Chapter 20 Reading Zainazain Book 2 Complete By Janafty Arewa Novels

Zainazain Book 2 Complete By Janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   20 / 37

57K to 60K   out of 108.5K words

ita Sa"adiyan Lafiya take ko.?

Nurse din na Mirmishi Musulmace sun saba ganin haka Tace"Eh..Bata Farfado ba ammh Zuwa 4 zata Farfado yanzu za"a gyara su ita da Bbys din akawosu Dakin Hutu."Zulaihat Ta kara Daka Tsallake Tana Fadin"Kai Masha Allah..'Daganan kawai ta Kwashi Gudu Zuwa Haraban asibitin Msallacin ta Nufa Daman Faridan Tagayamata Tana Masallaci Tana Shiga ta Isketa Tana ta Jan carbi da Gudu Ta Fada Jikinta Tana Fadin"Albishirinki Anty Farida..?


Farida ta Zabura Tana Fadin"Goro Fari kal Zulaihat..gayamin Sa"adiya ta Haihu ne..?

Zulaihat tace"Ta haihu Yan Biyu Anty Farida duka Mata.."Ido Farida ta Zaro kafin ta Rumgume Zulaihat Tana Fadin"Alhamdulillah..Masha Allah Allah ne abun Godiya.."mutanen Cikin msallacin sai kallonsu suke Tashi Sukayi Bakinsu yaki Rufuwa Suka Nufi Cikin asibitinn...




*Ku kara min Hakuri Don Allah..Banyi Editing ba*



*Shakira...*
8/2/21, 2:37 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ....B21️⃣7️⃣*


*IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*

"Da gudu Gudu Sauri Sauri suka karisa Cikin asibitin Suna Isowa Wasu Nurses guda Biyu suna Fitowa Da Jariran Guda Biyu Cikin kayan alfarma Daman Da zasu Shiga Tiyatan Sun karbi kayan Haihuwa.

Hannu na rawa Jiki na Rawa Farida Da Zulaihat suka karbi yaran Suna kallonsu kwallar Farinciki ya Cika Musu Zuciya Duk da Farida Bata Taba ganin Firstlove ba ammh ta Tabbata Wadanan yaran Dashi Suke kama kuma Domin Doguwar Fuska Sa"adiya Kadai suka Dauko ammh Har Launin Fata na Ubansu ne,Farida Taji Saukan Hawaye Bisa Kuncinta Lokacin Data Haifi su Hassana yana Dawo mata kamar yau ne Zulaihat ne ta kariso kusa da Ita Tana Nuna mata na Hannunta Tana Fadin"Anty Farida kalli Basa kama da Sa"adiya..?

Farida na Share Hawayenta Tace"Ammh suna kuma da Mahaifinsu ko Shakka bana yi.."Zulaihat Tace"Lalle kuwa In Hakane Mijin Sa"adiya Gangariya ne.."Mganarta Sai da ta saka Farida ta Murmusa suna nan Tsaye Likitan ya Fito Farida namai Godiya yace yanzu za"a Gunguro da Sa"adiya Za"a kaita Dakin Hutu Nan da anjuma Zata Farfado in sun shiga Dakin Kada Suyi Hayaniya suka ce Toh ko Minti Goma ba"ayi ba aka Gungurota Zuwa Daki na Musamman da Farida Tace a sskata suka Bi bayansu suna Shiga suka Tsaya kanta suna kallonta yadda Tayi wani iri Duk Wahalan Nagudan yagama Tafiya Da ita basu Dade aciki ba Nurse suka karbi yaran suka sakasu Cikin Dan gadonsu sukace suje waje su Jira Bayan Sun Fito ne Farida ta bama Zulaihat 1k tace ta koma Gida Tayi musu Abinci Ta kuma Hado ma Sa"adiya Zannuwa da Riga Tazo da kayan Tea da Fulas Din Ruwan Zafi da Zulaihat din ta Nemi su Tafi Tare sai tace baza"a bar Sa"adiya ba kowa ba Taje ta Dawo.

Zulaihat na Tafiya Farida Ta Daga waya ta Kira Alhaji Badamasi Tagayamai Daman Shima yasan Labarin Zaina kanwar Farida ne ganinta ne kawai bai taba yi ba Yana Kashe ma Farida da kudi Sosai Tana gayamai Sa"adiya Ta Haihu nan take ya Turo mata 150k Farida Taji Dadi Duk da Tana da kudi a Hannunta ammh Tana Bukatar kudu sosai ga Hidiman asibiti Gana masu Jego da Babys.
Bayan Shi sai ta Kira Uwar Mata Ta gayamata Uwar mata Dake Cikin Shagonta ita da Aminiyarta Hajiya Zabba"u Ta Tabe baki Tana Fadin"Wai Don Allah Farida waye Uban Cikin yarinyar nan..?gwara ki Maidamai kayansa ina Zaki iya Wahalan yara har Guda Biyu alokaci Daya..?

Farida Tace"Suna da Uba kamar Kowani Yaron Sunna..Kada ki Damu Lokacin Kadan yaRage na Sada Sa"diya da Danginta ammh mganar ina Zan iya kula da yara Biyu alokaci Daya baki da Damuwar wannan Kafin Sa"adiya Ta Haihu yan Biyu ni nafara Haihuwansu kinga kuwa Duk wanda Zai baki labarin Yaya Haihuwansu da Renonsu Barin Nice.."Uwar Mata Tace"Uhm..Allah ya raya Zan Shigo Sati na sama Sai muzo Muyi Barka Domin kece gaskiya Sholly.."Farida bata ce komai ba ta Datse Kiran Tana Wani Tunani ita kadai.

Har Zulaihat ta Dawo Sadiya bata Farka ba koda ta Dawo da kaya Niki Niki Ita da kacharalle suka Dawo Taje gida sai gashi yazo Shine take gayamai a asibiti suka kwana Jin Sadiya ta Haihu har yara Biyu Kacharalle nata Murna sun zo sun iske Farida na masallaci Sallar La"asar ta Shiga Dakin da Zaina Take ta Ijiye Fulas din Datazo Dashi da kayan Tea sai Basket din Data sako Abinci sai Ledan kayan Sadiya suka Fito nan suka ci karo da Farida Sun Tsaya suna gaisawa ne Likita ya Shiga Daki bai wani Jima ba ya Fito yana gaya musu Sadiya ta Farfado ya kuma ce kada su bata wani abu sai Zuwa Gobe da Safe Saboda aikin Jikinta suka ce nan suka Dumguma Cikin Dakin suka isketa Zaune an karamata Filo abaya Farida da Zulaihat Rumgumeta sukayi suna Murna itama Farinciki ya Cika Ranta Kacharalle na Gefe shima yana Dariya.

Zulaihat da Farida suka Daukomata yaran acikin karamin Gadonsu suka Sauke mata kan Jikinta Ta kura musu Ido Tana kallonsu wani irin Abu na yawo acikin Ranta Kana ta Dago Tana kallon Farida Kafin Tace"Anty Farida..Gabadaya yaran nan basu Dauko ni ba Kinsan wa suka Dauko..?

Da Zulaihat da Farida suka Hada Baki Wajen Fadin"Firstlove...! Mirmishi ta saki sai ga Hawaye bata Damu Data Share ba tace"Na Tuna Watarana Lokacin Tun Farkon auranmu ne muna Gaddama da Firstlove yana Fadin in na Haihu,Yaran Dashi zasu Dinga Kama Badani ba Ni kuma na Dinga Cewa Dani zasu Dinga kama muka kulla alkawarin indai na Haihu sukayi kama Dashi Yaci Gasan in kuma sukayi kama Dani ni naci gasan.."Tafada Tana Tuna Lokacin da Abun ya Faru.

Farida Tace"Lalle...Aikuwa ya Cinye wannan gasan wannan karon.."Zaina Ta Share Hawayenta Batare da Tayi mgana ba addu"a take ma yaran acikin Ranta Bayan Tagama Ta Mikama su Farida su suka mikama Kacharalle ya gansu yayi Allah ya Raya.

Nan asibitin yakai Dare kana ya Tafi daga Farida Har Zulaihat nan suka kwana Tare da Zaina Kowa baya son Tafiya,Washegari ma Jikin Sadiyar da sauki Tunda Har Farida Ta Taimakama sunje Bayi ta Dauraye mata Jiki kana Tasha Tea Likita yazo ya Dubata yaran kuma Tun Safe Nurse suka zo suka karbesu sukayi musu wanka.

*******

*Bauchi..*

Ayayinda Zaina Ta kwana Daya a asibiti da Haihuwa anan Bauchi Ranar alhamis ta Zagayo Gidan Abba na Cike da yan"uwana ana ta Hidiman Sunan Wanda Duka Hidiman Abba ne yayi Shi Tunda Uban gayyar ba wanda ya kara ganinsa Tun Ranar da Abba ya sashi Zuwan Dole.

Inna Rukayyah ma ta iso Tun Jiya kuma Gidan Abban ta Sauka Da Farko Tace bazata zo ba Sai Da Inna Hannatu ta saka baki kana Daga Kaduna Kuwa Ba wanda yazo Daga Baban Kaduna Har Mom Iklima sai dai sun Kira waya sai Mama Safiya ce Tazo,Tunda anyi ma Mijinta Takwara Wanda Zainab tace Za"a Dinga kiran sa ARMAN.

Bangaran Kwamishina kuwa Hajiya Batula Tazo Ita da Waleed da Walida Da kayan Barka Niki Niki na Bby dana Dina Wanda Kwamishina ya Siya mata sai kayan gara bangaran su Abinci Booth Guda Tazo Dashi Abba nata Fada ma,Hajiya maimuna kuwa ta Kira Chan Sudan ta sanar da Mahaifiyarsu Haihuwar Dina Tayi barka Har aka bama Dinan Tayi mata Barka da Fadan Yadda Zata kula da kanta Duk Da Kowa na iya bakin Kokarinsa Daman Da Hajiya maimuna Zata zo Tazo da kayan gyara da kayan kamshi irin nasu na Sudan yanzu sai ta Fito Dashi Tana yima Dina amfani Dashi.

Abba Shi ya siya Raguna Guda Biyun da aka yankama Aliyu arman Shi kuma yayi Hidiman Abincin Da aka Girka da komai dai da komai Hatta da kayan Sawa ya Dinkama Dina Alhaji Tsoho Dayaji labari yana ta sakama Abba albarka Daddy Abuja ma ya aiko Mama Safiya da Sakon kayan Bby abama Takwaransa Kowa yayi bajinta kamar Ba wani Abu daya Faru Hatta Haddir sai da ya Siyaman Arman kaya masu kyau ko bakomai Jinin Zain ne Uban gayya ne kadai bai Damu ba Sai dai Kullin ina kallon Hoton Arman a wayarsa Wanda Haddir ya Daukesa ya Turomai Allah naji yana gani Allah ya Doramai son yaron ko bakomai Shi ya Digashi har yazo Duniya.

Labarin Abunda Dina ta aikata ita da kawarta Zakiya yagama Zaga kannuwan Dangi kowa yaji sai yace Biri yayi kama da Mutum Daman Zakiya Daga ganinta Tafi Dina iya Shedanci Kana kuma Kowa Kwamishina yake Dorama alhakin Komai da Hajiya Batula wacce bata Dauki da A ya' ba koda ita bata Dauketa mataayin Uba ba ammh akallah ta Sauke Nauyin Dake kanta Allah bazai kamata Da Laifin yin Watsi da Rayuwar Dina ba.
Alhaji Tsoho Da Hajiya Mama ke Koramai Abunda ya Faru Mirmishi kawai yayi yace mata"Na sani..Nasan Daman hakan zai ne ya Faru.."

Cikin Mamaki Hajiya mama ke kallonsa kafin tace"Kasani fa kace..? Alhaji Tsoho yace"Eh..Tun bayan Faruwan lamari Zain yazo ya gayamin Wata mgana na Dora ayar Tambaya akansa na Fahimci ya Hadu da Shedaniyar mace tamai Sihiri Shi kuma yana Wasa da Addu"a Shiyasa Abun yayi Tasiri akansa Ammh Yanzu Insha Allahu ba ita ba Ko Wata ma Bazata iya Nasara akan Duka Jikokina ba.."

Hajiya Mama ta Jinjina kai Kawai Tana Fadin"Allah ya Tsaremu Ai ko da Chan ma Hadiru yafi Shi Kokarin Azkar nake ganin.."Alhaji Tsoho yace"Ada kika sani ammh yanzu ya Dage...Mganar Hadiru kuma daman nagaji da ganinsa ahaka Bayan Yarinyar nan tayi Arba"in zan Daura musu aure da Zainullahi na Cika alkawarin Dana Dauka Zan Dawo kan Hadiru da yarinyar nan yar Wajen Usman itama.."

Hajiya Mama tace"Wacce Zainab ko Zafeera..? Alhaji Tsoho yace"Zafeeran Dai Shedaniyar yarinya Ki Duba fa Taki yaron nan Ahmad kwanaki Aliyu ke gayamin yazo yana gayamai an sakamai Rana Aure.."Hajiya mama ta Waro Ido Tana Fadin"Kai don Allah...?

Alhaji Tsoho yace"Ah..ya zauna yana Binta Tanamai Wulakanci ammh nayi Mata Takaicin Rasa Gwarzon Namiji irin yaron nan Ahmed.."Hajiya Mama tace"Uhm Sha"anin Zafeera sai ita Bakar Zuciya kamar Hannatu ce Uwarta Bashir Ubanta Yanzu hakama Hutu suke Inji Rukayyah ammh Datace ko Zata zo ne tace Allah ya Tsareta Zuwa Sunan Dan Shege.."Alhaji Tsoho yace"Asssha..Kalmar Tayi Muni Da yawa..Allah ya Shiryeta bari dai nagama da Zainullahi kansu zan Dawo ita da Hadiru Wlh sai nayi musu Tsiyata.."Hajiya Mama Tace"Wlh Daka kyautamin.."

Da haka suka cigaba da Tattaunawa kan Batun ne acikin Ran Alhaji Tsoho kuwa Allah kadai yasan Abunda yake Tufka yana Warwara.

****

Zakiya Bata san Dina ta Haihu ba Tunda bata Kirata ba itama Tuni ta Fita Batunta Tana ganin Dina Zata Juya mata baya ganin ta kusa samun Cikar Burinta Kawarta ce ta Kirata wacce suka bar Ajiyar Motar Dina agidanta akan Suzo su Dauka an mata Transfer din Wajen aiki Zata Bar Gidan Data kama Haya sai da ma Ta Kira Zakiya ta iya Tunawa Da wata Motar Dina Domin ta manta Shaf Tunda suka kaita ajiya da Farko Tayi Tunanin ta Kira Dinar ne ta gayamata ta kuma ce sai Taje ta Dauki Motarta sai kuma ta Sauya Shawara bayan Tatashi Daga wajen aiki Misalin 3pm na Rana Ta Kira Ja"afar awaya tace kada yazo Daukanta Zataje kaima Dina Motarta yace Shikenan in Taje ta Kirashi yazo Ya Dauketa tace Shikenan..

Daganan Ta samu abun Hawa Zuwa Gidan kawarta Bayan sun gaisa ne Ta bata Key din Motar Dama ita suka bama wa Koda Mtsalan Sauyawa Motar waje ya kama Tunda ba Gidanta bane irin Gidan Hayane mai Dauke da Flat Falt ba kamar ita da Ta Siyi nata Gidan ba ita kuma Dina Mahaifinta ya Siya mata,Bayan Ta karbi Key din Motar sukayi sallama Ta shiga Motar tana wani yamutsa Fuska ganin Motar Duk Tayi kura batama Zata motar Zata Tashi ba ganin an Dade ba"a aiki Da ita Daganan bata Zarce ko"ina ba sai Gidan Abba.

Tana Zuwa Kofar Get din Tayi Hon Megadi ya Bude mata ta Sulala Ciki a  parking Space ta faka Motar kana ta Fito Tana gyara Zaman gyalen Dake Kafadanta Abunda ya bata mamaki ganin Waleed da Waleda a Haraban gidan suna wasa da Su Saudart Abun sai ya bata mamaki Cikin Haka ta Kwalama Waleed kira yana ganinta ya Taho yana gaisheta Cikin Harshen Turanci Kansa ta Dafa Tana Fadin"Waleed kai da wa kuka zo kuma..?

Waleed yace"Mu da Mom muka Zo Anty Dina ce ta Haihu yau Suna Kema kin zo ne muje kiga Arman Anty Zakiya Bby mai kyau ne.."Mamaki da Al"ajabi ya Daskarar Da Zakiya Tun Lokacin da Waleed yace Dina ta Haihu Lalle Dina Wuyanta ya isa yanka yau itace Har Zata Haihu yau suna ammh Bata da Labari Lalle kuwa Bari ta Shiga Ta ga da wani Ido Dina Zata kalleta ai Ta Dauka ko bata Cikin Hayyacinta Zata Tuna da ita.

Afusace ta Shiga Falon Gidan ko Sallama su Inna Rukayyah ne da su Umma ke Zazzaune afalon Zakiya Bata ji kunya ba Haka ta Wucesu Fuu Zuwa Dakin Dinar Data ga Kofar yau abude da Mutane aciki Su Umma suka Bita da Kallo Inna Hannatu tace"Wannan ba Shedaniyar kawar Dinan can bane..!?

Umma tace"Itace..Mana..'Inna Hannatu tace"Kuma koke barinta Tana Shigowa gidanan.? Ai bai kamata kuna barinta Tana Shigowa ba,Ko itama Dinar Domin kaddara ta Hadamu ne da Tuni Ta bar Gidan nan itama matsiyaci.."Nene Tace"Ai tama kwana Biyu bata zo Gidan ba sai yau.."Inna Hannatu tace"Yadai kamata kam a tsawarta mata Irin su ai ba Mutanen Kirki bane barinsu suna Shigowa Gidan nan akwai Damuwa.."

Zakiya kuwa Tana Shiga Dakin Ko Sallama batayi ba Hajiya Batula ne ke Ciki ita da Hajiya maimuna Wacce kema Arman wanka Dina na Zaune bakin gado Tana sanye cikin wani Leshi mai Tsada wanda Kwamishina yayi mata Fuskarta Duk Tayi Subu Subu Saboda Hajiya maimuna Bata mata Wasa Tanajin Ruwan zafi yadda ya kamata.

Kan Dina na Sunkuya ne Tana ganin yadda Ruwan Nononta ke Zuba Taji Zakiya ta Kira Sunanta kai Tsaye da Sauri ta Dago Tana kallonta bama ita ba Hatta su Hajiya Batula sai da suka Dago Suna kallonta ba Wanda Ma ta Tsaya ta gaida  Cikinsu Hajiya Batula Dina kawai ta Tunkara Tana Jifanta da wani Kallo sai da Taje gabda da Ita kana Ta Tsaya Tana Fadin"Sannu Dina Gaddafi Sherrif mai Jego ko..?

Tafada Lokaci Daya Tana mata wani kallo Mirmishi baki Dina Tayi mata kafin tace"Na"am Zakiya Nuhu Amaryar..Ko Amaryan Ja"afar Zence ko..?

Zakiya da Kalaman Dina ya bata mamaki Cikin Gadara Tace"Eh Fadi ki kara Amaryan Ja"afar nake nan da dan Lokaci kadan ko baki so bane..?

Dina Ta karkace kai Tana Fadin"Saboda akaina kike da Zan ji Haushi Domin zaki aure..? Ko Daya Wlh Murna ma Nake Miki Zaki yi aure ki bar Rayuwar Da kikeciki.."Zakiya Ta saki Kawai Tayi Tana kallon Dina Kafin tayi mgana Hajiya Batula Ta Rigata Da Fadin"Lafiyanku kuwa..? Zakiya uwar Yaro ki zauna mana..?

Hannu Zakiya Ta Daga mata Tana Fadin"Ba zama ya kawoni ba..Nazo na kawo ma Dina Motarta ce sai kuma Naji Har ta Haihu yau suna ammh bani da Labari..?

Hajiya Batula Tace"Ikon Allah Duk Amintan naku..? Toh ko Kun samu Mtsala ne..? Zakiya tace"Bansan mun Samu Wata Mtsala ba sai Dai kinsan Shi Dan Adam Daman Butulu ne.."Dina Ta kalli Zakiya Tana Fadin"Wani Bultulci Nayi Miki Zakiya.? Ni aganina Ban yi Miki Bultulci ba Tsakanina Dake Sai dai Ni nama ce Kekika Cutar Dani Kika Sakani na Fada Cikin Halaka Ga Zuwa Wajen Boka ga Zunuban Cikin da kikasa Dauka Har na Haifeshi batare da aure ba kin Taba Tunanin in na Mutu Wajen Haihuwa me zan ce ma Ubangijina..? Wlh Dina nayi Nadamar Duka Abubuwan dana Biye miki na aikata kuma na Fasa kwan na gayama kowa Zain bashi da laifi Nice keda alhalinki Duk Abunda ya Faru da Taimakonki Alokacin Ina Zargin Taimakona Kike ashe kina Neman kaini ga Halaka ne Bansani ba ai gashinan ke Zaki auran meyasa baki yi Cikin Shegen ba kafin kiyi Auran..? Sai ni kika Jefa Cikin Wannan Halin..? Wani Amsa Zan bama Allah in ya Tambayene meyasa na Haifi Arman Bata Hanyar Aure ba..?kin Cutar dani Zakiya kuma naji kin Fita Raina Nice ma Zan Miki Allah ya isa Wlh..Kuma Banga amfanin gaya Miki na Haihu ba Shiyasa ban gaya Miki ba Tunda ke ba Uwata bace.."

Dina Ta karishe Fada tana Sharan kwallah Zakiya da Mamaki da al"ajabin Dina ya gama Kasheta Ta Saki Wata Banzan Dariya da Shewa kafin ta Daka Tsalle Tana Fadin"Hehee...Hehe..Yau Ranar Tsonon asirin Wata ne Wlh kowa Yazo yaji wani abu kunya Kowa yazo yaji..Wlh wanda yasha Tuwo Dani Miya yasha Don Ubansa.."

Take Fada Tana Rike kugu Tana wani Girgiza Su Umma Dake Falo Cikin mamaki suka Rankaya Dakin da Dina Take suna kallon Ikon Allah,Zakiya Sai da Taga an Cika Daki Hatta Da Zainab Dake daki sai da ta Fito Jin Ihun Zakiya Hajiya maimuna Data gama yima wanka arman ta sakamai kaya Ta Rumgumeshi ajikinta Tana ganin Ikon Allah,Zakiya kuwa Sai da Ta Taka gaban Dina Tana wani Girgiza kafin tace"Ahayye...Naji Duk mganar Da kika Fada akaina Ta Ina Talle Zai ma Audi Gori..? Karuwanci Nake Shi kike yi Dina Ko ba haka ba..? Koda na ganki Daman chan kema Shedaniyar kanki ne sanda kika bama Zain kanki ina ina..?ni nasakaki Dole..? Kajimin yar Rainin Hankali mganar Zuwa Wajen Boka kuma ai ba Ni najaki ba da kafarki kika je kuma kika Saki kudi aka yi Mik aiki Lokacin Idanuwanki ya Rufe baki ji bakya gani saboda Zain Ni kawai nawa na Rakaki ne ammh Saboda Kin Raina ma kanki wayau kina Dora Zargin Lalacewar Rayuwarki akaina Kin Taba Zama Kiyi Tunanin ta Taya haka ya Faru..? Gwara ni Wlh Ko yau za"a Fada Albasa ce batayi Halin Ruwa ba ammh Kowa yasan Ubana Malami ne kuma Mutumin Kirki kuma Har Uwata Ta Rasu Tana da Shaida..?kefa..? Wlh ko Kaffara Ba Zan yi Ba Gado Kikayi Wajen Kwartoncin Ubanki..!!

Ta Karishe Fada Cikin Kakkausan Murya Da Gadara Tana kallon Dinan Ido Cikin Ido Dina Dataji mganar Kamar Saukan aradu,Ta Mike da Sauri Tana Zare ido hakama Hajiya Batula dasu Umma Dina Cikin Karaya tace"Kwarton Ubana..! Zakiya Rashin Mutumcinki har yakai kan Mahaifina..?

Zakiya Tace"Kwarai ke kika ja mganar Tayi Tsayi haka...Ko karya nayi Uban naki ba kwarto bane..? Wannan Taron Siyasan Dayake Zuwa Duk Cin mata yake Zuwa yi in ya karyata kirasa Ki Tambayeshi ya Taba Haduwa da Zakiya kawarki Wajen Kwartoncinsa,..? Zai Fada Miki Abokinsa ya Tabakai masa Ni a amtsayin Wacce Zai Raba Dare da ita Sai Kiji mai Zai ce Miki..?

Zakiya Ta Fada Tana Wani Girgiza Jiki,Dina

20 / 37