DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   79 / 105

234K to 237K   out of 313.1K words

kike masu kenan .
Murmushin dole na kakaro ina gaida ita tana tattara kayan take fadin nikan yanzu gida nayi tunda oga yazo karfe shidda sai ki tashi kiyi alluranki don Allah kada ki makara.
Dama akwai alluran da za,ayi ke nan kuma tace ehh saboda maleria ya dan shiga muna son muyi flushing dinsa kada yai mata yawa a jiki son hakan nada illa ga mai ciki.
To amma zata iya yiwa kanta da kinyi hakkuri din kin kwana a nan tunda kinyi niyar hakan zaifi don Allah baida matsala ai zata iyamana take tambayana nace zan iya.
Rukkaiyace ta rakata waje ta samu mota don bada motanta tazo ba lokacin ya shiga dakinsa shi koda ya fito nace masa ai ta wuce yana fadan meyasa dare yayi aida ankaita yafi.
Sai ga Rukky ta dawo tana fadin ta samu drop ta tafi ai nan sai ya zauna dole yasani a gaba saida na dan sha kokon kosai dan guntun dana gutsura ma na kasa hadewa a ranan duk son kosaina kuwa.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

7?? 8??
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Karshe dai yaya bai yarda ba saida ya daukeni zuwa asibiti likita yana ganin yai mamaki don ya sanni shima kuma yasansa sunyi karatu a waje tare.
Cikin mamaki yake fadin doctor zainab kanwarkace dama don baisan nayi aure ba yace sister dinace ai nazo ka duba min ita meke damuwanta ne ?
Cikin ba,a likitan ke fadin wanan ai tasan aikinta koda baku kawota nan ba ai saidai idan baku yarda da kwaraiwanta bane kan abinda ta fada.
Nan ya juyo gareni yana fadin doctor ya akayine yau kuma gaki gaba as a peceiant ya mike ya zagayo inda nake idona ya fara duba naga dan shock a tare dashi.
Kafun yace muga hannun ki na mika masa ya duba sai ya dan kalli yaya Aliyu dake zaune ya tsureshi da idanu yana son jin bayaninsa a lokacin.
Ya koma mazaunin shi yana fadin watau kagane ne mutumina ina ganin sai anyi test a wanan zancen a kara tabbatar da abinda nake zargi amma doctor ke ya akai haka kuma ?
Sai na dan kalli ya Aliyun yace watau kagane doctor munsan da tana da ciki ai amma amaine yaki tsayawa da zafin jiki shine ke damuna wallahi wanan ne damuwar mu yanzu akanta.
Da sauri likitan yace Ok ta fada maku cikine ko ke bata wahala ashe so sorry naji tsoron ganin hakan ne aida farko kinyi aure ke nan ?
Saina dan kallo yaya ganin hakan yasa yace wait wai ko auren da Umar ke fada min ka kara kwanaki zainab ce ka aura dama ?
Dan murmushin daya sake gefen fuska yasa doctor din gane shine dai mijina yace mun gane mutanen nan bakin wayau gareku sai kuzo cirani kano ku tara ku kwashe abinku kuma.
Dariya ya danyi yana fadin abinda ya kawoni garin nan ke nan wallahi don shekaran jiya na koma sai gashi bayana kuma jikin nata yaki dadi haka ?
Aman yake damuna saboda tana wahala ya kawar da dogon zancen zolayan da abokon likinta ya tsayayi dashi a lokacin yace ai ita madam din naka tasan me zatayi ya kalloni.
Cikin wahala nace dashi nayi komai yadda ya dace abin yaki tsayawa yace dama hakane ai kinsani saidai ya dan lafa amma barin maku dabaran mu na tsofin likitoci mu gani nan ya dan harharda min magani tun a office din yace insha nasha.
Ya kuma hada wasu ya bamu kafin mu mike shima ya mike har bakin mota ya rakoshi suna magana yana tambayanshi wai har yanzu yana wanan gidan daya sanshi ne ?
Don yabi wajen kwanaki bai gane gidan ba yace ina unguwar kasan unguwar yana da kyau ai bazanso in tashi nan ba yanzu sun dan tatauna a tsakaninsu yake tambayan me zai bayar yace haba dai kanwar matanmu kuma staff dinace fa ?
Suka tafa hannu kafin yaya ya shigo motan mu tafi lokacin idona ya fara rufe don karfin maganin a gareni kamoni yayi da hannu guda yana dan bubuga min bayana tare da yi min sannu gida ya nufa direct dani barci mai nauyi ya daukeni nidai na falka naga mama azumi zaune a dakin ta zuba min ido inda ta sallame sallah a dakin.
Cikin murya na mara lafiya nace mama ashe kinzone tace ba dole ba mun dauka ai zazzabine kawai ashe abin ba haka ba dazun muka ganshi kwatsam da rana yake fada muna ai asibiti kuka fito yanzu.
Shine nace barin taso don Rukkaiya ba zata iya ba ita kadai shine na biyosa mukazo tare mun samu kina barci ai na dan jima da shigowa nan din har munyi sallah.
Azahar tayi ke nan na tambaya ina mikewa daga zaunen tace har munyi sallah tun dazun ai haka na samu na mike zaune na kai tsaye na nufi ban daki na dan jima a ciki tunda saida nayi brush da alwala nafito.
Bayan na idar da sallah ina zaune cikin kasala ya shigo yana fadin ashe ta tashi na dauka har yanzun barcin take batayi sallah ba ai.
Kaiyyah sallah maiciki ai ragagene a yanzu don ba,a tashinta acewan manya lokacin barcine ake karawa yaro cikin cikinta girma don haka ban tasheta ba.
Amma da yake abin na zuciyanta kaga ta mike da kanta ai tashi tayi amma isan mai ciki na barci ba,a faye son ana tada ita daga barci ba don lokaci na wani baiwan da dan cikin mace yake samu ko wani mai rai yana son hutu tunda ba ita kadai ke rayuwa a wanan lokacin ba.
Amma mama harda sallah ai a tayar da mutum yayi ko sallah abune dake cikin zuciyar mumuni dukkan musulmi na kwarai duk abinda yakeyi sallah dole tana a zuciyarsa saidai in addani bai zauna a zuciyar mutum ba.
Ya juyo gareni don baida na fadi a lokacin gareta yana fadin may zakici yanzu ga Rukkaiya can ta gama abinci ko a debo makine ?.
Tuwo nake son ci miyar ganye da kulikuli irin abincin mu na kauye da muka baro shi naji ina sha,awan ci alokacin ya kwashe da dariya yana fadin tuwo zeey ina za,a samo tuwo yanzu.
Cikin bata rai da jin haushi nace abarshi kawai idan babu ina za,a barshi kuwa tunda shi kuke so ai dole a nemo a kawo maki indai zakici dib mama Azumi ta fada tana mikewa ta samu Rukkaiya a falo tana tambaya ina za a samu tuwo da miyan ganye ?
Tuwo ta fada cikin mamaki nan suka fara mamare Rukkaiya din tace barin kira inna naji luckly sai inna din tace bari a kawo mata yanzu.
Na idar da la,asar Asiya na sallama da flask din abincin tana fadin sannu anty ya jikin nace da sauki yasu inna tace suna gaidake.
Ta turo min tuwon tana fadin ga tuwon tace a kawo maki wai nace sannu da kokari Asiya dan dauko min plate in diba a kitchen don Allah.
Naci tuwon duk daya banbanta da wanda nake so irin na kauye din nan da akeyi kuli kuli zalla sai yan kwaran ganye shi nafiso a lokacin.
Yana dakin tare dani har zuwa karfe shiddan yamma ana kira yasa waya a silent yaki dagawa sai shidda ya mike yana fadin yaufa zan koma amAbuja karfe takwas jirgin mu zai daga.
Na dan kallosa kamar da mamaki yace naga kinji sauki ai yanzun hankalina ya dan kwanta kuma ga mama tare daku a gidan kome ke nan zanji daga garesu insha Allah.
Cikin wata yar murya nace dama yau zaka koma ashe yace tafiyan ma banyisa da niyar kwana ba ai don daga wajen aiki na wuto zuwa kano ko gida ban koma ba don hankalina yaki kwanciya inbada nazo din nan ba nagani.
Amma kila in dawo weekend yanzu haka Aishama ce mata nayi tafiya ya kamani zuwa photharcountne kwana kuma ya kamamu a can bata san kano nazo ba.
Na dan sake dago kai na kallesa ina dan yake nace zuma saida wuta ashe haka ake shara min karya nima wani lokacin ?
Yace karyan me zan maki kai dai ita bata da fahintane dakece kai tsaye zan fada maki inda nake ai tunda nasan ba zaki zargi komai ga hakan ba akaina tunda kinsan halina.
To ai tafini sanin halinka nida ko kaya ban sauke ba itako shekaranku nawa tare da ita mai hankali yasan hakan ai ki bar Aisha kawai inda kika ganta don bata da fahinta ko kadan zargi da iya shege yayi mata yawa a rayuwanta.
Hakan dai kuma kake son kayanka ba mum kance don baka son a zageta gabanka yasa take batata a gabanka sai yayi murmushi yana fadin aina sani don haka takeyi.
Malam wai ashe yau zaka koma muryan mamane a kofa take tambayanshi yace eeh mama yau insha Allahu nake son komawa tunda naga jikin yayi dama ina da aiki da yawa a can tunda gaku tare da ita ni zan koma wajen aikina ke nan.
To Allah yakai lafiya kudai bakwajin nauyin tafiya amma kam sai dare ko safiya yace ai mama jirgi zanbi in koma dama dashi nazo.
Bayan mama ta wuce yace matan malam hamza din nan tayi kokari zan ba su mama kudin kashewa zanso in hada da ita don duk shigowa zan ganta tsaye tana taya Rukkaiya aiki.
Aina tana da kirki sosai wallahi na fada kullun duk fadin gidan nan sai tayi masa shara biyu wallahi.
Kai,kai,kai naga alaman hakan gaskiya ya kamata ace ana dan mata hasafin haka???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?n don karta gaji don mutum idan yana kyautatama kaima ka nami hanyar kyautata masa.
Yana kunna waya kiran anty Nafisa yana shigowa wayanshi ya dauka yana fadin anty lectura don haka suke ce mata don da farko kowa gidan ya dauka shi takeyi.
Tace bros yanzun nake jin wani labarin banza wai kazo da wani zance mummy tace a,a yace ai wanan zance ya wuce Nafisa wani munafukin ya fada maki ?
Tace bari bros wallahi mummy ta cuceni ta kuma zalunceni inga samu inga rashi haka don nasan ba mutumin banza zaka kawo min ba indai kaine.
Subbahanallahi zaki fara abin shirmenki ko tace bari bros towa ta aje min a nan don Allah ni ka hadani dashi kawai kaji inda rabo sai anyi in huta.
Iam sorry Nafisa ai na baahi Rukkaiyan gidan baba garba har zai turo iyayyensa dama dan sarkin wani local government ne shi gun aikin mu daya babbane shima a wajen mu so sai matarsa ta rasu wajen haihuwa.
Almost two years ke nan baiyi wani aure ba shine yanzu yace an matsa masa a gida yana son in samo masa mata cikin yan uwana don ya yaba sosai da yan gidan mu.
Shine nazo da zancen na gabatar masu mummy kuma tace ai baki rasa masoyi ba aurene baki tashi yi ba dama ni kuma da naji haka nayiwa baba garba magana zan hadashi da Rukkaiya ya yarda.
Kai amma mummy wallahi ta cuta min sun dade da ita suna magana kafin yayi sallama da ita din ina kwance saman jikinsa ina jin duk hiran nasu.
Bayan ya kashe wayan nace mummy ba zata taba yarda ba saboda hassada robon ayi hakane kawai dama yace nima daga baya na godewa Allah da hakan bai faru ba zainab.
Don mummy bata da dadi nayi sanadi abu yazo ya koma min ciki daga baya kinga hakan baiyi ba gara dai Rukkaiyan da nake iya controling nata yafi.
Zuwan Umarne yasa yaya mike ya bar dakin bai dauki komai ba yadda yazo haka ya koma nasan kuwa kada matarsa ta gane hakan ne don ko kaya bai sauya ba ya fita.
Mun idar da sallah isha,ine Aina tashigo tana nuna muna kudin da aka bata tana ya godiya da fatan alheri mama tana taya ta ta fadin .
Muma an bamu ai gashi kedai wai kudin kashewa ko a ina zamu kashesu muna cikin wanan aljannan duniyan me zamu nema mu rasa a gidan nan yar nan ?
Aikuwa mama kaya shayi dai gashi kayan zakin nan gashi nan balle uwa uba abinci sai wanda ranka yakeso zaka zaba ina kuma zaka kwadai a waje.
Ba laifi naji dama ga kuma mama da Rukky dake dan rage min damuwa hakan yasa na dan samu karfin jikina dole na koma school don hankalina yana can kada a wuceni da karatu in samu matsala yasa dole na daure nake fita.
Acan Abuja kuma bata san komai ba son bai fada mata ba wasu mata suke bada kafan da ake samun galaba akansu wani lokaci.
Abinda yasa nace hakan shine rashin mu,amulan da Aisha batayi da yan gidan miji yasa ina samun galaba sosai akanta yanzu.
Don da nasan cewa tana mu,amula da wani da ba yadda za,ayi bataji zancen cikin nan nawa ba har saida ciki yakai wata bakwai a jikina ta samu labari tana mussun hakan.
Koshi ta kawarta taji don muna asibiti kawar nata suka shigo dubiya mun fito tare da mairo sai gasu zasu fita muka tsaya muka gaisa na danyi gaba take fadin .
Mairo wanan ba kishiyar Aishan Gentle bace Aliyu kt tace itace mana baki santa bane dama tace ba wai ganinta nakeyi ba ai dama tunda Aisha bata zama garin nan.
Tace itace tau cikine pa a jikinta mairo tace ga zahiri kina gani kuwa ciki har ya tsufa haihuwa ko yau zata iya insha Allah tace what ?
Ita shashan soso miji ta tsaya tana hauka kin gani ko kishiyar Aishab Gentle ce fa wanan sister din Usainan habibu ta Nasarawa.
Suka wuce suna gulman akan cikin da suka gani jikina din sai bayan kwana biyune suka hade da Usaina gidan buki take fadin ina Aisha ?
Tana Abuja da mijinta kinsan ita ke can da mijin zaune Abuja kishiyan tana nan kano an barta saidai ya dinga dan zowa lokaci lokaci.
Allah sarki ita bata da komai har yanzu kawar ta tambaya tace kinsan halinta ai yanzu ga kishiya koda yake karatu takeyi in anyi magana tace ina taga mijin da zai mata ciki.
Ai kuwa itakecan don ko kishiya ita taga miji don mun ganta asibiti shekaran jiya da tsohon cikinta wallahi da sauri usaina din tace ke ki bari don Allah tace wallahi ciko tsoho a jikinta ko raliya tana tambayan wace suke tare a lokacin.
Ta juyo tana fadin wacece wai tace wace muka gani asibiti mana nace kishiyar kawatace din nan tace kwarai kuwa wanan matar mai kyau din nan ba ciki ko tsoho.
Innalillahi Usaina din tace wallahi banjin Aisha tasan da zancen nan amma barin kirata muji haka sukaje gefe ta danna mata kira yana ringing bata daga ba har ya katse.
Ta sake danna wani sai can ta daga tana fadin kina ina haka inata kira baki daga ba tace wallahi wayan na daki yanzu na tashi barci yaya akayine tana tambayar yar nata.
Tace wai ashe cikine tsoho ga amaryan ki shine baki fada muna ba tace wace amaryana usaina tace zainab mana amaryan Aliyu .
Inji uban wa gunwa kikaji zancen nan tace wallahi ance ciki ko tsoho ne gareta har ya girma tace what wai tsaya ina kikaji zancen nan ni bai taba fada min ba.
Tace gun maimuna black gamuma tare gidan buki shine maimuna din ta karba tana mata bayanin abinda ta gani bata bari an gama wayan ba takashe waya ta barsu.
Sai fadi takeyi imposible ciki fa zainab haba dai don Allah ciki wani irin ciki wai kuma tsohon ciki kai ina what sai ta yunkura ta dauko wayab datayi wurgi dashi da farko tana neman layin mijinta alokacin.
Duk da tasan ba lalai bane ya dauki wayan don basu daukan waya har ta gaji ta daina ranan haka ta wuni cikin bacin rai sai waya takeyi da yan uwanta akan wai suje su tabbatar mata ko gaskiyane zancen cikin ?
Saida uwar ta dauki wayan tace ke ki natsu banson hauka da zubar da mutunci in tayi ciki haramun ne ba da mijinta ba ?
Ina ke kince baki tashi haihuwa ba har yanzu to ya auro mai haihuwa yanzu ai sai ki zauna kallo da rainon diya kin tsaya kinawa mutane haukan banza wai halan ke kadaine Aisha ?
Don haka banson shashanci ki natsu kada inji wani zancen banza ua fito daga gareki akan cikin don abin farin cikine a wajensu ya samesu dashi da yan uwansa.
Kashe wayan tayi a hasale bayan tasa kuka tana fadin haba mama haba dai mai Aliyu ya daukeni da ba zai fada min ba saidai inii ga shanun talla.

79 / 105