Chapter 37 Reading DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc Arewa Novels

DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   37 / 105

108K to 111K   out of 313.1K words

ya tabu kenan ta wanan dalilin ?
Kada kice haka kubura barta kawai mu koma gida wajena na dan wani lokaci albashin idan daga baya zata dawone saita dawo din bayan komai ya lafa akarshe duk da ban fatan tayi wani dogon zawarci a yanzu gaskiya.
Fadin hakan da yayi kuma saiya kayar min da gaba anan suka kwasa dasu ina duke sai aikin kukan danakeyi a lokacin duk da bamai sauti bane dai.
Karshe dai Dada din tace idan ya dage ga hakan bataki ba amma fa kafanta kafana don ba zata yarda baba ya tafi dani gidansa ba tunda bashi ya kawoni kano ba.
Dole ya koma lalashinta har dai ta fahince shi dole suna ji suna gani ya daukeni muka tafi gida sukuma sukace zasu kwashe kayana daga baya idan sunyi shawaran yadda za,ayi sai labari daddy yaji cewa baba ya daukeni ya mayar dani hannunsa ai ba tare da sanin sa ba.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

3?? 7??

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Kwance nake saman gadon innan mu datun danazo ina dakjn kumshe da sunan rashin lafiya wanda a zahiri bawai zance ga abinda ke mun ciwo ba lokacin.
Kawai dai gaba daya yanayina kunci da takaicine suka taru sukai min yawa tare da tunanen makomana a lokacin .
Kamar daga sama najiyo muryan daddy suna gaisawa da inna dake waje tana faman aikin abin karyawan gidan hakan yasa na dan zabura daga inda nake ina kai ido kan agogon bangon dakin inna din naga karfe bakwai saura na safe a lokacin.
Da sauri na dan yunkura ina mikewa zaune tare da kara fargaban zuwan daddy din don nasan a kainane wanan zuwan nasu din bawai zuwan wani abu bane..
Falon namu suke nan naji muryan baba ya fito suna gaisawa inda daddy bai tsaya karban gaisuwan nasa ba yake fadin Garba ni zaka nunawa kai ka haifi mama da har kaje har gida ka daukota ban sani ba ?
Haba yaya nina isa inyi hakan naji baba ya fada daddy din yace ai gashi kuwa kayi har ta kwana a gidan ka banda labari saida darene hjy take fada min data shigo duban jikina.
Hjy ta fada min komai dakace ba,a kyautama ba sai a bakin yan uwa ka samu labarin matuwar aurenta ni gani nake na isa da zainabu ai don ko bata da marabi dasu Nafisa dana haifa a cikina.
Wanan basai kafadaba yaya yanayine kawai ban kuma daukota nan don wani abu kawai ta dawo nan din ne don samun natsuwa a gareta na kwana biyu don na dauka da nan da can wajen ku din duk dayane ai.
Wani murmushin kasaita daddy yayi kafin yace to a ban yata mu tafi gida idan hakane don acan muka kaita gidan miji don yanzu an samu matsala ba zakace ka daukota ka dawo da ita nan a yanzu.
Adaiyi hakkuri yaya a barta nan din na dan lokaci idan yaso daga baya hankali ya kwanta sai ta koma gida daddy babbane don haka bai tsaya dogon jayayya da baba ba don ya fahinci me hakan yake nufi.
Dan shiru ya biyo baya kafin daddy din yace ina ita mama din take yanzu hjy ta fada min koda kukazo bata jin dadin jikinta ina son in ganta daga inda baba yake ya kwalawa sunana kira da zainab zainab ko tana barcine har yanzu ?
Bari na tayar da ita baba Asiya ta fada ta shige ciki da sauri falon ya kara komawa shiru na dan lokaci kowa da abinda ke cikin zuciyansa a lokacin.
A dan darare na fito kallo daya zakai min ka fahinci ina cikin matsakaiciyar damuwa ko ciwo a tare dani da yar sallama nashigo ina saye da blue hijjab mai hannu daya sauka min har kasa ya rufe min ko ina na jikina.
Kusa da daddy din nakai na zauna ina fadin cikin yar siririyar murya nake fadin sannu da zuwa daddy mama yaya naganki a haka ko har yanzu jikin ne ?
A,a daddy naji sauki na fada ina sake dukar da kaina kasa naji yace dani mamana you seens worried meke damun kine ki fada muna mufa iyayyenkine baki da wasu bayan mu a duniyan nan.
Ko har yanzu kina son mijinkine mu nemosa a gyara auren nan kinsan zan iya a yau din nan kada kiji kunya ko nauyin idanun mu mu masu share maki hawayenkine kin sani.
Da sauri mm a dago kai na kalli idanun daddy ina fadin ko a lahira daddy bana fatan hakan ya kara kasancewa a tsakanina da ya hafiz kawai dai damuwace da yadda mutane zasu fassara abin nake duba.
Murmushin takaici naji ya sake ya dan muskuta yana fadin komu mama ba zamu kara maki fatan zama da hafiz ba a duniyan nan a yanzu ma ina nadaman hadin da nayi maki dashi.
Kada kace haka yaya kaddaransune hakan dama akwai wanan zaman rubuce a tarihin rayuwansu don haka ba makawa sai anyi wanan zaman tsakaninsu koba yanzu ba baba ya fadi hakan.
Shi nakan tuna nayi shiru garba saidai nasan kulba jima kulba dade sai alhakin mu ya kama hafiz a,a yaya kada kace haka don Allah zamani ya bambanta yanzu da namu na baya don ko a baya din idan ka tuna ai akwai soyayya duk da akidan gidan mune kusan hakan akan aure fari ga yaro mace ko na miji.
Ka barsu kawai yaya kowa ya samu wanda yake muradi basai kaima wanin su baki ba zamanine yazo da hakan yayan yanzu ba darajan iyayye ko kimarsu suka sani ba asalima a yanzu din iyayyen ne ke tsoron yayansu wani lokacin sabanin su yayan suji tsoron iyayyen nasu.
Na yarda da hakan duba ga yadda malka take bin yaron nan a yanzu zakace wace ke gudun bakinsane kada ya kamata na kyalesu ne a sannu duk zasu girbi barnan su a hannunsu tunda bata son ayi zancensa ko kadan a yanzu.
Jeki mama tunda mahaifinki yana neman yi muna shamaki a tsakanin mu ya fito filine ya fada muna kawai ya kasa hakan da sauri na mike na barsu da baba yana fadin ba haka bane yaya zata dawo ai idan komai ya daidaita.
Sun jima a falon don ranan a gidan suka karya tare da babana har daddy din ya ban tausayi saida zai tafine ya saka aka kara kirana yake jaddada min akan kada nayi wasa da karatu sai yanzune ma yaji dadin shawaran Addil na in koma karatu da farko yaki hakan amma yanzu abin yafi masa dadi bisa ga kowa.
Nan ya kawo kudi ya ban wai ko akwai wasu abinda zanyi tunda ban kusa dashi nake ba yanzu naki karba yayi min jan ido na karba ya tafi.
Abu na farko dana fara haduwa dashi shine matsalan abin hawa don mashine ga babana bamu da mota gidan mu saidai ban yarda na nuna komai ba haka na shirya ranan monday na tukari school a motar haya abinda na dade banyi ba ke nan .
Ganin su hauwa yasa na dan sake suko da basu san dawa gariba sai sheri suke min wai shigan cikine ke damuwana na narke haka nidai sai murmushi nake masu bance wa kowa komai ba a cikinsu.
Saidai sun fahince na sauya sosai don har hakan yana son taba min karatuna lokacin da yake hauwa din ta girme muna da taimakonta irin shawaran da take ban ne har na samu na dan fara sakewa.
Saidai nakan rigasu fita kafin a tashi zan bar makarantar ko kuma in jira idan sun tafi zan fito nima in kama hanya zuwa inda zan samu abin hawa.
Duk ina hakane saboda gujewa surutun kawaye don kada su fara tunhumana na kuma gode a cikinsu ba wace ta fahinci hakan a gareni.
Zaman gidan mu kuma zance ba yabo ba fallasa don bama dasu nake wuni ba sai shidda na yamma wani lokacin gab da magariba zan shigo gidan don haka banda matsala.
Duk da hakan nakanyi kokarina sosai wajen taimakawa inna da yan wasu aiyukan gida kafin na fita da safe haka kuma idan na dawo nakan da taba dan aikin wanda ba,arasa ba dai.
Abu dayane shine ba sabo sosai tsakanina da yan uwana yanzu don suna daukana kamar bakuwa a cikinsu duk da sun sanni a baya ina zuwa kuma gidan har in wuni amma sai suke daukana bakuwan gidansu yanzu.
A bangaren baba kuma yana iya kokarinsa na ganin na ya kwantar min da hankali don daya dawo kasuwa zai nemeni ya dan ban tsaraban daya dawo dashi yace in diba inba yan uwana sauran.
Haka kuma idan dare yayi ya dawo daga sallah zamu zauna dukkan mu gidan ana hira kowa na fadin abinda yake zuciyanshi na wunin ranan.
Zan iya cewa dai we ar freely da iyayyen mu don rayuwan muna baya da muka taso a cikinsa har yanzu bai canza ba a gidan.
Sai hakan yake dan rage mun damuwa sannu a hankali na soma mantawa da abindake zuciyana a baya har nakan manta da zancen wani aure nawa idan ba wani abu ya jefo wanan tunanen ba yazo min.
Sai ya kasance a dan lokacin har na fara mayar da jikina ina kuma dan walwalana kamar kowa don yanzu babu wani fargaban dake damun zuciyana saina karatun da nakeyi kawai shine a gabana.
Yanzuma din jerabawane ya kusanto muna yasa banda lokaci ko dan zaman da mukeyi da baba idan ya dawo a yanzu na daina ina daki ina fama da karatu.
Rashin zuwana gidan daddy da farko bai damu mum ba amma yanzu yakai ta fara korafin an rabani da ita da karfi da yaji dai nakan ce ba haka bane mum karatune dai ya rikeni yasa ban samun lokacin zuwa ko ina takanyi murmushi kawai tace dani Allah ya bada sa,an wanan karatun dai na amsa da amin.
Don nakan kirata yanzu din nedai da banda time yakai har wani lokacin itace takan kirani da kanta idan taji shiru mu gaisa.
Anty Nafisa kuma mukan hadu lokaci lokaci da ita mu gaisa tayi min korafin rashin zuwa gidan da banyi tace aiko don Dada da daddy ko mum zanzo a gaisa kada in dauki mutuwan aurena da hafiz kamar raba zumuncin mune a yanzu.
Wanan bai damuna don inda mukayisa nan nake barin zancen nata don nasan babu yadda za,ayi kuma nace yanzu na koma wajen mum da zama don na fahinci mahaifina ya karbeni kenan daga hannunsu.
Daki nake tun safe ina karatu don monday zamu fara jerabawa idan Allah ya kaimu sam bansan abindake wakana a falon mu ba ashe yaya Nasir da ya Addel sun shigo gidan har da su autan mum da basu kasan sun zo.
Sai ganin ya Nasir nayi a gabana tsaye yana fadin fadin lalai alhudahuda sarkin karatu ke nan wai zakice bakiji shigowan mu ba kome ?
Wani ihun murna na sake kafin kuma in koma ina controlling din kaina nace ni wallahi nayi fushi ma ace wai mutum yana da yaya amma sam ya manta da kanwarsa don ya samu wasu kannen.
Lah ji wanan yarinyar fa wai zaki tare da dora min lafi keda kikai aure kika manta da kowa yanzu ko kiran wayan kowa bakiyi ke gaki yar dadin aure ko ?
Baki na turo nace ai kaji zancen ni banda ya Addel waya damu da damuwana shi kadai yasan da yana da kanwa har ya damu dani to taso gasu ai a falon hardasu muhusin da Bello gaba dayan mu mukazo bikon yar mum don kin gudu kin bar mum dinki ta damenu da korafin hakan.
Wai da gaske ya Nasir yace ki fito ki gani mana ya juya yana fita na mike da sauri na bi bayansa dagani sai yar rigar body hook ta zaman gida dake jikina baka a lokacin kaina daure da ribon don zama gidan mum yasa yanzu ban damu da yawan kitson dana taso a cikinsa ba wajen inna da.
Ina fitowa mukai arba dasu sai kunya ya kamani kuma na karasa har inda suke zaune cikin fara,a ina masu sannu da zuwa.
Suka amsa min sai na tsargi kaina da irin kallon da suke min din ya Addil ya anty Aisha na tambayeshi ganin yadda ya daure fuskanshi a lokacin.
Tana lafiya ya fada yana ci gaba da magana da innan mu akan aikin su muhusih din da sukeyi naji ina na fadin kai abin gwanin ban sha,awa wallahi.
Ba abin dadi kamar wanan ai yara suyi karatu su kare ga aiki a hannunsu kuma yace amma inna aisu mum basu son hakan sunfi son su dawo nan gida su zauna a gabansu yanzu.
To ta wani hanya kuma ai tana da gaskiyanta zama gidan shine alheri don gudun canza dabi,a kamar wancan dan uwan naku dako yaushe korafin Alh ke nan akansa.
Wai hafiz dama shi rayuwansa da banne da namu inna donshi a cikin gata yake komai nasa don haka ba za a hada wa yan nan dashi ba ai inna kawai dai abin iyayyene dai kawai.
Mikewa nayi zuwa waje na tasa Asiya gaba zuwa kitchen din mu na samu akwai kunnun ayyah da inna keyi na sayarwa a unguwa yakuma yi sanyi sosai na hado masu a tire da kofuna takai masu.
Dambun shikafa tayi ranan shima na zubo masu duk da nasan in sunci sai ta neme wani abincin amma karrama bako yana da kyau ai..
Ankoyi sa,a sunji dadin hakan don sun zauna sunci sosai har da ya Addel da bansa rai da zaici ba sai santin kunun ayyan yakeyi harda zasu wuce yana fadin in akwai in karo masu don Allah.
Leda na samu na zuba masu mai yawa aciki banko girga ba suka tafi sun zowa baba da tsaraba a cewan su duk da bamu bude komeye a ciki ba saboda sunce aba baba saidai drinks din dake fili da katon din sabulai da zamu iya ganewa lokacin.
Har kofa na rakosu na dan labe ina fadin zanzo har gida inyi masu sannu da zuwa lokacin ya Addil ke fadin kin dai gansu a nan ai tunda fushi kike da kowa na gidan ga baki daya.
Kin ban mamaki zeey da har kika yarda wanan abin ya rabaki da mamakin ai saboda hafiz zaki bar mum da Dad me sukayi maki da zaki masu hakan idan bada yardan ki ba baba ba zaice ki dawo gidan nan ba ai.
Shiru nayi na dukar da kaina kasa don ba abinda zan fada da zai yarda hakan ne shike jan motan ya tayar suka tafi ya Nasir yana ta mi sheri.
Kodana shigo na samu Rukkaiya tana fada waina kwashewa inna sana,arta na bawa yan gidan mu sun shaye mata naji inna na fadin ko abinda yafi wanan ta dauka ta basu wa zaiyi magana ?
Abinda hjy tayiwa yarinya ai yawa gareshi a duniya haka kuma babanku Alh don baki da kunya don yaranshi sunsha abin gidan nan yakai kina magana akul na kara jin irin zancen koba akansuvba saina bata maki rai ranan.
Haba Rukkaiya nima ai nasan da hakan da niyar biya na dauka tunda nasan abin sana,ace gani nayi suzo su tafi ba,a basu komai ba suna daukan nan gida a garesu hakan bai dace ba ai.
Kema da wani zance kike yarinya ki biyame wai dan wanan abun da suka sha komai ni yaran nan ban hadasu da kowa ba a cikin yan uwa kaf yadda suke daukan mu nasu koshi abin a yaba masune ai a gidan nan duba wacan tarin kayan da sukazowa mahaifinku dashi suwa zasuyi amfani dashi idan baku ba rashin kunyar Rukkaiya daine idan ya tashi.
Jin abinda inna ke fadi da yadda ta hau yarinyar da fada yasa na shige daki ba ranan ba kawai idan ina biyewa yadda yarinyar ke mun a gidan da tuni an dade da jin kan mu da ita.
Don takan nuna komai nasune su kadai su baba suka haifa duk da ance dama zaman gida gun macen data zauna a dakinta har kaddara ya dawo da ita gida abin da takan fuskanta ke nan na yarda da wanan maganan a yanzu.
Zuwan su baisa naje gidan ba kamar yadda nace don busy da nake a bakin baba nake jin ashe ya Addil din ya dawo wurin baba yazo mai da zance akan matarshi.
Da kuma zancen rikeni da baba din yayi wanda in anyi hakan ba a kyautawa uwarsu ba tunda muna tare yana bawa inna labarin yadda suka kwasa dashi har yace.
Ko daddy fushi yaje dashi har yanzu kan hakan da Dada don shine Dada tace ba zata zo gidan ba tunda ya nuna su basu isa dani ba shiya haifi abinsa.
Ina wanki yan tufafina da sukai

37 / 105