DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   84 / 105

249K to 252K   out of 313.1K words

riga kinci gabata idan ba godiyan mazuru zakiwa Allah ba kuma.
Ki dubafa nan Abu ta nuna yaran da hannunta Ainace ta karasa fadin kyautan Allah ke nan in bashi ba waya isa ya baka hakan lokaci guda tace fadi kedai yar nan ai ke Abu Allah ya tarfawa garinki nono ya rufa muna asiri .
Ta nuna ita Allah bai isa ba don bata kaunan raya sunnan ma,aikin Allah dayace a hayayafa al,ummansa sunyi yawa ranan gobe kiyama sai Allah ya barta da dubaranta ya kawo masake a rayuwansa ya kuma baku wanan yayan haka cikin dan lokaci kadan.
Kinga anan wani aya Allah ya saukarwa mata idan tana da ganewa saidai tsiyan abin kuma bata da fahinta yace don ranan munyi irin wanan zancen dashi ba karamin hakkuri yaron nan yayi ba a rayuwansa da yarinyar nan.
Duk da maganan da mama tayi min na fahinta hakan baisa na daina jin zafi a zuciyana ba saidai ina kokari wajen danne hakan a fili kada a gane.
Ba wani hutu nayi ba na koma makaranta ranan bayan na dawo daga school ina sauri don kiran da mama tayi min kan yarona baida lafiya.
Ganin wanan part din na Aisha a bude yasa duk saurin da nakeyi na shagala wata mace nagani ta fito daga ciki da kwali a hannunta sai daga baya na sheda maishi halima din nance kanwar mamansu.
Ban ko kallo inda take ba na wuce zuwa part dina kai tsaye da sallama nashiga suna falo zaune da mama din tana lalashin yaron nashigo suka amsa min mama din ke fadin kin karaso ba sai ince tun fitanki bamu zauna lafiya da yarin nan ba.
Kuka daine yaki kama madaran sai kuka yake faman yi tun safe na aje jakkata da gyale na karbi yaron rigan dake jikinsa na cire mai har permppers dinsa kafin na fara dubashi na dago kai ina fadin a danyi masa wanka da ruwa bamai zafi ba sosai ina zuwa na fada na kara daukan jakkata na fita da sauri tare da dauko wayata ina kiran hafsat don itace ke fanin yara a cikinmu.
Bayan nayi mata bayanin abinda na fahinta take fada min abubuwan da zan sayo nayiwa yaron a wani phamacy dake gaba damu na tsaya Allah ya taimaka nasamo maganin na juyo zuwa gida kai tsaye.
Ina packer mota sun fito suna maganganu tare da nuna part dina din nasan ba zai wuce gulman gyaran da akayi bane a yanzu gidan.
Motan dana bude na fito yasa hankalinsu ya dawo gareni duk da lapcort ke saman jikina sai gyare dana dora baki akaina saman kayan hakan bai hanasu yi min kallon tsab ba a lokacin.
Cikin sakewa nake fadin sannuku fa ashe kun shigo anty Usai tace munzo tun dazun ai baki gida lokacin nace Allah sarki har zaku tafi ke nan sukace ehh to a gaidasu mama don Allah na fada cikin sakewa kamar ba abindake damuna lokacin a rai.
Suka tafi ni kuma nashige ciki don in duba dana da mama dana bari a cikin damuwa suna falo tana jijigashi na zauna na hada maganin kafin a miko min shi na dura masa ya karba yasha sai lokacin na saka mai nono da kyar ya karba yana ajiyan zuciya kaida kai irin na yaran da sukasha fama da kuka.
Kafin naji zazzabin ya dan sasauta masa lokacin na dago ina fadin mama kinga dai zancen mu ya fito ko sai kikaga mutanen ki sunzo gyaran daki kuma yar uwarsu zata dawo gidan.
Wa ke nan kike nufi nace bakiga yan uwan mai shiyancan ba sun shigo ta kalli Aina tace yaushe lokacin Aina din ta dan zakuda tana fadin haba nikan ina ta jin motsi dazun din nan dana shiga wurun mu har da kamar dariya amma ban tsaya sauraron ko daga ina bane.
Yanzun nan nagamu dasu sun fito zasu tafi har muka gaisa okon Allah yaushe ke nan hakan ya faru kuma ?
Amma banji hjy kubura na fadin an daura aure ba ai don dadewanta gida irin haka sharia bai yarda ta tare ba tare da wasu shedu sun sheda hakan ba tunda saki ya shiga tsakaninsu tun farko har kuma ta dade a gida.
Ta dawo mana ai ance kome koma ma halinka mai hali ai baya barin halinsa don zatazo da sabon kissa da kisisina irin nata yanzu na daban kedai iyakarki ido dasu don Allah .
Illa iyaka dai idan suka shiga huruminki wanan kam bance ki kyalesu ba don aurene yanzu tsakanin ku ba yan uwantaka kadai ba wanan kam ki dauki mataki balle in Allah ya yarda ai ina nan tare daku yanzu.
Nasani ba karya mama ta fada ba zata tsawata din don dan zaman nan namu da ita idan nayi koshi yayi abinda ba daidai ba kai tsaye zataba maishi warning ya daina hakan agaban ka wurin zata nuna ita uwace a garemu.
Aiki ja Allah yasa mufi karfin zuciyar mu na fada ina kallon dana dake hannuna ya samu barci a lokacin ina dan taba jikinsa naji yayi sanyi ba irin dazun da jikin nasa yayi mugun zafi ba.
In gajarce maki dai a ranan haka na kwana a cikin damuwa a zuciyana wanda nasan mai karatu ba zaki fahinci me nake nufi da hakan ba idan ba kin taba shiga irin wanan ba.
Don nasan duk macen da hakan ya rutsa da ita a duk lokacin da akace fitinaniyar kishaya zata dawo ku zauna dole fargaba da zullumin da wace zata zo maki a wanan karon kuma ya kamaki to irin haka shine a kasan zuciyana a lokacin.
Don Aisha fa kinsan ba kyalen lasa bace ubangiji Allahne kadai ya dorani a kanta tun farko har na samu wurin bajewa ina sake rassa da saye a gidan.
Gidan da ba aimin tunanen zamansa na wata daya ba balle har akai ga zancen samun karuwa a tsakani sai gashi da ubangiji yasawa auren albarka har ankai ga tara iyali haka duk da manyan mu na fada wai gadon hakan nayi dashi kansa yaya din kakata wajen uwa tagwayece ita.
Hakama wace ta haifi mahaifin kakanmu namiji ta wurin baba itama irin wanan haihuwan namu tayi donshi dangi ke fadin mun dauko hannun hassanan malam ke nan duk wanda yazo abinda zai fada ke nan kun dauko hannun kakanin wataran har fiye da biyu sai kun zuba.
Irin wanan damuwan dake mai kishiya kika sanda akwai shine yaci zuciyana a wanan takin da zancen komen Aisha ya baiyana duk da banji daga bakin maigidan ba har yanzu.
Na kasa daurewa saida na shige dakin yaya na faki idon mama mukai waya da hauwana ta ban shawara shigen na mama tare da tausana kada in yarda in nuna zafin hakan agabanshi har ya gane nufi.
Indai itace yadda tayi kasasaba wajen auren ki ko gobe ta dawo ba dainawa zatayi ba don tun farko bata kaunan ki bama keba zainab da dama dole a yanzu bata taba kaunan ki kona munafunci har kowama da yafito daga zurian ku kingako yanzu shi ba zai yarda da hakan ba gareta ai.
Idan kin kwanta kin maida komai ba komai ba sai kiga tazo bata gane komai ba a karshe donshi hali zanen dutse ne ga bawa ba komai a tsakanin ku a baya.
Amma ta bude baki tace tana zarginki dashi wanda hakan ya juye ya zama gaske a yanzu to ko gobe sake maimaita kuskurenta zatayi indai kikai hakkuri zeey.
Ki jira mu gani zai fada maki idan bai fadaba ma ki kyaleshi don Allah su karata can gidane dai kin shiga fitan ki kuma insha Allahu abune da Allah ba zai yarda ba ko don yaran nan dake tsakanin ku a yanzu.
Abu dayane zan kara fada maki shine ki dage wajen tashin dare da yawaita sadaka da kyautatawa mai karamin karfi da kula da marayu kinga wanan idan kin rike har abada kin mata fincikau a rayuwa.
Munkai wani lokaci kafin mu gama wayan na fito na samu har su mama sunje sun kwanta zama nayi na hada tea nasha kafin na kwanta na kashe komai nashige dakina na samu yarana da mama ta shimfide min su don ita da manyan take kwana a yanzu.
Nasani nauyin yaiwa mama yawa amma ta nuna tana iyawa ita kadai yau din nan na kara tabbatar da ba zata iya ba don haka na kwana da niyar fadawa mum a samo muna wata mai kula da hidiman yara ko zata samu saukin hakan.
Saboda jikin dana ban shiga school ba ranan na zauna dashi gida don yaran sunfima na farkon shiga min zuciya ina matukar son su a raina har mama na fadin don sunyi kama sak da ubansu yas nake mutuwar son su.
A nan idan ta fada nakan ce haba mama kinfasan dole in sosu don nasha wuya da cikinsu wanan yasa nake son su ai mama sai tace ki dai fadi gaskiya.
Aisha da tafito don jin dawowansu suna ba mama labarin gyaran gidan da yaya yayi komai an sauya an gyara gidan fiye da da zakicema ba cikin garin nan kike ba isan kina gidan.
Tace don Allah ki bari anty Usai yar tajuyo tace ke da kinwa kanki hasara kinga kishiyarki yadda ta koma wata matar larabawa da ita ke kudi sunyi gaskiya.
Farin nan nata ya karu tayi wani kiba ni bansan ko kratun me takeyi bama mutum na cikin wanan daular har zai wahal da rayuwansa ga karatu ga karatunsu da shegen naci da tsawon shekaru.
Bar yar iska in koma zata raina kanta da duk wanan budawan da takeyi yanzu sai na mayar da shegiya yar kallo a tsakanin mu.
Koke kiki koma yar kallo ba kun daiji ba zata koma don Allah ba kika koma mai da tsiya ai Aliyune kinsan halinsa kashin mumuke zai maki a cikin ruwan sanyi aikun saba uwar da yar suka fada.
Sai ta bata rai wai an mata mugun nufi ana binta da bakin baki ko yaushe ba ai mata fatan alheri nan uwar tace kaiyya!
Barin fada maki Allah yana amfani da zukatan mune yake muna abu daidai da halin mu wallahi in zaki koma da wata manufa a zuciyarki matukar yarinyar nan ita bata nufeki da hakan ba sai reshe ya juya da mujiya ki ganki kasa.
Kedai kiyi fatan ki koma din yanzu ni wanan zuwa gyaran dakin banso ayisa yanzu ba sai yazo din da yace amma kun tashi kamar gandoki ragwan ragwan kujewa mutane gida don shashanci.
Don dai nasan usaina ba zata yarda ai abin asha bane yasa na barku amma inda wa yan nan ne kadai wallahi baku zuwa ko ina sai yazo din.
A,a mama wallahi zamu fitone ma muka hade da zainab din ta dawo kuma muka gaisa lafiya tace mu gaisheku lafiya lafiya sai halima tace kika dai gaisa da ita.
Kin gani ba wallahi halima ku kiyayyi duniya kafin ta basheku mutum duk abinda zaiyi ya dinga cizawa kafin ya tauna.
Zaman yarinyar nan da Hummaira ba abinda ya taba fitowa daga gareta irin yadda kullum hummaira ke tusguna mata kishi haukane ko akanku aka fara wai ?
Tashi sukayi tsam suka bar uwar zaune a falon tana fada ita kadai don tace indai zata koma ta zubar mata da mutuncine tun yanzu ta zauna gida don ba zata sa a dauketa mutumiyar banza ba.
Wanan yasa suka koma daki sukaci gaba da kitsawa a tsakaninsu saida usaina ta leko tana fadin to ni zan isa gida saimu jira zuwanshi kuma mugani din.
Nan ta samu sun banje yan abubuwan da suka samo suna kara bayani akansu ta zauna itama aka dan yan mata don suna da yarda akan kayan dari bisa dari.
Jin matsin kiran mummy yasa ya shirya zuwansu Nageria ba shiri da sunan zai kawota ga family shi su santa karo na farko.
Amma da alkawarin zata dan sauya wasu halaiyanta ta boyesu har sujesu dawo din da wanan alkawarin suka bar can zuwa Nageria din.
Saidai ga al,adan ibo baisan basu yarda da hakan ba don suna isowa lagos mahaifinta suka kirata sukai warning din ta kada ta fara taka arewa bata nemi sa,a ba a gida.
Wanan yasa ta tubure masa kan sai ta ziyarci kauyensu taga kakaninta kafin tazo kano din duk yadda ya nuna bacin ransa bata yarda ta sauya ba dole ya barta ta tafi da sunan bayan sati zata sameshi kanon.
Shi kadai ya sauka ya kara girma sosai a yanzu yayi kyau irin na mashaya yadda giya ke hurasu zakicema baisha a yanzu don yanzu ya iya tako sosai kan harkan ba kamar da ba da yake sha kowa ya gane hakan.
Daddy dai kallo daya yai masa ya fahinci har yanzu ba a sauya ba saidai Allah ya gyara kawai abinka da jininka duk da hakan yayi farin ciki da ganin dan nasa a yanzu.
Saidai dare yayi daddy ya kasa barci yana tunane game da dan nasa kasancewansa haka duk irin tarbiyan da suka taso a ciki amma yau dansane hakan daga ina ya samu wanan matsalan haka dansa ya kasance hakane ?
Iya tunane yasan matsalansa dayane a lokacin da diyan nasa suka taso shine nuna banbanci da uwar keyin tsaye tasashi kwana da dadin baki saiya fifita danta acikin yan uwa.
Kwarai kuma yasan yanawa hafiz abu aboye baiwa yan uwan nasa ba kamar yadda ake samun hakan wasu ubanne sunayi akan iyalinsu.
Tabbas yasan da yana masa hakan akan ya kyautatawa uwarsa a boye zai masa sako wajen sau uku baiyiwa Addel da Nasir daya ba a lokacin.
Idan ma zai aika din to kuma tare dashi hafiz din kuma zai masu sakon wani irin ajiyan zuciya ya sauke gano hakan ashe illa ta jefasa yanayiwa kansa kansa bai sani ba a lokacin.
Lalai anan ya samu matsala da hafiz kome kayi a cikin sabawa mahalicin ka karshe kai zaka girbi abinka da hannuka tun a nan duniya.
Wanan kudin suka jefa hafiz wani rayuwa ta daban a lokacin har ya fada shaye shaye bai sani ba yau gashi kusan abin ya zamo masa jiki ya kasa bari ayanzu .
Tabbas hjy malka ta cucesu baki daya saboda son kantane ya kaisu ga hakan alokacin ganuwar kurciyansu sun dauka gata da so suke nunawa Hafiz ashe illa suke masa a rayuwansa basu sani ba.
Haka kuma ba aiwa Allah wayau ke nan cikin lamarinsa yadda yabi son zuciya yake yawan tauye Addel a lokacin gashi yanzu shiya zamo mai taimako a garesu baki daya har ita hjy malkan.
Don yasan yayi abubuwa da dama a boye wanda ita abokiyar zaman nata baiwa iyalinta sai na hjy malka din da sunan itace maiyiwa diyanta hidima a cikin jikinta.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

8?? 4??
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Zaune nake saman sallaya ina lazumi karfe shidda saura na safe bayan idar da sallah asuba wayana dake lake a charge ya dauki karan kira alaman kira yana shigo min a lokacin.
Hakan yasa na daga da sauri zuwa wajen wayan don a zatona abokan karatunane zasu fada min wani information game damu don nabar school da wuri jiya na dawo gida don kaina dake dan sara min.
Nayi mamakin ganin sunan ya Addel a scream din wayan na dauka da sauri ina sallama gareshi tare da fadin ina kwana ya amsa sallaman shima da fadin zainab kun tashi lafiya ko ?
Alhamdullahi yaya na fada ya katseni da fadin ya jikin Abdulrahim kuma yaji sauki sosai na bashi amsa yace don Allah ki shirya kije yanzu gida ki duba daddy yanzu mum ta bugo min waya daddy baijin dadin jikinshi.
Subbahanallahi meya faru kuma ko shekaran jiya sunzo nan duba Abdul ai na fada cikin mamaki yace kina jina kiyi maza kije ayi duk abinda ya dace don nima gani nan zuwa kano yanzu.
Ina jin hakan nasan lalai abin babbane tunda da alaman hankalinsa a tashe yake magana a lokacin na basa amsa da yanzu zan tafi insha Allah.
Sai kin kira idan kin isa inji don mum tace min baya gane mutane ma a yanzu subbahanallahi na fada ina daukan key din motana dage gefen gadona ajiye na nufi kofan fita banma kula daya kashe wayansa ba lokacin.
Dakin mama na nufa ta idar da sallah tana gyarawa Abba kwanciya na shigo a hargitse ina gaida ita tare da fadin mama zani gida yanzu yaya ya bugo min waya ba lafiya gida zanje in duba daddy ne yau aka tashi ba lafiya dashi.
Duk na rude don yadda nake magana tace

84 / 105