DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   77 / 105

228K to 231K   out of 313.1K words

ko su kalla ni nama fara shawaran saya maki dogayen hijjabai wallahi har kasa idan kinje school ki dinga amfani dasu.




ZAINAB IDRIS MAKAWA

DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

7?? 6??
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


A mota na zauna shi yashiga shagon ya sayo abubuwan da yasan mum naso har nasu mummy kofan ya rufe saidai har lokacin Ac motan na bada sanyi.
Na dan dade a cikin motan can na hangoshi tafe da wasu abaya sun dauko kaya ya bude baya aka loda mai komai a ciki ya sallamesu ya shigo mota muka dauki hanyar gidan daddy.
Kamar kullun kofan gidan abude don yanzu ba maigadi sai Allah don jiya ba yau ba abubuwa sun canza hakan ya bashi daman shiga da mota kai tsaye ina bin ko ina da kallo naga har get din gidanma ya karye ta gefe tangaleshi akayi yadda na barshi haka yake yama kara lalacewa yanzu.
Ajiyan zuciya na sauke hakan yasa ya dan kalloni yana fadin duk shaukin gidane haka na kara nisawa ina fadin na dai tuna wanu abune kofan gidan nan kamar a wagalema suke kwana dashi yanzun haka.
Ya kashe mota yana fadin bari mantawa nakeyi wallahi kullun nazo raina yana baci da hakan time ne ban samu ba a gyara is not safe zaman su haka gida bude a wanan zamanin.
Gaskiya hakan baiyi ba na fada a hankali yace bari koba uwata a gidan ai daddy bai cancanci hakan ba a garemu yaran nan na rasa meyake damunsu shi Nasir ma gaba daya ya fara danbala yanzu a rayuwansa tun ba,akai ko ina ba.
Aiko yaya Nasir nada dama da ,,,,, sai nayi shiru ya balle gambun motar ya juyo gareni yana fadin yana da dama gawa ga wai hafiz shi zai hada kansa da hafiz ne kome ?
Kowa ba albarka da neman gamawa da iyayye lafiya yake nema ba a rayuwa lokacin da mahaifanka suka wahala dakai ka girma ka fara samu sai su huta kai kuma ka dora inda suka tsaya .
Haka rayuwa yake amma sun kasa gane hakan zasuzo ai zamu hade dasu zanci mutuncinsu a gaban mum ba sai bayanta ba.
Wanan yasa muka dan dade a motan bamu fito ba ashe anty habibi tana tsaye taga waye a motan daga part dinsu a lokacin.
Har muka fito yana fadin wanan fa yawan da akayi gidan nan ne yanzu ko yaran daddy enugu ai suna karya kofan nan wajen kinjinsu na banza.
A,a amarya da angone yau gidan saidai mucewa Addel maraba amma zainab kam munyi fushi tun auren ki fa sai yau kika tako gidan nan hjy tayi fadan hakan har ta gaji ta kyale muryan anty habibane ya katsemu a lokacin.
Na dan zagayo gareshi ina dariya nace anty habiba ashe kina kusa ina kwana ta amsa taci gaba da min sheri nace ita dada bata san aure nakeyi ba yanzu da zata damu inzo gida.
Shi gidan mijin nawa in barwa a gidan idan nazo gida ta kwashe da dariya tana fadin ai kun fi kusa da hjyn ku hadu batama da lafiya tun shekaran jiya kafanta ya tashi ba baki yanzu ai.
Murmushi yayi yana fadin aiya dada ba lafiya kuma aigara da mukazo din kar a lissafamu cikin yan rashin zuwa dubiyanta baida wuya gun dada kuwa wani yazo wani bai zo ba.
Ai dana yanzu tsufa da ciwo ya rage hjy tabar wanan fadan nata ta fada nace koda ai tasan inda take fadan ta ai muje mu gaida ita ya fada .
Tun banga uwata ba zanje ganin uwar wasu nikan wajen mum zan fara zuwa in kwashi albarka na fada anty habiba tana dariya tace haba zainab dadarkice fa kokema ai uwarkice hjy.
Allah dai ya sauwaka na fada na kama hanya yace ke zainab mu shiga gun dada din mu fito hakan yasa dole nayi kwana zuwa wajenta din muka jera muna dan magana game da dadan.
Babu kowa a part din sai ita da halimatu tana zaune tana shafawa kafan magani halimatu kuma tana gefe daya tana shan koko ba komai a cikinsa.
Mukai sallama ta kama kame kame kamar ta razana da ganin mu lokacin suna muna sannu da zuwa ya karasa har wajen dada din ya tsuguna yana kallon kafan yace dada ashe jiki ya motsu kuma tace bari dan nan.
Dazun nake fadin a kira min matarka koda maganin da zansha indanji sauki kafan nan yana damuna da dare dama da dan rana yakan dan lafa wani lokacin amma dare kam yadda na gansa haka nake ganin safiya.
Allah sarki ai gatama munzo nace baki bar cin nama ba ke nan dada tace naman ma ina nagansa inba wacan satin da babaku ya sayo muna shiba kowa yaci.
Murmushi yayi kafin ya daga yana fadin ai donki ne ba,a sayen naman yanzu gashi kinci kuma yanzu ya koma maki fitina tace kadai bari dan magana mukayi dashi tana kallon mu yace bari in na fito sai a sayo wani magani a gwada a gani.
Tau dan nan nagode Allah dai yayi albarka tun dazun nake bin yar banzan nan halima ta kira min Abu amma tace wai wayanta ba kudi a cikinsa.
Kina ciwo kina wanan zagin kuma haka shiya kafan ke tauna sosai ai d more kina zagin mutane kafan za aita murkushewa a fitar masu da hakkinsu gareki.
Ja,ira na dauka zancen gaskiya takeyi har na fara tuba a zuciyana au kika zageni to yaya kaji bazan rubuta maganin ba.
Yayi murmushi yace dole ki rubuta ko in kwasheta inkai maki gida kiyi jinyarta a can ja,ira aiba zataso hakan ba yanzu inje in hanata walawa a gidanta.
Mun dan dade ana ba,a a tsakanin mu kafin ya mike yana fadin bari mu leka mummy mu gaida ita sai lokacin halimatu tayi magana tana fadin.
Mummy bata nan wai taja dubiya a wudil dazun da safe daga gun dada muka nufo part din mum kai tsaye sai kuma naja na toge a waje daya na kasa karasawa dakin.
Juyowa yayi yana fadin ya haka kuma kin ja kin tsaya na dan marairaice murya ina fadin wallahi kunyan mum nake ji yanzu yaya.
Kunya kuma kunyan mum kowa nace ita mana kinsan abinda kikayi ke nan k??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ike jin kunyanta shige muje don Allah.
Ashe mama Azumi tana kusa ta leko tana fadin suwaye sai ta ganmu wajen take fadin ikkon Allah kune tafe yanzu ashe ?
Su waye mum ta fada ashe duk suna kusa lokacin a daidai kofan suna duban abu a waya mama din tace wallahi yarana ashe tafe sun tsaya kuma kamar kananun yara sai mum din ta leko ta ganmu tace a,a yau zainab ce gidan mu ?
Kagama ikon naka ka kawo min ita in ganta ke nan yace ko yanzu tausayi ta ban na kawota wai saida mukazo kuma tace tana jin kunyar shiga.
Kunya kuma zainabu wake kunyar uwarsa inba ke ba ku shiga don Allah mama azumi ta fada tana kaucewa a hanyan shiga part din data tsaya.
Tare muka jera muka shiga mum ta juya tana fadin kaidai kasani yanzu da tayi hakkuri ai gashi ka daukota da kanka ka kawota dama nace tayi hakkuri har kagama sallon ku na maza da dakeji.
Muna shiga falon mum din kasa na zube saman carpet ina gaidasu takai zaune tare da kallona tana fadin a kasa kuma zainab haba da zainab kama kanki don ni ba sarakuwarki bane uwarkice.
Shi daine surikina a yanzu ai don shine nan yake gidan ubansa bani ba shima zama yayi yana fadin gidan baban kowane fa yanzu gidan daddy.
Haka dai hjy ta fada mama Azumi tace lokacin yace yanzu muka fito wajenta ashe bataji dadiba haka wallahi jikin ya hade da tsufa ga sanyin nan da akeyi kuma sai abin yai mata yawa.
Zan fita yanzu in sayo mata magani zainab zata rubuta min tace maganin yana da kyau sosai Allah yasa a dace mum ta fada mama Azumi kuma cewa tayi shike nan yau yar Garbace da likitanci kin dauko hannun ubanki ke nan saidai shi na dabbobine nasa.
Zainab ai tayi kokari a wanan karatun nata da farko gani nake kamar ba zata iya ba sai gashi yanzu har ana zancen kai shekara kusan hudu ke nan a yanzu.
Kowama haka ya dauka da farko ba zata iyaba ai amma ni tunda naga tana da nacin karatu nasan insha Allahu zata iya idan an dage mata.
Wata ran ai muna da likita muma a gidan insha Allahu mama azumi ta fada sai mum tace Allah yasa dan naki ya bari tayi aiki don matarsama bata aiki gata tayi karatu kuma har kasan waje.
Tsoki yaja yace mum da wani kwali zatayi aiki wace bata tsaya tayi karatun komai ba bata da takardan shedan karatu taya zatayi aiki?
Kallosa nayi nasan ya manta da ina kusa ya fadi wanan zancen itako mum cewa tayi jam zuwan banza ke nan tayi turai ashe sai wayewa da fitsara data koyo .
Ya mike yana fadin rubuta min maganin nan naje na sayo naga tsohuwar nan tana jin jiki na dauko takarda da biro daga jakata na hannu na rubuta masa ya karba ya fita.
Lokacin mum ta kalloni har lokacin kuma ina zaune a kasa inda na zauna tun shigowarmu wai zainab ba zaki tashi a kasan nan ba saikin bata tufafunki ko ?
To ta zauna mu muna zaune tarbiyankice fa a girmama nagaba hjy Azumi zainab kuma bakuwa tace yau don Allah tashi ki shiga ki shiga ki dauko maku abinsha ciki kafin mijinki ya dawo banson shirmey ni.
Tashi din nayi abinda tace dan madaran hollandiar nagani shina dauko ina fadin insha wanan mum ta kallo tana fadin sarki zaki dauki kisha niba damuna yayi ba.
Ya dade aje a fridge din ba wanda yasha daidai lokacin yaran part din daddy enugu sukai sallama suka shigo da basket da sauran tarkace bansan ina ya samu manyan maza ba suka shigo da buhun shimkafa dasu mai karshe dashi aka shigo.
Yana fadin tsaraban yarkice mum wai bata iya zuwa gaidake hannu sake tace mum ta kalloni shine kika tsaya kikai wanan wahalan haka ?
Yo ai ni ganin nan naku haka yafi min komai dadi zainab kina zaune lafiya a dakinki haka aini nafi kowa farin cikin wanan abin Allah ya kara kabar da tsotsayi a tsakanin ku kuyi ta hakkuri da juna a zauna lafiya don Allah inji mum.
Zaman lafiya ai dole tunda ga alaman rabo a jikinta an samu da sauri na dago kai na kalli mama Azumi dake wanan magana sai kuma na dukar da kaina kasa cikin kunya.
Tau masha Allah Allah yasa hakan ya tabbata nima har na fara fada duk dashi ba mai zama bane kada tace zatayi wanan shirmen tsarin iyalin dataga anayi na banza.
Gara dai mutum ya gama haihuwansa ai ya koma tarbiyan yara yafi ace haihuwa da girma sai daga baya kuma kiga an koma ana neman haihuwan mama azumi tace ako rasa ba tunda ba aiwa Allah wayau.
Duk zancen nan yana tsaye yana zukan ruwan gora dagani har shi ba wanda yai magana ko ya nuna yasan sunayi alokacin don kawaici.
Saida ya fitane mum ke fadin ita fitinaniyar dai tana can abujan ko ko tare sukazo tunda ba ganinta akeyi ba ko tazo din nace ina ganin shi kadai yazo.
Ai haka yafima hjy ta zauna can tatayin barikancinta keyi zaman ki nan tunda kuna zaune lafiya da mijinki ba shike nan ba dama shi ake bukata aiga aure kwanciyan hankali ankuma samu.
Nan na dinga jin wasu maganganu da bansan dasu ba mum tana hira duk irin rikicin da akai tayi da ita bayan aure da fadan mota da tayi da tashin hankalin ubanta.
Yaya ya kawo magani yaba dada tasha ya dawo ya dan zauna kafin ya fita yace zaije ya dawo ya kara barin mu nan tare dasu.
Ina ba mum hiran abokan zamana dana samu a yanzu tace to ki kara hakkuri dasu shi mutum dadi garesa koba komai sun rage maki kewa ai.
Bayan azahar na fito zuwa gaida mum da akace ta dawo tunda nayi sallama ta kyala ido a kaina ta soke kai bata dago ba na dan jima da anty nafisa muna hira karshe dakinta ta tashi takoma ta barmu.
Sai kusan la,asar na dawo part din mum na samu yaya ya shigo yana cin abuncin da nazo dashi alwala nashiga nayi sallah na fada dakin mum na fara gyara mata har zuwa falo sai albarka suke saka min ita da mama Azumi din
Bn gama gyaran ba sai wajajen yamma sosai part din ya koma yana kyali kamar bashi ba wai kuma mum tana gyara ke nan na mummy baya kalluwa ko kadan duk ya hargitse ga ganina.
Sai kusan magariba mukai masu sallama muka fito mum nata jin dadin yadda ta ganmu din a lokacin don farin cikinta ya kasa boyuwa.
Naso na kaiki gidan baba amma lokaci ya kure yau sai wani lokaci idan nazo muje mu gaishesu suma ya fada.
Nace Allah ya kaimu ina gyara zamana yace kinje kin wahal da kanki azo tabaki kuma kice wash Allah nagaji sosai.
Na lumshe ido ina fadin aikin ladafa nayi yaya in gyarawa uwata daki kace wahala yace yayi da bakizo ba yau wazai gyara masu basu ba.
Baka da tausayi kai bakaga yadda part din ya koma ba garama na mum sau dubu dana mummy don ko kalluwa baiyi yanzu ga mutum don kazanta.
Kwana naga yayi ya dauki wani hanya na daban wani unguwa mukaje ya sayi kaji gassasu da abinsha da wani leda na daban muka nufi gida koda muka isa an kira sallah har an idar a wani wajen.
Don haka a gurguje ya saukeni ya nufi massalaci don shi yafi son sallah a cikin jam,i nima ban zauna dakina na shiga na dauro alwala nayi sallah .
Bayan na idar ne na fito don nasan ba zancen girki gareni tunda naga ya sayo muna abinda zamuci don haka na dan leka kitchen don tanadar abinda zanyi muna da breakfast idan Allah ya kaimu.
Ina kitchen din naji shigowanshi ya zube kaya falo ya nufi dakina daga bayansa nake fadin gani nan yaya OK ya juyo yana fada.
Sai kuma yanayinsa ya juya na mamaki yace me kikeyi a kitchen kuma yanzu nace dankali na fere don gobe kedai bakya hutu aiki bai dameki ba zeey .
Kizo ki cirewa mutanen nan kayancan ki mika masu kada yaransu suyi barci basuci ba son dasu na sayo na karasa wajen kayan ina dubawa.
Kajine guda hudu sai fresh milk dasu hollandiar kilishi da tsire ya kwaso muna sai su snacks mai hadi masu lafiya na raba biyu na bude kofan baya ta kitchen dina na samu suna waje saman baranda.
Aina najin na bude kofan tace hjy ashe kun dawo yanzu nake zance nace Alh yana nan balle naje muyi maki sannu da zuwa nace yanzu ma ya dawo daga massalaci ai.
Yasu hjy suna gaidaku na basu amsa yaran suka mike sukayo wurina nadan rungumesu ina fadin baba ga tsaraba nan a taba iyayyen suka shiga yi min godiya.
Nayi masu saida safe na dawo na samu ya shiga wanka naje na dauko plate da knife da kofuna na jera nan kasa saman carpet.
Wanka nima nashiga don nasha iska ajikina dana fito na dan gyara jikina na saka dogon rigan bubu na wani kamfala mai laushi na dan murza turare sai hula a kaina dana dora nafito.
Kusan tare muka fito dashi yana waya don haka na rigashi zama a kasan tare da mike kafata don naji dadin zaman.
Zama yayi yana lakato min hanci tare da fadin mai ciki na dan noke ina fadin kai yaya ka yarda da zancen mama ke nan ni kan banda komai wallahi ba yanzu ba.
Saina gama karatuna nasha amarcina kamar kowa kafin hakan yace kina wasa yarinya kada ku mai dani wani solobiyo mana.
Ita wacan idan bata san ciwon kanta ba zainab kema din baki sani ba zainab ki duba age dina yanzu duk agemate dina sun aje diya a gabansu.
Yaya wasa nakeyi kasan dai ba zan taba planning a yanzu ba kawai dai Allah bai kawo bane balle yanzu da naji kana son haihuwa ashe ai kaka ba zanyi gigin yin hakan ba.
Kin kaiwa mutanen can nasu kinsan Annabi yace ka kyautatawa bakonka don mu suke zaune a gidan nan mussanman don ni dake don haka don Allah ki kula dasu

77 / 105