Chapter 3 Reading Zainazain Book 2 Complete By Janafty Arewa Novels

Zainazain Book 2 Complete By Janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   3 / 37

6K to 9K   out of 108.5K words

Zaina Taji Tadan samu Natsuwa Ranar da yammah kuma gidan ya Cika da Maza da mata sai Shaye Shaye suke sun saka Waka atsakar Gidan suna ta Kida Har Zaina Tayi barci Basu Daina ba Abun yadaina bata mamaki ta Fara Yadda ma kanta Lalle Rayuwar data Tsinci kanta aciki ba Wacce Ta saba gani bane.

Washegari kuma Tun Safe Kuma aka kawo ma Farida Sakon Mota Cike da Kayan kwalama da kayan sawa kayan kwalliya Shopping dai kamar Za"a Bude Shago Tana JintaTana Godiya awaya kamar Harda Kudi aka Turo mata Su kacharalle suka Shigo mata Da kayan Cikin Daki Ammh sai da Ta Tura Zaina Cikin Labulen Wajen Saboda bata son su kara ganinta akwai haka kacha ke ta Dage yana kalle kalle Cikin Bacin Rai Sholly tace"Lafiya kake min kalle kalle Cikin Daki ko Kabani ajiya ne..?

Da Sauri yace"Inafa ajiya..Wannan Hajar da kikazo da ita ne bangani ba ko an har anci kasuwarta ne..? Dogon Tsaki Taja kafin Ta Hankadashi Waje Tana Fadin"Kacharalle ka Fita Daga idona...Iskancinka da kwartancinka ya Fita Daga kan Sa"adiya Domin ita din kanwata ce ba kuma irin Wacce kake Tunani bane.."Cikin Mamaki yace"Au daman sunanta Sa"adiya ah kice Sady Bby ce,wai kanwarki Dama ai Bariki Har Uwa da Uba zaka samu Sholly kebagashi kin samu Uwa ba Uwar mata kamar hakane ba Laifi in kema Ta zama kanwarki Ammh ya kamata ki Fito da Hajan nan kawai ki Tallata ta kowa ya Taya mai Rabo ka kwashe.."Banza Tayi Dashi bata kara mgana ba Ita kuwa Zaina Tana jinsa Jikinta sai Rawa yake Tana Danne kukanta acikin Ranta Tana Tuna tana da fa aure Yanzu in ta Fada wata Rayuwa awannan Gidan Menene makomarta..!?

Ganinta Cikin Wannan Halin yasa Farida Ta zauna Tana ta lallashinta Tana Fadin"Karki Damu da mganarsa haka suke kamar karnuka..Bazan Taba bari Kiyi karuwanci ba Sa"adiya ni zan Dinga Miki komai na Rayuwa Bazan bari Rayuwarki Ta Lalace ba.."Fadawa Jikinta Zaina Tayi Tana kuka Tana Fadin"Anty Farida..Meyasa na baro Su Umma..? Saboda Cikina ne da kuma Tserata da aurena..? Ammh yanzu na Fara Nadaman Abunda na aikata Anty Farida.."

Farida ta Dagota Tana Fadin"Sa"adiya me ya baroki Daga Gidan..? Ki gayamin gaskiya Domin Bana son karya kuma bana Shiri da mai yinta.."Zaina Ta Sunkuyar dakai Tana Digan Hawaye ta Fara Bama Farida Labarinta Tunda Farko Har karshe Har Zuwa Haduwarsu Koda Ta gama Sai ta kara Rushewa da kuka Tana Fadin"Anty Farida Wani Nauyi na Damuna acikin Zuciyata...Firstlove ya Sakamin wani irin Rauni acikin Zuciyata,Bazan iya Juran ganinsa ya auri Dina ba Zuciyata Ta Raunana bazan iya Juran ganinsa da ita ba.."

Farida Sholly Ta Dagota Tana Share mata Hawaye Cikin Taruwan kwallah acikiin Idanuwanta Tace"Ki Daina kuka Sa"adiya Lalle kin Hadu Da Daya Daga Cikin Cin Amanar D'a Namiji..Kinga Tsantsan Cin Amana kam Ayarintarki naga ma Kokarinki da Dauriyanki akwai Ciwo wanda ka yarda Dashi yaci amanarka kuma akwai Ciwo wanda yafi kowa saninka aduniya yaki yarda Dakai Sa"adiya kin ganni nan Nawa Labarin ba irin naki bame ni Sharrin Kishiya ya kawo ni wannan Rayuwar Da kike ganina ammh har yau bana Dora Laifin a kanta nafi Dorashi kam Mami da Abba na da kuma Shi kanshi Ya Musbahun Dayafi Sanina Fiye da kowa ammh ya Rufe ido ya Kirani karuwa Gaban iyayena da ya"yana Sa"adiya Naso na kashe kaina Allah ne yayi kwanana na gaba Har kika Hadu dani.."Tafada Tana Fashewa da wani marayan kuka Wanda Tunda Zaina Ta hadu da ita Bata Taba ganin Tayi kuka ba Zaina na Kokarin mgana Farida Ta Mike Tana Fadin"A"a Sa"adiya karki bani Hakuri..Ki barni nayi wannan kukan Shine samun Saukina da Salamana Ina da Ciwon Zuciya da Hawan Jini in ba kukan nayi ba bazan samu salama ba..Kada ki Damu Watarana In na samu Natsuwa zan baki Labarina kuma nayi miki alkawarin kula Dake da Abunda ke Cikin ki bazan matsa miki ki koma Gida a yanzu ba Saboda Zuciyarki ta Raunana Zan bari sai Lokacin Da kika ga Zaki iya Rike komai kuma ki Daure zan maidake Bauchi Da Hannuna Insha Allahu.."Daga haka ta Tura Kofar Tiolet Ta Shiga Ta kara saka kuka Sai Duk Jikin Zaina yayi Sanyi Yanzu mai kananan Shekaru irin Anty Farida ce keda Hawan Jini da Ciwon Zuciya..? Ya illahi Allah Sarki Hartaji ta Tsausayamata ta kuma Fara Tunanin Zamowarta karuwa ba Burinta bane Dole ya zame mata Ko daga yadda Faridan ke Tafiyar da Rayuwarta Abunda Yafi bata mamaki Sallah bata Wuce ta karatun Qur"ani Kuwa Dataji Tana yi sai da mamakinta ya Bayyyana acikin Ranta Tana Tambayan kanta Dama karuwai na Karatun Qur"ani Ta manta Zamann bariki kazo nazo ne kuma Kowasu Mutane akwai nagari akwai na banza aciki wasu su Dama chan Watsatsu ne wasu kaddaran Rayuwa ke sa su Tsinci kansu Cikin Wani Hali.

Zaina na nan Zaune Sai Taji Ihu Mai Karfi Da kuma karan ana Dukan Mutum,Tun Bata jin Ihun Sosai har ta Fara Ji Domin abun atsakar gidan yake Faruwa Jikin Zaina na Rawa Tatashi Tana gyara zaman Doguwaar Rigar Farida Dake Jikinta Dayake Faridan Bata da Jiki sai kayanta suke zama ajikin Zaina din duk da sun mata Yawa ammh Tana maneji hakan Tunda Faridan tace in Ta samu Lokaci zasu Fita ta Siya mata Wasu kayan

Ta Jikin Window din Dakin Ta Daga Labule Tana leken meke Faruwa Zuly Ce Ta gani Kwance Daga ita sai Sikat karami ajikinta Ba Riga sai Bra gabadaya Jikinta Awaje yake Gashinta kanta mai kama da Hammatan Dan iska Duk ya Bazu,sai wani Katon Namiji bakikirin Dagashi sai gajeren Wando Yana Tsaye kanta da Katon Belt yana ta Tsula mata Shi Tana Ihu Tana bangarewa Tana Fadin"Wayyo Allah na Shiga Uku.Zai kasheni Don Allah..Shafson kamin rai na Tuba nabi Allah bazan kara maka Sata ba.!

Take Fada Tana kuka Tana Sosa Inda yake Dukanta Abunda ya kara Bama zaina Tsoro gasu Deezee dasu Suby nan Tsaye suna kallo suna Dariya,Harda Wasu ma bakin Fuska da bata sani ba Domin Ta Lura ba Dukkansu ke kwanan Gidan ba Sai suyi Kwanaki basu Gida Wasu ma Haryanzu bata sansu ba Basu Gida Gabadaya duk sun Fito Suna Kofar Dakunansu suna kallo Suna Dariya Wata Ma Daga Cikisu Taba Take Sha Tana Fesar da Hayaki Lokaci Daya Tana Fadin"Shegiya Zuly....Bariki ba Riba Gobe ki kara Hannun Bera.."

Ta Kwashe Da Dariya Tana Fesar da Hayaki Zaina Ta Fara kuka Da Tsausayin Zuly ganin yadda Yake Tafkanta kamar Allah ya aikosa Yana Dukanta Yana Fadin"Ni zaki ma Sata Don Ubanki..? Watsatsiyar karuwa kawai Yau sai naci Ubanki naga mai kwatanki Shegiya mayya kawai.."Haka yake Fada yana Dukanta sai ga Kacharalle ya Shigo Har Zaina najin Dadi zai Cece Zuly sai dai Ina Shima Suby ya kallah yana Fadin"Ina Ta gidan Abincin Uwar mata nake jin Ihu Kamar na Kuka ashe kuma su Zuly ne ake amsan na Safe..?

Suby Tace"Eh kasanta Hannun Bera gareta Sata ta karamai itama kamar Jaka Bata iya Rabuwa Dashi,Kusan koda yaushe sai ya Daketa kamar Wata Jakata"Kacharalle yace"Allahu Akbar...Su Zuly dai ba'a Shigo Bariki a sa"a ba.."Yafada Lokaci Daya suna kwashewa da Dariya Harda Tafawa Zaina Taji Wani irin acikin Zuciyarta Ta manta da Gargadin Farida na karta Fita Bata san sadda Ta Fita da gudu ba Ta isa ga Gabansa ya Daga Belt zai Tafka ma Zuly Zaina ta saka Hannu Ta Rike Belt dib Cikin Dakewa Tana kallonsa.

Ba Shafson ba hatta su Deezee da su kacharalle haka suka Saki baki Suna kallon Zaina Wacce ta Yarfe Belt din Tana Fadin"haba bawan Allah baka da Imani ne me tayi maka Zaka Dinga yi mata wannan Dukan..? Kome Tayi maka ya kamata ka Daki mace haka..?Kai baka Daraja mace ne ko kuwa Kai Mata abun Wulakantawa tawan kane.?

Tafada Tana Sakarmasa manyan Idanuwanta,Gabadaya Cak ya Tsaya yana kallonta Da Jajayen Idanuwansa Yana kuma Kare mata kallo Lokaci Daya yana Wani Lasan baki Bata bi Ta kansa ba,ta Isa ga Zuly Dake kwance Tana Kuka Ta Rikota Tana Fadin"Sannu...Sannu Tashi Kinji.."Zuly Ta Dago Tana kallonta Hawaye suka Wanke mata Fuska bata da Zabi Ta Riko Hannun Zaina Data ke Mika mata Ta Tashi Tana Dingishi Jikinta Duk ya Kumbura Saboda Duka Kallonta Zaina Tayi Tana Fadin"Ina ne Dakin ki..?

Zuly Na Kuka ta nuna mata Room4 alamun nan ne Dakinta,Zaina Ta Rikota Tana Fadin"Muje na Rakaki Sannu..."Take Fada Tana Riketa Suna Shirin Fara Tafiya yasha Gabansu Cikin Bacin rai Zaina Tace"Bamu hanya mallam..' cikin Bariki Da zallar Iskanci yake kallon Wuyan Zaina da Rigar Tayi mata Rakwa rakwa Kirjinta ya bayyana,Yake Fadin"Ya zan baku hanya bayan Kudina ta satamin Kuma ta kashesu..Bazan baku hanya ba sai dai in zaki Famsheta ki Biya mata sai na Kyaleku ku wuce..!

Zaina Tace"Nawa ne kudinka..? Cikin Shafa Gemunsa yana mata Wani irin kallo yace"Kudi ne masu yawa Kuma basu Zaki biyani ba mai kyau yar Shila.."Yafada yana wani Dariya Su Deezee suka yi Tsuru suna Tunanin Ina Sholly ko Ta fita ne..? Basu gama Rufe baki ba Zaina tace"Dame za"a Biyaka..?

Kai Tsaye yana kallonta ya Fara Matsowa kusa da ita Cikin Bariki yace"Da wannan Lafiyayyan Jikin naki Zaki Biyani.."Yafada Lokaci Daya yana Kokarin kai Hannu zai Taba Kirjin Zaina kawai yaji an Damke Hannunsa yana Juyowa Kafim ma yagama Gane Waye yaji an Tsinkesa da Wani Mahaukacin mari sai da Belt din Hannunsa ya Fadi Cikin Huci Da Bacin Rai ya Dago Yana so yaga Wata mara kunya ce ta mareshi sai yaci karo da Sholy Tsaye Idanuwanta sun yi Jajir tana Jifansa da wani kallo Zaina kuwa Jikinta ne ya kama Rawa bata san sadda Ta kankame Zuly ba Itama ta Riketa Tana kuka Gabansu Farida Ta Tare Tana Nuna Shafson da Yatsa Tana Fadin"Kul din ka..Karka kara Kuskuran cewa zaka kai Hanunka jikinta sai na Sare maka Yatsu Wannan ba irin su Zuly bane da kananun Yan iskan da ka saba harka dasu bane Wannan Tafi karfinka Kada na kara ganin ko Kallonta kayi in ba Haka ba sai na Nuna maka Wacece Sholly.."

Tana Gama Fadin Haka ta Juyo Wajen Zaina Rai bace ta Finciki Hannunta Tana Fadin"Sakarta..Waya gayamiki kana mgana acikin Rayuwar da mutum ya zabar ma kansa..? Ki barta ya kashe ta mana itace karamar yar iska take Harka da kazamai irinsu Kada ki kara Fitowa koda Kisan kai za"ayi agidan nan Shiga Ciki.."Tafada Lokaci Daya Tana Tura Zaina Dakinta kafin ta Waigo Tana nuna su Suby Da yatsa Daya Bayan Dayan kafin Tace"kun gani ko..?Wlh Tallahi..Ko bayan Idona kuka bari wani Dan Iska yayi ma Sa"adiya Kallon banza ko kukayi mata sai nayi Muku Rashin Mutumci Daya bayan Daya Kun sani na sanku Bani da Wasa.."

Daga Haka ta Juya Fuu Ta Shige Dakinta Ta bar su Suby Tsaye,Shafson kuma yayi suman Tsaye Zuly kuwa Gefe ta koma Tana Makarkyarta Kacharalle ne yace"Tabdijam...Wani kaya sai amale su Shafson sai amaida yawu wannan Hajar dai bata Lasuwa.."



*Ki Biya ki karanta Cikin Salama..Jiya Daga fara Buk har an Fita dashi Waje bazan ce komai ba ammh ku sani Rashin Daraja ne ki jira abun Sata in kin isa mai aji komai kina mallakansa ne ya zama naki..*





*Shakira..*
7/9/21, 3:09 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B20️⃣3️⃣*

*IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*


""Shafson Haka ya Tsaya baki Sake Hannu saman Fuska yana wani Huci Mai Kacharalle zai yi Shida Suby in ba Dariya ba Harda Da Tafawa Adamalle Data Fito Daga Dakinta Da wani BoombShort kamar Tana Juyi Tayi Guda kafin ta Tsaya gaban Shafson Tana Fadin"In Takamarka Daman Iskanci Toh ka Hadu da wacce ta Fika...Sholly Ta isheka komai Kaima ka sani sai dai Hakuri.."Kalaman Adamalle sun kara Tunzurasa Cikin Fushi ya Dauki Belt Dinsa Ya Tunkari Zuly Tana Kokarin matsawa Baya ya saka kafa ya Taliyeta Ta Fadi Ya Fara Dukanta kamar Allah ya aikosa ihu Take da karfi ana jinta Daga Cikin Gidan Har waje

Zaina Dake Cikin Dakin Farida sai kuka Take Cikin kukan Take Fadin"Kina fa ji Anty Farida Har yanzu Dukanta yake yi fa..? Dariyan Takaichi Sholly Tayi kafin Tace"Gidan Karuwan kenan Sa"adiya...Kyalesu kwartonta ne abokin Shanshancinta ya Rainata ne kullum sai ya Daketa kamar Jaka ammh Bata iya Rabuwa Dashi Koda yaushe suna Tare..Mtseww ni bana son Iskanci In mutim zai sha giya yasha Ta Dubu kawai Tunda dai Giya ai duk giya ce.."!

Zaina Ta kalleta Tana Sharan kwallah Tace"Ammh Anty Farida kiji Tana ta Fa ihu.."Farida Tace"sai me..? Ki bar Kukan nan fa Domin yanzu kika Fara gani yayi ta Dukanta bamai Hanashi Sai ma Kara Zugashi da zasuyi Barikin kenan.."Bata ma gama Rufe baki Ba Taji Sowansu kacharalle da su Suby Ko ajikinsu Ita Abun ma mamaki yake bata Indai wannan ce ake Kira Bariki Abun kam ba Tsari kam Wato Gidan kazo nazo ne kuma Kowa Wayansa Shi zai Taimakesa

Jeep din Uwar mata na Parking kofar Gidan Taji Ihu Da Hayaniya Daga Gidan Ta Dago Tana kallon Hajiya zabba"u Lokaci Daya Tana Fadin"Ihu fa kamar nake ji Daga Cikin Gidan nan..? Hajiya Zabba"u tace"Bama kamar ba..ihu ne Nima naji.."Da Sauri Uwar mata Ta Bude kofar Motar ta Fito Tana Bin Wajen da kallo Hajiya Zabba"u ma ta Sauko Suka Fara Tafiya,Yan barikin Dake kofar Gidan suka Fara ganinta Yadda suke Girmamata sai Abun ya baka mamaki,ma"aikatan Gidan Abincinta da sukaji labarin Zuwanta suka Fara Fitowa suna mata sannu da Zuwa Cikin Bacin rai Ta Daga musu Hannu Tana Fadin"ku koma Bakin aikin ku zan dawo gareku.."

Daga Haka ta sakai Cikin Gidan da Sasssfar kamar zata Kifa Hajiya Zabba"u ta mara mata Baya Suna Shiga suka iske su Suby sunyi Dafifi suna Shewa Shafson na ta Dukan Zuly kamar Allah ya aikosa Ran Uwar Mata ya baci Ta kalli Hajiya Zabba"u itama Ta kalleta Batayi Wata Wata ba ta saka Kafa Tayi Fatali da Botokin karfen da Adamalle ta Fito Dashi Zata Debo Ruwa Tayi wanka ji kake kwaram kwaram Chamm!

Saboda yadda Ta Dagi Bokotin sai da ya isa Wajen Shafson ya Dakesa a kafarsa Gabadayan Wajen yayi Tsit,Suka kuma waigo Lokaci Daya suna kallon Wanda yayi wannan aikin Gabadayansu Rusunawa sukayi Ganin Uwar mata da kanta Cikin Ladabi Suka Fara gaisheta Da yi mata sannu da Zuwa Cikin Fadanci da Kirari Kacharalle yace"Manyan Manya mganin kananan Mata kaga Uwar mata da kanta ba Sako ba Hajajju makatan Hajiyar makka da madina Gaki ga Kawarki kuma Sahibarki Hajiyan Allah itama Sannunku da Zuwa Allah yaja da zamanink..!

Bai Karisa ba Uwar mata Ta Dagamai Hannu Tana kallon Shafson Lokaci Daya Tana Fadin"Wani irin maguzanci ne ko nace Tashanshi ne ku keman agida..? Zaman Bariki na yarje muku kuyi min acikin Gidan nan ban baku masauki domin kuzo kuna min Hayaniya ba so Kuke yan anguwa sumin Bore..!?

Tafada Cikim Bacin Rai Cikin Sauri Suby Tace"Bafa wani Abu bane Uwar mata kema kin sani Zuly ce tayi Halin Shi kuma Shafson kinsan sa Dukan Zuly Kadai ke sakasa Kiba.."Tafada Tana wani karkada Jiki Da kallo Uwar mata Tabi Zuly Dake kwance Tana kuka ta Daku kafin Ta saki Tsaki Tana Fadin"Ke ba Iskanci kika Fito yi ba Na lura Sata kika Fito yi ko..? Baki da aiki sai sata Zan Koreki fa Domin naga baki da wani amfani.."

Cikin Kuka Zuly Tace"Don Allah kimin rai uwar mata in kika Koreni ina Zani..? Uwar mata ta bankamata Harara Tana Fadin"Inda kika Fito mana..Gwara Uban kowa Dake..Domin banda Kwana da yin kashi baki da wani amfani.."Adamalle Ta Tabe baki Tana Fadin"Tama Ci da kanta Toh Uwar mata.."Itama din Hararan Uwar mata ta Sakar mata kafin tace"rufemin baki kema ai Duk kanwan jace..Duk cikin Gidanan Daga Sholly sai Rufy su kadai nake Moransu Sauran sai Dai su Cikamin Gida da Kwartanyensu kananan yan Iska Wadanda Ko Wando Uwayensu basu gama saka musu Toh Bata yuyuwa Duk zaku bar min Gidana nayi Sabbin Zubi Tunda Duk Naga baku da wani amfani.."Gum kowacce Tayi da bakinta ba mgana Uwar mata Shafson Ta Sakarma Ido wanda yake kallonta yana Tsiyayan Zufa Cikin Tsirtar da yawu Tace"Kai kuma Daga ina..? Na bani ni Hauwa na bi Duniya na lalace Yanzu ke banda Saunanci me zaki yi da wannan kazamin Zuly..? Tir Dake Wlh Shegiya mai Sufar yan Ruwa.."

Tafada Lokaci Daya Tana Wani Yamutsa Fuska ganin haka yasa Shafson ya Fara Taku Zuwa Wajen Uwar mata yana Fadin da katuwar muryansa"Hajajju Sata f..."Kai kai Tsaya inda kake karma ka kariso.."

Ta katseshi Tana Dole Hanci Hajiya Zabba"u ma Baya Taja Tana Fadin"Hajiya Hauwa haka Gidan naki ya koma..? A"a kiyi sallama Wasu kam sun Jahilci kalmar Bariki gaskiya.."Tafada Tana wani Matse baki kamar Wacce Taga kashi Uwar mata Tace"Umh...Bari kawai Zabba"u Duka Sakarkaru na Tara su bama su samo wani Abun Kirki Ballatana su sayi kayan gyaran nan su gyara kansu kullin suna nan kamar wasu Jakuna ko ni ai bana zauna haka ba Ballatana su da Kuruciyarsu ammh sun koma kamar wasu Tsoffi Daga Wacce Fuska ta Kone sai Wace Duwawu ya Shafe sai Wacce Nonuwa suka kwanta kamar Silafas.."Jin haka yasa Kacharalle ya kalli Nonuwan Suby da suka kwanta kamar Silafas din ya Sheke Da Dariya Yana Fadin"Kwarai Hajjaju makantu Tun ana Tusa su Cikin Rigan Mama ayi Barazana Har suka Daina zama.."Yafada yana wani Dukewa Hararansa Suby Tayi Cikin Takaichi.

Uwar mata Da Takaichi ya Cikata Tacigaba da Fadin"ni kuma Wlh na gama kashe Sisi kan kowaccensu Domin abaya nayi Wahala Dasu yanzu da zasu Famshemin Wahalata ina sai Kayan Haushi kawai Mtaww..Kai Shamo kake kowa..! Zo kaficemin Daga Gida kudinka kuma da Ta sata ka Dawo Da Daddare ka Famshe a Jikin Shegiya Tunda ita Bata da wata Zuciyar Cigaba sai ta Sata.."Ba Musu ya Kada kai yana kallon Zuly Lokaci Daya yana Nuna mata Hannu kan sai sun Hadu kawai kana yaja Babbam Jikinsa ya Fice Uwar mata Ta Bisa da Harara da Zubar da Miyau,yana Fita Ta kalli su Suby Daya bayan Daya Kafin Tace "Ina Zeezee Da Jido Suke..? nassn dai Zee Ta tafi Lagos ta raka wannan Alhajin nata Ita kuma Jido ina Taje..?

Cikin Tura ladabi Suby Tace"Bata gayama kowa ba Uwar mata..Ranar da Sholly Tayi Tafiya Ranar itama Ta bar Gidanan.."Kada kai kawai Uwar mata Tayi kafin Tace"Zan Kirata awaya..Nifa bana son Jaye Jayen Masifa Allah sa wani mai maikon ya Dauketa

3 / 37