Chapter 32 Reading Zainazain Book 2 Complete By Janafty Arewa Novels

Zainazain Book 2 Complete By Janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   32 / 37

93K to 96K   out of 108.5K words

PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ...B22️⃣8️⃣*

*IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*


"Dukkansu suka Nufi Falon Abba,Kowa kaga Fuskarsa Cikin Farinciki da Annuri,Suna Shigowa Falon kamshi ya Daki Hancin Zain,Ga kamshin Girkin Ga na Turaran kamshin da suka Turara gidan domin abinci kala kala suka yi Saboda Dawowar Zain din.

Kan Daya Daga Cikin kujerun Falo Zain ya yada Zango Dauke dasu Arman dasu Anun Gabadaya su Umma kuwa zagayesa sukayi Cike da Farinciki wanda ya kara bama Zain mamaki su Anun yake ta kallo suma suna makale Dashi Anan kuwa Lamgwabewa Tayi saman Kirjinsa Kamar tataba ganinsa kalmar da Nene ta Fada Shine Abunda yake mai yawo kuma uwa uba su Anun Daya kasa Dauke Idanuwansa Akansu yana ganin Tsabar kamarsu da Arman sannan kuma Suna mai kama da Firstlove Wanda Zuciyarsa ta Fara rawa nan take.

Cikin Sanyin Jiki ya Dago yana Bin Kowa da kallo kafin ya Sauke kallonsa kan su Farida Cikin Alaman Tambaya da Rashib Sani yace"Umma Naga bakin Fuska baki Mukayi..? Kuma wadandan yaran fa Umma..? Naji Nene tace suje wajen Abbasu kuma ni dai nasan Zareena ba yan Biyu ta Haifa ba kuma Zafeera bata Haihu ba Ballatana nace ya"yanta ne.."

Umma ta saki Mirmishi Farinciki Kafin ta karisa kusa dashi Ta Dafa kan Anun Tana Fadin"Ga Fatima Takwarata Anun kenan sai Maryama Anan Dukkansu ya"yanka ne Zainullahi.."

Mamaki da wani irin Sakewar Zuciya ya samu Zain Cikin mamaki yake kara bin su Anun da kallo kafin ya Dawo da kallonsa kan Umma ya kuma Kara Bin Kowa da kallo ganin Fuskar kowa Cikin Farinciki yasa ya kalli Abba yana Fadin"Abba kaji me Umma tace..? Taya suka zama ya"yana..?

Abba ya gyada kai yana Fadin"Da gaske take Zainullahi..Ya"yanka na wajen Halima ne.."Zain sai yaji kamar Kiftawan mgana Abba yace Halima Idanuwa ya Zaro yana Fadin"Halima...? Wata Haliman Abba...?

Nene ta karbe da Fadin"Wata Halima muke da ita anan gidan kuma Yarona..? Halimar ka Firstlove kamar yadda kake Fadin Ya"yanta ne Daga Cikin Data bar gida dasu..Aisha Farida da Zulaihat suka Taho Dasu.."Ai Nene bata gama Nuna mai su Farida ba Zain ya Mike da Sauri Anun da Anan ya Sauke Arman kuwa sai da ya kusa Faduwa Zainab Tayi Saurin Tareshi kada ya Fadi agaban Farida Zain yaci Burki Kirjinsa na Dukawa kamar zai Faso Rigarsa ya Fito Saboda Fargaba da Rawan Zuciya gaban Farida ya Zube Cikin Rawan Murya Dana Zuciya yake Fadin"Don Allah..Baiwar Allah ki Taimakeni ki gayamin inda Firstlove take..Kada ki gayamin Wata mgana da Zata Nesantani da Firstlove ki gayamin ina kika ganta ina kika ga ya"yana..! ? Don Allah kada ki Fadamin mganar da Zatayi Sanadiyar Rasa Numfashina Gabadaya Domin Saura na ne agabanki Zaina itace Rayuwata itace komai nawa saboda ita Kalli yadda na Dawo Ki Taimakeni ki gayamin koda Labarinta ne ko Zanji Sanyi.."Yafada Idanuwansa na Cikowa da kwallar Fargaba kada ace mai Firstlove bata yau agidan Duniya..

Kowa afalon sai da yaji Tsausayin Zain Dina na gefe Tana Sharan kwallah Farida da Taji kamar tayi kwallah Ta saki Mirmishi kafin tace"insha Allahu Bazan taba gayamaka Abunda zai Saka Numfashinka ya Bar gangan Jikin ka ba..Ka Tashi Tsaye Ba zo garin nan ba sai Tare da Halimarka kuma ayanzu hakama Tana Cikin Gidanan.."

Wani Sakin baki Zain yayi kamar Wawa kamar yana Koyon mgana yace"Tana cikin Gidan nan kuma..? Umma tace"Kwarai da gaske...Halima..Halima Fito Mana.."Tafada da Dan karfi Kowa sai ya Zubama Kofar Dakin Umma ido Harda shi Zain din da Sanyin Jiki yasaka kafafuwansa yin sanyi.

Zaina Dake Kofar Dakin Umma Hawaye ya gama Bata mata Kwalliyarta Tana jin Duk Abubuwan Dake Faruwa a Falo Duk Zakuwarta na Haduwa da Abun Sonta yau taji ta kasa kunya Mai tsanani ya Rufeta da nadaman Tafiya ta barsa,Dakyar take Daga kafa Saboda kasala da Rashin kuzari Taja Kofar Umma ta Fito sai gata ta Bayyana Zain daya kafe wajen da ido kamar Zuciyarsa zata Fito Haka ta Harba Daya ga Zaina ta Fito Wani irin Jim yaji kamar zai Mutu saboda wani Abu Daya shiga Zuciyarsa na Murna da Farinciki.

Kasa Dago kanta Zaina Tayi saboda Kukan Dayaci karfinta Nene ta kalli Zain Dayayi mutuwar Tsaye yana Bin Zaina da kallo Daga sama Har Kasa,Ta Riko Hannunsa Tana Fadin"Yarona ga Halima...Kayi Hakuri ta Dawo Tun last Month..Alhaji Tsoho ya hana agayamaka saboda ka samu Damar karisa Abunda yakai ka..Anun da Anan sune Cikin Da ta bar Gida dashi Farida da Zulaihat suka Rakota Labari ne mai Tsawo sai ka natsa Zakaji Komai.."Shi dai yaji Nene na mgana ammh bazai ce ga Hakikanin me tace ba Shi dai kawai kamar Walkiya sai gashi agaban Zaina wanda bai san yaushe yazo gabanta ba Cikin kallon kamar in na Rufe ido zan Daina ganinki yake mata Ganin Taki kallonsa yasa ya Daga bakinsa yayi masa Nauyi yace

"Firstlove....!.
"Firstlove...! In har kece ki Dago Idanuwanki ki kalleni Dashi kadai zan gane ke nake gani ba Gizon da kika sabamin bane.."

Zaina Dataji kafafuwanta sun Fara rawa Ta Dago Idanuwanta Cikin Zubar hawaye ta saukesu Cikin na Zain cikin wani irin Soyayyah Tsausayi kewa da kuma Muradi da kauna Hade da Zazzafar Kauna mai Zafi da Radadin kewa acikin Zuciya haka suke kallin Juna Zaina Data gama Raunana ta Lamgwabe kai Zain kuma Hannuwansa na rawa ta saka ya Riko Kafadunta yana Fadin"Firstlove Daman zan sake ganinki arayuwata..! Ina kika Tafi kikabar Mahadin Rayuwarki..? Wanda kika san cewa in baki bazan iya Rayuwa ba.."?

Yafada Twagayen Hawayen Farinciki suka Zubomai Zaina Data gama jin kunya da kalaman Zain ta Bude baki Cikin Kuka tana Fadin"Ka...ya..fe...min First...Love...ka..!bata ida mgana ba Yayi jawota Jikinsa da karfi yayi mata wata Rumguma mai Zafi Kamar zai Tsaga Kirjinsa ya sakata itama sai ta ware Hannayenta ta Rumgumesa Ta Fashe da kukan Data ke rikewa Shekara Daya da wani Abu tama manta da Tarin iyayansu Dake wajen haka suka kamkame juna suna kukann Farinciki.

Su Umma Kai kawai suka kauda suna Sharan Hawaye Zafeera kuma Tafi ta Farayi musu Cikin Taruwan Hawaye Tana Fadin"Finally...Yau dai Komai ya kare ga ya Dakta ga Ukti...Allah ya bar wannan kaunar har agidan Aljannah.."Gabadaya kowa ya amsa da Ameen Farida ma Baya ta juya Tana Sharan Hawaye kewa da Son ganin ya"yanta da iyayanta na Damunta Hakana Zulaihat Itama Tana Hawaye Tana Dariyan Farimciki Dina kuwa kukan Tsausayin kanta Take ba wanda ya sani ta samu Ta Sulale Zuwa Shashenta.

Anun da Anan da suka ga Zain da Zaina na kuka sai suka Nufesu sukaje suka Rungume kafafunsu ssuma suka saka kuka atare sai falon ya Dau Dariya Abba na Dariyan Farinciki yace"Sai ku hakura da kukan Tunda ga ya"yanku nan sun Fara suma.."

Nene kuwa baki ta Rike Tana Fadin"oh yaran zamani da wayansu ake haihuwansu ji yara wai sun san iyayannsu na kuka.."Aka saka Dariya kowa kagani Cikin Farinciki atare Zaina da zain suka Duka yana Share mata Hawaye yana kallin yace"Nagode Firstlove...Kin Saka Sunayen da suka Zama Ra"ayina.."Mirmishi ta sakarmai Dukkansu suka Taru suka Rumgume yaran Cikin Tsananin Farinciki Zaina ne ta Hangi Arman na Tsaye yana Kallonsu Kamar zai yi kuka ta Dago kanta Tana Fadin'Taho mana Arman.".
Sai da ta Fada kana kowa ya Lura dashi da gudu kuwa yaisa garesu Shima Zaina ta Hadashi Dashi suka Rumgume sai Zain yaji ya kasa mgana kamar ya Hadiye zaina dasu Anun haka yake ji sun Dade ahaka sai dai Nene tace ya isa haka ya tsshi yazo yaci Abinci Zainab da Zulaihat suka Shiga Kitchen suka Fara Jido Kololin abinci Zafeera kuma ta Shimfida katuwar darduman atsakar Falon Domin Kayattaciyar Walima suka Shirya saboda wannan Ranar.

Zain yana Rike da Hannun Zaina kamar Wani zai kwaceta ko kuma zai waiga yaga bata gani yake kamar mafarki yake wanda baya Fatan ya Farka Daga wannan Mafarkin mai Dadi yana Rike da Anun da Anan kamar zai maidasu Ciki ganin haka yasa Zaina ta Dauki Arman saman Jikinta Duk kunyar su Umma yau nemansa Tayi ta rasa kugu da kugu suka zauna ita da Zain suna Jifan juna da wani kallo wanda su kadai suka bar ma kansu sani.

Ko abincin ma Sama sama Zain yaci yana ta bama su Anun abaki Da Nene taga bayacin Abincin sai tace"Yarona kaci Abinci mana..Kyalesu Anun sun koshi fa.."Zain ya Tsaida kallonsa kan Zaina kafin ya Dawo da kallonsa kan Nene yana Fadin"Neneta don Allah ki gayamin gaskiya Shin da gaske ne gani ga Zainata ko kuwa Dai mafarki nake yi..?

Gabadaya suka sakamai Dariya Harda Zaina Zareena Dake gefensa Ta tsunguleshi Acikinsa sai da yayi yar kara Domin yaji Zafi Cikin Dariya tace"Yanzu ka yarda ba mafarki bane ko Sai na kara maka da mari..? Hararanta yayi yana Fadin"Wazaki mara..?Lalle kuwa da kin gane baki da wayau kuwa gaban ya"yana ki mareni ko ban Rama ba Jalal Son zai Ramin ko yaron Uncle..?

Jalal ya washe baki ya Daga kai Bai san me akace ba ya cika baki da Naman gabadaya aka kara saka Dariya Haddir yace"Ku kyaleshi mafarki ne.."Hararansa yayi yana Fadin"Kai nifa Haushinka nake ji ace Firstlove ta Dawo baka Kirani ka Fadamin ba..? Kafi kowa sanin yadda Na kusa raaa Raina Saboda Rashinta gaskiya baka kyautamin ba.."Umma tace"Umarnin Alhaji Tsoho ne..Baka gashi kaje ka Dawo ba kuma ka sameta ba ni banga Abun Damuwa ba.."

Kallonsa ya maida kan ZAINA itama shi Take kallo Cikin wani irin yanayi ya kara matse Hannunta Har sai da ta motsa Cikin Sanyinsa Ya kai bakinsa kusa da kunnuwanta yana Fadin"Naji ajikina Daman duk inda kike kin kusa Bayyana gareni sai dai yaushe ne bansani ba..Ki yafemin Firstlove ki kuma yarda da so Dayane ke na baiwa shi.."Zain ta Kallesa ido Cikin ido kafin Ta saki Lallausan Mirmishi ita me zatace..? In tace Firstlove baya kaunarta bata mai adalci ba Duk iya Labarin Halin Daya shiga bayan barinta gida sannan Umma da kanta ta bata Labarin da Dina ta Fallasa na kai Zain gidan Boka,ko ba Domin haka ta Riga yanzu ta kara Gogewa daRayuwa ta kuma yardan ma kanta Mace sai da juriya.

Mirmishin Data sakarmai ya kara Narkarmai da Zuciya ya Bude baki zai yi mgana ta Girgizamai kai Tana Fadin"Ba sai kace komai ba Firstlove...na yadda da Duka Abubuwan da suka Faru kaddaran Zuwan Arman Duniya ne ni kuma bazan Taba ja da ikon Allah ba.."Mamakinta ya kara kamashi ya saki baki yana kallonta Abun sai ya bata Dariya Tana Dagowa suka Hada ido da Umma sai Tayi Saurin kauda kai Zain ya Duke yana mata mgana ta Shareshi Sai Lokacin ya ankare dasu Abba ma Karamar Dariya yayi yana Fadin"Dole fa yau su Abba su Dagamin kafa..Shekara Daya Da wani abu cikin na Biyu ban sakaki a idona ba Tabdijam suma sun san akwai mgana..!

Haka dai Taron cin Abincin ya Tashi Cikin Farinciki Zainab da Zulaihat suka kwashe komai suka maida Kitchen kana aka sake komawa saman kujerun Falon aka zauna Wasu kuma suna zaune akasa irinsu Faruq da Zainab da su Saudart Zain ya matsa sai Zaina ta bashi Labarin Inda taje bayan ta bar Gida Tayi tayi ya bari sai gobe yace bai yarda ba Tana kusa Dashi yana Rike da Hannayenta Su Anun na kan Jikinsa Itama Arman na kan Jikinta har yayi barci ba wanda bai ji Zaina Ta Burgeshi ba ganin yadda bata Bambamta Arman dasu Anun.
Zaina ta Fara bama Zain Labarin Barinta gida Tundaga Fitarta Haduwa da Farida da duk Abubuwan da suka Faru Zulaihat kuma ta karesheu da bashi Labarin Shafsson da Suby Zain kafin ma su gama ya Fara Huci Cikin Zafin zuciya da Kishi yace"Allah ya soshi..Daya kuskura ya Tabamin Mata wlh da sai na saka duka an karar da Danginsu Wlh.."Kunya ya kama su Umma Haddir ne ya Dakeshi a Kafada yana Fadin"Ko kunyan su Abba babu..? Sai Lokacin ya Fara sosa kai yana Dariya su Anun ya Sauke ya mikama Umma Anan don Har ta Fara Barci ya nufi inda Farida ke Zaune ya zauna Kamar me Neman gafara yafara Fadin"Nagode sosai Antynmu..Allah ya saka Miki da alheri kin Daukin Nauyin da Nine ya kamata na Dauka yadda kika kularmin da Zainata da ya"yana Allah ya kula dake da Duka ahalinki Aranar Gobe kiyama Allah yayi Miki sakamako da Gidan Aljannah Bakina yayi kadan Wajen Gode miki Sai dai nayi Fatan ki gama da Duniya Lafiya.."Kowa ya rika amsawa da Ameen Idanuwan Farida suka kawo kwallah Cikin Mirmishinta kamar kullum Tace"Bakomai Wlh..Sa'adiya kamar kanwa take gareni kuma Sanadinta yau duka mun zama Daya.."

Zain yace"Wlh Hakane..Ina Fatan nima Zan zama kaninki Ki zama Antyna bawai Firslove bace kawai zata rika kiranki da Anty Farida ba.."Yafada Cikin Zolaya Farida tace"A"a Anty Aisha Farida duka naku Duka Ban fa kada ku kwacema su Anun Antysu.."Gabadaya su Umma suka saka Dariya saboda yadda Ta Fadi mganar Shima Zain sai da ya Dara gaban Zulaihat ya koma ya zauna yana kallonta itama kuma sai Tayi Saurin sadda kai Cikin jin Nauyinsa Cikin Sanyin murya yace"Zaki min alfarman na zama yayanki ke kuma ki zama kanwata..?

Falon sai ya Dau Shuru Zulaihat Ta Dago Cikin Taruwan kwallah tace"Me zai hana..? Ni da na rasa kowani gata ahakan ma ina Daukan kaina kamar mai Cikakkiyar yanci ne zama na acikin Dangin Sa"adiya.."Hawayenta suka Zubi Sharr Zain ya saka Hannuwansa ya Share mata yana Fadin"Kin Daina kukan Maraici da Rashin gata Daga yau..Ni zan zame miki yaya Umma ta zame miki uwa ita Da Nene Alhaji Tsoho da Hajiya Mama su zame miki kakani Abba kuma ya zame miki Uba su Faruq su zame miki yan"uwa da Yardan Allah.."Zulaihat da Farinciki ya saka ta saka Abba ya gyada kai yana Fadin"Da yardan Allah kuwa kidaina kuka..Zamu kai kije garinku Ko domin sanin kina Raye ammh Tun kafin Zain ya Furta munyi mgana zaki zauna Tare damu da Alhaji Tsoho.."Kowa yaji wannan Mgnar Musamman ma Zaina da Farida da suka Tashisuka Rumgumeta suma kamar su saka kukam Nene ce ta lura Tundazu ba Dina awajen yasa tace'Wai ni kam Jama"a ina Dina take...?

Zainab tace"Ta koma Shashenta Tun Dazu.."Kowa sai yaji ba Dadi Abba ya kalli Zain yana Fadin"Ka tashi ka karisa Shashenka Zainullahi..Ko bakomai matarkace tana da Hakki akanka kuma ka barta Wata Takwas Tana zaman Jiranka Tashi Kaje.."Zain dayaji kalamam Abba kamar Darma ya samai Cikin Firgici yace"Abba tare da Zaina zamu tafi ammh ko..?

Abba ya Girgiza kai yace"A"a kaje Wajen Matarka Daman ai iyayanka sunje chan gidan naku sun gyara komai Zuwa jibi Zasu rakata ita Sa"adiyan gidanta Kaga in mukayi haka Allah bazai kama mu da Rashin Adalci ba.."
Nene tace"Tabbas..Kayi Hakuri yarona tashi kaje..Kada damu da Sa"adiya ita Ta fahimcemu.."Zain Dayaji kamar yayi kuka yama kasa mgana Abba ya mike ya wuce Shashensa Haddir kuwa Dariya ce ta kusa kamashi Shima ya mike yana Fadin Zafeera tazo su Tafi Mikewa tayi tana yi ma su Umma sallama Tana kallon Zaina Wacce ta marairaice Tana kallon Zain da Bacin rai suka bayyana saman Fuskarsa,Basu musu mgana ba suka wuce bayan sun yi ma su Farida sallama.

Zulaihat da Zainab suka Dauki su Anun Nene ta Dauki Arman zuwa Dakinta Umma tabi bayan Abba Sadiq da Faruq kowanne ya mike suka Zuwa dakinsa Zareena ta Tashi ta Dauki Jalal da yafara barci su Saurdat kuma Nene ta tafi dasu Dakinta Lillte Umma na Hannun Farida ne Falon ya watse aka bar Zain da Zaina suna zaune suna kallon Juna.

Ganin yadda Bacin ransa ya bayyana ne yasa ta Marairace Tana Fadin"Haba mana Firstlove kayi hakuri Ka tashi ka Tafi..Ban Dade da Dawowa ba tafini hakki akanka.."Zain Daya ji kamar zaina ta watsa mai Ruwan zafi ne ya Dago a Zafafe yana kallonta kafin yace"Is ook..Daman Dake aka Hada baki ko..? Ta ina tafiki Hakki akaina Shekara nawa Bamu ga juna ba yau din ma baza abarni naji Dumin ki Ba Zainata kin ga anyi min adalci kenan..?
Yadda yake mganar ya kara Raunanata wani sonsa da kaunarsa yana Ratsata ita kanta karfin Hali take ammh Tana Bukatar Mijinta akusa da ita Cikin Tsausayinsa ta Dora kanta sanan Kafadarsa Tana Fadin"Am sorry...Kayi hakuri kaji Firstlove dina mukayi hakurin wadannan Wattanin ballatana Hakurin kwana Biyu..? Bai mata mgana ba illah Kanta Daya Daga ya Mike Daman kayansa Chan Shashen Dina Aka shiga dashi Tana ganin haka tasan Ransa ya baci Tana Mikewa Ta Rumgumesa kamkam ta baya atare suka Sauke Numfashi Sun fi Minti Biyar ahaka kafin ta sakeshi gabansa tazo tayi Dage ta sakarmai Sumba mai Tsawo kafin tace"Sai da safe Firstlve..Ka kularmin da kanka kaji ko..?

Baisan Sadda ya Daga Mata kai Mirmishi ta sakarmai ta wuce Zuwa Dakinsu ya Bita da wani irin Kallo ta san yana kallonta Shiyasa take wani kara Juyamai har ta Shige yana kallonta Kamar wani gaula kafin ya girgiza kai ba Haka rai yaso ba ya Fita Zuwa Shashensu

Abun mamaki yana Shiga yaga Dina zaune afalo ganinsa yasa Tayi mamaki Domin bata saka Ran ganinsa ba,Kallo Daya yayi mata ya Kauda kai ya kama Hanyar Dakinsa sai yaji muryanta Tana Fadin"Ina tayaka Murnan Dawowar Zaina.
"Cak ya tsaya Lokaci Daya yana waigowa Cikin Mirmishin Da Tun da sukayi aure bai taba yi mata ba Taga yace mata,"Nagode..."Daga haka ya Tura Kofa ya Shiga Dakin ya kullo Tabishi da kallon so da kauna da kuma Tsausayin kanta Ksfin Ta Kada kai ta Shige Bedroom Dinta Tana Daure Abunda Taji acikin Ranta,Shi kuwa zain ranar bai iya barci ba kwana yayi yana Sallar Godiya ga Allah daya bayyana Masa Firstlove dinsa washegari kuwa Daga sallar asuba ya Nufo Shashensu Umma Har Dakin su Zaina ya iskesu ita da Zulaihat da Zainab Zaina tana barci su kuma suka Fice suka barsa Sai dai Tana Barci Tajita Cikin Jikin mutum Tana Farkawa ta ganshi bata isa ta hanashi Abunda Ranshi ya Rayamai ba Ta Biye Mishi suka Maimata Abunda suka Dade basu yi ba koda bai mata komai ba ammu ya yi Romamcing dinta Sosai

Anan yayi Breakfast dinsa duk kuwa da Koran dasu Nene sukayi mai yaki Tafiya yana nakike da Zaina da su Anun sai Wajen goma ya tafi yayi wanka yazo yaje Zaina tazo ta rakashi Gidan Alhaji Tsoho Umma ta Hana Dole ya Tafi dasu Anun da Arman chan din ma Nasiha Sosai su kayi ma Wannan karon bakinsa har kunni Shi kan

32 / 37