Author : Jamila Janafty Category : Romantic Hausa Novels
Alhaji Tsoho Da bazai iya Tsayuwa ba saboda Kafa ya zauna Haddir yajasu sallar bayan sun idar Alhaji Tsoho ya Dinga Janyo ayoyo yana Fassarama Su Abba da Jikokinsa yana Nuna musu illah Yima yaro Baki wanda ke Binsa Duk inda yake wanda Kalaman da iyayan Farida suka Jefeta dashi Shi ya kaita ga Fadawa wannan Rayuwar.
Anty Yaha da Farida nan suka kawo ma su Abbba abincinsu da Abun sha suka ci suka sha Su Umma kuma na cikin Gidan bayan sunyi sallah sun natsa suma aka gabatar musu da abinci suka Sha suna zaune afalon sai ga Goggo Zaliha ta Shigo Tana kuka Tana Fadin Ina Faridan take ne..? Farida na ganinta ta isa gareta ta Rumgumeta Tana ta kuka Basu gama Koken ba sai ga Baffa Haruna da Baffa Umaru sun iso suma ai sai Kukan Rasuwar Abba ya Dawo Sabuwa Baffa Haruna yana kuka yana cewa Farida ta yafemai Shine Silan komai Daman Tuni Anty haya ta kira su Abba tace su Iso Falon su Baffa sun iso agabansu komai yake Faruwa.
Cikin Alamun Rashin Sanin Inda manganun Baffa Haruna ya Dosa,ganin haka yasa Anty Yaha ta kalleta Tana Fadin"Bayan Tafiyarki da Shekara Biyu Sirrin Boye ya Bayyana...Mummy ta Haukace sakamakon Fasa Tulin Duka Siirinta Dake Cikin Fulawowin gidan Baffa Haruna,Shikenan ta Haukace Ta rika Fadin Duka abunda ta aikata ita da yartaa Harda Asirin Datayi tayi Sanadiyar Rasuwar Goggo Fatu da kuma asirin da sukayi ma Musbahu ya auri Zubaida da wanda sukayi mai ya juyar da Hankalinsa zuwa kan ZUBAIDA..faruwar wannan Lamarin ya Tsorata mu sosai ganin Haka yasa Zubaida ta Tsorata Da bakinta ta Taramu ta Fadamana duk makircin da suka kullamiki wanda yayi sanadiyar Hawanjini ya kwantar da Abbanki yayi ta Jinya yana ganin Shine Silan Tafiyarki Tunda shi ya Koreki,Har Allah ya Dauki Ransa Mummy bayan An kaita gidan iyayenta Baffa Haruna ya saketa Achan ta Gudu Ta shiga Duniya ba"a ganta ba Zubaida kuma Musbahu ya saketa saki uku yanzu Haka tana Gida Tana Fama da Jinya na Ciwon Cancer Nono Har Guda Daya ya Rube an yanke yanzu Dayan ma ya Harbu..."
Kowa Sharan kwallah yake afalon Farida na wani irin kuka Tace"Ina ya"yana..?Anty Yaha tace"Suna Wajen Musbahu Daman Tun bayan tafiyarki suna Wajensa yana kula Dasu bayyanar gaskiya yasa yayi kuka sosai kuma yazo ya Roki gafaranmu Shi yake Dauke da Duka Nauyinmu Bayan Rashin Lafiyar Mahaifinki Har Rasuwarsa wannan Gidan ma Da kika gani shi ya gyaramana shi ya bamu Dukkan wani ajin Dadin Rayuwa Zahra Tayi aure Shekara Daya da barinki Gida a kano Wlh Farida kullum addu"a muke Allah ya bayyanaki Dakyar su Baffa Haruna suka saka Musbahu ya kara aure Wata yar Nan Jemeta ya Aura mai Suna Bara"atu Wata Biyar kenan da auran suna Abuja inda Musbahun ya koma da aikinsa Yayi gida achan Duka dasu Hassana da Usaina suna Wajensa ya sakasu a makaranta Satin Daya wuce ma suna Gidanan nan sukayi mana Hutun karshen mako.."
Farida kuka kawai Take Abubuwa Biyu sune ke kara sakata kuka na Farko Rasuwar Abba na Biyu kuma Da yau Taji Labarin Mummy ce Tayi sanadiyar Mutuwar Goggo Fatu sai taji ta kasa Daina kuka Nene da bata iya Shiru sai da Tayi mgana Tace"Sakamakon Daya kamata Dasu kenan..Duk wanda ya aikata Zalunci Tun aduniya zai ga karshensa.."Umma tace"Sosai ma Allah ka Rabamu da Zuciya mara kyau..."Gabadaya aka amsa da Ameen
Ana Cikin Haka sai ga su Hassana da usaina Sun Fara Shigowa da gudu suna kiran Umma Domin tun achan Musbahu ya gaya musu Umma ce ta Dawo yaran basu manta da Uwarsu ba Farida na jin muryansu ta tashi ta isa garesu ta Hada ta Rumgume Tana kuka Tana Fadin ashe basu manta da ita ba Areef ne Bai ganeta ba sai ta Jawosa ta Rumgume tana Fadin Umma ce Al"ameen dina Duk da bai ganeta ba Dumin Jikin uwa na Dabam ne haka Farida ta kamkame ya"yanta Tana Dariya Tana kuka Lokaci Tana Dagowa taci Karo da Musbahu Da Matarsa Bara"atu Kallo Kallon sukayi ma Juna Wanda Tayi Saurin Dauke kanta Ta tashi Dauke da ya"yanta ta koma Gefen Goggo Zaliha ta Zauna Tana Sharan kwallah.
Baffa Umaru ne yaga Musbahu ya Tsaya Shuru kamar bazai Shigo ba sai ya Daga baki ya Kirashi yace ya shigo sai ya Shigo ya zauna suka gaisa dasu Abba da Alhaji Tsoho ganinsu manyan Mutane Bara"atu ma Ta gaishesu ta samu gefe Ta zauna Tana Kallon Farida wacce Daman tasanta a Hoto a matsayin Mamarsu Hassana.
Goggo Zaliha ce ta kalli Farida Tana Fadin"Aisha Farida kinji Abubuwan da suka Faru Bayan Tafiyarki..ina so ki gayamana ina kika ke Bayan barinki gida Meyasa baki Je kaduna Gidan kawata Kamar yadda nace ba..?
Farida Ta sunkuyar dakai Tana Kuka ta Fara basu Duka Labarin Barinta Gida da Komai da komai da Rayuwar da Datayi a gidan Uwar mata,Da Haduwarta Da Zaina da Haihuwarsu da Maidata Bauchin Data yi har zuwa yau da Suka iso nan ta karishe Cikin kuka Tana Fadin"Na Yanke Shawaran Shga Duniya ne Tunda har iyayena suka Ambace ni da Karuwa Da Duka Ahalina sai naga bani da wani Sauran kima Da kaina Na nemi naZama Karuwa mai zaman kanta saboda Fushin Abubuwan da suka Faru dani.."
Kowa sai kuka yake Goggo Zaliha na Girgiza kai Tana Fadin"Ba laifinki bane Farida..Makircin muguwar Kishiyace Tsakaninmu da Zubaida da uwarta Allah ya isa.."Alhaji Tsoho yayi gyaran Murya yana Fadin"Ai aduka Abubuwan da suka Faru akwai Sakaci da addu"a da kuma Baki da iyaye kiye ma ya"yansu batare da Sun tsaya sunyi Bincike ba..Na Farko dai Dukkanku kunyi Sakaci da addu"a har taci galaba akanku kaima Musbahu kayi sakaci Sosai...Sai kuma Bakin da iyayen Farida sukayi mata na Kiranta Karuwa batare da sun yi Bincike ba Duk ya Taimaka wajen Faruwar haka Shiyasa ana son komai yaro zai maka ka Daure ma Zuciyarka kada kayi mai Baki Domin zai Bisa.."Kowa sai gyada kai yake yana Yarda da mganar Alhaji Tsoho Baffa Haruna yace"Tabbas hakane...Mun yarda muyin Sakaci da addu"a abaya ayanzu kuma Insha Allahu mun gyara.."
Kowa ya amsa da Allah yasa,nan aka Cigaba da Tattauna Agaban kowa da kowa Musbahu ya Duka ya bama Farida Hakuri tace ta yafe ya kuma ce yana so a amaida musu da Auransu da Farko taki yarda wai Ita fa karuwanci Tayi bata Dace da zama matar kwarai ba sai da Alhaji Tsoho ya kara yimata Nasiha kana ta yarda Bayan Godiya da Fatan alheri ga Su Alhaji Tsoho da kuma jin Dadin Karamcin da sukayi musu suka Dawo da Farida gida Ana kuka sai aka koma Dariya Lokacin ana Kiran Sallar La"asar suka Hadu Duka Mazan suka Hadu sukayi Jam"i matam kuma na Cikin Gidan sai Lokacin Zahra ta iso Bata Dade da Zuwa ba sai ga Saratu itama Tayi aure Harda yarta Daya Aseeya.
Gida sai ya koma Kuka kuma Zahra da Farida suka Rumgume juna da Saratu suna kuka Sosai da sukayi suka gaji kana aka koma Tambayan Bayan Rabuwa sun gayamata Abunda,ya Faru bayan Batanan da duk Abunda ya Faru dasu Mummy itama ta gaya musu Irin Rayiwar da tayi Suka Hadu suna ta kuka da kuma Tuno Rasuwar Abba sai da sukayi suka gaji kana suka Hakura suka koma Hiran yaushr gamo.
Su Abba dai Yammah Tayi kwana ya kamasu Dole suka Tsaya sai.zuwa Gobe, abincin Dare ma a Restaurant Musbahu yayi Oder akaci akasha Matan Acikin Gida suka kwana Mazan kuma Shashen Baki Da safe ma Oder Abun karyawa Musbahu yayi musu sukaci suka sha suka Fara Shirin Tafiya Karfe 10am na safe suka Rakosu Haraban Gidan Farida suka Rumgume dasu Zaina suna kuka Kamar kada su Rabu haka su Anun ma Suna ta kuka Sabo Sun Rabu kam zasu yi mgana ta waya Tunda Zaina Tayi sabuwar waya wacce Zain ya siyamata sun Rabu Cikin Dattako da Godiya su Abba na Godiya su Baffa Haruna na Godiya su Umma sukace sai Bikin Maida Auran Farida zasu dawo Mami Walwarta ya Dawo haka aka Rabu Cikin Mutumci Har suka Bar Haraban Gidan suna Daga musu Hannu da Fatan Allah ya Tsare su kuma suka koma Cikin gida suna kara maida Zencen dayi ma Allah Godiya Daya Dawo Da Farida gida Hatta da Bara"atu ta saki Jikinta Domin Daman Musbahu ya gayamata komai Duk Ranar da Farida ta Dawo Zasu maida auransu.
Sai wajen yammah suka iso Bauchi Saboda basu yi gudu ba,Gida aka Fara kai Alhaji Tsoho Saboda ya Huta,Bayan sun sauke su Umma Zaina da zain suka Nufi Gidansu Domin warware gajiya nan dai suka bar ma su Umma ya"yansu suka Tafi gidansu Domin Basu gama amarcinsu ba.
Sai Washegari suka samu waya da Farida suka gayamata sun iso Lafiya Daman tana da Lambarsu su Umma Duk ita ta kirasu ta yi musu bangajiya suka Rabu Cikin Jin Dadi,Ko bakomai Farida ta koma Cikin ahalinta Saura Zulaihat wanda Abba ya Tsara Tafiyan sati mai zuwa.
Haka kuwa akayi sati na Zagayowa suka Tafi yashe Dangin Zulaihat,Sun Tarar da Baffa ya Rasu wasu Daga cikin ya"yan Larai duk sun Kara lalacewa Harda Barawo wanda Gwammati ta kama Larai kuma tana kwance tana Fama da Jinya Kafarta ta Rube Tun bayan Sanadin Saran Macijin shine Sila Bata da mai kula da ita Tana kwance adaki sai wanda yaga Allah yaga Annabi Gidan Gabadaya Warin Kafar Larai yake wanda yake Fitar da Ruwa Gwano Dataji Zulaihat ce da kanta Haka take kuka Tana Rokonta Gafara Zulaihat na kuka tace ta yafe mata yakubu gala najin Zuwan Zulaohat yazo yana Bata Hakuri Shima ya Shiryu Har yayi Aure ya Haihu koda Abba ya Nemi Zai Tafi da Zulaihat ta zauna Wajensa Maigari bai yi Gaddama ba Tunda kowa yasan Zaluncin Larai ga Zulaihat Haka kuwa akayi su Zain ko Tsausayin Larai basu ji ba Abba ne kadai ya Bada 50k ayi mata mgani Suka Tattara suka Dawo Bauchi Da Tunanin Tabbas Mutum yaji Tsoron Duniya Domin Bai sam wani Hali zai Kare ba.
Bayan dawowarsu da kwana Biyu Zain yaje ya samu Alhaji Tsoho Da Tambayar ya makomar yankan da Farida Tayi ma su Anun..? Da kuma Rainon su da akayi da kudin Haramun..?Shin za"a kara Musu Sabon yanka ne ko kuwa dai Wannan din yayi bakomai..? Alhaji Tsoho yace kada ya Damu Yanka yayi Ai Abunda ya Faru Tskanin Farida ne da Ubangijinta Ita Zata Nemi Gafaran Allah mganar su Anun kuma yara ne kuma Tayi musu Komai da kyakyawan ZUCIYA saboda Haka babu bukatar kara Tabbatar da Sunansu Sai mganar Zaman dasu Zaina sukayi Wajenta Tana Ciyardasu da kudin Haramci Suma ba Hujja bane Tunda suna sane ba Cikin Rashin Sani bane sunyi Haramcin Sai dai Allah gafurun Rahimun ne su Rokeshi Gafara zai yafe musu ammh Ko gobe ba Hujja bane ka zauna ana ci Dakai da Haramun Da gangan.
Da wannan Bayanan Zain yaji Hankalinsa ya kwanta ya Koma Gida yana Gayama Zaina Tayi ta kuka Tana Fadin Bata da mafita ne Zain ya Dinga Lallashinta Dakyar Tayi Shuru Tundaga Ranar suke neman gafaran Allah Ita da Zulaihat.
******
*Bayan wata Biyu..*
Bayan Wata Biyu Abubuwa Dadama sun Daidaita Tuni Zulaihat ta zama yar gida Har Abba ya sama mata wata Private school da hanya dakomai aka sakata SS1 sai dai kuma Sadiq nayi mata Lesson In ya Dawo Gida da yammah Tunda Tasu Tazo Daya Farida kuma suma waya koda yaushe Bikinta da Musbahu nan da Kwana Arba"in kuma duk su Umma zasu je suka ce Zafeera Ta Dawo Hutu sau Daya Tayi Sati Uku ta koma ammh Shi Haddir din yana Zuwa in ya samu Lokaci Kamar Ranar weekend Tana chan Tayi Rashin Lafiya sai ga Labarin Cikin Wata Biyu da kwanaki ashe Lokaci Daya suka Dauka da Zaina ita ma ta Fara Laulayi ana Dubata itama Cikin Wata Biyu da kwanaki sai murna da Farimciki Wajen Duka Iyalan Alhaji Tsoho.
Dina ta Dawo bayan ta Shafe wajen kwana50 asudan koda ta Dawo Cikinta ya Shiga watan Haihuwarsa Haihu ko yau ko Gobe Tun bayan Dawowarta Zaina ta matsa ma Zain Dole ya Raba musu kwanqa yau in ya kwana Wajentq Gobe wajen Dina zai kwana sai zaina ta saka aka Dawo mata dasu Anun Harda Arman yana wajenta bata Nuna Bambamci Dina kuwa ta Tabbatar da Darajan Zaina take ci da Har yanzu take samun kulawar Zain Duk da dai babu Abunda ya kara Shiga Tsakaninsu Sai dai ba laifi yanzu yana Kulata da Tambayar Lafiyarta Har ya bata kudi Masu yawa yace Zainab Ta rakata ta Siya kayan Haihuwa haka kuwa akayi Zainab da Zulaihat suka Rakata tayi Siyayyah kayan Haihuwa sai dai wannan karom Dina batayi Awon Ciki ba.
*****
Yau a Wajenta Zain ya kwana ya kai Dare yana aiki Cikin Sytem dinsa bai yi Barci da wuri ba Duk da ba Daki Daya suke kwana ba tana jin Motsinsa Shiyasa yau bai tsshi da wuri ba kuma Ta kama Lahadi ne ba aiki.
Fitowa tayi Daga Bedroom dinta Zuwa Kitchen da katon Cikinta Ruwa ta Dauko Ta Tsiyayo a kofi tazo Ta zauna afalo Tana Sha Kamar amafarki Taji ana Sallama Dago kanta da Zatayi taci karo da wata yar matashiya Mata Da katon Ciki Tana Sanye da Wata Riga baka da Hijabi Duk yaji Jiki Ta Rame ta lalace Tayi baki Fuskarta sai Kuraje Manya duk sun bata mata Fuska sai karamar Jakar matafiya Dake hannunta.
Arazane Dina ta mike tana Watsar da kofin Dake hannunta Cikin Nuna ta da Hannu tace.
"Zakiyyyyya!!!!..."
*Kada ku saka Ran ganin wani Update din yau..Sai gobe da Safe In Allah ya yarda..*
*Janafty...*
8/12/21, 11:32 AM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B23️⃣0️⃣*
*IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*
*END*
_ALHAMDULILLAH_
"Zakiya Da take Tafiya Dakyar ta Fara takowa cikin Falon tana Sakin wani marayan Mirmishi Wanda kiris take jira ta Fashe da kuka ga Katon Cikinta Datake Faman Turoshi kamar ya Kifata.
Dina Data Daskare a tsaye Tana kallon Zakiya Cikin mamaki da Al"ajabin ganin yadda Zakiya ta dawo,sai da Zakiya ta iso kusa da Dina kana ta Bude baki tace"Na"am Dina..! Kinga yadda Allah ya Maidani ko..?
Dina Ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Zakiya me ya Faru Dake ne haka..? Zakiya bata samu Daman mgana ba ta zagaya ta Nemi Waje ta zauna Tana Sauke karamar Jakarta Lokaci Daya Tana Mike Kafarta Saboda Cikin jikinta,Dina ta Zo gefenta ta zauna Tana kare mata kallo Cikin mamakin ganin Cikin Dan Wattanin da suka Dade basu hadu ba.
Zakiya bata kara mgana ba sai da ta Dauki Ruwan Da Dina ta Dauko ta kafa a kai Bata Sauke ba sai da ta Shanye kana Ta sauke Gora Lokaci Daya da Numfashi,Dina Da mamakin ganin Zakiya yasa ta kasa mgana sai dai binta da kallo kawai sai da Zakiya Taji ta Natsu kana Ta Dago Tana kallon Dina Lokaci Daya Tana kare ma Falon Kallo Tana Fadin"Nazo ina Tambayan Megadi Ina kike Zaune sai ya sanar dani ai kina ma Wannan Shashen ne Dina..!
Dina Data Zaku Taji me ya Faru da Zakiya Tace"Eh nan nake Zaune Zakiya..Meya Faru Dake ne..?Gabadaya kin Sauyamin..?
Zakiya Ta Share Hawayen da suka kwaranyomata Tana Fadin"Allah Sarki Rayuwa Dina da alamu Kekam kinyi Nadaman Wasu Abubuwan da muka aikata Tun afari Tunda gaki Cikin Jin Dadi Har da wani Cikin..Ni kuma Dina na Fara Girban Abunda na Shuka Tun a Duniya..."
Tafada Lokaci Daya Tana Fashewa da kuka Dina sai Taji Gwiwanta yayi sanyi Cikin Alhini tace"Meya Faru Zakiya..?Ina Ja"afar din..? Wattanin Baya Da muka Hadu da Ashanty Take Fadamin Kinyi Aure A Bauchi..'Zakiya Tana Matsan kwallah Tana Fadin"Ashe Hashashen da kika gayamin gaskiya ne...?ashe Ja"afar ba Sona yake ba..? Ashe ba Mutumin Kirki bane..? Ashe Dan Damfara ne Ja"afar Bansani ba Wlh Dina ayanzu haka Ja"afar ya kwashemun komai nawa Daga karshe ya Hadani Da Abunda zai kasheni Har Abada.."
Take Fada Cikin kuka Da Nadama mai Karfi Dina Ta Dafa Kafadarta Tana Fadin" innalillahi Zakiya Don Allah ki Daina kuka ki gayamin Abunda ya Sameki Kika koma Haka..?garin ya Ja"afar ya Rabaki da komai naki..?
Zakiya Ta Dago Tana Sharam kwallah Take Fadin"Tun Bayan Kafin Auranmu Dina na Riga na Sangarta Ja"afar komai ni nake mai Har komai na Auranmu ni nayi shi Bayan Aure ma bata Sauya Zani ba Nice Mijin Babu Abunda bana mai na Sakashi a Makaranta na Bude mai banki Ina Raba kudin albashina Kashi 2 ina Bashi Rabi ammh Kafin Sati sai yace ya kare Ban Fara Damuwa da Lamarin Ja"afar ba sai bayan Samuwar Cikin nan nawa Dina Ja"afar ya Sauyamin Gabadaya in ya Fita Gida sai Dare yake Dawowa wani Lokacin ma sai Tsakar Dare,Da nayi mgana sai yace Makaranta yake Wuni Danayi Bincike sai na gani sai yayi Sati ma bai Shiga makarantan ba Daya Lura na Fahimci komai sai ya Fara Sauyamin ya Daina Min Dariya ya Daina Kula dani kamar baya Ashe Duk yana Hadamin Tarko ne Dina Tabbas naga Mganar Baba Dayace Ja"afar makaryaci ne Address din Daya bada Na Karya ne Tabbas Hakane Ashe Ja"afar Dan Bariki neDina Kamar yadda nake yar Bariki Ashe Dan Damfara ne Haka yakee Dayaga Kana da kudi sai ya aureki Da Suffar Daya Aureni Daga Karshe ya Damfaresu kmar yadda ya Damfare ne Bayan Haka ba Haka kurum yake barin su ba sai ya Lura Miki Ciki Ya likamiki Cutar Dayake Dauke da ita Daga Karshe ya Kwashe komai naki ya Gudu ya barki.."Zakiya ta karishe Fada Tana Wani Gunjin kuka.
Dina Ta Saki Salati Tana Fadin"Mun Shiga Uku Zakiya Wani irin cuta kuma..? Zakiya na kara Tsananta kukanta Tana Fadin"Cutar nan mai Karya Garkuwan Jiki Mana Dina.."Ido Dina Ta Zaro Tana Fadin"Kanjamau Fa kenan Zakiya..! ?
Zakiya na Sharan Kwallah Tana Fadin"Eh Ita Dina..Ashe Ja"afar na Dauke da wannan Cutar mgani yake sha bata nuna ba Kuma Kinga Kenan Tabbas Ina Dashi Tunda munyi aure kuma Munyi Tarayyan Aure ba adadi.."
Dina Ta Dora Hannu akai kawai Tana Salati Zakiya Tana Sharan Hawaye Tana Fadin"Kafin ya Tafi ya Rubutamin Takardan Sakina Har uku da wadanan Bayanan anan yake Fadamin In je a gwadani ya bani Tsaraba Da ya saba ba mata irina Wato kanjamau da kuma Ciki Dina Nayi kuka Kamar zan yi Hauka Ja"afar yagama Cutata ya kwashe Duka Atm dina ya Saida Gidan dana siya ya saida Motata ya Saida