Chapter 17 Reading Zainazain Book 2 Complete By Janafty Arewa Novels

Zainazain Book 2 Complete By Janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   17 / 37

48K to 51K   out of 108.5K words

Shirya Tunda dai Shi baxai yi mata baki ba kada ta kara lalacewa yanzu ma ya Ta kaya..? Ammh mganar gaskiya wannan yaron bai kwantamai arai ba yana ganin Kamar Zakiya Zata Tafka wani Kuskure ne ammh zai ce bincika akwai Wani abokinsa achan Yola yaji Wani abu game da yaron.


******

*Zaria..*


Zaina na Zaune akasan Cafet Din Dakin ta mike kafafunta da suka Kumbura Zulaihat na Gefenta Tana dan Mtsa mata Kafafun suna Hira sama sama Farida kuma yau tana Gida Bata Fita ba Tana kan kujera Tana Latsa wayarta

Zaina Zata muskuta sai Taji bayanta ya kage ta Fara Cije baki Tana Fadin"Wash...!Da sauri Farida tayi wurgi da wayar Hannunta Ta kariso Gareta Hakama Zulaihat Duk ta Rude kusan tare suke Tambayanta Lafiya..? Wani abu ne ke Damunta..? Me take ji..?.
Abun sai ya bama Zaina Dariya ma sai ta Dara Lokaci Daya idanuwanta sun Cika da kwallah tace Cikin wani abu Dake Fitowa Daga Kasan Ranta.

"Allah Sarki Umma..Allah Sarki Firstlove..Goggo Halima da Sauran yan"uwana na Tabbata addu"arsu ce Ta Fado ni Dani Hannayen masu kula dani Da so na..Allah zan gode mawa kawai Domin Nayi Rashin Wasu ahalin yau gani Cikin wasu ahalin.."Tafada Tana Sharan Kwallah Daga Faridan Har Zulaihat din kusa da ita suka Zauna suka sata atsakiya kowacce Ta Dafa kafadarta Cikin Soyayyah da kauna da Muradi mai Girma.

Farida ce ta Fara mgana Tana Fadin"Karki Damu Sa"adiya..Ina Kallon ki ne kamar kanwata Zahra..Ina Miki kallon kamar ke din Wata ahali nane Nayi alkawarin kula Dake da Abunda Ke Cikinki Zaki Haihu Lafiya da Izinin Lahi.."Tafada itama yanayinta ya sauya Zulaihat kuwa ce Tayi"Ni kuma Ina Jinki Tamkar Wata Haske gareni Wacce Ta Fitar dani Daga Duhu Zuwa Haske..Tabbas Haduwa Dake Wani Cigaba ne Sa"adiya Anty Farida kuma Bani da tacewa da ita sai dai ina mata addu"an Allah ya Biyata da al"jannah Firdausi..!


Zaina Dake Sharan kwallah Tace"Nagode muku sosai...Allah ya saka muku da alheri ya gadda kuke Kula dani Allah ya Biya ku.."Suka amsa mata da Ameen suna Mata Mirmishi Farida Tashi Tayi ta Shige Cikin daki Tana Kokarin Boye Kukanta Wanda Tuni Zaina ta Riga Tagani Tana Fatan Allah yasa Tunanin Gida ya Dawo ma Farida Taji Tana son Komawa Gida Tabar wannan Rayuwar.

Farida kuwa kuka Tayi Sosai kewar Ya"yanta ya Kamata Tana Kallon Hassana da Usaina acikin Idanuwanta Tana kuma Tuna Al"ameen arif Tana Tunanin yanzu wani Hali suke Ciki..? Bata sani ba Shekaru Biyar ba wasa ba Tasani sun kara Girma sai dai Tana Fatan Allah yasa Zubaida bata Azabar da ya'yanta ba,Allah ya bama Ya Musbahu sauke Nauyin Dake kansa na Kula da ya"yanta Ba kukan komai take ba sai kukan Kewan Uwa da Abunda ta Haifa wanda abaya baya taso mata sai yanzu Take jin wani iri kewa kamar Ta Rufe ido ta Bude ta ganta agabansu,Ta Rumgumesu ko Zataji Dadi Sai da taji Motsi kamar Za"a Shigo kana Tayi Saurin Share Hawayenta Zulaihat ne Tana Tambayanta me Zasu Dafa ne Tunda Lokacin Safiya ne Wajen 11:30am na Safe Cikin Shakewar Murya tace"Ki Dafa kuskus mai Kifi Naga Sa"adiya Tana so..!

Zulaihat Tace"Sosai ma.."


Daga Haka ta Fice tabar Farida na Cigaba da kokawa da Numfashinta Zulaihat bata Damu ba Domin indai Farida ne Lokaci bayan Lokaci Tana Shiga wannan Halin sai dai suna kyaleta Tayi Tunanin makomar Rayuwarta Da kanta Domin itama Tana Fatan Allah yasa Farida Ta daina wannan Rayuwar Bata Dace da ita ba sam.


********

*Bayan Wata Daya..*


A zuwa Lokacin Tuni Cikin Jikin Dina ya Shiga watan Haihuwansa ita kawai ake Jira,Bangaran zaman Hajiya maimu agidan Abba zama take Cikin wayewa da kuma sanin Rayuwa Duk Rashin Son Mu"amala da ita da Umma keyi da ita ita bata damu Duk da ta Fahimci ga inda Umma ta karkata sai bata Biye mata ba ta Nuna ita Babbace mai ilimi da Hikima.

Bata yadda Tayi zaman Daki Da tagama Taimakawa Dina Zata Fito Falo su Fara Hira da Nene,Umma kuwa Har Dakinta Take Bita su gaisa Ko Kitchen ne suna aiki Hajiya Maimuna bata zama Zata Shiga suyi tare Tun Nene na Hanata Har tagaji Ta bari Domim Hajiya maimu tace Bazata iya zama Haka tafi son ta Rika Motsa Jikinta Tun Umma na Basar da ita har tazo ta saki Tunda Tsakani ga Allah Hajiya maimuna bata da wata mtsala macece mai Kirki mai ibada da Dattako Harta da Abba ya Sheda haka wani Lokacin in ya Dawo Gida da wuri haka zasu zauna suyi ta Hira Tana Bashi wasu labaran dake Faruwa a Chan Sudan suna kuma Tattauna wasu lamuran Dake Faruwa anan Gida Nageria.

Hatta da Zainab Ta saki itama Saboda Hajiya maimu ta iya zama da mutane Sosai ko Haddir da Zain sun Shaida wannan Duk kuma Rashin Sakin Fuskar Zain Baya iya ma Hajiya maimu Saboda ko bai nuna ya ganta ba ita bazata Damu Ba in ya Shigo Zata mai Sannu da Zuwa da kuma Tambayarsa ya aikinsa Gidan Alhaji Tsoho kuwa in su Nene zasu ba"a baribta abaya Tana Binsu suje su gaishesu su Hadu da Hajiya mama suyi ta Hira Kowa ya Shaida Lalacewar Dina Tasowarta Hannun kwamishina ne Ammh Sun Tabbatar da tana Hannun Hajiya Maimu da ba haka ba.

Ita kanta Dinar Tayi tajin Haushi wai Hajiya maimu Tana wani Shige ma su Umma bata Damuwa da ita Domin ta sani yarinta ke Damun Dina Har yanzu bata san me Duniya take Ciki ba Shiyasa take kyaleta in tana wani mganar.

Zakiya Tazo Sau Biyu Zuwanta na Farko Tazo gaida Hajiya maimuna ne domin Tunda tazo bata zo ta gaisheta ba,Daga wajen aiki ma Ta Shigo adaidaita tazo Motarta na wajen Ja"afar ya shiga Cikin gari da ita Shiyasa ta Shiga adaidaita azuwan ne ta gayamata Sun je kano ma sun Dawo Insha Allahu Zasu aure Soon Dina tayi mata Fatan Alheri suka Rabu akan cewa Zata kawo mata Ja"afar din su gaisa.

Shine ta Cika alkawari Ranar Lahadi Ta kawo mata Ja"afar Bayan sun Je yawon Shakatawansu sun dawo wata irin Soyayya suke nuna juna kamar su Lashe juna ba ma kamar Zakiya Data ke jin kamar Tana Cikin wani sabuwar Duniya ne Saboda Farinciki bata Ji bata gani Komai nata Ja"afar ne harta yan wajen aikinta sun Sheda Ja"afar a mtsayin wanda Zata aura Sai Zundenta ake Ana Fadin Zata yi Kuskure domin wannan yaron ba Sa"an Auranta bane ammh ba wanda ya Tareta ganin Idanuwanta sun Rufe bata ji kuma Bata gani.

Komai nata ta sakarmai Sirrinta kuma ba wanda bai sani ba,abu Dayane ta Boyemai Zamanta yar Bariki nuna mai take ita ta Allah ce Hatta da duka Atm dints suna Hannunsa Duka Dukiyar da Zakiya Tagama Wahalan Tarawa Zata karar dasu ga Ja"afar Ta maidashi wani Babban yaro kamar wani Hamshakin mai kudi Haka daman take so ya koma.

Lokacin da Zakiya ta kawo Ja"afar wajen Dina aharaban Gidan ta barsa Cikin Mota Bayan ta Shiga gidan sun gaisa dasu Nene ta karisa Dakin Dina Hajiya maimu Afalo ta barta Tare dasu Nene,Dina Taga Fuskar Zakiya ba wani Annuri take Tambayanta meya faru Duk da itama Tana Fama da kanta nan Zakiya ta zauna Cikin Damuwa Tana gayama Dina Babanta Mallam Nuhu ya Kirata yace Ta hakura da auran Ja"afar makaryaci ne sunan daya Fada yasa an mai Bincike a anguwan daya ce sun Zauna an Tabbatar da mai da ba mai irin wannan sunan bama su sansa ba ya Sheda mata Yana Jiye mata Watarana Tayi kukan da idanuwanta Zakiya Tana gayama Dina Sharri kawai Mallam Nuhu yahada saboda kada ta auri Ja"afar ammh Ja"afar bashi da wata matsala kuma Bazata Rabu dashi ba In bazai daura musu aure ba zata samu mai Shige musu gaba suyu aure ammh Ita Bazata iya Rabuwa da Ja"afar ba.

Ta Gayama Dina Zata Siya Musu Sabon Gida zasu je su gina sabon Rayuwarsu bayan aure Ko da Izinin Babanta ko Babu Taji Tagani ba wanda ya isa ya Hanata Insha Allahu nan da wata uku ta zama matar Ja"afar mamaki ya Cika Dina Tana ganin Tana Haukan son Zain Zakiya tana ganin Wautanta ashe ita in Tatashi nata sai ta Fita Domin bazata iya ja da Mahaifinta kan wani Namiji ba Dina Mamakin Zakiya ya Cika tana Tuna sanda Take Fadin Allah ya Rabata da Son Namijin kamar ya Kasheta ita kaxa ita kaza sai gashi kan Namijin Tana Neman Bijirema mganar Mahaifinta wanda Daman Tuni Ita ta zama salamammiya.

Dina Dai Bata iya mgana ba aranta tace sai taga Ja"afar din nan da Zakiya ta Maidashi Rayuwarta Bata kara Jin Zakiya Tayi kuskure ba sai da take gayamata yadda ta mallakamai komai nata kuma Tana gayamata Ita Zata bashi Sadaki ya bada komai kayan aure ita zatayi ma kanta kamar dai itace Mijin,Dina dai mamaki ya kumeta Tama kasa mgana sai kallon Zakiya take tana Jinjina kai.

Zakiya Ta Daddako Dina Kan Taje su gaisa da Ja"afar ta ganshi ba Domin ita kanta Dinar na Bukatar ganin Ja"afar din ba ahalin Data ke Ciki na nauyin Jiki Dana Ciki babu Abunda zai Sakata ta Fita ammh Tana son ganin wanda ya Rikatata Zakiya haka.

Suna Fitowa Falo suka ci karo da Hajiya Maimuna da Nene wannan karon Harda Umma Dukkansu baki suka saki suna kallon Dina Dake wani Tafiya atale kamar yar kaciya da Uban Ciki agaba ita adole mai Tsohon Ciki abun sai da yabama Umma Dariya ta Murmusa acikin Ranta Tana Tunanin Dina Bata san me ake kira Haihuwa ba ammh Zata sani Kwananan Zata gane bata da wayau ne Ranar.

Kafin Hajiya Maimun Tayi mgana Nene ta Rigata da Fadin"Ke kuma ina zaki da wannan Kayan Cikin agaba..!? Ko tsauyama kanki bakya yi..?

Hajiya Maimuna Tace"Uhmm..Kema kya Fada dai sai ina Haka..? Dina tayi saurin Cewa"Zan raka Zakiya ne na kuma gaisa da Mijin da zata aura Tare suke.."Hajiya maimuna ta washe baki Tana Fadin"Au..To..To Masha Allah Aure Zakiya zatayi..? Allah ya sanya alheri ba Laifi kuje ku gaisa Motsa Jikin ma wani Abu ne da zai Taima ka miki.."Zakiya ta Sunkuyar dakai alamun taji kunya Nene da Umma suka Bita da wani kallo Tare da kallon Dina Wacce take taku Cikin Bakar Doguwar Rigar Dake Jikinta.

Suna Fita Haraban Gidan Ja"afar na Cikin Mota sai da Zakiya tayi ma Glass din Knooking kana ya sauke glass din ta leka Tana mai mgana kana ya Bude Murfin Motan ya Fito Tundaga sama har kasa Dina ke karema Ja"afar kallo har ya kariso gabanta shi da Zakiya Tana masa kallon Kurillah Yana karisowa Gabanta sai ta basar Cikin Murna Zakiya kemai bayanin ga kawarta Dina Datake bashi Labari Abun ya bata mamaki Dataji Zakiya na Shararamai karyan Tayi aure ga Cikinta nan ma ta kusa Haihuwa Cikin Fara"a yake gaishe da Dina ta amsa Cikin Fara"a Tare kuma da yi musu Fatan alheri suna Tsaye aharaban Gidan sai ga Motar Zain ya Shigo Haraban Gidan Tundaga nesa ya gansu sai dai Ja"afar din bai gane ko waye ba suma ganinsa sai suka Sha Jinin Jikinsu Har yayi parking din Motarsa ya Dade kafin ya Bude Murfin Mota ya Fito yana Sabe da Coat din Suit din Dake Jikinsa Ta gabansu yabi ya wucesu kamar ma Allah baiyi Ruwansu a wajen ba Dukkansu Da kallo Suka Bisa Har ya Shige sai Dina da Zakiya suka kalli juna suka Basar kawai basu Dade ba sukayi ma Dina sallama suka Tafi ita kuma Tana Takun Daya Daya ta koma Cikin Gida Tana Tunanin ya zama Dole ta ankarar da Zakiya Kuskuran Datake Shirin aikatawa Taga yau Tana sauri ammh Zasu yi mgana ta waya.

Haka kuwa akayi Washegari Dina Ta kira Zakiya awaya bayan sun gaisa take cemata"Any Zakiya wannan Auran da Zakiyi ba kuskure bane..?

Zakiya Tace"Bangane kuskure ba..! Dina ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Nagani Gabadaya Hadin bai yi ba Wlh..Wannan yaron ba ajin auranki bane Zakiya Ko kyansa ne ya Rudeki..? Naga dai Cikin Abokan Shashancin Naki akwai masu kyau ba Laifi kuma Wadanda basai kin Wahala dasu ba Su Zasu Wahala dake Ko Dr.Imran kika Samu wlh sai yafi wannan Yaron da Zaki aura Kiyi mai Wahala Da Lafiyarki da Dukiyarki.."Tun kafin Dina Tagama mgana Ran Zakiya ya gama Baci Daman Tana Wajen aiki ne afusace Ta Daki Teburin Gabanta Ta Mike Tana Fadin"Bangane bai dace dani ba..? Wannan wata irin mganar Banza ce Dina..? Ban taba Zaton akwai Abunda zan nuna miki amtsayin abunda nake so ki kishi ba Dina Har kin manta yadda nayi Fadin Tashin Ganin Burinki ya Cika..? Har kin manta..? Wani Taimako na nema awajenki Da Zaki Fadamin mganar banza Da kike mganar su Dr.Imran din ai nasan dasu kuma abunda na Dade ina gayamiki Shi zan maimaita miki yau Bazan auri wanda mukayi Harkan Bariki ba Nagayamiki Salihi zan aura Wanda bai san komai ba kema kin san Kowani Wanzami baya son Jarfa kuma mganar zan Wahala Dashi ina Ruwanki Ni naji nakumaa gani ko Mahaifina Wlh bai isa ya hanani auran Ja"afar ba Ballatana ke Ba In zaki Fatan alheri kiyi in kuma bazaki yi ba ki Kama bakinki kawai malama.."

Dina Da batayi wani mamakin Zakiya ba Ta Jinjina kai Tana Fadin"Allah ya bada sa"a ba Nufina kenan ba..? Yanzu yaushe ne auran..!? Cikin gatse Zakiya tace"Nan da wata uku lokacin nagama Tsarkake kaina Kinsan nagayamiki Sahihin aure zanyi kamar yadda Zakiyi nakki..Mun Riga mun gama mgana da ogansa na gareji zai nemi Rakiyan wasu abokansa Zuwa Wajen Baba sukaimai Sadaki Da kayan gaisuwan iyaye in ya karba Fine in bai karba su Dawo Dashi Gari da yawa na Tabbata bazamu Rasa masu Daura mana aure ba.."

Dina ta Kara Jinjina kai kafin Tace"Zai ma yarda Insha Allahu.."sai Lokacin Zakiya ta Sauko Tace"Allah yasa kin san Baba da Fitina yagama Damun kansa da Zakiya kiyi aure..Yanzu na kawo mai Mijin yana Min Korafi.."Dina Dai batayi mgana ba Har Sukayi sallama da Zakiya Ta koma kuma Tana Tunanin Abubuwan da suka aikata Tunda ga Farko har karshe Cikin Jikinta Ta kalla wani Tunani ya Shiga ranta Dayasa Taji gabanta ya Fadi taji Tsoro ya Shiga ranta Sosai.



*Ki biya ki karanta cikin Salama...*



*Janafty...*
7/25/21, 9:05 AM - Aisha Srtr Mt: *ZZ..B21️⃣5️⃣*

*IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*


"Bayan sunyi Haka Da kwana Uku Da Dina Zakiya ta Shirya komai ogan Ja"afar mai suna Oga Usmanu Bakanike da wasu abokansa Guda Biyu Suka Tafi kano Dauke da Sadaki 100k sai gaisuwan iyaye 50k sai Kayan Saka Rana sai Dai Kawai mallam Nuhu ya gansu kwatsam Dayake Zakiyan ta basu Full Address.

Lokacin da suka iso suka ce ga abunda ke Tafe dasu Bai yi mamaki ba Domin Zakiya daman ba Tun yau take Tsallake Umarninsa ba Bai yanke Hukunci ba sai da ya Kira Dangin Mahaifiyar Zakiya Dake Minjibir ya kora musu Duka Bayani sukuma sukace babu Ruwansu ya bata abunda take so Tunda Daman Shi kanshi Bata Darajashi ballatana su Matansa ma haka sukece gwara ya aura mata Shi Tunda ita Taji Tagani Koma miye ya Faru Daga baya sai dai akirashi Darasin Duniya.

Da wannan Shawaran ya karbesu Hannu Bibbiyu ya kuma Saka musu Ranar aure Nan da wata uku Daman dsshi Wani abokinsa ne suka karbi Mganar su Oga Usman suna mamakin Yadda Auren yayi Nisa Haka ammh sai Mallam Nuhu yakauda Zargin Hakan aransu Da cewa Zakiya ta Bukaci Haka saboda akwai Shiryan shirya da zata karisa Da haka suka Rabu bayan anyi musu abinci sunci sun sha kana Suka Juya Cike da mamaki ganin Ilimi Tare da Dattakon Mallam Nuhu kuma amtsayin Mahaifin Zakiya sai dai Basu yi wani mamaki ba sanin Halin Rayuwar yau ka Haifi Mutum baka Haifi Halinsa ba.

Tun Kafin su isa Bauchi Mallam Nuhu Da kansa ya Daga waya ya Kira Zakiya yace Mutanen DataTuromai ya karbesu kuma ya Sanya Ranar auranta nan da wata uku Lokacin Tagama Isbira"i Dinta Daga haka ya Datse Kiran Ranar sai da Zakiya Ta Hada musu kayattacen Party Ita Da Ja"afar na Happy Enggement,Farinciki kuwa kamar zai kasheta Taso Ta Kira Dina Ta gayamata Komai yayi daidai sai kuma Ta Tuna yadda suka Rabu Ranar Taji ranta ya Baci Domin ahalin Da Zakiya Take Ciki In har wani zai Nuna bayason Auranta da Ja"afar Sai Taji Ta Tsaneshi Hakan ce ta Faru Tsakaninta da Dina sannan kuma Tana ganin Dina Ta Mata Butulci bayan Tagama Wahalan ganin Ta samu wanda Take so ammh yau ita Dina na adawa da abunda take so da wannan Dalilin ta Tattara Dina ta Watsar Ta kama Harkokinta Tana Tunanin ko Zataji sai Bikin ya kusa Kilama Ta Rigata Shigewa Daga Cikin Domin ayanayin Zain Datake gani da Jin Labarinsa Bata da Tabbacin Burin Dina zai Cika aikuwa Zata so ganin Dina ta Dawo Tana Rokonta Mafita Wlh sai ta Wulakantata.

*****

Washegarin Ranar da aka Sanya Ma Zakiya Rana Misalin karfe 3:00am,Na Dare Dina Tayi Fama da Juyin Ciki,Kamar Zata Haihu haka Ta Dinga Ihu Tana kukan Zata mutu Sai da Ta Da da Kowa na Gidan Banda Zain Wanda Tunda ya Fito yaji wai Dina ce ke kukan Zata mutu Tana Dafe baya Yayi Tsaki ya koma ya kulle kofarsa acikin Ransa yana Fadin Dama ta Mutu Uban kowa ya Huta bai Taba Tsanar wani abu yadda ya Tsani Dina ba.

Hatta da Abba sai da ya Taso Umma ma Haka dasu Zainab,Nene ce da Umma suka Shiga Dakin suka Iske Hajiya maimuna na Rike da ita sai Kururuwa take Tana Dafe Ciki Da Baya Tana Fadin Zata mutu Hajiya maimu sai mata sannu Take Tana Fadin kiyi salati Dina bar wannan wayyo din nan Ammh ina ko Jinta ma Batayi Duk ta Fita kamaninta Nene sai sannu Take mata Umma kuwa kallo Daya Tayi mata ta gane ba Haihuwa bace in Haihuwa ne karyanta Wlh

Abba ne ya kira Alhaji Tsoho ya gayamai Shi kuma ya ce Hajiya Mama Ta taso Haddir Su Je su gani Ita Ta Bugamai Kofa ya Bude yana Barci Tace yazo su Tafi Gidan Abba an Kira Dina Zata Haihu Cikin Tura baki ya Sako Jallabiya ya Dau key din Mota suka Tafi suna Zuwa Tundaga Falon Gidan suke jin Nishin Dina da kukanta Abba da zainab da Umma suna Falo Zaune Sai ga su Hajiya mama Haddir suna gaisawa da Abba yace

17 / 37