Author : Jamila Janafty Category : Romantic Hausa Novels
Tunanin Mafita,Washegari kuma Zain ya Tafi Gada Yaje yayi ma Goggo Halima Sallama Da Sha Tara na arziki da zai Tafi ita kuka Shi kuka yana Rokonta kada ta gaza wajen yin addu"an Allah ya bayyanamai Firstlove Shima Dagachan In Lokacin Zuwa saudiya yayi zai biya ya Tafi yaje gaban Ka"aba ya Roki Allah ya Bayyanamai Firstlove.
Kwana Yayi a Dakin Goggo Halima suna Hira Sai da suka kusa Raba Dare daman kuma Tsakanin Goggo Halima da Zain sai Allah tana ta yimai Nasihan Hakuri da Rayuwa Dangin su Zaina kuwa sai zuwa gaidashi suke Tare kuma da Fatan Allah ya Bayyana Halima Koda ya Dawo garin bai Zauna ba Shirin Tafiya yake tayi Dina kuwa batama san Baya nan ba abakin Nene take jin Zain din yaje Gada Dangin Su Zaina sai taji ta kara Raina kanta Lalle ga Maganar Zakiya Datace kada Tayi murna don Zaina ta bace gwara aganta akan ace ba"a ganta ba Gashi kuma Tagani Tatafi da duka Rayuwar Zain Dana Ahalinsa.
Zainab Ta Tambaya yaushe Zain zai tafi ita kuma ta gayamata Gobe Tashin Dare zai yi ammh ta Abuja Zai tashi so Gobe Haddir zai Rakasa Abujan yaga Tashinsu kana sai ya Dawo Tunda Taji haka sai hankalinta ya Kara Tashi ta koma Daki Tana wani Tunani Har ta dauko Waya Zata kira Zakiya wata Zuciyar Ta Hanata da Tunanin In ta Kirata Duk Wulakancin Dayayi mata ita ta Siya da kudinta Dole ta fasa sai Chan wani Tunani ya Fado mata taji ta yadda da Shawaran da Zuciyarta ta bata.
Da Daddare ta Rubuta sako acikin Takarda ta aiki Direban Abba zuwa wani Babban Chemist ya Siyo mata Tana Kofar Shashensu kada ma ya Dawo Wani ya Tareshi ya karba mganin asirinta ya Tonu Duk da in ba Likita ba ba wanda zai san wani irin mgani ne Cikin lokaci sai gashi ya Dawo ta Karba da Sauri ta Shiga Ciki Daman arman na Wajen Zainab kai Tsaye Kitchen ta Shiga ta Samu Lemu Coke wanda Zain kesha Daman shi yake ijiyarsu Guda 3 ne ta kwashe Biyun Ta Dauki Dayan zuwa Cikin Bedroom dinta Ta Fasa kwalbar mganin ta Samu Sirijin Ta Zuka aciki Ta Tsira Cikin Lemon sai da yagama Shigewa tsab kana Ta saki Mirmishi Goge komai tayi ba wanda zai gane an saka wani abu ta maidashi Cikin fridge din Sauran 2 kuma ta Sakasu Karkashin Gadonta,Sirinjin kuma da kwalban mganin Ta Kullesu Cikin wata bakar Leda ta Tusa Cikin Wardrope dinta Yadda ba wanda zai gane akwai wani abu awajen.
Da Sauri ta Shige Tiolet Tana wanka Zuciyarta Cike da Farinciki yau ko Zain naso ko Bayaso sai wani abu ya Shiga Tsakaninsu,Tana Cikin yin wanka Taji Shigowar Zain Shashen nasu daidai Lokacin ana Kiran Sallar Isha"i Tana Cikin Bayin Tayi Dariyan mugunta Koda ta Fito sai taji Motsin Fitarsa aranta ta saka Kila masallaci Zashi.
Zain Daga masallaci Shashensu Umma ya Biya ya gaishesu Yaga Arman bayan Nene yana barci Abunsa Da ya nemi ya Tafi Dashi kamar Nene ta san wani abu Tace ya barshi Tunda yana Barci ne Haka yayi musu sallama ya Fice.
Yana Shiga Direct Kitchen ya Shiga ya Bude Fridge abun ya bashi mamaki ganin Coke Dinsa ya Rage saura Daya Alhalin yasan Dina bata Sha bai Tsaya bama mamakinsa muhimmanci ba Ya Dauki Dayan Daya gani ya Hada da karamin Kofi Zuwa Falo kan Daya Daga Cikin Kujerun Falon ya Zauna ya Bude Lemon ya Tsiyaya ya kafa kai yasha Dina Dake leke ta Daka Tsalle alamun Murna Tarkonta ya kama kurciya.
Cikin Bedroom dinta ta koma Tana Mirmishi Ta Fara Shiryawa Cikin Farinciki da Jinjina ma kanta yadda Lokaci Daya Tunaninta yayi aiki Sai da ta Gogama kowami Lungu na Jikinta Turaren kamshi Wanda Dan Sudane Hajiya maimuna Tazo mata dashi kana ta Dauki Wata arniyar Rigar Barci Sabuwa ce Cikin Wanda Tazo Dashi Tundaga Gida ne bata taba Sata ba Mai kalan ja mai Budadden gaba pant kadai ta saka bata Saka bra ba Nonuwanta da suka Cika da Ruwa sukayi wani Luhu Luhu suna wani kyalli Ta gyara gashinta Tayi mai parking mai kyau ta koma Gefen gado ta Zauna Tana auna Iya Lokacin da mganin Zai game Jikin Zain sai ta Fita Lokacin Tasan bashi da wata mafita.
Munti Talatin Tayi tana Jiran kafin ta Fito Daga Cikin Bedroom dinta Tana wani Takun Isa Daga kofarDakinta ta Tsaya Tana kallon Zain Daya Durkushe Dafe da Cikinsa sai Hada Zufa yake Dariyan Farinciki ya kamata Ta Fara Taku Zuwa garesa Kamshinta na Tunkaransa Kamar almara haka Zain ya dago kansa yana Bin Dina da wani Kallo wanda ya kasa gane wani Hali yake Ciki..? Ya tabbata wannan yanayin Dayake ji ayanzu Rabonsa Dayajisa har ya manta Tun Bayan Tabarbarewan komai kuma ma bai Taba jin irin wannan yanayin ba yana ji in bai yi ba zai iya mutuwa.
Shidai Dishi Dishi ma yake gani Yadai ga sanda Dina ta iso Gareshi Ta Tallafeshi Tana mgana bai ma Fahimtar me take Fada,Shi dai yaga Ta Tallefeshi Sun Shiga Bedroom dinsa Daganan bazai iya Dora komai ba Domin Komai Daya Faru ba Cikin Hayyacinsa bane Domin Gushewar Tunani ya kamashi Daya kasa Fassara abunda ya Faru.
Shi dai ya Farka 6am na Safe ya gansa kwance kan gado Tare da Dina suna Barci sai Lokacin Komai ya Fara Dawomai Daki Daki bai Nemi amsan Kowa ba ganin Dina ba kaya Lullube Cikin Blanket da kuma yanayin Daya ga kansa da kuma abubuwan da suka Faru Jiya suka Fara Dawomai Ya gane Dina ce ta Sakashi Cikin Tarko Ko bai sani ba Shi Likita ne Tabbas kwaya ta sakamai a lemo yasha Domin Komai ya Faru Tsakaninsu Duk da yayi Bakinciki Kara Zama Daya da Dina ammh kuma bashi da ta Cewa Tunda shi Mijinta ne kuma Tana da Hakki akansa Gashi kuma yana Shirin Barim kasar kansa ya Dafe ya tashi ya Shiga Tiolet yayi wanka Tsarki Dana Sabulu yanayi yana Tunanin Zainarsa da kuma Irin yadda Dina ta iya Sakamai mganin Karfin Sha"awa Cikin Lemon shansa Lalle ashe bata Saduda ba Iskancinta na nan..
Ya Dade kafin ya Fito ya Fito Daure Towel ya ganta Ta tashi Zaune Tana kuka Ko kallonta bai yi ba ya Dauki kayansa ya Koma Cikin Tiolet din ya Zura ya zo ya saka Darduma yayi sallar asubar data Subucemai Ita kuwa Dina Tana kuka ne kukan Bakinciki gashi Dai Burinta ya Cika Komai ya Faru sai dai kuma Tsawon Daranan nan Zain Ambaton Firstlove yake kamar wanda ya Zauce Tayi bakinciki Sosai ta kuma Kara Tsausayama kanta ganin a Ke bancewa Tsakanin Mata da Miji ma Zaina Bata bar Ran Zain ba Lalle ta kara Tabbatar ma kanta wannan kaunar Daga Allah ce.
Har ya idar da Salla bata bar kuka ba Ya Zo ya Fara hada kayansa Cikin karamin akwati Domin karfe 10am zasu bar Bauchi Shida Haddir Zuwa Abuja 7pm na Dare Jirginsa Zai Tashi Zuwa Delhi.
Sai da yaga Abun nata na Iskanci ne kana ya Dago Rai bace bayan ya bar Abunda yake yake Fadin"kukan nan naki yana Cikamin kunni malama..? Yafada yana Kafeta da ido Sai Jikinta yayi sanyi ta kauda kai Cikin Sanyin murya tace"Kayi hakuri.."Karamin Dariya ta kama Zain sai da ya Dara kafin yace'Hakuri..? Sorry for u Self Malama Dina wannan kukan munafuncin naki ba inda Zai kaiki Kinsan dai Ni ina gabanki aharkam Likitancin nan ko..? Karya ne ki Min wayau Malama tashi ki Fitarmin adaki Tunda Abunda kike nema kin samu banga amfanin Zamanki ba..!
Yafada yana Nuna mata Kofa Kunya Duniya ta kama Dina Taji ta Muzanta Cikin Sanyin Jiki ta Mike bayan ta Dunkule Cikin Bargon Jikinta Tunda bata da kaya Rigar barcinta bata ganta ba Ta gabansa ta Wuce tana wani Rangaji Da Tsaki ya Rakata Kawai har ta Fice ya Cigaba da Hada kayansa Cikin Kunar rai yana gamawa ya Fice Zuwa Shashensu Umma Chan ya karya ya iske har Nene tayi ma Arman wanka ta Shiryasa tana Fadin bai yi Rigima ba Sau daya ya Tashi Cikin Dare tana bashi Madara yasha ya koma Barci.
Dina kuwa Tana wanka Tana kuka Tana Tunanin tayi aikin Burni Inji Tusa Ta gama Hada Duka plan dinta ya Fashe da ita Ina amfanin Abun kunya Mijinka ma sai ka Gusar mai da Hankali Zai kusance ka kuma Daga karshe ya gamo ka.? Bata Taba Zton Haka ake Jin kunya ba Daga Ranar da Zakiya ta Kira Daddy da kwarto sai yau Dakyar tayi Sallar Asuba Komai bata saka acikinta ba ta koma ta kwanta Tana kukan Wannan Abun Bakinciki.
Tana Kwance sai ga Zainab Tazo Cikin Shirinta ma na Tafiya makaranta ne tace Ta fito bata san Yau Ya Dakta zai Tafi ba suna Haraban gida dasu Umma Dole ta Mike tana mamakin Tayi Nisan Tunanin Tunda bata ji Shigowar Zain ba Da Sauri Ta Zari mayafinta da Takalmi Tabi bayan Zainab Dukansu Gidan a Haraban Gidan ta gansu har da Abba Sadiq da Haddir ne Tsaye Wajen Motar Haddir din Akwatin Zain kuma Tuni aka saka Cikin Booth.
Zain na Dauke da Arman suna kara sallama dasu Umma suna ta kwararamai addu"an Samun Abunda yaje nema Nene na Fadin ya Rike addu"a ya kuma kula da kansa Abba ma Haka Shidai sai Mirmishi kawai yake acikin Ransa yasan Fargaban da suke yi kada ya kara Komawa Ruwa Shi kuwa me ya aikeshi..? Ai Ruwan Daya Dake ka shine Ruwa.
Dina na Gefe Tana kallonsu gabadaya ta kasa koda Motsi,Har sai da Zain din ya kariso gabanta ya Mikamata Arman ta saka Hannu ta karba Tana Kauda kanta Cikin Rada yace mata"Zan tafi ki kula da Arman..Sannan ba zan ce Miki ki kula da kanki ba ammh Ki sani Zunubi ne mai Girman yin Zina da Aure..Tunda kikayi iya Yimin Fyade na Tabbata bazaki Zauna haka ba sai dai Ina Gargadimki Da ki kiyaye.."Daga Haka ya Dago yana Mata Mirmishi kamar irin suna Sallaman Masoya Dina kuwa duk sai ta Raina kanta Idanuwanta suka Fara Tara kwallaj da Sauri ta Juya Dauke da Arman ta koma Cikin Gida su Umma suka bita da kallon Tsausayi suna Zaton kukan Tafiyan Zain ne hatta Arman Dake yaro yana waigen Babansa.
Agabansu Umma Zain ya Shiga Mota Haddir ya Shiga suna Dagamai Hannu yana Daga musu suka bar Haraban Gidan Zain shi ya hana Sadiq Zuwa Tunda Haddir din sai gobe zai Dawo Abujan,Asibiti kuma wani Dr.Aliyu zai maye Gurbin Zain har Allah ya Dawo dashi lafiya.
Sai da suka Biya ta Gidan Alhaji Tsoho Zain yayi mai sallama kana suka Dauki Hanya Wajen La"asar suna Abuja Sallah sukayi sukaci Abinci Lokacin Daddyn Abuja ya Dawo nan suka Zauna suna Hira har Sai 6:30pm sai da sukayi sallar mganariba kana Harda Mama Safiya da Hajiya karama suka Dumguma Raka Zain Zuwa Filin Jirgin Nmandi Azikiwe International Airport.
Jiran kadan kawai sukayi aka Fara Kiran Jerin masu Tafiya Zain ne na 4 nan da nan sukayi sallama Bayan Rumgume juna da Haddir ya Dauki kayansa ya Wuce Layin Tantancewa wacce bata Dauki Lokaci ba 7pm da wasu Mintina Jirginsu Zain ya Lula Sararin Samaniya Sai da su Haddir suka ga Tashinsu kana suka Koma Gida Cike da kewa Musamman ma Haddir daya jisa Cikin wata irin kewa na Zain sai dai yana mai Fatan Allah yasa Abunda yaje nema ya Dauke mai Hankaki Daga Damuwa Da Tunane Tunane.
Kwana Daya Shima yayi a Abuja Washegari ya koma Bauchi Cike da kewar Zain
*Naga Sharhinku jiya Sosai kuma Naji Dadin haka..Sai dai Don Allah kada yau ayi kare jini Tsakanin Team Dina da Team Zaina...*
*Shakira...*
8/6/21, 1:28 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B22️⃣2️⃣*
*IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*
"Sai Washegari Zain ya Kira Waya ya sanar ya sauka Lafiya kuma gashi ma a Masaukinsa Daman Ta Internent yayi komai har Muhallin da Zai zauna har ya kamallah karatunsa kuma Dayake Wajen ba bakonsa bane sai komai ya zo mai da Sauki.
Duka Kashe kashen da yayi na Kudi Da Guminsa yayi bai nemi Taimakon Kowa ba,Shiyasa Lokacin nan yaki yarda ya Siya Ma Dina Komai saboda bai yi Ra"ayin haka ba,sai da zai Tafi ne yaga in ya Tafi ya barta haka bai kamata ba ko Domon ita ba Domin Arman Shiyasa ya bar mata Daya Daga Cikin Atm dinsa anan Falo inda Zata gani,Duk da yasan Har yaje ya Dawo Zata Zauna karkarshin Kulawarsu Abba ne ammh a kallah ya Sauke wani Nauyi Dake kansa Tunda ya baro Nageria ya Tattara Dina da Duka Abunda ya Shafeta ya Watsashi Gefe Zaina ce kadai ya yarda Tunaninta yayi mai Kutse Cikin karatunsa.
Dina kuwa Da Tun Tafiyar Zain ta kule kanta adaki Tana kuka yau ko Arman bata bi ta kansa ba Tun yana kuka har ya gaji ya Daina ya Bingire da Barci Gabadaya Sai yanzu take Nadamar Abunda ta aikata gashi Ta kare ba wani Riba sai kunya,Sai Zuwa yammah Ta iya Tashi tayi wanka tayi ma Arman ta Sabashi Zuwa Shashensu Umma Yunwa take ji kuma yanzu ko Ruwan Tea bata iya Dafawa da kanta.
Taci Sa"a tana Shiga ta iske Zainab Ta Dawo makaranta Ta iske abinci ya kare sai ta Dafa Jallop Din Taliya da Kifi Nene tacr ta Zuboma Dina Din Daman Bata wuce Tayi,Arman kuma Umma ta Karbeshi ganin Daga ganinta yana ta Dariya nan Zainab ta Zuboma Dina abinci taci ta Koshi Sai Lokacin Hankalinta ya Dawo Jikinta Sosai,nan tayi Sallar mangariba da Isha"i Kana ta Koma Shashenta ita da Arman.
Sai da ta koma ne ta Lura da Atm din Dake kan Center Table Din da wata karamar Takarda Sai da ta kai Arman Daki kana ta koma Falon ta Dauki Atm din Ta Duba Taga na Zain sai Lokacin ta Duba Takardan.."Ki yi amfani dashi.."Abunda Taga an Rubuta kenan ajiki Wani Mirmishin Takaichi ta saki Domin ita yanzu babu abunda Take Bukata sai Farinciki kuma Ta Rasaahi Ta riga ta sani sai dai bata da yadda Zatayi Ya zama Dole ta Zauna aduk yadda Rayuwa ta zo mata ahakan ma ta Gode ma Allah da iya Abunda ta Shuka take Girba.
Jin Isar sa ma Sai da ta shiga Shashensu Umma Washegari taji Nene na Fadin ya Kirasu yace ya isa Yau da Safe,bata nuna bai yi mgana da ita ba Domin batama da Abun cewa sai dai ta Riga ta yanke ma kanta Hukunci bazata Zauna Bakinciki ya Kasheta Zata Rika Zama wajen su Umma ko bakomai Zata ci takoshi kuma Za"a kular mata da Arman kana Zata Rage zaman kadaici Da kewa Tunda yanzu Duka iyalan Na Saulawa Sun Daina Nuna mata wannan kyamar Ta Tun Farko Saboda Darajan Haihuwan Arman Da yaron ya Shiga Ran Kowa,Da kuma Duba da Kaddaran Samun Armam ne Duk ya kawo Abubuwan da sukayi ta Faruwa..Kuma Bawa bai isa ya Hana Kaddaran Allah ta Faru sai dai addu"a Tana iya Sauya kaddara.
******
*Ina Labarin Zakiya..?*
Zakiya Tuni Ta Zama Amarya Tun bayan Wata ukun da Mallam Nuhu ya saka na Auranta da Ja"afar ya cika Bayan Ta Samu Tsarki Ma"ana jini uku agarin kano aka Daura auran Wanda Mallam Nuhu ya bama Ogan Ja"afar na Gareji Auran Zakiya Shi kuma ya karban ma Ja"afar kan sadaki Naira Dubu Dari...
Zakiya itama Ana Gobe Daurin Auran ta Taho nan kano,Bayan Tagama Duka Shirinta ta Siyar da Gidanta ta Siya wani Babban Gidan Da Sauran kudaden Dake hannunta A anguwan baulu Area anan garin Bauchi Duka Shiryan Shiryan Bikin da Abubuwan da akayi duka na Auran Ko Biyar din Ja"afar bai yi Ciwon kai ba,Zakiya ce tayi komai ita tayi ma kanta Kayan Lefe na gani na Fada,Ita ta Siya ma Ja"afar kayan Fitan angonci da Duka Abun Bukata ita kanta Tasan Kudin Data Dade Tana Tarawa taci Ubansu sai dai bata damu bq Domin Daman Don Ta Mori Rayuwarta ne ta Tarasu yau kuma ga Ranarsu tazo.
Hatta Duka Kayan More Rayuwar Dake gidan ita ta Siya komai saboda Tana so ta Fara Wata Sabuwar Rayuwa Shi kanshi Ja"afar din bayan ta sakarmai komai nata yasan Duka Sirrints,har Banki ta Bude tana Turamai kudi Domin nashi Hidiman ya zama kamar wani Bawanta ta maidashi wani Dan gata shi kuma sai Susuta yake da Salon Soyayyarsa tana kara jin Tagama yin Dace Duniya da Lahiya.
Abunda ya Faru kuma Tsakaninta Dina kuma Sai da ta bama Ja"afar din Labari ammh bata gayamai gaskiya ba ta Dai Nuna mai Dina tayi mata Butulci Shi kuma ya bata Hakuri Tundaga Lokacin Zakiya taji Dina ta Fita Ranta tana ganin Ta samu Muradin Ranta bata Bukatar Kowa acikin Rayuwarta Shiyasa ta Watsar da ita ta Cigaba da Duka Shirinta.
Dangin Mahaifiyarta Dake Minjibir sun zo Bikin Tunda Mallam Nuhu ya sanar musu Gida kuma Samira da Amarya Luba sunyi gayyah kuma Duka Kannen Zakiya sun zo Ana gobe Daurin Auran ta iso Amotar Haya Motarta ta Barta agida Tunda in za"a kaita Gobe Tashar Mota Zatayi yan"uwanta suje su kaita su Dawo kada ace aurants ya Fita Dabam tazo da Kudi na Hidiman Biki sai dai Mallam Nuhu bai karbi ko Biyar dinta ba Shi yayi Komai Yace Yarsa ce kuma Hakkinsa ne na ya aurar da ita.
Taji Dadim haka Kanta ya kara Girma Kowa sai Tambayan Dina yake musamman kaninta da Suka sansu Tare da Dina sai tayi musu karyan bata kasar ne ita da Mijinta suka Dinga mamakin Daman Dina Tayi aure Zakiya tce musu eh Saboda bata son mganar Dinar sam,Ranar Daurin Aure kuwa Mota Hudu Daga Bauchi Ja"afar da abokansa da Waliyansa Shi dai a Motar da Zakiya data siyamai yazo Shi da wani abokinsa wanda suke aikin Gareji Tare kafin Allah ya Daga Darajansa.
Karfe 11am na Safe aka Daura auran kuma Ba laifi yayi Jama"a Domin Mallam Nuhu ya Raba Goro ko Domin Mutane su daina mao kallon yaki Aurar da Zakiya ya barta Tana Lalacewa sai dai da yawan Mutane sun zo Ne Domin ganin ma idonsu,Kuma sun ga Mijin Zakiya aka koma ana Gulmar ai tama Girmeshi Kila Shima abokin Shashancin nata ne suka Daidaita komai dai menene Tadai yi auran kowa ya Huta.Wasu Daga Cikin Abokan aikinta sun mata kara sun je har kano Daurin Auranta
Tawagar ango da Mutanensa aranar suka koma Bauchi