Author : Jamila Janafty Category : Romantic Hausa Novels
ba Tunanin Kowa yake ba sai Tunanin Yanzu Dama Da Gaske Zainarsa Ta barsa..!? Wani Hali Take Ciki..? Ina Take a Halin yanzu..? Yaya Abunda ke Cikinta..? In ya Tuna Haka acikin Zuciyarsa Rauni yake Ji Sosai kamar ya Zauna yayi ta kuka Haka akeji.
Damuwarsa Ta Ragu ne saboda Yadda Yan"uwa kowa Hankalinsa ya koma kansa Domin Yanzu Zain ya zama Abun Tsausayi kuma Kowa ya Shaida Abunda ya Faru Tsakaninsa Da Dina Wata kaddarace ba wai Domin baya son Zaina ba Kowa ya Shaida wannan Kaunar Dayake mata Gashi Dalilinta yana neman ya Zauce Umma Da Nene Kusan Dakin Sadiq suke Wuni suna Kula Dashi Motsi kadan sun kama Tambayansa Ko yana Son Wani Abu ne Umma Tayi kuka Tana Rokon Zain Daya yafe mata Itace Sanadiyar Tafiyar Halima Shima ya Rumgumeta yana Share mata kwallah,yau gashi Umma Ta Cire alkunyar Data kemai Tana Nuna mai Dukkan Kulawarta Ita da Nene sai ka Rasa waye yafi Wani Kula Dashi Haka Abba ma in ya Dawo Daga Office yana Tare da Zain din yana Ta Mai Nasihan Daukan Kaddra Kuma Alhamdulillah ana ganin Cigaba Sadiq ya koma makaranta Haddir ma Ya koma Gidan Alhaji Tsoho Tunda yaga Zain din ya Fara samuwa sai dai Yace bazai koma Chan Lowcoat ba Ba Firstlove Dole kayansa aka Debo masa ya Tare gaban Iyayan Nashi Suma Hakan ya yi Musu Dadi Domin yanzu Sun Fi Bukatarsa Kusa Dasu Fiye da Kowa.
Goggo Halima Ta koma Gada Da Tarin Damuwa na Farko Batan Halima Na Biyu Halin da Zain yake Ciki Ranar da Zata Tafi Da Tazo Ta kara Dubashi Suyi Sallama kuka Reras Zain yayi ma Goggo Halima Itama kukan Take Tana Shafa kansa Tana kuma Gayamai ya kwantar da Hankalinsa da Izinin Lahi lafiya lau Halima Zata dawo Garesa Ita da Abunda ke Cikinta Abba ya bada Direbansa yakai ta Har Gida Da Sha Tara na arziki Koda Ta Koma gida ya Fara Cika da yan"uwa Domin Daman Hankulansa atashe yake da Batan Halima da kuma Labarin da Matar Isuhu Tazo Dashi Goggo Halima Tana kuka Tana basu Labarin Halin da Iyalan Alhaji Tsoho ke Ciki na Batan Halima sai ma suka ga ai kara zasuyi musu na Tayasu Add"an Allah ya kare Halima Duk inda Take Allah kuma ya Bayyanata Ita da Abunda ke Cikinta.
Zareena ma Jawaad yazo ya Dauketa ana Gobe Zasu Tafi,Daman Zarena ta gayamai Abunda ya Faru Domin bai samu Zuwa Daurin Auran Hamdiya ba Shima yayi ma su Umma Jaje sosai kafin Zareena Tayi sallama da iyayanta Tana kuka Sosai Suka Tafi Bayan Sun Biya Tayi ma su Alhaji Tsoho Bankwana chan ma da kuka Suka Rabu Tana kuma Fatan Allah ya Bayyana Halima Ko domin Dan"uwamta Zain ya koma kamar yadda Ta sanshi,Bayan Tafiyan Zareena sai Gidan yayi Shuru Kowa kagani Ba wani Walwala Zainab Ta koma Zuwa makaranta Saboda sun Fara Jarabawa.
Allah Sarki kawar Zaina Laila Tazo Gidam Umma Tana ta kukan Batan Halima Tace Rabon Data ganta Tun Zuwanta Gidanan na Karshe Ta Shiga Har Wajen sa suka gaisa yana Ce mata Taga Yanda ya koma ko..?Firstlove Ta tafi Ta barsa In Tasan Inda Take tayi ma Allah da Annabi Ta gayamai ko nawa ne zai iya bata indai Zata gayamai Inda Zainarsa take zai iya bata. "laila Tun Tana Daurewa Sai da Ta Fashe da kuka Tana mai Rantsuwa Wlh bata san Inda Halima Take ba Umma ce Tajata suka Fita Daga Dakin Haka ta bar Gidan Tana ta kuka kamar karamar yarinyar Makaranta ta Wuce har sun Fara Jarabawa,tayi kukan Rashin kawa kamar Halima Tana Tuna Rayuwarsu a makaranta da Son karatun Zaina ammh yau Wannan Burin nata ya Tashi a abanza Duk wani Motsi na Zuciyarta sai Tayi Addu"an Allah ya Kare Halima aduk inda Take karin Abunda ke sakata kuka Dataji Labarin Halima da Ciki Ta bar Gidan Sai Taji ta kara Raunana Tana Fatan Allah ya Tsareta aduk inda Take Allah yasa Ta Fada Hannu Nagari...
Bangaran Dina Kuwa Jikinta Yayi Sanyi Ganin yadda Zain ya koma Allah ya gani Tana Son Zain Ko Zaman Datake agidansu Saboda Kaunar Data kemai ne,Tana Shiga ta Dubashi Safe da yammh Ammh In ta gaida Zain baya amsa mata kansa ma yake kaudawa Saboda bayason ganinta Tana Tasomishi da wani Miki kuma yana ganinta Akan Itace Faruwan komai,Sai da Nene tamai mgana kana yake amsa mata in ta Shigo Gaisheta Wani Abu Dake sukan Ransa ganin Cikin Jikin Dina Har ya Fito Nene tace Dinar Tana Daga Cikin Mata masu Girman Ciki Alhaji Tsoho yayi ma Haddir mgana kan zai Rika Duba Dinar agida Har Zuwa Ta Haihuwa Saboda kada asamu Wata Matsala.
Yanzu Dina Ta Rage zaman Daki,Tana Fitowa Falo Ta zauna Tayi Shuru,In Taga Umma tana Gaisheta Sai dai Umman ne bata mata wani kyakyawan kallo hae Gwarama Nene,Harta dasu Saudart Dake yara Dina ta Fahimci Sun Tsaneta Shiyasa Take Allah Allah ta Haihu a Daura mata Aure da zain dinta su koma Gidansu bata Damu da Kowa ba ada Tana Jin Dadi Da Tafiyar Zaina sai Daga baya Da Komai ya Rikice ta Fahinci Mganar Zakiya Gaskiya ne Datace Tafiyarta ba Mafita bace Domin Zain Zai zama sai ahankali kuma ko Ta aureshi Baxata Ji Dadinsa ba aikuwa Tagani Gashi Ta kanta yana neman ya Fara Hauka,Wannan Dalilin yasa Tayi Laushi ammh acikin Ranta Tafi Kowa Murnan Hakan Kuma Tana Fatan Allah yasa kada Haliman ta Dawo Taje Chan Ita da Abunda ke Cikinta su mace ta zama ita kadai ce Tauraruwa awajen zain Kuma Uwar ya"yansa,Zakiya dai bata kara Zuwa ba sai dai suna Mgana ta waya Lokaci bayan Lokaci.
Su Baban Kaduna da Daddyn Abuja kullum Cikin Kiran waya Suke Tambayan ya Jikin Zain..? Kuma ba wani Labari ne..! ? Haka su Inna Hannatu suma Hankula dai sun Fara Kwanciya ganin Zain din ya Fara Dawowa Hayyacinsa sai dai suna ta Addu"an Allah ya Dawo da Halima gida Cikin Koshin Lafiya ita da Abunda ke Cikinta Allah kuma yasa Ta Fada Hannu Nagari Haddir kam ya Cika Aminin kwarai Kullum in ya Dawo aiki yana Wajen Zain yana kara Bashi Baki Shi Zain zai tama mganganu yana Rokonsa ya Tashi ya rakasa Neman Firstlove shi kuma yana Nuna mai Kada ya Damu Zata Dawo Sunanan suna gayama Allah Shima ya Cigaba da gayama Allah aduk inda Take Allah ya Tsareta Ita da Abunda ke Cikinta.
Allah Sarki Zafeera Tana chan kano Duk ta Rame Saboda Damuwa Jarabawan ma Tana dai yi ne kawai ammh Tafiyar Halima ya Tabata Sosai Hakama Faruq na chan Chicago Cikin Damuwa Hotunan da Zafeera Ta Turomai ne wanda suka Dauka Ranar Bikin Hamdiya ne yake kallah yayi ta Sharan kwallah haka in ya Kira su Umma yayi ta Fadin Umma yanzu Shikenan haka zamu zauna Ukti ta bar Gida..? Yanzu in na dawo Hutu bazan ganta ba..? Umma sai Ta Share kwallah tace"Sai Hakuri Faruq..Addu"a zamu Tayata Dashi Allah yasa Tana Hannu Nagari Allah kuma ya Tsareta Ita da Abunda ke Cikinta,Haka zasu gama Zuciyoyi ba Dadi Zafeera kam kullim Dare sai Tayi kuka In Tana kallon Hotunansu Da Zaina Tun suna Yanmata Da wanda suke da Faruq tun suna gida album guda Gareta Tayi Ta kallo Tana kuka Tana Fadin"Allah ya bayyana mana ke Ukti Aduk inda Kike Allah ya kareki Dake da Abunda ke Cikinki.."Tanayi Tana kuka Sai da Shema Taga Abun nata ya wuce na Lafiya Ta Sanar da Inna Rukayyah Kana Tazo Tana Ta lallashinta Da Nasiha Ta kuma karbi Duka Hotunan Datake kallo yana sakata kuka ammh Duk da hakan Damuwar Abun na Cikin Ranta Karatun ma Jarabawar Ma Tana dai yi ne kawai ba Domin Tana Fahimta ba Fatanta akoda Yaushe Allah ya Tssre Ukti..Allah ya Sa Tana hannun Wadanda zasu kula da ita Allah kuma ya kaddara suna da Rabon ganawa da juna Ameen.
******
*Zaria.*
Zuwa yanzu da Zaina keda Wajen kwana Goma a zaria akuma Gidan Uwar mata Hannun Aisha Farida Sholly Zuwa yanzu Ta Fara Fahimta wani irin Gida Take Ciki Ta kuma Fara Fahintar me ake kira Bariki Ta kuma Fara Fahimtar Wadanda ke Gidan irinsu Zuly Suby,Da Deezee Da Su Rufy Ta Lura Sauran kamar basunan Domin wasu Dakunan bata Taba ganinsu an Bude su ba
Ta Fahinci kacharalle irin kawali ne mai kai ma Maza Mata Suna Shashanci Dasu Domin Duk shi yake kawo ma su Suby Costumer,Ta kuma Lura agidan suna Bala"in Tsoron Farida Ko kusa da Dakinta basa Zuwa Batare da Izininta ba, kuma kamar Faridan Tafi Shiri da Zuly Domin Ko wani Abu ne Zata kyautar ita take bamawa Tunda Ita Zuly kamar itace karshe agidan Barikin bai karbeta ba Watarana ma Abunda Zataji Gagaranta yake,Sun Ji gargadin Sholly da Uwar mata bamai Shiga Sha"anin Farida da ita Tunda bama Fitowa Take ba sai dai in Dambe ya Tashi Ko wani Abu ta Tsaya Jikin Window Tana Kallo Tana Hawaye Domin Yanzu Ta Daina Tsausayin kanta Ta Fara Tsausayinsu Suby Tana Tunanin in BakaFito Duniya ba ina Zaka san ana irin Wannan Rayuwar...?
Tunda Farida Ta kawota Gidan Bata Fita Taje wani Waje ta kwana ba ammh Takan Fita Taje Ta Dade kafin ta Dawo In ma Girki ne Zuly take sawa Tashigo Dakin Ta Girka mata ko Kuma Ta bama Kacharalle Kudi Tace ya kawo ma Sady baby kamar yadda yake Fada abinci Taci kafin ta Dawo kwarai Farida ta Cika alkawari Domin Banda wanka Babu Abunda Zaina keyi sai dai taci mai kyau tasha mai kyau ta koma ta kwanta Ga Kallo Farida Tna kunnata mata Saboda Debe kewa ammh bawai Domin Tana Fahimta ba cikin Lokaci Ta Fara maida Jikinta,ga mgangunar Da Likita ya bata suna sakata Kiba Laulayin nata ma ya Ragu yanzu kuma maida Jikinta Take yi Tayi wani Fresh kowa ya ganta yaga mai Cikin Datake samun Hutu Duk da Farida ta Zame ma Zaina garkuwa bata Sakankance ba Ta manta da Addu"a ba, Koda yaushe Rokon Allah take ya Tsareta ya kuma Tsare Abunda ke Cikinta Saboda cika alkawarin Datayi ma Firstlove.
Babu Wanda yasan Tana da Ciki Sai Farida kuma Bata gayama Kowa ba ko Uwar mata bata gayamawa ba,Kuma dogayen Riguna Take sakawa Cikin Daya Fara Tasowa yake Boyeshi Ko kuma pakistan Riga da Wando Abunta kanta kuma Sau Daya Farida Ta kaita cikin Sabongari aka ggyara mata akayi mata Kitso,Ba wanda Farida Ta yarda Tayimgana Dashi Daga Kacharallle sai Zuly Suma ba wai Ta yarda dasu bane kawai Tafi yarda dasu akan kowa na Gidan ne Shiyasa in ta Fita ta kan Bar Zaina da Zuly Tare acikin Dakin Tun Zainar bata sakin jiki Har ta Fara saki da Zuly Wacce Tace mata ainihin sunanta Zulaiha ce kuma ita yar Kauyen Yashe ne Dake garin Katsina Daganan ne bata gayamata komai ba ammh Zaina Tayi alkawarin sai ta Tambayeta Watarana me ya kawota wannan Rayuwar..? Ammh sai ta yanke acikin Zuciyarta Anty Farida Zata Fara Tambaya Labarinta Domin itace Bata mata kama da Wacce Rayuwarta ta Dace da zama karuwa ba yadda Take da Zuciya mai kyau ammh Faridan Taki ce mata komai ko Tayi mata Mgana sai tace mata Zata gayamata Komai Watarana.
******
Yau ma kamar kullum Farida Tun Safe Tayi Wanka ta Chakare Kwalliya kamar zata gasan kyau,Tace ma Zaina kaduna Zata Je Direba ma yazo Daukanta a wata katuwar Mota Kafin Tatafi Ta Kira Zuly ta Roketa Ta Zauna da Zaina Ta Tambayeta Abunda Take so Taci Ta Dafa mata Ta saka mata Ruwan Wanka Tayi wanka ta kwanta Ta Huta sai Zuwa Dare Zata dawo.
Da Gudu Kuwa Zuly Daman Tun Jiya Rabonta da Cin wani Abinci Daman Wajen Sholly Take samu Sai Wajen Sady kuma ita yau ba Gida Ta kwana ba Taje Hause Services,Har Farida Tatafi Zaina na kara wani Nazari akanta Tun da Tazo Gidan Bata Taba ganin Farida Wani Kato yazo Wajenta ba Sai dai Ta kanyi mgana awaya Ko kuma aturo mata Sako ko kuma azo da Mota adauketa Tun Safe sai yammah Zata Dawo da Shopping kalakala nata Dana Zaina Komai ta samu sai ta Siyo ma Zaina kayan kwalama irin na masu Ciki har Gajiya Zaina Take da Cinsu Duk Ta Tusa shi Cikin karamin Firizan Dake Dakin Kada ya Lalace Ita dai da Idanuwanta Bata Taba ganin Wani yazo wajenta ba,ammh Tasan Farida Tana Harka da manyan Mutane Domin in ba Haka ba su waye ke bata kudi..?badai irin Wadanda su Zuly ke harka dasu ba Ko Ita ta Raina su irinsu Shafsoon.
Zaina na Saman Kujera,Zuly Ta Shigo Cikin Fara"a suka gaisa Kana Tace mata me zata karya Dashi..?Zaina tace Ta Bata Complex tasha kawai Cikinta ya Cika Tasha Icecream Jiya Da Daddare da nama,Cikin Sauri Zuly Ta kunna gas ta saka Ruwan Zafi ta Hadama Zaina Complex cikin wani karamin Kofi Ta mika mata ta Fara sha kenan Taga Zuly na kallonta sai Tace ta Hada itama Tasha Ta kuma Dafa wani Abu Taci Karta Damu.
Kamar an saka Zuly agidan Aljannah haka Taji nan da nan ta Hada Complex Kofi Daya Ta Tadashi,Da Sauri Ta Dora Indome guda Uku Ta Dafa Ta Hada da kwai Biyu,Bayan Ta gama Ta Juye afilet ne Zata Fara ci sai Zaina Tace Ta Daga Labule Saboda ba wuta Zafi ya Fara Shigowa Taga Zuly sai Zufa Take Nan da nan kuwa Tatashi Ta Daga Labulen Fuskar Tsakar Gida na kallonsu.
Tsausayin Zuly ya kama Zaina ganin yadda Take cin Abinci Hannu baka Hannu kwarya Allah Sarki Itama ba Domin Ta Hadu da Anty Farida ba Da Tana Cikin Wata Rayuwa Mikewa Tayi Tsam Ta Bude Fridge ta Dauki mata Roban Yourghot din da Farida Tazo Mata Dashi Jiya Bata sha ba da Maltina Guda Daya Ta Nufeta Dashi Tana Zuwa Ta mika mata Zuly Data Fara Dawowa Hayyacinta Ta Dago Tana kallon Zaina da Sigan Tambaya Cikin Tsausayinta Zaina Tace"Karbi Ki sha..!
Mirmishi Zuly Tayi mata kafin Ta karba Tana Fadin"Nagode...Sadiya.."Tafada Tana bude Maltinan ta kwankwade Rabi kana ta Ijiye komawa Zaina Tayi Ta zauna Tana kallonta kawai Dukkansu sai sukaji Muryan Adamalle akansu ta saki Shewa da Guda Da Sauri Zuly Da Zaina suka Dago Suna kallonta Zuly tayi ma wani kallo Kafin Ta kura ma Zaina Ido Tana kallonta Ganin Ta Cikin pakistan Riga da Wando ammh Ta yane kanta da wani karamin Vail,Baki ta Rike kafin Ta kara Leko Da kanta Dakin Tana Fadin"Ba Shakka Hajiya Zuly..Daman ai ke haka zaki kare ba Zuciyan neman nakai sai dai Kwadayi..Karki manta dai Duk wanda yahau Motar kwadayi Karshensa Tashar Wulakanci muna nan Dai zamu gani.."
Tafada Tana kara kallon Zaina ganinta Ta kara Girma da Fari Tayi kuma Kiba Tana mata wani kallo Zaina ta kauda kanta kawai gabanta na Faduwa,Zuly ce ta Dago Ta kalleta Tana Bude Yourghout din Gabanta Tace"Eh din naji ai ba Wajen wata naje yin kwadayin ba ko..? Mtsww Kema kiji Da kanki Don Allah kafin Kizo Kiji da wata Mun Riga mun san komai Shikanshi Farkan naki Bake ke ke Ci dashi ba..? Me yake baki banda Yazo yayi Shaye Shayensa ya Tila miki Amai ya barki da Kwashewa..?hmm munsan komai Fankan Fankan ne ai bata Bada Kilishi.."
Tafada Lokaci Daya Tana Zabgama Adamalle Harara Turus Adamalle Tayi Jin yau Zuly Tayi mata Wankan Tsarki Dariya Taji Daga bayanta Tana Waigawa Taga Deezee ce Daure da Towel da Botiki Zata wanka Sai ta Saki Dariya kafin Tace"Bariki Ba riba..Komai kayi ba Sirri sai kajishi aduniya.."Ta kara Dariya kafin ta Wuce bakinciki ya kama Adamalle bata kara mgana ba ta Wuce tana wani Turo Kugu kamar Wata mai Kurga.
Da kallo Zaina Ta Rakata acikin Ranta Kuma Tana Fadin Topha,Ita dai Tana ganin Rayuwa kala kala bata Dawo Hayyacinta ba sai da Taji Zuly Tayi wata katuwar gatsa Kana ta Kalleta Tana Fadin"Alhamdulillah ya kamata Kice Zuly..Irin wannan gyatsan Bata da kyau Annabi ya Hana.."..
Zuly Ta kalli Zaina kafin Tace"Nagode Sa"adiya.."Kawai Ta iya Fadi kafin tace Alhamdulillah a Ahankali mikewa Tayi Tana Fadin Bari ta Juyema Zaina Ruwan wanka kai ta Girgizamata kafin tace"bar wankan nan ba yanzu ba...Zauna Don Allah dama ina so Nayi Miki wata Tambaya..?
Komawa Zuly Tayi ta Zauna Bayan Ta kauda Filer din Datagama ci Daga gabanta Cikin Mamaki Tace"Allah yasa na Sani Sadiya.."Zaina ta gyara Zama tana kallon Zuly kafin tace"Meyasa Kuka zabi irin wannan Rayuwar ne Zuly naga ku kan ku baku jin Dadinta banda Wahala da Wuya Babu Abunda kuke ci Ina amfani Rayuwar da Abunda Zaka ci mana yana Gagaranka Ki koma Gaban Iyayenki mana Zuly kinemi gafaransu Ki Tuba ga Allah Wlh na Tabbata Rayuwarki Zatayi Daraja Fiye da yanzu da Babu Komai Cikinta sai Rashin Kima da Rashin Daraja Kullum fa sai da wannan Katon yazo yayi Ta Dukanki kamar jaka.."
Zuly Ta Sunkuyar dakai Hawaye suka Zubo mata Cikin Share Kwallah Ta Dago Tana Fadin"Da gaske ke kanwar Sholly ce Ta Jini..? Zaina ta gyada mata kai Mirmishi Zuly Tayi kafin tace"Ko Baki Fadamin ba Nasan gaskiya baki Hada komai da ita ba..Zan gaya miki Wata gaskiya Kinyi Sa"a Samun Uwar daki Farida Bazata Taba Cutar Dake ba Macece mai Zuciyar Zinare Shiyasa ma Uwar mata Ta barki Kika Zauna awajenta Batare da wata Matsala ba,Saboda Sholly Tana Tara ma Uwar mata Jari Sosai Fiye da Zaton kowa Shiyasa Ta kaasance yar Gaban Goshinta.."Zaina ta gyada kai Tana Fadin"Na Fahimci hakan ammh ku meyasa bakwa Tara mata kudin Data ke so..?
Zuly na Sharan kwallah Tace"Ni ahakan ne zan Tara wani Kudi Sady..? banda Shafson ba Namijin Dake kulani Shima na In samu Abun d zan ci da kaina ne,Kullum in yazo Wajena Bayan ya kwantani kafin ya bani Wani Abu sai ya Dakeni ya maidani kamar Wata Dabba Daya Turke in zai Bata abinci sai ya Daketa Sa,"adiya Kada Kiji Watarana zaki Sha"awar wannan Harkan Bariki batayi ba..Bariki ba Rayuwa bace sam ."Ta Fada Cikin kuka Zaina ta Rarrafo Gaban Zuly Tana Dafa kafadanta Lokaci Daya Tana Fadin"Nasani Zuly Tunda nazo Gidan kece wacce na Fara Tsausayamawa..Shin Meyasa bazaki bar Wannan Rayuwar ki koma Gaban iyayanki ba..?
Zuly Tayi Mirmishi Tana Zubar Hawaye Tace"Ina ina ma..Ina ma ace Ina da Iyayen..Da ina da Uwa da Uba da kuma Tsayayyin Dangi Da baki ganni anan ba Sa"adiya..Ni Da