Chapter 12 Reading Zainazain Book 2 Complete By Janafty Arewa Novels

Zainazain Book 2 Complete By Janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   12 / 37

33K to 36K   out of 108.5K words

Dashi Ta saka ta koma ta Kwanta Tana Tunanin Bazata iya barci Yau agidan nan ba matukar akace da Kidan nan zasu kwana kuma in ba wani Ikon Allah ba Dashi Zasu kwana Ta Fara Gajiya sai Juye Juye kawai Take,Sai kuma Tunanin Gida ya Bullo mata Ta Fara Kewar Firstlove dasu Umma Hawaye ya Cika mata Ido Tana Dafe da Cikinta Take fadin"Kayi Hakuri..Insha Allahu zan Sadaka da Ko zan sadaku da mahaifinku Watarana..I so much Miss u Firstlove..."Take Fada Tana Share Hawayen da suka Zobomata Ta Koma ta Rumgume Filo kawai Ta Fashe da kuka Kukan kewa da Soyayyah mai Tsanani Kan Firstlove dasu Umma Tana Fatan Allah ya basu Juriya kan Abunda ta aikata Musu.

Cikin Wannan Halin Barci ya Fara Fizganta ganin Shuru Shuru bata ga Shigowar Zuly ba,Barcin nata har ya Fara Nisa Domin alokacin goma na Dare ya Wuce,Suby Ta Daga Labulen Dakin Ta Leka Ganin Hankalin yan Gidan ya Dauke yasa ta Karisa Shiga Cikin Dakin Tana Kallon Zaina Data Dunkule Tana Barcinta Cikin Dariyan Nishadi Suby Tace"Dakyau...Komai zai Tafi Daidai..Nagama da Zuly Tunda na Bata Juice din dana gauraya da mganin Barci Tana chan ta Bingire Dakina Tana Barci Yanzu Lokacin Shafsoon ne bari na Kirashi So sorry Sholly..'

Ta Fada tana kara Sakin Wata Dariya kafin Ta Fice tana Kokarin Fito da wayarta Cikin Breziyanta Sai da ta Fita Kofar Gidan Tunda hayaniyar kida bazai saka Shafsoon ya jita ba,Tana Kiransa ya Daga yana Dagawa tace mai yazo Komai ya Zama Daidai Shi kuma Cikin Dariyan Shakiyanci yace gashi nan Zuwa Daman yana kusa Ya gama Jika kansa da mgungunar maza so yake ya Dagargaza yarinyarnan,Ya huce Takaichi Da Zafin Marin da Sholly Tayi mai gaban Mutane.

Hankalan su Rufy da kawayenta Duk yana Wajen Rawa Shafsoom ya Salalo ya Shigo yana Shigowa Suka ci karo da Suby Ta Dagamai Gira karaf a Kan Idon Deezee sai Abun ya bata mamaki Sai ta maida Hankalinta kan Shafsoon Taga Sadaf Sadaf ya Sulala ya Fada Dakin Sholly ya Kulle Kofa gaban Deeze ya Fadi Ta kalli Suby Wacce Take ta Dariyan Mugunta Ta Shiga Rawa Tanayi Tana Girgiza Hankalin Deezee sai ya Tashi Data Fahimci Abunda Suby ke Shirin aikatawa,Da Farko taso ta Share sai kuma ta kasa Domin har ga Allah bazata so Shafsoon yayi ma Zaina wani Abu ba Kamar fa amana take ga Farida Mikewa Tayi Zumbur Tana Neman Zuly Tunda Tasan Ita Farida ke bama Amanar Zaina sai dai Bata ganta ba Waje ta Fita Neman Kacharalle Har Gidan Abincin Uwar Mata Akace mata yana Kaduna Sai Hankalinta ya Tashi Ta Rasa yadda Zatayi sai ta Tuna Tana da lambar Sholly Da Sauri Ta Dauko wayarta Ta Lalubo lambar Sholly Ta Kirata Wajen Kira Biyar bata Daga ba Ganin ba Mafita sai Deezee Ta Tura mata sako kamar haka.

*Sholly Kina ina ne..? Ko ina kike ki zo Gida yanzu Suby Ta ci Amanarki Tayi ma Shafsoon Kwangilan Yarinyar Dake wajenki Yanzu naga ya Shiga Dakinki ya Rufe....Deezee ce..!*

Tana Tura mata Ta koma Cikin Gidan da Gudu Tana Raba Ido Hankalinta Gabadaya na Kan Kofar Dakin Sholly Gabadaya Bata da natsuwa Gefe Daya kuma Tana mamakin Ina Zuly Ta Shiga..?kodai da ita aka Hada baki Za"a ci Amanar Farida..?Bata samu Amsanta ba Shiyasa ta Fara Zagaye kamar mai Rawa Tana Kuma kasa kunni cikin Dakin Sholly din Abunda yasa Bazata shiga ba Saboda Shafsoon yafi karfinta Dama Kacharalle na nan ne tasan in ta gayamai Shi zai iya Shiga ammh Ita bazata iya da wannan Gabjejen katon ba.

*****

Zaina Na Cikin Barci Taji kamar Tana Shakan wani Numfashi Mara Dadi Gefe Daya kuma Tana Jin kamar ana Tabata Ana Shafa wuyanta Zuwa saman kanta kuma ana Kokarin Cire mata Karamin Hijabin Dake Jikinta kamar amafarki Tayi Zumbur Ta Mike Tana Kokarin Tashi sai Taji wani Kakkauran Hannu yariketa yana neman Maida Ta kwance,Abunda ya bata mamaki,shine ganin Wutar Dakin Tana kashe ne alhalin kuma Ita Tasan bata kashe ba Bata ganin Komai sai Duhu ko Tafin Hannunta bata iya gani Ballatana Taga wanda ke kokarin Maidata kwance ya Danne ta.

Hankalinta ya Tashi Cikin Tsoro Ta Fara ja da baya Cikin Duhun Taga Mutum na Biyota kafin tayi wani Yunkuri ya Riketa Ta Fara Mutsu Mutsu Tana Fadin"Waye..? Zuly ce..? Wayyo Allah na waye nace..?

Take Fada Tana Kokarin kwatan kanta ammh Ina Shafsoon yayi mata Riko na Sosai Cikin Zafin Nama ya Kama Hannayenta ya Murde Duka Biyun Da Dayan Hannunsa Dayan kuma ya saka Hannu ya Tuge karamin Hijabin Jikinta Hade da Ribbon din Data Daure gashinta,sai gashin ya watse Saman Fuskarta,Zaina Taji Numfashinta na Kokarin Daukewa ganin yana Shinshinar Wuyanta Lokaci Daya yana Shafa Wuyanta Zuwa Kirjinta gashi ya Rike mata Hannuwa Numfashi ma Dakyar take yinshi Hankalinta ya kara Tashi Data Fahimci Manufarsa gashi Bata iya ganin ko waye yake neman keta mata Haddinta ba.

Ihu Ta Kurma Lokaci Daya da kuka Tana Fadin"Na Shiga uku Don Allah waye..? Ko waye ya Taimaka Kada ya ketamin Haddi ni Matar aure ce Don Allah kada ka ketamin Mutumcina Don Allah.."Take Fada Tana kuka Tana Kokarin Kwatan kanta Shafsoon ya saki Wata Karuwar Dariya Yana Kallon Fuskar Zaina Ta Cikin Duhun Dakin Yana Fadin"Matar aure..? Matar aure agidan karuwai..? Kuma kike kwana adakin karuwa..? Rufemin baki yau Mai Ceton naki bata nan sai nayi yadda naga Dama ke.."

Yake Fada yana Saka Harshensa yana Lasan Wuyanta Zaina Taji Muryan yayi mata kama da wanda ta sani ammh Ta rasa gane ko waye Ga Zuciyarta na Tashi Jin wani wari na Fita Daga Bakinsa da Jikinsa warin Wiwi da Sigari,Kuka kawai Zaina Takara sakawa Tana Ihu Shafsoon ya Shafo Kirjinta yana Fadin"Kiyi ihun ki yadda kike so..Na Tabbata yau bame Jinki Har sai nagama Abunda zan yi Dake.."

Jin Haka yasa Zaina Ta Fara Kokarim kwatan kanta Suka Fara Kokowa Cikin Hakane yaji ya Tokare Cikin Zaina Wanda yasa Ta saki Ihu Tana Dafe Cikinta Abun sai ya bama Shafsoon mamaki da Sauri ya saka Hannu zai kara Rikota Tayi saurin Zillewa ta Dirka Daga kan Gadon da karfi Duk da yadda Ya"yan Cikinta ke Juyawa alamun an Tabasu,Duhu ne bata ganin Ko gabanta Ammh bata yanke kauna ba ta Fara Bin Dakin Tana Cimnkaro da abubuwa,Lokaci Dayakuma Tana Toshe bakinta kada yaji kukanta ya gane inda take,Tana Ta Lalube Taci karo da Bango Kanta ya Kume sai tayi kasa ta saki Ihu,Shafsoon na jin Ihunta ya Saka Hannu a Aljihun wandonsa ya Lalubo wayarsa ya kunna fitilan wayarsa ya Haske Fuskar Zaina Wacce ganin ya Haskata yasa ta Mike Zumbur Tana Rawan Jiki shi ya bama Cikinta Daman ya Bayyana Shafsoon Dake kallonta Daga sama Har kasa sai ya saki baki yana kallon Katon Cikon Dake Cikin Zaina Ido ya kwalalo waje Kafin ya saki Dariya yana Fadin"Au Daman Cikin Shege kikayi Shine kike wani Fadin ke matar aure ce..? Kice an Dade ana Morewa Nima Kuwa ya zama Dole na More zama kifi Dadi Tunda kina da Ciki ko..?

Yafada yana Kallonta Zaina Ta Fara Ja da baya Tsoro ya Cika mata Zuciya gashi ko Tayi Ihu bamai Jinta Kida da Hayaniya ya Cika gidan,Ta Fara ja da baya Domin sai yanzu ta Fahimci wanene yake neman Keta mata Mutumcinta,Wato Shafsoon ne kwarton Zuly Zuciyarta ta Fara rawa Daman Zuly ba da Zuciya Daya ta Dauketa ba Daman gaskiya Anty Farida ne Datace Dan Bariki ba abun yarda bane shiyasa Kwata kwata bata ganta ba ashe tasan me ta Shirya

Ganin yana Nufota yasa Ta Kai ga Bango Hannunta na kasa Tana Laluban Abun Duka Tunda ba maceto sai Allah Cikin Ikon Allah taci karo da Karamar Tukunya saman Gas Da Ruwa aciki Sai ta Tuna dazu Zuly ta saka Ruwan zafi ai bata Jira komai ba Ta Daga Tukunyan da Ruwanta da komai ta Wurgama Shafsoon sai Saman kansa ya Saki Ihu wayarsa ta Fadi gefe Shima ya Duka Dafe da kanshi Ganin Haka yasa Zaina ta Nufi Kofa da Dan Hasken fitilar Wayar Shafson Ta samu ta Bude Kofa Ta Fice da Gudu Tana kuka Tana Fadin"Don Allah ku Taimakamim zai Ketamin Haddina.."

Take Fada Tana kuka Tana Fita suka ci karo da Deezee wacce Daman ke Zagaye kofar Dakin Ta kasa Natsuwa Ita ta Riko Zaina ganin kamar bata Cikin Natsuwarta Ihun da Zaina keyi yasa Hankalin su Rufy ya Dawo kansu sai aka kashe Kida Daman ga Tsakar gidan da Haske kwai ana ganin Kowa da kowa Tunda akwai Wuta Tuni Duka Hankula ya koma ga Zaina Wacce ke Tsaye Ga Katon Cikinta gaba Daga ita sai Rigar Barci kanta ba Dankwali Duk Tayi wani Buzu Buzu da ita Tasha Kuka Batama samu Zarafin mgana ba sai ga Shafsoon ya Fito Dafe da kansa Ruwa Duk ya Jikasa kansa har ya Kumbura Harda Jini Suby Dake gefe ta Zaro Ido Tana kallon Shafsoom Da Zaina wacce Cikin Jikinta yabama Kowa Mamaki Har da kuwa ita kanta Deezee din.

Shafsoon Kuwa da Ransa ya gama baci ya Nufi Zaina yana Fadin"Wlh baki isa ba..Yau sai na More da Jikinki Kina wani Tsoro kina kyarma,Cikn Jikin ki a ruwa kika sha..? Ina ce wani ki bama Jikin naki yayi yadda yaga Dama Dake..? Toh Nima yau ko Kina so ko baki so sai na Dandanin Zumarki alkawari ne na Daukan ma kaina.."

Yafada Cikin Tabbatar da Mganarsa Yana kuma Nufar Zaina wacce ta Fara ja da baya Tana kuka Suby Ta Ratso Tsakiyar Wajen Lokaci Daya ta Saki Shewa Tana Fadin"Ahayye..Daman Abunda ake ta Boyen kenan Cikin Shege..? Lalle Sholly Ta manta ne Uwar mata bata barin a haifa mata Shege Cikin Gidan Sai dai ta sanda Inda zata kaiki ammh badai nan Gidan ba.."Zaina na kuka Cikin Bacin Rai Tace"Kada ki kara Kiramin Da Cikina Shege..Cikina ba D'an Shege bane Dan Sunna ne Cikakke mai asali.."Tafada Tana Kallon Suby kai Tsaye Wacce ta Sake Baki Tana kallon Zaina Daga sama har kasa Kafin Ta kalli Shafson Tana Fadin"Au Allah..?to kai fa kaji ashe Daman Tana da baki kake Tsaye Jata Zuwa Daki ka aikata mata Da Hujja.."

Ta Fada Cikin Son Zigasa Jin Haka yasa ya Nufi Zainar da karfinsa sai dai me Dezee Ta sha Gabansa Ta Tare Zaina Ta Dawo Bayanta Cikin Daure Fuska Tace"Kada Ka kariso Shamsu..Yarinyar nan Amanar Sholly ne Kema Suby In da adalci bai kamata ahada baki Dake wajen Cutar da wannan Yarinyar ba ke baki ma Tsausayin Halin Data ke Ciki..? Gaskiya ka wuce ka Fita Ko kuma na Kira Uwar mata yanzu na Fada mata..'

Dagashi Har Suby Dariya suka saka Kafin Suby Ta kalli Deezee Daga sama Har kasa Tana Fadin"Topha..Ikon Allah yau kuma Deezee kema Kin zama yar Koran Sholly kenan yo Allah na Tuba Dakike Fadin Adalci anan Gidan Uban waye adali Kowa fa Dan Iskan kansa ne kuma Ita Data kawota Gidan Ai Matsayin Haja take Tunda dai Tsan nan Gidan Gidan Zaman karuwai ne ba Wajen zaman Mutanen Kirki ba saboda haka Ko Zaki Mutu yau sai Shamsu ya More Allah da na san Kema Kina Tare da Zuly Da Tare na sakaku Barci.."

Wani Kallo Deezee ke bin Suby Dashi Kafin Tayi mgana Suby Ta saka Hannu Ta Tureta gefe sai da Ta Fadi Ta isa ga Zaina ta Riko Hannunta wacce ke Zillewa Tana kuka ta Nufi Shafsoon Da ita Tana Fadin"Gata Shiga da ita Ciki acikin Dakin nake so kayi mata Fata Fata In Sholly ta Dawo Ta saka a konani In ta isa.."

Shafsoon yayi Mirmishi ya saka Hannu zai Rike Zaina yaji karaf an Rike Hannunsa Cikin mamaki ya Dakata Lokaci Daya Dashi da Suby suka kai Dubansu kan wanda ya Rike Hannunnashi sai da gabansu ya Fadi ganin Farida Fuskar nan Ba Fara"a Cikin Bacin rai da kuma Nadaman yarda da wasu Datayi acikin Gidan nan Ganin yadda Farida ke Binta da wani Matsiyancin kallo ne yasa Bata san sadda ta saki Hannun zaina ma ita kuma Daman Rauninta ya Bayyana ta isa ga Farida ta Fada Jikinta ta Fashe da kuka Farida ta Rumgumeta Tana Jifan Shafson da Suby da wani Matsiyacin kallo.

Daman Tana Hanyar Dawowa Zaria Taga Sakon Deezee,kiran ma Ta gani kawai Bata Daga bane bakuwar lamba ne ganin Sakon ya Daga mata Hankali Daman kuma Alhaji Badamasi ta Raka Abuja,taro Kuma sai Basu kai yawan kwanakin ba Tafiya ta kamashi zuwa Lagos na Tsawon Sati Biyu Yace tazo tamai Rakiya saboda Zaina yasa ta ce bazata jeba Shi kuma ya kyaleta Shine ya Hadata da Direba ya maidota Zaria bayan sun kai sa ya Hau Jirgi Lokacin Dataga Sakon Hankalinta ya tashi Ta Kira Kacharalle yace mata yana kaduna wajen Uwar mata Bata da Lambar kowa sai ta Zuly kuma wayarta yana Kashe Ranta ya Baci Zuciyarta ta Fara zafi Tana Tafasa,Tashin Hankalinta kada wani Abu mara kyau ya Faru da Sa"adiya Ina Zata saka kanta,Ta Fara Nadaman barinta Hannun Zuly Domin Tana Tunanin da Hadin bakin Zuly komai ya Faru Daman Suna gabda shigowa Zaria ne nan tace ma Direban ya saki Motan ana Jiranta agida nan da nan kuwa ya saki Motar sai gasu sun iso Ta Shigo Gidan ma ba wanda ya sani Duk Tana Tsaye akayi Diraman Deezee da suby Batayi mamaki ba sanin Suby Daman bata kaunarta.

Bata iya Cewa komai ba kawai kai ta Kada kai Bayan ta Dago Zaina Ta Share Mata Hawaye Tana Fadin"Ki daina kuka..Matukar Ina Raye Haka zan maidaki gaban Iyayenki ko kwarzane bai Sameki ba..!kai kuma Katon banza Sakarai Wlh sai na Kulleka sai ka gane da wa kake Zencen,ke kuma Karamar yar Iska ba zan ce Miki Komai Ki Saurari Mganar Uwar mata..Deezee nagode Sosai Sadiya Muje Ciki.."

Ta Karishe Fada Tana kama Hannun Zaina Zuwa Dakin Har sun kai Kofar Dakin Daga Suby Har Shafsoon sun kasa mgana Saboda sanin Sholly zata aikata Suna Shiga Dakin Farida ta maida Kofa ta Rufe kaawai sai Wajen ya Dau Ihun Rufy da abokanta da su Abokan su Jido ran Shafson ya baci ganin Deezee ta kalleshi Ta saki Tsaki ta Wuce kawai sai ya Shake Suby Yana Fadin ta Biyashi Kudinsa ganin Zata mutu ne yasa Mazan Dake Gidan suka kwace ta ammh Fa Taci na Jaki Domin har Ta Taba 5k cikin kudin nan 15k kadai ya samu aciki Kuma ba wanda ya kwaceta Banda ma Dariya Da Busan Sigari Babu Abunda su Rufy keyi Duk Zaina da Farida na Daki suna Jinsu basu kara Fitowa ba.

Koda suka Shiga Dakin Tambaya Daya Farida Tayi mata Taci Abinci tace mata eh..Sai tace ta koma ta kwanta Ita kuma Ta Fada Tiolet tayi wanka Tazo Tayi sallolin Dake kanta ta Sauya kayan Barci Ta kwanta Gefen Zaina Jin Motsinta Daman tasan Batayi Barci ba Tace"Kada Ki damu Cikin Satinan zamu bar Gidanan..Alhaji ya bani Kudi masu yawa Zuwa Gobe in kacharalle ya Dawo zai Samamin karamin gida na Siya mu koma Chan Hankalina zai Fi kwanciya Duk kuwa Daman da nasan Kafin Gobe Uwar mata baxata barki Ki Zauna mata agida ba.."

Zaina Ta Juyo Tana Fadin"Saboda Mene..? Farida tace"Saboda Abunda muke Boyewa ya Bayyana..Ko nawa zan bama Uwar mata bazata Taba yarda ki Haihu manta agida ba..Ta Hana kuma Dokarta ce Duk wacce ta bari Tayi Ciki Zata Koreta saboda haka Ki Zama Cikin Shirin Na Riga na sani Tuni Uwar mata Ta samu Labarin Komai Daman ko Bata Kirani ba Ni zam Kirata na gayamata Tayi mganin Suby Shafsoon kuma Kilama Yan sanda sun kamashi Domin Tun Ina Mota nayi waya da Shugaban Headquater su na nan Sabon gari Zai gane Kuransa ne.."

Zaina Tayi ajiyar Rai kafin tace"Allah ya kaimu..Ammh Tare da Zuly zamu Tafi ko..? Kai Tsaye Farida tace"A"a ke wannan Abun da ya faru bai baki Tsoro ba..!?

Zaina Tace"Ba laifinta bane itama yaudaranta Tayi..Tace fa mganin Barci Ta bata fa Tayi ta Barci Tun dazu.."Farida tace"Uhmm..Ki kwanta sai da Safe."Daga haka ta Juya Baya Tana Jan Blanket Ganin kamar yarinta da kuma Girma Cikin Kudi suna Damun Rayuwar Zaina Har yanzu.

*****
Washegari Tun Safe Sai ga Kiran Uwar mata Farida Bata Daga ba sai da ya katse ta Kirata da kanta bata ma bari Tayi mgana ba Ta Shiga Koramata Bayani kan Suby ta kuma ce ko Ta Kirata Tayi mata mgana Ko kuma Ta sakayata kamar yadda ta sakaya Shafsoon Tun Jiya jin Haka yasa Uwar mata tace Zata Kira Suby Taci Ubanta Tun kafin ma Uwar mata Tayi mganar Zaina Farida ta gayamata Zata Bar Gidanta Zata Siya wani Gida ta Koma Inda Sadiya Zata Haihu Cikin Salama.

Uwar Mata Da Taji Haka Cikin Tashin Hankali tace"Harda ke kuma Sholly..? Ina zaki kuma Ai ita Ta Karyan Dokan ki barta Tatafi mana.."Farida tace"A"a Ba Laifi Tayi ba Nice mai laifin Domin Daman da Cikin na kawotq na kuma san da Dokar karki Damu Komawata bawai yana Nufin Rabuwarmu bane Ana Tare.."Uwar mata Tace"Ban yarda ba Sholly in kin Dage sai Kin Kula da wannan yarinyar naji ki Zauna nan da ita Har ta Haihun ina ce ba Shikenan ba..?tunda ke kika Zabar ma kanki Rumgumar Dan Gaba da Fatiha wanda ba"a san ma waye Ubansa ba.."

Da Sauri Farida tace"Ba Dan Gaba da Fatiha bane Dan sunna ne Cikin Sadiya Kamar kowani D'a da iyayensa ke alfahari dasu mganar kumana zauna da ita anan ta Haihu bata Ayanzu ban yarda da kowa ba Bariki ce Gidan fa nazo kazo..Bazan iya zama ba Saboda Cikin Satinan Zamu sauya wajen zama Kada Ki damu zamu yi mgana ta waya. "Daga haka ta yanke Kiran Hankalin Uwar mata ya Tashi da mganar Farida tana ganin kamar in Tatafi ta Raasata kenan Hajiya Zabba"u ta gayama Komai ita kuma ta bata Shawaran Ta Kira Suby Taci Ubanta Tukunnah.

Haka kuwa akayi Uwar mata ta Kira Suby Ta Zageta sosai ta kuma Gargadeta kan Sholly ta kuma ce Tayi Hankali ba Domin ita da yanzu Tana Sakaye kamar Shafson Hankalin Suby ya Tashi Jin Farida ta saka an kama Shafson sai ta Shiga Taitayinta Uwar mata kuma aranar da yamma Ta Shigo Zaria ita da Kacharalle Da Hajiya Zabba"u kan Farida kada ta koma wani Gidan da zama ammh suka gama mganarsu tace Tana kan Bakanta Uwar mata taji Tama Tsani Zaina

12 / 37