DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   42 / 105

123K to 126K   out of 313.1K words

kiyayyan duniya ta dorawa yarinyar nan sabodani.
Mum ba gashi yanzu yayana zai saya min ba ba tare da gori ko cin mutunci ba da zai biyo baya ba don nasan wallahi daddy na saya min a lokacin nashiga ukku dasu ke nan.
Zata aika duk wani sheri da hafiz keyi aida sanin uwarshi ta dauki kiyayyan duniya ta dorawa yarinyar nan duk sabodani don kawai zainab na zama a tare dani.
Mum kubar tuna zancen su don tuna wanan abin baida dadi a yanzu bari Addel abinne da bacin rai idan na tuna yarinyar nan da karfi da yaji sun mayar da ita bazawaran dole yanzu.
Ai zainab ba bazawara bace mum ga wanda bai sani ba zai dauka hakan shiru nayi ina saurarensu yadda suke hira lokacin a tsakaninsu tare da kuma tuno wasu abubuwa na bacin rai daya faru a baya zamana a gidan ya hafiz din.
Komai zai wuce ta dai dage da karatunta a yanzu shine babban burin rayuwan duk wani wanda yasan ciwon kasa don hafiz saiya dawo yana dana sanin abinda ya aikata nan gaba.
Allah yasa mum ta fada ta juyo inda nake zaune a gefenta tana fadin ke kinji abinda yayanki ya fada saiki dage kila zaiyo maki bazawarine acan inda yaken ?
Bazawari kuma mum aita samu ko maza nawa ke sonta ayanzu kidai mata fatan alheri nan gaba shine kawai na dago kai ina kallonshi cikin mamaki .
Shigowan anty Nafisa data dawo ta samu an sallamo mum ya katse masu hiran suka koma zancen rashin lafiyan mum din dashi take tambayanshi ba ance da madam dinka kazo ba ?
Bangata ba tun jiyan da naje asibitin yace tare muke cikin daure fuska kamar ta tsikareshi lokacin ya mike yana fadin barin leka sanusi ina da appointment dashi kada ya tsaya jirana ya fice.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

4?? 2??

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Sallama biyu tayi a falon ba a amsaba hakan yasa tasa kai ta shige ta nufi dakin yar uwar nata can ta hangota saman gado tayi rub da ciki taci kuka har ta gaji a lokacin idonta yayi hulu hulu don kuka.
Aisha wai meke faruwane haka duk kinbi kin birkita kanki lokaci guda haka namiji fa ba,ai masa haka don komai a hankali ake binsa ba cikin fitina ba.
Cikin kuka ta dago tana fadin wanan dan iskan zai kasheni so yake ya manna min hauka in mutu kowa ma ya hura dani.
Wani kallon mamaki Usaina din take jefa mata kafin takai zaune saman gadon tana fadin waiko da hankalinki kuwa Aisha kike zagin mijin ki haka ?
L?lai dole kijawa kanki bacin rai indai namijine waima dame Aliyu ya rageki a rayuwan auren ku mijine irin wanda kowa keso Allah ya baki amma radhin hankali irin naki ya hanaki gane hakan ku zauna lafiya.
Mutumin nan kinsan irin son da yake maki tunkan kuyi aure yake maki duk abinda kikeso haka kuma kowa yasani a yanzu kece farin cikinshi a duniya don me zaki tsiro da wani rayuwan banza yanzu rsakanin ku ki hana kanku zaman lafiya.
Kai Anty Usai wallahi kuba zaku gane bane kindai san yan uwansa da iyayyensa ba kaunata sukeyi ba musanman ma mahaifiyarsa da yanzu ta dauko idanunta ta dora akan mu.
Nagane so take ta tursasashi yanzu ya kara aure kuma ni wallahi bai isa ba don ubansa zanci dagashi har iyayyen nasa don basu kai min can ba wallahi.
Wa,iyazubillahi Aisha kina da hankali kuwa nida Abdul ya kara aure ragewa nayi kome yasameni a yanzu ya kara mana ba kansa zai daukowa ba ko a kanki zatazo ta zauna ne ?
Idan kinajin shawara maganan gaskiya a yanzu dolene ki sauke wanan girman kan da fadin rai da kikeji har in kina son gane kan mijinki da kowa nasa dole sai kin bisu kinyi biyayyan aure kuma.
Abincinsa shimfidansa dama yan uwasa da duk wani motsi nasa dolene ki basu kullawanki a yanzu amma idan kikace ba haka ba wanan halin zakici gaba da nuna masu kema kinsan ko yan uwasa basuce ya kara ba dolene ya nemo mai masa hakan.
Au hakama zakice min Anty Usai toni wallahi Aliyu bai isa yace zai sake min haliba a yanzu don wani na zugashi akaina kawai.
Wani biyayya zan masa bayan wanan da nake masa in kashe kaina ke nan akansa kike nufi ko to wallahi bai isa min ba kuma baikai can ba.
Aure kuma wallahi bai isa yace zai karo min kishiya ba gidan nan don ba haka mukayi dashi ba da farko wai yau nice har Aliyu ya daga hannu yayiwa mari biyu kan wanan yarinyar don na fadi gaskiya kan abunda na hango atsakaninsu.
To ai kinga irin abin ko kin fara kaisa makura ke nan a yanzu da ya taba daga hannu ya dukekine amma yanzu fa fitinan ki da ikonki ya fara isansa ke nan da alama.
An dai zugoshi yana jin haushi na kira yar iska naci mata mutunci ta uwa ta uba shine ransa ya baci yazo ya sauke min haushin hakan bayan an zugoshi din.
Wai kina fadin an zugoshi ki rabu da namiji wazai zugoshi akankine da tun farko bai dauki zugi ba sai yanzu ki matsa har kikai babin da zaice ki bar masa gida sai muga ta tsiya kuma tunda ke bakijin shawara.
Duk wanan baisa jikinki sanyi ba sai bori kike kina zaginsa akan gaskiyanshi to mama tace in fada maki kishiga hankalinki wallahi kafin kikai ta tako gidan nan da kanta taci maki mutunci .
Don wanan abin da kika farayi idan ya gaji sai ya dank????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
ara maki saki muga abinda zakiyi din dole ko a koma dodofa ana ban hakkuri a karshe bayan ke kika lalata komai da kanki da gangan kuma don rashin hakkurin ki.
Gabantane ya fadi don yadda taga yai mata yau din tasan komai makamancin hakan zai iya faruwa a tsakaninsu gashi ya fada da bakinsa cewa aida baiyi wanan tunanen ba amma datayi haka ta haska masa hanyane ai.
Ganin yadda tabi jikin gado ta jingina jikinta yasa yar nata gane ta fara saukowa a lokacin tace don haka idan zaki natsu wallahi ki natsu kiwa kanki fada.
Don wallahi duk gantan nan da kike ganin kanki a cikinsa yau idan akace kin zama bazawara an gama dake don zaki zube ga idon kowane,.
Don haka shawarata gareki kibi sannu kibi mijinki ku zauna lafiya kuma ki girmama iyayyensa ki watsar da wanan rudin shedan dake damun zuciyarki a yanzu.
Haka dai Usaina din tayi ta bata shawara donta fahinci kuskuren da take shirin tabkawa kanta din kan bakin kishi saida da alama hakan baiyi wani tasiri sosai a zuciyar ta ba.
Haka dai yar ta gaji ta tafi bayan wani dan lokaci ta barta tana kiyasta irin matakin da zata daukarwa kanta a zamansu don wallahi basu isa suce zasu jagula mata rayuwaba ita kan anata fahintar.
Kusan satin su daya kano din amma haka zaizo nan gida ya karya yaci abincin rana tun mum na fadan hakan har ta gaji ta kyaleshi wani lokacin itace da kanta zatayi mai tayin abinci idan ban nan don ba zata iya kyashi da yunwa ba.
Safiyan lahadi ina gyaran falo don saboda jikin mum ban koma gidan mu ba har lokacin, sai gashi ya shigo banji shigowan nasa ba sai kamshin turarensa danaji a hancina .
Hakan yasa nadago da sauri ashema yana kusa dani lokacin tsaye ban sani ba cikin kananun kaya daya saka a jikinshi don kusan sune suturansa shi su yafi sakawa ko wani lokaci zan iya cewa hakan kamar dabi,an yaran gidanne maza saka sutura irin na kasashen ketare.
Ganin na dan firgita yasa ya dan kara tsuke fuska yana fadin wanan tsoron fa ina mum tana dakine ya tambayeni ?
Amsa na bashi tare da gaidashi nace yanzu ta fita zuwa gaida daddy ina kwana yaya ?
Ya amsa da lafiya zamu koma nazo muyi sallama naso sai gobe amma ina son shiga office gobe din da wuri bari inje can in sameta ya juya ya fita na tsaya ina bin inda yabi din da kallo.
Ina mamakin sake min daya farayi a yanzu don gaskiya ba wani saki sosai tsakanina dashi yadda matarsa take tunane din bai dade da fita ba naga mum din ta shigo.
Nace kinga yaya yace zasu koma yau tace ehh tana zama saman kujera ya shiga wajen Alh naji yana fadin hakan ita yar ikon bata biyoshi ba ke nan ko sallama muyi da ita aina dauka tare sukema ?
Mum kyaleta wanan kamar bata da wayaune zata raina kantane ai wata rana don iyayyen miji ai ba wasa bane da ba,a haifesa ba ina zata gansa ta aura ?
Har tana wanan iya shegen yadda take so daine insha Allahu ba zata gani ba don bata iya rabashi daku duk tsiyanta aiko a nan idan tana da tunane tasan ta rage.
Humm,kowa yasan niyarta ke nan ai na sani ai mama wai ace ni yarinyar nan zata mayar makiyiyar ta saboda Allah wanan wani irin zamanine haka ?
Mum rashin sanin darajan manyane fa tun gida inkinga haka bata da tarbiya rashin sanine kawai yakai yaya aurota kawai a fita zancenta tunda ba,a neman komai a wajenta ai alhamdullahi.
Idan taga kowa ya shareta zata dawo hanya ai ita din banza in badon yaya da take aure ba ina ruwan wani da ita da har zata so rainawa mutane wayau haka ni ban dauketa mai hankali bama wallahi naja tsuki ina kawar dakai sai kuma na juyo cikin takaici nace.
Wai dani zata zargi yayana kuma ina hankali a wajen nan don Allah mum ta dauka zan biye matane mu zamo daya mu tayarwa mutane da hankali a banza niko ko kallo bata isheni ba yanzu.
Kin gane ke nan shiyasa na kyale zancen ai don naga dukkanku baku dauki zancen nata da wani muhinmanci ba jiyanema naji wanan na sakin habaici nasan taji zancen abinda ya farune a wajen hjy.
Wake nan kuma mum na tambaya a cikin mamaki tace Mummy dinku mana ai kinsan ba hankaline da ita ba.
Cikin mamaki nace ita fa mum koda yake ba abin mamaki bane tunda gaba Dada aikai zancen doleko suji nima abinda na nasa ke nan ai yasa ban tsaya kulata ba.
Amma da yake ba kunyane da ita ba wai shine ta nuna wai yanzu kamar ana son cin amanansune tana kiran cin amana ai ansabashi a gidan nan dama don ba,asan kunya ba sai anyi din su gani koda yake ansan hanyar makirci ai don taga har gidan kika dawo da zama yanzu ashe abinda akeson kullawa ke nan dama ?
Shirmen banza dama ai irinsu daya da Aishan son kai yai yawa yake sakasu hakan na fada cikin takaici mum tace sherinsu dai zai bisu ai.
Nidai ga Allah na dogara duk abinda Allah yayi mai kyaune don ba wanda yasan gobe banda Allah lokacin yaya din ya shigo yake kallon mu .
Don ya fahinci akwai maganan da mukeyi mai muhinmanci daya bata wa mum din rai shi kuma a yanzu ya tsani yaga bacin ran mahaifiyar nasa ga komai don gudun tashin ciwonta din dake barazana da rayuwanta a yanzu.
Don haka ya zauna yana kallon uwar a cikin kulawa da tsarguwa yana fadin ya akayine kuma tace zancen mutanen gidan nan mukeyi wanan haukan na matarka datayiwa mama nasan hjy ta fada shine mummy ku take habaici a kai.
Tsoki yaja kafin yace ki basar da zancen su a ranki mum kin saba da halin matan nan kinga baki da lafiya don Allah kada zancen ya dameki kuma ki bar sauraren shirmensu .
Itama Dada da bakin kwarmato take dama nasan sai tayi hakan ai ita kuma mahaukaciyar zata san tayi da dan halas don sai na aikata abinda take zargi din zata raina kanta.
Ita mummy har tana da bakin magana koda hakan ya kasance din tsakanina da zainab don kawai ba,a son gaskiya idan sunce basu so shike nan kar wani yasota kuma ?
Ni zan tafi yau mum don ina da aikin gobe insha Allahu saidai idan munyi waya ke kuma don Allah ki kula da bata magani akan lokaci yadda akace da cin abinda duk takeso kada ku zauna da yunwa.
Duk abinda babu ki kirani ki fada min nima zan dunga kira lokaci lokaci ina jin halinda kuke ciki insha Allahu nayi magana da baba jiya nace ya barki nan don kada a raba maki hankali ga karatu ga kula da mum din kuma ya yarda da hakan.
Ga wanan ku rike a dinga amfani dashi Nasir ma yace zaizo satin nan mai zuwa insha Allahu ya mike yakai kudin gaban mum ya aje sai cewa mum tayi mikawa zainab tunda itace me sayo abu din zaifi sauki.
Ya juyo ya miko min kudin nasaka hannu na karba ina fadin mum da kin barsu wajen ki tace bani nace ya mika maki ba yanzu ba dabane ko laluran karatun ki ai zai cinye kudin nan.
Har me za a saye haka ki rike kina amfani dashi tunda kin dawo nan yanzu ke nan kafin kuma wani zance ya taso bayan hakan don nasan dole sai anyi tsegumin dawowanki gidan nan kuma indai gidan nan ne.
Ina ruwanku da zancen wani mum naso tunda zainab din zata koma school asamu wata yar dattijuwa da zata zauna nan din din tana maku yan aikace aikaice gida haka zaifi.
Nan kan ina zamu samu sai dai can gida katsina zansa a duba yace nima nayi tunanen hakan zan idan an samu sai in sani ya fada ya kara daga zuwa wajen mum din har kasa yakai yana magana da ita kasa kasa ganin hakan yasa na shige daki don in adana kudin naji muryan mum na fadin kizo zai tafi fa.
Na fito na samu har ya fita nabi bayansa nace Allah yakai lafiya yaya ya dan juyo ya yafutoni da hannu alaman na karaso hakan yasa na tako da dan sauri zuwa inda yake na sameshi.
Ina isowa ya dan kalloni yace kinga dai zaman kida mum bai kare ba ina son ki kula sosai ki taimaka muna baki daya don Allah kada ki bari damuwa yana shiga zuciyanta ku zauna freely ko wani lokaci.
Insha Allahu amma sai,dai dole kaima yaya a bangareka saika gyara kana dan kiranta lokaci lokaci ka daina daukan lokaci mai tsawo bata jika ba hakan zai kara rage mata damuwan nata don,,,,
Zainab ki bar zancen nan a yanzu ki dai dan saurara min zakuga canji dabaku zata ba din a wajena nasan abubuwa da dama sun faru a baya insha Allahu hakan ba zai sake faruwa a yanzu ba kuma.
Dariyan jin dadin wanan zancen nayi har yakai anty nafisa dake fitowa ta samemu tana fadin tow yau yaya da kanwace ake zancen siri haka ?
Murmushi yayi yana fadin ashe baki fita ba tace kasan muna gida yau yanzun ma gun gyaran kai zani na fito kada layi yai yawa nadade a candin gashi nayi sa,a na sameka sai a ban na gyaran kan ke nan ko ?
Kufa zawarorin nan wayau tsiyane daku akan me zan bada kudin gyaran kan da bani zan gani ba kije gun bazawarin ki ya biya mana ta kwashe da wani irin dariya tana fadin.
Ke kinji zainab wai ashe wayaune damu haka suke fada ke nan na zata inna samu ita kanwata zata samu ai ashe kai da naka zaton a zuciyar ka.
Aiba karya na fada ba ko jiya na shigo gidan nan na samu bakuwar mota nasan ko gunki yazo hira amma ai kasan yanzu bani kadai bace bazawara gidan nan ba ko ?
Ya kalloni yace wai hakane zainab ko har kin fara hirane don baida wuya a wajenku na dan make nace hai anty banda sheri fa ni bama wanda yasan ni ina zawarci ai a gidan nan.
Kima tsaya ai zanji koda ba a garin nan nake ba zan sani kada ki tsaya biyewa shirmen banza kiyi facing din abindake gabanki yafi maki sauki yana fadin haka ya tura hannu ga aljihunsa ya fito da kudi masu yawa yan dubu ya mika mata yace a gyara masu kai lafiya .
Ta amsa tana dariya tace kin gani ba Allah nasona zainab dana fito yanzu gashi rabona ya ratsa ga aljihunsa dan dariya nayi nace yaya Allah ya tsare hanya.
Take fadin wai tafiyan ke nan dama amma Addel gaskiya baka da kirki da sai inji kawai ka tafi

42 / 105