Chapter 14 Reading Zainazain Book 2 Complete By Janafty Arewa Novels

Zainazain Book 2 Complete By Janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   14 / 37

39K to 42K   out of 108.5K words

Saudart ma Nene ta kadasu Suje suyi sallah ita Tana Hutu Shiyasa kuma sun gama Girki Tun dazu ita da Umma.

Zakiya kuwa na Shiga Dakin Dina Ta ganta zaune saman Cafet ta Mike kafafunta da suka kumbura ga Tulalen Cikinta wanda ya kumburata Ta zama wata iri da ita Fuskarta Tayi kwaba kwaba komai ya Bude na alamun Ciki fa ya Tsufa Zakiya sai Da Taji Tsausayin Dina kusa da ita ta zauna Tana Jera mata sannu Cikin Taruwan Hawaye Dina Tace"Zakiya anya Ban kai kaina Cikin Mutuwa ba kuwa..? Kalli yadda Cikin nan ya maidani fa.? Zain baya kallona Sai nayi Sati ban sakashi acikin Idona ba Wlh bai Taba tako kafarsa Dakin nan ba sai sau Daya Indai Ina son ganinsa sai na Daidaici Lokacin Fitarsa Da Safe na Leka na ganshi ammh bai Taba mim kallon arziki ba Ballatana ya Tuna da Abunda ke Cikina.Anya Zakiya Ina Tunanin Komai namu bazai lalace ba kuwa..? Ina aikin da Boka yace yayi mana banga alaman har yanzu zain yana Sha"awata ba koda zamu Tsarkake auranmu ai kulawa yabawa ko..?

Zakiya Tagumi tayi Tana kallon Dina Domin sai alokacin Ta Fahimci Irin Zafin da Dina keji acikin Zuciyatta game da zain Domi itama yau kadai data Hadu da Ja"afar yagama Tafiya da Zuciyarta Ashe haka Dafin so yake ita ta Fada Tundaga ganin Farko ganin Kamar Zakiya bata Ma san me take Fadi bane yasa ta Zungureta Tana Fadin"Kina Jina kuwa..?

Sai Lokacin Zakiya Hankalimta ya Dawo kan Dina ta kalleta Tana Fadin"Najiki Dina..Ina Auna Dacin Da kike ji acikin Ranki ne wanda yau kawai na Tsinci kaina aciki yaya Zan kare Watarana Kuma..?Dina Tayi mata kallon Mamaki kafin tace"Topha Bangane ba..?

Zakiya Ta gyra Zama kafin tace"Kema kinsan Dole na samar dake komai..ammh kafin nan bari muFara da naki Mtsalan yanzu dai menene Damuwarki Dina..?Ga ki acikin Gidansu Zain fa Ga Cikinsa ajikinki kuma Insha Allahu nan da wata Biyu zaki Haihu a daura muku aure da Zain,me kuma kike nema ahalin yanzu..?

Dina Ta batarai Tana Fadin"Zain nake so kuma nake Muradin mallaka Zakiya ai kema kin sani..?

Zakiya tace"Mallaka ta nawa kuma..?banda wacce kika mallaka kuma zaki kara mallaka nan gaba kadan.."Dina Tace"Ba wannan ba..Ni ban mallaki Zain ba Zakiya kuma bana Hangi mallakansa nan kusa Baki ji me nake Fada Miki bane ya Tsaneni faKo kaunar ganina Bayayi haka ne mallaka Nifa burina na Samu Zain Daidai da yadda nake so ya Soni ya Kaunaci kwatankwancin Yadda nake sonsa koma yafi haka ya nuna yana Sha"awata da son kasancewa dani kamar Baya.."Zakiya tace"Tab..Kema kinsan ai haka bazai Faru ba Dina Ba Soyayyar Zain kike son mallaka Shi kikesn Mallaka kuma na Taimaka miki Komai ya kusa Zuwa Karshe..Ai Tun abaya nagaya Miki Zaim bazaki Taba Samun Soyayyarsa ba Mace Daya ya baiwa Kuma Halima ce.."

Dina tace"To yau ina Haliman inace bata Shiga Duniya ba wama ya sani Ko batama da Rai.."Zakiya tace"Kada kiyi Fatan Halima ta mutu..Kiyi Fatan aganta ta kuma Dawo Gida In ba Haka ba Har Abada baxaki samu kyakyawan kallo Daga Zain ba Daga ke har Shegen Cikin ki kuwa.."Ran Dina ya baci ta kalli Zakiya Tana Fadin"Bangane ba..?

Zakiya Tace"zaki gane ne nan gaba..Alokacin da Zain zai Dankara Miki saki bayan anyi auran Domin bazai kara yarda yayi ma iyayansa gaddama ba Ki sani Halima itace Rayuwar Zain da duka ahalinsa Rashinta Tamkar rasa wani Gibi ne kuma yanzu ke yake kallo asilan komai Saboda haka Fatan ta Mutu ma bai taso ba Wlh kanki kawai kike sokama Wuka kina Kirari.."

Dina Tayi Shuru Tana wani Tunani kafin tace"Naji..Ammh Ina son ki komamin Wajen malamin nan."Zakiya tace"Shikenan Zanfara gayamai ta waya yadda mukayi zaki Jini...Allah ya saukeki Lafiya ya mganar da mukayi a waya Ummi Maimun din zata zo Har Ki Haihun ne..?

Dina Tace"Eh..haka Dady ya gayamin kuma itama munyi mgama da ita tace Watan Gobe zata zo.."Zakiya tace"Naji Dadin haka..Domin ni ban yarda da Iyayen Zain ba kada su kashe Yaron Tun Ranar da yazo Duniya.."Dina tace"zasu aika Musamman ma Uwarsa da wannan Shegiyar kanwar nashi.."Zakiya tace"Bar yan kutumar Uba Ta Allah batasuba suna ji suna gani Zamu yi auranmu Wlh.."

Dina Ta kalli Zakiya Tana Fadin"Zamu auranmu kuma..? Zakiya tace"Yes..Nima na samu MrRight dina Insha Allahu kinayi aure Nima zanyi.."Dina tawashe baki Ta bata Hannu suka Tafa Tana Fadin"Bani nasha Shegiya kice kin Fada.."Zakiya na Dariya nan da nam ta kwashe komai ta gayama Dina Ta karishe Da Fadin"Ban taba sanin Haka so yake ba sai yau Dina..Zuciyata na Bugawa Saboda Ja"afar kuma nayi Dace na samu Daidai da Ra"ayina bashi da Kudi ammh yana da kyau sosai kashe mai kudi In aureshi Yarone wanda bai san Komai ba ba gane komai zai yi ba.."

Dina Ta kara bata Hannu suka tTafa Tana Fadin"Dakyau Tawan..Gaskiya Tsarinki yayi fa..Kinga Shikenan kin samu Dami akala kawai.."Zakiya tace"Kwarai makuwa.."Dariya suka saka ma juna kafin su Cigaba daTattauna Zakiya na gayama Dina Zata kaishi Har kano Wajen Baba in suka gama Daidaitawa Tunda ta Lura kamar yaron yana da Saukin kai kuma Zata bashi Kudi Kudi kuma Babu Abunda basa kawowa.

Zakiya Batayi Shirin Tafiya ba sai Pass 9pm suna Hira ko Salla ba wacce Tayi Tunanin tashi Tayi Bayan tayi sallama da Dina taRakota Zuwa Falo Saboda Cikinta yayi nauyi Daman Haddir yace mata ta Dinga MotsawaTa Daina zaman waje Daya Ta Rakota Falo kenan ba Kowa Su Umma Kowacce Tana Dakinta Sai ga Zain ya Shigo ya Dawo Daga asibiti sanye Cikin Suit black and White,Coat dinsa da wayarsa Hade da key din Motarsa suna Hannunsa ya Shigo Falon sai suka ci karo Gabadayansu kallo Daya yayi musu bai kara ba Zakiya tana gaisheshi yayi kamar bai jita ba da Sarsasarfa ya Karisa Dakinsa ya Banko Koda Daga Dinar Har Zakiya da kallo suka Bisa kafin su koma su kalli Juna Zakiya ta Jinjina kai Tana Hango Tsana mai yawa Daga Idanuwan Zain akan Dina Bata Fatan Hakan ta Faru ammh Zata Kira Mallam Taji da Haka tayi ma Dina sallama ta Fice ta Shiga Motarta ta Bar Gidan Tana Tunanin Ja"afar Domin har ga Allah yanzu ba Tunanin mafitan Dina bame agabanta Tunanin yaya Makomar kanta take domin a Hakikanin gaskiya Ja"afar ya Tafi da Duka Imaninta.





*Ki biya ki karanta Cikin Salama Hajiya...!*






*Janafty...*
7/19/21, 2:11 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ....B21️⃣2️⃣*


*IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*



"Ranar Zakiya Dakyar ta iya Yin Barci Saboda Tunanin Ja'afar Daran nan gabadaya Tayi shine Cikin Tunaninsa da kuma Son ganinsa,zakiya tun adaran Jiya Tagama yardan ma kanta ta Fada Tarkon son Ja"afar wanda kuma yayi mata Mugun kamu.

Washegari Idanuwanta Luhu Luhu Ta je wajen aiki Saboda Rashin Barci,Office din ma Tadai Zauna ne kawai ba domin Tana Cikin Hayyacinta ba Wuni Tayi Tunanin Ja"afar Data Runtse Ido kallonsa Yake Dawowamata Cikin Xuciyarta yana Sarrafa gangan Jikinta kamar Tana gabansa.

Ganin Bazata iya jurewa bane yasa karfe 2:30pm na Rana ta bar Ma"aikatan su Zuwa Garejin su Ja"afar saboda ta ganshi Tana Zuwa kuma sai taci Sa"a Shi Ta Fara gani yana gyaran Wata Mota Tana ganinsa Ta Shiga Washe mai baki,shima Sai ya sakarmata Mirmishi Wajen ogansu Ta Nufa suka gaisa saboda Taji Labari Daga bakinsa yasa ta Fara mai Godiya Tana yaba aikin Ja"afar din nan yake gayamata Yaron bashi da wata mtsala,Sabon Zuwa ne bai Dade yana aiki Tare dasu ba,Maraya ne bai da uwa bai da Uba Taji Abunda take son ji bata Dade ba Tatafi Batayi ma Ja"afar din mgana ba ammh Shi ya gaisheta Ta amsa Farinciki na Cika Ranta Ta ganshi sai taji ta samu Sauki Haka ta koma Gida tana sakawa Tana warwarewa Tana ganin Ta Samu wanda ya Dace da ita Zata Jarabashi Tagani Indai irin wanda Take Muradi nezata sakarmai kudi Ta kuma Bayyanamai Bukatarta Ta Tabbata bazai ki ba.

Da wannan Shawaran Tayi amfani ta Fara Kiran Ja"afar ta wayarsa suna gaisawa shi kuma ya kwantar dakai yana Bata Girmanta,Yana Nuna mata Kamar wani Sakarai wanda bai san Duniya ba,Zakiya Bata iya kwana Bata saka Ja"afar acikin Idanuwanta ba Shiyasa bata iya kwana Bataje garejinsu ba Koda Daga Nesa ne zata Tsaya ta gansa Taji Dadi Duk Abunda take yi Ja"afar yana sane da ita Ya kyaleta ne Domin ya Riga yagama Dana mata Tarko kuma ta kama kaf Labarin Zakiya a tafin Hannunsa yake Daman kuma Yasan bazai Tamai wahalan Fadawa Tarkon Daya saba Danama yanmata ba Ashe Rabon samun wannan Hajiyar ne ya kawosa Bauchi Lalle kakarsa ta yanke Saka.

Gabadaya Tunanin Zakiya da Duka Rayuwarta ta koma Wajen Ja"afar ne da yadda zata Tsara musu Rayuwa mai kyau tama manta da Mganarsu da Dina sai da Dinar Ta gaji Da Jiran Kiran Zakiyan ta Kirata Tana kara Tuna mata,Sai alokacin Zakiya ta Tuna Bayan sun gama wayar sai ta Kira wayar malamin Tamai mganar ta kuma Sanar dashi Halin Da ake Ciki yace ta bashi kwana Biyu zai Bincika yagani komai ake Ciki zai Kirata ya sanar da ita.

Aikuwa Bayan kwana Biyu sai ga Kiran Malamin bayan sun gaisa ya koramata Bayanin Abun yagani ya sanar da ita Yanzu zain yafi karfinsu Domin Kakansa ya Tsaya akansa kuma Shi kanshi yanzu ba zaune yake ba ya Mike da addu"a Dare da Dara ga sadaka da kuma Saukan Karatun Dayake sakawa anamai Tuni Sihirin Jikinsa ya lalace kuma ya gayamata ko an sake mai wani da wahala ya kamashi Mganar auransu da Dina kuma Da gaske ne yaga auran sai dai acikin Auran yaga Duhu sosai,Kuma Daga baya sai yaga Haske Tare da Tauraransa na Farko wanda yazo ya Tunkude Tauraron Dina baida Masaniya kan Abunda zai Faru agaba Ya kuma gayama Zakiya Ayanzu Zain ba wacce ya Tsana sama da Dina Zuciyarsa Daman bai Taba sonta ba asiri ne ke Dawainiya dashi yanzu kuma ya Lalace Jin wannan Labarin ya sanyayama Zakiya jiki Bata iya gayama Dina Haka ba Saboda Bata so Ta tashi Hankalinta itama kuma Ta Tada mata da nata Hankalinta,Sai kawai tace mata yace da Zaran ta Haihu aka Dauran auran komai zai Dawo Daidai da wannan mganar Dina Taji Hankalinta ya kwanta Batare da tasan me Zakiyan ta Boye mata ba.

Sati Biyu da Haduwan Zakiya da Ja"afar ta riga tagama Tsara Yadda Zata Jaraba Ja"afar tagani Tunda Zuwa Lokacin Tagama yarda ma kanta Ta Fada Kogin Sonsa mai Tsanani wanda bazata iya Rayuwa bashi ba.

Weekend ne Ranar Lahadi bata je aiki ba Tun safe ta shiga kasuwa Tayi Cefene,Tazo Tayi Lafiyayyan Girki da Lemukan sha Ta tsala wanka Taci kwalliya Da Damammun kaya Wadanda suka Fitar mata da Suran Jiki tayi Barin Turare ajikinta,Bayan mangariba ta Kira Ja"afar tace Ko zai zo Gidanta akwai mganar Datake so su Tattauna Cikin Ladabinsa yace mata Zai zo in yagama gyaran Dayake a garaje yabiya inda yake kwana yayi wanka Ta Turomai Adireshin Gidan nata Cikin Rawan Jiki ta Turamai Shiko Lokacin yana Cikin garejin Daman nan suke da Daki suna kwana Shida sauran kananun Kanukawa da basu da Gidan Iyaye nan kusa.

Wanka yayi ya sauya kaya Zuwa Riga da wando duk sun Muje Na gwanjo ammh kuma suna wamke Tas dasu Mashin ya hau Zuwa Gidan Zakiya yana Isowa ya sallami mai mashin din kana ya Kira Zakiya yace mata gashi ya iso tace Gatanan Zuwa ba Dadewa sai gashi ta Fito Tana wani Rangwada da Rangaji Kamar wata Tarwada,Tun Daga nesa yake kallonta Cikin Mayen Kallo da wani Sha"awa har yana Sude baki acikin Zuciyarsa kuma Allah ne kadai yasan Abunda yake kullawa Tana karisowa ya Sunkuyar dakai Yana gaisheta bata amsa ba ta riko Hannunsa Zuwa Ciki ya Shiga Binta kamar Rakumi da akala.

Har Cikin Falonta Takaishi Bayan ta Rufe kofar Falon kan Daya Daga Cikin Kujerun Falon Ta zaunar dashi kana ta Koma Kitchen Tana ta Jera mai abincin Data Hadamai Bisa karamin Center Table din Dake gabansa Bayan Tagama tace mai Bismillah ya Fara Nokemata yana Jin kunya Zakiya ta Zauna gefensa Tarika Diba Tana bashi abaki Da Farko kin karba yayi sai da Zakiya ta bata rai kana ya Rika Bude baki Cikin Tsoro yana karba ya Takure Waje Daya kamar ace Kai ya Zura da gudu.

Sai da Ta Tabbatar daya Koshi kana Tattara komai ta maida Kitchen Tana Dawowa Ta Haye kan Cinyarsa ta Fara Shafashi Kota Ko'ina Cikin kwarewa da Bariki Tuni Jikinsa ya Fara Bari yana Kokarin Kauce mata ta Riko Fuskarsa Cikin Tafukan Hannayenta Tana kallonsa kafin ta Sumbaceshi saman Lebensa Tana Kokarin Hada Bakinsa da nata ne ya Daddage ya Tureta Sai da ta Fadi Gefen Kujera ya mike da Sauri yana Goge Bakinsa Cikin Sanyin yace"A'uzubillahi Haba Hajiya Zakiya me kike yi ne haka..? Karki manta ni ba Muharran minki bane bai kamata ki kebance Dani har kina Tabani ba wannan Haramun ne.."

Yafada yana wani kauda ido Cikin Jin Dadi Zakiya ta mike Tana kallonsa Tana Kokarin isa Gabansa ya Daga mata Hannu yana Fadin"A"a kada ma ki kariso kusa dani  ni bakowan kowa bane face Takala bakanike mai gyaran Injinan Motoci Ina Kebe kaina Da Haramun Tunda dai Abun ya koma Haka kada ki kara Gayyata ta Gidanki indai kinsan Ba abun alhrri ne acikin Zuciyarki ba.."Yana gama Fadar haka ya Bude Kofa ya Fice da Sauri Zakiya Tana Tsaye Tana Binsa da kallo Farinciki ya Cika Zuciyarta Yana Fita Ta Koma kan kujera Ta Fada Cikin Farinciki Tana Fadi a fili"Allah nagode maka na samu irin Mijin Da na Dade ina jira.."

Bata Damu da Fushin sa ba ballatana Tafiyarsa ba Daman Abunda Take son gani kenan ta Tabbata da yaron dan Hannu ne bazai gujema Tayinta ba Sai gashi ya nuna mata shi na Allah ne Taji Dadin haka,Lalle Zakiya Kina Nufin zaki ma Allah wayau ne..? Uhmm

Bata Nemeshi Washegari ba sai da yammah tayi ta Kiranshi awaya bai Daga ba sai da Tatashi aiki Ta Bishi Chan garejin ta sameshi,Tayi ta bashi Hakuri Tana gayamai ba Nufinta kenan ba kawai Ta Jarabashi ne,dakyar ya Hakura yaran garejin Harda ogan nasu Suna ta mamakin Shige da Ficen da Zakiya Take wajen Ja"afar sai dai sanin Ja"afar don akwai kyau da kuma Haiba Kodomin haka yana Jan hankalin yanmata Da kyansa Zuwa Garesa.

Da Daddare ta kara Gayyatan Ja"afar Zuwa Gidanta sai dai wannan karon Harda babban mayafi ta sanya Ta Rufe Jikinta Bayan Ta gabatar da abinci yaci kadan sai ta Fara Tambayansa Tarihin Rayuwarsa Shi kuma ya gayamata Cewa Shi Maraya ne bashi da uwa bashi da Uba yataso hannun kakarsa Wacce Ta Rasu Shekaru Biyar da suka Gabata Shine Dalilin Rasuwarta ya Shiga gararin Rayuwa Har Lagos yaje yayi Bin Mota yayi Faskare da saida Icce ayadda yake gayamata Basu da wani Dangi Shiyasa Rayuwar Tataso sai ahankali Har Allah ya kawo shi Garin Bauchi ya Hadu da wani saurayi shi yayi mai Hanya Zuwa wajen ogansa mai Garejin gyaran Motoci Har ya Daukesa yana aiki Dashi Zakiya Ta Tambayeshi ko yayi karatu yace mata iyakarsa Secondary Taji Tsausayinsa Sosai Harda mai Hawaye Daga karshe tace kada ya Damu Insha Allahu Zata mai Komai yake so arayuwa,Jin haka yasa Ja'afar yasa ya Dinga ma Zakiya Godiya Kamar ya kwantamata Tace kada ya Damu ya Dade agidan suna Hira sai Wajen 10pm ya Tafi Washegari kuma ta kama Jumm"a ne bayan an sauko Daga Masallacin Jumma"a Zakiya Tabiya Gareji ta Dauki Ja"afar ta kaishi Babban Shago Ta Jidan mai kaya kama Daga na sawa Takalma Agogo Kananun kaya da manyan kaya wanda Basu Dawo ba sai da suka Biya aka aunasa Ta bada dinki Ta kuma kaishi Shagon Saida waya ta Siyamai Waya mai kyau da Tsada babu Abunda Zakiya Bata Siya ma Ja"afar na gayu ba Daga Ciki Har Waje so Take ta Fito Dashi Ta kuma Nuna ma Duniya Mijin da Zata aura Shima ya isa kuma yakai Bayan nan kuma Ta kama mai Hanyar wani Gida nan kusa da Anguwan Datake zaune Ta Cikamai da kayan alatun Rayuwa Tace ya Dawo nan da kwana mganar aikin kanikanci kuma Tace karya Kara Komawa Tana da kudin da Zata Rikesa ogansa kuma Daman ta Riga Ta gayamai auransa Zatayi Ja"afar din bata gayamawa ba ammh Har samarin da suke kanikancin Tare sun san da Labarin wasu da yawa suna Taya Ja"afar murnan ya Tsinci Dami a akala Duk da bai Dade da Zuwa garin ba.


*******

Yau Abba bai Dawo Gida da Wuri ba ya biya ta gidan Alhaji Tsoho ya gaishesa Shida Hajiya Mama ya kwana Biyu bai lekasu ba chan yayi mangariba yayi Isha"i Sai ga Zain da Haddir sun Shigo suma bayan sun gaisa ne da Abba zai Wuce sai suka Fita Tare da Zain din Ko agidan Alhaji Tsoho mganar Dayane kan Zain ya Cire Damuwa Halima addu"arsa take Bukata Damuwa Tana Bayyana akan Fuskarsa Duk ya Rame ya lalace kamar bashi ba Inda Allah ma ya Taimakesa Zuwa asibiti da Duba marasa Lafiya na Debemai kewa ammh Kowa yaga Dr Zain yasan Yana Cikin Tashin Hankali da Rashin Natsuwa.

Bayan sun Dawo sun Dade aharaban Gida suna mgana da Zain da Abba,Abba yana mai Nasiha da kuma Jan hankali kan ya yarda da kaddara Tunda Shi Musulmi ya kamata ya Zama Jarumi Akan wannan lamarin,Zain dai yana jin Abba ne kawai ammh Tayaya Firstlove tabar Gida Dauke da Cikinsa baisan wani hali Take Ciki ba kuma ace ya zauna Cikin kwanciyar Hankali wannan ai bata yuyuwa Dole ne ya mike Tsaye Kan Jiki kan karfi Ko Allah zai sa adace Shiyasa Duk masallatan Jumma"an Dake garin Bauchi ba inda bai kai Neman addu"a ga Halima ba Da Fatan Allah ya bayyanata.

Atare Uba da Dan'sa suka Shigo Gidan Umma da Nene dake Falo suka Tarbesu,Zain ne ya dan Zauna afalon yana wasa Da Saudart da Junior Abba kuma Ciki ya Shiga Nene tabi Bayansa Zain kuma Bai Dade ba ya Tashi Zuwa Cikin Dakinsa Umma ta saka Zainab takai mai abinci ko Ijiye Farantin batayi ba yace ta maida Baya Bukatar cin wani Abu Tana Fita ba Dadewa sai ga Umma da Kanta Ta Dawo Dashi Ya shirin Shiga wanka ne Yaji Shigowar Umma ya Dago yana kallonta Dauke da Farantin Abinci bai samu Zarafin mgana ba ta Ijiye nan saman Cafet din

14 / 37