Author : Jamila Janafty Category : Romantic Hausa Novels
Dake Dakin Tana Fadin"Zainullahi Yanzu ace Fisabillahi Haka zaka Dinga zama baka cin Abinci..? So kake wani Cutar ta kamaka ta kwantar dakai tayi maka illah..? Wa gari ya waya in aka wayi gari Haka ya Faru..?
Zain Ya Sunkuyar dakai kafin yace"Ba haka bane Umma..Kawai Bana jin Cin komai ne Nasha Tea a office Dazu.."Umma tace"Tea ne kadai zai rike ka..? Ina fa Lura dakai baka son cin Abinci in banice ko Nene muka matsa maka bafa..Hakuri zakayi mu kam muna Cikin wannan Damuwar na Rashin Halima ammh ka sani addu"a itace mafita Tunda Damuwar bazai Dawo da ita ba Face Allahn da zamu kaima kukan mu Shi zai Bayyana mana ita Cikin Koshin Lafiya da yardan Allah.."
Zain Dayaji kamar ya Fashe da kuka Idanuwansa sun kala sunyi Jajir,jijiyoyin kansa sun Tashi Radau yana jin wani Suya acikin Kirjinsa ya kalli Umma araunane yana Fadin"Umma Ni Damuwata Ina Firstlove ta Shiga..? Rashin Sanin Wani Hali take Ciki yana sakani Shiga Damuwa Uwa uba kuma Umma Ciki gareta Cikin Fari Umma Zaina Duka Nawa take..? Zata iya kula da kanta da Abunda ke Cikinta..?umma bazata iya ba Na tabbata aduk inda Take Cikinta ya Tsufa ta kusa Haihuwanshi Umma a ina Zata Haihu..? Tana ina ahalin yanzu..? In ina Tuna haka Umma sai naji komai ya Fita kaina Taya zan zauna ina Farinciki Ina cin abinci ina Nuna muku komai ba komai ba alhalin Zuciyata ba Huta ba Natsuwa Bazan iya ba Umma Wlh Firstlove itace Raunani da Duka Zuciyata Rashinta gareni kamar Rasa wani Bangare ne najin Dadina.."
Ya karishe yana Runtse Idanuwansa Cikin Halin kuna da Bakinciki in ya Tuna wani Abu Umma da Kalamansa suka Sakata Jin Taruwan Hawaye ta isa Garesa sai dai ji yayi ta Dafa kansa Tana Fadin"Nasani Dole zakayi wannan Tunanin muna Muna yin irinshi..Wlh kullum bana iya kwana na tashi ban yi ma Halima addu"an Allah ya Tsareta ba Duk sadda Tunanin haka ya Fado maka kayi Tawasalli da sunayen Allah ka saka acikin Ranka aduk inda Halima Take tana Cikin Koshin Lafiya kuma da yardan Allah zata dawo garemu Cikin Lokaci kalilan.."Zain Daya Bude jajayen Idanuwansa yana kallon Umma Sai ta gyada mai kai Tana Fadin"Kadaina Damuwa kaji ko..? Insha Allahu Halima Zata dawo Cikin kwanciyar Hankali ita da Abunda ke Cikinta.."
Zain ya Bude baki yace"Zata dawo garemu Umma..? Umma Tace"Da yardan Allah...Domin Ubangiji baya barci kuma baya Gyangadi Yana Karban Duka addu"an Bayinsa Salihai.."Da wannan kalaman Zain yaji hankalinsa ya kwanta Umma bata barsa ya Shiga wanka ba sai da Tajashi Ta bashi Abinci abaki yaci ta bashi Ruwa yasha kana Ta barshi ya Shiga wanka ita kuma Ta tattara komai Zuwa Kitchen acikin Ranta Cike da Tsausayin Halin da Zain yake ciki Gefe Daya kuma Ta Fatan Allah yasa Halima Tana Cikij Koshin Lafiya Har ga Allah Itama tana wannan Zullumin kuma in lissafinta yazo Daidai kamar Cikin Dina itama Halima Tana Kusa Shiga wata Takwas kenan koda ba"a aunata ba alokacin Ta Tuna Mom ikilima Data Fara gane Halima nada Ciki tace yakai watansa na uku alokacin In Hasashenta yazo Daidai Tare Zasu Haihu da wannan Yarinyar da Zuwanta ya Zame musu bala"i koma miye zasu Cigaba da gayama Allah Da Izinin Lahi Halima Zata Dawo Gida Ita da Abunda ke Cikinta lafiya.
Nene kuma Tana Dakin Abba sai da ta Taimakamai yayi wanka Ta gabatar mai da abinci Daman Ranar ita kedashi Sai da yagama cin Abinci ya wanke Hannu Nene ta Hada komai Zuwa Kitchen ta maida kana ta Dawo Ta iske Abba ya saka wani Farin Gilashin mai karamai karfib gani ya Bude System dinsa gefensa ta samu ta Zauna Batare datayi mgana ba Ganin Haka yasa Abba ya Dakata da Abunda yake Ya juya yana kallon Nene yadda ta kurama wani Waje ido gs duk alamu akwai Abunda ke Damunta da kuma Mgana abakinta.
Gyara Zama yayi yana Fadin"Hajiya Nene lafiya..? Daga gani akwai mgana abakin ki..? Meya faru ne..?
Nene ta Muskuta Tana Fadin"Mgana kam akwaita Abban Saudart..."Yana Danne Danne Bisa System din sa yake Fadin"Uhm ina Jinki.."Nene ta gyara Zama Tana Fadin"Daman nace bari zan maka mgana Tunda naga ko nayi ma Umman Zareena mgana ba Kulani Zatayi ba kan mganar wannan Yarinyar Dake wajenmu ne Abban Saudart.."Kansa na kasa yana Cigaba da Abunda yake yi yace"Wata yarinya kenam..? Kuma wata mgana ce Da Fatima bazata Saurareki ba.?
Nene tace"Yarinyar nan Dina mana..Mganar Cikin Dan'mu Datake Dauke dashi ne Abban Saudart kaga Haddir fa yace Watan Gobe ne zata Haihu Bamu siya ko wando na yaro ba ama Ture uwar,ammh ai Abunda ke Cikinta Dolenmu ne Abban Saudart Tunda Bawa fa bai isa ya Ture ko ya kaucema Kaddaransa ba Abun nan bafa yau ya Faru ba,Ba kuma Jiya ya kamata mu daina kallonsa ta wanmi Fannin mu kallesa da Idanuwan Basira ko ina akaje dai aka Dawo Wannan Abunda Zata Haifa Wlh ya zama namu har Abada Shine naga bari kai nayi maka mgana Tunda gashi Zain bama zan mai mgana ba Shi kanshi bayama Cikin Natsuwarsa kan Batan Halima bana so kuma na kara sakamai wani Rauni acikin Zuciyarsa.."
Har Nene ta gama Mganarta Abba na Jinta bai ce komai ba sai Da tagama Kana ya Sauke Nunfashi ya Dago yana kallonta kafin yace"Ikon Allah har Haihuwan ya kusa zuwa kenan..? Nene tace"Da yardan Allah ta kusa sai dai muyi Fatan Allah ya Raba Lafiya.."Abba ya gyada kai yana Fadin"Ameen...Yaushe ne akace Kanwar maman nata Zata zo Daga Sudan ta zauna da ita..?
Nene tace"Bansan Rana ba ammh an ce Tana Tafe Insha Allahu..Shiyasa nake son kafin Tazo Ta iske an siya komai,Ko bakomai ai an zama Daya Tunda bayan Ta Haihu aure Za"a Daura musu su Tare agidansu Kaga kuwa An Riga an zama Daya.."Abba yace"Hakane..Kada ma ki ma Zain mgana ki kyaleshi Ni zan bada kudin da za"ayi siyayyah In Fatima ba zata je ba ko keda Zainab sai ku Shiga kasuwa ku siyo Abunda ya kamata ya zamu yi..? Haka Allah ya kaddara sai Hakuri ita kuma Halima Allah ya bayyanata Shi kuma Zain Allah ya yayemai wannan Damuwar ya bashi Ikon Cin wannan Jarabawan Rayuwar Data sameshi.."
Cikin Tsausayama Abba dashi Kanshi Zain din Nene take ta amsawa da Ameen Haka dai suka Cigaba da Tattauna mganar Har suka kwanta Kowa da Abubda ke Damunsa acikin Ransa Nene taji Dadi Dataga Abba ya saki ba kamar baya Koda yake ta lura Tun bayan Tafiyar Halima Abba yayi sanyi ya koma kamar bashi ba.
Abba ya Cika alkawari Washegari 100k ya bama Nene kafin ya Fita yace su Tafi kasuwa ita da Zainab su siyo komai,ya fita ya barsu zasu Shirya su tafi Nene ta gayama Zainab Amotarta zasu Tafi Zainab din bata so Zuwa ba Jin Mganar Daga Abba yasa Dole ta hakura da Shiga Cikin makaranta Zain baima san Abunda ke Faruwa ba Tun safe ya Fice Zuwa asibiti Umma kuma najinsu ammh Tak batacr ba karshenta ma Daki ta koma Tana kuka Tana Kukan Nadama da Danasanin Hukuncin Data Dauka a dace Tun Farko ta baiwa Zain matarsa da yau Zaina bata bar gida da Ta tabbata da ita za"a shiga kasuwa itama tayo ma yarta Duka Siyayyan kayan Haihuwa.
Sai wajen 11am suka Fita Suka Shiga kasuwa sai wajen 2pm suka Dawo Inda Nene ta Siyo komai da komai na Bukatan Jariria mai Amfani da mace Da Namiji Tunda basu san me Zata Haifa ba Kaya fa kamar za"aBude Shago hadd dan gadon Daura Bby,Bayan sun Dawo sun Dawo Gidan Alhaji Tsoho suka wuce da kayan suka Nuna Mishi Shi da Hajiya Mama suna ta saka albarka Alhaji tsoho yaji Dadi har acikin Ransa ya kuma yabama Usman kan wannan Abun da yayi yaji kuma azuciyarsa sun Fara karban wannan kaddaran da Hannun Biyu.
Daganan Gida suka Dawo da kayan nan Falo suka baje suna kara gani Umma kuwa Ko Fitowa batayi ba Daman Nene tasan bazata Fito ba Shiyasa bata Nemeta ba,Kayan Nene ta kwashe takai Dakinta da Abba ya Dawo ta kwasa takai mai Yace kada taDamu ta kai ma Dinan Dakinta ta adana Bata kaima Dina ba sai Washegari Lokacin Zain yana Shirin Fita yaga Nene na Jidan Ledoji Zuwa Dakin Da Dina ke Ciki Cikin mamaki ya kalleta bayan sun gaisa yace"Nene lafiya.? Wannan kayan fa..?
Nene ta Dakata Tana kallonsa Dauke da Ledojin overroll Tana Fadin"Kayan Jariria ne Abbanka ya bada kudi aka Siya Saboda Dina lokacin Haihuwan nata ya matso.."Kuri kawai Zain yayi ma Nene Kafin taga ya Rabata kawai ya wuce ya Fita kanxil bai ce ta Bishi da kallon Tsausayi Shi kuwa har yakai Cikin asibitu ransa na kuna yanzu Dai Ta Tabbata Dina agidansu Zata Haifi Cikin Shegen nan..! Kai kaichonsa Daya Biyema Rudun Duniya dana Shedan da ace yaji Tsoron Allah sa da Duk Haka bai Faru ba Cikin kunci Ya Shiga Cikin Office dinsa yana jin wani Nauyi acikin Kirjinsa haka ya Fara Duba patient duk bashi da wani Natsuwa ballatana kwanciyar Hankali.
Dina kuwa Tana Kwance Tashiga Shigowar Nene da kayan niki Niki Tana Daga kwancen Ta Tashi Dakyar Tana gaida Nene ta amsa Tana ce mata"Ka kaya nan ki adanasu..Kayan Baby ne.."Daga Haka ta Fice Batare data Jira Cewar Dina Ita kuwa Dina Tuni Zuciyarta ta kawo mata Zain ne ya Siya Lalle malam yayi aiki Sosai kan Zain daman Tana Tunanin in bai siya komai ba In Ummi Maimun tazo Sai Ta gayamata Bata da komai na Tarban Haihuwa,Duk da Tasan Daddy bazai bar Ummi maimun tazo Hakanan ba Komai Tana da yakinin zai yi mata ammh na Zain abu ne na musamman awajenta wayarta Ta jawo ta Kira Zakiya Ta gayamata sai dai kuma Zakiyan bata Daga Kiran ba bata rai Tayi tana wani Tunani yanzu kwata kwata Zakiya bata son Daga wayarta sai Taga Dama ta lura gabadaya Hankalin Zakiya ya koma ga wannan Yaron Data samu yanzu bata Cika bi ta kanta ba Tabe baki tayi ta maida wayar gefenta Kafin ta koma ahankali ta kwanta Tana yamutsa Fuska Jin Dan Cikinta na Motsi.
*Kuyi hakuri da jina Shuru..Sai ku rikamin Uzuri ga sallah ka Bikin kanwata da Za"ayi mun Shiga Hidima Da zarar na samu Dama zaku dinja jina Nagode..*
*Shakira...*
7/22/21, 2:44 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B21️⃣3️⃣*
*IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*
*Zaria*
_gyallesu.._!
""Zuly da ta dawo Zulaihat yanzu Rayuwarta Ta inganta Tuni ta Fara tsarkake kanta Gefe Daya kuma Zaina na Kokari wajen koya mata yadda Zatayi addininta da kuma yadda Zata karanta Bakin Hausa yayinda ita Kuma Farida ta Dauki Nauyin Kula dasu Duka Biyun.
Uwar mata Hankalinta bai kwanta ba Sai da tazo Taga Inda suka koma kana Taji sanyi Domin Abaya Tana ganin kamar Faridan Ta Subuce matane Tare tazo Ita da yar Rakiyarta wato Hajiya Zabba"u,Lokacin Datazo mamaki Take tana kara kallon Zaina Da Katon Cikinta,ammh Batayi mgana ba Tunda Farida Bata Bada Damar haka ba
Lokacin Dataga Zulaihat agidan Bata Yi mgana ba Tadai ce Faridan Taji tagani sai tayi ta kaya Daman Zulaihat din ba wani Tara mata abun Arziki Tayi ba Saboda Haka koda Ta ganta ta Sauya bata wani Damu ba.
Bangaran su Suby kuwa Sai da Uwar mata tayi mata Tijira kana Ta Shiga Taitayinta Bayan Tashin Farida sai Suby ta Kwashe kayanta ta koma Dakin da Uwar mata tazo Tagani Tayi ma Kaca kaca ta kuma sa aka Fitar da Duka kayan Suby ta sakama Dakin Kwado Tace Bayan Sholly ba wacce keda Lasisin zama acikin wannan Dakin Tunda bata Ciki sai dai ya Tabbata yana Kulee,Wannan Abun ya kara Bakantama Suby Rai sai da Tayi kwallah Tana Tunanin Ta kashe maciji ashe bata sare mai kai Tana Ganin Tunda Sholly tabar Gidan Darajanta zai Ragu kuma Uwar Mata zata koma Tana ganinsu da Kima sai dai Ba haka abun yake ba Ita Sholly Tun Farko mai Sa"a ce kuma karuwa ce mai aji da Lasisi Uwar mata ta sani In Tayi Rashinta Bazata Taba Maida kamarta ba Domin kaf karuwan Data daukesu babu Wacce Ta kama kafar Sholly.
Su Adamalle da Deezee sai Dariya suke ma Suby Domin Ranar a waje uwar mata Tayi mata Tijara Daman shi Bariiki Ko Dan Bariki baya Jin kunya Ko kyashi yaci maka Zarafi gaban Mutane Suby sai kuka Ta Ruga Xuwa Cikin Gida da Borin Kunya Kacharalle ne kadai yasan Inda Farida ta koma Ammh ya kama bakinsa Duk wanda ya Tambayeshi cewa yake bai sani ba Ko bakomai akwai Amana Tsakaninsa da Sholly bazai yarda wannan Amanan Ta Zube ba Suby Har Kudi ta bashi ya Fadamata yaki ya maida mata da kudinta Tunda Farida na bashi Wanda ma yafi wanda ta bashi.
Bayan Kacharalle babu Wanda Farida ke Bari yana Zuwa Inda suke To wama ya sani..?uwar mata ce kuma Tana kaduna Hankalinta ya kwanta ganin Farida bata bar Harkan karuwanci ba Tunda duk sati Tana ganin aleart dinta Shiyasa bata ma Damu Data koma Gidan Malaminta ganin Komai ya Tafi Daidai Abunda Uwar mata Bata sani ba Koda Farida batayi ma kanta addu"a Zaina tana yi mata Tana mata addu"an Allah ya Rabata da wannan Rayuwar ya maida Hankalinta Zuwa Gida ahankali ahankali Tasirin Sihirin yana sakin Jikin Farida Batare da Ita Uwar mata ta sani ba Tunda ayan kwanakin ma Kullum sai Tayi mafarkin Su Mama da su Hasaana da Usaina Tana ganinta Cikin mafarkinta Suna kukan kewanta kuma Tasha ganin Ya Musbahu Cikin mafarki yana kuka yana Rokonta ta Dawo Gareshi In ta Farka sai Tayi kuka ta wuni Cikin Damuwa watarana ma Haka take wuni bata Zuwa Ko"ina Da ka ganta Tana Cikin Damuwa Dalilin Dayasa Jininta ya hau kenan Ta Fara Faman da Ciwon kai da Jiri sai da sukaje asibiti aka Dubata aka bata mgaguna Ita kuma Zaina akayi mata awon Ciki anan asibitin almadina inda Cikinta yake Cikin Wata na bakwai bai karisa Wata na Takwas ba ammh yayiGirma sosai Duk ya Cika Zainan komai na Cikinta ya Kumbura ya kara Girma sai kace Wata Big Mama ita kanta In Ta kalli Kanta amadubu sai Taji Tsoro ganin yadda Tayi wani Muni ga Kuma Girman Data kara Domin Ta Ninka biyunta Lokacin Farkon zuwanta.
Babu Abunda Zata ce ma Zulaihat da Anty Farida sai Godiya Domin suna Bata Dukkan Gudummuwarsu Anty Farida Da Lafiyarta Take bata Nata Gudummuwar yayinda Zulaihat Take bata da karfinta Daidai gwargwado suna Kula da ita Farida ta zama kamar Uwa gareta Yayinda Zulaihat Take kallinta kamar wata yayarta Basa bari tayi Ihim ma Saboda yadda Suke ji da ita Wanka kadai ne Zaina keyi wanda zatacr Tana wahala ban dashi Komai yi mata suke Tasha Ta zauna Tayi kuka Tana Tunanin da me zata saka musu Bayin Allah da suka Sadaukar da komai nasu saboda Inganta Nata Rayuwar Tayi alkawarin Da Ikon Allah sai ta Rabasu da wannan Rayuwar Ta Fara Nasara kan Zulaihat saura Anty Farida wanda Take da Burin Ta Rakata Har Gombe kamar yadda Zata Dauketa ta kaita Har Bauchi Zulaihat kuma Bauchi Zata Tafi da ita Ta Tabbata ahalin Alhaji Tsoho bazasu ki karbanta su inganta Rayuwarta ba
Rayuwarsu suke Gudanarwa Cikin kwanciyar Hankali Basu da matsalan komai yanzu Daga Sholly Har Zulaihat suna Jiran Haihuwan Zaina ne Tuni Har Farida ta Siyama Zulaihat karamar waya ta bata ahannunta Saboda In wani abu ya Faru bata Gida ta Kirata ta gayamata Domin Tagama yarda da Zulaihat din har ta Fara sakin Jiki da ita Tafiya takan kama Farida na kwana ammh hamkalinta nakan Su Halima ta Dinga Kira kenan Tana Tambayansu Lafiya tana Fadin Ko an buga Gida kada su Bude Ko waye in ba Kacharalle bane Zulaihat tace toh..bama su Budewa Gidan akulle yake Wuni kuma akulle yake kwana Karatin dasuke da Zulaihat yana Rage ma Zaina kewa sai da Tana Tuna makomar nata karatunta Data Rasashi Har Abada In Lissafinta yatafi Daidai Su Laila suna Aji uku kenan Sun kusa Hada Digrre dinsu Ita kuwa Gatanan zaman Kila wakalan Rayuwa Waya sani ma Ko wajen Haihuwa Allah yayi mata Rasuwa,Insha Allahu kafin haka Zata Rubuta Takardan Ta bama Anty Farida kafin Ta Haihu In Ta haihu Lafiya Shikenan in kuma Karshen Wahalarta kenan Zata Roketa Ta kai Takardan Har Gidan Ta bama Firstlove Ya Cire Tsammanin Tana Raye.
******
*Bayan Sati Biyu..*!
Alokacin Tuni Hajiya Maimun ta sauka a Nageria agidan kwamishina,Koda ta Sauka Tuni Daddy ya bama Hajiya Batula magudan kudade Taje tayi ma Dina Siyayyan kayan Haihuwa Komai da komai ita kanta Dinar Akwati guda Kwamishina yayi mata na kayan alfarma.
Da Hajiya Maimuna Taga kayan Sai da ta Jinjina Son da kwamishina yake ma Dina Hatta da madaran Shan na yara Gasunan kala kala Tana kallon Kayan Tana Sharan Hawaye bawa bai isa ya kauce ma Kaddaransa ba yau da ace Dan Sunna ne Dina Zata Haifa ta Tabbata Duniya sai ta Sheda Dina yar kwamishina Ta samu karuwa Shi kuma ya samu Jika Ammh Dalilin Abubuwan da suka Faru yau Dinar ma Bata gabansa Tana wani Gidan Chan Dabam ba Domin komai ba sai Domin Rufin asirinsu Duka Godiyarta ga Allah Daya ne Tunda Iyayan yaron masu Mutumci nr Da Dattako Shiyasa har suka karbi Cikin su kuma Yadda Da Duka Wahalansa Har Zuwa yazo Duniya ga wani karin Abun Jin Dadi kuma auran da zai Tabbata Tsakanin zain da Dina Yaron su bazai Taso Cikin Wulakantattacen Rayuwa ba.
Kwamishina ya Tsara Tafiyar Weekend ne Ranar Lahadi kenan Saboda yana so Yaje Yayi ma Alhaji Tsoho Jajen Abunda ya Faru na Batan Halima Dina Ta Kira Hajiya Batula Ta gayamata Ita kuma Take gayamai Duk da ya Kira Alhaji Tsohon tawaya yamai Allah kyauta ammh akwai Bukatar yaje yakara Jaddadamai Godiyarsa ana Gobe zasu Tafi Kwamishina ya Kira Alhaji Tsoho ya gaya musu suna Tafe da Hajiya Maimuna Alhaji Tsoho yaje sai sunzo Ranar da Daddare Abba yazo yake gayamai yace in ya koma Gida ya gayama Matansa Wacce Zata Zauna da Dina Har ta Haihu Suna Tafe gobe Abba yace Shikenan ba Damuwa Allah ya nuna musu.
Washegari kuwa da Wuri su Kwamishina suka iso Duk da Tafiyar Mota ce Gidan Alhaji Tsoho suka Fara yada Zango Bayan an gaisa kuma Da Jajen Batan Zaina sai Godiya Da Fatan gamawa da Duniya Lafiya ya