Author : Jamila Janafty Category : Romantic Hausa Novels
ma Dina wankan Gawa Allahu Akbar su Zaina suna ji suna gani aka Fita da gawan Dina Zuwa Haraban Gidan Alhaji Tsoho Allah sarki Rayuwa kenan Mutane Da Dama suka Sallaceta suka kuma Rakata Zuwa Gidanta na gaskiya.
Daman Haka Rayuwa ta Gada Ka Shuka alheri Domin Watarana Za"ayi kamar baka ne,Bangaran su Anun Zainab Tazo dasu,Zaina Ta karbi Arman Ta Rumgumesa Tana Tuna Mganarta Da Dina na karshe Tayi alkwarin Zata rike Arman Kamar su Anun Baxata Taba Nuna mai Bambamci ba,Haka suka wuni karban gaisuwa su Abba Suna Haraban Gidan suna karban gaisuwa Tunda abokan Siyasan Kwamishina suna ta Zuwa Washegari Harda gwannan Jahar Bauchi yazo Ta"aziya,Aranar kuma Inna Hannatu tazo ita da Mijinta suka kwana Daya suka koma Bayan sun yi gaisuwa abun gwanin Ban Tsausayi Farida ta Kira Har Zain tayi mai gaisuwa,Harda su Anty Yaha da Mami sun gaisa Sun ma su Umma gaisuwan Rasuwar Dina Har da Zaina Ma sunyi mgana.
Sai da akayi Sadakar bakwai Gida ya watse Baban Kaduna da Daddyn Abuja kowanne ya kwashi Iyalansa suka koma Hamdiya ma Tazo Daga kaduna Tayi gaisuwa ta koma Zafeeera bata bi Inna Rukayyah sun koma ba Saboda suna hutu Ga Ciki ya Fara Bayyana Sai Shagwaba iri iri,Shema dai ta koma itama an saka mata Rana Ranar bakwai su Umma suka koma Gidajensu a kuma Ranar ne kwamishina da iyalansa suka koma Kano Cike da alhinin Rashin Dina Shida Hajiya Maimuna wacce ta iso Ranar da akayi Hudu Ta kwana uku suka juya kano Ranar da Dina Tayi bakwai da Rasuwa sai dai Fatan Allah ya Jikanta da Rahma.
Laila Ma tazo Gaisuwa Domin Zaina ta kirata ta Fada mata da Tazo ta ke cema Zaina ta kara Tsorata da lamarin Duniya yanzu,Ta kuma yardan ma kanta Dan"adam ba abakin komai yake ba wajen Ubangiji Ita kanta Zaina haka take Fadi Tana kuma godema Allah Tun Zamanta da Dina wani Sabani bai Taba Shiga tsakaninsu ba Koma ya Shiga kafin ta Rasu sun yafi Juna,Zaneera bata samu zuwa ba sai dai ta kira waya Tayi ma su Umma gaisuwa Domin kwamishina yayi musu kara yace su akayi ma Mutuwa shi kawai Uban Dina yake Abun gwanin ban Tsausayi.
Zaina kuma Ta koma Gidanta Sai da Zain yayi da gaske Zaina tabar Arman wajensu Umma da tace sai Ta Taho dashi yace ta bari ta Haihu Mana Sai ta Faramai kuka Tana Fadin Zata Cika Wasiyan Dina ne ya Lallabata Da Za"a Daukomata shi Tare dasu Anun Daya kira Umma ya gayamata sai tace yazo ya Dauki Yaran ya kai mata Hakan zai Rage mata Radadi da kuma Zafin Mutuwar Dina Haka kuwa akayi Yaje ya Dauko mata su ya kawo mata sai aka samu Lafiya,Zain har mamakinta yake yarda Take kula da Yaran Musamman ma Arman kamar ta maidashi Ciki Wani Lokacin Haka Anun da Anan zasu yi ta Kuka taki Daukansu tana Chan wajen Rawan jikin Kula da Arman Zain sai dai ya Daukesu kawai ba Halin mgana saboda Sanin Halin Zaina na yanzu komai akayi kuka kamar wata karamar yarinya Shima Lallabata yake yi.
Ganin Haka yasa Zain yasa Goggo Halima tayi mgana aka basu Diyar Isuhu Kaltume ya Daukota Saboda ta Taimaka ma Zaina ga ciki ga wahalan yara Tunda Ta matsa ma kanta Kaltume din Shekararta 15 Ta gama Jss Zata Fara SS sai kawai Zain ya Daukota yazo ya sanya Ta makaranta Tana Zaune Saboda Ragema zaina wasu ayyukan,Kuma ba Laifi Tana Kokari sosai kuma zainan Taji Dadi Tana Dauke mata wasu Hidomomin Koda Zain ya Dawo Daga asibiti Sai ta bar ma kaltume din yaran Taje ta kula Dashi.
Bayan Wata Biyu da Rasuwar Dina Lokacin Cikin Zaina na wata na Shida ita da Zafeera suka Tafi Gombe Bikin Komen Auran Farida Da Musbahu Harta da Zaneera sai da ta zo Bikin Saboda Amintarsu da Farida Tayi Nisa Tun Ranar al"amis suka Tafi Da Zaina da Zafeera da Zainab da Zulaihat da Umma Nene sai Ranar Daurin Aure zata Biyo su Abba Zaina Tazo da Kaltume saboda su Anun Da Tazo dasu Farida Taji Dadi sosai na ganin karan da Iyalan Dr.Saulawa sukayi mata Goggo Halima Bata zo ammh ta aiko da sakon kayan gyaran Amarya Abba ma ya bada Gummuwa 100k,Mami da Anty Yaha suna ta Godiya dasu Goggo Zaliha.
Tare dasu duk akayi Shagulgula Zahra ma ta iso Dasu Saratu sun Hade Cikin su Zaina ana ta Hira ana Dariya Alokacin ne Zain ke Tambayanta Ya labarin Uwar mata Farida tace bata dashi Domin ta Karya Layinta kuma Tun zamansu bayan sunan garinsu Gombe bata san wani abu akanta ba bata da Hanyar samunta Alhaji Badamasi ne kuma Shima ta yanke alaqa dashi Zaina tace gwara Hakan Domin Daman Burinta kenan Taga Farida ta koma Rayuwar Kamar kowacce mace mai yanci.
Zubaida kuwa Allah yayi mata Rasuwa itama Lokacin Dataji Labarin Dawowar Farida ta Rikice Tana ta kuka Da Rokon Akaita Ta nemi gafaranta toh Farida Taje har Chan Family House din su Mommy Inda Zubaida ke jiyan Da Taga Halin Da Zubaida ke Ciki sai da Tayi mata kuka Taji To kuma me ya Rage mata..? Bata da wani Sauran amfani Tun aduniya Taga Karshenta Zubaida na kuka Tana Rokon Farida gafara tace ta yafe mata Data koma Gida Ta kira Ya Musbahu Tana Rokonsa Ya Taimaka Ya kai Zubaida asibiti Tana zaune agida ba wani kulawa yace Tsakaninsa da ita Har Abada Bazai Taba yafe ma wacce Tayi Sanadiyar Mutuwar Mahaifiyarsa ba jin Haka yasa Dole ta kyaleshi Tunda har Baffa Haruna ma yace shi da ita Har Abada ko Sati Biyu Farida Batayi da zuwa ba Allah yayi mata Rasuwa Farida ta kara Tsorata da Duniya ta kuma kara Jin Tsoron Allah ya kara kamata Allah ya tsaremu da aikata Aikin Danasani.
Ranar asabar aka Maida Auran Farida da Musbahu Su Zain da Abba da Haddir da Sadiq duk sunzo Daurin Auran Tare suka zo da Nene Ana Daura auran suka Juya saboda Ranar Aka Tafi da Amarya Abuja su Zaina ne yan Rakiya chan suka kwana sai Washegari suka Dawo Bauchi da kayan Biki Niki Niki,Farida bakinta yaki Rufuwa da wannan karan Haka Zaina Burinta ya isa Yau Farida gata Cikin Tsabbataciyar Rayuwa Kamar yadda take Fata sai da tayi kwallar Farinciki
Washegarin Ranar da suka Dawo Daga Abuja Zaneera ta wuce katsina Yayar Mijinta Allah yayi mata Rasuwa Dagachan kuma Bazata Dawo ba Zasu koma Ranar da akayi uku dai su umma sun je gaisuwa Chan katsinan basu kwana ba suka Dawo.
*******
*BAYAN SHEKARU BIYAR..*
Bayan Shekaru Biyar da suka Gabata abubuwa Da Dama sun Faru wasu na Farinciki wasu na aka sinsu Sai dai na Farincikin yafi yawa.
Acikin Farinciki ne sune Harda kamallah karatun Sadiq karami da Faruq sun Dawo Gida Har sun Fara aiki Sadiq karami yayi Auransa da Matarsa Hafsah yar kanwar Mom Iklima ce ya aura Dake kaduna Baban Kaduna an samu Suruka.
Sai kuma Auran Sadiq babba da Zulaihat wanda da kansu suka Hada kawunsu aka sha Biki Abun yayi ma kowa Dadi Sai da Ta kamallah Secondary School din kana akayi Auran yanzu har ya neman mata nan ATBU bauchi Ta Fara Rana Daya akayi Bikinsu da Zainab da Hajiya Mama karama A gidan Alhaji Tsoho,zainab a Lagos Tayi aure Yaron kanin Mijin Inna Hannatu Haka ma kannen Haddir Lauratu da Waleeda ma sun yi Auransu Shekaru Biyu Daya Gabata.
Zainab Har ta Haihu Ta samu Mace Taci Sunan Zaina Sa"adiya Suna Kuma kiranta da Zaina ne,Zainab kuma Tana da Ciki Tayi Jinkiri wajen Samun Ciki ammh su Lauratu Duk sun yi Haihuwan Daya Dayansu Tunda Har Zainab din Ta Rigasu aure
Zafeera da Zaina kusan Lokaci Daya suka Haihu Zafeera Ta Samu Namiji yaci sunan Zainullahi Sai Zaina da Yarinyar taci Sunan Aisha suna Kiranta da Aira,Zafeera Ta gama karatunta Har tayi Service sai da Haddir yace ba aiki Bayan Zain karami Ta kara Haihuwan mai Sunan Abba Wato Usman suna Kiransa Abba karami sai Zaina itama Data kara Samun Mace Taci Sunan Hajiya Mama Amina suna Kiranta da Hajiya karama.
Bangaran Farida itama Ta Samu karuwan yan Biyu ma wannan karan Duka mata yara sukaci Sunan Zaina da na Zulaihat Domin bazata Taba mantawa dasu ba Har Abada Zumunci ya Dore an zama Daya Tazo Sunan Aira itama Zainan Taje Sunan Su zaina ita da Zulaihat Zumunci kuwa da Zareena sai Abunda yayi gaba Har U.s sai da Taje ita da ya"yanta da Mijinta Musbahu wanda arziiki yaci Uban na Da Yayi kudi Soaai na Ban mamaki Farida ta Sauya kuma suna Zaune Lafiya da abokiyar Zamanta.
Lokacin da Suka zo Kaduna Bikin Hajiya mama karama Dayake a Kaduna akayi Bikin Zaina ta Hadu da Suby Tana bara abakin Randa Duk ta kode ta zama wata Tsohuwa karfi da yaji Shine Take kuka Tana gayamata Uwar mata Ta rasu yan Kidnapping Suka Harbeta a Hanyar kaduna Suka kuma Tafi da Hajiya Zabba"u Cikin Daji Har yau ba wanda yasan Labarinta,Daman Tun kafin Haka Jarabawowi keta sauka mata Shagonta ya kama da wuta Babu Abunda aka Fitar Gidanta kuma Gwammati Ta Karbe tace Filin tane aka Saida mata Tayi Gini Bayan Faruwar Haka kuma Yan anguwa Suka yi Fata Fata Da gidan Abincinta da Gidan karuwan suka Fatattake su suka Kone wajen Ta gayama ta Deezee ta koma garinsu su Zeeze kuma bata san isalinsu ba Kacharalle kuma Yayansa yazo Ya Tafi Dashi Daman dan nan Kauri ne Dake kaduna Rashin Ji da Daudu yasa ya gudo Daga Gida Labarin Dai ba Dadin Ji Suby Tana kuka Tana Rokon Zaina Gafara Tana kuma Tambayan Ina Sholly Zaina ta Fito da waya Ta Nuna mata Sholly ita da su Hassana da Usaina da Arif da Musabahu da Yan Biyun data sake Haihuwa da kuma Hoton Zulaihat da Sadiq da Yarinyarsu Suby sai kuka da Nadaman Rayuwa nan Zaina ta Zube mata kudi Ta shige Mota suka koma Gidan Baban Kaduna Dayake Zulaihat bata zo Bikin ba Saboda makaranta Yasa sai da a waya Zaina ta basu Labarin Abunda ya Faru Dukkansu sukace Daman Hakan ya Dace da Irinsu Uwar mata.
Bangaran Kwamishina Mahaifin Dina Tuni an sauke shi Daga kwamishina Shekaru Uku da suka Gabata duk yayi Laushi ya koma Wani nagari Bayan Rasuwar Dina sanadin haka ya gina Makaranta sadakatul Jariya ga Dina Hajiya Maimuna ta koma Sudan Hajiya Batula ta kara Haihuwan Mace Alhaji Gaddafi ya maida mata Dina Saboda kaunar dayake ma Dina yanzu ya gyara Kasuwanci ya koma yi ya bar Siyasa yana kula da matarsa da yayansa Domin ya Fahimci Shine Babban kuskure a Rayuwar Dina,Zumunci kuwa sosai da sukeyi da su Abba Kwamishina yace ko Babu Arman iyalan Saulawa Sun Gama yimai komai arayuwa Ballatana ga Arman a Tsakani,In suka samu Hutu Zaina ta kan matsa ma Zain sai ya saka Direba yakai Arman kano yayi musu Hutu Tun Arman yana kin Zuwa Saboda ya saba dasu Anun Har ya Fara sakin Jiki sai dai Har yau har gobe ba wanda ya Taba gayamai ba Zaina bace Uwarsa kawai An nuna mai Kanon ma gidan yan"uwane.
Bangaran Zakiya kuwa Ashe Koda ta koma Gida Mallam Nuhu bai karbeta ba sai Da ta gama Gayamai Abubuwan da suka Faru da ita yace Shine Daidai ya Koreta yace badai Gidansa ba Ta kara gaba Tana kuka Tana Komai ta Tafi Bata da wajen zuwa Dole Tatafi Minjibir Dangin Mahaifiyarta suma Duk wanda yaji Tana da kanjamau sai ya gujeta Dakyar wacce suke Uba Daya da mamarta Uwani Ta bata Faka ammh ita ke aikatau Tana ci da kanta Ta Haihu Y'a mace Yarinya ba inda ta bar Ubanta ko Ragon suna ba"a yankamata ba Taci Sunan Siyama Yarinyar Tun Haihuwarta Take Cikin Rayuwar Talauci da Wahala Zakiya Ta kara Lalacewa ta Jeme,Ciwo na neman ya kwantar da ita Dole ta Fara Zuwa Cikin Kano Tana karban mgani abangaran masu irin Cutarsu,Bata san Dina ta Rasu ba sai da akafi shekara Lokacin da Sahura Kanwarta Tazo garin Dayake yar Mijinta nan take aure Shine da Tazo suka Hadu Take gayamata Dina Ta Rasu samira Mahaifiyarsu Ta Hadu Da Hajiya Batula Take gayamata Ta Rasu bata ma Haifi Cikin jikinta ba Zakiya Taji wannan Mutuwar sai da ta kusa Tayi Hauka Tana Tuna Rabuwar da sukayi Da Dina Ashe da gaske ne Rabuwar Karshe sukayi Mutuwar Dina ta kara Saka Zakiya Ta kara Jin Nadama ta kara Shiganta Tayi kuka Har taba Uku Lada Tana Fatan Allah ya Jikan Dina ita gashinan Tana Girban nata sakamakon yau ita ke Rayuwa a kauye Cikin Kazantattaciyar Rayuwa da kuma Cutar Dake jikinta ga kuma Siyama wacce kullum Take Kallonta Tana kukan Bakincikin Damfaranta da Ja'afar yayi.
Tuni Shashen da Dina ta zauna da Sadiq zai yi aure ya Saka aka Bugemai wajen aka karamai Fadi da kuma girma ya gyara Shashen Aka saka Zulaihat anan Su Umma da Nene kuwa Farinciki ya Dabaibayesu Kowani Buri nasu ya cika Jikoki sun Fara Dabai bayesu Hakama Tsoho mai Ran karfe Alhaji Tsoho Yana nan Da lafiyarsa sai dai Rashin Lafiyan kafarsa kawai Haka Hajiya Mama Burinsu ya gama Cika ya"yansu suna Da Hadin kai suma Jikokinsu da Tattaba kunnuwansu suna na alfahari dasu ta kowani Fanni Cigaban Rayuwa ya Dabaibaye wannan ahalin.
******
Zaina Ta koma makaranta Tayi Degree dinta sai dai Su Laila sun Tsere mata itama Har Masters Tayi ya"yanta Uku,gwanin Ban Sha"awa.
Zaina Ta cika alkawarin Data Daukar ma Dina ta Rike Arman kamar Dan Data Haifa kuma ba wanda zai gansa yace ba ita Ta Haifesa ba zaina naji da Arman tana Sonsa Duk wanda ya Tabasa zai ga Bacin Ranta Harta dasu Anun kuwa Kowa jinjinama Zaina yake ganin yadda Tamaida Arman Dan gata Dan gaban goshi.
An sakasu makaranta Shi da su Anun Kaltume na nan Tare Dasu Ta gama Secondary School Har ta Fara Fce,Batayi Aure ba Tana Tare da Zaina Tana Tayata Kula da yara ga Aira ga Hajiya karama Zain kuma Asibiti Saulawa yanzu ya Bunkasa ba kamar da ba yanzu a Nageria ana ji da asibitin Sosai Suna yawan Samun katin gayyata Daga Manyan asibitoci shi da Haddir Basu Zaune Waje Daya Sai suyi Sati Biyu basu Gida Suna Chan wajen Karban gayyata Domin kara ma Juna sani.
A wannan Satin ma Zain wani asibiti ya karban ma gayyata Dake Ilorin Yaje yayi sati Daya ya Dawo a gajiye Tunda ya Dawo Yake barcin gajiya Dakyar ya Tashi ya iya Sallan Asuba ko Massalaci bai je ba agida yayita Ya koma ya kwanta Ya Kamkame Zaina ita kuma Bata jin Dadin Haka Domin yanzun Bata samun Lokacinsa Sosai Saboda Baya Zama.
Karfe 7am na Safe Zaina Tatashi Kitchen ta shiga Domin Samar da Abun kari Asabar ba makaranta Boko sai da Hadda da Zasu Tafi Hajiya karama kuma Gidan Su Umma zata kaita yau Tana son samun Zama da Mijinta sosai ko Ta gayamai albishir Dake Cin Ranta Tun Satin Daya wuce.
Dankali Ta soya musu da kwai Sai tace su sha Complex da Madara Dakin yaran Ta wuce Domin Taji Hayaniyarsu Kaltume nata Fama Dasu Tana shiga Aira ta Rugo da gudu Ta Rumgumeta Tana Fadin"Gud Mrning Mommy.."Dagata Zaina Tayi Tana Fadin"Mrning my Swt Dota Kin tashi Lafiya..?
Tafada Tana Shafa kumatunta Aira Ta bangale Baki wacce ke Tsananin kama da Zafeera Tana Dariya Kaltume na Shirya Anan Tana Ta Tura baki Anun na gefe Tana Dariya Zaina ta karisa Shigowa Dakin Tana kallon Anan Data bata rai Cikin Mamaki Take Fadin"Ah kaltume me ya samu Anan din Daddy ne naga Tana bata rai..?
Tafada Lokaci Daya Tana Sauke Aira Daga kan Jikinta Kafin Kaltume Tayi mgana Arman Dake gefe Sanye da kayan Hadda yace"Gud Mrning Mommah.."Zaina Ta Dago Tana kallonsa Hannuwanta ta Bude mai Ya Taho da Sauri ya Fada Ta Rumgumeshi Tana Fadin"Mrning My Swt son Ka tsshi lafiya..? Yana Mirmishi kamar Zain yace"Lafiya lau Mommah Ina Daddy..?
Zaina Tace Tana Shafa kansa "Daddy Yana barci bai Tashi ba Son.."Kai ya gyada Mata yana kara kwanciya kan Jikinta sai Ta shafa kansa Tana Mirmishi Taji yace"I Love u Mommah.."Cikin Kaunarsa tace"Love u too Son..Allah yayi maka albarka.."ya amsa da Ameen Shida Kaltume Tana Dariya ganin Haka yasa Aira ma Ta Rumgume Zaina da Arman Tana Fadin"I Love u Mommah.."Sai Zaina Ta Fara Dariya Kaltume Ta Dago Tana Fadin"Mommy wai fa Saboda nace Anan ta Tsaya na Shiryata Shine take wannan bata ran Anun kuma na mata Dariya...'
Zaina Tace"Kyaleta Ki Gyara Min Diyata Hajiya Yanzu In su Arman zasu Tafi Hadda Ki bisu ku sauka Gidan su Umma anjuma zamu shigo Nida Daddynsu.."Ta Fada Tana kallon Hajiya karama Dake ta Tsalle Tana wasa da kayan wasa akan gado ba ta wuce Shekara Daya da Rabi ba sai Lokacin da Ta lura da Zaina ai kuwa Ta Tako Zuwa Gareta Ta saki su Arman TaDauketa Tana Dagata sama Ita kuma Tana Dariya Sai Lokacin Anan ta saki ta gaishe da Zaina itama Anun ta gaisheta Ta amsa Tana Shafa kansu Tana sska musu albarka Tattarasu Tayi Suka Nufi Falo suka karya Ta bar Kaltume na Shirya Hajiya karama Daman Tayi mata wanka Suna Cikin karyawan sai gata ta Iso Ta gama Shiryawa ita da Hajiya Karama Zaina ta karbeta Ta Bata Nono Itama kuma kaltume ta Zauna tana karyawa Dankalin da kwan Zaina ta saka musu cikin Fulas,Saboda sai 6pm suke tashi Tana Hade da islamiya ne.
Bayan sun gama kaltume Ta Fita da jakunkunansu Zuwa Mota Tunda Zain ya Daukan musu Direba Zai biya dasu Ta Gidan Haddir ya Dauki Zainullahi,Shima nan yake yi zuwa Sukuma yaran suka Shiga Cikin Bedroom dinsu suka Tada Zain wai zasu Mai sallama zaina na su bari su bari suka kiji sai dasuka Tadashi Dole ya mike yabi kowanne da Rumguma da peck kana suka yi musuBye bye suka Fice Hajiya karama kuma Zaina ta Fita Falo Ta mikama Kaltume ita da Jakar Madaranta da ruwanta Tace akai ma su Umma Da Nene Tunda su zama iyayan yara Yanzu Zulaihat takai nata chan Zafeera Takai nata itama Zaina Takai Gidan Abba yanzu ya koma Gidan yara.
Sai da suka Tafi ta Dawo Cikin Bedroom din Ta iske Zain kwance Cikin bargo ammh ba barci yake ba ya Dai Lumshe ido Tana ganin haka Tayi Mirmishi Ta