Chapter 69 Reading DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc Arewa Novels

DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   69 / 105

204K to 207K   out of 313.1K words

Yanzun haka nasan suna can suna kwasa dashi don kowa ya watse mum ta ban kayan nan a kawo maki wai shiru nayi sai faduwa gabana yakeyi don tsoro.
Ya gama zolayana ya fita nan kanwar mahaifiyata ta shigo ta sameni ina nade kayan dana cire ganin yanayina take tambayan meke damunane wai ko akwai damuwane Zaina ?
Na juyo ina fadin ba komai mama kawai dai zancen wanan matar ya tsaya mun a rai nan na kwashe komai na fada mata.
Budan bakinta sai cewa tayi shineme Zaina wanan tanayine ta tsorataku kawai daga ke har mijin naku idan kun tsorata tun yanzu shike nan hakan abin zai tafi.
Zaina kin sanni dai babu inda ban shiga a yanzu nasan irin matan nan nasan halinsu sarai kaidine kawai irin na matan birni dake haukacewa kan kishi.
Don haka kada ki yarda har wani ya gano kin kariya da ita a yanzu in kinyi hakan abin kunyane a wajen mu zaki shiga a goga tunda tace hakan a zuba a gani ba boka ba malami sai Allah.
Hikima duk wace tazo dashi akan kishi munsan kalansa ina garin nan ai zan kwana biyu don nazo da kaya masu yawa da zan tallata a garin kinga komawana gida ba yanzu ba.
Murmushi nayi wanda shine dabi,ana ban faye dogon magana da babba wanda yafi karfin shekaruna wani lokacin.
Ko nasan abu nakan koma ban sani ba a tafi a hakana itace take kokarin sama muna wajen barci saiga baba ya shigo daukan shimfidanshi.
Yana fadin saiki kwana a nan kedasu Asiya ni zanje can falon makwabcin mu in kwana yanzu yake min tayin wajen kwana ya ganmu dasu halilu waje can zamu mu kwana tare dasu.
Allah sarki baba Abubakari mazan zakari irin biyu suke gyara gari kirarin mai suna Abubakar nayi mai watau magana daya yakeyi baya biyu dayaje dasu gidan daddy su kwana ya kwanmace su matse a nan tare dasu Allah ya sakawa duk iyayye na duniya Amin.
Anan muka kwana dasu inna Luba magana guda takeyi na sakani a hanya har lokacjn data fahunci nayi barci don bataji ina amsa mata ba ta kyaleni.
Washegari na tashi tunda safe inna Luba daice take dawainiya dani ruwan wanka abin karyawa na don baba ya sayo manyan bread da kayan shayi.
Sai kuma masa da kosai da koko da akayi nan cikin gida makwabtan inna sunzo mata kara abin gwanin ban sha,awa gida ya cika fam da jama,a
Zuwa goma safe su anty hauwa sun iso gidan mu nan suka hade da inna luba suka shege lungu tayi ciniki sosai a wajen kawayena.
Tare dasu muka kwasa zuwa gidan daddy akai walima waliman kuma ya kayatar sosai don malam kungiya na mata sukai wa,azin saboda mum na cikin kungiyar nasu.
Karfe daya da rabi aka tashi wajen don sallah gaskiya mutane sunyi kara sosai abin yazowa mutane a bazata auren da ake gani tarewane kawai sai gashi abubuwa sunba mutane mamaki.
Ina zaune kuma akace ai gidan baba zan koma can zasuzo su dauki amarya ko babana da yaga mun dawo gidan saida abin ya bashi mamaki.
Ya daice ba komai shiga gida Allah yasawa aure albarka ya baku zuri,a masu albarka shigowan inna luba take fadin wai iyayyena na katsina suka shirya hakan cewa in dawo nan azo a daukeni
Don duk da an daura aure da dadewa wanan taron na al,adan matane saidai sukazo daga katsina.
Haka kuma iyayyen mu maza sunzo sosai daga katsina sunzo da daman su an cika taro dasu sun nuna mu yan dangine gabaki dayan mu a wajen.
Saidai duk abin nan da akeyi a kunnen ya hafiz yake haka kuma mummy tahau sosai ga duk wanda yazo don bukin daga gida.
Har yakai mutane sun gane hakan a cewanta wai kwadayine don anga yanzu daddy baida karfi irin na da can baya yasa suka koma wajen Addel haka suke fada da yaranta son sunzo suma su zaunawa uwarsu daki.
Karfe hudu baba ya shigo yana fadin sai ku shirya na kirashi Addel na fada masa gamu nan zuwa dake yanzu yace yana gida.
Ita hjy kubura munyi waya tace motoci zasuzo yanzu su dauke ku yan rakiya yanzu da mun fito sallah zaku fito muna da ita ga daddysu nan yazo tun dazu suna kofan gida.
Irin gudan nan na yan Niger wata daga cikin dangin inna ta sake saida kowa ya zabura don a bazata yazo masu gudan ta samu kudi sosai tayi ta bazawa a wajen.
Su Anty habiba matan babanni nane suka shigo sunyi mamakin ganin gida cike da jama,a kasa boye mamakinta tayi saisa tace wai bukin bazawarace haka ?
Aiko aurenki na farko zainab bakiyi wanan goshin jama,aba haka wata yar uwar inna dake gefensu tace hakan yana cikin albarkan aure inji manya.
Yadda baba ya fada haka ya faru dani don ko yana zuwa sai cewa yayi dasu ina take ku fito da ita ana jira a waje ba fashi dole na fito sai lokacin kuka yazo min na aure sha kan yaro.
Motan daddy muka shiga su Anty hauwa suka shiga motocinsu sukai gaba kafin mu isa har sun isa su sun karbi key sun bude part din.
Ihunsune ya sanarwa jama,an dake part din anty Aisha akwai baki gida the other part saidai basuyi mata magana ba a lokacin.
Tarkon da suka danane ya sanar da ita don turaren da zuka baza ko ina sun fesa turare masu karfin tashi dama da tanadinsu a jakkan kowacensu.
Wanan kamshin yaje mata har tasan da isowan mu yadda daddy ya saba ko wanan karon har dakina ya kaini tare da kara min nasiha suka fito daga gidan suka bar mata.
Wai ina matan nan mai guda ke rangada muna guda son Allah sai kace mun kawo mugun abu zuba muna asan mun iso son Allah ?
Gudan data ragada su kuma suka karba da shewa wanan ya kara harzuka Aishan ta fara fada cikin isa da izza tana fadin.
Wanan ai iskancine wanan shashanci haka kamar gidan karuwai fa zasuzo gida sunawa mutane ihun banza suwaye hakane ma wai ?
Yan kawo amaryane Amarya ta tambaya a wani yatsune ehh sun iso aida amaryan yanzun nan daga inda anty halima take zaune tace sun iso shine basu kawota nan ba.
Wanan wani sallone kuma an kawo amarya ba zasu fara kawota nan ba sai su shige daki da ita kamar dama a jirace suke da dakin.
Wanan ai sallon sabon iskancine najan magana ai dole azo da ita nan aba Aisha girmanta da Allah ya bata tunda haka akasan anayi.
Daga gefe kishiyan anty Usaina su tace keko mumsi ai an daina wanan yanzu ba kowa bane ke hakan gaskiya saboda an daina.
Nan suka so yi mata caaaa tace mu dai an daina yanzu don an rage yin hakan dakinka ake kaika kai tsaye idan an shigo.
Muryan anty habiba sukaji shigowa tana fadin mukan zamu gudu don gari yana hadewa da hadari bari mu gaisa da Aisha mu fito.
Take tayi wani hade fuska kallo guda tayi masu tagane ta kara daure fuska haka suka gaisa da taron jama,an dake falon suka fito daga part din suna fadin abinda suka gani.
Su shidda a cikin anko sai iyayyena mata uku dani goma muka shiga part din nata sai wasu da anty Usai suka amsa muna.
Sukai muna sannu da zuwa tare da bamu wajen zama a falon ita haliman nasuce ta mike tashiga inajin taki fitowane son itama bata dawo ba suka barmu a zaune.
Sai Usai din ta mike ta shiga muryoyinsu na dan zuwa falon don munji wata na fadin hakkuru zakiyi mana kije kawai ai gaisawa za,ayi shike nan.
Inna Luba ta kalli anty hauwa ta gyada kai aiko anty hauwa ta mike tsaye tana fasin inna don Allah mujen ku tunda bata fitowa mintin mu nawa nan a zaune.
Kishiyar anty usai tana fadin lalai dai kan abinda ba,a fara akan ka ba balle a kare name na barnan suna don ita tana kusa damu zaune tana ba danta abinci.
Fuskana tar don sin hanani yafa mayafi har kai jikina da wani shadda milk yasha aiki irin dinkin mali sai gyalen da zai shiga dashi kusan irin dinkin ne suma a jikinsu na ankon mu da sukayi.
Saidai nawa yafi kwaliya da daukan ido yadda duk ake fitowan alfarma dai mun fito gaskiya a wajen don munyi kyau sosai a ganin mutum.
Sun mike tsatsaye sai gata da tawaganta itama a bayanta suke fadin sannuku da zuwa suna bin fuskana da kallo kwam.
Kawayenta yan karya da ji da kansu sun fito suma su bamu tsoro sai gashi an hade an fara fadin mairo clean kune dama yan kawo amaryan ?
A,a Giwa bukan daki bakiyi da yara sai manya ashe kuna ciki dama wallahi fa mune kinsan amaryan ai besty din muce tare muke karatu da ita ba mun taba haduwa dake ba asibiti kikace tana da kirki ko baki shedata bane.
To ina uwar gidan matar baba gambo ta fada aka nunata tace Allah sarki to uwargida ga amarya kuma abokiyar zama mun kawo maki don Allah sai ayi hakkuri a taushi zuciya ku zauna lafiya.
Wai wanan ai ta sanni na kuma santa don haka ba baki muke ga juna ba duk dame tazo nan tazo daidai da ita don gida ta tazo.
A,a gara dai a zauna lafiya don Allah mushi muke fata tunda kunsan juna zaman lafiya kan ai zainab bata soshi ba kuma kun sani tunda ta rasa mijin aure sai dan uwarta.
Don Allah ku tashi mu tafi tunda munzo din dama na fada maku an daina hakan sai a nemi rainawa mutane wayau a banza .
Hjy murja ta fada ta mike sauran suka mike suma anty hauwa da inna Luba suka riko min hannu a daidai lokacin da take fadin .
Dama ban kiraku ba ai ku kuka sameni zata gane bata da wayau harku din da kuke ganin kunci bulus haba Aisha wanan wani zancene kuma ?
Yarta Usaina ta fada a hasale yayin da suka hau bakinsu amarya ta shigo ke nan har abada mutu ka raba da yaya Addel daga gidan nan sai kabari duk abinda zakiyi kije kiyi andai shigo gidan yau kuma dakinta zai kwana ko bakya so.
Iyayyena na fadin amma baku kyauta muna ba wanan abin ayisa a gama lafiya don Allah ke kuma Allah ya baki hakkuri ansan an maki laifi kiyi hakkuru haka muka gada mu mata.
Ina zagi take jefo masu suna jefa mata haka muka fito saida muka dawo part dina suke fadin ko yanzu mun manna mata haushi don mun barta da kamshi da zaisa ta tuna son mubi kujerun mun shafesu da kamshin hannuwan mu.
Ayi dai ba dadi har mahaifinta na fadin shi zaizo gidan wallahi in abin baiyi a bashi yarsa don bai daukan wullakanci.
Mata sukace ina ruwasa da zancen mata kuma tunda ita ta fara ai suka amsa mata adaiyi hakkuri komai zai wuce insha Allahu.
Duk da hakan saida ya kira ya Addel yana fada inda yake shiga ba nan yake fita ba shi bai daukan wullakanci don an mayar da yarsa bare za,ayo hayan yan iska suzo gidanta suna ci mata mutunci.
Wani abu ya farune Addel din ya tambayeshi wai kai baka ma san abinda ya faru ba ke nan sai yaji ya kashe wayan nan yabi wayan da kallon mamaki.
Basu bar gidan ba sai bayan magari ba suka kara gyara ko ina suka tafi sai mairo da anty hauwane suka rage suda mukw kud da kud dasu.
Bayan mum sallame sallah insha,ine anty hauwa ke fadin in tashi in watsa ruwa a jikina banki ba wanka nayi sosai dama ai ina jin hiransu don a gaba suke hiran mazajesu.
Koba wanan ba ai shekaru yakai nagane inda mata keda matsala da inda ya dace a kula dashi tare da taimakinsu na shirya tsab cikin wasu material masu taushi na dora da gyale sai kamshi ke tashi.
Tare da umar suka shigo falon a zatonsa kowa ya watse a lokacin saida yayi sallama yaji sun amsa suna mashi sannu da zuwa.
Au kuna ciki ashe mun dauka har kun tafi ashe kunanan suka gaidasu tare da mikawa mairo ledan ta shiga dasu daki umar din ke fadin ina amaryan tamune ?
Tana ciki yake fadin naso mu zauna dasu kafin in tafi ita da abokiyar zamanta akan a zauna lafiya don Allah da sauri mairo tace a,a kada ai hakan yanzu .
Don ba za,a kwashe da dadin raiba a karshe nan suke dan basu labarin abinda ya faru dazun da sauri yake fadin.
Wallahi a barshi kira min ita wanan indan mata nasiha don Allah ta kirani muka fito tare falon a nan na samesu muka dan gaisa dashi.
Yake fadin tau Amarya zance yau kanwar mu ko kuma madam din mu dukka dai kinci a yanzu kuma yanzu mun tashi ga yaya kawai mukamin namu ya zamo biyu a awajenki zuwa ukku don yanzu wani babban halaka kuma ya sake kulluwa a tsakani.
Nan ya fara muna nasiha akan aure da zaman mace fiye da daya a gida gaskiya shi din abokine na kwarai a wajen yaya gaskiya mum ke fadin yafi kwanta mata a rai cikin abokansa data sani.
Sai yanzu na gaskanta hakan ta wanan nasihan da yake muna inda suma su hauwa suka dora da nasu da suka iya sukai addua suka mike.
Har kofan part din muka rakasu inda mukai sallama suka tafi lokacin ya juyo yana fadin masha Allah muje ciki ko ya fada yana shafo fuskansa tare da riko min hannuwa a haka muka juya zuwa ciki.
Dan iska munafuki dama a matse yake da ita Aisha dake tsaye jikin taga ta fada tana jaye jikinta daga wajen a hankali.
Halima dake gefe tace banson ki da hakan don inkice duk motsinsu zaki sa ido zuciyanki ba zai huta ba kullum yanzu bari mu gani zai shigo nan ko shike nan saida safe kuma.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

6?? 9??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Ajiyan zuciya naji ya sauke tare da hankadoni nayo baya lokaci guda ina juyowa gareshi ido na zubawa yanayinsa na dan lokaci kafin na sauke da sauri ina kallon kasa.
A hankali naji ya kara mastowa gareni tare da hada goshinsa da nawa a hankali yana sauke ajiyab zuciya.
Kafin naji yana fadin Alhamdullahi mun godewa Allah daya tabbatar muna da hakan tsakanin mu ta hanyar halalliya a garemu sai ya kaiwa goshina kiss yana lumshe ido naji hannunsa saman bayana yana matseni a jikinsa.
Zainab nagaji yunwa nake ji ina son in watsa ruwa na huta hakana abinda ya fada ke nan a lokacin kamar rada a cikin kunnena.
Dagowa nayi na dan saci kallonsa yace yes wanka nake son yi kafin na danci wani abu a cikina tun safe rabona da saka abu a bakina koshi saida hjy Fattu ta tsureni suka barni na karya din.
Barin hada ma ruwan wanka na fada ina kokarin ya sakeni daga rikon da yai mjn din amma kuma naji kara matseni a jikinsa yakeyi kuma.
Wanan yasa na kallesa ya juya min idanu yana fadin banson kamahin nan naki ya fita a hancina yanzu kamshin ki yana rikitani sosai zainab duk lokacin dana shakeshi.
Uumm,humm wai Kamshi kuma na fada a lokacin daya sassauta rikon nawa ina kokarin jaye jikina daga nasa yakaiwa gishina kiss yana lumshe ido.
Na juya naji yana fadin wacan dakin zaki barmin don yafi zama a lungu sai kiyi amfani da wayan nan ukkun zasu isheki ai da sauri na dan juyo don jin abinda ya fasa din dakin na nufa yana a gyare tsab da komai a cikinsa.
Bandakin nashiga na hada mai ruwan na kara tsabtace wajen na fito na sameshi tsaye yana rage kaya kai duke nayi zuman fita daga dakin don ganin abinda yakeyi lokacin yake fadin.
Na dauka kece zaki min wankan ai tunda nagaji da yawa haka murmushi nayi na fita falon naje na dan zauna saida na kwantaci ya shiga bayin na koma dakin kayan daya cire ya zuba saman gado suna tsunce na bude wardrobe da niyar zubasu kayansa na gani a ciki jere wanda hakan ya bani mamaki sosai.
Watau dama dai ya shirya hakan ke nan kafin nazo gidan tsayawa nayi ina nazarin inda

69 / 105