DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   55 / 105

162K to 165K   out of 313.1K words

don sun kusa karasowa yanzu.
Ke nan sammako sukayo indai har zasu kawo accikin wanan lokacin haka kome suka samu kuma zasuzo yi nan oho ?
Wani iri naji don gabanane ya fadi ke nan baba bai san da wanan zaman bama kiransa kawai zasuyi su fada masa ra,ayinsu a wajen don na gama fahintar abin hadin bakine garesu.
Ko an samu wani abune gidan naku kuma muryan baba naji yana tambayana hakan da sauri nace a,a saidai ina ganin kan zancen hafiz dani zai kawosu don sun kwasa da mum shekaran jiyancan akan zancen.
Zancen ki kuma da hafiz akan me meye hadinki da hafiz yanzu bayan zumunci zainab baba ya tambaya cikin mamaki yana kafeni da idanunsa.
Baba babu komai fa su dau so suke wai sai na koma gidan hafiz din yanzu tunda ya dawo yace ya mayar dani shine suka hade kai gaba dayansu wai mayar dani zasuyi gidansa.
Amma zainab shine ke ko gwaggon naku baku sanar min da komai ba amma ko yanzu bai baci ba ai hankali ke saurare ba baki ba.
Sai bayan fitan baba inna ta samu bakin magana ta nisa tana fadin akwai wani abune tsakanin ki da yayanku mai sunan malam dan wajen gwaggokine ?
Jin tambayan nayi a bazata daidai ina mikewa tsaye yasa na tsaya ina fadin inna wani abu kamar,me kuma ,,,?
Ai gara kiyi magana don yadda yaran nan ke bani labari kamar kina tare dashine gara dai kuyi tunane dagake harshi don kunsan ba,abu bane da zai yuyu kuma kun sani kundai take sani kawai.
Daki mm ashige ba tare da nayi maganan komai ba gado na haye na kwanta banji daga yaya ba kuma koshima yana hanya sun gaiyatoshi shima.
Barcine ya soma daukana naji wayana tana tsuwa na dauko gefena mum ce ke fadin kina gida har yanzune don ina ganin kamar iyayyenku zasu nemeku a yau din nan don naga su yayan katsina sunzo.
Ina gida mum barci ma nakeyi yanzu kika tayar dani to bari dai idan sun bukaci kizo zan kira wayan naki nadai san zancen sukazo yi su don naga tun da safe ana girke girke wurin hjy malka.
Duk da gabana ya fadi ban nunawa mum komai ba har muka gama magana na fahinci itama hankalintane ya tashi sosai lokacin ta rasa abin yi ta kirani.
Na dade kwance kafin na mike na hari bandaki bayan na fito na zauna nayi alwala don ingabatar da nafila in kaiwa Allah kukana kan abinda ke shirin faruwa a taron iyayyen namu.
Ya dan makara don sai sha biyu da yan mintuna ya iso kano din kafin kuma ya karsso gida sha biyu da kusan rabi yayi don haka yana isowa shi ake jira falon dama.
Ya iso cikin shiga ta shadda kalar maza dinkin yar gajeran hannu ya tsaya mai iya gwiwa kadan dukda bai karasa sauka sosai ba hular kanshi kuma kalan kayanne sak kallo daya zakai mai kasan ankashe kudi masu yawa wajen sayen hular kadai.
Kafasa da rufafun takalma sai agogon hannu daya daura a hannusa na silver yana sheki ke kinsan an kashe kudi wajen wanan shigar da yayi din.
Ya shigo falon da sallama suna zazzaune su kaf dinsu yan uwane yanayin amsawan nasu ya kara daurewa babana kai shi yayi karfin hali yace mai sunan malam taro har da kaine ashe ?
Yace ehh baba jiyan nan da dare daddy ke sanarmin kuna nemana yau shine nazo ikon Allah baba ya fada daga haka bai kara cewa komai ba.
Baba sale ya fara magana yake fadin a bude taro da addua aka bude kafin yayi sallama yana fadin tobyan uwa sallamu alaikum suka amsa mashi.
Yasoma magana da fadin ina maiba wasu daga cikinmu hakkurin dakatar dasu wajen sana,oinsu da mukayi magana ce babba ta taso a cikin yan uwa akan yayan mu gasu nan su biyu kosu ukku nan baba ya daga ya dan saci kallon ya Addel din.
Baba sale yaci gaba da fadin shiyasa naga gara muyi maza muyiwa abin tufka tunkan hakan yakai ga taba zumunci shekaran jiya shi hafizu ya sameni gida ya karonto min duk abindake faruwa nan.
Wanda ya nuna nadamansa kan sakin matarsa da yayi a baya yanzu kuma ya dawo yana son matarsa sai dai kuma akwai kalubalin da aka samu bayan hakan.
Don yanzu shi mai sunan malam gashi zaune ya fito da zancen cewa yana son ita yarinyar kuma har sun daidaita a tsakaninsu wanda wanan abin bai muna dadin ji ba ko kadan.
Don hakane na tara wanan taron a yau don in tabbatarwa shi mai sunan malam abinda yayi baiyi daidai ba daga gefe wani ymdan uwa yace kwarai kuwa don ko ana barin halak kodon kunya.
Sam bai cancanci kai haka ba don koba komai Alh yai ma komai ya rikeka Allah ma,aiki ba bambamci da diyan shi nan suke ta kawo shahi duk akan mai sunan malam dai a cewan su bai kyauta ba abinda yayi din.
Sai baba Isah ne yace kai jama,a ya kamata fa adubawa yaron nan shin don kasa ya rufe ido ga nasa mahaifin kuke son mayar da abinda yayi kamar haramun ?
Kaiko isah kakan fara zancen ka ke nan wallahi ai maganan gaskiya ake fada a wajen nan yanzu kaima kasan bai kyauta ba sam ta yaya dan uwansa zai saki mace ya dawo yana nemanta kuma don Allah fa isah ka fadi gaskiya a nan ?
Ku dakata don Allah don tun dazun da ake zancen nan ni ban fahinta bafa wai wata matar ake zance akaine don ni bansanda wanan zaman ba zancen da kukeyi kuma ban ma sanda shiba sai yanzun nan .
Daddy ya dago ya kalli baba don yasan akwai rikici ke nan da baba din don da jin dadinsu guda sun nunawa baba sun isa ya kuma yi shiru sai gashi yana son ya ballo masu aiki yanzu kuma.
Baba Sale yace kamar ya baka fahinta ba zancen hafisu da yar wajenka mukeyi dashi mai sunan malam ya bulo yanzu yana son ya aura shiya zaunar damu wurin nan yanzu don muna son a mayar da auren nasu a yau din nan.
A bisa umurnin wa za,ai hakan ya dago a harzuke yana kallon baba sale din dake dauriyan bashi amsa lokacin don kowa ido ya zuba masu don sunsan rikicin baba sarai.
Baba sale yai dauriyan fadin abin ba sai ka sani ba don mu mun isarwa zancen ai ohh hakane to gani gani ina jiran jin wanda zai daurawa zainab aure a cikin ku.
Baba ya mike tsaye baba sani ya jawoshi yana fadin haba Garba ai abin baikai na haka ba ina su manyane sun isar maka basai ka saka baki a zance ba ai yace nasaka.
Ko lokacin da yaron nan Hafiz ke ci min mutunci kan hadib da Alh yayi akwai wani babba da ya dakatar dashi ga hakan koko lokacin dayaciwa yarinyar mutunci akwai wani wanda ya wanko kafansa yazo jin ba,asi a cikin ku don haka ban yarda ba nakuma fadi ban yarda ba in akwai wanda ya isa kaf dinku nan ya daura ya mayar da ita yau dakin mugani.
Ya nufi hanyar fita falon kafin ya koma juyowa yace kai ????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
isa kabar bata bakinka son koka fada ba zasuji ba tunda suka iya raba daya biyu don yau kasa ya rufe idon Abdulrahaman dansane bare a cikinsu.
Muba hakane manufar muba kaima kasani hannu daddy ya daga yana fadin ku barshi bacin raine duk abinda garba yayi yau yarsace bamai iko kamar yadda ya fada da yarsa a cikin ku.
Kwarai nayi na farko nayi na karshe watau don bai samu la,anta min itaba yake jin haushin dan uwasa yanzun da yace yaji yagani akanta ko yake son ya idda nufisa idon baba ya rufe maganganu sosai ya fada masu wajen .
Harshi baba Auwal dake dadin karatun nawama a dakatar in zauna dakina don gudun abinda kaje ya dawo ya nuna baba Auwal din yace kai tsaban bakincikine ma kawai ke cinka don ka fada a fili kowa yaji
Kai Garba kada ka fassara min zance da wani manufa anan nan baba yayo kansa yana fadin idan na fassara Auwalu da abinda zakayine baka fadabane.
To bari kuji wallahi ko bayan raina wanda ya kara daurawa zainab aure da Hafiz gashi nan ban yafewa maishi ba sai Allah yai min hisabi dako waye gobe kiyama.
Subbahanallahi asha garba kanka daya kuwa wanan furcib fa haka yace kai yanzu dai ba anzauna anan bane kan yaron nan Aliyu to kaje ni Garba na baka zainabu duniya da lahira in yazo kake da sadakinta kawo dubu ashirin a daura aure anan inga wanda bai shedawa a cikinsu ?


ZAINAB IDRIS MAKAWA

DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

5?? 5??

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Amma baba inkai min hakan bakai min adalci ba gaskiya don kowa yana kuskure ya gyara Allah ma da kansa ana masa laifi ya yafe muna,,,,
Balleni ko to ban yafe ba nace ban yafe ba jeka kwaso katsina kazo dasu nan bazan yafe ba din ka manta lokacin da kakejin kamar ka tsusheni ka yanka don kawai nice na haifi zainab?
Akan auren da bansan yadda aka hadashi ba kuma nayi kawaici na kawar da idona don magabatana sun gudanar da hukuncinsu yadda suke so amma hakan kai bai makaba saida kaci min zarafi ko ince akaci min zarafi dani da diyata a idon duniya.
Shima hafiz mikewa yayi a fusace yana fadin wanan ai kuskurene kuma ya wuce na fada maku ban saki matana ba don na mayar da aurena inga wanda zai daura wani auren akanta kuma ?
Kaji jahili kaji wai wanan zan bawa mata wata rana daga diyar harni ya kwaso ya make mu tunda bamu da gata a sa ido ana kallo ana fadin nayi hakkuri sherin shedan ne ko shida bamu gani.
Aure ko to zan daura aure da Aliyu gashi zaune miko min sadaki a gabanshi za a daura yau ya gani baba ya mikawa ya Addel hannu alaman ya kawo sadakin.
Shi kuma ya tura hannu cikin aljihun shi ya ciro bandir din yan dubu guda ukku wurin baba Isah ya juya yace gashi baba wanan dubu dari ukune dari biyu sadakin zainab dubu dari kuma a rabawa shedu su sheda tunda ba goro ko alawa a nan.
Ehh lalai ashe ba Garba kadai bane mara kunya har dakai mai sunan baba watau kana kan bakanka saika auri macen da dan uwarka ya saka kuna gida daya?
Ubansa ya ci dakai ya tufatar da kai ya dauki dawainiyanka yai ma komai na rayuwa amma yau sakaiyan da zakazo kai masa ke nan cin fuskan dansa a gabansa tun yana raye.
Kai ya girgizawa baba Sule yace banyi hakan don inci fuskan kowa a nan ba shi daddy ya sani ko kowa zai fada nasan daddy ba zai fadi hakan ba gashi zaune.
Sunnace na raya ta ma,aiki alaihis salam banyi wani abin asha ba anan da zaku zargeni haka zainab dai bata zauna zaman aure da hafiz ba tunda bai taba saninta ya mace ba har suka rabu.
Wani tabure fuska baba Sule yayi ya kallo daddy daddy din ya gyada mai kai alaman gaskiyane haka Addel yaci gaba da fadin a kaddara yasanta din duk hakan aure ya halasta a tsakanina da ita.
Banyi auren nan da jiyar cin zarafin wani ba Allah ya sheda sai hango iri mai albarka da nayiwa kaina kwadayi daga zainab a yanzu don nasan shi daddy yaiwa Hafiz yayi facali dashi abaya.
Don yanzu nace ita nake so zan aura na wanke zukatan iyayyen mu daga bakin cikin da suka shiga a baya ashe hakan kuma laifi nayi babba a wajen ku yanzu ban sani ba.
Daddy ko mum basu taba ban shawaran in nemi zainab ba ni karan kaina naga dacewan hakan gareta nakuma nuna mata bukatana ta amince da hakan ba cikin wani matsala ba.
Kayi daidai sai me hankali kadai zai fahinci manufarka mai sunan malam don manuface mai kyau Allah ya baka ikon zantarwa a yanzu makin a bari na waje yazo ya dauka ai gara gida a samu ance gida bai koshi ba ba akaiwa daji .
Alh sule ku dakata da zancen nan kome ya faru duk hafiz ne ya jawoshi a yanzu don haka yaje yayi hakkuri yanzu a daura da shi malam duk zancen nan ya kare.
Daddy what kana nufin kaida bakinka kaba da go ahead a daurawa mata aure da Aliyu hafiz ya fada daddy ya wani kalloshi yace ka rufe min baki sakarai a wajen nan tun kafin ranka ya baci yanzun nan.
Kana son mayar dani mutumin banzane a idon jama,a kome yaron nan abinda yayi yayi kyau don me kuke son ku ruguza muna zumuncin mune wai ?
Kai Garba ka dakata idan an sauko daga jumma,a sai,a daura auren a masalacin don kowa ya sheda hakan.
Ina shike nan kowa yasan matsayansa a yanzu a wuce wurin da kyau kan gara dai kowa yasan matsayan nasa zaifi sauki babana ya fada ya juya ya fita daga falon.
Nan Hafiz din ya tayat da wani sabon hayaniya waishi bai yarda ba an nuna masu girma ana son a cuta mashi don haka shi sam bai yarda da hakan ba zai je kotu yai kara.
Daddy yace saika dawo shashasha kawai wanda baisan ciwon kansa ba aina fada maku wanan abin da wuya ya yuyu kun ki yarda don nasan halin garba da kafiya idan aka tabashi har inyna da gaskiya yana da wuyan sha,ani.
Baidai da mutncine kawai yadda kai masa har Garba yana da bakin musawa agareka kan dansa yarinyar wajen wa take waya dauki nauyin karatun nata ina kaine ?
A,a ga wanda ya dauki nauyin karatun nata nan zaune tun farko na fada mashi bada yawuna ba shida uwarshi sukace su iya daddy ya fada.
Amma dai ai a hannunka take ko kaike rikonta baba Auwalu ya kara fada tsam Addel ya mike yana fadin zan shiga in gaida dasu mum don ban shiga ciki ba.
Baba isah ya iya tofa mashi a fito lafiyaya gaidasu yana fita yana jin suna fadin abindai baiyi dadi ba yaron nan sam baiyi tunane ba bai kuma maida halarci ba gaskiya.
Hayaniyar da yake ji daga part din mummy baisa ya tsaya wurin mum ya shiga tana falonta zaune sai ganinsa tayi da mamaki ta amsa mai sallama tana fadin dama kana hanya kaima ke nan ?
Tun dazun nazo ina falo dasu babane da sukazo dama na nasa hakan nasan akan zancenka da mamane wanan taron nasu ko ?
Shine kagani ba kagani nasan abinda zai faru ke nan a karshe yanzu sun kiraka sunci ma mutunci abanza abindake yuyuwa aishi mutum keyi ba wanan da dukkanku kun sani abin ba zai kai ko ina ba.
Yakai mum don kuwa bava Garba ya gama magana idan an fito jumma,a za,a daura aure yau insha Allahu zan fita yanzu don akwai inda nake son zuwa yanzu.
Yana fita baifi minti biyu ba Dada nashigowa cikin fada tana fadin ina yan cin amanan da basu maida ragon suna daga Garba din harke kubura da danki kun zamo butulu yai butulun kuma na karshe.
Ai kubura ana barin halak ko don kunya yau ina zaku kai alhakin yaron nan gashi can ya haukace muna tuburan mutum kamar hafiz yana irin wanan tabatan ai kasan an samu matsala in ba ai hankali ba.
Shi kuma garban da kuka hada kai dashi har yake ikirarin ko bayan ransa bai yafe ba an fada masa yarsace autan mata ko yaji ance mata sun karene a duniya ?
Dama ance dan kishiya bai taba zama naka yau Garba ya nuna min cewa dan kishi yake wurina to ni koda mukai zamar kishi da uwarsa komai bata diba ba a wajena don na shige gabanta tunda nice uwargida.
Shima tsohon mijin naki har in yabarwa dansa wasiyana na yaki kika munafunce mu to bai taba shiga min gaba har me akai akai Abule Abun banza mai zubin dan buzu ?
Idon Dada dai ya rufe maganganun data fadawa mum masu zafine da kunarai sai a gaba zakuji insha Allah mum bata kala ba har ta gaji ta fita daga part din ita da halimatu data rako ta a lokacin.
Haka ta barta da dibin mamaki na yadda ta iya rufe ido a lokacin taci mata mutunci taciwa danta da baiji bai gani ba gori ko tayishi kwando kwado a wajen ido rufe.

55 / 105