DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   58 / 105

171K to 174K   out of 313.1K words

ga yan uwa tun yanzu kan hakan da haka barci ya daukeshi bai sani ba a wajen.
Washe garine yana fitowa yake jin Aishansa na waya baisan dawa take wayan ba don itama Aishan bata san ya tashi ba lokacin don weekend ne yana dadewa kwance yana barcin safe.
Sai yaji tana fadin ni zai kawowa iskanci ai in fada maki jiya ya gane kuresa don kememe nayi mai yana kallo bai taba ba yaje can inda yace za a bashi kwanciyan hankali ni za a rainawa wayau ?
Yaji sun kwashe da dariya daga inda yake zaune ya murmusa karan karan tv da yayine don ya saurari malamin dake wa,azi yasa ta gane ya fito a lokacin kala baice da ita ba illa tsarguwan kanta da tayi kawai alokacin.
Daki ta shiga yasan wayan zataci gaba dayi ya mike ya shiga kitchen dinsu kayane barkatai ya gani kitchen din duk yayi kura don son gyara a lokacin.
Tsuki yaja yana fitowa ya tsaya falo yana kwala mata kira ta fito a hasale itama tana fadin lafiya yace wanan wanibirin rayuwane mutum ya zauna a cikin kazatane wanan kibar kaya haka a kitchen cikin kazanta ?
Kai ke gyara min ko ni ka barni duk lokacin dana samu time zan gyara abina nagaji da wahalan banza kullun gyara kuma ba,a gani yar aiki ma zan dauko daga kano ta dinga yi.
Wanan kuma ruwanki nidai bana son kazanta kin sani wanan ai sai gida ya dauki wari in dai banice ke warin ba aida sauki ya kalleta yace towa ya sani tunda kin fara hakan yanzu.
Haba ina wuta ta sakashi lokacin a lokacin ta shiga fada mai bakaken maganganu take fadin ai namiji kake tunda na fara kazanta saika dauko mai tsabta mu gani gidan ga.
Yaushe kuma ki kwantar da hankalinki lokacine bai yi ba ai amma tana nan tafe karya kake wallahi saidai ku gama gantalewan ku a waje amma ba gidan nan ba.
Zakiko gani insha Allah Aisha zan baki mamaki fiye da tsamanin ki duk wanan iskancin da kike min kada kice don wani abu nake raga maki.
Ina tausaya makine don mama ina jin kunyar mama over in ba haka ba ke kinsa baki isaba wallahi kinyi kadan a gidan nan irin ki goma ma basu isheni ba.
Sunyi bacin rai sosai a tsakaninsu duk da hakan bai fada mata zancen aurenshi ba so yake yacfada mata ta hanyar daya dace taji ba,a cikin sababi ba.
Amma ita tana zaton bai iya mata komai cika bakin maza kawai yake mata ba zai iya daukan wani mataki ba a lokacin don ta damashi ta shaye ga komai take gani.
Haka suka zauna kwana biyu ba dadi kowa na harkan gabansa abinda ya bata mamaki shine wanan karon yafita daukan zafi sosai don bai taba mata hakan ba a rayuwansu.
Dole uwar naki tunda taba bukace dashi ta nemi shiri dashi tayi masa girki ta gyara gida ranan har kwaliya tayi mai kodaya dawo bai bita kanta ba yana daki zaune bakin gadonsa suna waya da mum tashigo.
Waya suke mum na labarta masa halinda suke da Dada da hjy malka na fushin da sukeyi da ita yake fadin mum ki kyalesu kawai lokaci zai nuna cewa kin fisu harga Allah.
Shigowan Aishan data tsaya mai a kai tana danjin muryan mum yasa yace mum bari zan kiraki mu karasa zance kawai ki kyale kowa don Allah ban,son kina kulasu.
Ya dago kai ya kalleta take fadin naga baka fito kaci abinci bane kai ya gyada mata yana fadin zanci ya mike ya shiga bandaki ya dade bai fito ba koda ya fito cikin shirinsa bai tsaya ba kuma ya fice gidan.
Tun ranan dasu Dada da daddy da mum sukazo gidan akayita ba dadi tsakanin Dada da baba tun ranan daddy yayiwa baba wani kalamin da zasu tafi yace.
Duk abinda zamuyi garba ya tsaya a tsakanjn mu kada ya shafi yaran mu ko iyalinmu don Allah don haka mama dai yatace ta dawo gida hakan yasa na koma gidan daddy washegari Sunday da yamma.
Monday kuma muka shiga yin test don karatun mu almost test ne da exam kan abinda mukayi practical don hakane karatun mu ya banbanta da saura ko yaushe busy muke.
Kuma daban muke din ko a school kamar specialist muke don baki ganin mu sosai cikin school din yawan kara kama kaina da nayi a yanzu da dora hijjab yasa suka fara min sheri wai ina son aure ko ustazancine ya taso min.
Saidai in masu dariya kawai bancewa dasu komai mairo ko fada takanyi dani wai wanan ai sai ace ko matar wani ustazu nake wa zai gane ni bazawarace ina hakan.
Nikanyi dariya kawai in basar don nayi alkawarin ban fada masu yanzu saidai idan sunji don ina gudun sherinsu don su din yan duniyane na karshe kowa na takaman itace a cikinsu.
Fada masun zaisa su zugani aikata abinda ban tashi yi ayanzu ba don haka naja bakina nayi shiru alokacin taimakon Allah gareni bamu haduwa da anty Nafisa.
Wace tun auren ma sau daya muka hadu a packing space din gida da yamma da ita na dawo ita kuma tayi kulliya zata fita horn kawai nayi mata ta mayar min dashi.
Dani da mum kuma zakice ba wani sauyin alaka daya hadani da ita yanzu yadda muke kamar da can baya haka muke har yanzu da ita ba wani sauyi na sarakuta a tsakanin mu.
Dada daice ban shiga gunta don a gabana taso wullakanta min iyayyena don haka nima yanzu na sharesu ko part din kowansu ban shiga tunda na gane abin son kaine.
Ban taba zaton ko tsamanin abinda Dada tayi min ba ko ta manta cewa itace tayi sanadin dawowana hannun daddy da zama inma ance da ita aka kula komai tun farko yanzu ban musu ga hakan.
Don son kai karara da nuna wa duniya ga jikanta a cikin mu tayi a lokacin don me ba zan gwada mata nasan zafin iyayyena ba don haka nima na sharesu baki daya a yanzu.
Harkokin gaban mu mukeyi a part din mu bamu nema mun rasa komai ba don mum ta cinma riban haihuwa a yanzu yaya ya kawo su yaya Nasir kuma su aiko dashi don haka muke cikin wadata har sai munba wani.
Ya hafiz ko ban kara jin komai a wajensa ba don ban tsamanin yana kasan ma dama yaudaran kansa ya tsayar dashi yana nufin ni ya yaudareni don sha,awata da yakeji kawai a lokacin da kuma nuna isa da gadara.
Sai Allah ya rufa min asiri ya hau dani kan sherin daya kula min din su kuma mahaukatan nasa basu ganoshi ba suka biye masa a munana min a lokacin anuna bamu data cewa dani da iyayyena.
Sam ban damu da rashin zuwan yaya ba tun daura auren mu don nasan yanayin aikinsa dama yana dadewa bai shigo kano ba waya ka wajibine kullun muna kai muna zance dashi.
Amma rashin zuwan basa bai taba damu naba ni don ban dauku hakan komai ba sai gashi wani jumma,a na taso daga barcin safe na fito wajen mum na zauna a falo.
Mum din ta kalleni tace yanzu Alh ya gama tambayanki nace kina barci nasan dole daddy ya tambayeni don na dade banje gaidashi ba nafada.
Kai mutum wai kinsan me hjy malka ta fada dama naji hjy ta fara fada nasan suyi zancen zasuce ai gashi nan yaron nan bai zo ba tunda aka daura aure matarsa ta rikesa.
Sai gashi ko yau Alh na tambayan ki take fadin dama ai in anki cin biri aci dila dolene ba zakaganta ba tunda zama daki ya kamata a yanzu .
Shine Alh yake tambayanta meya kawo wanan zance akanki kuma ko anyi wani abinne akan ki kuma kinsan su maza ba zasu gane ba sai cewa tayi a,a dai taga ko ina ban fitane yanzu dai ko yaushe ina daki.
Shine Alh ke tambaya na wai baki fita school ne nace to nidai naga kulun kina school din ban dai san abinda take nufi ba da hakan.
Kinga ke nan azatonsu matarsa ta hanashi alaka dake ita ta rikeshi yaki zuwa yanzu shima bansan dalilinsa nakin zuwa ba kana da sabon aure haka dole mutane su zaci haka ai.
Mum barsu su fada mana duk abinda zasu fada sun dade aikinsa yakeyi ko yazo nan me zai masu banda wani gulman da zasu dauko su dagwara muna kuma akai.
Dakuwa tayi min taba fadin karbi nan sakarai can inda yake ba gun matarsa yake ba ke yanzu ba matarsa bane kina zaman sa ko zaman wani kikeyi anan din ?
Waiko kinsan hakkin aure kuwa ke ina ga daga ke harshi baku dauki auren nan da muhinmanci ba bari kiji zaman aure dole zakuyi da dan uwanki a yanzu.
Bance kuyi fitina ko tashin hankali ba da abokiyar zaman ki amma kema yanzu kisan duk wani right dinki ya baki hakkinki na matsayinki na matarsa .
Kema kuma hakan ki basa hakkinshi na mijin ki kamar yadda zakiba kowa kika aura a waje nauyinsa don hakan zaisa a rufe bakin mutane masu bakin fata gareku .
Suna ganin ke baki isa Addel ya aure ki ba haka kuma shi matarsa bata bari ya auri koma waye ana ganin nina hadaku don kawai na fashe haushin matarsa akaina nayi hakan.
Dukar da kai nayi kasa ina sauraren mum din don ba wasa ko sanyi a fuskanta lokacin don haka na fahinci zancen da mum ke nufi har cikin zuciyanta hakan yake.
Allah sarki uwaye mata sun ga jiya sunga yau akan yayansu wasu ma ganasu gana yayansu dana mutanen gari duka sai abin ya taru yai masu yawa lokaci guda hakan kesa kwana biyu yanzu da zaran yara sun fara tasawa abubuwa da yawa ke taruwa akan mace ta tsofe ko wani ciwo ya kamata Allah ya sakawa iyayyen mu da alheri amin.
Zancen mum din ya tsaya min a raina sosai kamar yadda tayi min fada na fahinci tayiwa ya Addel shima fada don ko cewa yayi min zainab kece kika nuna damuwan ki da rashin zuwana ?
Kamar ya yaya yace naji mum tana fada nace a,a saidai in maganan dasu Dada sukeyi kan matarka ta hanaka zuwa na fadawa mum kada ta damu da zancesu.
Na dauka dai kece kika damu har yasa tayi min magana naso na barki a gida harku kare wanan zangon zuwa lokacin nagama gyaran inda zaki zauna.
Amma yanzu ma ba laifi zan shigo ayi maganan tarewan ki sabon wata inaga hakan zai kwantarwa mum da hankali don ba zata gane shirin da nake sonyi ba a yanzu .
Akwai wani program da abokina ya fada min suna dauka a federal government akan dannunku na likitanci shi nake planning na turaki kuna kare wanan karatun naku.
Abune da yake son kwakwaran shiri don haka nake ta faman kokari akan hakan amma kona fada iyayye ba zasu gane nufina ba na wanan shirin tunda an soma wanan tsegumin.
Ni kan banyi magana ba don narasa me zan fada a lokacin har muka kashe wayan lokacin zuciyana tana tunane akan zancen yaya din din na fahinci ba zancen tarewa a zuciyarsa yanzu.
Saidai ban fadawa mum yadda mukayi da yaya din ba nabarwa cikina zancen dukko da cewa ina samun irin wanan matsin tambayan daga iyayyena idan naje gida.
Inna zata fara bugun cikina taji wani hali muke ciki dashi zance muna waya dashi dai zata Allah ha kyauta amma mahaifinku ya damu da rashin tarewanki gidan mijiki har yanzu.
Shiru nakanyi ban cewa komai a lokacin hakan yasa tun abin bai damuwa na har ya soma taba min zuciyana gashi alkawarin da yaya yayi na zuwa baizo ba illa wayan da yayi sun fita waje da matarsa zasuyi wata daya ance saboda yaje wani course acen yace.


ZAINAB IDRIS MAKAWA






DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

5?? 8??

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Abi duniya ya taru yai min yawa don damuwan da nake ciki a wanan karnin wana shi ake kira da tsaka mai wuya ba auren baka huta ba anyi kuma wani fitina nason ya bullo kai ayanzu tsakanin mu.
Duk dani a bangarene ban dauki hakan komai ba da farko don yayi min bayani na kuma gamsu amma yanzu yawan maganganun da dangi suka farayi yasa na fara zargin ko gaskiyane matarsa tafi karfinsane din.
Amma ko in yaya yai min hakan bai min adalci ba don ko shi ya cusa min ra,ayinsa da karfi da yaji har na biye masa muka afka soyayya dani dashi.
Dukko da irin korafin dana sha agun bakunan jama,a dake tsoratani alokacin yake sakani tunane don kowa zai tofa idan yaji cewa zaiyi ke zaki iya matar Addel kuwa ?
Wanan idonta ya bude da yawa sosai fa irin matan nan ne dake zama fitina a gida gaba shiga wurin irin matan nan gangancine da izgili ga mutum.
Shi nakan tuna yanzu inji gabana ya fadi nakan ce zainab wani rigima ya kaiki sai kuma inba kaina amsa da so da zumunci to ina son yake yanzu ya dauki matanshi sunyi gaba ya barki nan da igiyar aurensa akai.
Hankalina kan tashi matuka idan na fara irin wanan tunanen gashi yafi zuwa min da dare idan nazo barci lokacin da ko wani bawa keson hutu da natsuwa.
Har yakai a yanzu na fara yarda dako asiri dai ke aiki akanmu ne don ban yarda kai tsaye yaya yana iya abounded dina haka akan wata mace yadda muka shaku dashi da irin kalaman soyayyan da yakan fada min a waya.
Zakice ba zai iya taba hakan ba idan ya fadi wani abu ko yayi wani abinda saidai ke kiji kunya amma shiko a jikinsa tunda na mijine.
Amma haka kawai tun bayan daura aure nake hango wasu sauyi ga yaya din gareni duk da anawa bawa uzuri don haka nima na nuna mashi ban damu ba kuma ban yarda na zake ba in ya kira zan dauka idan bai kira ba a zauna lafiya haka muke yanzu dashi.
Wanan yasa naso kaucewa don na fara tunanen saka hannu aikaiwa lamarin namu don yadda auren namu ya kasance ko kusa ban kawo matarsa ba nafi danganta hakan da bangaren mu ne don suga yadda za,ayi auren da suke ganin nacin amana ne a wajensu.
Sai daga baya nabawa kaina shawara da ke zainab ki natsu kibarwa Allah lamarin ki kada ki yarda shedan yayi tasiri a zuciyan ki kan cewa wani yayi hakan ki dauki alhaki wasu.
Haka yasa na basar nacigaba da rokon Allah tsari da kariya da neman daukaka da fin karfin makiyana wurin ubangiji subbahanahu wata,alah.
Wanan damuwan da nake ciki yasa aka fara samun bakin cewa na rame kwana byuin meke damunane haka saidai nayi murmushi kawai in basar da zancen.
Sai gashi ranan na dawo agajiye na zauna falo a nan nayi kokarin rage kayan jikina saboda zafin da akeyi alokacin mum dake fitowa ta saba cewa dani kin dawo mama mu gaisa ?
Amma sai naji sabanin hakan ranan cewa tayi tana fitowa subbahanallahi mama haka kika fada me yake damun kine wai haka ?
Kardai ince kinsa rai ga tunanen mijinkine kuma yanzu har kika fada haka lokaci guda kinyi wani fau dake kamar wace tayi ciwon kwana biyu duk kin fige ba dadin gani.
Da sauri na dago kai ina kallonta nace mum aiko banji na rame ba zafin nan ne kawai da a keyi da karatu ya ramar dani mum bamu da hutu fa ko kadan daga school wata rana zamu kwasa muje asibiti a can zamu wuni tsatsaye muna bin ward ward ana muna lectures.
Haba dai inda karatu harda wani abu indai zancen Addel ne gara ki fitar dashi a zuciyan ki aure daine an riga an daura na fada maku kuma ba rabuwa sai mutuwa .
Ki barshi tara masa nakeyi muna nan zaizo ya samemu duk ya gama gantalinsa da matarsa dole dai su dawo gida su tarar damu wata rana don haka bana son ki sakawa ranki damuwa saboda shi kinji na fada maki.
Nasihan mum ya karasani watsar da komai nakoma facing din karatuna haikam don ko yanzu ba lokacin wasa bane garemu ko banza don yanzu zakayi wasa ka samu matsala.
Mun sha fama akan mairo data samu mataala don hakane na kara dagewa sosai ga karatuna lokacin duk na dakatar da komai duk da zancen yaya Addel ba yadda zaifita min a rai amma cikin kashi dari na cire sittin alokacin gaskiya karatuna kawai nasawa gaba.
Dan abinda ke hannun baba shi ya fara

58 / 105