DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   76 / 105

225K to 228K   out of 313.1K words

ki dawo indan kama maki ta tambaya tana dukar da kai dan murmushi nayi kafin nace ba komai Ai,na na kammala komai kafin in fito saina dawo.
Da haka nasa kai nayi wajen motan mijin naganina ya taso da sauri zuwa inda nake yana min ina kwana na amsa da lafiya ya baki kuma ya na dan murza hannunsa waje daya yace ai baki aun zama yan gida hjy.
Za,a fita nace ehh yake fadin to a dawo lafiya Allah ya tsare ya kare na amsa da amin na bude motan na shiga da bissimillah a bakina.
Sai naji motar tayi min gwangwarangwan dana zauna cikinsa a hankali na lumshe ido inawa ubangiji Allah hamdallah da wanan daman daya ban don abinda nake gani wajen wasu yau gashi ya mallaka min shi a hannuna.
Kodana isa school haka nasha kallo a ranan duk da a wayence ake hakan ammaz nasha nune a wajen mutane cewa nazo da motan miliyoyin kudi don maza har zuwa duban motan sukeyi ana gardama.
Saukin abin dai na samu mun fara lectures hakan ne yasa ba kowane ya tsaya magana dani ba a cikin ajin lokacin.
Bamu samu sauki ba saida muka fito sallah lokacin muka samu gaisawa da junan mu anyi yaushe rabo mussanman ni sai Allah bada zaman lafiya ake min ina amsawa a cikin kunya.
Ashe suna zuwa airport da tsiya suka tafi tun lokcin da ya Addel yace abokinsa umar ya kawo min key kasa hakkuri Aisha tayi tana fadin akan me za a kai mata key kuma ba motocin zasu biyomu bane ko sai gobene zasu iso Abuja ?
Dashi zata dinga amfani kafin in saya mata na,,,,,, bai kai karshen zancen shi ba ta amsa da kutumar uban nan motan naka zaka barwa yarinyar nan don tana yarwa a garin ?
Ita din diyar waye a cikin kano da zata shiga wanan motar kagani ko umar kagani ko to wallahi baka isa ba Aliyu na fadama baka isa ba Aliyu,,,,
Ke dakata kada ki tara min mutane a nan idan ban isa ba tunda nakine ko da kudinki na saya ki amshi key din motar kada a kai mata .
Bada kudina ka saya ba amma dani aka samu arzikin ai haka kawai daga zuwanta sai ka nuna tafini don tana yar uwarka kome zaka fara nuna bambamci akan mu tun yanzu.
You're kidding Aisha na memi kudi dake yaushe idan wasa kikeyi kice Allah kin tuba tun yanzu ko kina haukane wai Aisha ?
Ganin da gaske takeyi inda take shiga banan take fita ba yasa yayi gaba ya barta ya dauka zata fasa zuwane sai gashi ta shigo daga baya ta zauna kusa dashi.
Lokacin yana waya da umar yana worning dinsa ni dai naga umar din ya kawo min key yana dariya yake fadin saikin kula sosai da motar nan don kinsan me tsadace sosai kinji zainab nace insha Allah zan kula ya umar.
To har suka kai Abuja ba wanda yaiwa dan uwa magana suna isa kuma bai tsaya ba ya fice zuwa office ya barta komai batayi ba bayan fitanshi .
Don bayan tagama buge bugen wayanta ta kwanta tayi ta barci inda Allah ya taimaka yasa yaronsa ya dauko masu gyaran gida an gyara masu komai nagidan don haka ba wani kazanta a gidan lokacin.
Koda ya dawo yasan halin bai tsaya neman abinci ba wanka yayi ya kwanta nan ta sameshi a daki kamar abin arziki sai bayan sun natsune ta kara dauko zancen tana fadin.
Nifa bangane zancen motan nan da kace akaiwa yarinyar nan zeey key ba kayi min bayani yadda zan fahincika yanzu in gane .
Wani irin haushi da takaicine suka ziyarceshi lokaci guda ya mike yana fadin isan na bata mota ita din ba matana bace kome don nace akai mata key din motana ?
Ehh lalai matarkace kuwa naga alama yanzu sai ka zaba koni ko ita ke nan don ba zan zauna da wanan yar iskan yarinyar tana ganin kamar kan mu daya yanzu dani da ita.
Saida ya karasa mikewa tsaye yace ke wawiyace haka ashe yarinyar nan tunda ta shigo gidan nan har yau din nan da muka bar kano ban taba jin tayi zancen ki ba.
Asalima bata ko sanda zamanki a gidana ba son harkan gabanta kawai takeyi bata kawo sunan ki a gaba amma ke ,,,,,, ta tareshi da fadin ba dole ba son tasan ni din ba sa,ar yinta bane ai.
To kinga ina son in baki warning daga yau din nan kada ki kara min zancen zainab agabana irin haka babu ruwanki matatace ina da right din mata komai naga dama a rayuwana.
Ko kina nufin kinfita a wajenane wai ki fada min inji yau dame kikafi zainab dashine wai ilimi, addani kyau ko hali koko tarbiya wanan dai akewa mutum duba ko fada min wanda kikafi zainab dashi don Allah ?
Wani kallon banza ta watsa mashi kafin tace dashi dama nasani nasan abinda z?,a kitsama ke nan yasa aka tilasta maka ka aure ta don azo aga iyakata don kawai ba,a sona dakai .
Har yakai kofan ban daki ya juyo yana fadin waye ya sani hakan bake ba kece nan kika haska min ya kuma zamo min alheri a yanzu.
Karya kake munafukin Allah maganata bashi zaisa ka auri zainab ba sai dai idan dama kanada niyar hakan abinda aka dade anayi waya sani ma ko danshi kuka kashe auren nata ta fito ta aureka.
Idon ta ya rufe har bata san lokacin daya tako zuwa gareta ba saijin saukan mari tayi a kumatunta zata dago ya karama tare da nunata yana fadin bari kiji.
Idan kun saba shedanaku mu bamu saba hakan ba gidan mu zargin ya isa Aisha ya isa hakana don Allah kada ki bata min aure da zargi a idon duniya duk kika koma maganan banza irin wanan zakiyi mamakin abinda zan maki a gidan nan.
Ganin yadda ya taso mata yasa bakinta mutuwa don tasan yana iya halakata a lokacin don haka taja bakinta tayi shiru tana hawaye ya juya ya shige ban daki kodaya fito filo ya dauka ya koma falonsu ya kwanta cike da bacin rai a zuciyar shi.
Saida safe ta tashi fuska a kumbure ta kira gidansu da kuka tana fadin Aliyu zaiyi kasheta koya illantata akan amaryansa uwar naji tace shike nan kin zama jaka akan kishi hummaira ?
Kankine farau sin kishiya da zaki hana zuciyar ki shakat ku zauna lafiya da mijinkine wai son Allah uban yace ba kanta bane farau amma ba zan yarda da duka ba haka na fada mashi tun ranan .
Karasa zanyi yau cikin mamaki uwar tace Alh karan surikinka fa yace kwarai gara in kaishi ga hukuma a daukar mata fansa yafi.
Zakako ji kunya tunda yarka tana son mijinta hakkurine dai bata dashi wani irin hakkirune bata dashi donke ba ai maki kishiyan kinsan zafinta ha ko ?
Ko ba kai min kishiya a gidan nan ba aina zauna da kishoyoyin waje hauka nayi ko karanka nakai a lokacin wani irin cin kashine banganiba a gurinka gurin wanakai kara a lokacin yanzu bagashi ka rage ba.
Ohh don wanan kikecewa tayi hakkuri barin watsa ruwa in fito kigani ya daga zuwa dakin kwanansa ya barta zaune .
Tasan halinsa zai iya abinda ya fada hakan yasa ta daga waya ta kira yarta usaina ta fada mata halinda ake ciki tace gata tafe.
Kafin ya gama kintsawa ya fito ta iso gidan a sukwane yana fitowa suka tare shi da fadin baba kayi hakkuri abinciki zancen nan aji metayi masa meya kawo hakan tsakaninsu jiya jiya da komawansu.
Sai jikinsa yai sayi Usaina tacigaba da fadin Abba kasan halin Hummaira haka kawai Aliyu ba zai daga hannu ya duketa ba kasani Aliyu yana da hakkuri da wani iskancin nan da hummaira keyi ba zai dauka ba.
Wani kallo yaiwa Usaina din tace kwarai Abba ka fara bincikan Aliyu din kaji amma barin kira Hummaira din yanzu muji.
Koda ta daga waya ta kirata murya dishe ta dauki wayan take fasin hummai meke faruwane wai ga Abba ya tafi yayi karan Aliyu wajen hukuma ?
Sai cewa tayi kara kuma shi Abba me zaisa yaje gun hukuma ya zubar muna da mutunci kuma don na kirasa na fada masa abunda ya faru.
Kallon uban Usaina tayi sai ya cire hullasa yana fitara dashi yakai zaune Usaina din tace ke meya hadaku haka dashi daga komawanku kuma sai fada ?
Nan ta fara mata bayani tun abinda ya faru airport har zuwansu Abuja din katseta tayi da fadin ina ruwanki don ya bar mata motarsa kinsan dalilin hakan.
Keda kike shiga motarsa fa a Abuja waya hanaki hakan imda ta fito yar ta tare wanan yasa ta kyale karshe saita kashe wayan ta barsu suna mamakinta.
Shagon daddy yaje da korafinsa akan aiwa Addel magana yabar dukar yarsa aure ba dole ba inda yake shiga ba nan yake fita ba.
Su daddy suka samu suka lalabashi ya wuce akan ba,a kyauta ba za,aiwa Addel magana kada ya koma da daddy ya dawo yake fadawa mum abinda ke faruwa.
Shine mum ta kirasa tana masa magana ya kwashe abinda ya faru ya fada mata tadai tsawata masa kan ya bar biye mata kada ta mayar dashi namijin duka kuma don kasan idan ka dokar min ya bazan kyaleka ba ranan .
Nima haukacewa zanyi irin surukinka mu hade yayi murmushi yana fadin insha Allahu hakan ba zai sake faruwa ba yayi kuskure.
Mum tace ai sai ka samu surikin naka ka basa hakkuri nan yace da mum wanan kan mum banyi alkawari ba naso abarsa yaje wajen hukuma ai mu hade a can .
Duk wanan labarin a bakin su mama Azumi da sukazo min wuni nake jinsa don bansan anyi ba ni jin hakan yasa nakara tsaro akan motar fiye da yadda nakeyi a yanzu sai gashi naga an karo min maigadi gidan sun koma su biyu yanzu.
Gaskiya naji dadin zama da matar maigadi din nan a gidan saboda ba laifi gaskiya tana da kirki matan dama ance ko wani mutum da ranansa.
Haka zatayi min yan aiyukan gida tun ina a,a,a har nagaji na kyale dole munayi tare yaranta kuma ina dan koya mata yadda zata gyarasu wanka da safe a canza kaya.
Haka kuma da yamma sai anyi wanka don nan suke taruwa suce sunzo tayani hira wani lokaci in shige daki ina karatu tana falo da iyalinta suna kallo don nasan shike kawosu wurina da dare hira don akwaisu da son kallo.
Zuwan da yaya yayi na farkone yaga zasu takura mai sai gashi ya sawo masu tv da receiver ya kafa masu a wajen su wanan ya rage yawan shigowansu wajena din.
Saidai bata bar zuwa kama min aiki ba shara goge goge iyaka kuma falo sai wanke wanke kaya tunda na gyara mata ta iya yadda nake so muka zauna lafiya dasu.
Aisha kuma tun wanan zuwan bamu sake haduwa ba don koda sunzo saidai yace tana gidansu don zuwa biyu yana fadin tana gidansu tare ai sukazo da ita.
Haka zata juya ta koma ba tare datazo gidan daddy ta gaidasu ba sai hakan yai min dadi sosai don nikan aita kashe min tsegumin gidan daddy ne.
Harkokina nake gudanarwa a gari hankalina kwance cikin wata ukkun da nayi a gidansa lokacin zuwansa biyu sam ban nuna na damu da hakan ba.
Karatuna na mayar da hankali akai don na kula da yana son karatun nawa sosai tun ina gida don haka dole na tsaya na mayar da hankali yadda zan gane.
Allah ya ban kwakwalwa saurin gane abu da fahintarsa don hakane ban samun matsala kamar sauran don yanzu agaskiya hurdan mu ya dan ja baya kadan mufi hurda da hauwa ita da take da aure.
Hakan kuma ba yana nufin mun rabune a,a muna tare a school sa wajen pratical saidai idan zasu fitane ban faye sa kaina cikinsu ba sai in kawo korafi in saka ina hakane kuma saboda tsaro.
Don yanzu a zagama sheri ba wani abu bane me wahala hakan yasa shima ya gamsu da matakin dana dauka don nagane yana targuwa dasu idan ya gansu da farko.
Amma yanzu ba korafin komai tunda baiji wani abu daga wajen wani a kaina ba banda yabo da yakanji din a bakunan mutane wani lokaci.
Zuwana gidan daddy na farko tun bayan aurena tare dashine ko shi saida nayi da gaske ya yarda zamuje din mu gaida mum .
A ranan na rasa wani kalan shiga zanyi don in burge yan gida idan naje ba kwaliyan buki nayi ba tunda ba buki zani ba lokacin.
Don haka na dauko atamfan super da hauwa ta bayar aka dinko muna a kaduna atamfan koriyace da surkin fari kadan a jikinshi.
Zani da rigane normal akai dinkin mai kyau dashi na dauko fararen takalma sai farin gyale mai stone babba yana rufe jiki ko ina idan ka yafa.
Na daura dan kwali tsab zakice hula na kafa don yadda ya kama min kai ya kara fito da fuskana shar sarka da dan kunnen gold har awarwaro na saka a ranan.
Falo na fito na karasa wajenshi a hankali yana zaune yana duban wayarshi jin takon takalmana yasashi dagowa yana dubana.
A hankali nace na shirya yaya bina yayi da kallo kamar yana tuhumar wani abu gareni kafin yace dani zeey wanan kyau hakafa ?
Anya zan iya fita dake haka kuwa kallon jikina nayi ina fadin shigar batayi bane in sake wani duk da nasan is hard in sake wani bata lokacin kwalliya kuma alokacin .
Ya dan lumshe ido yana fadin gani nayi kin wani kara kyau kamar bake ba dai na dan marairaice kai ina isa garesa nace kullum haka kake fada ai wanan kwalliyan zuwa wajen mumcy ce ba takaba.
Ai naga alama ya fada yana daukan key din mota ya mike tsaye kafin yace kada inyi wata magana yanzu kuma ace mun ba hakana bane bari dai muje gida kyaji.
Dan marairaicewa na karayi ina fadin wata magana kuma yaya ai gara ka fada son ka fara tsoratani Allah ko mujedai zan fada maki a mota ai.
Hannuna ya kamo muka fito tare Ainau dake jiran mu a waje da tarun kayan da baisan dashi ba sai a lokacin ya gani ya kalloni yana fadin wanan kuma meye kika kwaso ?
To haka zamu zikau dagani sai kai hannu sake dan tsarabane dai zankaiwa daddy mum da kuma dada kada tayi min korafi tace iyayyena kawai nasani kasan dai halinta ai.
Hancina ya lakato bai damu da Aina da yaranta dake wajen suna kallon mu ba yace kin kyauta sosai da kikai hakan yaran Ainace suka nufomu suna fadin sai kin dawo hjy.
Kai Nana bana hanaki kirana da hjyn nan ba niko tayan jirgi ban sani ba daga inda Aina take take fadin Allah ne bai kira ba hjy in lokaci yayi aiba fashi.
Murmushi kawai yaya yayi ya zauna a mota na bude bayan muka loda basket din da sauran tarkace a ciki kana na zagaya na shiga ina kallon yaron na kuka uwar tana jansa wai zai bini .
Dama haka yake min idan zan fita a gaban idonsa sai ya lake saboda sabo da sakin fuska yace zai bini don hakane inzan fita sai uwar ta boyesu.
Ina zama ya rufe glass din motar naji ya sauke ajiyan zuciya lokaci guda yaya miskiline ko magana na cinsa zai barwa cikinsa nasan da hakan yasa na dan kallosa.
Yace yes wani abune kawai yazo min a raina wani abu kamar me ya lumshe ido ya shaki ni,imtaccen kamshi jikina daya cika masa hanci yayi kasa da murya kamar me rada yana fadin kawai dai ranan da zanga nawa dan yana min haka sai ya bini idan zan fita.
Na dan kallosa da mamaki a fuskana nace na dauka ku duka ai baku son haihuwane a yanzu shiyasa ma baku damu ba amma yanzu aurenku da Anty Aisha kusan shekara shidda ake nema fa.
Ya lumshe ido ba tare da yai magana ba sai zuwa can naji yana fadin kin taba ganin dan haihuwa ya guji haihuwa zainab niba haihuwana akayi ba da zance ban son haihuwa .
Shiru nayi ina dan tunane ba tare da nayi magana ba sai zuwa can na dan kallonsa yana murza sitiyarin motan a hankali kamar baison tukin a lokacin.
Nace ya kamata muyiwa mum dan shopping muje mata dasu tunda ka dan jima baka gari gashi kuma ba ita kadai bane yanzu dole wani abin ya kare masu.
Shiru yayi na dan lokaci yaci gaba da tukinsa sai can naji yace baki tashi wanan maganan ba tun dazun sai yanzu kina nufin dake zanje gun shopping haka ?
Nace sai yanzu dabaran hakan ya fado min kada muje hannu sake so kike muje a kama kallonki kome ?
Ni kuma yaya wani irin kallo kuma kamar anga wani hallita na daban sun ganine dole

76 / 105