DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   52 / 105

153K to 156K   out of 313.1K words

tafi ita kuma ta koma dankinta tana duba kayan da mum ta aiko mata dashi saida ta tabe baki take fadin zancen banza kawai ta dauka zuwa uwar dakinta dashi.
Ban samu kaiwa Dada nata ba saida na kwashe abinci nakai mata na samu halimatu da Dada din suna hira na zauna bayan na bata muna dan hira kwatsam ya fado falon Dada din.
Saida gabana ya fadi na dake dai na zauna kai tsaye yace ke zainab zoki sameni waje wani kallo nayi mai na watsar zakice badani yake maganan ba a lokacin.
Har ya fita ya dawo a sukwane yana fadin waiba dake nake magana bane daga inda Dada take zaune take fadin wai meye hakane ya juya gareta yana fadin bakijin ina kirantane tayi banza dani.
Kai hafizu ban son diban albarkan nan naka ina yarinyar nan dai kace baka son ta meye kuma yanzu zaka dawo ja matsawa yar mutane da shashancin nan naka wai ?
Ka dinga abu kasan ka girma mana inda kace baka sonta yanzu kuma itace bata da lokacin ka don haka kafice kaban waje tun ranka bai kai ga baci ba gidan nan.
Dada dama nasani kina cikin masu zuga kamarin nan don kawai inyi bakin ciki to banyi ba kuma banga wanda ya isa ya hanani naida matata ba a yanzu.
Don shirye nake da duk wani abinda zaku fada a kaina na dade da shryawa hakan ba yau ba duk mai fada ya fada nace matata nakeso yanzu.
Lalai kayi hau kila abin ya fara taba kwakwalwan ka da alama kanka ya tabu to bari kaji koda ake fasin an mayar da aure wanda bai dadeba ake mayarwa haka kai tsaye ba irin naka ba daka share shekaru baka juyo ba sai yanzu.
Don Allah Dada idan ba zaki gyara zancen nan ba ki mun shiru ki bari ta taso muje don Allah kai ka fice min daga sashe nan idan ba so kake ranka ya baci ba wallahi dama na dade da sanin ka fara tabuwa ai a gidan nan.
Ki daina inba haka ba kafin raina ya baci naki zai fara baci sosai wallahi anty nafisa nayi wa text sai gasu a sukwane ran uwar ya baci sosai zaginsa takeyi kamar karamin yaro a lokacin ya fita na samu na koma part din mu ina labartawa mum abinda ya faru.
Da dare sai ga Dad ya aiko kiran mu har mum ta tasani a gaba almost kowa na gidan nan lokacin kusan mu muka shigo karshe falon daddy ya aika anty Nafisa ta kira hafiz din yazo.
Baya kowa ya natsune yake fasin hafiz wani hauka kakewa mutane gidan nan ne ya tambaya yana kallon dan nasa daya zauna ya dukar da kansa kasa.
Yaci gaba da fadin kasan ko girman abinda kake kokarin aikatawa a yanzu lokacin dan ya dago kai yana fadin daddy nime nayi cewa nayi dasu matata nake bukata yanzu kawai and kuma bana son ganinta da kowa a gidan nan period.
Kaci gidan ku mara hankali irin na mutane kawai anki a baka matar naka ina matar naka take dan kawai ga rashin kunya irin na hafiz sai ya dago kai ya kalleni da idanuwansa da sukai ja nikan na dukar da kaina kasa da sauri.
Ina iya mutunci munyi maka shi a gidan nan kace ba haka ba bamu iya ba wani iri kunyane baka ban a duniyan nan kan aurenka da yarinyar nan ?
Amma haka ka watsa min kasa a idanu har zumuncin mu ya tashi tabuwa da dan uwana badon mukai zukata nisa ba da yanzu babu alaka a tsakanina da Garba kowa yasan da haka dangi kaf duk a dalilin ka.
Yanzu shine son baka da kunya ka dawo ka tada zaune tsaye waikai matarka kakeso mara kunyar banza kawai kai in me hankali ne aiba ta haka zaka bullowa zancen ba .
Amma da yake kanka bai aiki daidai da mutane shine ka yamutsa min gida a bayana don kana dan takife ko kai gaka issashe ko to bari kaji a yanzu ban saka baki ga komawan mama gidan ka kaje ka nemi so a wajenta inta yarda kuzo muna tare ku fada muna hakan amma yanzu mama ai a kasuwa take don allurace yanzu a cikin ruwa mai rabo ka dauka.
Gaskiya daddy in anyi min hakan ba ai mun adalci ba gaskiya don dani da zainab ai duk a karkashin ka muke kaji mara hankali ko hjy mena fada maki dama ?
Kukan mummy ya katse masu zance da take fadi a cikin kuka nikan nashiga uku da makiya a gidan nan dama don aga wanan ranan aka bi dare akabi duhu don kawai a ga fita hankalinsa ai muna dariya.
Haba mummy don Allah kibar wanan zancen kansa daya wallahi tsaban iskancine kawai da lalacewa ya dauka kowa kalansane da baisan ciwon kansa ba da yace yana bukatan matarsa sai kawai a dauka a mayar masa don ana tsoronsa yaje yayi duk abinda zaiyi yanzu din ai.
Yo Allah na tuba waye ma zai rsaya bata lokacinsa wurin shirka da zaije yai wani abinda zai kauce akan zancen nan ai magana ya kare yanzu tunda taji daga uban gaiyan allura mama take a cikin ruwa sai ya shiga sahun manema a fafata dashi.
Karyene wallahi donshi kinsan shirin da kikayi kika turo Addel ya nemeta dama nasan shirinki hjy kubura kamar yunwar cikina shirina da haukanki ke karanto maki ko ? Mum ta fada.
Addel kuma daddy ya tambaya cikin mamaki mummy tace kwarai dazun saida muka rabasu gidan nan akan zainab din ta kwashe kaf ta fadawa daddy yayi shiru kamar yana nazarin zancen a zuciyarshi.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

5?? 2??

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Cikin mamaki ya kara maimaita tambayan da mai sunan malam yana son mamace ko mai ya dago yana binsu da kallo ba wanda zaibada wanan amsan me amsan kuma baya wajen alokacin.
Sai anty Nafisace tayi karfin halin fadin daddy shirmen hafiz nefa kawai da kurman kishinsa na maza don yaga zeey da yaya tsaye suna hira shine ya hausu da zagi dazun da safe.
Kai daddy ya girgiza kafin yace nasan a rina dama don amana aiba wasa bace burin ko wani namiji kuma ya auri mace kamila ta zamo uwar yayansa gobe .
Don hafiz ya saki mata ka gansu tare ba haramun bane hakan ai din sunna ya yarda da hakan addini bai haramta hakan ba balle kai da ba zaman aure kayi da mama ba me zaisa ba zai gwada sa,ansa ba shima.
Haba dai kasan hakan bazai faru ba ai yadda ta haramta ga nonon uwarta ai haka ta haramta ga mai sunan malam shi dan uwansa ya saki mace yace zai aura kuma ? Dada ta fada cikin bacin rai.
Addini bai hana hakan ba hjy koda kuwa akwai haihuwa a tsakaninsu saidai malam ba haushe yace ana barin halas don kunya sai in wanan akabi yaga yana iya barwa dan uwan nasa wala ba,asa komai yakare.
Kai yanzu sai kashiga layin maneman mama a yanzu a fafata dakai wajen nema amma ka tuna kaine da kanka wanan karon zakaiwa kanka yakin neman zabe ba wani ba ga fili ga mai dokinan gaban ka a yanzu.
Mu namu fatan alheri game rabo a cikinku ina ka fahinceni yayi shiru don ji yake kamar ya kama da wuta alokacin don bai zaci hakan ba ga daddy.
Ya zata illa fushi da sharhi daddy zai masa kan kuskuren daya aikata abaya sai gashi daddy din yanzu yana koro masa wani zancen daba shi don baiyi tunanen hakan ba sam.
To dawa zaiyi takaran a yanzu daddy ke nufi wanan doctor ne da yake ganin yana kawowa zainab ziyara ya kuma gama dashi tuntuni daya farga da hakan in dai ba Addel dake son shiga masa hanci da kudundune ba ayanzu.
Addel kuma ya san ta inda zai biyo masa yayi maganinsa a cikin ruwan sanyi don haka ya mike tsaye suka bisa da kallo ina kuma zaka haka ana magana Dada ta fada a hasale.
Ina ruwanki ya juyo ya fada a hasale gareta tace miskili yau aiga ranan rashin kunyar taka bata haifar maka da komai ba sai tarin nadama da dana sani .
Hannu daddy ya dagawa Dada din yana fadin hjy kyaleshi don Allah ya dauka zancen wasa yazo muna dashi ya manta lokacin da muke lalashinsa abaya.
Ya manta da irin bakin cikin daya kumsawa zukatan iyayyen yarinyar nan da ita kanta a lokacin shine don baida kunya ya rainawa mutane hankalivshiga mara kunya ya dawo da zancen baya yanzu.
Kuma daga yau na kara jin ka takurawa yarinyar nan a gidan nan zan ma iyaka da gidana tunda bada kudinka nagina abina ba dukkansu suka kallo daddy har uwar nasa yace kwarai na kara jin wani abinda yayiwa yarinyar nan na takura hukuncin da zan dauka ke nan akansa.
Sakai yayi ya fice a falon a fusace daddy yace kaje ko ina zaka aure dai nine mai daurawa mama aure a dangi kaf itama mummy mikewa tayi a fusace ta fice a falon.
Nikan ji nayi kamar an rabani da kaya a lokacin cikin zuciyana don banga ta don banga ta inda hafiz zai tun kareni da wani zolayan kaunarsa ba yanzu da zaisa in yarda dashi da wanan mugun halin nasa dana sani tun ina karama.
Dan bayani daddy yayi muka mike zuwa sassan mu kowa da abindake zuciyarsa da yake ina son leka school da safe don haka ban tsaya hira da mum ba nashige na kwanta na jawo wayana nan na samu miscalled din yaya ya kira ban kusa lokacin.
Ba tunanen komai na danna masa kira ashe a lokacin suna tare da Aisha itace ta dauki wayan ina jin muryata na kashe da sauri ance abinda baka so kada kaiwa wani anyi ta kira daga baya amma ban dagaba.
Wanan ya jawo masu rigima a tsakaninsu sosai da har ta kawo karansa wajen mum mum tace zatayi muna magana abinda kawai mum ta fada ke nan sai hakan ya kona mata rai kuma wai mum bata dauki wani mataki ba.
Da wuri na taso school don haka na biya gidan mu in gaidasu na kwana biyu banje ba don exam da mukeyi nagama kuma na kwanta rashin lafiya don haka yau na biya in gaida su.
Ina shiga yanayin inna na gane ba lafiya ba nake tambayanta bayan mun gaisa inna waiko lafiya ta nisa tana fadin bari yarinya waya aka bugo min innawo ba lafiya da cewa mahafiyarta.
Innalillahi na fada tare da fadin ya kamata ki gagauta zuwa ki gani inna tace nima da hakan na kwana a raina saidai babanku yace wai sai ya shirya zan tafi.
A,a inna tunda har kikaga sun bugo maki gaskiya ba sauki lamarin gara dai kije ki gani da idonki tun wuri yafi a tsaya baki labari har wani shiri baba zai tsaya yi akan ciwo ina dai kudin motane sai dan abinda zaki rika ki kai masu tunda kin dade bakije ba.
Take fadin nima shina gani ai don ma nayi sayayan kayan sana,atane shekaran jiya da kudin dake hannuna zai isheni komai har inje in dawo.
Ko yanzuma ba,a rasa yadda za,ayi ai don akwai dan kudi a hannuna bari baba ya dawo sai asan abinyi ki kama hanya kije ki dubosu kika ya jikin nata a can din.
Mun jima muna zance akan jikin innawo din kakarmu don nikan rabona da ganinta gaskiya tun muna katsina datazo ganin inda yarta ta dawo da zama lokacin tun wanan lokacin ban kara ganinta ba kuma.
Wayanane yai kara na duba ya Addel ne a layi yadda yaji amsawana yasa yake tambaya meke faruwa ga kuma hayaniyan yan uwana yana ji na nisa ina fadin ba komai .
Kina inane haka nake jin hayaniya kuma ?
Nace nazo gidansu innace sai kuma na samu inna din ba dadin rai anbugo mata waya mahaifiyarta ba lafiya shine muke magana ka kirani yanzu.
Subbahanallahi da sauki dai ko ya tambaya nace bamu sani ba amma tunda suka kira kila tana jin jikine sosai tunda ba wata tsohuwa bace sosai.
Ok yanzu yaushe inna zata tafi nace to sai baba ya dawo don tace wai sai baba ya shirya zata tafi yace ina aiba tsayawa wanan garin nasu a can tsakiyan Niger yakene ?
Nace a,a ba nisa da Nageria sosai nan dai boundary din nageria ne dai bari kawai in turo maki kudi if possible goben nan ta kama hanya sai a dauki mota shata su tafi.
Wai yaya kada baba yayi fadan hakan yace kona rokekane fa yace common wanan ku kadai ya shafa halan duk ya shafi kowan mu ai zancen.
Yanzu zan turo maki da kudin tafiyan ku gagauta zuwa sawo mata tsaraba tunda safe ta kama hanya Allah ya ba kaka lafiya ya kuma kiyayye hanya na amsa da amin muka kashe wayan akan da dare zai kirani yaji ya mukayi da baba din.
Ina kashe wayan na dago inna kallon ina take fadin wayene cikin tsureni da idanu kai tsaye na bata amsa da ya Addel ne inna Addel kuma nan nake fada mata abinda yace.
Wai anya babanku zaiyi fadan hakan sosai idan yaji nace nima nayi tunanen hakan don nasan halin baba sarai zai iyacewa kene kika turani na rokesa.
Wanan kan kema kin sani ai bansan abinda yasa mahaifinku ba ai masa kuskure ba shi karan shigowan sako a wayata ya katse muna zancen.
Inda na tsaya na duba sakon bankine daga yaya kudin da nagani yasani fadin wai har dubu dari biyu inna sufa yaya ya turo maki na tafiya.
Dubu dari biyu fa kikace nace wallahi shiko dan nan wani irin aiki yakeyi hakane wai da baijin wuyar fitar da kudi haka masu yawa inna ta tambaya fuskanta da alaman damuwa.
Nace naji ance a matatan mai nakasa dake Abuja yake aiki ikon Allah inba yauba bansan aikinsa ba har yafi dan wajen hjy Malka aiki ke nan ko ta tambaya ?
Nace to kusan dayane dai kila don shima ai likitane saidai ba,a gane samunsa tunda ba shiga tsabangansu mukeyi bamu .
Baki inna ta tabe tana fadin ko banza uwarsa bata da marmari ko kadan kullum idan mun hadu fuskanta a daure yake batayi min fara,a na mike ina fadin ina ruwanki dasu inna.
Banda hauka wai sai ga danta yana min hauka shiya mayar da aurensa jiya saida daddy yayi muna iyaka dashi a gaban kowa na gidan mu ai.
Anya kansa daya kuwa yama kuwa san me ake nufi da aure ko addini shidai ya sani a gurguje na dan bata bayanin abinda ya faru naja kanwata muka fita sayayan abinda ya dace na tafiya muka hadowa inna har abincin da zasuci don a can akida ya dan bambamta da namu data saba dashi yanzu don haka naga baba yana shirya mata idan zata gida.
Saida muka dawo na kitsa mata abinda zatacewa baba din idan ya dawo kada yai fada a lokacin hakan ko ta fada sai fadan yazo da sauki amma yayi yace wai ta rokeni ko?
Tace haba malam kata ji ko ganin wanda na roka a duniya balle yar cikina ko halin banza kake zaton ina koya mata yanzu kuma duk daba hannuna take ba?
Yace ba hakana bane banson abin ashane ni amma ban fada da wani manufa ba dama akwai dubu hamsin awaje saimu kara mu tafi saidai yaran nan yanzu nake jiwa ko gidan babansu na Enugu zan kaisu kada muyi rashin hankali in muce a kaisu wurin hjy kuburah kuma ?
Nan take fada mai abinda ke faruwa wani zabura yayi yana sakin ashar ga hafiz din kafin ya koma ya zauna yadda yake da farko yana kutawa yace zamu hadu ai.
Anan sukaji sallamana da hjy mum datasa mu fito acikin daren don tazowa inna jajen abindake faruwa da mahaifiyarta din sun jima suna magana kafin ta tambaya koda yaran zasu tafi yace to shawaran ke nan mukeyi kika shigo .
Tace a kaisu gida aisu ukune tunda da karamin zaku ko yace haka naso amma basuyi yawa ba tace asha yaya yawa kuma kosunfi hakan baka da wanda yafimu a wanan garin ai.
Bamu dawo gida ba sai tare da kannena do sammako zasuyi zuwa katsina daga katsina zasu dauki hanyar zuwa Niger kauyen su inna din.
Koda muka dawo dare yayi a lokacin don haka ba kowane yasan zuwan mu gidan da yaran ba saida safene bayan na fita mum take fadawa daddy zancen zaman yaran a nan.
Yace banda abin garba ina za,a bar yara su kadai a gida ga gida

52 / 105