DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   103 / 105

306K to 309K   out of 313.1K words

kakeyi anya kana ganin kayiwa kanka adalci ke nan Addel ?
Mum karana takai gurinki ke nan ko bata fada maki yadda mukayi bane da ita ai nace ta kawo takadanta taki shine zata kai karana.
Me kake nufi data kawo karanka tasan darajata da kimanane yasa ta kira ta fada min in yaso sai ka kwashe ka fadawa ita zinarun naka tunda naga tsoron zainab din kaji yanzu.
Mum kin taba jin inda aka samo aiki bada takardu ba don Allah yaarinyar nan fa bata da takardu mum kuma taki ta koma makaranta ta nema.
Ba yadda banyi da ita ba akan hakan don irin gudun haka amma taki wallahi in yau ta kawo min takardunta goben nan zan samo mata aiki a garin nan.
Haka zancen yake itako ya za a samo aiki ba takardun sheda don Allah yanzu ka kara bincikanta aji tana da takarsun ne ta kawo ko kuwa.
Munyi zancen nan da ita fa mun ta daiga daman kawo karanane kawai akan karya mum din tace ina takardun karatunta datayi can england da taje karatu?
Babu mum nima daga baya nasan hakan na kuma bata shawara ko a nan abujane ta fara karatu taki tace ko tayi me zatayi dashi yanzu.
Kaji shirme ba yanzun kuma ta dawo tana fadan hakan kasan dai yadda za ayi da ita din da banson nuna banbanci akan iyali.
Yanzu mum haka kawai zan samuwa saura aiki in barta ita laifin me tayi min da zanyi mata hakan wallahi itace taki kadaiji abinda na fada ai yanzu yace zanyi tunane mum.
Sai kuma ta dauko mai zancen wani dan uwasa da baida lafiya tana sanar mashi tare da fadin da ace kabar ita zainab a nan aida kana zuwa gida akai akai don haka ka shirya kazo ka duba shi yace jiyan nan Basiru ya kirani yake fada min zancen ciwon nasa.
Amma munyi magana zasu kaishi nan federal medical center a dubashi duk abinda sukace daga baya zamuyi waya dasu na tura masu kudin zuwa asibitin ma .
Tace kaga mutanen mu ko amma basu kira sun fada min ba duk da ya mayar da wayan silent lokacin da yaji ta fara zagina hakan bai hana ina dan jinsu ba nima kuma na dan jaye a wajen kadab don kada inji abinda zai bata min rai.
Jin hakan yasa na danyi murmushi karo na farko da naji abinda tace din suka gama ya sauke ajiyan zuciya yana fadin mum kan gaskiya yanzu ta canza.
Murmushin na kara masa yace rashin mu a kusane da rashin diya mace data haifa ta dauki son da za,taiwa diya mace ta dora muna a yanzu ko mata ta dauke mu oho ?
Yadda na fahinta shine tafi son duk lokacin da zamuyi wani abu sai da saninta sai idan ta bamu umurnin yin abu zamuyushi.
Bandai yi magana ba don nasan ba hurumina bane hakan naja bakina nayi shiru ina saurarensa yace wanan karon zanwa Aisha tsiya a gidan nan lokacin ne nayi magama nace dashi.
Abinda take nema ke nan a yanzu kai magana ta kira mum ta fada mata ta sameka taci maka mutunci ta koma gefe tana dariya.
Kawai ni abinda naga yafi shine ka tsara yadda albashi zai dinga shigo mata duk wata koka bude mata shago ma,ana yadda wani abu zai dinga zuwa mata hakan zai rufe bakinta.
Kina nufin in bata jari ke nan nace haka naga yafi banda bakin cikin hakan a yanzu nikan son nima kayi min nawa hanyar dayafi nata ai.
Ba ita kadai nake aure ba ai yace dani nace Allah da a kiraka anama fada kanta kamar wani yaro gara kawai kabi shawarata shiya fi yace zanyi tunane da kyau kafin na shirya komai wanan ko kudin aka bata kina ganin zasukai wani lokacine .
Na rasa yadda takeyi da kudi ita baki gani a jikinta sai shiririta kuma ba yan uwa takeba ba ni wanan abin na Aisha yana daure min kai wallahi.
Nan yake fada min zancen su Nafisa da yaiwa kokari dawo da ita aiki Abuja din har su yaya da zasu dawo gida yake fada min daddy ya damu kwarai da zamansu can.
Kusan ko yaushe yana masa korafin hakan shiyasa yayi amfani da wanan daman a yanzu ya samo masu aikin yi su dawo gida.
Naji dadin hakan koba komai kila mum ta kawar da idonta akan mu yanzu tunda shi Nasir aure zaiyi zancen Asiyan mu kuma da muhusin na hana saboda nima bansan makomana ba ga mum har yanzu.
A shekaran muka je aikin hajji gaba dayan mu saidai hikimar da yaya yayi shine ni ta katsina ya biya min ita kuma ta kano ta tafi shi ya tafi ta Abuja.
Wanan yasa bamu haduwa balle wani tsegumi ya fito a tsakanin mu kuma a can din har mu saida hali a kasan mutane.
Wanan shawaran dana bayar shiya yaya yai amfani dashi don muna dawowa makka yayi amfani da shawaran saidai da yake dan halak neshi yadda ya bata kudin jarin haka nima ya dunkula ya ban nawa a raina nace aini gaba ta kaini gobaran titi.
Na kuma godewa Allah da yake nina kawo shawaran hakan a kanta gashi har alherin hakan nima ya shafeni yanzu.
Kudina baba na budewa katon shagon maganinsu na dabbobi yana shiga Nijar yana dauko maganinsu na can yana kuma alluran dabbobin har yanzu don mutane sunsanshi sosai a yanzu.
Madam din gidan mu kuma bata san dawan gari ba sai budawa yakeyi tana shakar iska tana sake min habaici wani lokaci ta dinga fadin.
Aiki ko wahala ai ta yanzu sam bata son aiki business dinta yafi mata tunda kudi nashigo mata account dinta bata da damuwan komai yanzu.
Mun bar wacan gidan da muka fara zama mun koma babban gidajensu duk da kusan a waje dayane saidai wanan yana da dakuna har shida hakan yasa ya ban ukku daya mama ke cikinsa zaune daya kuma yarana mata su Laura da yar uwarta sai daya nike amfani dashi .
Ita kuma tana da biyu a yanzu shi kuma ya kama daya a zauna lafiya duk da hakan an dan taba fitina don tace bata yarda ba da farko ban san me ta gani ba dai muka tare a hakan duk dai a gida daya.
Anty Nafisa da dawowanta Abuja ya zamowa alheri a yanzu tana da wata bakwai da zuwa Abuja Allah ya hadata da wani dan katsinan mu suka daidaita dashi yana aikin bankine ta auresa itace ta uku amma tana zaune a cikin kwatas din ma,aikata ita saidai ran girkinta yazo ya sameta gidanta.
Hakama mairo ta samu miji tayi aure wanan ne ya kaimu kano alokacin tsawon shekara biyu da barina kano ke nan don gudun mum dole ba yadda na iya tunda tasan munzo garin washe gari mukaje ga

DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

1?? 0?? 0??
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,


Komai a yanzu masha Allah dama ance mahakurci mawadaci Allah ya nufa gurin rayuwa ya cika garemu don yau kuwa ni zainab kt na zamo daya daga cikin likitocin da kasa take alfahari dasu a yanzu.
Da taimakon mijina ya Addel wanda ke kara min karfin gwiwa ga komai na rayuwa idan ya kalla ya duba abin ba illa a cikj addini da al,adan malam bahaushe zai ban goyon bayan abin yaga ya tabbata a gareni.
Ance duk mairai baya debe tsanmani ga rahaman ubangiji bawai haihuwan gata ke saka ka zamo wani abu a duniya ba wanan nufine da baiwa na ubangiji kawai.
Don idan hakane ni da aka haifa a kauye kauyen ma gungurumin daji da ko mota sai tayi wata bata shiga kauyen ba a lokacin nice yau ubangiji ya haska haka a duniya har ake alfahari dani.
Haka kuma dace da aminnan arziki yana kawowa mutun cigaban alheri shima a rayuwansa yan gidan mu sun kini don zama da mum don ina ba yar kowa ba a lokacin.
Ganin hakan nayi watsi dasu da komai nasu na dage akan karatuna da mayar da kaina natsatsa tare da bin umurinin iyayye tare da adduan iyayye shi zance yayi tasiri a kaina yanzu.
Na taso daga wajen aiki na nufo gida a gajiye cikin babban motana da yaya ya saya muna son yana da kokarin wajen sauke nauyi da hakkin iyalinsa.
Duk da yasan muna samu hakan baisa shi rauni ga sauke nauyin hakkinsa ba a kanmu wanda kuma bai damu da wai ina aiki ba ko wani abu komai ya tashi daidai yake muna shi.
Ehh zan iya cewa zaman da dama a yanzu dama zaman gidan na mijin bahaushe kowa ya san sai hakkuri don babu feedom kamar na sauran kabilu.
Dokana dole kibi yadda miji ya tsara yana son gidansa ya tafi masa haka kuma yau in kinji dadin rai gobe sai an saba maki hakkuri kowa keyi a gidansa muma din hakan ya kasance.
Bamu faye samun matsala dashi ba gaskiya inkinji matsalan mu akan yarane wani lokaci sabanin Aisha da har yanzu abu sukeyi kamar yara wani lokacin.
Ina da shekara ukku abuja ya fara fadan wai nayi planning don kada in dauki ciki nayi din don ina son yarana su dan tasa kafin na kara wani wahalan goyo ko ciki a yanzu saboda aikina.
Fitinan naga yayi yawa dole nasa anty hauwa ta cire min roban wanan yasa har na dauki ciki kuma.
Tun ranan da Aisha ta kyala ido ta ganin da wanan cikin suke jidali dashi nayi kamar bansan da hakan ba har fita sukayi tare zuwa ganin likita don dai a zauna lafiya.
Wanan bai dameni ba don aikina yasa na rage zafin kishi akanta yanzu nima sin kuma yakan fita dani wani lokacin har da yaran mu don me zan tsaya bata lokacina kan fada kuma akanta.
Abinda na sani Allah ya dorani kanta ta ko ina wanan nasa dole yaji zafina akan hakan ga miji nayi mata kutse kamar yadda take fada ga haihuwa Allah ya ban a cikin sauki ga kuma ilimin da nake amfana dashi duk ta sanadiyarsa aiko Allah yai min yaki don duk bata taba zaton wanan ba a baya.
Sunje sun dawo shiru har na haifo yarana maza wanan karon masu kama da ubansu sak dasu suma don yaran kusan kamaninsu daya.
Saboda yawan matsalan mu mata yasa ban tsaya wani hutu a gida ba sosai sati biyu nayi dole na fito bakin aiki tunda already nayi biyu kafin in haihu hudu ke nan.
Don ko a gidan ba wai hutu nakeyi ba har gida ake biyune da aiki don sun sani yanzu akan aikina baiwa idan Allah ya baka kayi amfani da lokacin ka ka more.
Su yaya Nasir sun dawo dukkansu Abuja yanzu da aikinsu yasa muka kara yawa kan wanan haihuwan dole inna ta turo min wata mace da zamu zauna tare sai muka kara yawa a part dina kuma ina jin dadin zama da matar sosai.
Ranan weekend yana gida tare da yaransa ga baki dayansu shidda ina wajen aiki sukayi matsala da ita har da doke doke dana dawo mama ke ban labari tace yau munga tashin hankali gidan nan Abbu.
Meya faru mama na tambayeta tace kedai bari matar gidan nan ba zata taba girma ba duk yadda akayi rashin hankalinta gadonsa tayi inaji ?
Kan yaran nan suna karatu da uban sai gata tazo ta sameshi wai akan me zai zauna da yara yasan lokacintane ita ba zai zauna da itaba saiya dawo wajen yara ya hanata hakkinta yaushe malam yake samun lokacin zama da yaran nan yanzu don Allah in ba yau din da yake gida ba ?
To wai son bai taso ba shine fa ta dawo ta fara zunduma masa zagi na yankar kauna da cin mutunci duk kun shasa ayau din nan can ga bakinta.
Haka ya bashi haushi ya tashi yayi ta dukanta kai ashe wasu matan tun a duniya baki yake halakasu Abu ?
Ta fada indai itace mutu ka raba tsakaninsu har da uwarku yau bata barta ba don tace ta gama da ita saura shi wanan ne yasa yayi mata dukan tsiya din ai.
Mama wanan ba komai bane a wajenta zaku gani gobe kamar basuyi ba indai itace ya fada ai yau yace shegiya ba zaki damu ba tunda kin saba shan dukan kaita a turai kin bude ido dashi wurin karantun ta zubar da ubanki ya turakiyi a can baki koyo komai ba sai shaye shaye na kayan maye.
Kin halaka mahaifan ki a yanzu Allah na tambayaki zakice ni kada in kula da yarana murmushi nayi ina fadin kaiya Allah dai ya sauwaka mama yanzun tana ina.
Tana daki tun lokacin bata fito ba aahe neman haihuwa sukaje abin kuma yaki duk ya fada mata yau a gaban mu wallahi.
Lab coth dina na zare saman kayana a hankali tare da sauke numfashi nace nasani ai amma suna zaton ban san hakan ba don shima bai fada min ga abinda zasujeyi ba ai.
Sai bayan kwana biyu da yin hakan wai kayanta ya iso daga indiya take min talla ko zan saiwa yara don nakan sa??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ya idan tayi odan indiya kona indonsia .
Irin hakan mukan dan zauna ayi hiran arziki da sauransu kafin haka kawai kwana biyu kuma ta shiga sha muna toka duka gidan.
Na mayar da hankali a tv ina kallon wani shiri na kiwon lafiya a wani tasha na turai naji muryanta tana fadin zainab kin dawo ashe ?
Na juyo ina fadin na dawo tun dazun ai sannu da gida nace mata don har gobe ina bata girman ta biyu da take dashi a wajena.
Na farko dai ta gime min a shekaru don koshi yaya ba zai nuna mata shekaru ba saina biyu girmanta na wace ta rigani shigowa gidan.
Taci gaba da fadin kayane suka iso nace barin bari kizo ki duba ko zaki zabarwa su Abba kayan suna da kyau ainun ta fada.
Aiko dai zanso hakan mu fara shirin bukin yaya Nasir tun yanzu waya ta dauka ta kira yar aikinta tace ta dauko kayan wuri kaza baki dayan su.
Aka dauko kayan yar aikin na fitarwa a haka na zabawa yaran kaloli har biyar da kuma takalma wasu na mata nagani suka ban sha,awa suma na dauka Rahana sabuwar yar aikina tana fadin hjy wanab aina matane nagani ?
Nace kin sani kodasu zan rufe ina son diya mace wallahi amma Allah bai banba sai Aisha tace diya mace ce akwai dadi wallahi kya iya dauka ki aje don kune masu haihuwa ai.
Ji Anty fa kema ai ba a debe rai ga tsamani ni har nagaji na debe rai ai da wanan nace no lokacine fa baiyi ba amma za,a iya samu ai insha Allahu.
Zainab ina ne banje ba zancen haihuwan nan amma abu shiru nace ki dinga hadawa da addua duk da hakan anty ai Allah maji rokon bawansane ta daiyi murmushi kawai.
Nace da zaki gwada wani hanya dana dora wata mata kuma Allah ya taimakemu ta samu har ta haihu last week akai suna ma.
Tace kin gani ba nikan nagaji wallahi nace ai ba a gajiya da nema a wajen Allah itama wanan matar sunyi 25 years da aure fa sai bana Allah ya bata.
Zainab wai da gaske kikeyi nace wallahi indai zakibi dokan maganin baki ketare kwanaki ba yanzu sai in rubuta maki shi a nema ki gwada.
Ai maiso bayaki ba yar aikinta ta fada tace lalaikan fatu don Allah ki taimaka min ki rubuta in gwada hakan yasa na bude jakkata na rubuta mata maganin na mika mata tare da mata bayanin yadda zatasha maganin na tsawon wata daya daidai ta gama period akeson ta fara sha zuwa wani lokaci period din.
Tace insha Allahu ko yanzun zan fita in nemashi sai ta ban tausayi wallahi rashin haihuwa masiface babba don yau akansa har godiya tayi min.
Zata daga nace ta ban account in tura mata kudin kayanta tana mamaki take a wajen na tura mata don kada tace ai shine zai biyata kudin taje tana jinini.
Ban taba dauka zata karbi shawarata ba sai gashi ta dauka ta kawo maganin gabansa tana nuna min waiko shine na karba na duba shine na kara mata bayani yadda zata sha din.
Allah da ikonsa tana shan searches kamar biyu Allah ya bata ciki mai laulayin da bai boyuwa don yawan amai da miyau da takeyi.
Duk da basu fada min ba amma na gane hakan da kaina sai abu dayane nayi magana yawan taunan kankara da takeyi kamar

103 / 105