DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   94 / 105

279K to 282K   out of 313.1K words

tsakiya yasan a nan nake kwana murda kofan yayi yashi a rufe gam saidai na ciki inba barci yakeyi ba zai iya jin maishi a lokacin.
Juyawa yayi ya koma dakinsa ya dauko waya ya danna min kira yaji wayan yana kashe a lokacib tsuki yaja ya dangwara wayan saman gadonsa yakai zaune.
Tunane ya fara kan abinda nakewa fushi haka shi baiga abin fushi ga zancen nan ba saidai dama idan ina da wata a kasa kan zancen zanyi wanan fushin.
Yaji din akwai abinda bai kamata mum ta fada min ba a wajen don shima baiji dadin hakan ba to amma kuma ai mum uwatace ko banza zata iya fada min abinda ranta keso a zauna lafiya.
Zaune yakai bakin gadon yana cigaba da tunane a zuciyarshi shima fa ya fahinci akwai wani sauyi dangane da mum akan zainab yanzu gaskiya to amma meyeke faruwane haka ya kasance.
Da irin wanan tunane barci ya daukeshi a wajen ya kwanta a rigigine har baisan ya saceshi ba saida ya falko ya gansa haka yaja tsuki yana gyara kwanciyarsa tare da jin wani iri kasan zuciyarsa.
Allah ya taimaka ya samu ya koma barcin nasa a lokacin don har ya soma a inda ya tsaya sai asuba ya tashi yayi sallah a gida.
Bayan na idarne na fito na hada abin karyawa ko su Laura ban tayar ba a lokacin nikadai nayi aikin komai na kamnala na gyara wajen saida nayi wanka na fito na kaiwa mama nasu har daki muka gaisa nace aiwa yaran wanka.
Zan fito daga dakin su Laura din muka hade dashi a ciki ciki nayi masa ina kwana ya amsa min sama sama ya nufi dakin mama yana sallama dakina na nufa na dan kwanta.
A can wurin mama sin bayan sun gaisa take fadin tana ganin zata koma katsina tunda zainab ta kammala karatunta lafiya kaga yanzu tana da lokacin zama gida cikin iyalinta.
Yace akan me kuma mama ko an karayin wani abune bayana tace a,a ba abinda ya faru sai alheri dama yaran nan suka tsayar dani garin nan yadda za,a barsu uwar na faman jigilan karatunta ba tare da wani babba a tare dasu.
Yanzu ko tunda ta kammala zan koma gida sun dameni da nadawo gida hakana suma suna bukatana ya gyara zama yana fadin a,a mama duk mai bukatan ganinki yasan inda kike ai.
Wallahi tun banyi aure ba nake da wanan kudirin a raina sai kuma ya kasance danayi auren da farko ga yadda abin ya kasance min da Aisha yasa ban daukoki ba sai wanan lokacin.
Nan zaki zauna tare damu har in babu wani matsala daga ita zainab din inma akwaishi a fada min in maganceshi mama amma nan gidan dankine halak malak babu inda zaki a yanzu.
Inma katsina kike son zuwa sai a kaiku idan zainab ta gama jerabawanta naso in na kare gidana nacan katsinan in dinga kai iyalina hutu lokaci lokaci.
Don su saba da yan uwa a can akwai rai akwai mutuwa mama in mune yau ba mune gobe ba don haka gara ka nunawa iyalinka yan uwanka tun kana raye.
Kinga gara su san yan uwansu najini sunsan kuma ya ake da wani alaka dake tsakanin mu da wasu wanan yasa nayi shawaran gini can katsina din yanzu ginan kuma yayi nisa sosai a yanzu haka.
Masha Allah kayi dabara malam Allah yayiwa rayuwa albarka hakan nada kyau sosai wallahi kaga zasu san yan uwa yan uwama MPPzasu sansu.
Don wayan nan yan uwan naku sai a hankali tunda kaji mahaukacin nan ya fara tutsiburutsunsa haka gara ka yi hakan shine alheri gareka da iyalinka tunda sunsan raba daya biyu yace kwarai mama.
Duk da mum wai idan nayi hakan daddy ba zaiji dadi ba mama tace da dansa yayi haukansa a kanka wani mataki ya daukar masa kaidai kawai hakan shine daidai a gareka.
Ko ita wanan idan ma bazata kaisu wajen danginka ba ga zainab nan ta zuba iyali ai saita kai nata ita tunda can ne tushenta itama ai.
Murmushi yayi yana gyara zama yace wai Aisha kike nufi mama ai ita wanan bata san Annabi ya faku ba har yanzu don ba wanan a gabanta.
Yanzu fitinan da mukeyi shine wai a dole sai in tafi da ita Abuja tunda dama can take zaune in bar zainab a nan kuma mum ta kama mata hakan don har karana takai gun mum din wai naki zuwa da ita abuja ina mata yawo da hankali .
Akan me mama ta fada yace shina gani nima mama yanzune zuwan zainab ya zama dole ai tunda ta gama karatunta can nake aiki ina raba hankali gida biyu yaran sun isa karatu a yanzu ina son sakasu makaranta a can din bada dadewa ba insha Allah.
Wanan shine shawara mama tafada yace wai a,a sai barsu a nan kusa da ita hankalinta zaifi kwanciya kafin ya dora mama ta tare da fadin.
Kwanciya dame akanta suke yanzu bansan abinda ya shiga kan kubura ba yanzu game da zamanku da zainab ?
Ga yarinya matar rufin asiri anyi fari anyi baki duk ba a jinsa a bakinta wai ita kuma kubura ta saka a gaba haka.
Na rasa me yake damun kubura wallahi ina jiye mata kar yarinyar nan ta kasa hakkuri ta fasa wata rana .
Sai idan an fada mata gaskiya tace sun mayar dakai shanun tatsa ita da iyayyenta kana abu baka sanar da ita akan iyayyenta da yan uwanta.
Umuran nan da sukaje ta dawo tana jinini wai uwar ashe bata da hali saida na kwabeta gashi kuma tana fadin da tayi mura a madina itace tayi ta dawainiya da ita sai a watse a barsu tare tana kula da ita harta samu lafiya me kuma take nema yanzu don Allah ga wanda yai maka haka ?.
Yayi murmushi yana fadin mum damuwan ce kawai ke damunta a yanzu damuwan datayi ta hadiya a baya sai yanzu take samun fitar dashi abinda na dauka ke nan amma bai kamata tayi haka ba kan zainab ko don irin halarcin da iyayyenta sukai muna abaya.
Kirikiri mama iyayyena suka zaunar dani lokacin suna kokarin aibantani gaban kowa kan hafiz har gori amma haka baba garba ya rufe ido yaci masu mutunci ya nuna nima dane sai baba yusufa daya tayashi a lokacin.
Kaikan aiba ka manta ba ita kan ta manta da wanan a yanzu nifa tun kan auren yarinyar nan Rukkaiyatu hjy kubura ta sauya wai ka kashe kudi baka neman shawara sai abinda zainab ta sakaka yi a zancen kakeyi .
Murmushi yayu yana fadin mum ke nan nan muka tashi da zainab mukaje neman shawaranta ita ta tsara ga yadda za ayi lokacin fa .
Shiyasa nace wallahi damuwace kawai ke taso mata a yanzu ba komai ba mama sai ana tausanta din kafin yarinyar nan ta farga.
Ai ta farga mama zainab tasan komai ta kuma fahinta saidai bata san laifin ta gareta bane shine kawai babu kuwa don ba zatace ga laifin yarinyar nan ba mama ta fada .
Tace ki zauna da yarinya tu tana karama kinsan halin mutanen yanzu kuma ki dawo kina masu haka abin gaskiya sai addua ni kan in an barni sai ince aikin asirine hakan.
Asiri kuma mama waya damu da zamansu da zai tsaya masu asiri irin wanan tace Allah sarki kai dai ayi adduan Allah yasa ka gane hakan akwai matsala sai kabi a sannu a rabu lafiya da kowa .
Ya jima suna zance kafin ya mike ya fito ya samu yaran nacin abunci saman wani babban mat da suke shimfidawa su karya ya dan tsaya wurin su kafin ya nufi part dinsa kofana yakaiwa kallo yana rufe duk da yasan ina cikin dakin a lokacin.
Daki ya shiga ya fito ya dauko wayoyinsa har zai fita sai yaga bari yayi breakfast don haka ya nufi dinning don ya karya din ya hango ba,a shirya komai ba a wajen.
Ya juya zuwa dakina cike da tunane kodai kayan abinci sun karene tunda har yau naki daukan kudin da yake aje min bai hana idan zai wuce kuma ya aje min wasu na kawar masa saman drower na aje mai.
Ya tura kofan ya shiga kwance ya hangoni nayi rub da ciki kamar barci nakeyi a lokacin ya tako zuwa bakin gadon tare da dan ja min kafa yana tambayan ina abin breakfast dina ?
Nace ban aje ba yace ba,a girka dani ba ke nan kome don naga yara na karyawa a waje nace naji jiya kace muci abin mu shiyasa.
Wai zainab kina ganin haka yafi maki alheri ke naki sallon ke nan ki dafa mutum a cikin ruwan sanyi har ya mutu kome ?
To naji kace damu muci kayan mu yace ehh mana abincin da kike dura mi ne kawai bukatana a wajen ki ko kanki da kika hanamin na kwana da kwanaki kina ganin hakan kiyi min addalci ke nan tunda gani maciyi bari ki zauna ki ta ban abinci ba biyan bukata ko ?
Shiya fada nina naji kunya amma cikin dakewa nace me zakayi dani yanzu kuma tunda matarka da kake kauna kakeso kowa kuma yake so don anga can hankinka yake .
A yanzu ta dawo dama ni ai an ajeni wacingadi kawai gidan nan ashe yanzu ko matar ka tadawo dole in jaye ko inga wullakaci idan na nace da binka.
Wani kallo yayi min kafin inga ya juya da zumar barin wajen sai kuma ya juyo ya kalleni yace bansan nufinki ke nan ba ai yanzu na sani duk lokacin da kika sauko daga rudin shedan ki dawo hanyar daidai ai kanki kike cutarwa a yanzu bani ba.
Nace babu ruwanka idan na cuci kaina din abinda zai fidda nine nakeyi kiri kiri ba kunya don an mayar dani sakarai haka ka dawo kana rawan kafa kai ga matarka ta dawo.
Ai ba sakarai nake ba na barta dakai kuje kuyi tayi shike nan ai gara inyi gaba in nemawa kaina mafita tun yanzu da zama ana kafa min dokan dole don nice sakarai a cikin matan duniya
Waya kafa maki doka akan Aisha gidan nan ya fada cikin tsureni da idanunsa da suka kada sukai ja a lokacin don bacin rai.
Nace koma waye dai na barka dama ba wanda yayi min dole a kanka ninace zan iya yanzu kuma ba zan iya ba din shike nan ko ?
To ni hakkina da aka tauye min ban yafe ba tunda ina son abina kirikiri kike min rowan akan abunda Allah ya mallaka min shi.
Don Allah keko tausayina bakyaji ina zaki da alhakin hakan a kanki zainab na jefa masa wani irin kallin takaici ina fadin.
Ai bansan kana da hakki a kaina ba tunda banga ka damu dashi ba yanzu ko da idonka ya bude ka gama jagula wancan kakeson dawowa nan kaji nasa kalan tona yafe aje aitayi can din indon zainab.
Ya karkada kai yace zainab zainab kina ban tausayi wallahi koda yake nasan dama sai naga hakan saboda kawayen nan naki idonsu a bude yake dole kiyi hakan ai yanzu.
Su zugaki kiyi min iya shige su fitar dake gidan cikin yayanki su koya maki bin maza au zargin da kake min ke nan ko yace ban zargeki ba ban kuma taba zarginki akan hakan ba abinda da suke so ke nan dake na hango yanzu.
Sai kin fita su dawo suna bina in shedani nake kalansu kinga sai in biye masu ki koma jin haushi hararansa nayi nace suzo ai gasu ga gidan in wani dadi ke cikinsa yanzu.
Au gidan nawane ba dadi a yanzu don Aisha ta dawo ko lokacin da bata nan ai bantaba jin kince ba dadi ba sai yanzu ashe kema dai kin iya kishi haka ban sani ba kema ?
Kishin wa zanyi ba dai Aisha ba a yanzu ni zakaci abincin namune in zuba ma ko kuma can zaka kaci son ban bakin ciki idan kaci can din.
Eeh ai naga alama sosai kuwa ba fahinci komai a yanzu don ko ba zainab dita ta asali dana sani bace a gabana ba yanzu.
Kamawa yayi hakan don naga ana son raina min wayau nida iyayyena da basuji basu gani ba haka kawai ana dora masu sheri shike nan don Allah yayi mutum baidashi a cikin dangi akace haka zai tabbata .
Meye amfanin haihuwa dama in Allah bai baka ba sai yaba yaranka amma ankasa gane hakan ala dole komai da dukiyan ka nake facaka sai an durkusar dani kasa.
Zainab mekike son fada min ne kuma yanzu nace aika sani na taso daga kwancen na fito na barshi a dakin yana mamakina.
Koda ya fito abincin dana adana masa a kitchen don gudun hakan na dauko ina jerawa ya ganni saidai bai tsaya ba naga ya fita part din Aisha ya nufa.
Barci take sosai a dakinta ya kare mata kallo kafin ya fara tada ita yana fadin waima kinyi sallah ta watso masa kallo tace sallah yaushe kuma tana dauko wayanta ta duba time tace ni banko sallah ma .
Yace shi yasa kike barci haka babu ko gyara ki duba time ki gani Aisha isan wani ya fado haka yaya zakiji don Allah ban tsamanin falon tunda na tafi ya samu gyara a wajen ki.
Yau zan gyara idan na tashi ta fada tana hamma ya juya take fadin nace yaushe zanje gida muyi sallama dasu kada tafiya ya girsheni ban samu zuwa ba.
Ina zaki ya tambaya cikin mamaki hakan yasa ta tashi zaune tana fadin bangane ba Aliyu kana nufin kano zan ta zamane kome ?
Sai ya kara hada rai yace wanan kuma sai mun zauna daku naji shawaran kowanku kafin na yanke hukunci yanzu.
Amma kasan in kayi min hakan ba kai min adalciba Aliyu ya kalleta dakyau yace akan me na taba yi dake cewa sai Abuja zaki zauna ?
Ita wanan watau in barta a kano ko don kinfita asali kome look Aisha tun farko saida na fada maki tsarina a yanzu kin sani bake kadace gareni ba a yanzu.
Zainab dama karatu ya hana inje da ita Abuja yanzu kuma tagama karatunta ina son saka yarana makaranta a can insha Allahu.
Au don zainab da yaranka ke nan yasa ba zaka dani Abuja ba yanzu sannu mai yara tanan kuma zaka bullo min ashe ko akwaita akan yaran nan indai don ka tauye min hakkina da sunan yarane ?
Ni za a kawowa lauya yanzu daka fada mi uwar yayanka yar dangi ce yasa baka kaini can ba to ko ka yarda ko kada ka yarda satin nan abuja zan tafi na gaji wallahi.
Ai kaji irin ta abinda nakewa gudu ke nan akanki Aisha gashi tun ba,akai ko ina ba na fara gani to bari kiji wallahi ki bini a sannu yanzu a zauna lafiya shine mafita garemu.
Yara dai dole in saka diyana makaranta haka kuma ke nan ba zaki kula min dasu ba a can idan kin tafi tace kaima ka sani don ban zama boyi boyin wata.
Aina sanda hakan ba yanzu ba tunda kin nuna hakan a gaba saboda wauta irin baki da baki tunane komai yinsa kikeyi gaba gadi.
Yaran da kiri kiri kike nuna min baki son shigowansu ma nan wajen ki a gabana idan na kaiki abuja ke kadai kece zaki zauna min dasu a can ?
Don kawai nacewa yaro ya bar goga min hannu a kujera shika rike tun ranan au ba zan rike ba ko kin manta komai na falin nawa haka kuma danane yake tabawa .
Aiko kuka ta saka ganin hakan ya juya ya bar mata dakin rai bace yana tafe yana bin falin da kallon takaici a zuciyarsa.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

9?? 3?
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,


Uwar na zaune taji waya ta dauko tace nikan isan kin kirani har gabana faduwa yake Hummaira ya akayi sai taji yar nata tana kuka a ci??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????kin wayan.
Lafiya take tambayanta nan ta fara fadawa uwar yadda sukayi uwar tace don Allah ya isa banson shirmen banza don Allah dama nasan wanan sakaracin naki bai gushe ba har yanzu ai.
Yanzun da kika kirani so kike ince dashi bai isa yaje da yaransa ba saike kome ki dinga yin tunane mana kafin kiyi abu don Allah hummaira.
Mama akan yaransa zai cuta min ko kan matarsa to tsaya wai cewa yayi ki zauna a kano ne kome da kike wanan kukan haka ?
Cikin sheshekar kuka

94 / 105