DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   41 / 105

120K to 123K   out of 313.1K words

zaune saman kujera yayin da mum da Dada suka kura min idanu mum ke fadin yaya me ya faru ?
Na dukar da kai na dan lokaci kafin in dago lokacin anyi daidai wani kira nata ya kara shigowa har wayan ya katse ban daga ba don nasan cin mutuncine kawai zatayi min.
Nace meya faru mum ta fada da dan karfi na dago idanuwana da sukai ja nace mum matar nan tana da hankali kuwa wai zagina takeyi in rabu mata da mijinta ko ta canza min kama.
Salati Dada ta saka tana fadin zata aika wanan yar zatayima abinda yafi hakan don ba hankali gareta ba mum kuwa kasa magana tayi don bacin rai a lokacin.
Sai gashi ya fado dakin da sallamanshi yadda ya ganmu yasa ya fara fadin meya faru na mike kawai nafice daga dakin saboda hawayen dayazo min a lokacin na bacin rai.
Yau gashi tun ba,aje ko ina ba zancen su anty hauwa ya fito ashe dama abinda take min kallo ke nan ban sani ba ta rasa wace zata zarga da mijinta saini zainab don Allah.
Dadace ta mayat masa da zancen ransa yayi mugun baci sosai a lokacin haka ya daure ya gaushesu kafin ya nufi wajen kayan dana hada din yana fadin bari nakai kayan nan mota indawo.
Ya fito yakai kayan kafin ya koma ya fito da mum din da Dada har zuwa wajen mota lokaci mum ke tambaya ina zainab din ina tare zamu gidan da ita.
Yace bari na kirata ya daga waya ya kira kira uku nadaga yake fadin kina inane kizo mu tafi mana nace ku tafi kawai yaya idan nagama zanzo gidan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

4?? 1??

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Motan yake ja kawai yayin da zuciyarshi yake chunkushe da bakin ciki da bacin rai yana faman tunane da kulla yadda zai fitowa Aisha din don yanzu kan tagama kaishi makura ga halaiyanta.
Ta rasa wace zata zageshi da ita sai zainab kanwarsa yarinyar da yake dauka tankar uwa dayace ta haifosu itace Aisha ta dauko bata masu suna a tare.
Abin bacin rai gaba mum da Dada Dada dako ba,ayi hakan ba zata fada don kiyayya a gareta balle anyi din yanzu kowa a family dinsu sai yasan da wanan zancen a cikin takaici yakaiwa sitiyarin motan duka da hannunsa duka biyu lokaci guda.
Mum dake zaune a gefensane ta kalloshi tana fadin ka bari ka saukemu kafin ka fara wanan haukan naka na banza ta isane ta fada ai don ba kaunar kowa naka take da alheri ba dama kai kadai takeso don haka bata son kowa yanzu.
Don tana ganin Idan tayi hakan ai zaka dauke kai ga zainab din da taga kana kula lamarinta a yanzu kakoga dole ta samu sherin da tayiwa yarinyar da zaisa daga kai har zainab din ku kiyayi junan ku a yanzu shine kawai wanan kissan data kulla maku ai.
Ai wanan yar takai makira ta bugawa a jarida har yaushe wanan miskilim mijin nata yake da lokacin tsayawa duban wata mace tana gabanshi da makircinta haka ?
Baidai tankasu ba har suka shiga get din gida ya fito ya budewa Dada kofa ya koma gefen mum ya bude mata sai lokacin yai magana cikin karfin hali yana fadin na rikekine mum ko zaki iya shiga ciki.
Zan iya ta bashi amsa a takaice ba tare data tsaya kallonshi ko kulashi ba a daidai lokacin daddy ya fito sai ganinsu yayi a kofa suna shiga gidan don baisan da zancen salmaman ba don shima yana fama da kansa a lokacin karfin haline kawai yakeyi.
Saida ya kwashe kayan kaf yakai ciki ya kunna na,uran sanyi kafin ya fito lokacin suka shigo har daddy din dake faman yiwa mum din sannu da jiki a lokacin.
Nan ya barsu zaune a falon ya nufi gidan nasa cike da bacin rai yana zuwa ya samu tabar falon tana dakinta dakin ya nufa ya sameta zaune tana waya.
Kallo daya tayi mai ta kawar da kanta gefe daya tana ci gaba da waya da yarta Usaina don tana labarta mata abinda tayine shigowanshi yasa tace bari zan kiraki anjima antu Usai.
Cikin takaici yace me kikayi Aisha cikin kura mata idanunsa da suka kada sukai ja a lokacin batayi sanyi ba tace dashi kamar me fa ?
Look Aisha bansan baki da hankali ba sai yau din nan don ko hakan da kikayi kin tabka babban kuskure a rayuwan zamana dake wallahi.
Aiko baka fada ba nasani nasan munufuncin da kuke kokarin kulla min don kana ganin wanan yarinyar a yanzu tayi clean ta kara kwandewa ake kokarin cuna maka ita da karfi da yaji kaiko kana afkawa don idon ka ya rufe.
Watau dama donshine ka matsa min saina nazo duk da zuwan yai min amfani a yanzu ai da banzo din ba ai ba zan fahinci makircin nan ba.
Tun jiyan nakula da akwai makircin da ake kullawa ai har kana wani sherini kana nuna kamar ni banzace dolene saina bi kowa ina gaidashi har ana wani daure min fuska ana shareni kai kuma ka biye ma hakan don ka nuna ni,,,,
Tas ya dauketa da wawan mari biyu masu kyau lokaci guda saida ta dafa gado kamar zai kara mata ganin har lokacin bata dagoba tana dafe da kumcinta don zafi .
Ya nunata yace ahir dinki wallahi in kina cin kasan ki ki kiyayyi na shuri Aisha ina kyakekine da iskancinki don kawai ina duban wani abu amma ba fin karfina kikayi ba ki sani.
Don haka duk iskancin ki da rashin mutuncin ki kada kice zaki kawo tsiyanki kan mum ko wani nawa a gabana ko don kinga ina kyaleki ban kula wullakancin ki kike tunanen kinfinkarfinane har zaki nemi ciwa mahaifiyana fuska a gabana.
Da kina da wayau da bakiyi hakan ba sakarai kuma ki sani ba komai ko zaton da kikeyi a raina amma yanzu kin haska min wata manufa a zuciyana zan auri zainab bako soyayyan da kike zaton mun fara ba kuma dole ki zauna da ita a matsayin kishiyar ki gidan nan muga abinda zakiyi din.
Kin tabka wa rayuwan ki kuskure babba wallahi na aikata hakan da kikayi don da farko ban taba tunanen hakan ba ga zainab amma yanzu ba fashi aure a tsakanina da ita sai wani ikom Allah zai hana hakan.
Tana dafe da kumci ga hawaye na zuba mata ta dago tana fadin wallahi karya kakeyi baka isa ba dakai da duk wani mai zugaka kan hakan baku isa ba indai nice.
Kuma sai kun raina kanku kan wanan cin amanan da kuke shirin min Allah ya tona maku asirin hakan don wallahi sai naga bayan ku nima mu zuba dani daku din.
Ya daka mata tsawa yana fadin saina tatakaki awajen nan yanzu don kin gama kaini makura da iskancin nan naki zaki gani kuma wallahi don sai kin raina kanki gidan nan ya fice yana jan tsoki.
Itako taci gaba da zaginsa tana fadin duk abinda yazo mata abakinta lokacin bai tsaya kullata ba ya shirya ya fice abinsa don gidan ma ya fice masa a ransa lokacin.
Nan ta zauna ta rasa meke mata dadi a lokacin ta dauki waya cikin kuka ta kira anty Usai dinsu tana fada mata yadda sukayi dashi din lokacin.
Hankalin anty Usai din ya tashi jin yar uwarta a cikin tashin hankali take fadin kece Aisha idan kika tashi tsula tsiyar ki baki tunanen abinda zaije ya dawo lokacin.
Jin kukan kanwar nata yayi yawa tace ki jirani ganinan zuwa gidan naku yanzu shi Aliyu din yana gidane tace D's a kyar ni ban sani ba ko yana nan ina dakinane kai kema Aisha wallahi sai a hankali.
Bata zo ba saida ta biya gidansu take labartawa mahaifiyarsu abindake faruwa uwar a cikin tashin hankali tace dama nasan halim nan na Aisha saiya kaita ga haka.
Ta dauki rayuwan turai ta dorawa kanta kamar bata san darajan aure ba komai acikin isa da izza takewa yaron nan don ta samu yana da hakkuri bai biye mata.
Yanzu ki tashi kije kiji amma kada ki biye mata kuyi rashin hankali don Allah ki samu ki lalabasu ki bashi hakkuri nasan bacin rai yasa ya fada mata hakan ko zata natsu.
Banda rashin hankali irin na Aisha ki mayarda yan uwan miji abokan gaban ki harda uwar miji don shashanci shi sakaraine da zai zauna tana wullakanta masa uwa yana kallonta.
Waima mama baki sani ba kanwarsa fa ta zageshi da ita yanzu wanan wani irin shashancine wai ga Aisha da har zata furta hakan ga mijinta shi sakaraine da zai kyaleta don Allah ?.
Kinji iskancin nata ko Aisha bata da wayau ko kadan wallahi nina rasa irin wanan halin nata na rasa inda ta koyi wanan halin nata ?
Suna cikin zancen saiga wayan Aisha din ya shigo don taga nawan yar nata bata zo ba lokacin ta dauka tana fadin Aisha gani tafe na biya gidane wajen mama.
Anty Usai kizo don wanan dan iskan so yake ya kasheni kowa ya huta cewa yayi wai saiya auri wanan yarinyar tunda har na zargeshi da ita.
Cikin mamaki yar tace mata Aisha da hankalinki kike zagin mijinki haka yanzu mijin naki Aliyu ne dan iska ?
Ki bari ganinan tafe yar ta fada cikin bacin rai ta kashe wayan tana kallon uwar tace kinji wautan tako har ya fada mata tunda ta zargesu sai ya auri wanan yarinyar.
Wai wace yarinyace haka ake wanan rigiman kanta uwar ta tambaya tace yarinyar nan mana da uwarshi ta rike wace aurenta akace ya mutu.
A lalai Aisha ta dauko ruwan dafa kanta da hannunta don ko ba zasuki ba tunda a hannun uwarshi take zaune dama aini kace kai kafi kowa iyawa sai a baka bautan gatari ka hade koma meye yanzu ita da kanta ta jawo wa kanta ai.
Tashi kije tun bai fita ba kiji meke faruwa idan ya kama inji sai ki kirani a waya in sameku yarinyar kawai an fada mata samun dakin miji haukane bada hakkuri ake hadawa ba wajen zama.
Nan zan bar yaran nan saina dawo in daukesu tace dama ai kije kiji musan abinyi ni shiyasa ko zuwanta garin nan bani kauna wallahi don ba,a zuwa sai anyi fitina kan abu daya.
Gida ya koma lokacin na dawo ina daki na shiga yin wanka koda na fito na sameshi zaune yana shan madara a glass cup nagaidashi ya dago yana amsawa tare da fadin ke yaushe kika dawo ?
Kafin na bada amsa mum tace ai bamu jima ba ta shigo motarkace ba zata shiga ba dama don haukan matarka donshi kawai taki zuwa damu nasani mum ta fada cikin bacin rai.
Mum na rasa hauka irin na yarinyar nan Aisha duk iskancinta ina dubawa iyayyentane nake raga mata mussanman ma uwarsu don mutumiyar kirkice ita.
Amma bata san hakan ba ita ta dauka fin karfinane tayi wanan karon sai tasan bata da wayau wallahi zan gwada mata halina da bata sani ba .
Dama ai manya sunce idan zakayi aure ka nemo yar dattawa ma,ana yar babban gida ance kuma yar babban gida bawai ana nufin yar gidan masu kudi ba ko mai saurata ba ana nufin yar dattijai mai tarbiya koda sun kasance tallakawane kuwa.
Yar gidan da suke da tarbiya da rikon addini tare da sanin mai shari,an aure ya kumsa masu mutunci ke nan don idan sunce ehh basu cewa a,a har idan mutum ya dace da hakan yayi dace dashi da yayansa.
Yayi shiru yana wasa da cup din dake hannunsa yana sauraren mum din ganin hakan kuma a gabana mum keyi masa wanan maganan yasa na yi saurin fadin.
Daga inda nake nace dashi yaya a zubo maka abincine naga madara kake sha yanzu sai naji mum tace wani abincin zaki zuba masa an dafa dashine ?
Haba mum rowan abinci kuma kika fara yanzu na fada ina dan dariya cikin son in basar da zancen na fara a yanzu kuma akan yayanki yaje matarsa ta dafa mashi yaci mana ba nan ba dan abincin da Amina ta dafo muna ina cewa kin huta da dafa wani shine zaki kwashe ki bashi yanzu ?
Mum ai hardashi aka dafo ina zamu kai wanan abincin mai yawa haka karshema ya lalace ba,aci ba ba sai a zubar ba idan ya lalace na wani irin juyo ina kallonta.
Ba wasa a fuskanta nace ayiwa yayan mu hakkuri don Allah ke zainab zubo min na zatama ba abincine a gidan ai nace akwaishi yaya dama inna tayi muna abinci da za,a kai asibiti ta zata muna can har yanzune Allah sarki yace na nufi kitchen din.
Na hada masa komai har ruwa dama in na bashi ina son in koma daki in kwanta don ina son hutu da natsuwa a lokacin don har lokacin raina yana a bace da zancen Aisha din matarshi.
Saidai zancen Anty hauwa yasa na danji sanyi a yanzu da tace tayi hakane don taga akwai shiri a tsakanin mu yanzu ko da tayi hakan ai zan jeye daga komai na mijin nata son haka kada in nuna bacin raina.
Ita da kanta zata dawo taji kunyar abinda tayi min din idan tana da kunya don hakane na basar da zancen araina nake kokarin nuna masa zancen bai dameni ba a yanzu.
Kodana kawo masa sai naji ya furta kallaman thanks a bakinsa yana kokarin jawo abincin zuwa gabansa ke nan dama yunwa yake ji a lokacin baida abinda zaicine yake shan madaran.
Kin ba yayan ki amma ni mara lafiya baki damu da ki ban ba shiyasa ai matarsa ta fara maku zargi don shashanci nace mum ai zan baki kema yanzu idan bamu bashi ba nasan can ba tsayawa zatayi bashi ba.
Tunda yau fushi take da kowan mu harni laifin yaya ya shafeni an sauke min masifa a kaina ai zanje gidan na bata hakkuri mutumiyatace bamu haka da ita.
No kada kije gidan nan da sunan bata hakkuri don Allah ita wacece da har zakije bata hakkuri tayi abinda zatayi idan ta iya mara mutunci kawai zanyi maganintane ai sai tayi dana sanin fadin hakan.
Kaci abinci don Allah da wanan zancen da bai karewa kullun ai tasan in tayi dama binta zakuyi ku bata hakkurin daga kai har zainab din matsorata shiyasa ta gwadaku ta gani me za,ayi indai kanawa kanka fada kayi.
Madam din mucefa mum dole ai mu bata hakkuri kodon yaya ke rufa min baki don Allah jeki dauko min abinci inci ta fada a hasale may be tsoronta takeji yasa zata ta bata hakkuri yaya din ya fada.
Jin hakan yasa na dan kalloshi bai kalloni ba sai abincin da yakeci abinsa nashige na debowa mum din abincin na shirya a gabanta.
Zan dago naji yana fadin yanzu kuna asibitine ko nace ehh amma mun kusa komawa school ai nan zuwa next month insha Allahu yace ok kafin lokacin zanyi kokari inga motarki ta iso saiki koma school din da ita kawayenki su daina roka maki ko ?
Zaune nake gefen kujeran da mum take zaune ina fadin mota yaya ni zainab za,a sayawa mota yace to menene baki iya bane kafin na bada amsa mum tace samu yafi iyawa ai.
Kwana nawane ta koyi mota ai rashin maida hankalintane yasa bata iya mota ba ko Nafisa ba zata koya mata mota ba gidan nan.
Wai wayaga zainab a mota wallahi idan naga mace tana jan mota yana ban sha,awa nakanyi fatan ace nice ashe ina da rabon shiga motar kaina nima.
Kibar murna in matarsa ta barshi ya saya maki ko kada ya shafa maki mai a baki da kun koma yazo ya share zancen ke kina nan kina faman saka rai.
Haba mum ya zan mata alkawari kuma in fasa zainabce fa yarki ai dole in saya kodon ke mum in har hakan zai saki farin ciki ya fada yana dukar da kansa kasa.
Ko yanzuma mum ai kinyi farinciki balle in motar ta iso na fada ina dan kwantowa mum din ajiki tace ga tsiya ni matsa don Allah kada ki karyani ina fama da jikina.
Ai Allah ne bai nufa ta samu mota ba wajen Alh lokacin wanan bakin auren nata da hafiz don Alh da bakinsa naji yana zancen mota don zuwanta school bansan ya akayi ba kuma daga baya naji shiru sai malam balane ke kaita school din.
Nasan ko sherin hjy malkane hakan itace zatace ba sai an saya mata mota ba a lokacin don bakin ciki irin nata ta dauki

41 / 105