Chapter 8 Reading Zainazain Book 2 Complete By Janafty Arewa Novels

Zainazain Book 2 Complete By Janafty

Author :  Jamila Janafty Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   8 / 37

21K to 24K   out of 108.5K words

Dashi Bai wuce sau Daya ba Gaskiya Shima a Family House dinsu Abba Lokacin ma Tun kafin ya Tafi Kano ne kuma afizge ta gansa,ammh yanzu Data gansa taga ya kara Girma kyansa ya Fito Da Zatinsa da Haibansa Hade da Duka kwarjinsa,In ka gansa Alokacin sai ka kara Kallonsu Domin Duk inda ake Neman gaye mai kyau da Haiba aka samu Musbahu anzo karshe,Gashi Miskili mara son Hayaniya.

Tun daga Lokacin sai Zubaida ta Fara Shigemai da sunan Zai Dinga koyamata karatu Mkaranta Tun yana Basar da ita har yazo yana Dan Kulata Darajan Baffa Haruna ammh Shi kanshi Bayason Tana yawan Shigemai,Mommy kuwa Tasan komai Tunda Zubaida bata aiwatar da komai sai da Izininta Sai wani Jin Dadi Take Domin Musbahu Namiji ne wanda Ko wace Uwa Zatayi Fatan ya zama Surukinta.

Zubaida Tayi iya Bakin Kokarinta ganin Musbahu Ya Fara Shiga Tarkonta Kuma Tayi Nasara Domin ashekara Dayan Dayayi agidansu suka Shaku Har Musbahu zai zauna yana Hira Sosai da Zubaida suci Abinci Tare har fita suna yi Tare,Lokacin da ya gama Bautar Kasar nezai koma Gida Domin Cuku cukun Dora Masters dinsa wanda ya nuna ma Baffa Haruna Ba aiki yake so ba yanzu Karatunsa zai Dora Da zai koma Gida haka Zubaida ta Dinga kuka kada ya Tafi a kuma Lokacin ne ta Furtamai kalmar Tana Sonsa Duk da alokacin ba wani Sonta yake ba sosai ammh Yana Sonta kuma tana Burgeshi Sai ya karba mata Tayin Soyayyarsa ammh Da Sharadin bazasu bayyana ma Iyayansu ba sai da Ta gama Sakandiri School dinsa Shima Lokacin ya gama Masters dinsa.

Da haka sukayi Shuru da bakinsa har Musabahu ya koma Gidan Goggo Fatu Suna Cigaba da Soyayyarsu Da Zubaida ta Waya Batare da Goggo Fatu ta sani ba,sai bayan ya Koma BUK kano ne Yin Masters dinsa Mganar ta Fita Kuma Mommy ce ta Fitar da ita Tana wani Fi"ili ga sauran Matan Baffa Haruna Tana fadin Zubaida Zata Auri Musabahu ai hakan ya kamata Tunda Ai shi Baffan Haruna shi yayi ta Wahala da Musbahu gwara Ya auri yarsa Ko ya Famshemai Wahalarsa Mgana Tai ta Zaga Dangi Har tazo Kunnuwan Goggo Fatu ta Bakin Goggo Zaliha wacce Tatako da kanta Tazo Ta Fada mata Abunda ke Faruwa tace Itama abakin Matar Baffa Umaru Taji itama tace wajen Matan Baffa Harunan taji Zencen suka ce Mommy ke Ta Fadin mganar.

Goggo Fatu na Jin haka Ta Daka Tsalle Tace Musbahu bazai Taba Auran Zubaida ba Aisha Farida zai aura gatanan itace Matarsa Tuni na Hanata Kula kowa shi nake ma kamu ammh Ya auri Zubaida sai dai bayan Ranta Goggo Zaliha tace Tana Bayanta Ba Saboda kowa ba sai Saboda Mommy Matar bata da Hali mai kyau Batare da Goggo Fatu ta Jira Kowa ba Ta Kira Musbahu tace yazo Gida Tana nemansa Yana Zuwa ta Zaunar dashi Ta gayamai Wlh sai dai In bata da Rai Zai auro mata Zubaida Ammh ya sani Indai Tana Numfashi Aisha Farida ce Matarsa Baya iya ma Goggo Gaddama ammh yaso ya Nuna mata Zubaidan yake so ba Aisha Farida ba Goggo Fatu Bata Tsaya ma Sauraransa ba Tatashi Ta bashi Waje.

Da Farko yaso ya Hakura ya bi Abunda Mahaifiyarsa ke so sai dai kuma Yana son Zubaida Aisha Farida kuma kanwa ya Dauketa kuma ba Wata Shakuwa atsakaninshi da Ita Damuwa tamai yawa ya kasa Boyema Zubaida ya gayamata Tun da Taji haka ta tashi Hankalinta Tana kuka Tana Komai Tana gayama Mommy Ita kuma Tace Abunda bata yuyuwa kenan ta samu Baffa Haruna Tana gayamai Cewa ga Sakayyar Da Goggo Fatu zata mai Bayan ya gama Gina mata Rayuwar Danta Shine zata ce Bazai Auri Zubaida ba Sai Aisha Farida shi bama san mganar ba sai Lokacin da Farko ya yarda da mganarta ammh da Suka Hadu da Baffa Umaru ya Nusar dashi ya Tuna da Zumunci dake Tsakaninsa da Goggo Fatu Tunda sunyi Jinkiri Basu Furta ma Har Goggon Fatu ta Rigasu Furtawa sai dai Yayi Hakuri Musabahu ya auri Aisha Farida Allah barshi Daga Bayan sai ya Auri Zubaida..

Mgana Tayi Tsamari Domin Zubaida Harda kwanciya asibiti Saboda Damuwa Ni sai alokacin ma naji Labarin Abunda ke Faruwa Nima bani da Tacewa Domin ban iya Tsallake mganar Goggo Fatu,Bayan an sallami Zubaida Family House din su Abba aka Hadu gabadaya Harda Ni da Musbabu da Zubaida Inda Baffa Ya Dinga neman alfarman Goggo Fatu ta yarda ayi auran Mu Dani da Zubaida rana Daya da Musbahu Ganin Halin da Zubaidan ke Ciki Goggo Fatu ta Mike gaban Kowa da kowa tace Wlh sai dai bayan Ranta ammh Da Ranta Musbabu Bai da Wata Mata Face Aisha Farida har yau har Gobe Tana kallon Hoton Abunda Zubaida da uwarta sukayi mata Shi kuma ya Goyi Bayansu Bazata iya Juran ganinta a amtsayin Surukanta ba Tana kuka ta Fice Daga Dakin Jikin Baffa Haruna sai yayi Sanyi Abba na gefe bai saka baki ba ganin Hardani aciki ake mgana Ya Musbahu sai ya Fara mamakin meya faru ne...?

Goggo Zaliha ce Ta zaunar dashi Ta sanar dashi Komai Tundaga Lokacin Yaji Zubaida ta Fitarmai akai Yaji ya Tsaneta Tunda ta Saka Goggo Fatu kuka ya koma Gida ya Roki Goggo Fati gafara ya kuma ce zai aureni Insha Allahu Goggo Fati taji Dadi Tana ta sakamai albarka Musbahu bai yarda ya koma Kano ba sai da ya san yadda yayi Ya Tusamin Sonsa Daman chan yana Burgeni kawai Rashin Samun Fuska ne yanzu kuma da ya nuna ba wata sai Ni,nima sai na saki Jiki na Nuna mai Shi nake so.

Koda ya koma kano Soyayyah Ruwa ruwa ta wayar Goggo Fatu muke waya Koda yaushe sai dai in Yana karatu,Ba"a Saka manq Rana ba Sai da ya Fara Defence dinsa kana aka Tsaida Lokacin Bikin mu in na gama Makaranta nan da Shekara Daya Lokacin ya Musbabu ya gama Karatunsa har ya samu aiki.

Baffa Haruna Sai Lokacin ya Dinga Nadamar Abunda ya aikata su Goggo Zaliha da Baffa Umari suka Goyi Bayan Goggo Fatu Abba ne ma yaje har Gida ya Roki Goggo Fatu ta bari ya auremu Duka tace sai dai in bata Raye Dole ya bar mganar Mommy da Zubaida suna Ji suna gani aka sanya Lokacin Bikina da Musbahu basu da yarda zasu yi ammh Mommy tayi alkawarin ko Zatayi yawo Tsirara Sai Zubaida ta Auri Musbahu Ko da Goggo Fatun Zata Rasa Rayuwarta za"ayi Bayan Ranta kamar yadda tace din.


*Ki biya ki karanta Cikin Salama Mace mai aji bata Jiran Abun Sata mallakan komai nata Take..Rashin Daraja ne ki Siya abu da kudinki ki mai Dashi kamar Gwanjo ko wani Haja Mara Daraja..*






*Janafty....*
7/13/21, 4:34 PM - Aisha Srtr Mt: *ZZ....B20️⃣7️⃣*

*IS NOR FOR FREE...Via Card ₦300 via bank ₦250 0552179550...Jamila Umar Gtb*
              

"Sai da Mommy ta Taso da mganar ai shi yayi ma Musbahun komai har ya kawo yanzu ya kamata shima ya rama mai Abunda yayi mai sai alokacin Baffa Haruna ke Fadama Duka Matansa harda Mommy din Cewa duk Abunda yayi ma Musbahu bada kudinsa bane akwai Dukiyan Musbahun Da Yagada Wajen Mahaifinsa Tunbayan Rasuwarsa Goggo Fatu Ta dankamai komai a Hannunsa Tace tana Bukatar ya cigaba Da Juya Dukiyar har Zuwa Lokacin da Musbahu Zai mallaki Hankalin kansa ya maida mai Dukiyarsa kuma ayanzu Haka cikin kashi Uku na Abunda ya mallaka Kashi Biyu Gadon Musbahu ne kuma Duka yan"uwansa Duk sun sani Tunda agaban Idonsu akayi Domin su Zama Shaida.

Jin haka sai Jikin Mommy yayi sanyi bata kuma da tacewa ammh Hankalinta ya tashi Ganin Halin da Zubaida ke Ciki Ta Rame ta lalace Saboda Rashin Musbabu shiyasa tayi alkawarin ko Zatayi yawo Tsirara ne sai Musbahu ya auri Zubaida Domin ko Ita Bata Nemi Abu ta Rasa ba Haka Zalika ma yarta bazata Taba Neman Abu ta Rasa ba.

Ni kuwa Soyayyah Tsakanina da Ya Musbabu sai wanda ya gani Sai na Fara Tunanin Daman chan muna son Junanmu,kawai Rashin Sakar ma Juna Jiki yasa muka kasa ganewa,Shima haka yace min Ya tabbata ni yake so ba Zubaida ba,Kafin Shekaran Daya da aka Dibamana na Auranmu wata Shakuwa da Soyayyah mai Tsanani ya Shiga Tsakanina Dashi Bana iya Boyemai komai shima haka Goggo Fatu kuwa tafi Kowa Farinciki ganin Mu Hada kanmu yanzu Baya wani Dadewa Karkari yayi sati Biyu a kano zai Dawo Gida Har Gombe Munje Tare Abba da Mami da Anty nata saka mana albarka.

Ana Saura Wata Biyar Bikim mu Ya Musbahu ya kamallah Masters Dinsa ba bata Lokaci Kuma ya samu aiki inda yayi Bautar kasarsa wato Hukumar Wutar Lantarki na Garin Jemeta Dama Tuni suke so su rikesa sai yakizama akan cewa zai koma karo karatu yana gamawa kuma suka Daukesa kuma da Babban Ofishi da kuma albashi mai Tsoka,ganin Bikinmu na gabatowa yasa Goggo Fatu ta Tara Su Abba dasu Baba Umaru da Baffa Haruna tayi mgana kan Dukiyar Musbabu Tace Tunda Nauyi ya hau kansa yanzu Ya kamata Duka Dukiyarsa ta Dawo Hannunsa Ko ya samu yayi wasu Shirye Shirye Cikin Lokaci Baffa Haruna ya gabatar da kudaden da Riban sai Goggo Fatu tace Baffa Haruna ya Raba Riban kashi Uku ya Dauki kashi Daya Ladan Juya Dukiya haka kuwa akayi sauran aka Damkama Musbahu Duka Dukiyarsa Baffanin nashi Kuma suka Bashi Shawaran ya saka Kudin Cikin Banki kafin ya Fara Shawaran Business din da zai yi da Kudade.

Da Kudin Goggo Fatu ta saka ya Musbahu ya gyara Filin Gaban Gidansu ya Fitar da Flat Domin tace nan Take so mu Zauna Kusa da ita ni da Ya Musbahu Nima Da naji haka naji Dadi Domin na saba da Goggo Fatu bana son wani Abu ya Rabamu Cikin Lokaci Flat din ya kamallah Tunda ga kudi 2bedroom ne,da Falo sai Kitchen sai Haraban faka Mota wacce Batafi Biyu ba bai da Girma Bangaran kayan Daki Kuwa Goggo Fatu ta Hana iyayena siyan ko Tsinke Duka Ya Musbahu ta saka ya Siyamin Komai Domin tace Itace Uwata Goggo Zaliha kuma uwar Ya Musbahu.

Biki Yana ta karatowa Shirye Shirye na kara Kamkama Tun Biki na saura kwana uku baki suka Cika Gidan Goggo Fatu Domin Duka Taron nan Za"ayi shi Su Mami da Anty Tun saurab Sati suke Ni kuma ina Tare da Saratu goggo Zaliha da Zahra sune kawaye ne Tunda bani da wasu Tarkacen kawaye,Ya Musbahu kuma yayi gayyah Domin Daga abokan aikinsa har abokan karatunsa Duka Sun zo Tun ana Gobe Biki a Hotel Duka ya Saukesu.

An Daura Min Aure da Ya Musbahu Ranar Wata Jumma"ace 12/05/2018,da Misalim karfe 11am na Safe Inda Baffa Haruna ya zama Waliyin ango Baffa Umaru ya zama Waliyina Muna Cikin Gida Domin Duka Dagamu har iyayanmu nan muka zauna sai ga Labari yazo wai Zubaida ta suma Tana asibiti Bayan Taji an Daura aurena Da Ya Musbahu Daman Mommy da Zubaida basu zo Gidan Bikin ba,kuma ba Wanda ya Damu sai dai Sauran Kishoyoyin Mommy din ne suka zo.

Saratu ke gayamin yadda Zubaidan ta Rame ta lalace Saboda Rashin Auran ya Musbahu alokacin matuka ta bani Tsausayi Tunda Daman shi da Kanshi ya gayamin Tana Kiransa Da Lambobi Da Dama Baya Daukan wayanta Tunda ya gayamata Tayi Hakuri bazai iya auranta ba ni zai aura Nidai Allah ya kyauta kawai na iya Cewa Aranar Goggo Fatu da Hannunta takaini Har kan Gadon Aurena Ta Dafa kaina Tamin Nasiha ta sakamin albarka Ta kuma Hada Hannayena da Hannun ya Musbahu tace ko Bayan Ranta bata yarda mu Raba Hannayenmu ba Ranar nayi kuka Sosai Domin naji Daci da Ciwon Rabuwa da kwana da Goggo Fatu wacce nake gani Tankar Uwar da ta Haifeni Duka Iyayena sunmin Nasihan zaman Aure da kuma Hakuri Zuwa Washegari kuma Biki ya Tashi Kowa ya koma Gidansa aka barni Daga ni sai Goggo Fatu Dake Chan Barayinta Sai dai akwai Kofa ta Gidana Inda zai kaini Gidan Goggo Fatu ko Kyakyawan Ihu nayi Zata jini Shiyasa ma sai na kwantar da Hankalina.

Bazan Taba mantawa ba Ranar Litini da Daddare Ya Musbahu ya karbi Budurcina Cikin Soyayyah da kaunar Juna Kuma ya Cigaba da kula dani har na Warke muka Cigaba da zamanmu Gwanin Ban Sha"awa in ya Fita aiki da safe ni kuma nagama Abunda zan yi Shashen Goggo Fatu nake zuwa Musha Hiranmu sai Rana Tayi kana Zata kadani naje na Daura Girki Zamanmu abun Sha"awane Domin na riga na gama yardan ma kaina Ya Musbahu Garkuwata ce kuma Bangona ne Domin Komai na jin Dadin Rayuwa yana Min shi Watan mu Biyu da aure muka je gombe muka kwanan musu Biyu Muka je Gidan Goggo Zaliha Har Gidan Baffa Haruna Munje nan ma akace Mommy bata nan ita Da Zubaida suna Adamawa Wajen Danginta,Ban wani Damu ba Tunda ni Daman ba wani Shiri muke da ita ba.

Auran mu da wata Uku na samu Ciki Lokacin ma Ya Musbahu na Shirin maidani makaranta ne Samuwar Ciki ne mai Lailayi Wannan Dalilin yasa Goggo Fatu ta Hana na Shiga wata Makaranta Saboda cikin ya bani Wahala yana karami sai da na koma Wajen Goggo Fatu da kwana Tana kula dani Bayan Haka kuma Zahra sunyi candy Tazo Tana Taimakamin Dalilin Dayasa ma na koma Gidana kenan sai da cikina yakai Wata Hudu Cikin na Biyar kana na Fara Dawowa Daidai Alokacin Kowa ya ganni sai yayi Tunanin Cikina yakai Wata Takwas Mamaki Mutane suke in sukaji Labarin Cikina Iyakarsa Wata Hudu ne.

Cikina nada Wata Shida Goggo Fatu ta kwanta Rashin Lafiya Daga Dare Zuwa safe tatashi Da Laluran sai dai a kwantar a Tayar Wannan Halin Data Shiga Ya Dagamana Hankali Ni da ya Musbabu Wajen Watan ta Biyu asibitin Jaha ammah ba wani Cigaba Mutane suka Dinga bada Shawaran Adawo da ita gida ayi na Hausa bayan an Dawo Gidan an Fara na Gargajiya Shima ba wani Cigaba Domin Goggo Fatu ta Daina mgana sai kawai tabi Mutum Ido Tana kwallah.

Wata Mata aka Samo Ya Musbahu na Biyanta Duk Wata Tana kula da ita Tunda ni gani nayi Nauyi Cikina yayi Girma sosai Su Abba suma ba"a barsu abaya ba Duk inda sukaji wani Taimako Zasu nemo su kawo a Jaraba Babu Wanda bai zo Duba Goggo Fatu ba sai Mommy Da Zubaida wanda ni kaina Sai da nayi mamakinsu ganin Irin Halin Da Goggo Take ciki Ta Daina ma gane wanda ke kanta ammh Mommy Bata Leko ba Duk da ance Ita kadai Ta Dawo Ta bar Zubaida Chan Adamawa wai Saboda ta samu Kwanciyar Hankali na kwana Biyu Shi kuma Baffa Haruna Daman bai da Ta cewa.

Watarana Ranar da bazan Taba Mantawa da ita ba Cikina ya Shiga Wata na Tara Har Lokacin Zahra na Tare dani Alokacin Goggo Fatu tana watanta na Hudu da Rashin Lafiya kenan Ranar wata Jumma"a da misalin 11am na safe na Baro Sasan Goggon kenan Nazo nayi wanka sai ga Zahra tazo da Gudu Tana kuka ta Kirani Cikin Rudewa Nabi Bayanta Ina Zuwa na Iske Matar Dake zama da goggo, Ta saka Hannu Ta Rufe mata ido Tana Jan Mayafi Tana Rufe mata Fuska dashi Ganin haka yasa na Fahimci Goggo Tatafi Sai naji na kasa Tsayuwa da kafafuna Bansan Wani Lokaci naji ni na Kai kasa ba Saboda Jin Marata ta Murda Ina kuka ina Salati Radadin Mutuwar Goggo Fatu yasa Naguda Tatashi Gadangadan Zahra ita ta Kira Ya Musbahu Dasu Abba ta gayamusu kafin kace kwabo Sai gashi Ganin Halin Dani ke Ciki yasa ya kwashemu Zuwa asibiti ga Mutuwar Goggo Fatu ga Halin da nake Ciki Muna asibitin ya Kira Baffa Haruna ya gaya musu Rasuwar goggo Fatu.

Allah Sarki Rayuwa ban iya Haihuwa da kaina ba sai da akayi Min C.S aka ciro Min Ya"ya Guda Biyu Duka mata Ina Kwance gadon asibiti aka Sallaci Goggo Fatu aka kaita makwancinta,nayi kuka kamar Idanuwana zasu makance,nayi kukan Rashin uwa Domin na Tabbata da Tana Raye da yau ban Tsinci kaina Cikin Wannan Rayuwar ba Rasuwar Goggo Fatu ne yasa na Fahimci Itace Gata na kuma itace Garkuwa Gareni.

Ba"a sallameni Daga asibiti ba sai Ranar addu"an bakwai naje na Iske gidan Cike da yan"uwa sai Kukan Mutuwa ta dawo Sabuwa,Dakin Goggo Fatu Anty Yaha ta wuce dani nayi ta kuka Ni da ya Musbahu Domin mun Tabbata Munyi Maraici,Saboda Rasuwar Goggo Fatu yasa Bamu yi wani Suna ba Ya Musbahu yayi ma yaran Huduba da Sunan goggo Fatu da kuma Goggo Zaliha ammh zamu rika Kiransu da Hassana da Usaina.

Saboda Halin Damuwar da muke Ciki,Yasa Gidan basu Watse ba sai Da akayi sati Biyu kana su Mami suka koma Gida Abun mamaki Mommy Tazo Gaisuwa ammh Fuskarta ba alamamun Jimamin Mutuwar na Goggo Fatu sai ma wani Murna Datakeyi ba wanda dai yabi ta kanta,Anty yaha aka barmin Tana Kula dani Duk da Zahra na Tare dani.

Bata Tafi ba sai da mukayi arba"in Ni da su Hassana muka Maida Jikinmu,kana Ta koma Gida,Ta barmu Muna Cigaba da kula da kanmu,Ni da ya Musbahu sai muka koma muka Rungume junanmu Tunda Mun Rasa Goggo Fatu Uwa garemu,Bayan Rasuwar Goggo Fatu ya Shawarci su Abba suka bashi Shawaran ya Fara Sana"ar Motoci Yana Shigowa dasu da wannan Shawaran yayi amfani Ya Fara Sana"ar Shigo da Motoci Daga kwatono yana kawosu nan  yana Saidawa Cikin Shekara Daya sai ga ya Musbahu yayi Fice Yayi kudi na Shahara har ya Bude kamfaninshi na Kanshi,Lokacin su Hassana sun Fara Tafiya Dagani har shi Mun Sauya Rayuwarmu ma ta Sauya Mun bar Gidan nan Ya Musbahu Yagina mana wani Katon Gida mun Koma nan kuma sai ya saka yan Haya Kada abar Gidan Ba kowa,Ya Musbahu ya bani wani Jin Dadin Rayuwa ya Siyamin Motoci ya Budemin Banki Duk wata yana sakamin Kudi Ya maidani yar gata Dani da Iyayena Zahra tana Wajena Ya Sakata Jami"a Ita kuma ya Siyamata Mota Cigaban Rayuwa dai alhamdulillah.

Ana Cikin wannan Halin na Fara Laulayin Ciki kuma alokacin ne Ya Musbahu yazo Min da mganar zai kara aure kuma ba kowa zai aura ba sai Zubaida mganar ta Dakeni kuma naji Zuciyata ta Tsinke Zubaidan Da Nadade ban Ji Labarinta Itce ya Musbahu zai aura Da Farko nayi Boren Ban yarda ba ammh sai Ya Musbahu ya Nuna Ko

8 / 37