Chapter 87 Reading DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc Arewa Novels

DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   87 / 105

258K to 261K   out of 313.1K words

abinci an kuma ce yaci sosai tace masha Allah haka muke son ji ai dama Allah ya tada kafada ya amsa da amin.
Tare da kalloni yace zainab yaya baya cin abincinne har yanzu sai anyi daga dashi nace nina rasa gane me yake damun yaron nan .
Mama tace halittansane hakan ku barshi idan ya kara girma zaici ai tunda anta bashi magani bai daina ba akwai irin hakan dama ai duk mace mai haihuwa tana haduwa da hakan wani lokaci.
Duk maganan nan idonsa yana a kaina yana kallona yaga yanayina ya kara fadin Rukky ta kiraki kuwa sun kira an basu daddy dazun sun gaisa anyi sa,a mun shiga lokacin.
Batako kirani ba na fada mamake fadin ba dai suna lafiya ba yace Alhamdullahi kyale yar nema ai rana mun hadu dasu hanya nake mata sheri.
Rukky taso kawai ta cazawa mutane kai nace sherin halimatuce fa ni dama ban yarda da sarkuwansu ba wallahi ai tun lokacin na rabasu fafir.
Inba tsiya ba da sheri Rukku sa,artace koni halimatu ta girma balle Rukky da take sakon haihuwa na wai da ita kuma ta koma ta dinke don komawa baya.
Nina rasa me iyayyen yarinyar nan suke jira da ita haka yace dogon buri ni dama sam yarinyar batai min ba don na fahinci munafukace tun farko.
Bari kaidai kowama ya fada ai amma naji ga kwanaki ana fadin wai ta samu miji a manufashi sai kuma naji shiru nace nima naji wanan zancen ai bayan auren rukky.
Ya mike yana fadin bari na dan kwanta zuwa yamma in shiga gida mu gaisa dasu har ya juya sai kuma ya juyo yana fadin wai ya kukayi da kawayen Aisha ce.
Shiru nayi kamar ban jishi ba lokacin naci gaba da ballewa yaron bottom din da nakeyi a lokacin yace bakiji bane lokacin na dago nace dashi wace Aisha wai ?
Kamar ya wace Aisha Aisha nawa muke da ita gidan nan Aisha dai ta part din can nace me kuwa ba ai komai ba na ina kokarin mikewa tsaye don daurewa yaron hannu.
Naji yace ya zakice ba ai komai ba bayan yanzu na fito asibiti takirani da ban dauka ba shine tayi min massage wai kawar ta ta kiraki suna fada maki maganan banza don Allah ince kiyi hakkuri.
Murmushi nayi na kalli mama nace kinji kissa ko mama Allah yasa a gaban mamane ai ina da shedan komai a nan nan mama ta fara sallati tana mayar masa da abinda ya faru har na fito da yaron na fara saka mai kaya a jikinsa.
Ba wata kawarta muryantace karara muna ji idan baka yarda ba ka kira aina ta sake maimaita maka kaji a bakinta idan nayi kari
Subbahanallahi haba mama akan me zan kira wata aina can gaki zaki fadi karyane akanta me tayi maki da zaki fadi karya akanta.
Nasan halinta yar iskace shiyasa nacewa mum a barta kawai banda ra,ayin irin halinta a rayuwana don ba dainawa zatayi ba.
Dole kubura tace haka malam tunda a gabana ma an fadi ta saka ka auri Abune dama don a kore ita wanan din kaga tana son ta wanke kantane ga mutane.
Inma wani ya saka har naji ina sha,awan auren zainab ai bai wuce ita Aishan ba tunda itace ta zargeni da zainab tana son ta bata min suna hakan kuma sai Allah ya mayar min dashi alheri.
Ni bata gabana donta sani na dade da rufe babinta a rayuwana abu dayane dai ta tsaya inda take iya shegenta taci riba don wurina kan ba riba idan tazo.
Ai Allah ma ya gyara zainab din ba mai irin rayuwan rigiman nan bace ita don ko dazun data kirata ni ta ban shawa amsan data bata cewa.
Allah dai ya dawo da ita lafiya ai tafi bukatan ta dawo dakinta ta huta zaman gidansu don zaman gida miji aishi yafi ga mace sai ya dan kalloni yaga reaction dina.
Gyarawa yaron fuska nayi ina fadin je ku gaisa da Daddy ya nufi wurinsa kai tsaye nan ya kamo hannun yaron yana fadin babana kokai fa dakaci abinci bakaji dadi ba.
Yayin da itako mama taci gaba da fadin fitina ai baya da kyau kinyi fitinan nan dai ba,a kulaki sai ki kama kanki mana a zauna lafiya.
Mama bata sanni bane ina daga mata kafane don yaya fitinan nan kowa ya iyasa ai duk abinda take ji take takama dashi kowa ya iyasa fa.
Abu dayane ban dauka ka fada mata duk ranan data kara zagan min iyayye ba zan kyaleta ba wallahi saidai duk abinda zai faru ranan zai faru.
Uban nata da take kirun yana da kudi yanzu ina kudin suke Allah ai ba ai masa alfahari balle tacewa wani wai dan tallaka bai iya samun waje ba.
Ita dame ubanta yafi naki bari yar iska zanyi maganinta ai saita raina kanta ni zatyiwa siyasa ke nan ga mutumin banza ta samu ko ?
Ya mike ya shiga jin yace zai dan huta yasa ban bisa ba lokacin ga kuma raina a bace yasa na kara sharesa kawai .
Tsab na shirya yarana don harsu zamuje ganin daddy da albishir yazo muna cewa daddy ya zauna da dare har anyi hira dashi.
Don haka muka fito muka rufe gida nayiwa aina sallama direct asibitin muka nufa kai tsaye inda na dauki baske din kayan abincin dana daho shi kuma yaya ya dauki yaran masu shab nono dukkansu biyu sai mama ta rike hannayen masu tafiyan.
Tun daga nisa na hangosu gaba daya sun zuba muna ido bandashi dana kula tunda ya hangomu ya tsiri wayan karya ya bada baya ta yadda ba zaici gaba da kallon mu din ba.
Daidai mun karasone wani nurse yazo ya karbi basket din a hannuna yana fadin a,a doctor ke da kanki da wanan kaya haka nace Awar aida ka barshi akwai nauyi fa yace waneni duk a kan idonsu.
Har yayi gaba ya juyo yana fadin number dakin da zaikai nace masa ehh lokacin na juyo ina gaidasu a cikin jam,i da ina wunin ku ?
Anty Nafisa kawai ta amsa min shiko yana ba yaya hannu mummy kuma tayi kicin kicin da fuska a lokacin kamar taga abin ki a gareta.
Yau dai tafi da gidanka kukayi ga baki daya nace sunzo duba jikin abokine suma hannu na mika na amsanwa yaya yaro guda ya miko min shi kafin na ji yanawa mummy ya jiki lokacin nima nace ya karfin jikin mummy ?
Da sauki zainab ta fada a darare nafisa tace jiya ai naso kiranki ki auna mata bp din ta a gani ko allura ta samu sai kuma tasha wani magani da kika taba bata shine ta mike.
Ayya jiya ko nashigo nan saidai ban jima ba na fita nace ta dinga sha akai akai don kariya daga haka na nufi hanyar ciki shima yaya ya biyoni muka jera.
Kagani da yaran nan yanzu jikokin mummy ne ka tsaya shiririta irin naka yanzu gasu don Allah gwanin sha,awa hakan yasa ya dan sha mur yana sauke idonsa kan yaran yace.
Ko yanzu ai ban debe rai ga yarana bane waya sani ko yadda ya kwace min ita haka ya kwace har da cikin gidana a jikinta dan iska kawai.
Dariya sosai nafisa ta kwashe dashi tana fadin kaji wani shirme don Allah ka taba ganin mace tayi ciki ba miji in ba shirmenka ba ?
Wai shirme don Allah ku rabani da sakarcin nan naku haka ya isa don Allah ku har kunga wani abin sha,awa anan ina dai sauri take ta cika masa gida da yaya haka dama .
Waye zai yarda da wanan shirmen haka mummy koma meye dai ai tadai samu shi gashi yaki zuciya har yanzu yayi auren shima ya dan zaburo a gani.
Yace ita matan nawa ina kika barta tana tafe a cikin satin nan insha Allahu zasuzo su diba jikin daddy da iyayyenta kafin ya kai karshe uwarta kara katseshi da fadin .
Karka soma ka kawo kafiran nan nan yanzu cikin wanan halin da ake ciki ku tsaya can kuyi tsiyar ku inda ba,a gani wa zaka jawowa abin kunya yanzu kuma ?
Abin kunya zata musulunta fa mummy na fada maki nace dakai dai kada suzo ko ban yarda ba kuma ka shirya kaje kaga yarinyar nan yar gidan hjy Amina da nace.
Wai zancen yana nan ne anty nafisa ta fada wanan idan ba haka nayi masa ba kinga yana da niyar maida kansa abin kwarai ne yanzu ka duba can ji yadda su daddy ku ke rugumar yaran nan kai hakan bai baka haushine wai kaiwa kanka fada ?
Mummy na fada maki indai wanan zancen ne a bari in nema da kaina amma hadin nan gaskiya ban faye sonsa ba aje a daukowa mutum wace ba choice dinsa ba.
Haka kace da wanda Alh yai maka a baya ai daga baya kazo kanawa mutane haukan cinzon yatsa wanan karon ba wasa a cikin zancena idan kana son mu gama lafiya da kai.
Juyawa yayi ba tare da yayi magana ba ya bude motar nafisa da ya mayar nasa yanzu ya shiga ya zauna kafin ya kurawa su babana da daddy ennugu dake wasa da yarana ido na dan lokaci yana ajiyan zuciya.
Zancesa da anty nafisa yake tunane bana uwar ba lalai da yanzu yaranan nasane duk ya tsaya rudan kansa ko yayane sai ya rama abinda Addel yai masa ya fada a fili.
Yana ci gaba da kiyasta mugun abu a zuciyar sa tunane kala barkatai yayi a wajen kafin su shigo mota ya jasu suka tafi ba tare da kowa yasan da tafiyansu ba a lokacin.
Ciki kuma mun samu daddy an zaunar dashi yana ganin mu ya dan sake murmushi tare da mika hannu wai zai dauki yarin dake hannuna a lokacin.
Nan su mum ke fadin yi ta kanka wanan zakaran turawan idan ka daukeshi ai kuna faduwa wajen nan ana dariya baidai magana amma yana murmushi idan anyi wani abin dariya a wajen.
Mun dan jima kafin mu yi sallama zamu tafi don lokacin kwanciyarsa yayi a lokacin mum tace zata bimu don ance su hjy sun tafi dama Hafiz ya kawosu tare kuma sun wuce sun barta a nan.
Au sun tafine yaya ya fada cikin mamaki mum din tace gashi ko daddy ku ya shigo yana fada dazun sun tafi tare muka fito da ita bayan mun kara yiwa daddy Allah ya kara sauki.
A hanya yake fadin mum wai meye matsalan taki motar ne tace tunda akai gyara shiru sai daga baya Alh ke fada min ai ya sayar dasu gaba daya to me zance kuma tunda ya sayar ?
Amma ai baki fada min ba mum ni kuma ba kula nake da hakan ba irin wanan yanzu ina dadi inma yanzu baki son driving ne sai a samo maki driver ai.
To naga ai dukan mune yanzu ke bukatan motan a gidan shiyasa nayi shiru yace mum yanzu idan zan saya maki abu sai ince saina sayawa wani mum ?
Yanzu fa mutanen nan sun koya min wayau ai sosai na daina hakan abinci kan nayi alkawarin wanan insha Allah amma bayan nan ba zance komai zan maki sai nayiwa wani ba a gidan.
Garama da muka hadu dama ina son ganin ku yara na tafe da zasu kula da yaran nan ita mamaku ta dawo gida hakana bauta ya isa kuma.
Ai kafin muyi magana mama tace na fada maki ina bauta ina samun ladan aure zaki kashe min kasuwa ai saidai yaran suzo na dubasu duka nikan a barni can yafi min zama gidan kun nan da girmana.
Lalai dai kam mama nima nafi bukatanki wajen mu don hankalina yafi kwanciya da hakan yaran suzo mama ai ga mama kusa ta saka masu ido tunda zainab zasu fara jerabawansu na karshene yanzu.
Mum tace ni me zance yanzu tunda wace nake nemanwa saukin tace ba haka ba yaran dai na nan zuwa akace cikin wanan satin insha Allahu.
Amma mum da naki ko wace zata dinga kama maki yan aiyuka na fada yace abinda nake tunane ke nan itako sai tace wani aiki gareni yanzu banda dan girkin Alh wani lokaci.
Mum duk da haka akwai su shara da wanke wake da dan wanki da yanzu ba sai kin zauna yinsu ba yanzu jikinku hutu yake son samu a dai barni don banyi da kowa ina son yaro a yanzu ba.
Ina zaune kalau zakuja min magana yaran nan yanzu da basujin magana irin naku nada inda na ajeki anan kike tsayawa baki dauko min maganan kowa ba har muka rabu lafiya dake.
To gasu Abba nan ai saisu koma ku zauna tare na fada cikin gatse tace ai suzo ina maraba dasu aida ace matane kan zan kwashesu mu zauna tarene.
Shidai yaya sai murmushi yakeyi kafin yace mum aikosu zasu rage maki son zaki samu abokan hira tace kona su sakani surutu ba.
A dai nemo yarinyar mum baga zainab nan ba saita dinga bibiya tana ganin abinda take da dai yarinya gara babba wace tasan ciwon kanta gidan nan namu baida dadi kun sani.
Gidan muka kawo yasa muka fita mun samu hafiz zaune saman mota yana waya ko kallon mu baiyi ba yama nuna baisan mun shigo ba shima yaya hakan yai masa ya kwashi iyalinsa muka shige cikin gida kai tsaye.
Mun jima a nan gidan wajen mum don na dafa abincin dare na saka a kula nan ma gidan mum mun danyi ciye ciye kafin ya dawo ya kwashemu zuwa gida.



ZAINAB IDRIS MAKAWA

DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

8?? 7??
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,


Tsaye yake dakinsa tun bayan shigansa dakin yana kai da komo tare da tunanen zuci akan me Addel zai dinga masa hakane ?
Ya gane yana hakane gareshi don kawai ya bata masa rai akan kuskurensa daya tabka a baya wanda da taimakon mummy sa dama kowa har hakan ya faru Addel yayi amfani da wanan daman ya aure masa mata.
Da ayanzu ta zamo madubin dubawa ga kowa a gidan a yadda ya kula kowa na girmama wa yan nan rai biyu a gidan ko basu kusa zaiji ana fadan wani kalma na yabo akansu ko a gabanshi.
Zai gwadawa Addel shi bai isa ba wallahi shida gidan ubansa yana son ya kawo masa gadara da isa hakan yasa ya kwashi fushin zuciya yayo waje a fusace ya tsaya a inda muka sameshi da farko.
Sai ga yaya din ya fito ya nufi mota da niyar shiga yaji yace dashi malam tunda nan ba gidan ubanka bane balle ka kama shigowa mutane gida kai tsaye yadda kaga dama daga yau ka daina shigowa kaje gidan naka uban idan akwashi ka zauna.
Bai dauka dashi yake ba hakan yasa bai damu da yajoba duk da zancen ya daki zuciyarshi a lokacin amma hakan bai daga masa hankali ba.
Sai yaji ya kara fadin haka kawai zaka dinga kwaso kafa don iskanci kana shigowa mutane gida a gadarance gida ba na ubanka ba ?
Lokacin ya juyo ya waiga yaga ba kowa a wajen sai shida shi yace kanka daya kuwa hafiz kaidawa ke magana haka wai ?
Kaina gomane kaji mena fada ai nace kada ka kara shigowa mutane gida haka idan ma uwarka kake son gani a sallamaka ita ta fita can wajen get ka ganta daga yau nayima iyaka da gidan nan.
Au Allah ko yau haukan daka shawo ke nan kuma kai yaushene wai zaka girma saboda Allah wanan rayuwan fa ba zai kaika ko ina ba hafiz .
Gara ka gyara tun wuri zaifi ma alheri da wanan rayuwan zubda mutunci da kakeyiwa kanka da iyayyeb mu haka ?
Meka dauki kankane wai ko kana ganin kafi wanine wai na fada maka kada ka sake shigowa gidan nan idan ka sake kuma zakaga matakin da zan dauka a kanka this is your last worning.
Ya daga kai ya dan dubi gidan yace dashi wanan ai gidan daddy ne ko ba gidan ka naje ba saika bari idan kaga kafata gidan ka zakai min worning.
Gidan daddy din gidan ubankane kaje gidan naka uban mana idan kana dashi amma ba nan ba kana daukan kanka wata tsiya har me ka zama kake ganin hakan kai ?
To aida sauki tunda dai ina da uban bakin ciki daya shine yau ace banda uba haka kuma saukin abin inda ubana yaje ai baiyi

87 / 105