DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   100 / 105

297K to 300K   out of 313.1K words

shiga ya kyaleta har yafito yana jin tana faman buge bugen waya bai tsaya kulata ba yake fadin abinci fa ta dago ido tana watsa masa kallo.
Direct ya fita kayan abincin da yagani ya bude akwai saura abincin da na zubawa ibrahin kadan ya diba don yaci abinci a erea 1 da yaje.
Nan shima ya zauna ya dibi yaci ya koshi sai lokacin ya fara tunanen ba girkin Aisha bane wanan don batada time din tsayawa dafa abinci irin haka ai ita.
Ya dan jima zaune kafin ya mike ya nufi kofofin gidan yana rufesu yaje yai muna saida safe ya murda kofan yaja yaji dakin a rufe gam hakan yasa ya juya ya koma dakin su.
Dagashi har ita barci rabi da rabi sukayi a ranan kowa da abinda zuciyarsa yake saka masa kan dan zaman duniya da Allah ya hadamu na dan lokaci kafin a shudemu cikin dan taki wasu kuma su wanzu a bayan mu suma suyi nasu baje kolin idan kayi mai kyau kanka kaiwa idan kayi mara kyau kaga aikin ka tun a duniya Allah yasa mufi karfin zuciyar mu amin.
Washegari kamar yadda na saba tashi a gida haka na fito zuwa kitchen na hada duk wani abinda nake son hadawa a breakfast din mu ranan.
Na rage wuta na dawo falo na gyara tsab kafin na shiga dakunan na tayar dasu laura suyi sallah suna idarwa ta farayiwa yara wanka.
Ni kuma na shirya muna abinci kafin na shiga daki na shirya yarana muka fito falo dukkan mu ina zubawa yaran abinci ya fito daga daki cikin shirinsa.
Daddyna ya fada daga saman step hakan yaran suka sanda fitowanshi suka nufishi da murna yana cabesu daya bayan daya.
Nan ya sauko yana fadin madam kun tashi lafiya hakan yasa na dago ina gaidashi ya amsa a sake.
Tare da fadin ya gajiyan hanya kinyi kokarin biyo hanya da yaran nab meyasa baku shigo jirgiba kuka biyo mota haka dasu ?
Motan yafi min sauki don kayan dake garemu ni zanje office ya fada babu dai matsalan komai ko babu na fada.
Ina mamaki a raina na rashin nuna komai gareni na zuwan mu da baiyi ba ko a fuska sai haba haba da yakeyi da yaran nice ma naki bada fuska da zai samu kafan ya korani cikin wullakanci duk da banga alaman hakan ba a yanzu wajen shi.
Can ya juyo yana fadin za a samun abincin na danci kafin nafita jin hakan yasa na dan kalloshi ina fasin abincin mu iyamu na dafa mawa.
To ki zuba min naki inci in fita sai ki dafa wani hakan nayi na zuba mashi yaci ya fita har waje yaran suka rakashi ya tafi .
Ga karin mamakina dashi ya tafi baifi awa da tafiya ba akai sallama kayan abinci aka shigo muna dashi sai manyan tv guda uku da za,a kafa a dakuna.
Ga matar gidan tunda ta shige bata fito sai bayan na shiga dakine laura tazo tana fada min cewa taga matan nan ta sauko ta debi abinci a falo ta koma daki nace ba ita bace ashe ?
Hauwa na kira ina sheda mata abinda ke faruwa tayi dariya kamar ta sheke tana fadin yarinya kin kuru ai zuma saida wuta in fada maki.
Da shike nan an barki nan har abada an
mayar dake matar kauye saidai kiga anzo ana daga maki kai ki koma yar kallo .
Haka ake tauyewa mata hakki ba gaira ba dalili saboda son kai a tauyewa mace hakkinta a banza kan wani jahilci shi miji bai da dama ya zartanda hukuncin daya dace akan iyalansa uwar miji tace ga yadda ta tsara masa.
Kada ki yarda da wanan tsarin duk nasan da wuya kuma hakan ya kara faruwa don zasuji shakkun yi maki wani barazana akanki kuma a yanzu.
Nan nace da hauwa din tayi mana abinda na sani dai shine ba zan taba yarda inyi gaba da gaba da ita mun har in mata rashin kunya da zaija zubewan mutunci a wajen yayanta ba.
Amna duk sanda ta bullo min ta haka ni kuma zan biyo ta baya na kwantawa kaina inci a cikin ruwan sanyi irin haka.
Mun dauki lokaci muna tautaunawa kafin muyi sallama ina idar da sallah Rukky tashigo munyi murna da ganin juna nan muka zauna na bata labarin yadda tafiyan mu tazo muna tayi dariya sosai itama.
Har take fadin wai nikan Anty zainab Aishan nan ba asiri tayiwa mum ba kuwa nifa kullum ina ganin hakan ?
Haba dai ni ban dauka wai asiri bane dama mum dai tayi amfani da daman tane ta yarda da auren mu da yaya don wani manufarta akaina.
Yanzun kuma taga hakan ba zai yuyu ba shine take ganin hada kai da Aisha a yanzu shine mafita a gareta don ta nuna min kuskurena akanta na rashin yarda da tsarita da banyi ba.
Yanzu ita mum tana ganin hadin kai da wanan matar shine daidai a gareta data zaunar dake ta fada maki shakurwata kafin takai karshe nace No hakan ba zai yuyu ba a yanzu.
Da dai dane zata iya fada min hakan amma yanzu ita tasan hakan ba zai yuyu a gareta ba yasa ta biyo ta wanan hanyan da take ganin shine sauki ta hada kai da Aisha din suna musguna min.
Amma aishi yaya ba zai yarda ba shifa mutum ne mai natsuwa da hangen nesa yasan yadda zai zauna dakai bai shiga hakkin ka ba haka kuma yana kokarin sauke hakkinsa akan kowa na tare dashi ko wani lokaci.
Shine saukina ai don yau da ace wanine bashi ba gargadamu zaiyi mu koma kano nida yaran nan amma kinga saboda hangen nisansa yasa ko a fuska bai nuna min ransa ya baci da zuwan mu nan ba.
Shine saukin ki yaya yanayin sa daya da faruk wajen hakkuri anty ni matsalata yanzu shine wanan yayanasa tasani agaba wallahi har ya gane hakan.
Ance ko wacen marigayiyar matar nasa haka sukai ta kwasa da ita har ana zargin cewa da hannunta cikin mutuwanta .
Nace wata sabuwa wanan kuma matsalan zamu fuskanta a wajen ki yanzu ko shiyasa yaki aure a gida dama yazo kano neman mata ?
Gaskiya haka sukace min wai yana tsoro nema a nan don kowa na tsoron big sister yanzu haka tana nan Abuja tafi sati uku wajen mu.
Wallahi in gari ya waye har tsoron fitowa nake don matar nan kuma dole in fito inyi girki inba haka ba insha masifa a wajenta.
Candi jam wanan yasa nace ki dage da karatunki a yanzu Rukkaiya kingani nan karatuna ba karamin taimako na yayiba a yanzu wallahi.
Wanan na daga cikin abinda yasa nakan dan dagawa yaya kafa sosai Rukky don shine yayi min hanyar karatuna har na zamo haka a yanzu.
Duk abinda zatayi maki yanzu na dan lokacine da zaran taga kafanki ya fara kama kasa ita kanta zataji shakkar yi maki wani abin nan gaba.
Humm anty waiko kinsan big sister wanan matar banjin akwai ranan da zata saduda ta daina wanan halin nata nifa ko bankunta batayi min ba ta fara nuna min halinta .
Nace dake zata bari kiyi hakkuri a yanzu har in gama da case dina mu fara taki kuma don sai munyi da gaske inba haka ba akwai aiki kam gaba ki gaskiya.
Kukan yaron da najine ya hanani cigaba da magana ina kwalawa Laura kira tashigo dauke dashi tana fadin ya fado saman kujerane anty .
Karban yaron nayi ina rarashinsa kafin in dago ina fadin haba Laura kiname har ya fado saman wanan kujera don Allah jifa har bakinsa ya fashe.
Anty dincan ne tace mu sauka saman kujerun naje daukansa shine ta daka muna tsawa yaji tsoro ya fado kasa kafin na daukoshi.
Murmushi nayi da naga Rukky ta kalloni nace neman abinda zamu saida hali takeyi a yanzu ba zance mata komai ba da kansa zaiga hakan ai ya tambaya ince ya tambayi Laura ke kuma saiki fada masa yadda akayi.
Mun kai wani lokaci da Rukky din kafin drivern su yazo ya dauke ta a falona zauna bayan wucewanta na zata zata kara fitowa saida bata fito din ba.
Har nagama hada abinci na kwashe na koma sama tana ciki rufe karfe takwas ya shigo duk da yana a gajiye hakan bai hanashi bata lokacinsa da yaran ba yake tambayan Abdul din nan laura dake jirace ta fara jero masa abinda ya faru da yaron .
Da sauri ya mike zuwa dakin da nayiwa kaina masauki yana fadin wai meya faru da yarin nan bayan fitana ?
Cikin rashin damuwa nace ai da yamman nan ne ya fadi ko sunce saman kujera ya fado falo yace bata fada maki abinda ya faru bama ke nan ?
Nace muna nan da Rukky lokacin yasa na koreta bayan na karbeshi ta faye son wasa da yawa bata maida hankali ga abinda tazo yi.
Juyawa kawai naga yayi ya fita baya ya dan tsaya ya kalli yaron ya tambaya idan anbashi magani nace na bashi naga ya fita.
Daki ya samu Aisha din fushi take dashi akan zuwan mu din yasa kallon arzikima bai samu ba a wajenta don tana ganin idan ta nuna mai fushinta zaisa mu koma kano.
Aisha akan me kika furgita yaran nan dazun har karami daya ya fado daga kan kujera ya fasa bakinsa haka ?
Sai lokacin ta kallosa tana fadin abinda kuma ta kitsa maka ke nan yau har yakai ta fara kulla min sheri daga zuwanta dama nasan abinda ya kawota garin nan ke nan ai ?
Ta yara zata biyo min don taci galabanka a kaina ko don tana ganin ta cika gida da wa yan abu kamar ,,,,
Ke dakata ni zainab batayi min maganan komai ba a kanta yanzjn na shigo ina tambayanshi yaran ke fada min abinda ya faru.
Don ita uwar batama sanda kece sanadi fadowan yaron ba har yanzu data sani kina ganin bata daukarwa kanta matakin hakan gareki ?
Dokana zatayi ke nan idan ta sani auto ashe kinsan kece sanadin hakan ko ba za a tsawata masu ba ke nan saboda gasu yan gwal ko ?
Ba mamaki ai tunda ansa ka maida yaran abin tunkahonka a yanzu baka da wani zance saina yarana da yaran ke nan aka shirya yakata ashe a gidan nan ?
Idan ma wanan ke a ranki yasa kikai hakan ina warning dinki da kada ki kara da kike fasin hakan kin haifo min yaran ne na gaza dasu komai mai ?
Don haka wace tayi niyar bani bayana tazo ta van zakice wani abu to kada ki yarda irin hakan ya sake faruwa idan yarana basuyi wasa z gidan ubansu ba ?
Gidan makwabta kike son suje su sakata kome don haka ki fida idon ki akan yaran nan mu zauna lafiya banson abinda zai kawo muna matsala a yanzu .
Wanan ya kawota nasani don kawai anyi amfani dasu a hanani zama lafiya dakai zaman lafiya a ina haka ki fada min tunda kika sauka garin nan kin taba shiga kitchen din nan da sunan girki ko gyara gidan nan ?
Yanzu kizo kina zancen zaman lafiya haka ake rayuwa a cikin kazanta ya nuna dakin da hannunsa ta tsuke fuska tana fadin don bansan matsayana bane a gidan saboda ba zan zauna dasu a nan ba.
Me kike nufi wai in gargada zainab tare da yara su koma kano wai don bansan ciwon kaina ba kome inma mafalki kike ki sani nan gidanane su din kuma iyalina ne suna da ikon zama a duk inda suke so a rayuwansu tare dani.
Kano ko nan inda nake idan kinga kina iya zama ki zauna dasu lafiya kuci moriyan juna har Allah ya baki naki kema idan kina da rabon samu ko kin shirya a yanzu don ya baki kin tsaya jayayya dashi a baya.
Lalaiko baka nemi a zauna lafiya ba Aliyu ko kafin ta aureka kowa yasan Abuja nake zaune dakai ai ta kutsa ta shigo muna yanzu kace in koma kano don kawai ta kwaso yara tazo nan din saboda hassada ?
Hassada akan me Aisha zuwa nan a zauna tare danine hassada a gareki to ba inda zan tura zainab a yanzu don kawai haka kikeso ke zainab sunzo ke nan zama abuja don dama wanan ne niyata a zuciyana.
Wallahi saidai ka nema min wanu gida don ba zan zauna dasu haka ba ko barcin kirki mutum bai samun yi saboda hayaniya da kukan yara.
Amma kinyi hasara idan wanan ne kawai point dinki ke baki damu da cigabana ba Aisha sai bakin kishi dake cin zuciyanki na banza .
Ba zan nemi wani gidan ba kije ki fadawa duk wanda zaki fadawa haka ba zaki jamin zubewan mutunci ga kowa ba a yanzu kuma ina warning dinki a kan yaran nan kada wani abu ya kara saman min yara ta dalilinki gidan nan na fada maki.
Haba nan ta fara kokarin daga murya akansa da har muna iya jiyota da sauri ya dakatar da ita yana fadin bako a gidan nan ba son ba zaki zubar min da mutuncina ba ina babba a waje don haka ki kama min baki yanzu ko kiyi mamakina a wajen nan don zan baki mamaki sosai wallahi.
Wanan yasa ta rage sautin muryanta tana fadin lalai za a yita gidan nan tana jawo wayanta a gefe zata kira mum don ita kadaice mafita yanzu a gareta.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

9?? 8??
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Ya kasance jumma,a a ranan kuma zan karbi girki na farko zuwan mu abuja mai karatu idan baki manta ba mun tsaya a kaduna mun karbi sako wajen wata da mukai karatu tare har muka dan zauna gidansu na yan mintuna muka gaisa da iyayyenta.
Wanan sakon na jawo ledan a yanzu don in duba inyi amfani dasu kuma ba komai bane illa sakon kayan da muka bada a Sokoto shine ya iso gareta.
Saiga tafiya ya kamani na tsaya na karbi nawa don in wuce dasu ledan nafito dashi ina dubawa inda naga dan stickers din shangon an rubuta.
Name: Retro by Samix
Location: Sokoto State
Address: Runjin Sambo federal housing estate sokoto
Phone Number: 08105409242
Tufafine na sakawa wanda dinkinsa yake kwanci tankar redmede a jikin mace zaki rantse ba tailor din mu na nageria sukai dinkin ba indan kinga dinkunan don yadda aka hadasu.
Muna ganin tana amfani dasu yana bamu sha,awa kinsan mata da son kyale kyale kinfi son a gani gareki baki gani a gun wata kina bi ba yasa muka tura a dinka muna a can don fitan mu.
Sai gashi na wuto zuwa abujan nan yasa na karbi abina a hannunta don inyi amfani dasu a can din idan naje un zaman ya taba a gareni baizo da akasi ba.
Ganin har yau din nan da nake son karban girkina yasa na daukosu a lokacin ina dubawa gaskiya dole hauwa ta rudewa dinkun nan saboda sun tsaru kuma sunci kudin su duk da da sauki sosai sama ga wanda aka saba yi muna a kano ko zaria.
Wani atamfa mai launin pink na zaro don ina son kalan sosai a rayuwana dinkin half gown ne da sirkrt na mata wanda shape dinsa ya fita sosai .
Saida na gama komai na shiga wanka na saka saboda already ya fada min kafin ya fita zai dawo ya kwashi yara suje sallah jumma,a dasu .
Hakan yasa na zauna na tsala ado da atamfar haka suma yaran na yi masu adon jumma,a muka dawo falo muna jiransa yayin da nasa Laura ta saka kamshi a ko ina na gidan ya game dana jikinmu da muka saka .
Zaune nake ina waya da inna ya shigo jin muryansa da inna tayi yasa ta kashe wayan ba tare da munyi sallama da ita ba a lokacin.
Don tana jin ina fadin sannu da dawowa yaya tace Aliyune nace eh shine sai naji dip ta kashe wayan nata ina dariya na dago.
Fuskanshi gareni yana kallona ya kashe min ido ta yadda yaran ba zasu gansa ba da min alaman nayi kyau ga shigan hakan yasa ni murmushi ina fadin na gode nima.
Kafet din sallah na yara naba su daddy su dake da dan wayausu su kuma shi da Faruq ne suka dauki yaran biyu suka fita daga gidan mukai masu sai sun dawo.
Hakan ba karamun dadi yai min ba

100 / 105