Chapter 26 Reading Zainazain Book 2 Complete By Janafty Arewa Novels

Zainazain Book 2 Complete By Janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   26 / 37

75K to 78K   out of 108.5K words

ita kuma Zakiya Mallam Nuhu yace sai Washegari in da akayi Tashan Mota Biyu suka Tafi,Da dan kayan Dake Dake da Wasu abubuwan da ba"a rasa ba wanda Mallam Nuhu ya bada kudi aka yimata Duk da tace bata Bukatar komai,Duka kannenta sunje da Wasu Daga Cikin Dangin Mahaifiyarta sai Amarya Luba Samira Tana Gida bata je ba.

Sunje sun ga Gidan Da Zakiya Zata zauna suka Dawo suna Labarin Cikin Daular da Zakiya Zata Zauna nan suka kwana sai Washegari ta saka aka maidasu bayan ta Cikasu da kudi sai mamaki suke Amarya ba Kawa kuma Komai ita take yi Shi Angon baya wani abu Wasu suna ganin Zakiya ta Tsinci Dami akala ne suna Ganin kyan Ja"afar ya Rudeta Wasu kuma Suna Tunanin Shi Ja'afar din yayi Sa"a wasu masu Dogon Tunanin suna ganin anya Zakiya bata yi kuskure ba kuwa..?

Daran Ranar Ja"afar ya Kadaice Tare da Zakiya wanda da Farko kamar ita ta Sarrafashi sai da ga Karshen ya Nuna mata Shima ya Kware akan wannan harkan Daman Tayi banke banken mganin mata Harda Dinki Taje asibiti akayi mata Saboda Kada Ja"afar ya gane ita ba Budurwa ce,Sai dai abu Daya ya bata mamaki yadda Ja"afar ya Sarrafata ba Sarrafa ne na wanda bai san Hannunsa ba sai dai kuma Tayi la"akari da wannan Zamamin sai ta Daina wani mamaki,Da safe ya Dinga Lallabata Tana mai Shagwaba ita adole Ta kawo Budurcinta Wajen kwana Uku yayi yana Jinyarta Tana nuna mai taciCiwo shi kuma yana Biye mata kafin su koma suna ta Cin Amarcinsu Cikin Farinciki da kaunar juna Zakiya tana ganin ta gama yin Sa"a Duniya da lahira Data samu Ja"afar gashi yaro ga kyau ga iya Soyayyah.

Sati Daya sukayi suna cin Amarci ta koma Office Daman Hutun Sati Daya suka Bata Kuma Tana Son aikinta Bata Hadashi da komai Dole ta Koma ammh Wuni suke suna waya da Ja"afar In Kuma tatashi aiki Shi yake Zuwa Daukanta Su Fita suje suci abinci sunyi yawo acikin Garinsu Ransu Fes Har Wasu Daga Cikin abokan aikinta Suna ganin Tayi Dabara Datayi auranta yafi wannan Gantalin Data Yi abaya.

Auransu yasa Ja"afar ya kara Zama wani Jini da Hantan Zakiya ta Riga ta gama yarda Dashi ta sakarmai komai nata,Sirrinta da Duka Dukiyarta Babu Abunda bai sani ba sai Boyemai datayi Ita din Tayi Harkan Bariki kuma Tana Tunanin har Abada bzai Taba Fahimta ba Koda wani Zai gayamai Dina ce tasan komai kuma Basa Tare bata san Isalinta ba Tana ma Tunanin Kila Zain din ma yaki yarda ya aureta Tana Chan Gidan Kwarton Ubanta ita da Da"n Shege.


Cikin Kwanciyar Hankali da Soyayya Da Muradi mai Girma Zakiya da Ja"afar suke Gudanar da Soyayyarsu Basu da Wata Mtsalan Komai na Rayuwa sai Zakiya Taga Dama take girki sai suyi sati suna Fita suna cin Abinci Basu damu ba Zakiya take Hidiman Tunda ta Hana Ja"afar aikin kanikancin Tace ba Girmanta bane Mijinta na Aikin Gyaran Mota Karatu zai Koma Zata nema mai Addmission anan ATBU bauchi ya Dora Karatunsa ya nuna mata bai san inda Takardan Sakandirinsa yake ba tace kada ya Damu Zata Siyamai Komai zai zama Daidai Shima zai yi karatu kamar Kowa Ja"afar yaji Farinciki ya Cikashi Sosai.


*****

*Zaria...*!


Achan Zaria kuwa abubuwa Duk sun Rikice Ga Farida Domin Bata da Natsuwa kwata kwata Saboda yawan Mafarkan Datake yi Tana ganin Goggo Fatu Da ya"yanta Cikin wani Hali Tun Abun baya Damunta har ya Fara Damunta yana Bayyana ajikinta.

Ta Rame duk ta Lalace kamar ba ita ba gefe Daya kuma bata Samun Zama,Domin Uwar mata bata Kyaleta ba Koda yaushe Cikin kawo mata Sabbin Costumer take tana Zuwa House Service ko Hotel Service Kudi kam Kaca kaca haka take samu su kansu su Zaina sun Shaida hakan Domin Uban Siyayya Take Narko musu,Kayan abinci kuwa wasu basa karewa Wasu ke Tarar da wasu su Anun kuwa kaya ba adadi wasu basu Taba sakawa ba Tunda Suke Saboda kayan yayi musu yawa kayan wasa Kuwa sai Wanda ya gani Zaina Tana auna Ko Firstlove dayake Mahaifinsu sai haka A hidimar da Farida ke yi dasu Ita kanta da ita Zulaihat in ka gansu da Irin Rayuwarsu da kayan da suke sakawa ko Gidan Wani mai kudin albarka Tabbas Gasiiyan Uwar mata Tauraron Farida na Haskawa kuma Barikin ya karbeta

Tun Farida na Boye Halin Datake Ciki har su Zaina suka Fahimta,Domin Ta Rame a tsaye sai Idanu da Dogon Wuya Duk Tayi wani iri in Tana Gida Sai ta Shige Ciki Ta zauna Tayi Shuru Cikin Tunanin zaina Data Fara Lura batayi mgana ba sai dai Tana Ma Farida addu"a a duka Sallolinta Allah ya maida Hankakinta Zuwa ga ya"yanta da Iyayenta Domin Kwata kwata Bata mata Sha"awar wannan Rayuwar.

Yau ta kama Asabar Ne Jiya Farida ta Dawo Gidan Wajen kwananta Hudu Bata gida Tana Kaduna tace Tun kuma Jiyan Da Tadawo bata Fito Daga Cikin Bedroom ba Tana kwance Da Safe da Zaina ta Tambayeta sai tace mata batajin Dadi ne nan kuwa Tunanin mafarkin Jiya ne ya bata Tsoro Abbanta Tagani yana Kuka yana Kiran Sunanta Tana Kokarin Zuwa Garesa ne Wani Hayaki ya Tare Tsakaninsu anan ta Farka Tun Lokacin Bata Runtsa ba Mafarkin ya Tsaya mata acikin Ranta Ta kasa Sukuni gashi bata wani Jin Dadin Jikinta Ciwon kai da Jiri Ga shi bata da mgani ya kare kuma ta Dade bataje Taga Likita ba.

Tana Jin Sallamar Zulaihat ta Runtse ido alaman Barci Take ganin Haka yasa Zulaihat ta Koma Falo Inda Zaina Take Zaune Tana karatun Littafin Ahalari Anun da Anan na Tsakar Falon suna Wasa da Kekensu Zulaihat tazo ta Zauna Kusa da Zaina Tana Fadin"Ni kuwa Sa'adiya bari nayi miki wata mgana..?

Zaina ta Dakata da abunda take yi Ta Dago Tana kallon Zulaihat Lokaci Daya Tana Fadin"Ya akayi ne Ummu Anun ko Ummu Anan zan ce..?


Zulaihat Tayi Dariya Jin sunan da Zaina take kiranta yanzu Tace"Duka Duk wanda kikace Daya ne...Ya"yana ne na Tabbata Ko Firstlove bazai Raba wannan kaunar ba (Dayake Zaina ta bama Zulaihat Duka Labarinta Ganin sun Riga sun zama Daya)

Zaina Tayi Dariya Tana Fadin"Wane shi bai isa ba Zulaihat..ina Jinki Meya Faru ne..?zulaihat ta gyara Zama Tana Fadin"Game da Anty Farida ne ni kam baki Lura kwanakin nam duk ta Sauya ba bata san Zama damu koda tana Gida koda yaushe Tana Daki Kifa Duba Duk yadda take Kaunar su Anun yanzu bata Cika Daukansu ba.."Zaina ta Ijiye Littafin Dake hannunta Saman Kujera ta Muskuta Cikin Damuwa Tana Fadin"Uhm..Ashe kema kin lura..? Ai na Dade da Lura da yanayinta Zulaihat..Na lura bayan Damuwa ma Harda Rashin Lafiya na Damunta baki ga Duk ta Rame a Tsaye ba..? Ina Zargin Jininta ya hau kuma bataje asibiti ba.."

Zulaihat ta sauke ajiyar Rai Tana Fadin"Nima Haka nake Tunani...Na shiga Damuwa ko Zamu sameta muje meke Damunta ne..? Zaina tace"A"a koda munje Bazata gayamana ba..Ammh Ki bari Zan Duba Lokacin Daya Dace zan mata mgana Allah yasa adace.."Cikin Sanyin Jiki Dana Zuciya suka Cigaba Da Tattaunawa mganar kafin su gangara kan Mganar makarantarsu.
Zulaihat tatashi ta Shiga Kitchen Tayi musu abun kari suka zo suka karya kana Tayi ma su Anun wanka Zaina ta Shiryasu suka Hadasu da kayan Wasa bayan sunsha Nono Hade Da madaransu suka Kama wasansu har Lokacin Farida bata Fito ba Zaina da Zulaihat suka Zauna Zaina na kara ma Zulaihat Bitar karatun Qur"anin Inda Zasu Biya yau a makaranta.


Sai Wajen gabda Azahar Farida ta Fito Duk ta wani Zama wata iri Wanka Tayi ta sha Tea,kadan ta koma Daki Daga Zaina har Zulaihat bayan gaisuwa basu ce mata komai ba sai Zaina ta Dafa Jallop din Shinkafa da Rana Kana ta Fito sukaci Tare har ta Saki ma Da Zasu tafi makaranta suka bar mata su Anun Allah ya Taimaka yaran suka Debemata kewa har suka Dawo Tana Walwalwarta Har Zuwa Dare.

Bayan sun gama Hirarsu su Anun Tuni sunyi Barci Zulaihat ta Kwashesu Zuwa Dakinta Wani Lokacin Tare take kwana Dasu Farida Daman ta Dade da Shiga,Sai Zaina da Bayan sunyi Sallama da Zulahait Ta shiga Dakin Wanka Tayi saboda Taji Dadin Barci ta iske har Farida Tayi Barci Sai itama tabi gefenta ta kwanta bayan Tayi addu"An barci.

Cikin Dare Zafi ya Tada Zaina an Dauke Wuta Tana Tashi Taga Farida Zaune kan gado Tayi Tagumi Batayi mamaki ba ta Mike Tana Tambayanta me ya Faru..? Kuma meke Damunta sai Farida ta kama kuka Dakyar ta iya Gayamata irim Mafarkan Datakeyi Tanayi tana kuka Zaina ta Rumgumeta Tana Lallashi kafin ta Dagota Tana Share mata Hawaye Tana Fadin"Anty Farida ki Tsaida Zuciyarki Waje Daya..ya"yanki da iyayanki da duka Danginki suna Bukatar ki ne,ina ji ajikina Ko wani Hali ake ciki Asirin Zubaida Ya Dade da Tonuwa..!"

Farida Tayi Shuru Batace komai ba Zaina ta Dafa hannunta Tana Fadin"Kiyi Tunanin mganata..Ya kamata kiyi Tunanin komawa Gida kema ki bar wannan Rayuwar Don Allah.."Ta Dade Zaune batare da Tankama Zaina kafin ta Ture Hannunta Ta tashi Ta Shige Tiolet Zaina ta Bita da kallo aranta Tana addu"an Allah ya Sa Addu"antace ta karbu Domin ta fara Zargin Da hannun Uwar mata a Tsanar Komawar Gida da Farida ke yi.

Tana Kwancen Taga Tazo ta saka Hijabi ta Tada Sallah Itama bata Koma ba ta mike taje ta Dauro alwalan Tazo ta Bita Sallar Bayan sun Idar kowa ya daga Hannu Sama yana Addu"a ita Farida Tana Rokon Natsuwa ne acikin Rayuwarta ita kuma Zaina Tana addu"an Allah ya karkatar da Hankalin Farida Zuwa Gida ya Rabata da Rayuwar Sabon Datakeyi.


Kwana Biyu sai Faridan ta saki kamar ba ita har Tafiya ta kamata Abuja tatafi Bayan Tafiyanta da kwana Biyu Su Zaina suka Daina ganin Kiranta kamar ko yaushe Tunda in bata Gidan kullim sai ta Kirasu awaya sai gashi har aka kwana aka Wuni basu Jita ba,Sun kirata kuma wayar na kara ammh Bata Dagawa ba,hankalunsa gabadaya ya Tashi Barin ma Zaina da Duk ta Tsure ko abinci ta kasa ci Da Karachalle yazo yaji Labari Shima ya gwada kiranta bata Daga ba sai ya Kira Uwar mata ya gayamata itama sai nata Hankalinta ya tashi Ta kira Alhaji Badamasi Tunda Tana da Tabbacin Tare suka Tafi Abuja aikuwa ta sameshi shi yake gayamata Farida ba Lafiya kwanansu Daya da Zuwa Jiri ya Debeta ta Fadi suna wani asibitin kudi a Abuja Jininta ne ya hau kuma Gefen Zuciyarta ya Fara kumbura,Allah ma ya Taimaketa Bata kai kasa ba ya Tareta Data Fadi da ta samu Ciwon Barin Jiki tun jiya bata san Wanda ke kanta ba ammh Da Sauki yau ta Farfado sai dai sun mata alluran barci tana samun Hutu ne.

Wannan Labarin da Karachalle yazo ma dasu Zaina dashi ya kara Tayar musu da Hankali Zaina kuka Zulaihat kuka su Anun ma suka kama Tuni Zaina tayi Damara tace sai taje Abuja Taga Halin da Farida ke Ciki Kilama Ta Mutu ne ba"a gayamata ba Lokacin da Karachalle ya kira Uwar mata yana gayamata Haka tana asibitin Tare da Farida da Alhaji Badamasin da Kawarta Hajiya Zabba"u.

Jin Su zaina zasu Taho yasa Farida ta karbi wayar tayi musu mgana tace su kwantar da hankalinsu ta samu Sauki su Zauna agida Tana nan Dawowa Jin Muryanta yasa Hankalinsu ya kwamta har Zaina taci Abinci tabama su Anun Nono Jin Muryan Farida Domin da Farko Ta Fara kukan Maraici a karo na Biyu ammh Jin muryanta ya kwantar mata da Hankali.

Farida kuwa achan asibiti Daga Uwar mata da Alhaji Badamasi suke akan ta bari ya Fita da ita kasar Waje ayi mata aikin Zuciya Ta samu Lafiya ammh Ta kafe taki yarda Saboda Tana Tunanin in Tatafi ina Su Zaina Zasu..? Wazai kula dasu..? Bazata iya Zuwa ko"ina ba sai ta Maida Zaina Bauchi kamar yadda Tayi alkawari Sunyi Sunyi ammh Taki yarda Uwar mata Haushi Duk ya Kamata tace in Domin Sa"adiya ne Tayi mata alkawarin Zata kula da su Har ta Dawo ammh Farida tace bata yarda ba Dole suka kyaleta Ranar Farida ta saka aka asallameta bayan Gargadin Likita na Rage Tunani da kuma kula da Shan mgani.

Bata yarda Ta kara kwana ba Alhaji Badamasi ya Saka Direbansa Ya Dauko Farida Su kuma Uwar mata amotar ta taho Har Gyallesu Wajen 10pm Dare sai gasu da Zaina da Zulaihat Rumgume Farida sukayi suna kuka Da murnan ganinta itama sai ta Rumgumesu Tana Dariyan Farinciki Allah Sarki Tabbas su din Wasu ahali ne nata haka su Anun sukayi ta Mika mata Hannu suna Dariya ta Dauke su Tana Rumgumansu Cikin Farinciki.

Uwar Mata suka kawota Har Gida ko Zama basu yi ba,Suka koma Zaina da Zulaihat suna Rige Rigen kula da Farida duk ta Rame kamar ba ita ba Zuwa kwana Biyu Farida na Gida su Zaina na kula da ita tana kuma Kiyaye Shan mgani sai ta Fara Jin Sauki Zuwa Sati Uku Farida ta Warke Garau Taji Sauki Sai kuma Ta Koma Bakin Sana"arta Duk da Zaina da Zulaihat din sunyi Sunyi Farida ta Zauna agida ammh Tace ba yanzu ba da Sauran Lokaci.



*Adai yi Hakuri a Fahimci Juna Yan Gidan Zaina Da Dina..*🤣




*Janafty...*
8/6/21, 1:28 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B22️⃣3️⃣*

*IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*

*Bayan Wata Hudu..*

"Bayan Wata Hudu da Tafiyar Zain Zuwa Lokacin Abubuwa sunyi Sauki ta Bangaran Rayuwa ga Iyalan Dr.Saulawa Sai dai ta bangaran Dina Akwai Bambamci Tana Zaune ne kawai ba Domin Tana jin Dadin haka ba Miji a kusa da ita bame gane Damuwa da Halin Datake Ciki Ba.

Tun Tafiyar Zain bai Taba Kiranta awaya ba Sai dai sunyi mgana sau Biyu ta wayar Umma Shima ta shiga ne Taga suna Waya aka bata bayan gaisuwa Bai ce mata komai ba ya kashe Wayarsa Dina Tayi kuka Har Ta gaji da kukanta ta Hakura ganin bame Lallashinta gashi Dai ta Samu Cikar Burinta ammh kuma A banza Tunda bai da wani amfani agareta Kullum Daga Zaman Daki sai Zuwa Shashen su Nene ta Wuni achan Arman kuma yana Cikin Wata na Takwas ne yayi yawo har ya Fara Rarrafe yana Tsayuwa bai dai Fara Tafiya ba Gabadaya Rayuwarsa Tana Bangaransu Umma ne, Su ke kula dashi in ka ganshi Wajen Dina yaje shan Nono ne Zainab Ba inda bata Zuwa Dashi Ko Haddir Ranar Weekend zai zo ya Daukeshi ya kai shi Ya wuni Wajen Hajiya Mama da Alhaji Tsoho sai Dare yake Dawo dashi iya kulawa su Umma nayi mata Ammh ba nasu Take Bukata ba kulawan Zain take Bukata da Soyayyarsa sai Yayi mata Nisa kuma ta Tabbatar da mganarsa dayace Tunda ya Rasa Farincikin itama sai ta Rasa nata.

Duk da tana samun Duka Jin Dadin Rayuwa Zuciyarta ba Farinciki Ta Zauna ta auna Tagani Cewa Barin Zaina Rayuwar Zaina bashi kadai yayi ma Illah ba Harda ita sai gashi Ta Koma Tana Rokon Allah ya bayyana Zaina ko Dalilin Dawowarta Zai sa Zain ya Dubeta amatsayin ta na matarsa Har Lambarsa ta Sata a wayar Nene Ta Rika Kiransa Tunda ya Dauka sau Daya yaji Muryanta Daga Ranar ko ta Kirashi baya Dagawa Dole ta Hakura Ta rasa wa zata Fadamawa Taji Dadi Dalilin Haka yasa Ta Tambayi su Umma Tana so taje kano Suka gayama Abba Shi kuma yace Taje Tunda Mijinta baya kusa.

Zuwan Dina kano Tayi Sati Daya yasa Hankalinta ya Kwanta,Ta Samu Natsuwa Tunda Zasu Zauna Suyi Hira da Daddy da kannenta Da Take jawosu Jikinta yanzu,Domin Ta lura bata da kowa Bayan su,Hajiya Batula yanzu wani Girma Take bata Domin Duniya ta Fara Koya mata Hankali,Arman kamar kada ya Dawo Daddy da Hajiya Batula suna kaunarsa Balle su Waleed Har suna Cewa Anty Dina ta bar musu shi Dina na Dariya Domin Tasan ta koma ba Arman ta bani Wajen su Umma Haka Daddy ya Narka musu Uban Siyayyah ya bada Direba da Excort dinsa aka Maido ta Gida ita da Arman Ranar da suka Dawo kowa yayi kewar Arman wanda ya Fara Tata Hajiya maimuna Tana Sudan Dina na yawan aika mata Hotunan Arman Kuma tace mata Tana so Tazo Taga Dangin Mahaifiyarta ammh sai Zain ya Dawo kasar.

Bayan Dawowar Dina Daga kano Ta Fara ganin Canji a atare da ita yawan cin Abinci Da kuma Kiba Datakeyi Wuyanta ya kusa Hadewa da Jikinta ga yawan Barci kamar kasa sai ta Fara Tunanin kila ta samu Chanji ne Dataje kano Kowa ya ganta sai yayi mganar Kibanta Ta kara kuma Fari da Cika Har Nene na Fadin Cikar Jego ne batayi ba sai yanzu Ashe ba haka bane Ciki ne Dina keda Shi ba"a sani ba Itama bata sani ba sai Da Watarana Ta Fadi Ta Fito Zata Shashensu Umma Ta Fadi Nan da nan aka Kira Haddir yazo ya Dubata yayi mata Wasu Tambayoyi Tun kafin ya Dibi Jininta Dina ta Fahimci komai Sai jikinta yayi sanyi Lalle Ta zama Wawiya Dabata gane Tana da Shigar Ciki ba kamar ba Likita ba sai dai Bata gane komai ba Saboda Tun, Haihuwan Arman bata kara yin Jini ba Shiyasa bata kawo komai ba alokacin ashe Abunda ya Faru Tsakaninta da zain Rabo ne yasa ta sakamai Mganin karfin Sha"awa har komai ya kamallah Domin Tana da Tabbacin Ranar ta samu wannan Cikin Tunda Tun bayan Auransu wannan ne Haduwarsu na Farko Kuma na karshe illah kuwa Domin da yammah da Haddir ya Dawo da Sakamakon Cikin Dina na Tsawon Wata uku ne da wasu kwanaki Dina na Jin haka Daman Tuni tayi Lissafi Domin In bazata manta ba Zain yana Da Wajen Wata Hudu da kwana Goma ne da Tafiya.

Kowa yaji Labarin Dina Nada Ciki sai ya kara Sanyi Da lamarin Ubangiji ashe akwai Rabon Haihuwa a tsakaninsu Shiyasa komai ya Faru Kowa yayi Murna Wannan karon Fiye da Karon Farko Haddir da kanshi ya Kira Zain ya gayamai Lokacin Da yagamai ya kasa Tsayuwa sai da ya Zauna Da yayi lissafi shima sai ya Fahimci cewa Ranar da Komai ya Faru Tsakaninsu ne Dina ta samu Ciki Ranar Haka ya Wuni ba Walwala Jikinsa Duk yayi sanyi bai da ta cewa yanzu haka Firstlove Zata dawo Taga Dina ta Haifi Arman kuma Harda wani Ciki..? Da wani kallo Zatayi mai..? Bashi da yadda zai yi da Abunda

26 / 37