shige Ciki har ta kwanta Tana Tumanin Mafita har garin Allah waye bata samu Wata Mafita.

Da Safen ma Tana gani Yazo ya Duba Arman ya bashi mgungunarsa Tana kwance kanta ke Ciwo ko ta kanta bai bi ya Dauki Arman suka Fice Shashensu Umma yakaishi Nene ta karbeshi yace ayi mai Wanka yaga Jikin nashi da Sauki Zai Tafi asibiti ya Fito kenan suka Hadu Da Haddir yazo Duba Arman suka koma Ciki ya karbesa ya Dubashi yace ba wani Mtsala basu Tsaya ba suka Tafi kowa ya Shiga Motarsa Zuwa asibiti.

Zuwa yammah Arman ya Watsake yana ta Sha"aninsa,Dina kuma da Ciwom kai ta Wuni da kuma

24 / 37